repost page 1 asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu, mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ Bismillahi Rahmanu Rahiim GODIYA TA MUSAMMAN Ina mai miƙa godiya ta ga Allah Madaukakin Sarki, Mahalicci, Mai Rahama, Mai Jinƙai. Shi ne ya bani ikon rubuta wannan littafi, ya azurta ni da hikima da basira, ya kuma ba ni kwanciyar hankali da natsuwa har na iya kaiwa ga wannan matsayi. Ina roƙonSa cikin rahamarSa da girmanSa, da ya ci gaba da tsare ni daga sharri, sharri daga mahassada, daga makirci, daga shaidan da kuma dukkan fitintinu na duniya da lahira. Allah Ka sa ni cikin kariyarka, Ka kare ni da wannan rubutun nawa, Ka kuma sa ya zama alheri a gare ni da duk mai karantawa. Godiya ga Manzon Rahma, Annabi Muhammadu (SAW), wanda shi ne mafificin abin koyi, mai cika da hikima da adalci. Allah Ka kara masa salati da aminci har abada. GODIYATA GA IYAYENA, 'YAN UWANA, ABOKAN ARZIKI, DA MASOYANA Ina miƙa godiya ta musamman ga iyayena masu daraja ku ne ginshiƙina na rayuwa. Kun raine ni cikin ƙauna, kun bani tarbiyya da kulawa har na kai ga wannan matakin. Allah ya saka muku da mafificin lada, ya tsawaita rayuwarku cikin ƙoshin lafiya da nutsuwa. Ya gafarta muku dukkan kura-kuranku, ya albarkaci zuri’a da al’amuranku. Amin. Ga ‘yan uwana na jini kun kasance tare da ni a lokutan farin ciki da bakin ciki. Ina godiya da ƙaunarku da haɗin kan da kuke bani. Allah ya daɗa haɗa zukatanmu da soyayya da fahimta, ya wanke zukatanmu daga hassada da ƙiyayya, ya sa mu haɗu da juna a Aljannah. Abokan arzikina da dukkan masoyana ba zan iya ƙirga irin goyon bayan da kuka bani ba. Da addu’arku, da karfafa gwiwa, da kulawa. Ina roƙon Allah ya biya muku buƙatunku na alheri, ya tsaida ku a kan hanya madaidaiciya, ya ƙara muku daraja a duniya da lahira. Kowa da kowa da ya taɓa zama silar kwanciyar hankalina ko ci gaban rayuwata ku sani, kuna cikin addu’ata kullum. Allah ya ƙara mana soyayya da fahimta, ya kare mu daga fitina da sharri. Amin. SADAUKARWA Wannan littafi na musamman na sadaukarwa ne ga matasa da ’yan mata na wannan ƙasa mai albarka Najeriya. Ku ne gatanmu, ku ne makomar ƙasa. Ina roƙon Allah ya ba ku basira, juriyya, da jajircewa wajen cimma burin rayuwa cikin gaskiya, kamala, da tsoron Allah. Ga shuwagabannin mu, waɗanda ke da nauyin jagorantar al’umma cikin gaskiya da adalci wannan littafi yana mai tunatar da mu cewa jagoranci amana ne, kuma tarihinku zai ci gaba da rayuwa a zukatan jama’a muddin duniya na numfashi. Ina fatan wannan littafi zai zama tamkar haske mai haskaka zukata, ya zaburar da masu karatu su yi rayuwa cikin nagarta, tsantseni da tunani mai zurfi. Allah ya sa wannan rubutu ya zama sanadin canji mai kyau a zukatan al’umma. Amin.... BOOK ONE page 1 to 2 ______________________________________ 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Kullum da safe Amal tana fita wurin aiki da tsohuwar rigar ƴan jarida da take alfahari da ita, duk da cewa ta daɗe tana amfani da ita.. Zata fita cikin murmushi tana yi wa Inna fatan alkhairi cikin ƙwanciyar hankali tare faɗin “Inna, ki yi min addu’a yau ma dai kada wata tambaya ta fi karfina.” Inna kuwa ba ta taɓa gajiya da addu’a ba ta ce “Allah ya taimake ki Amal, ki yi ƙoƙari kamar kullum.”.. Amal, wacce ake ƙira da "Amal Voice" a kafafen sada zumunta, ta shahara da muryarta a tashar RAYUWA FM. Kowanne lokaci idan ta fara shirin “Labari da Muryar Rai”, gari kan lafa, motoci kan tsaya, kowa kan ji daɗin muryarta mai sanyaya zuciya. A Instagram da TikTok, shafin ta ya cika da shahararrun faifan bidiyo, inda take bayar da labaran soyayya, dariya da tausayi. Idan ta yi dariya, sai zuciyar masu saurare ta natsu, idan ta yi kuka cikin labarin, mutane kan ji kamar su ma su zubar da ƙwalla. Duk da shahararta, Amal tana rayuwa a gidan laka tare da Kakar ta, Inna, wacce ke tsananin ƙaunar ta. Albashin Amal bai fi dubu ashirin ba a wata, amma bata taɓa ƙorafi ba, tana son aikin ta, kuma tana ganin ba komai ne a rayuwa kan zama silar farin cikin wasu ba.. ★★★★★ ...Wata rana a cikin babban falon sa mai ƙayatarwa da shimfiɗar furanni na ƙasar waje, Maleekh Cashbank hamshaƙin saurayin nan da ke tafiya akan iska irin ta masu kuɗi yana zaune yana shan coffee, yana busar hayaƙin shisha kamar wanda ke ƙoƙarin goge ƙiyayya daga zuciyar sa, Fuskar sa a ɗaure kamar bai taɓa yin dariya ba tun da aka haife shi. A gefe escort ɗin sa tsaye tamkar dutse, baya motsi kamar wanda aka shuka don kare masa kwanciyar hankali, sai kawai TV ɗin da ke gefe ya ƙara sauti da kansa, kamar yana da ikon sanin lokacin da wani abu zai ja hankalin mai kallon sa. A cikin TV: Amal sanye da rigar journalist, tana zaune cikin nutsuwa a cikin gidan rediyon RAYUWA FM, tana gabatar da shirin tattaunawa mai taken “Girman kai..." Muryarta ne ya shiga kunnuwansa kamar ƙaran sauti daga wata duniya. kalamanta suna da nauyi da natsuwa, tana faɗan maganganun da babu wanda ke iya furtawa cikin rashin tsoro, bata jin tsoron kowa, bata nemi jin daɗi daga wurin kowa ba. Maleekh yana zauna ya kafe TV da ido, fuskarsa ɗauke da alamun mamaki duk da bai bar zuƙar shishar ba. A TV da internet da labarai, kowa ya fara magana akan Amal. Shafukan sada zumunta sun cika da faifan bidiyonta. An fara rubuce-rubuce masu taken: “Wacece Amal Voice?” “Muryar Kaduna da ta girgiza girman kai.” Maleekh ɗaukar wayarsa ya yi yana magana da ƙarfi kamar wanda bashi da lokacin komai yana faɗin “Akwai wata yarinya a Nigeria, garin Kaduna. Sunanta Amal. Tana aiki a wani gidan rediyo, RAYUWA FM. Inaso ka nemomin bayanenta. Ina so in san komai game da ita, asalinta, rayuwarta, da dalilin da yasa mutane ke yawan magana akanta.” Fuskar Maleekh ba ta sauya ba ko ɗigon dariya babu. Yana ɗaure da fuska kamar dutsen da aka ajiye a rana. yana tunanin cewa wata 'yar talakawa na ƙasar da ya baro, tana iya maganar da zata ja hankalin duniya?. Amal bata san cewa yanzu haka wani idanun duniya na kallon ta ba. Kuma Maleek ba irin mazan da ake wasa da su bane. Ya shirya domin jin meye sirrin Amal, sannan ya tabbatar mata cewa girman kai ba laifi bane idan ka san darajarka.... Washegari da safe......... Cikin ofishin Maleekh Cashbank dake England, babban ofishi komai a tsare sai ƙamshi da shishar hayaƙi da ke cika dakin. Maleekh yana zaune, yana duba laptop ɗinsa, fuska ɗaure kamar wani shugaban ƙasa. Kamar bai taɓa kallon kowa ba, kamar duniyar gaba ɗaya tana ƙasansa. Security yana tsaye cikin ladabi, hannuwansa a gaba Ya ce "Sir... na kammala binciken kamar yadda ka umarta.".. Maleekh ba tare da ya ɗago ba, yana zuƙan shisha tare da latsar mouse ya jinjina kai ba tare da ya furta komai ba... Security ya ci gaba da cewa: "Sunan ta Amal Abdulsamaad. Tana matakin Diploma. Tana zaune da Kakarta a wani yankin talakawa. Ba su da wani gata ko arziki, sai ilimi da basira. An ce yarinyar bata jure raini, amma tana iya sarrafa magana mai ƙayatarwa. Wayayyiya ce, sai dai..." Maleekh ne ya ɗaga masa hannu, tare da katse shi, muryarsa cikin ƙarfin izza Ya ce "Stop right there! Kai, dallah dakata! Bance ka kawo min yabon ta ba. Domin ba ita nake buƙata ba. Ka samu number gidan rediyon su?" Security yana dukar da kai cikin girmamawa Ya ce "Na samu, sir....." Maleekh ya ja tsaki tare da ɗora kafar hagu akan dama Ya ce: "Inaso in tattauna da ita... a cikin gidan rediyo... ta hanyar voice call, yanda kowa zai ji. Ba sirri bane saboda bata kai matsayin da zan ɓoye maganata da ita ba." Maleekh ya ɗau wayarsa, ya jefa wa security Ya ce "Ka ƙira min su yanzu." [RAYUWA FM Kaduna, Nigeria] Amal tana zaune a cikin studio, ta gama karanta wani rubutu akan gaskiya da mutunci, muryarta cike da natsuwa, tana tafe da lafazi mai daɗi.. Sai aka katsar da ita tare da nuna mata ƙira daga waje. Producer ne ya girgiza kai yana faɗin: “international call.” Amal ta ɗaga ƙiran da murya mai taushi Ta ce: "Hello, wa ke kan layi? Fatan mai sauraro yana jin mu lafiya?" Shiru akayi ba tare da an furta komai ba sai da aka ɗau tsawon mintuna biyu kafin muryar Maleekh ta bayyana cikin izza, babu girmamawa, kamar yana magana da ƙasa ba mutum ba, kamar bazai yi magana ba ya furta: "Amal Abdulsamaad, ko ke ce? ki saurara da kyau, kada ki katse ni, ba wai ina son jin tarihin ki bane ko jin daɗin muryarki, ina da tambaya guda ɗaya." Amal ta ɗan yi shiru sannan ta dai daita murya cikin nutsuwa Ta ce "To, ina sauraron ka, amma a nan tashar muke, abin da za ka faɗa zai shiga kunnuwan jama'a." Maleekh cikin murya mai sanyi da tsawa ya furta “Ke ƙaramar yar jarida ce… kina magana akan girman kai? kin taɓa sanin me ake nufi da asalin darajar mutum kuwa? ko dai kina magana ne saboda baki da komai?” [Live broadcast ke gudana... kowa a Kaduna yana sauraron su...] A cikin studio, Amal ta zaro ido na ɗan wani lokaci. Sai da ta yi shiru kamar mai nazarin wani abu kafin ta gyara zama, ta dai daita mic, ta fara magana a hankali cikin fara’a da natsuwa, muryarta na kaɗawa cikin ilimi da wayo... Ta ce: "Tambayar ka mai ƙayatarwa ce, kuma na gode da samun damar jin irin wannan ra’ayi daga wurinka." Tana ɗan murmushi cikin nutsuwa, muryarta na kwarara kamar ruwan sanyi akan dutse mai zafi, ta kuma cewa "Ina ganin girman kai abu ne mai faɗi sosai, idan mutum ya san darajarsa, ya mutunta kansa, yana kare mutuncinsa wannan ana ƙiran sa ne da kamala. Amma idan girman kai ya hana ka ganin kowa, ya hana ka sauraron gaskiya daga bakin talaka, ya hana zuciyarka karɓar nasiha daga inda baka zata ba to wannan ba girman kai ba ne, hakan rashin fahimta ne da kuma tsoron gaskiya. Mutane da yawa suna ɓoye rauni da fushinsu a ƙarƙashin girman kai. Amma zuciyar da take da hankali tana karɓar gaskiya ko daga bakin mahaukaci ne...." *Reaction daga sauraro a garin Kaduna, har da online comments* “Kai amma yarinyar nan Amal wayayyiya ce gaskiya. Ta ba shi amsa cikin nutsuwa!” “Wai wanene wannan mutumin da yake nuna raini haka?” “Kalli yadda ta yi magana cikin ladabi da kuma hikima! Lallai Amal Voice!” Duk waɗannan maganganun mabiyan bayan Amal Voice ne ke mita akai, sai kuma Online Comments da suke ta shigo wa, kowa da maganar da yake tofawa..... A cikin ofishin Maleekh a England Maleekh yana kallonta ta cikin laptop ya yin da suke voice call, yana sauraron amsar ta, ya ja dogon numfashi, wannan karon ya tsaya bai ce komai ba, fuskar sa ta nuna kamar wani abu ya tsaya masa a zuciya, amma saboda nuna ƙwarewar sa ya buƙaci ƙara turowa da wata magana. Maleekh Ya ce: "Kina magana kamar wacce kika kware, amma ai ilimi da bakin magana ba su isa su sauya duniya ba, Ke fa ƴar talakawa ce, Ina ke, ina mafita?" Amal, ba tare da ɓata lokaci ba, ta amsa cikin kulawa tare da faɗin "Ni ƴar talakawa ce, hakane. Amma talauci ba cuta ba ne, kuma mafita ba a cikin kuɗi kawai take ba, akwai waɗanda suke da dukiya amma basu da kwanciyar hankali, akwai wanda yake da iyakar ilimi, amma baya jin daɗin zaman duniya. Ni bana so in sauya duniya, amma ina so in fara da mutum ɗaya wanda zai saurari muryar gaskiya ba tare da tambayar daga inda ta fito ba." [More Comments from listeners] “Ina ma ace duk ƴan Najeriya suna da nutsuwar Amal.” “Kamar dai wannan mutumin yana jin wani abu a zuciyar sa yanzu…” “Gaskiya wannan mutumin ya shiga uku… Amal dai bata da sauƙi amma tana da mutunci.” ★ Maleekh shiru ya yi na wasu sakanni tare da lumshe ido sannan Ya ce "Ke fa kina magana akan girman kai, amma kin san ma’anarsa kuwa? Ko kina faɗa ne kawai dan baki taɓa sanin matsayin da zai sa mutum ya yi girman kai ba?" Amal ba tare da fargaba ko tsoro ba cikin nutsuwa ta ce “Girman kai ba ya auna kuɗi ko motar da kake hawa. Girman kai na gaske shi ne lokacin da kake girmama kowa, koda kuwa kana da ikon wulakanta shi, kai dai kana da kuɗi, amma daraja? Hakan akwai bambanci.” Shiru ya yi, saboda kalamanta sun yi masa nauyi fiye da duk wani kuɗi da ke cikin aljihunsa. A fusace ya kashe ƙiran.. Security na gefe na kallon sa ba tare da ya ce komai ba. Security a hankali ya furta "Sir, should I follow up?" Maleekh ba tare da ya kalli yanda yake ba, ya furta a hankali: "Kar a sake min magana da ita... amma ku cigaba da sauraron shirin ta... kullum."....... Asmeetah writer ✍️ *TAƘABBALALLAHU MINNA WA MINKUM...* *EID MUBARAK KHARIM....* *INA YIWA ƳAN UWANA BARKA DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA🙏🙏🙏* *WANNAN FARKON PAGE ƊIN LITTAFIN AMALEEK SHINE BARKA DA SALLAH NA, UNSUSPECTING NEW BOOK ON FRIDAY....* *The Eid al-Adha Prayer for Animal Sacrifice in the Year 2025*..... asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ __BOOK ONE___page__3 to 4_______________________ 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 A daren nan bayan Amal ta gama aiki, ta koma gida... cikin ƙanƙanin lokaci Kaduna ta ɗauki zafi da magana game da tattaunawarta da wani mutumin England da bai bayyana sunansa ba, sai dai magana ta yaɗu sosai, ta fara zama trending a X, Instagram, da Facebook... A gida, gidan laka, cikin ɗaki mai ɗauke da ƙamshin turare... Amal ta shiga ciki tare da cire hijab, ta zauna a gaban Inna da take ta yankan alayyahu, Inna cike da jin daɗi take faɗin "Yau kin ƙara burge ni Amal, ai har ni da na ke nan na tsaya na saurari tattaunawarki da mutumin England, ina tunanin cewa da gaske wannan yarinyar da ke maganar ce jikata? ina mai ƙara alfahari da ke Amatullah..." Inna tana murmushi da kwarjininta na dattijai.... Amal ta kwantar da kanta akan cinyar Inna, cikin nuna gajiya Ta ce: "Inna, dole idan kana irin wannan aiki ka samu maƙiya, wasu ba don su fahimce ka suke saurare ba, sai don suna neman wata hanya su durƙusad da kai." Inna Ta ce: "Na san haka... kuma kin yi magana cikin hankali, da kuma Allah ya baki hikima, baki mayar masa da martani ta yanda ya zo miki ba, da kin biye masa da mutane sun ga rashin tarbiyyar ki...." Amal ta murmusa da jin wani ƙarfin gwiwa Ta ce: "Amma Inna kin ji irin muryar sa? wani irin girman kai ne da shi, kamar shi kaɗai ya ke da kuɗin duniya... yana so ya ƙaskantar da ni a idon masu sauraro, amma gaskiya da taimakon Allah na cinye wannan jarabawar...." Inna ta dafa kafaɗarta a hankali Ta ce: "Amal, idan Allah yana tare da ke babu wanda zai iya hana ki kai matsayinki, sai dai kiyi addua, kuma kar ki bari wannan abu ya rikita miki zuciya, shi da kansa zai dawo da hannu biyu yana roƙon ki, idan bai bayyana a fili ba to zai bayyana a ɓoye...." Meanwhile a England... Maleekh ya na zaune yana kallon clip ɗin hirar da aka yanke a social media wani video ne da aka ɗora: "WACE CE AMAL? WATA ƴAR NIGERIA TA BA WA HAMSHAƘIN MAI KUƊI AMSA CIKIN HIKIMA!" yanda ake ta comment “Kalli wannan yarinyar da ta girgiza wani saurayi mai ji da kansa a rediyo!” #AmalVoice #KadunaPride #WisdomNotWealth Maleekh ya matse bakinsa. ya ƙura wa allon laptop ido ba tare da ya motsa ba, sai dai yana jin kamar wata ƙaramar guguwa tana ɗan kaɗawa a cikin zuciyarsa... RAYUWA FM. Amal on Air Amal a wurin aikin ta. Sauti ya cika ɗakin rediyo. Murya ce mai raunana zuciya cike da karyewar rai da hawaye da ke kunno kai daga karshen ma'koshi. Amal tana kan microphone, hannunta na girgiza, idonta cike da hawaye amma zuciyarta ɗauke da ƙwarin gwiwa. Amal cikin sassanyar murya da tausayawa ta furta “Yau labari zan bayar, ba don na gigita ku ba, sai don zuciyarmu ta koyi darasi. Wannan labarin na Hadiza da Fahad ne. Masoya ne, ba don kuɗi suke son juna ba, ba kuma don nasaba da cancanta ba ko shahara, sai don zuciya, zuciya mai gaskiya, zuciya mai tsarki.” Amal ta lumshe ido tana jan numfashi da kyar, kamar tana kallon su a gabanta Her voice trembling with emotion. Anan ta bada labarin wasu masoya biyu waɗanda aka kashe su ba tare da sun ci hakkin kowa ba, kuma har ila yau an kasa ɗaukan mataki akai... Ta kawo ƙarshen labarin cikin harshen turanci.. Amal ta share hawayen ta da tissue, tana matuƙar kame kanta, tana kuka, ta kammala bada labarin masoya biyu kuma Aminan ta... Ta kuma cewa. “Rest well, Hadiza and Fahad. The world failed you but history will remember your truth.” Sautin slow instrumental piano ya shiga a bayyane yayin da kukan jama'a ke tashi a comments da wayoyi da messages da ke shigowa kai tsaye a tashar RAYUWAR FM. England Maleekh’s Private Apartment Maleekh yana zaune a kan white leather couch ɗinsa, sanye da 3-quarter da singlet, ƙafa ɗaya a ɗore kan ɗaya, hannunsa yana riƙe da remote amma idanuwansa ba sa ko motsi daga laptop ɗin gaban sa, Amal ce akan Screen ɗin laptop cike da hikima, da harshen turanci mai girgiza zuciya, tana kuka tana magana... Maleekh tsaki ya ja cikin jin haushin Amal, ya furta: "Look at her... What kind of manipulation is this? So this is the game now? Make the world cry so they forget your status?" Ya miƙe tsaye ƙirar jikinsa kamar basamude domin ko ina a jikinsa a cike yake, full built, jikinsa fari tas kamar madara, yana motsa kai kamar wanda ke buƙatar tashi daga wani irin mafarki... Maleekh yana son kashe laptop amma ya kasa, tsayar da hand ɗin sa ya yi ba tare da ya motsa ba, fuska a yamutse, gira a haɗe sai faman huci yake, cikin muryar tsawa yake faɗin: "This is nonsense, absolute nonsense, Why... why is she still echoing in my head?" Ya sunkuyar da kansa yana hargutsa gashin kansa da hannu daya, ya girgiza kai a hankali yana magana kamar yana ƙoƙarin tsoratar da zuciyarsa Ya ce: "She's nothing, Just a radio girl, A local girl, A nobody. How dare she touch the part of me I buried years ago?" Kwantar da kansa ya yi a jikin bango, yana numfashi da ƙarfi, ba tare da ya san me ke tafiya a ransa ba, ya tuna kalmomin Amal da take cewa “You are heard, you deserve better...” Wani abu yana girgiza a cikin zuciyarsa... Amma Maleekh ya ƙi amincewa da cewa wani abu daga maganganunta ya taɓa wani yanki a zuciyar sa.. Yayin da labarin Amal ke ƙara karɓuwa a faɗin ƙasar, wani fitaccen dan jarida mai suna Rikky Blaze, wanda ke da shahararren podcast ɗin “Nigerian Voices Unfiltered”, ya kalli clip din Amal daga RAYUWA FM. Hankalinsa ya koma kanta nan take. Rikky Blaze yana magana da PA ɗinsa cewa: “Wannan yarinyar... Amal... tana da murya, tana da harshe mai daɗin saurare, she speaks from pain and depth. I want her on the next episode! live from Abuja! Arrange it, komai da komai, tikitin jirgi, hotel, VIP treatment. Kaduna is too small for that kind of voice.” Da daddare Amal na zaune tana karanta littafin journalism cikin fitilar lantarki mai launi, Inna na kan sallaya tana jan carbi, wayar Amal ne ya yi ƙara saƙon email ya iso... Amal cike da mamaki ta ce: “Inna... kinga sun ce wani shahararren podcast daga Abuja yana so in zo tattaunawa kai tsaye, sun ce ba tare da na kashe kuɗina ba, hatta jirgi da hotel sun riga sun shirya komai...” Inna ta ɗaga gira tare da faɗin: “Lah! To wa ke bibiyar ki haka Amal? Ai wannan... akwai ƙalubale a cikin sa in har zaki fara zuwa garuruwa ke ba ƴar kowa ba, amma idan da gaske ne kuma halal ne Allah ya buɗa miki.” Amal ta riƙe hannun Inna da murmushin dole ta ce: “Inna, wallahi ban san ko me yasa mutane ke bani kulawa haka ba... amma dole ne idan kana irin wannan aiki, ka sa rai da farin ciki yana iya janyo kishi da ƙiyayya.” ♡♡♡ ♡♡ ♡ Maleekh yana duba social media sai poster ya bayyana a fuskar laptop ɗinsa an rubuta: “Coming Up: AMAL ABDULSAMAAD The Voice Behind Kaduna’s Radio Gold, Live on Nigerian Voices Podcast with Rikky Blaze!” Maleekh ya tsayar da numfashi, a cikin ransa yake faɗin: “So... she’s really trending now? Abuja? Seriously? wannan ƴar talakawan yarinya ta kai wannan mataki? Nigeria really is upside down, but let’s see... let’s see how far she can go.” Ya janyo wayarsa tare da ƙiran ɗaya daga cikin abokan cinikinsa a Abuja... yana shirin tura mutum don ganawa da Rikky Blaze... ♡♡♡ ♡♡ ♡ AMAL A AIRPORT ZUWA ABUJA Amal na sanye da doguwar riga da ƴar hijabin ta marar nauyi tana lanƙaye da jakar ta, Mutane da dama na kallonta a harabar jirgi suna murmushi. Yaran wasu ma na cewa: “Mama kinga Aunty Amal ta cikin rediyo!” Amal ta ce a zuciyarta “Duniya kenan... tun da na fara aiki a ƙaramin gidan rediyo, ban taɓa tunanin har podcast na ƙasa zai gayyace ni ba, amma wallahi zan tsaya akan gaskiya, ba zan canza wa kaina ba.” Wasu zafafan motoci ne suka zo ɗaukan ta, kai tsaye babban hotel na masu kuɗi aka kaita, yanda aka tanadar mata da komai... Bayan ta ci ta sha tayi wanka tare da tsayar da sallah ta huta cikin kwanciyar hankali har bacci ya ɗauke ta, ga sanyin A.C na ratsa ta kamar ba'a duniya take ba, ita kanta tasan ta shigo duniyar masu kuɗi, Washegari da safe ta kammala shirin ta tsaff, already motar na jiran ta a compound na hotel zasu je wurin da za'a gudanar da shiri.... THE NIGERIAN VOICES PODCAST" Amal ta tsaya a gaban duniya, domin a wurare da dama ana kallon tattaunawar da zasu gudanar... Abuja, babban studio na Rikky Blaze. Amal na zaune a gaban mics guda biyu, sanye take da rigar abaya da gyalenta marar nauyi, Rikky ya zuba mata ido cikin girmamawa yana murmushi, gyaran murya ya yi tare da faɗin “Ladies and gentlemen, today we have with us a very special guest, she may not have a mansion, or billions in her bank account, but her voice has broken down walls and reached the souls of thousands. Amal Abdulsamaad welcome to Nigerian Voices.” Amal cikin nutsuwa ta furta: “Thank you very much, Mr. Blaze, It’s an honour to be here. And I speak not with power, but with pain because pain is universal.” Rikky ya gyara zama sannan Ya ce: "Akwai lokacin da kika ce, "Idan har ya zama dole ne sai ka cutar da wani, to kar ya zamana ka cutar da wanda ya taɓa ƙaunarka’ wannan magana ta bazu sosai a duniya.... Daga ina kika samo ta?" Amal ta ɗan gyara zamanta, ta kalli mic cikin sassanyar murya ta ce: "Na samo ta ne daga ganin mutanen da suke shan wahala a asirance, na taɓa yin hira da wata yarinya da aka kashe mijinta saboda ya kare ta daga ‘yan ƙungiyar asiri, ba ta kai wa kowa kukan ta ba… sai dai kawai ta zuba ido, kuma hakan ya karya zuciyata. Ba kowace zafi ke yin ihu ba, Malam Blaze… wasu dai suna nan kawai… suna jiran a ji yo kukan su...." Wannan maganar ta saka ɗakin yin shiru, har cameraman ya tsaya yana kallon ta. Rikky cikin nutsuwa Ya ce: “You don’t speak, you cut. But in a good way like surgery.” Amal ta murmusa kaɗan, idanunta sun kaɗa da ƙwalla, tayi gaggawar kawar da kai ta tsaya cikin ƙarfin hali. Ta ce: “I’ve seen people mock the poor... I’ve seen people say, your background is your curse But wallahi, Mafi ƙarfafa mutane da na taɓa haɗuwa da su, su ne waɗanda ba su da wani ginshiƙi sai Allah kaɗai, kuma ina magana ne a madadinsu.” ♡♡♡ ♡♡ ♡ Maleekh na zaune kan sofa, yana kallon wani big screen, amma ba podcast ba yana duba data a kasuwancin sa. A gefe guda kuma laptop ɗinsa na nuna thumbnail ɗin Amal a podcast amma bashi da lokacin duba ta... Maleekh yana maganar zuci.. “Tunanin ta ya isa haka, i don’t need this noise, there are millions like her why should i care?” ɗaukan remote ya yi yana shirin kashe screen ɗin gaba ɗaya, amma kafin ya kashe, yana ganin Amal cikin nutsuwa tana faɗin “Muna tashi ne ta hanyar ɗaga waɗanda ke ƙasa da mu…” Maleekh jan tsaki ya yi yana faɗin: “Ƴar talakawa kawai, ƙaramin abu ya dameta, kuma yanzu kowa na wahalar da kai wurin sauraron maganarta.” Ya ɗauki wayarsa ya ƙira PA ɗinsa, bugu ɗaya aka ɗauka, Maleekh Ya ce: “Tell Alhaji Dikko in Abuja he should handle that oil deal directly. And tell him to stop this social media buzz about any radio girl. I’m not interested.” Recording Amal da Rikky ya janyo tasiri har zuwa duniyar siyasa, sannan wata kafar TV ta Abuja tana neman ta zama host ɗinta, lamarin da ya tayar da hankali a RAYUWA FM. 🌍🎙️ A cikin maganganunta ta sako har da ƴan siyasa, duk wata gaskiyan da suke ɓoyewa tana shirin binciko wa, tana ƙaryata maganganun su akan talakawa na cewa zasu taimake su nan kuma cin amana ne da kuma yaudara, truth out maganganun ta akan siyasa ta yi su, kuma ta ba da isasshen lokaci..... THE ECHO OF TRUTH” LABARIN AMAL YA GIRGIZA MANYA A babban ofishin wani ɗan siyasa da ake zargi da cin hanci a Abuja, TV yana nuna podcast ɗin Rikky Blaze tare da Amal, wani babban hadimi yana kallon boss ɗinsa da fargaba Ya ce: “Sir… ina ganin wannan yarinyar za ta zama matsala, ta ambaci matsalar ƙarancin ruwa, har da adadin alkaluman da ka umarce ni in ɓoye.” Ɗan siyasan ya miƙe da sauri yana kaɗa hannu cikin zafin zuciya Ya ce: “Who gave her that data? Ta yaya ƴar gidan rediyo ta Kaduna ke da wannan cikakken bayani? Shut it down! Cancel the links, do damage control! I don’t want her voice on the internet again!” Hadimi Ya ce: “But sir... it’s already viral. The clip is trending on Twitter, YouTube, even BBC Africa quoted her...” Ɗan siyasan ya ɗaga hannu cikin tsawa yana faɗin: “To hell with BBC! If we don’t silence her now, she’ll open more cans we thought were buried, find out who trained her. And who she works for.”... Abuja TV Headquarters Bayan kwana biyu.. A cikin babban ɗakin taro da aka yi wa ado da fatauci da na’urorin zamani, Amal zaune ce a gaban babban kwamiti na Abuja TV. A gabanta akwai wata fitacciyar producer, Madam Ebun, mace mai lallausar murya da kuma cike da dabara. Madam Ebun cikin murmushi Ta ce: “Amal, your voice touches the soul, we are impressed, but on national TV, we don’t just speak we control narratives.” Amal ta ɗaure fuska tare da faɗin: “I control only the truth. Nothing more.” Wani daga cikin committee ya kalli wata takarda sannan Ya ce: “Kin ce Ministan Muhalli ya yi amfani da kuɗin ruwa wajen abin da bai dace ba, wannan magana ta yi haɗari da yawa, kin ƙira hakan cin amana ga yaran da ke cikin jin ƙishirwa, idan muka ɗauke ki aiki, muna son kauce wa maimaita irin wannan magana kai tsaye a fili.” Amal ta lumshe ido cikin nutsuwa Ta ce: “Abin da na faɗa ya fito ne daga rahoton da tashar ku ta yi watsi da shi If you’re scared of truth, then I’m not your girl.” Ɗakin yayi shiru kamar ba mutane. Amal ta miƙe, ta ɗauki jakarta tana shirin barin wajen, amma wani daga cikin Committee Member Ya ce: “Wait. Kina da jarumta, amma ki sani ƙin amincewa da mu yana nufin yanzu kin zama abin bibiya. ’Yan siyasa sun san sunanki yanzu. Ki yi hattara.” Amal Ta ce: “They should be careful too. I have a microphone.” ♡♡ ♡ England, Maleekh's Private Apartment Maleekh yana zaune a gaban babban taga yana kallon gari da motocin dake wuce wa, hannunsa na cikin gashinsa yana murɗawa cikin takaici, ya koma ya zauna kamar marar lafiya. A gefensa laptop na nuna headline: “Kaduna Girl With Radio Courage Lands Abuja TV Offer” Yayi tsaki, ya tura laptop ɗin gefe, ya miƙe yana shawagi cikin ɗakin da kayan alatu ke ko’ina, yana lumshe da idon da ke bayyana karfin hali da ƙiyayya. Maleekh yana zancen zuci yana faɗin : “Ajin me? Yarinyar da bata da kafa da tuta a rayuwa tana ƙoƙarin taka manya? wane irin raini ne wannan?” Ya ɗauki waya ya ƙira wani ɗan sanda dake aiki a Abuja. Maleekh Ya ce: “I need someone to pull her files, i don’t trust that girl, i want to know who is backing her or if she’s just another loud mouth.” Muryar ɗan sandan ne ya fito yana faɗin: “Sir, you want us to tail her?” Maleekh Ya ce: “No... Not yet. Let her shine small. But if she crosses me again, i will remind her that power... is not in the mic. It's in money.” Ya kashe wayar yana fitar da numfashi, amma wata kalma daga bakin Amal tana yawo a kunnen sa: “Gaskiya ba ta da albashi, amma tana biya da gadon suna bayan barinka duniya....” Maleekh ya ƙara jan tsaki yana faɗin: “Tsk! Yar talakawa da poetry…” ♡♡♡ Rayuwa FM, Kaduna... Amal ta dawo daga Abuja da takardun offer da ta samu, Babban producer tasharsu, Mr. Salis, ya ƙira ta ofishinsa. Amal bayan ta huta gajiyar ta a gida duk da jirgi ta shiga, daga baya ta amsa ƙiran Ogan ta dake gidan rediyo Rayuwa FM.. Gidan rediyo na RAYUWA FM, Amal na shigowa, fuskarta ɗauke da fara'a, tare da karfin zuciya. Babban editan tashar yana tsaye yana taya ta murnar dawowa.. Editor yana ƙoƙarin bayyanar da murmushin sa Ya ce: “Amal... welcome back. Yayi kyau. Amma akwai batun da zamu tattauna da gaggawa.” Amal ta tsaya, tana dubansa kai tsaye Ta ce: “Na san me kake nufi. Abuja TV sun aiko mun da offer. They want me to be their national youth host for a new program. They want truth and i have it.” Editor ya ɗan dafe goshinsa sannan Ya ce: “But this is RAYUWA FM, Amal. We trained you. We gave you the mic. Ba za mu iya kallon ki kina tafiye tafiye ba... and Abuja TV na da sauƙin sayar da ra’ayi you’ll be controlled.” Amal Ta ce: “But wallahi a nan ma ana ƙoƙarin dakatar da ni, i speak for the people ba wai domin na yi suna bane, Idan rayuwa zata zama cin hanci da gori, to ba zan ci albashi dubu ashirin haka nan ba...” Shiru ya biyo baya kamar an kunna recorder a zuciyar kowanne ma’aikaci. Amal ta bar wurin kai tsaye ofishin Mr Salis ta nufa daman shi ke neman ta, haka ta shiga office ba tare da jin komai ba, a zuciyarta tana tunani tare da maganar zuci: “If they want to fight me for speaking truth, I’ll still speak. One mic. One voice. Millions of hearts.” Murya cike da damuwa. Mr. Salis Ya ce: “Amal, muna farin ciki da irin cigaban ki. Amma… idan kika karɓi wannan offer, za ki fice daga Rayuwa FM ne....” Amal ta kalle shi kai tsaye tare da faɗin: “Na zata zaku yi alfahari da ni, ba ku ja ni ƙasa ba.” Mr. Salis Ya ce: “Wannan ba batun kishi bane, batun tsari ne. Gidan rediyo yana da policy idan an same ki da wata kafa na waje, sai an cire ki daga jerin ma’aikatan nan...” Amal cikin takaici ta furta: “To ni wallahi idan akwai inda zan iya faɗin gaskiya ba tare da an tsoratar da sunan gwamnati ba ni can zani.” Ta miƙe ta bar ofishin, a bakin ƙofa ma’aikata da yawa suna kallonta da mamaki da tausayawa, wasu na ta cewa “kada ki tafi Amal, kin fi ƙarfin Abuja TV su rufe ki da dokokin su...” Amma Amal bata tsaya ba. A zuciyarta murya ɗaya take faɗi: “Mic ɗina ba mallakin ku bane. Na talakawa ne.” Amal ta dawo gida daga aiki, fuskarta cike da gajiya da damuwa, bata tsaya ko'ina ba sai a ɗakin Inna, a zaune Inna take akan tabarma tana tsane ganye, Idonta ya sauƙa akan Amal da take ƙoƙarin boye damuwarta. Inna ta ɗaga ido cikin tausayawa Ta ce: “Amal, zo ki zauna mana, ki zauna nan gaban Inna, yau zaki saurari shawara, ko ba haka ba?” Amal ta zauna a gefen Inna kamar wata yarinya da aka kama da laifi, ta ɗaura hannu biyu a cinya, idanunta sun kaɗa da kwalla... Inna Ta ce: “Amal, ki dubi maraicinki ki zauna kiyi haƙuri, ki tuna ke ƴar talakawa ce, karki manta da asalinki, wannan Abuja da kike shirin komawa, meye a cikinta? Siyasa? Kuɗi? Ko alfahari?” Amal ta kalli Inna tana share hawaye, amma bata iya cewa komai ba. Inna ta cigaba da faɗin: “Masu kuɗi sun fi ki iko, a lokacin da kike haskawa, kowa zai dinga ƙiran sunanki, amma idan kika faɗi ƙasi wallahi babu wanda zai tsaya miki, su masu mulki sai sun ɓata miki suna, su wulakanta ki, su jefar da ke kamar marar daraja, bayan ke kaɗai kika rage mun, idan kika tafi Abuja, wa zai dinga kula da ni?” Amal ta fashe da kuka tana faɗin: “Inna...idan har bakya son na koma Abuja...zan haƙura. Wallahi zan zauna dake, zan ci gaba da aiki a Rayuwa FM.” Inna ta janyo Amal ta rungume ta tana share mata hawaye. Inna Ta ce: “Allah ya miki albarka, wallahi ban hanaki ci gaba da rayuwa ba, amma bana son ki afka cikin tarkon siyasa da haɗin kai da masu kuɗi, ki dage akan ilimi da gaskiya nan ma za’a gan ki.” RAYUWA FM.... Bayan kwana biyu Amal ta koma tashar Rayuwa FM da murmushi a fuska, kowa ya nuna farin ciki da dawowarta, shirin ta na yau ya kasance mai taken: “Kaunace ko Wulaƙanci?” Amal ta shiga studio cikin kwanciyar hankali, ta ajiye headset ɗinta, sannan ta fara magana cikin tausasawa: “Assalamu Alaikum wa rahmatullah masu sauraro na Rayuwa FM. Ina tare da ku ni ce Amal Abdulsamaad. A yau zan ɗan ba ku labari mai raɗaɗi labarin soyayya da ƙyama...” Ta ɗan yi shiru, tana murza idonta da tissue, muryarta na ɗan karyewa. Ta cigaba da cewa: “Wani saurayi da budurwa ɗalibai sun shafe shekaru uku cikin soyayya mai tsafta, basu da komai sai soyayya da girmama juna. Amma wata rana...an tarar da gawar su a cikin motarsu...an harbe su.” Daga nan muryarta ta shiga rawa sosai. Ta cigaba akan cewa: “Wai meyasa ƙiyayya take cin nasara akan soyayya? meyasa mutane basa jin zafin rasa wanda suke so? wannan duniya fa babu tabbas…” Idon Amal ya cika da kwalla, amma har yanzu kalmominta na fita cikin turanci mai hikima. Tana faɗin: “Matasa ne, talakawa, amma al’umma ta hana su damar rayuwa. Saboda kawai ba su da suna, ba su da kuɗi, ba su da iko… an kashe muryarsu.” Amal cikin kuka Ta ce: "May Allah grant them peace. Ameen." A lokacin da take magana, a can nesa a England, Maleekh na kwance kan gadon sa, yana sanye da 3quarter a jikinsa da singlet, laptop ɗinsa na nuna live stream na Rayuwa FM. ya harari screen ɗin yana tura keyboard da karfi. Ya ce: “Damn it! wannan yarinyar har yanzu tana da baki? ta ɗauki kanta kamar wacce tasan komai... Ƴar talakawa ke baƙin ciki da soyayya...” Yana buɗe wata folder a laptop ɗinsa wanda yake ɗauke da sunan: "CASH TALK FM PRIVATE." Maleekh yana murtuƙe fuska yana faɗin: “Zan janye ta daga Rayuwa FM... by force or by money... She will work for me. She must!” Sai ya ɗaga waya ya ƙira wani hadiminsa daga Abuja. Maleekh Ya ce “Hello!...Prepare the contract, i want Amal Abdulsamaad. She'll join us at CashTalk FM. Abuja is waiting...” Bayan Amal ta ci gaba da aikinta a Rayuwa FM, koda yake tana ƙunshe da damuwa a ranta sakamakon matsin lambar siyasa da kuma saƙonnin barazana da ake aiko mata daga Abuja TV. Duk da haka, ta cigaba da shigowa cikin shirye-shiryenta cikin ƙwazo, musamman shirin “Ra’ayinka Hakkinka” inda take ba mutane dama su bayyana damuwarsu game da rayuwa da halin ƙasar. Sai dai, bayan kowanne shiri, Amal ta fi zama shiru a cikin office. A zuciyarta tana jin kamar tana yaƙi ne da manyan da ke son murƙushe ta, amma shawarwarin Inna kullum su ke kwantar mata da hankali: "Ki tsaya da ƙafafunki, Amal. Talaka baya rasa daraja idan har yana da gaskiya da himma." A Ƙasashen Waje A can England, Maleekh Cashbank ya gama tsara duk wata hanya da zai jawo Amal zuwa sabuwar tashar sa, CashTalk FM. Amma ba don yana sha’awar ta ba, A'a, yana so ne ya mallake ta da kuɗi, ya ɗorata a ƙarƙashin ikonsa, domin ta yi masa mummunan rauni a gaban duniya. Yana zaune cikin ɗakin sa na musamman, yana duba zafafan shirye-shiryen Amal da ke ta yawo a social media, yana wani tsaki da cizon yatsa. Kallonsa ya koma sama, ya furta: "Ƴar talakawa ce fa! Me yasa nake jin kamar maganganunta suna shiga jikina? wannan wulakancin da ta min ta rediyo sai na rama shi a duniya." Ya buga laptop ɗinsa da ƙarfin zuciya, yana ƙara hura hayaƙin shisha... Location: Kaduna... Amal ta samu wani ƙira daga wata baƙuwar lamba a cikin mako, tana ɗagawa sai wata murya ta ce: "Miss Amal, muna so mu tattauna da ke akan wata sabuwar dama a tashar rediyo, muna neman fitattun muryoyi masu rinjayar jama’a." Amal Ta ce: “Waye ke magana? Kuma wace tasha ce?” Other site: “Zaki ji komai idan kika zo Abuja, muna fatan zaki ɗauki wannan damar da gaske.” Amal ta amsa cikin ladabi amma a zuciyarta ta ƙuduri aniyar ba zata sake barin Rayuwa FM ba.... ★★★ Maleekh ya aika da tawagarsa ta PR su je Kaduna a asirance domin su fara tattara duk wata dama da zata iya kawo Amal zuwa CashTalk FM. Ba don yana buƙatar taimakonta ba, sai don ya wulakanta ta ya nuna mata duk ilimin ta da basirar ta ba zasu hana shi murɗa ta ba...... NEXT TARGET 🎯🎯 READERS INASON JIN DAGA BAKIN KU, A CIKIN AMAL DA MALEEKH WAYE KUKE SON JIN SCENE ƊINSA?.... asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 5 to 6 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 ___________________________________________ Kaduna Gidan rediyon Rayuwa FM Amal ta dawo cikin ayyukanta amma a bayyane take cewa "An fara sanyaya yanayin da nake ciki..." Daga ranar da ta gabatar da shirin da ya fallasa yanda wasu ‘yan siyasa ke yin amfani da talakawa don cimma burinsu, wasu na jin tsoro, wasu na jin karayar zuci amma Amal bata tsaya biye wannan ba. A bayanin ta a gidan rediyo Tana cewa: “Ku sani, talaka ba ƙaramin abu bane, kada ku yarda a rinƙa amfani da ku a lokacin zaɓe, sannan a watsar da ku bayan an ci zaɓe, Kuyi hankali da waɗanda ke muku alƙawuran ƙarya. Ku tambayi kanku: ina ƴan takara suke bayan zaɓe?” Wannan magana ta yaɗu sosai, har aka ɗora ta a TikTok da X (Twitter), inda mutane suka rinƙa cewa: “Amal ce muryar gaskiya!” “Allah ya kare ki Amal, daga sharrin masu sharri...!” Amma akwai wasu da hakan bai yi wa daɗi ba. Bayan kwana biyu Wata rana, Amal na tsaka da shiri a ofis ɗin Rayuwa FM, sai aka kawo mata wata leda mai ɗauke da kwali. A ciki akwai envelope guda ɗaya, a jiki aka rubuta: "Ki yi shiru kafin a rufe miki baki da ƙarfi." Cikin takardar, akwai hotunan Amal tana fita daga gidan rediyo da kuma wasu bayanai da ke bayyana cewa ana bin sawunta. A ƙarshe akwai kalmar da taji wanda ya sanyaya mata zuciya: “Mu muna da ikon gyara muryarki kar ta mutu.” Amal ta daɗe tana kallon takardar. Hankalinta ya tashi, amma ta daɗe kafin ta nuna damuwa a fili. A zuciyarta, tana addu’a kawai. A bakin ta kuwa murmushin ƙarfin hali take tare da faɗin: “Toh su sani zan cigaba da faɗan gaskiya. Idan zasu kashe ni, to su fara kashe gaskiya gaba ɗaya kafin nan...” Bayan Amal ta dawo gida da dare, tana zaune a ƙasan tabarma gaban Inna tana ta ƙarewa letter barazana da kallo. Inna na kallon fuskarta, cikin damuwa ta ce: “Ki daina gaya musu gaskiya cikin ƙarfin murya haka Amal. Ki tausaya mana. Me zamu ce idan wani abu ya same ki? Gaskiya gaskiya ce, amma a Nigeria gaskiya tana buƙatar wayo.” Amal ta share hawayenta. Ta ce: “Inna, idan muka yi shiru, su waye zasu kare talakawa? Idan ba ni ba, wa zai faɗi makircinsu? Su sun daɗe suna rura wuta, yanzu lokaci yayi da za’a haska gaskiya.” A can Abuja, wasu manyan mutane sun fara tattauna yanda zasu “rufe bakin Amal” ta hanyar amfani da hukumar da ke kula da watsa labarai National Broadcast Control Commission. Sun nemi hukumar ta dakatar da Amal daga gabatar da shirye-shirye saboda "kalaman tada zaune tsaye". A yau an samu wata jarida da ta fara ɓata sunanta da wasu rubuce-rubuce marasa tushe, suna cewa: “tana tada zaune tsaye ne saboda tana neman suna daga ƙungiyoyin waje.” Duk da waɗannan matsaloli, Amal ta koma rediyo da safiya take cewa cikin murya mai ƙarfi: “Wanda ke tsoron gaskiya shi ke son murɗe ta. Amma ku sani, mutuwar muryata ba zata rufe gaskiyar da ta fita daga bakina ba. Idan Allah Ya so, rayuwarmu zata canza.” A lokacin da take faɗar hakan, Maleekh yana duba ta daga laptop ɗinsa a England, kifa kansa ya yi a kan tebur yana furta: “Wannan yarinyar ba ta tsoro? me yasa na kasa kawar da tunaninta a raina?” Tsaya wa ya yi tare da wani ɗan nazari daga baya ya ɗauki wayarsa tare da ƙiran wani Manager campanyn sa a Nigeria garin Kaduna, kamfanin gudanar da kasuwancin chanjin kuɗaɗe daga Dala zuwa Naira da kuma kamfanin tace finafinai da shooting, sunan kamfanin sa CASHBANK hakan yasa ake ƙiran sa da suna Maleekh cashbank, asalin haifaffen garin Kaduna ne iyayensa suka koma Abuja amma akwai sauran family a Kaduna, Bayan ya ƙira Manager bugu ɗaya aka ɗauki ƙiran, Manager ne ya fara faɗin: "Hello Sir! Barka da wannan lokaci...." Maleekh cikin izzah yana yamutsa fuska Ya ce: "Campany na! komai yana tafiya normal?..." Manager Ya ce: "Komai normal Ogah, ana tafiyar da komai yanda ya kamata, sannan ana samun ƙaruwa sosai...." Maleekh Ya ce: "Good! Gobe da safe zan shigo Kaduna, inaso zan ziyarci gidan rediyo Rayuwa FM, sannan zan zauna na ɗan wani lokaci domin gudanar da aiki a kamfani na...." Manager Ya ce: "Haba Ogah ka rasa ina zaka kai ziyara sai a wannan ƙaramin gidan rediyo? ga manya-manyan gidan rediyo masu capacity....." Kafin manager ya ƙarasa maganar Maleekh ya katse shi da cewa "Nan nayi niyyar zuwa...zan sauƙa a gidana na GRA a mun gyara na musamman...." Manager Ya ce: "Okay Sir...." Daga nan suka yanke wayan... Maleekh ya sa a karɓa masa tikiti domin a yau zai bar England, yana so zai sauƙa a Abuja domin gaishe da iyayensa, idan ya kwana da safe sai ya wuce Kaduna..... Bayan Awanni Maleekh ya sauƙa a Nigeria, motoci sun fi goma waɗanda suka zo ɗaukan sa a airport, iyayensa sun yi matuƙar farin ciki da ganinsa tsawon shekaru a ƙasar england, duk da su ma iyayen suna yawan zuwa ƙasashen waje har su ziyarce shi... Maleekh shine babban ɗa a wurin Minister Alhaji Abdul-Majeed. sai ƙannen sa mata biyu, bayan ya bawa iyayensa isasshen lokaci washegari da safe sai da ya ziyarci gidan rediyon sa mai suna CashTalk FM. ba ƙaramin kuɗi aka kashe a wurin ba, komai na musamman, duk ƙofofi da winduna na glass ne, upstairs mai hawa takwas ne a gidan rediyo, amma ba'a fara gudanar da aiki a cikin sa ba, wurin yana nan a tsare sai matakan tsaro da aka zuba da sojoji.... Yana gama wa da nan kai tsaye Kaduna ya nufa amma a wannan lokacin shi kaɗai yake tafe ba escort, domin idan ya isa akwai wasu security sa acan masu jiran sa... A gidan rediyo Rayuwa FM kuwa an sanar musu cewa zasu yi babban baƙo, an tanadar masa wuri na musamman..... Ya sanar wa mutanen sa cewa sai ya fara sauƙa a masauƙinsa dake GRA kafin ya zo gidan rediyo... Bodyguard's ne sun kai sha biyar waɗanda suka je gidan rediyo, suna tsaye da bindigu a hannayensu, kowa yasan cewa za'a yi babban baƙo kuma sun san ɗan hamshaƙin mai kuɗi ne, mai ji da kansa domin kaf Kaduna babu wanda bai san Maleekh cashbank ba da Mahaifinsa Alhaji Abdul-Majeed... Da wasu baƙi na musamman masu kuɗi kafin kace mai wurin ya cika da motoci masu bala'in tsada, domin kaf ƴaƴan masu kuɗi ne babu talaka a cikin su ko mai rufin asiri.. kafin zuwan Maleekh.. Director gidan rediyo ya sanar wa Amal ta waya cewa ta fito da wuri domin akwai hira ta musamman da zata jagoranci shirin..... ★★★★★ A cikin wata safiya mai ɗan sanyi a Kaduna, Amal ta tashi daga karamin ɗakin da ta ke tare da Inna, tsohuwar da ta raineta tun tana shekara biyar. Ta shirya cikin doguwar riga mai launin ruwan-saman madara ta ɗaura gyale a kai, sannan ta ɗauki jakar aikin gidan rediyo. Yau akwai wani shirin tattaunawa da za ta jagoranta, ba ta san cewa shi ne zai zama karo na farko da za ta haɗu da Maleekh ba. A gefe guda kuma, Maleekh ɗan gidan Minister yana sanye da rigar designer, agogon zinare a wuyan hannunsa ya fito daga sabon masauƙin sa a GRA, lokacin yanzu yana ɗokin bayyana sabbin manufofin da zai tallafa wa kamfaninsa. Manajan sa ya shirya masa hira da tashar rediyo domin ya yi tsegumi ga jama’a game da sabuwar kungiyar tallafawa al’umma da su ka kafa. Amma a zuciyarsa, hira ce kawai za ta ƙara masa sunayen jaridu, ba wai ya damu da jama’a ba. A Studio ɗin Rediyo Lokacin da Amal ta ga jerin baƙin da za su shiga shirin, ta ɗan murmusa, sunan Maleekh Cashbank ne a rubuce, a cikin ranta Ta ce: “Hmm, waɗannan ƴan manya ne da ke yawan ɗaukan iska,” ta furta a hankali. Ta gyara na’urorin sauti, ta ƙira editan shirin Ta ce: “Ku tabbatar an dai-daita mic ɗin babban baƙon, kar ya zo ya fara ƙorafin ‘voice quality.’ ” Ba a ɗauki lokaci ba, ƙofar studio ta buɗe. Shigowar Maleekh ta cika ɗakin da ƙamshin turarensa mai tsada, sannan yana wani ji da kai kamar shi kaɗai ne mai kuɗi a faɗin duniya, Ya kalli Amal daga sama zuwa ƙasa, kamar yana tantance ta. Maleekh a zuciyarsa yana faɗin " Haka kawai za a ce wannan ce mai jagorantar shirin? Wata ƴar diploma da ita...." Amal a zuciyarta Ta ce: "Tafiya ɗaya ne da yaro mai jin kansa, zan nuna masa ba duka za a wulaƙanta ba...." Amal ta yi masa sallama cikin ladabi da kwanciyar hankali. Ta nuna masa kujerar zama da microphone, sannan ta fara shirin da sallama ga masu sauraro. Sauti na kunna intro jingle… Amal cikin sassanyar murya Ta ce: “Assalamu alaikum warahmatullah. Masu sauraro barkan mu da warhaka daga tashar Rayuwa FM. Ni ce Amal Abdulsamaad, kuma yau muna da baƙo na musamman… ɗan siyasa, ɗan kasuwa, kuma ɗan gidan Minister, Malam Maleekh Abdul-Majeed. Barka da zuwa.” Maleekh cikin dariyar ƙasaita Ya ce: “Barkan ku Amal. Yana da kyau ganin yadda kuke ƙoƙari… duk da cewa studio ɗin nan da ku kanku sai kun ƙara tsabtace kan ku kaɗan...” Ya ƙare kallon ta daga sama. Amal cikin murmushin ladabi Ta ce: “Za mu yi la’akari da shawarar ka… mun gode. Za mu fara da tambaya: mene ne dalilin dawowar ka Najeriya bayan shekaru da dama a ƙasashen waje?” Maleekh Ya ce: “Hmm, kin sani, wasu daga cikinmu ba za su iya rayuwa da ƙalubalen waje ba. Ni dai na ɗauki digiri na acan, sannan na yi Masters ɗina a England, sannan na yanke shawarar cewa lokaci ya yi da zan taimaka wa ƙasata. Yana da wahala ki fahimta idan baki taɓa fita daga Najeriya ba.” Amal cikin sakin fuska Ta ce: “Wannan ra’ayi ne mai kyau. Amma na sani yawancinmu da muke nan cikin ƙasar muna iya bada gudummawa, koda ba mu taɓa fita ƙasashen waje ba.” Maleekh ya zaro ido, yana ɗan dariya sannan Ya ce: “Toh kenan Amal, idan zan tambaye ki a ina kika tsaya ne a karatun ki?” Amal Ta ce: “Na gama diploma a fannin sadarwa. Kuma ina ci gaba da karatu yanzu a matakin digiri.” Maleekh ya kwashe da dariya tare da faɗin: “Diploma? Subhanallah. Wannan ai kamar keke ne a gaban mota! Amma kinsan ba laifin ki ba ne, ai ba kowa ke da damar zuwa Cambridge ba.” Ya tafa hannayensa biyu yana dariyar raini yana faɗin: “Ku dai ƴan talakawa ku na jin kuna da ilimi, amma…” Ya kawar da fuskarsa gefe, sannan ya tofa yawu a gefe ɗaya kamar yana ƙyamar abin... Amal ta ɗaure fuska, tana danne zuciyar ta cikin kwanciyar hankali Ta ce: “Eh, gaskiya ne. Ba kowanne ne yake da damar zuwa Cambridge ba. Amma ba kowanne ɗan Cambridge ne ke da ilimi na ainihi ba. Wasu su na da takarda, amma babu tarbiyya. Wasu kuma suna da ƙwarewa da mutunci ko da suna da ‘diploma’.” Maleekh ya ɗan ɗaga gira cikin ɓacin rai Ya ce: “Oh, ke kina nufin kina da ƙwarewa a fannin rediyo kenan?” Amal Ta ce: “Eh. Kuma wannan ya fito fili. Hira ce kake yanzu da ni kuma jama’a suna sauraron ka. Za su iya auna nagarta, ba sai na gaya musu ba. Ilimi ba wai inda ka karanta shi ba ne kawai, har da yadda kake amfani da shi.” Maleekh yana ɗan harararta Ya ce: “Kin iya magana sosai. Amma ki sani, a wannan ƙasa, kuɗi da suna ne ke tafiyar da komai. Ba diploma ba.” Amal Ta ce: “Eh, amma a kowanne lokaci ƙasar da ke gina kanta kan kuɗi da girman kai faɗuwa ƙasi take Amma ƙasar da ke amincewa da kishi, basira da aiki tuƙuru tashi sama take....” Gaba ɗaya shiru suka yi cikin studio. Edita da sauran ma'aikata suna kallon juna. Kowa na sauraron tattaunawar.. Maleekh ɗan yatsina fuska ya yi, tare da ɓoye mamakin sa Ya ce: “…Wannan magana ce mai nauyi. To mu gani a ƙarshe, wanne ne zai fi ƙwaƙwalwa ko kuɗi?” Amal ta ɗan saki murmushi tare da faɗin: “Ko wanne yana da kyau a mallake su, zaman lafiya tsakanin su ne zai gina ƙasa. Ba raini ba.” Sauti yana ƙarewa da outro music... A karshe shirin ya kare, Amal ta yi godiya ga Maleekh, Da suka fito daga studio, Maleekh ya matsa kusa da ita yana faɗin: “Kin san dai baki yi min adalci ba, maganar ki ya yi yawa....” Amal ta sake murmushi ta ce: “To idan ka san kana son yabo, ka shirya tambayoyi kafin hira amma ni aikina na ke yi.” Kafin ya yi ƙarin magana, wata ƙiran gaggawa ta shigo wayarsa. Maleekh ya yi tsaki ya juya, ya tafi ba tare da sallama ba amma zuciyarsa ta fara tunanin wannan yarinya mai kuzari. Maleekh ya bar studio ɗin da zuciyar sa a ɓace, amma yana ɓoye baƙin cikin sa saboda mutanen da yake tare da su... . Amal ta dawo ofis cikin numfashi mai nauyi, amma tana jin daɗin yadda ta tsaya da mutuncinta. Wannan ya zama matakin farko na rikici, kuma watakila farkon juyawar tunanin Maleekh kenan ...… Bayan rana guda, wani bidiyo na shirin ya yi trending a social media. Masu sauraro sun yaba da yadda Amal ta ɗan yi masa “ƙwaɓe” cikin ladabi. A gefe guda, an fara sharhi kan girman kai da rashin natsuwar Maleekh. Wannan ya sa Maleekh ya ji ɓacin rai sosai amma kuma akwai wani abu a ransa: sha’awa da mamakin jarumtar Amal. ★★★★★ Amal ta dawo gida da yamma, ta jingina jakar ta gefe, ta cire gyalen kanta cikin gajiya. Fuskar ta cike da damuwa, amma tana ƙoƙarin ɓoye shi. Inna ta leƙo daga ɗaki ta ga a yanda Amal take kamar akwai damuwa, Ta ce: "Ke Amal, lafiya? Yau kin dawo kamar wadda aka buga da tukunya." Amal ta zauna a tabarma, ta sauƙe ajiyar zuciya sannan ta ce: "Inna... yau kam ban ji daɗin aikin ba. Na haɗu da wani mutumin da ba ni da kwarin gwiwar sake hira da shi....." Inna ta matsa kusa da ita Ta ce: "Waye kuma? kin san ke ba kya son hayaniya. Me ya faru?" Amal Ta ce: "Sunansa Maleekh… ɗan gidan Minister, shine wanda muka yi hira da shi daga England, An zo hira da shi a studio… amma ki san me Inna? Bai da kunya. Wai don na faɗi cewa na gama diploma, sai ya fara raina ni, yana cewa kamar na koyi keke ne a kan hanya, sai har ya tofa yawu yana nuna kyama." Inna ta ɗaga hannuwa tare da faɗin: "Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Tofa! Yaro yazo studio don ya ɗaga kansa, amma sai ya saukar da kai da harshensa. Wane irin mutum ne haka?!" Amal ta ɗaure fuska tana faɗin: "Inna, ya ƙira ni yar talakawa a fakaice, yana dariyar raini. Amma ban bari ya raina ni ba. Na faɗa masa gaskiya cikin nutsuwa ko da kuwa yana sanye da agogo mai daraja." Ta ƙarasa maganar kamar irin sakalan yaran nan... Inna ta zaro ido Ta ce: "Amal wallahi maganar gaskiya Ni dai na tsani irin waɗannan samari. Masu kuɗi amma babu tarbiyya! Don Allah ki rabu da wannan yaron ni ma har zuciyata na tsane shi!" Amal ta furzar da iskar bakin ta tana faɗin: "Ni ma Inna. Wallahi na tsane shi. Idan ya sake bijiro min da wata magana, sai na taka wuyansa gaba ɗaya." Shiru ya ɗan biyo baya. Inna ta juyo ta kalle ta cikin tausayawa. Ta ce: "Amal... ki riƙe mutuncin ki kamar yadda na koya miki. Talauci ba laifi ba ne, amma girman kai babu aji a cikinsa. Idan ya dawo neman shahara a gaban ki to ki sa shi ya gane cewa 'yar diploma ta iya kafa duniya da ilimi fiye da takardar da babu hali a cikinta." Amal ta ƙyalkyale da dariyar taƙama cikin kwarin gwiwa Ta ce: "Hakan za ayi, Inna. Wallahi ba zan bari ya raina ni ba." Sashen Maleekh Maleekh na kwance a kan katafaren gadonsa mai launin azurfa, A.C yana busa iska mai sanyi. Ya juya gefe, ya kalli silin ɗin ɗakin, amma zuciyarsa cike da ɗaci. Wayarsa a gefe tana ring ging amma bai saurari ƙiran ba. Kawai maganar Amal na yawo cikin kwakwalwarsa kamar ƙaho ne ke bugawa. Maleekh a zuciyarsa yana faɗin: "Yar diploma… amma kalamanta kamar lecture. Ta ce: 'Wasu suna da takarda amma babu tarbiyya'... Aibanta kenan ko?" Ya juyo gefe yana huci. Maleekh a fili Ya ce: "Ni ɗan Minister wanda ya gama Cambridge yarinyar talakawa ta ƙira ni marar tarbiyya? Cikin rediyo? A gaban kowa?!" Ya miƙe zaune, ya ɗauki remote, tare da jefar da shi gefe... Maleekh cikin haushin ta yake faɗin: "Ta raina ni. Wallahi ta raina ni. Kuma in ba ta gane inda take ba zan nuna mata bambanci tsakanin gata da ƙasa. Ba zan bar wannan batun lafiya ba." Yayi shiru, yana jujjuya kalmarta a rai. A hankali, ya sauke murya... Cikin raunin zuciya Ya ce: "Amma fa ta iya magana... Ba kamar sauran ‘yan jaridu da ke jin tsoro ba. Ta tsaya da mutuncinta. Hakan ya… ya ɓata min rai sosai." Sai ya ɗan murmusa, yana jin baƙin ciki da nauyi a zuciyarsa. Ya cigaba da cewa: "Yanzu ni wanda ake ji da ni a birni, yarinya ‘yar unguwa ta ruguza min kwarin gwiwa? Sai na saka ta daina jin daɗin aikin nan. Sai ta daina jin kamar tana da ƙima." Yayi tsaki, ya kashe wutar ɗakin gaba ɗaya. Duhu ya mamaye ɗakin, amma zuciyarsa cike take da barazana... da tsantsar jaraba. ★★★★★ Bayan kwana uku, Maleekh ya gama siye Ogan gidan rediyo da kuɗaɗe kimanin five billions akan ya tura Amal cikin wayo da dabara ta fara aiki a kamfanin sa dake nan Kaduna, Ya nuna cewa anyi mata ƙarin matsayi ne daga gidan rediyo Rayuwa FM zuwa Kamfani CashTalk, dake Amal bata san waye mallakin wurin ba.... Washegari Shugaban gidan rediyo ne ya aiki Amal washegari da safe bayan taje wurin aiki, wai taje kamfani ta kai takardu a shugaban kamfanin, ya sanar mata cewa zata ɗan musu aiki a wurin na wani ɗan lokaci... Cikin mutunci da kulawa da kuma ganin girman shugaban nasun ta amsa cikin girmamawa.... Amal ta hau keke napep taje har kamfanin da aka aike ta dake yau ba da wanda zata tattauna a rediyo, Amal na fitowa daga napep, ta kalli ginin kamfanin mai beni hawa hawa mai sheƙi, sannan ta shiga cikin harabar. Bayan tambayoyin da ma'aikatan suka mata sai da ta nuna takardu, da ƙyar aka barta ta shiga cikin kamfanin kamar wata mai neman taimako. tana shiga ta tambayi office ɗin shugaban kamfanin aka nuna mata sai dai daƙer suka barta ta nufi office ɗin har sai da ta nuna musu ID card ɗinta tukun, tana zuwa bakin office Ta tsaya a bakin ƙofar office, ta kwankwasa a hankali. sai da ta ɓata lokaci kafin aka bata umarnin shiga ciki... Muryar daga ciki mai sanyi da kuma cike da izza ya furta "Shigo..." Amal ta buɗe ƙofar a hankali, da sallama a bakinta. "Assalamu alaikum..." Tana ɗaga kai, sai ta tsaya cak. Idonta ya sauƙa akan Maleekh, wanda ke zaune cikin kujera a matsayin shugaban kamfani. Sanye yake da farar riga mai kyau, hannunsa na ɗauke da shisha, yana hura hayaki a hankali. Ya ɗago kai yana kallonta daga ƙasa har sama cikin salon raini.. Maleekh yana hura hayaƙin shisha, cikin izzah ya furta: "Toh toh… ga yarinyar da bata gajiya da tunkarar manya. Wane saƙo ne kuma kika kawo yau? Ko kin zo ne ki ƙara mini 'lecture' kamar ranar?" Amal ta ɗaure fuska, zuciyarta cike da takaici. ta miƙa masa takardun da aka bata daga ofis. Sannan ta ce: "Wannan ne takardar da aka ce in kawo daga gidan rediyo. Nazo ne don isar da aiki." Maleekh ya karɓi takardar kamar bai damu ba, Ya ce: "Aiki kenan… Yar diploma, mai azama. Kina durƙusar da kai ne don ki nuna kina da hankali da ilimi ko kuwa?!" Amal cikin natsuwa, da murya mai taushi Ta ce: "Ba don nuna hankali nake ba. aiki kawai nake, kuma ina mutunta kowa ko da kowa bai mutunta ni ba." Maleekh ya saki dariya mai cike da izza tare da faɗin "Wannan muryar kamar mai wa’azi. Sai kace ke ce HR ta duniya. Kin ƙirani marar tarbiyya ko dai kin manta?" Amal ta saki murmushi mai kaifi sannan ta ce "Ban manta ba. Kuma ban faɗa da bakina ba. Idan kai ne ka karanta hakan a cikin kalmomi na, to hakan na nuna inda matsalar ya ke." Maleekh ya yi shiru na ƴan daƙiƙu. Ya kalleta sosai kallon da ke cike da mamaki da ƙyashi. Amma a can cikin zuciyarsa, kalmarta ta sake sosa shi... Maleekh Ya ce: "Toh tunda ke mai ilimi ce, menene burinki a rayuwa? Wani matsayi kike mafarkin kaiwa?" Amal cikin ƙarfin gwiwa Ta ce: "Burina shine in rayu cikin mutunci, in taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi, in yi amfani da harshena da ilimi na wajen tallafa wa al’umma. Ba wai kawai in ɗora ƙafa akan tebur in sha shisha ba." Maleekh ya riƙe murfin shisha sosai, idanunsa suka ɗan sauya launi amma bai nuna ba. Ya juyo gefe yana faɗin: "Hmmm… kamar dai wata ce ke jin haushin masu gata. Amma me yasa duk lokacin da na ganki, sai nake jin kina ƙoƙarin cewa ni ne matsala?" Amal Ta ce: "Saboda ka ɗauki kujerar gata, ka manta da nauyin da ke tare da ita. Ba kowa ke da damar zama babban mutum ba, wasu kawai manyan suna ne da ƙaramin hali." Shiru suka yi . Sai dai wannan karon Maleekh bai ce komai ba. Ya janyo wata takarda, ya sanya hannu kai tsaye sannan ya miƙa mata cikin sanyin murya Ya ce: "Zaki iya tafiya yanzu." Amal ta jinjina kai tare da faɗin "Nagode." Ta juya cikin kwanciyar hankali, ta fita daga ofishin. Amma a ƙirjinta, zuciyarta na harbawa ba don tsoro ba, sai don mamakin yadda kaddara ke juyawa. Shima Maleekh yana zaune shiru, yana kallon ƙofar da ta rufe bayan ta fita. Ya furzar da iskar bakin sa... Maleekh a zuciyarsa yake faɗin: "Wannan yarinyar… tana da zuciya. Kuma tana da baki. Amma sai ta gane ban faɗi kalmar ƙarshe ba tukuna." Amal ta fito daga ofishin, ta rufe ƙofar a hankali. Ta jinjina kai kamar wacce ta gama jarabawa mai wahala. Tana takawa zuwa ƙofar fita, amma zuciyarta cike da faɗuwa. Amal a zuciyarta take faɗin: "Me nake yi a duniyar masu kuɗi? Wannan mutumin dai… ya raina duk wanda bai kai sa ba. Amma wallahi… sai yaga cewa ba gata ke sa mutum zama nagari ba." A lokacin da ta ke fita harabar kamfanin, wata murya ta tsaya mata a baya. Muryar mace.. "Excuse me, ke ce Amal daga gidan rediyo?" Amal ta juyo, sai ta ga wata mace doguwa, fara, tana sanye da kaya na ofis masu kyau. Fuskar mace ce mai wayewa Amal Ta ce "Eh, nice. Lafiya?" Matar Ta ce: "Ni sunana Amira, ni ce Personal Assistant ɗin shugaban kamfanin. Na ji ɗan ƙaramin ɓangare na tattaunawarku daga ciki. Ki sani, ba kowa ke iya tsayawa gaban Maleekh har ya faɗa masa maganganu ba." Amal ta kalli Amira cikin mamaki ta ce "Ban gane ba..." Amira ta ce "Yana da zuciyar ƙyashi, amma idan mutum ya kasance da gaskiya da daraja, sai ya ƙyale jin haushi ya koma sha’awa. Ki kula da yanda kike magana da shi, sabo da idan mutum kamar shi ya fara jin haushin mutum... yakan rikice." Amal ta ɗan danne dariyarta, tana kallon Amira da murmushin tausayi ta ce "Ni bana kula mutane irin sa. Sai dai mutanen da ke da daraja a zuciyarsu, ba a kuɗinsu ba." Amira ta jinjina kai ta ce: "Na gane. Amma ki sani, akwai abinda ba ki sani ba. Maleekh yana da wani bala’i da baya so a ambata. Ya tsani wanda zai fallasa rauninsa." Amal ta ce "Idan yana da rauni, to bai kamata yana cutar da mutane ba. Duk da ina aiki a ƙarƙashinsa yanzu, bai cancanci mutum ya ba shi zuciya ba." Amira ta ce "Zan kula dake. Idan wani abu ya tashi, ki kira ni. Amma ki sani ke kin taso da ruɗani a zuciyar wanda ba’a saba masa ba." Amira ta juya ta bar Amal tsaye cikin ɗan mamaki da nauyin tunani. Maleekh yana tsaye a tagar ofishinsa yana kallon Amal tana fita. Yana zuƙar iska daga shishar sa, yana kallon ta cikin rashin natsuwa. Maleekh a zuciyarsa ya ce: "Yarinyar nan… bata da kuɗi, amma tana da daraja. Na tsani irin kalaman da take faɗa amma me yasa nake tunaninta? Me yasa kalmarta ke yawo a kunne na kamar ƙira?" Ɗaukar wayarsa ya yi ya ƙira wani Abokin sa mai suna Baba Dan London... Yana ɗaga ƙira Maleekh ya ce: "Baba Londo… kana free ne? Zo ofis ɗina yanzu. Muna da aiki akwai wata ƴar rediyo da nake so na koya mata darasi. Ta raina manya." Yana kammalawa ya kashe wayar... Maleekh yana zaune a ofis ɗinsa, gaban rigar sa ta buɗe sai ƙirji a waje, yana ta juya shisha da ƙasaita kamar basarake. Wayarsa ta yi ƙara sau ɗaya. Ya dubata. Maleekh yana murmushi ya ce: "Yo! Baba Londo ka shigo mana..." Kafin minti biyar su wuce, ƙofar ofishinsa ta buɗe. Sai ga wani saurayi mai yawo da kaya na zamani, sanye da tabarau a cikin ofis. Shine Baba Londo mashahurin ɗan yawo da gurɓataccen tunani, wanda ba ya gajiya da yaudarar mata. Baba Londo yana dariya ya ce: "Kai kai kai! Maleekh ɗan Minister! Gani nan! Wai kai ka ce akwai wata drama a nan?" Maleekh yana hura hayaƙin bakin sa ya ce: "Baba… wata yarinya ce daga gidan rediyo. Yar talakawa ce, amma fa kyan ta ya wuce misali, farar fata ce kamar farar larabawa. Amma fa... tana raina hankali na! Wai saboda ta karanci journalism shine take taƙama...." Baba Londo ya zauna a gefensa, yana gyara agogon hannunsa ya ce: "Kai ka bari. Talakawa da wayo sunfi wuƙa mai kaifi. Amma kai fa ba'a raina ka haka fa.... sai mu koya mata darasi." Maleekh ya ce "Kai nake jira. Gaya mini yadda zan danne mata girman kan nan cikin kwana biyu." Baba Londo ya matso kusa da shi tare da da rage murya ya ce: "Ka ji plan. Tunda tana aiki a ƙarƙashinka, zaka sa a ƙara mata aiki kullum... har sai ta gaji, Idan tayi kuskure, sai a nemi soke kwangilar ta ko a hana ta albashi." Maleekh yana jin hakan sai ya lumshe ido yana jin daɗin wulaƙancin da zai mata.. Maleekh ya ce: "Hmm... wannan ra'ayin ya fara birge ni." Baba Londo ya ce: "Daga nan sai ka fara jan hankali ka nuna kamar kana jin tausayinta. Ka shiga cikin lamarin ta, ka rinƙa bata kulawa da magana mai taushi. Sai zuciyarta ta fara rikicewa. Amma fa kada ka nuna mata zafin nama. Ka fi dacewa da wasanni da hankali." Maleekh yana dariyar mugunta ya ce: "Zaka ce ni ba master bane a wasan zuciya? Ni nake barin manyan ƴan ministoci suna jira, ga su nan beautiful model. Amma wannan 'yar diploma za ta ci kaina?" Baba Londo ya ce: "Wallahi ba zata ci ba. Amma kayi hankali irin wannan mata idan ka fallasa musu rauni, sai sun rikita rayuwarka." Maleekh ya ce: "Don haka zan koya mata darasi da hannuna. Ni ba zan so mace 'yar talaka ta ga girma na ta raina ni ba. Sai ta gane ban da sakarci nake yi, maye ne kawai ban fara ba." Sai suka yi dariyar mugunta tare. Maleekh ya kira PA ɗinsa ta waya. yana sanar mata cewa: "Amira… ina so a shirya meeting na gaggawa da Amal gobe da safe. Ki ce da ita, akwai wani 'special project' da zan so mu yi tare. Tell her it’s top priority." Yana kashe wayar, ya kalli Baba Londo da murmushin mugunta Ya ce: "Let the game begin." Amal ta dawo gida da yamma, jikin ta duk a gajiye amma zuciyarta na tafasa da tambayoyi. Tana shiga daƙin su, ta ajiye jakarta tana huci ƙasa ƙasa. Inna na zaune tana yanka kayan miya ta ɗago kai da kallon tambaya Ta ce: "Amal! Lafiya?..." Amal ta zauna a ƙasa, ta sauƙe ajiyar zuciya sannan ta ce: "Inna... kin san ofishin da aka aike ni yau?" Inna ta dafa goshi tare da faɗin " Wajen marar mutunci?" Amal ta ce: "Na sake samun gayyata can gobe. Wai shugaban kamfanin ya ce yana so mu yi special project tare. Kuma wai top priority ne..." Inna ta miƙe da sauri tana faɗin: "Subhanallah! Wannan ai ba aiki ba ne makirci ne! Kin san irin mazan nan Amal? Su suke fara da “project”, su ƙare da lalacewa!" Amal ta lumshe ido tare da faɗin "Ni ma ban gamsu da maganar ba, amma kuma Inna… aiki ne. Idan na ƙi zuwa, zasu ce ban bi umarnin su ba amma a zahiri bazan je ba..." Inna ta zauna tana faɗin "To ke ma ki zauna da wayo! Ki je gobe amma ki saka idanu kamar likita. Kada ki yarda ki zauna da shi kaɗai. Kuma wallahi, ki saka hijabinki sosai ki nuna masa ke cikin ƴar halak ce..." Amal ta ce "Inna, ni ma zanyi taka tsantsan. Amma wani abu ya daɗe yana damuna..." Inna ta ce "Wane ne?" Amal ta ce "Maleekh … ba kamar sauran mazan ne ba. Zuciyarsa na daban ne. Na lura da yadda yake kallona... ba wai kallon sha'awa kawai ba, kamar kallon tambaya ne... ko ƙiyayya..." Inna ta tsare ta da ido sannan ta ce "Amal, ki ji tsoro da irin kallon nan. Wani lokaci mugun mutum yana jin yana ƙaunar mutumin da zai ɓata. Ki kiyaye. Ki bari Allah ya fitar da ke da mutunci." Wuraren dare misalin ƙarfe 10 Maleekh da Baba Londo suna cikin wani VIP lounge a cikin wani babban hotel tal. Wuta mai launin purple da blue tana ta walƙiya, kuma ana rawa a gefe. Amma su suna zaune suna cin nama da lemon shayi... Baba Londo ya ce "Kana ganin zata zo?" Maleekh yana dariya ya ce "Wai don tana kare kanta ne zaka ce ba zata zo ba? Duk mace tana da buɗaɗɗen lungu. Sai dai kai ka samu hanyar da zaka shiga da sirri." Baba Londo ya ɗan runtsa sannan ya ce "To amma ka tuna... akwai wasu mata da ba sa fallasuwa, sai dai ka ɓata kanka. Idan wannan yarinyar ce ɗaya daga cikinsu..." Maleekh yana hura hayakin shisha sannan ya ce *"To zan bata ƙaunar da zata rikita ta, sai dai idan zuciyarta dutse ce. Amma idan ta ƙi da gaske..." ya ɗan langaɓe ya ƙarisa da cewa: "Zan mata abu ɗaya wato hukunci. A daina wasa da ni, ni ba wanda ake wulakanta wa ba ne." A wannan ranar Amal ƙin zuwa wurin tayi, har suka gaji da jiran ta, ran MALEEKH ya ɓaci amma sai dai Baba London ya bashi shawarar kada ya nuna mata ɓacin ransa.... Washegari da safe, Amal ta iso cikin kayan aiki masu kamala, hijabinta tsaf, fuska cike da kwanciyar hankali amma zuciya cike da damuwa. Tayi sallama, PA ɗinta Amira ta nuna mata za ta iya shiga.... A cikin ofis, Maleekh na zaune yana faman latsa laptop, yana kallonta da ɓoyayyen mugunta. Bayan ta zauna, ya fara magana cikin wani salo, ba kamar Maleekh ɗin jiya ba... Maleekh yana murmushi ya ce: "Yanzu Amal, na ƙira ki ne saboda na lura kina da basira sosai. Muna da wata sabuwar shirin nuni mai taken “Rayuwar Gaskiya” – kuma ina so ki zama presenter ɗinsa." Amal cike da mamaki ta ce: "Ni? A matsayina na ƴar kwangila kawai?" Maleekh ya lumshe ido tare da faɗin: "Kwarai kuwa. Sai dai akwai wasu abubuwa da zamu gwada. Na tsara zamu je location ɗin wani shooting gobe a resort da ke wajen gari." Amal ta ɗaure fuska ta ce: "Wajen gari? Da kai ko da tawaga?" Maleekh ya yi murmushi tare da hura shisha ya ce: "Ni da ke za mu fara don gwaji ne. Sai mu tantance style ɗin ki kafin a haɗa da crew." Amal ta ji wani abu ya motsa a zuciyarta. Duk da salon maganar sa, akwai wata muguwar niyya da ta ji tana tashi. Sai ta miƙe cikin nutsuwa ta ce: "Zan buƙaci takardar umarnin tafiyar da kuma cikakken bayani a rubuce. Ina kuma so Ogah na ya sani da kansa...." Maleekh ya ɗan daure, domin zuciyarsa tafasa take, ya ce: "Yanzu dai ki zauna mu gama magana. Bayan nan sai mu shirya komai." Amal ya ce: "A'a sir, ba komai da yafi tsari. Aikin da babu sahihanci ko rubuce-rubuce, ba ni da wani hannu a ciki." Maleekh ya kafe ta da ido, sai dai maganarta ta nuna masa ita ba yar wasa ba ce. Amma ya kame kansa Ya ce: *"Alright. I respect that. Za a rubuta komai." Amma cikin zuciyarsa yana cewa: "Zaki ga shirin da zan yi miki, yarinya!" Bayan Amal ta tafi, Shima fita ya yi tare da shiga motarsa ya nufi gidan Baba Londo. Bayan sun gaisa da dariyar sheɗanci.. Maleekh cikin ɓacin rai yake faɗin: "Plan A bai ci ba. Tana da wayo sosai. Amma zamu juyar da plan B." Baba Londo yana shan taba ya ce: "Ka shigar da wata yarinya cikin lamarin. Wacce zata shirya yin bidiyo da rigimarsu kamar suna faɗa... ko faɗa kan mijin aure... sai Amal ta fito kamar mai masifa, hakan zai baka damar ɗaukar ta a video ka tura cewa ƴar rigima ce bazaka iya aiki da mafaɗaciya ba...." Maleekh ya ce: "Za mu saka hidden camera a ofishina. Zan sa wata yarinya daga cikin ƴan nuni ta zo cikin shirin faɗa gobe ta tinkari Amal yanda zata biye mata suyi rigama tare, zan ɗauki Amal da camera cikin faɗa, zamu sa suna faɗa ne akan makullin sirrin ƙofar dukiyar al'umma, suna tsara yanda zasu yi su kwamushe kuɗaɗen ne, ɓarauniya ba zata iya wakiltar kamfani ba." Baba Londo ya ce: "Kai, wannan zai jefa ta cikin matsala! Ba za su sake yarda da ita ba. Daga nan zata roƙi gafara... kai kuma ka bata sharaɗi kafin ka yafe." Maleekh ya ce "Game on, Amal." Washegari da safe, Amal ta shirya cikin kayan aiki masu kyau rigar atamfa cikin tsabta da hijabi mai ƙyalli, amma a zuciyarta ta riga ta ɗauki matakin tsaro. Tayi addu’a kafin ta fita. Tana zuwa ofis, wata sabuwar mace tana zaune a cikin ofishin taro tana duba waya. Ita ce 'yar wasan da Maleek ya ɗauka don ya kunna rikici.. Amal ta gaishe da masu tsaro, ta nuna ID ɗinta, sannan ta shigo office ɗin Maleekh... Maleekh yana murmushi ya ce: "Amal, good morning. Kin iso da wuri. Mu jira ‘yar uwar da zamu yi rehearsals tare da ita. Akwai script ɗin faɗa ne zamu gwada." Amal cikin nutsuwa ta ce: "Toh, amma ina so in karanta script ɗin kafin a fara komai. Ina so in ga abinda zan faɗa da abinda nake nufi da shi." Maleekh ya ce: "Ai improvisation ne wato ki yi da kanki. Ki yi acting kamar da gaske." Amal ta yi murmushi mai kaifi tare da faɗin: "Haka kuwa? Amma wannan ba ya cikin tsarin aikin da aka tsara ni a kai. Kuma... ni presenter ce, ba actress ba." Maleekh ya yi dariya kamar ba komai a ransa ya ce: "Ki bar komai a hannuna, Amal. Daga nan zamu iya ɗaukar ki full time. Zaki daina zama ƴar hanya, kuma... wataƙila har ki samu gida a city." Amal ta gane ya na ƙoƙarin cin mutuncinta cikin zance. Ta ce: *"Sir, kamar yadda kace ni presenter ce. Kuma ni bana barin mutunci na ya zube akan gatan talauci." Ta miƙe tsaye cikin ladabi ta ce: "Nagode da gayyata, amma ba zan iya cigaba da wannan wasan ba. Ina da girman kai na halal." Ta juya zata fita, sai ga wata yarinya ta shigo ta fara acting kamar faɗa... Yarinyar ta fara faɗin: "Ke wacece da kike tunanin ke kaɗai kika iya wannan aikin! Marasa asali ba su da kunya! Kuma nasan cewa kina ƙoƙarin buɗe ɗakin tsaro na kuɗaɗe, kina so ki nuna mana cewa ke ɓarauniya ce? ina key ɗin da kika sata?..... " Camera ta kunna daga gefe, Maleekh yana dariya a cikin ransa.... Amal ta tsaya, ta juyo da fuska cikin sanyi rai, fito da ƙaramin recorder daga jakar ta tayi tana kallon Maleekh domin bata da lokacin yarinyar balle ta mayar mata da martani... Amal tana murmushi ta ce: *"Da fatan za ku cigaba da recording amma yanzu zaku ji cewa tun jiya da dare, na san shirin ku." Ta kunna recorder ɗin da ke ɗauke da muryar Maleekh da Baba Londo suna shirya plan A da B.... Amal ta ce: "Na san kuna so ku dauƙi bidiyon karya, ku ɓata mini suna. Amma Allah baya barin mai gaskiya. Recorder ɗin nan zai isa wajen shugaban network ɗin mu. Haka kuma, lauyana zai tuntubi kamfanin ku." Maleekh ya firgita, ya kasa tashi. Yarinyar da aka kawo acting ta fice da sauri. Amal ta nufi ƙofa cikin ɗaukaka kamar sarauniya... Kafin ta fita ta juyo tana kallon sa tare da faɗin: "Mutunci ba shi da farashi, Sir. Amma rashin mutunci yana da sakamako.....na yanke shawaran bazan cigaba da aiki anan ba, tin farko inda nasan cewa kaine shugaban wannan kamfanin da bazan kusanci yanda kake ba, zan koma asalin tushen da na fito wato aikin gidan rediyo.....' Tana kaiwa nan ta fice... A ruɗe Maleekh ya buga table ɗin gaban sa cikin ɓacin rai yana huci.... yana hura shisha cikin takaici, yana jin kamar Amal ta maida shi ɗan iska a zuciyarta. maimakon ya gane laifinsa, sai ƙiyayya ta mamaye shi... Maleekh a cikin zuciyarsa yana faɗin: "Wannan yarinya... zata gane waye ni. Duk da wayonta, ba zata tsira ba. Zanyi mata abinda ba zata taɓa mantawa da shi ba..." Cikin dare a cikin masaukin alfarma, Maleek yana zaune da Baba Londo da wasu abokansa guda biyu masu kuɗi, suna shan shisha. Idonsa jajir, zuciyarsa cike da haushi. Maleekh yana faɗa cikin murya mai ƙarfi... "Wannan yarinya Amal... ta ɓata min suna a ofishina. Ta kuma raina ni a gaban mutane. Wannan ba abinda za a barshi haka ba." Baba Londo ya ce: "Sai ka lalata mata suna gaba ɗaya. Babu mace da zata tsira da karfi idan ka shigar da police ko kafafen yaɗa labarai." Abokin Maleekh wato Nasir ya ce: "Ai akwai hanya mafi sauƙi. Muna da aboki a CID unit. Sai ka shirya cewa Amal tana zargin ku da cin zarafi ne saboda baka amsa mata soyayya ba, ka jujjuya lamarin. Da sunan tana cutar da kai. A kama ta, a tsare ta, ko a duba gidan ta da sharri." Maleekh yana murmushi mai cike da mugunta ya ce: "Perfect... Zamu rubuta ƙarar karya, mu ce tana amfani da kafar rediyo wajen tada ƙiyayya da fitina a tsakanin manya. Zamu ƙara cewa tana da haɗin guiwa da wani NGO mai kalubalantar gwamnati." Baba Londo ya ce: "Wannan zai hana ta aiki a kowanne channel. Zata durƙusa ta roƙe ka." SASHEN AMAL A washegari Amal ta tafi aiki cikin natsuwa. Ogan ta ya ƙira ta ofis yana faɗin: "Amal, akwai wata ƙara da aka kawo daga babban kamfani na kasuwa. Sun ce kina amfani da kafar rediyo wajen tayar da ƙiyayya da jita-jita. Wannan abu yana da nauyi sosai." Amal ta ɗan razana, amma sai ta daure ta ce: "Sir, wannan ƙarya ne. Sai dai na san daga inda yake fitowa..." Ogah ya ce: "Ba zamu yanke hukunci yanzu ba. Amma ina ba ki shawara ki tura duk wani hujja da ke hannunki. Kuma ki lura da matakan aikin, Wannan ana iya kai shi kotu." Amal ta fito daga ofis din cikin nutsuwa amma zuciyarta a ɓace take, Tana tsaye a bakin ofis sai wata mace daga HR ta zo da saƙo. Ta ce: "Amal, anyi suspend ɗinki daga aiki har sai an kammala bincike." Amal ba tare da ta ji wata damuwa ba ta amsa, domin tasan tana da gaskiya .... Da dare, Amal na zaune a cikin ɗaki tana kuka a gefen gado. Inna na shafa bayanta tana lallashi. Bayan sun yi addu’a, Amal ta ƙira wata ƙawatarta da take aiki a cikin wata NGO “Voice of Justice.” Amal ta ce: "Na shiga matsala, Hafsa. Sun kulle ni daga aiki saboda sharri. Kuma na san Maleekh ne. Ya jujjuya gaskiya zuwa ƙarya." Hafsa a waya ta ce: "Kar ki damu. Zamu turo da lawyer kuma zamu shiga tsakani da hujjoji. Amma kina da audio recording da suka shirya sharri tun daga farko, ko?" Amal ta ce: "Ina da shi. Kuma zan tura muku gobe da safe." Hafsa ta ce: "Amal... yanzu wannan ya wuce shari’ar aiki. Zai iya zama babban case defamation da false accusation. Wannan karon... Maleekh zai san kina da garkuwa mai kyau!" A cikin wani shahararren club na Kaduna, Nasir da Baba Londo suna zaune suna jiran Maleekh, amma Maleekh bai zo ba. Nasir ya yanka masa message ba tare da samun reply ba... Nasir ya ce "Wannan Maleekh yana ƙara fita hayyacinsa. Ko ya manta cewa ba duniya ce ke karkata saboda kuɗi ba ne. Wannan karyar da yayi wa Amal zai dawo masa da baƙar aniya..." Baba Londo ya ce: "Kai Nasir, me ya dame ka? Kai fa shi ne ya fitar da kai daga matsakaicin rayuwa. Yanzu kana da mota, kana da suite, kana shan shisha duk saboda shi. Kada ka fara goyon bayan waccan yarinyar." Nasir cikin jin haushin gorin da Baba Londo ya yi masa, ya ce: "Na lura da wani abu game da Amal. She's smart. She's classy. Kuma ba irin matan da zasu zube saboda kwaɗayi ba ce. She reminds me of my late sister… kuma Maleekh ya fara wuce gona da iri." Baba Londo ya ce: "Toh me kake nufi?" Nasir ya ce: "Ina nufin zan fara kare kaina kafin abin ya shafe ni. Na tattara abubuwa da yawa da Maleekh ke yi, ciki har da audios ɗin da ya shirya domin ɓata wa Amal suna. Kuma yanzu na fara tuntubar wani babban ɗan jarida a Abuja." Baba Londo a firgice ya ce: "Kana da hankali kuwa?! Wannan abu zai rushe Maleekh, ya kuma iya jawo mana matsala!" Nasir yana juyawa da murmushi mai cike da nufi ya ce: "Ko da zai rushe shi, zai wanke wata rayuwa. Zai wanke Amal. Kuma a duniya karshen mugunta ba shine girma ba." Washegari da safe, Amal na gida tare da Inna. Tana duba waya, sai ga saƙo daga wani lamba da bata sani ba. Ta buɗe ta karanta... Message: “Ki daina tsoro. Na fara ganin gaskiya. Zaki ji wani abu nan bada daɗewa ba. Kada ki yarda da kowa a work ɗin su duka. Daga wanda ke ganin haske a cikin duhu.” Amal ta karanta saƙon sau biyu kafin ta kalli Inna ta ce: "Inna, wani da nake zaton Abokin Maleekh ne ya aiko min da saƙo. Yace zai tallafa min, cewa zai tona gaskiya." Inna ta harari wayar tare da faɗin: "Toh Allah ya tabbatar da alheri. Amma ki yi hankali. Kada ki shiga jikinsa da sauri. Duk mai cece-ki a duhu, akwai dalili." Amal ta ce: "Inna, zan saurara. Amma na fara jin cewa wannan yaƙin, ba ni kaɗai ce ke cikin sa ba..." A wani café na sirri, Nasir ya gana da ɗan jarida mai suna Faruk, wanda ke aiki da wata jarida mai zaman kanta. Faruk ya ce: "Kai abokin Maleekh me kake da shi?" Nasir ya miƙa masa flash drive ya ce: "Gaskiya da shaidun shirye-shiryen da Maleekh yayi domin ɓata suna da cutar da wata mace mai gaskiya. Wannan shi ne bugun farko. Sai dai ka tsaya da gaskiya, kada a saye ka da kudi." Faruk ya ce: "In da gaske ne wannan abubuwan da ke ciki, to kuwa... gobe Nigeria za ta san wanda Maleekh yake neman tozarta wa ta musamman ce......" asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE. page 7 to 8 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Washegari da safe, an farka da labari mai firgitarwa... “Ɗan Minister Maleekh ya yi Amfani da Ƙarfin Mulki da Kuɗi Wajen Cin Zarafin Ma’aikaciya A Gidan Rediyo.” A ƙasan labarin: An samu shaidu daga sahihan majiyoyi da faifan sauti da ke nuna yadda Mr. Maleekh, ɗan Minister Kaduna ya shirya ƙaryar shigar da ƙara domin tozarta wata yarinya ƴar ƙaramar gida mai suna Amal, wanda saboda ta ƙi amincewa da soyayyarsa ne yasa ya ci mutuncinsa a wurin aiki...” “Bincikenmu ya nuna cewa Maleekh ya tura saƙonni, ya haɗa magana da wasu jami’an tsaro, da nufin ƙaryata sunan Amal a idon duniya. Amma wasu daga cikin abokansa sun tona sirrin, suna goyon bayan gaskiya.” SASHEN MALEEKH.... Maleekh yana tsaye a falon gidan mahaifinsa lokacin da ya ga hotonsa da taken labari a babban plasma TV. Minister ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, ya sa Maleekh a gaba sai faɗa yake ta masa tare da faɗin "Maleekh... me wannan yake nufi? Wannan ai rushewar gida ne. Ka manta da kujerar da nake kai ne? Wannan ai zargin cin mutunci ne, da amfani da iko!"..... Maleekh yana ƙoƙarin kare kansa da cewa: "Dad, waɗannan maganganun duk ƙarya ne. Amal da abokinta ne suka shirya wannan domin su ɓata mun suna. Kawai saboda na ƙi su!"... Minister Ya ce "Enough! Sai an fara bincike. Kuma har a gama ba zamu so ka fito bainar jama’a ba. Zaka koma England kwanan nan. Kuma ka daina shiga harkokin gwamnati." Maleekh Idonsa ne ya yi jajir yana nuna ɓacin ransa, tare da tunanin hukuncin da zai yiwa Nasir da Amal... Bayan fitan mahaifinsa, maganar zuci ya fara yana faɗin "Na rantse da Allah, bazan bar Amal ta tsira ba. Zan tabbatar da cewa zata nemi gafara a idon duniya, kuma sai na sa an ɗaure Nasir, sai naga abinda za'a mun ..." SASHEN AMAL Amal tana zaune a ofishin lauya da Faruk ya haɗa ta da ita. Faruk ya nuna mata duk wasu hujjoji... Faruk ya ce da Amal: "Kinga? Wannan ba ƙaramin girgiza bane. Na fitar da labarin amma hakan zai sa Maleekh ɗaukan hukunci, domin ya shiga kololuwar ɓacin rai. Ki cigaba da saka ID card da recording a jikin ko’ina." Lawyer Ta ce "Zamu kai ƙara. Suna, aikinki, lafiyarki duk sun ci karo da sharri. Zamu nemi compensation da public apology." Amal cikin tsantsar natsuwa ta ce "A shirye nake. Amma ban so a ci mutuncin Maleekh ba, ina so ya san illar abinda yayi. Ya tuba, ya fahimta cewa ba kowa ne talaka bane marar daraja ...." Faruk yana murmushi ya ce "Wannan shine bambancinki da shi. Kin fi shi zurfin tunani da tarbiyya da daraja." SASHEN BABA LONDON A cikin gidan rawa, Baba Londo yana karanta jaridar yana karkarwa, gaba ɗaya ya gama tsorata ganin yanda ake ta maganar Maleekh... Baba Londo Ya ce "Na shiga uku... Nasir ya jan yo mana masifa! Maleekh zai iya fallasa ni idan ya gano ni ma na taimaka wajen shirya ƙaryar. In kuwa Amal ta kai ƙara, shikenam kashi na ya bushe, gwara Maleekh yana da gata amma Ni babu mai duba Ni ....." Ya latsa wayarsa, bugu ɗaya aka ɗauka, Baba London ya ce "Hello Nasir... Dan Allah, muyi magana da gaggawa." Nasir ya ce "Faɗan bada kai bane da maleekh ne don haka ka kwantar da hankalin ka...." A gaban ofishin gidan rediyo, Amal ta fito daga mota, tana sanye da doguwar riga mai kyan gani da hijabinta, Tana tafiya cikin nutsuwa, sai taga ƴan jarida suna ta ɗaukar hoto da tambayoyi..... Ɗan jarida 1: "Miss Amal, ya kike ji yanzu da gaskiyar ki ta fara bayyana? Kinyi sanyi a cikin rikicin da yawa ..." Ɗan jarida 2: "Shin akwai wani abu da kike so ki faɗa ga sauran mata da suke fama da cin zarafi a wuraren aiki?" Amal ta tsaya, ta kalli Faruk, wanda ke tsaye a bayanta, sai kuma ta fuskanci Camera... Tana faɗin: "Ina so duk wata mace ta sani ba dole bane ki ɗaga murya cikin tsawa domin a saurare ki. Ilimi da nutsuwa suna da ƙarfi fiye da hayaniya. Kuma ki yarda da kanki ko da duniya ba ta ganinki....." Ɗan jarida na 3 ya fashe da sowan farin ciki yana faɗin "Powerful words! Wannan ce jarumar Kaduna!" A kafar TikTok da Twitter, hoton Amal yana yawo tare da kalmarta: “Ilimi da nutsuwa suna da ƙarfi fiye da hayaniya.” Ana reposting da tags kamar #JarumarRayuwa #MaceMaiDaraja #NotAllHeroesWearSuits. Wata matashiya a bidiyo ta ce: "Ni Amal ce a cikin raina. Yarinya marar dukiya amma tana da wayewar zamani, Muna tare da ke!" ★★★★★ Maleekh na zaune a ofis ɗinsa a Abuja, yana kallon TV da bidiyon Amal ke yawo. Yana ji ana yi mata ƙirari ana cewa “Jarumar da ta kare martabarta ba tare da zagi ko cin mutunci ba...." Maleekh yana dafe da goshinsa a zabure ya ɓuga tebur gabansa da hannunsa, yana huci yana faɗin: “Amal! Sai kin dawo kin nemi gafara ta ko da dole ne!” A cikin ofishinta, Amal tana zaune ta samu ƙira daga babban lamba: “Office of the Governor” Governor yana wayar da murya mai sanyi, bayan Amal ta je ƙiran ya karɓe ta cikin darajawa tare da faɗin: "Amal, kin bamu mamaki. Kin ɗaukaka darajar mace a cikin al’umma. Ina so mu haɗu da ke domin baki wani kyauta ta musamman, na baki kyautar Gida da mota bisa jajircewa, domin na ji daɗin irin hali da tunaninki. .." Amal ta dafa ƙirjinta cikin mamaki ta ce: "Na gode Your Excellency. Na ji daɗin wannan kyautar...." Amal ta ƙara sa tare da sharar hawayen farin ciki... Kafin ka ce mai ko ina ya baza cewa Governor ya yi wa Amal kyauta ta musamman gida da mota da wasu kuɗaɗe... Bayan Amal ta koma gida itama Inna har da kukan farin ciki, tana farin cikin sun yi kuɗi su ma... Amal ta ce "Inna mun yi kuɗi amma bana taɓawa bane..." Cike da mamaki Inna take kallon ta sannan ta ce "to uban me zamu yi da ƙudin in ba taɓa wa ba? Haka kawai sai mu zuba musu ido muyi ta kallon su kamar madubi?....." Amal tayi murmushi sannan ta ce "Inna idan muka bar su zuwa gaba zasu yi amfani, zamu cigaba da zama a yanda muke yanzu...." Inna ta turo baki tare da kawar da fuska gefe ba tare da ta furta komai ba... Amal da ta fahimci haka, ta sa hannu a jaka ta ciro 50k ta bawa Inna tana faɗin "Ga shi Inna, dubu hamsin ya yi miki ko? nasan ba wani abun kirki zaki saya ba...." Inna da sauri ta juyo tare da sa hannu ta karɓa tana faɗin "ba ni! ba ni!! zasu mun amfani nikam a yanzu, kuɗin haram nake gudu bana halal ba, ato...." Murmushi Amal ta yi tare da kwantar da kanta akan cinyar Inna.... Wata daga cikin ma'aikatan gidan rediyo wanda suke tare da Amal.. mai suna Zulaihat tana zaune tana ƙiran waya cikin fushi, ta kasa ɓoye damuwar ta duk da bata bayyanar abinda ke damunta ba. Zulaihat fitacciyar ce da ake yiwa kallon jaruma mai class a gidan rediyon a shekarun baya kafin zuwan Amal, amma tin zuwan Amal tana ganin kamar ana barinta baya, shafin ta ya rufe, taurarinta suka daina haskawa dake bata kai Amal jarumta da tsayar da magana ɗaya ba... Zulaihat tana waya cikin hawaye take faɗin: "Look, Amal tana ta ɗaukaka ne kamar wata waliyyar Allah, alhalin ni na fara sanuwa kafin ita, Na san me zanyi da ita, za mu ga wanda zai ƙara reposting bayan wannan."... Cikin zafin rai ta kashe wayar sannan ta fara duba laptop dinta tana shirya wata ƙarya da za ta farfaɗo da wani scandal akan Amal tana hada hoton jabu na Amal da wani tsohon saurayi da ta taɓa yi masa hira a gidan rediyo, tana fassara hoton da kalmomin soyayya da cin amanar aiki..... Washegari da dare, wani asusun bogi (@_ExposedGistNG) ya wallafa hoton Amal da rubutun cewa: “Shin wannan ce jarumar da kuke yi wa ƙirari? Ga hoton Amal da wani babban ɗan siyasa suna soyayya cikin sirri a lokacin da take aiki... Kuɗin wane ne ke ɗaga ta?” #Scandal #AmalExposed #ƳarTakiJaruma A cikin awa ɗaya, comments sun fara zuwa da zagi da tambayoyi. Wasu na goyon bayanta, wasu kuma sun fara baza magana da zargi. Amma Amal bata ce komai ba tukun na amma ta ga duk abubuwan da suke faruwa, sai dai ta ɗauki hakan a matsayin jarabawa.... Amal tana zaune a ofishinta na gidan rediyo tana karanta comments cike da raɗaɗi.... Faruk da lawyer suna kallonta cikin tausayawa. Faruk Ya ce "Ki ce komai mana, Amal! Maza suna ta rubuce-rubuce, wasu sun fara janye goyon baya." Amal cikin nutsuwa Ta ce: "Faruk... Idan ina da gaskiya, ba zan buƙaci in ɗaga murya ba. Amma wannan karon zan maida martani. Amma ba da zagi ba ko cin mutunci ba, domin ba hali na bane...." Lawyer Ta ce: "Kiyi shirye-shiryen rubuta statement. Kuma mu fara gano waye ya wallafa wannan, za mu yi barazana da court order. Wannan cyberbullying ne...." Bayan sun gama tattaunawar su, daga baya Amal ta sanar cewa zata yi jawabi a tashar su na rayuwa FM.. An shirya zama, Amal na zaune a cikin studio ɗin gidan rediyo. tana fuskantar cemara ba tare da ado ko yanayin farin ciki ba, tana zaune cikin hijabinta, murya cike da natsuwa take faɗin: “Akwai wani abu da na koya a rayuwa, gaskiya bata buƙatar ihu. Kuma wanda ke da komai a zuciyarsa ba ya jin tsoron ƙarya da aka ɗinka masa daga waje. Na ga hoton da aka watsa kuma na san me ke ciki. Hoto da aka ɗauka shekaru biyu da suka wuce lokacin da nake hira da wani baƙo a studio. Wani da yake son wulakanta ni ta hanyar shirya ƙarya, sai ya fassara abin da bai fahimta ba. Ina da iyayen da suka koyar da ni tsoron Allah. Ina da Kakar da ta raineni da hawaye da addu’a. Kuma ba zan yarda a gina sunana a kan ƙarya da hasashe ba. Amma wannan abu ya koya min abu guda cewa, akwai mata da yawa da ake mana haka kullum ana ƙulla mana sharri saboda kawai muna da tsayin daka da nutsuwa. Don haka wannan bai shafeni ni kaɗai ba, Ya shafi kowace mace da ta gina kanta akan gaskiya kuma ake neman cin zarafin ta saboda dai ta ƙi lankwasuwa. Ina tare da ku. Kuma zan ci gaba da wakiltar ku cikin gaskiya da ɗaukaka....” Dakata wa tayi tare da sakin murmushi kaɗan, ta ƙara da faɗin: “Ba wai ni ce jaruma ba ku ne jarumai da kuke tsaye akaina. Na gode.” Ƙarshen tattaunawa... A kafafen sada zumunta TikTok, Instagram, da Twitter sun ɗauki bidiyon yana yawo kamar wutar daji. Mutane da dama sun fara reposting da kalmomin: #DignityNotDrama #AmalStandsTall #VoiceOfDignity Wani sanannen ɗan jarida ya rubuta cewa: “Wannan ba kawai magana bace, wannan darasi ne. Amal ta koya mana cewa mace mai gaskiya ba buƙatar shela.” Wata likita a Abuja ta rubuta cewa: “Ni ban san Amal da farko ba, sai yanzu ganin farko naji ta burge ni, zan so ƴaƴana su girma su zama kamar Amal.”... A wani sashen, Maleekh na kallon bidiyon Amal daga wayarsa, yana a zaune a cikin motarsa mai sanyi da leather seat. Ya dafe kansa, yana juyayi... a hankali ya furta: "Ta fi kowa. Wannan ba ƴar talaka ce kawai ba... wannan wata Queen ce. amma hakan ba yana nufin na goyi bayan ta bane...." Wani babban kamfani da ke da alaƙa da gwamnatin jihar, suna da hannun jari a gidan rediyon Amal ke aiki. Sun ƙira taro a sirrance. CEO ɗan manyan mutane, mai suna Alhaji Ma’aruf yana faɗin: “Wannan yarinya tana yawan fitowa da ra’ayoyi masu motsa mutane. Muna son kwanciyar hankali. Idan mutane suna sauraren Amal, ba za su saurari shugabanni irin mu ba.” Wani daga cikin su ya ce: “Za mu samar mata da wata hanyar da zata shigo cikinmu, mu rufe bakinta da kuɗi… ko kuma mu wanke ta gaba ɗaya daga kafar sadarwa.”... Washegari, Amal ta karɓi gayyata zuwa wani taro. A can ta iske babban mutum Alhaji Ma’aruf yana mata tayin aiki: albashi mai girma, gida, mota, kwangila. Amma da sharaɗi guda..... Alhaji Ma’aruf cikin ƙwarewa yake faɗin: “Kina da wayo, Amal. Muna son ki shigo mu gina Najeriya tare. Amma ki rage yawan fitar da abubuwan da ke ɗaga hankali. Duniya bata son masu sa mutane tunani sosai.” Amal cikin kwanciyar hankali ta ce: “Ina son ƙasata, kuma ina son gaskiya. Amma idan wannan tayin yana nufin in yi shiru akan abubuwan da ke damun mutane to ku ci gaba da neman wata mafita....” Ta miƙe cikin natsuwa ta bar wurin, kowa yana kallonta cike da mamaki... Bayan kwana biyu da faruwar haka.. Wasu saƙonni marasa suna sun fara shigowa wayarta: “Kada ki ɗaga murya fiye da haka…” “Ki zabi zaman lafiya, ko zaman lafiya ya ƙi ki.” “Mun san inda tsohuwar da ta raine ki take.” Inna jin labarin tashin hankalin da suke shirin shiga, sai kawai ta fashe da kuka... Amal fashe wa tayi itama da kuka tana rarrashin Inna tare da faɗin: "Inna in sha ALLAH babu abinda zai faru da mu, muna kan hanyar gaskiya, kuma Allah yana tare da mai gaskiya, ki kwantar da hankalin ki Inna...." Itama Inna kuka take tana rawar murya ta ce: "Amal ina tsoron wannan rayuwar da kike gudanar wa, ina tsoron rasaki Amal, in da hali ki bar aikin gaba ɗaya kizo mu zauna a gida..." Amal ta ce: "Kar ki damu Inna akwai lokaci..." Da haka Amal ta rarrashi Inna har suka yi bacci... ★★★★★ Maleekh kuwa cike da jin haushin Amal yake kwana yake tashi, gaba ɗaya ya tsani yarinyar har cikin ransa, cike da damuwa yake faɗin "Ni zata tozarta a idon duniya? ballagazar yarinya ƴar talakawa..." Cikin zafin rai ya nufi gaban mirror, nan ta ke ya fara farfasa mirror yana ihu, yana tarwatsa kayan ɗakin sa... Jin ihu yasa mahaifiyarsa ta shigo da gudu tare da ƙannen sa mata, daƙer Uwar ta riƙe shi tana rarrashin sa domin tinda abun ya faru ya kasa kwantar da hankalinsa, ko ci da sha baya samu damar yi, kullum a cikin tunani yake, takaicin sa tinda yake babu macen da ta taɓa tozarta shi sai Amal da take talaka faƙiriyar yarinya.... Sai da iyayensa suka tura shi England kafin ya samu kwanciyar hankali, domin a Nigeria kullum zafin takaicin Amal hana shi sukuni yake, da ya koma wa can kuwa sai abubuwa suka fara fita masa a rai, ya rage damuwa amma ya kasa manta da Amal... Dake a can akwai masu kula da shi sosai, basa barin sa yana shiga damuwa, da haka ya koma normal kamar bai je Nigeria ba, amma idon sa akan Amal yake a TV da laptop ɗin sa...... ★★★★ Washegari bayan Amal ta kammala aikin ta na yau a gidan rediyo Rayuwa FM...... Amal ta fito daga gidan rediyo Rayuwa FM tana shirin tsallaka titi domin komawa gida, sai ga wata baƙar mota ƙatuwa tazo ta sha gabanta tare da jan yo ta ciki suka wuce da gudu ba tare da mutane sun an kara ba, Wani tsararren gidan gomnati aka kaita wurin da Governoni da manyan ƴan siyasa suke taruwa, Zaunar da Amal akayi a ƙasin carpet an rufe mata baki da fuska gam, a lokacin aka cire mata baƙar hular da suka rufe mata fuska da baki, idonta ne suka sauƙa akan wasu manyan ƴan siyasa wanda bata taɓa ganinsu ba sai a poster da kuma jin labarin su, yau ta gan su a zahiri, Ga wasu manyan security a tsaye a gefe guda suna riƙe da bindigun su, an tsawatar wa Amal sosai tare da barazanar zasu sa a kasheta idan ta cigaba da fito da gurɓatattun bayani akan su,. Suka zazzage ta tare da ƙiranta da ƴar talakawa, sunyi barazanar zasu kashe ta kuma su kashe Kakarta kuma babu hukumar da ta isa ta hukunta su domin sune suke riƙe da hukuma, Amal ko kaɗan bata ji tsoron su ba ko fargaba haka ta tsaya tana musayar yawu da su, cikin jarumta..... Wani dattijo mai tumbi wanda ta taɓa ganinsa a poster na zaɓe, ya buɗe baki cikin murya mai cike da izza ya ce: "Kece Amal Abdulsamaad? Wannan baƙin ciki da kike yaɗawa a radio da social media zai ƙare yau. Mun gaji da sharrinki!"... Wani ɗan siyasa ya ƙara da zazzafar murya cewa: "Ƴar talakawa mai rainin hankali! Me kika sani game da mu har kike shisshigi cikin rayuwar mu? Mu muke riƙe da wannan ƙasa!" Amal ta ɗago kai, tana kallon su ba tare da rawar murya ba, duk da hannunta a ɗaure yake. Muryarta cike da ƙwarin gwiwa ta ce: "Na sani, ku da kuke cewa kuna riƙe da ƙasa, ƙwarai kun riƙe da zalunci. Amma Allah yana kallon ku. Ku ne kuka haddasa halin da talakawa ke ciki, kuna sace hakkin marasa galihu kuna fakewa da dokokin da kuka rubuta da kanku." Wani daga cikinsu ya ce: "Zamu kashe ki! Kuma ba wani hukuma da zai sani balle yayi bincike!" Amal ta ce: "Ku kashe ni, amma gaskiya ba zata mutu ba. Ina jin kunyar cewa ni marainiya ce kuma talaka wanda bani da halin taimaka wa talakawa, amma ni ba zan ji kunyar faɗin gaskiya ba. Ku ne matsalar ƙasar nan, kuma ku ne dalilin da yasa yaran da ke da basira kamar ni ke cikin wahala. Sai ku ke raina mu, kun hanamu ci gaba a rayuwa!"... Wani babban jami’i ya matso da bindiga a gefe yana huci, yana kallon Amal cikin ƙyashi. Amma Amal ta cigaba da magana cikin fushi da karyewar zuciya: "Idan da gaske kuke kuna da iko, to me yasa kuke tsorata da murya ta? me yasa baku so na bayyanar da gaskiyar halin da mutane ke ciki? Wannan ƙasar ba mallakin ku bace. Ku ne kuke damun ta!" Sauran 'yan siyasan ne suka fara kallon juna cike da mamakin ƙarfin gwiwar yarinyar. Ba yanda suka iya da ita haka suka bada umarni a ɗaure ta a ɗaki har sai sun yanke hukunci akan rayuwarta.... An nemi Amal an rasa, Inna ta shiga damuwa, gidan rediyo Rayuwa FM tayi sanyi jin labarin anyi kidnapped Amal... A Rayuwa FM, ma’aikata sun ruɗe. Sun katse shirye-shiryensu, suka bada sanarwar bacewar Amal. Jama’a sun fara magana a gari, an fara ƙirarin za'a yi zanga-zanga na rashin tsaron lafiyar marubuta da 'yan jarida masu gaskiya. A gefe guda... Inna tana kuka a gida, tana addu’ar Allah ya fitar mata da Amal.... "Ya Allah ka dawo mun da jikata lafiya... Amal, ki dawo gida mana." A nesa, cikin ɗaki a ƙasar england, Maleekh ya zuba coffee a cikin cup, yana sanye da singlet da 3quarter. Ya kunna laptop, yana kallon rahoton da ke cewa Amal ta ɓace. Sai ya saki wata ƙaramar dariya mai cike da izza yana faɗin: "that's good! Nasan wannan lokacin zai zo, yarinya marar kamun kai, zaki gane da ruwa ake shayi a hannun manyan mutanen Nigeria.... Ya yi wasu maganganu da rashin damuwa akan abinda ya faru da Amal, Sannan ya furta: "Let her learn the hard way, This is Nigeria, ba wani yanki bane inda 'yan talakawa ke zagin manya su tsira lafiya." ★★★★★★ A cikin ɗakin da aka ɗaure Amal... Tana zaune a ƙasa, an ɗaure hannayenta da ƙafafunta, amma zuciyarta bata ɗaure ba. Kamar mai jin ƙarfin wata iska daga sama, ta ɗago kai tana sauƙe ajiyar zuciya. A hankali ta fara karanta addu’o’i da ayoyi cikin ranta, ba ta yi kuka ba sannan ba ta girgiza ba, amma jikin ta yana bada wani sanyi da tsantsar jarumta. ɗaya daga cikin jami’an tsaro ne ya matso da abinci ya ajiye a gabanta ba tare da ya kalle ta ba, ya since mata hannaye tana gamawa aka ƙara ɗaure ta .. A lokaci guda a waje... Wasu daga cikin ma’aikatan gidan gomnati suna ta waya da mutane daban-daban suna yunkurin ɓoye labarin bacewar Amal. Amma a waje, duniya ta fara motsawa. Rayuwa FM sun fitar da sanarwa cewa: "Mun rasa ɗaya daga cikin ƙwararrun ma’aikatan mu, Amal Abdulsamaad, bayan fitowarta daga ofis jiya da yamma. Muna ƙira ga hukumomi da jama’a da su taimaka wajen gano inda take..." Social Media ta karaɗe da hoton Amal da rubuce-rubucen: #FreeAmalNow #JusticeForAmal #TruthIsNotACrime Gaba ɗaya gari ya ɗau zafi. Ƴan jarida da kungiyoyin kare hakkin ɗan adam sun fara yawo da labarin. Wasu fitattun mutane suna wallafa goyon baya gareta, wasu suna cewa: “Kalmar gaskiya duk wanda ke faɗin ta sai an ɗauke shi”, hakan ya jefa tsoro cikin zukatan wasu, amma ya ƙara juriya cikin zukatan wasu da dama. A wani ɓangare kuma... Maleekh yana zaune yana kallon wannan hayaniya a tv. Cikin zuciyarsa yana fargaba amma a fili sakin murmushi ya yi, Ya ƙira Rikky Blaze ta video call yana faɗin "Rikky, ina so ka kawar da wancan yarinyar daga labarai... ba damuwata me za ka yi ba, amma dole muryarta ta ɓace!" Rikky ya ce: "She’s already disappeared, boss. The problem is people won’t shut up." Maleekh ya ce: "Then shut them up. Everyone has a price.... Bari ta gama shan wahala, zata gane rayuwa ba wasan yara ba ne. A Najeriya take ƙasar da ‘yan ƙasa irin ta ba su da wata kima idan sun raina manya. Wacce 'yar talaka ce za ta fito tana zagin giwa ta kuma yi tsammanin zata tsira? Ai sai ta ɗanɗani azaba, ta gane cewa hauka da raini na da farashi mai tsanani!" Rikky ya ce: "Ogah! Yarinyar tana da taurin kai ne, sannan tana da jarumta dubi yanda ta tozarta sunan ka a ƙasar...." Maleekh cike da mugunta yake faɗin: "Zata sha wahala ne, zan koya mata darasin da zai ɗaure mata kwakwalwa har abada. zan nuna mata cewa ƙasata ba kasar tatsuniya bace, Najeriya ne! Inda ‘yan talaka ba su da murya idan sun taka layin manya. Wacce ce ita? Wacce 'yar raini ce da za ta fito tana zagin giwa a gaban jama'a? Ai sai ta ɗanɗani wahala, ta gane cewa a Najeriya, rainin hankali yana da farashi. Kuma wallahi, zan tabbatar an biya wannan farashin sau biyu!...." Yana huci ya kuma cewa: "ƴar matsiyata jikan talauci, ban da talakawa wa zai tsaya ɓata lokacin sa wurin sauraron ta...." Rikky ganin yanda ran Maleekh ya yi matuƙar ɓaci yasa shi cewa: "Sorry Ogah...." Maleekh Yana magana idonsa na haskawa da ƙiyayyar Amal yana faɗin: "A gaban duniya za ta fallasa ni? Ni Maleekh?! Wacce ce ita? Wace ‘yar tasha ce zata tsaya a gabana ta ce wai zata yi magana akan gaskiya? Gaskiya? A ƙasar da kowa ke sayar da gaskiya don ceton kansa?" Zama ya yi daga tsayen da yake ya miƙar da ƙafa tare da durƙar da kansa akan table ɗin gaban sa yana magana yana ƙwanƙwasa teburin da yatsarsa: "Zan koya mata darasi ta hanya mai tsanani. Zan nuna mata cewa Nima ɗan Najeriya ne, Ba a waje nake ba da ‘yan talakawa ke wulakanta manya su tsira. Wallahi sai ta gane cewa rainin hankali a kasar nan yana da tsada, kuma zan tabbatar ta biya da wahala." "Ka yi mata fiye da haka," Rikky ya ce shima cikin ɓacin rai. Sannan ya ci gaba da cewa "Za mu nuna mata yadda ake wasa da wuta a ƙasar da ba ruwan kowa da gaskiya." Maleekh ya lanƙwasar da kansa, cikin sassanyar murya ya ce: "Lokacin dariyarta ya ƙare. Yanzu lokaci ne na hawaye. Kuma zan tabbatar hawaye ya maye gurbin karfin halinta." Daga nan ya kashe wayar, yana kallon fuskar Amal daga wani video da aka ɗora a online yana jin wani abu mai nauyi a zuciyarsa, wanda ya kasa fassara shi, ya ce: "Me ya sa tunaninta baya barin kaina, duk da irin ƙiyayyar da nake mata?" ---★★★ A cikin ɗakin Amal... Ƙofar ɗakin aka buɗe da ƙarfi. An kawo wani babban ɗan siyasa wanda shine shugaban hukumar ɗaya daga cikin manyan bangarorin gwamnati. Ya zauna gaban Amal yana kallonta tamkar ba mutum ba: Shugaban Hukuma ya ce: "Idan kin yarda zaki zauna lafiya to ki daina magana, zamu baki gidan zama, mota, da naira miliyan ɗari. Amma sai kin yi alkawarin komai ya ƙare." Amal ta ɗago kai cikin ƙarfin zuciya tana murmushi ta ce: "Ba zan siyar da gaskiyata da farashi ba. Ko zaku bani duniya gaba ɗaya, idan talaka yana kuka saboda zaluncin ku, zan cigaba da magana... In har na mutu a haka, Allah zai karɓi hakkin talakawa da bakin da suka nema masa." Wani security ne ya shaƙeta da hannu yana zazzaro mata ido amma shugaban ya dakatar da shi yana kallon Amal da tsantsar mamaki da takaici ya ce: "Bata tsoron mutuwa.... Haƙura ya yi, shima ya bata wuri... A gida... Inna ta kwanta rashin lafiya. Mutane sun zo suna ɗaukar nauyin kulawa da ita. Tana ta kuka tana faɗin: "Allah ka dawo mun da Jikata lafiya... Amal zata iya shiru amma ba zata iya cin zalunci ba..." Zuwa yanzu... Gwamnati tana cikin tashin hankali. 'Yan jarida daga kasashen waje sun fara bibiyar batun. Tura ta kai bango. Haka nan mutane sun fara tashi da zanga-zanga a Abuja da Kaduna, suna ɗauke da hoton Amal tare da tambari: “TA BA Da ƘARFI GA MURYAR MARASA ƘARFI!”.... Wata mace ce ta shigo cikin ɗakin da Amal take, Tana sanye da kayan masu aiki, ta zauna kusa da Amal cikin sautin muryar da ba kowa ke iya ji ba. Matar ta ce: "Sun ce in kawo miki abinci… Amma na zo da saƙo daga waje. An fara neman ki. Duniya na magana. Ki ƙara juriya, zan dawo da labari." Amal ta zuba mata ido da hawaye a idonta ba tare da ta iya cewa komai ba. Matar ta latsa mata hannu a asirce, ta miƙa mata ɗan karamin zare alamun cewa ba ita kaɗai bace a cikin gidan da ke goyon bayanta. A GIDAN GWAMNATI... Wasu daga cikin shugabannin gwamnati sun fara yin shakkar tsare Amal. Labarai sun bazu zuwa kasashen waje. Ana barazanar dakatar da haɗin gwiwa da gwamnati idan ba a fito da bayanin da ya shafi Amal ba. Ministan Cikin Gida ya fuskanci matsin lamba. Ya ƙira taro na manyan jami'an tsaro da 'yan siyasa da su ka tsare Amal. Cewa: "Duk abinda za ku yi, ku yi shi da wayo. Idan aka samu gawarta a matsayin evidence, mu ne za mu durƙusa. Kiyasta illar hakan..." A RAYUWA FM... An gudanar da wani gagarumin shiri na musamman da aka ƙira "AMAL, MURYAR GASKIYA". A cikin shirin, an sake kunna sautin wasu daga cikin tattaunawarta da talakawa da labarinta na masoya biyu da aka kashe wanda ya taɓa zuciyar mutane a baya. A ƙarshe anchor ya furta: "Idan har gaskiya ce laifi, to duk mai gaskiya zai ɓace kamar Amal... Amma Amal ba zata ɓace ba. Rayuwarta ta riga ta zama muryar al'umma!" A CIKIN ƊAKIN MALEEKH, ENGLAND... Yana zaune cikin duhu, kofin coffee yana hannunsa, yana kallon projectorin da ke nuna masa tashar Rayuwa FM da yadda mutane ke zanga-zanga a ƙofar gidan rediyon da hoton Amal a saman banner. Ya yi murmushi cikin rashin jin daɗi, yana ƙara karanta wani email da Rikky Blaze da ya turo masa: Rikky yana cewa: "Sir, we may need to drop the girl soon... The pressure is building. She may die, but her voice won’t..." Maleekh ya runtse idanu yana faɗin: "Damn it, Rikky... why is this girl messing with my world?" Ya jefa glass cup na coffeen a bango yana buga ƙafa cikin fushi. Daga nan ya ɗauki waya ya ƙira wata lamba yana faɗin: "Release her. But make sure she learns something first... Let her walk out, but her heart will broken." TO PAH TASHIN HANKALI, ASHE DAI ƁATAN AMAL DA SA HANNUN MALEEKH🤔🤔 A CIKIN GIDAN GOMNATI...CIKIN DARE! Amal tana zaune a cikin duhun ɗaki. Aka buɗe ƙofa, wasu mutane biyu masu baƙaƙen kaya sun shigo. Ba tare da an yi mata komai ba, suka kwance ta, suka cire mata ɗaurin baki. Mutum na biyu ya ce: "Zaki koma gida. Amma ki sani... wannan ba ƙarshe ba ne. Wannan faɗa ce tsakanin ƙarfi da ƙasa. Ki nutsu, Amal..." Suka sa mata fuskar rufe ido (eye mask), suka fitar da ita daga gidan. Sai da suka yi tafiya mai nisa sosai a mota kafin suka fitar da ita a cikin duhu suka cilla ta cikin wata mota, suka bar ta kusa da wani titi mai duhu inda wasu masu mota suka same ta da safe.... LABARI YA KARAƊE KO INA... An same ta a rana mai ɗumi, da 'yan sanda da ma'aikatan Rayuwa FM suka kai ta asibiti. Ta zauna jinya tsawon makonni biyu sakamakon fesa mata tiyagas da akayi.. Inna ta yi kuka sosai tana rungume da ita, tana faɗin: "Amal... na riga na sani, ke ba za ki yi rayuwa kamar sauran mata ba... Amma Allah yana tare da mai gaskiya!" Bayan wasu kwanaki, A gaban tagar asibitin da rana ke haskawa, Amal na zaune a kan kujera sanye da farin hijabi da doguwar rigar marar ado. Kamar wacce ba ta da ƙarfi, amma idan ka duba cikin idanunta zaka ga karfi da sabuwar fahimta. Inna tana gefenta, tana riƙe da hannunta, tana faɗin: "Na ce miki ki bar harkar siyasa, amma na fahimci ba ke ki ke zaɓar wannan hanyar ba, kamar dai mutanen ki ne ke zaɓar miki wannan hanyar ta fuskar tausayi...." Amal ta juyo, da hawaye a idanu cikin murmushi ta ce: “Inna, da ace ba ni aka yi wa wannan ba, wata rana wata ce za ta fuskance shi. Amma yanzu da na riga na faɗa ciki wallahi zan kare kaina, da sauran masu rauni da ba su da murya.” Inna cikin kalar tausayi ta rungume ta tare da faɗin: "Allah ya cigaba da tsare mu gaba ɗaya..." ★★★ Kwana biyu bayan fitarta daga asibiti, Amal ta koma Rayuwa FM. Kowane ma’aikaci ya rungume ta cikin tausayawa suna jajanta mata, Sun ajiye mata wani guri na musamman a matsayin “Mai Tsaron Gaskiya”. A shirin ta na farko bayan dawowarta, ta fara da ƙasa da murya, tana kallon microphone kamar tana kallon duniya: Ta ce: “Na rayu a inda yawancin mutane ke barin ran su. Suka ce zan mutu, amma Allah ya raya ni. Na dawo da murya ta, ba don jin daɗi ba sai don kare gaskiya.” Jama’a a gari sun fara yi mata kallon girmamawa fiye da da. Tashar Rayuwa FM ta karɓi goyon baya daga ƙungiyoyi na duniya da kafafen watsa labarai na kasashen waje. Maleekh: Tashin Ƙiyayya da Shirinsa na Dawo Nigeria A cikin ofishin Cash Empire da ke England, Maleekh na tsaye gaban mirror. Yana kallon kansa da gilashi a idanu, yana sanya necktie. A gefensa Rikky Blaze ya tsaya da wani file mai taken: “Project: CashTalk FM Abuja Launch.” Rikky ya ce: "Kafafen yaɗa labarai sun fara canza salo, Rayuwa FM da Amal sun fara samun ƙarfi da motsin da ba kowa zai iya dakatar da su ba."... Maleekh ya juyo cikin fushi. Idonsa ya yi jajur. Ya ce: "Don dakatar da murya, ba sai ka rufe ta ba. Kana nutsar da ita ne da hayaniya mafi ƙarfi. Mu yanzu muna ƙirƙirar murya da ta fi tata ƙarfi...." Ya kama jacket dinsa, ya fesa turare mai ƙamshi da tsada yana faɗin: “CashTalk FM za ta zama gidan ‘yan Nigeria masu iko. Ba gidan gajiyayyu ba. Ba wurin kuka da hauka ba .....gida ne na gidan makamai da babbar murya. I’ll give them the opposite of Amal.” ★★★★★ Maleekh ya iso Nigeria da ƙungiyar sa a boye. A wani sirrin fili kusa da Maitama, an fara ginin CashTalk FM. Tashar da ke da fasahar zamani fiye da Rayuwa FM. Ya sanya mutane su fara neman sabbin masu gabatarwa amma duk wani tallace-tallace yana da manufa guda: Yi wa Amal ƙasa a gwiwa da jawo hankalin matasa daga gareta. Maleekh yana so ya yi ganawar sirri da Amal... Yana maganar zuci a yayin da yake zaman kaɗaici shi kaɗai domin a yanzu ya zaɓi ya yi maganar sirrin sa da zuciyar sa a kan ya sanar wa wani, domin ya koyi darasi a gun abokinsa Nasir.... "Ba sai na kashe ta ba. Zan goge ta a hankali… da suna, iko, da tasiri. Kafin ta gane me ke faruwa, zata dawo ita kaɗai babu kowa a gefenta.." 🔊 GIDAN REDIYO RAYUWA FM. ZUWAN MALEEKH CASHBANK A KADUNA Washegari da safe Amal na zaune a ofishinta mai tsabta da kyau, tana gyara wasu takardu. Wata ma’aikaciyar FM ta shigo da hanzarin ta Ma’aikaciya ta ce,: “Amal, akwai wani mutum daga Abuja... ya ce sunansa Maleekh Cashbank, ya ce ke ya zo nema.” Zuciyar Amal ne ta buga da ƙarfi. Ta ɗago kai da mamaki da tausayi a lokaci guda. Amal Tayi shiru na ɗan lokaci sannan ta ce... “Shigo da shi.” Bayan ýan seconni. Ƙofar ce ta buɗu, sai ga Maleekh ya shigo sanye da suit mai kyan gaske da tsada, yana ɗauke da tabarau. yana mata kallon sama da ƙasa kamar wanda ya zo yi wa ƙasa gadin mulki. Yana dubanta cikin raini, kamar bai san darajarta ba. Ya zauna a kujera yana ƙare ta da kallo daga sama har ƙasa, sannan ya murmusa da wulakanci ya ce: “Toh, ke ce Amal? Ashe ba da microphone kawai kike da ƙarfi ba... a zahiri sai na gane ke ‘yar talakawa ce dai dai misali.” Ya yi mata magana ba tare da ya nuna ya santa ba, kamar bai taɓa sanin ta ba haka yake ta yatsina fuska... Amal na zaune ba tare da ta yi motsi ba, tana kallonsa ido cikin ido. cikin ladabi ta ce: “Na gode da ziyara. Wannan gidan rediyo ne na kowa da kowa.... Maleekh ya ce: "So... kece Amal da ake ta surutu a social media? Muryar marasa gata... ƴar talakawa da take firfitar da batun siyasa kamar wata jagora?" Amal ta kalli agogo sannan ta kalle shi cikin kulawa ba tare da damuwa ba Ta ce: “Ni ce. Barka da zuwa Rayuwa FM, gidan da yake sauraren kowa, ba tare da fifita darajar mutum bisa dukiya ba.” Maleekh yana dariyar raini ya ce: “Kina da ƙwarewa, zan ba ki hakan. Amma kuɗi basu tare da ƙwarewa a Nigeria. Na zo ne in ba ki wata dama. Ki bar wannan gidan rediyo mai ɗan ƙaramin tasiri, ki zo CashTalk FM tashar da zata fi Rayuwa FM nesa da gani.” Amal ta saki murmushi cikin nutsuwa ta ce: “Dama tana iya zama mai kyau, amma ba kowacce dama ce ta dace da kowane mutum ba. Rayuwa FM ba ta ciyar da ni kuɗi amma ta ciyar da ni gaskiya da ƙaunar talakawa.” Maleekh ya ce: “Kina nufin ba kya son ƙaruwa? Kina son ki zauna da ƴan talakawa har abada? Kina gudun cika mafarkin ki ne? ko kina jin tsoron canji?” Amal ta ce: “Ina son ƙaruwa. Amma ba zan sayar da zuciyata ba saboda hakan. Na fi son in bar tarihi da murya mai amfani fiye da na bar makudan kuɗaɗe da aka samu ta hanyar wulaƙanci.” Maleekh ya daka tsaki, yana ƙare ta da kallo Ya ce: “You talk too much for someone who is replaceable. Don’t forget, I can build a station, create a voice louder than yours, and bury your name in days.” Amal ta gyara zama, ta ɗaga kai cikin murya mai sassauci ta ce: “To bury someone’s name, dole ne ka goge, yadda sunan tasa wasu suka tashi domin binne ta. Kuma Maleekh murya ba ta girma da speakers, son samu ta girma da gaskiya.”... Shiru ne ya ratsa ofishin. Maleekh ya kasa ce wa komai. Ya kalle ta da wani irin kallon ƙiyayya da mamaki.... Maleekh a hankali ya furta “Hmm... interesting.” Ya juya ya fita ba tare da sallama ba. Amal ta lumshe ido, ta ce a ranta... “Da wuya babban mutum ya yarda da ƙaramin murya, sai dai idan muryar tana da gaskiya.”..... Yayin da Maleekh ya shigo ofishinta a Rayuwa FM, Amal ta riga ta kunna ƙaramar mic recorder da ke haɗe da tsarin studio ɗin su. Ba mic ɗin da ake gani ba ne, amma yana da ƙarfin ɗaukar duk wata magana da ta faru a cikin ɗakin. A zuciyar Amal tana faɗin: "Zan bar duniya ta saurara da idanuwanta. Zasu ga wanda suke ƙira ‘jagoran zamani’ da ainihin halayensa." 📻 'ON AIR' BA SANI BA SABO!!!! Tattaunawarsu da suka cika da wulakanci, kaskanci da rainin hankali daga ɓangaren Maleekh ta cigaba kamar yadda muka tsara a baya. Amma wannan karon duk maganganun suna tafiya kai tsaye zuwa wani system na backup audio a cikin ofishin Amal, kuma daga baya wani technician ya yanke hukuncin ya ɗora su a shafin YouTube da X (Twitter). Bayan awa guda Maleekh ya bar FM, recording sautin yanda ya ƙasƙantar da Amal ya bazu kamar gobara! Mutane sun fara posting da hotunan fuskarsa da sautuka na yanda yake cewa: “Ke ƴar talakawa ce kawai... ki gode da na zo…” “I can bury your name in days!” 👇 (Zan binne sunan ki cikin ƴan kwanaki...) “CashTalk FM za ta maye gurbin wannan ƙaramar tashar ku...” 🔥 Comments a social media suka fara tashi kamar haka: @ArewaRight: “Shin wannan ne shugaban da zai kafa sabon gidan rediyo? Me ya sa yake wulakanta mace mai gaskiya?” @NaijaWoke: “Yadda Amal ta ba shi amsa cikin nutsuwa ya nishadantar... Maleekh ya ci karo da ƙaramar mace mai girman zuciya.” @TalakawanVoice: “Idan yana da gaskiya, me ya sa yazo da barazana da cin mutunci? Kuɗi ba su da daraja idan babu mutunci.” Haka maganganu suka rinƙa yaɗuwa .... MALEEK CASHBANK NA FUSKANTAR RIKICI A daren nan, PR team ɗinsa a London da England da Abuja sun shiga tashin hankali. Yana kallo a gida, yana shan coffee, sai ya ga trending topic: #WhoIsMaleekCashbank #IStandWithAmal #TalakawaMukaNe Ya finciki remote ya buɗe rikodin yana sauraro da ido wujiga-wujiga... Maleekh cikin zafin rai Ya ce: "Taya wannan sirrin ya fito fili?!".. Ya jefa kofin coffee ƙasa da karfi. Kunnensa yana ƙara kamar sauro. yana faɗin: “She played me... she outsmarted me!” (Ta yaudare ni… ta fi ni wayo!"). Washegari, kafafen yaɗa labarai sun fara ɗaukar labarin. Wasu suna gaya wa Amal "kin farka mana idanunmu", wasu kuwa suna tambayar: "Shin Maleekh da yake shirin kafa rediyo, haka zai kula da ma’aikatansa?" Rayuwa FM ta samu karɓuwa sosai. Amal ta koma bakin aikinta kamar ba abun da ya faru, amma ƙarfin ta ya ninka nasa sau ɗari. A labarai ana sanar da labarin MALEEKH... Maleekh Cashbank ɗaya daga cikin attajirai mafiya ƙarfi a Najeriya, ɗan asalin Kaduna ne, amma mahaifinsa babban ɗan siyasa ne mai tarin dukiya wanda ke zaune a Abuja. Shi kuma Maleekh ya kwashe rayuwarsa a ƙasar Ingila yana gudanar da wasu kasuwanci kafin ya dawo don kula da sabon tashar rediyon sa CashTalk FM da ke Abuja. Maleekh ba ƙaramin fusata ya yi ba, ya yanke hukuncin komawa tashar rediyo inda Amal take aiki... A cikin motar sa mai tsada, yana sanye da farin suit, baƙin glass, da ƙamshi mai ƙayatarwa. Yana tunanin tashar rediyo Rayuwa FM da ke Kaduna inda Amal ke aiki... Bayan isar sa ko tsayawa bai yi anyi mata sallama cewa ya zo ba, kai tsaye ya kutsa ciki... Da ƙarfi ya buɗe ƙofar office ɗin ta har sai da ta tsorata, tsaya wa ya yi yana kallon ta cikin takaici... Itama miƙe wa tayi tsaye ganin Maleekh... Yana da niyyar tattaunawa da ita a fili, amma ba tare da sanin cewa Amal ta ƙara kunna mic ba domin duk abinda zai faɗa ya isa kunnuwan al’umma kai tsaye. Maleekh yana kallon Amal daga sama zuwa ƙasa Ya ce: “To me kike tunani da har kike yawo kina faɗin magana kamar ke ce mai kula da rayuwar al’umma? Me kika sani game da siyasa da iko? Kin taɓa ganin naira miliyan ɗaya da idon ki kuwa?” Maleekh tsabar kansa ya ɗau zafi bai san wani magana yake yi akai ba, haka zuciyar sa take harbawa tana bugawa da ƙarfin gaske... Amal ta ƙyalkyale da dariya cikin kwanciyar hankali ta ce: “A'a, ban taɓa gani ba. Amma na taɓa jin yunwa, na taɓa zama da kakata da safe ba tare da mun ci abincin rana ba. Na kuma san cewa duk wanda bai ji zafin talauci ba, bazai iya jin raɗaɗin talaka ba.” Maleekh yana girgiza kai ya ce: “That’s why you’ll always be poor. Ke da kika yi tashin baƙin ciki, me zai canza? Wannan shine dalilin da yasa CashTalk FM zai ɗauki ragamar rediyo a Nigeria. Ku dai Rayuwa FM sai ku ci gaba da sauraron kan ku ...” Amal cikin nutsuwa, ba tare da ɗaga murya ba ta ce: “Mu dai ba mu da ruwa da kuɗin ku. Amma muna da murya. Muryar da zata faɗi gaskiya koman zafi. Kuma wallahi, idan muryar talaka ba zata kai ga wayar da kai ba, me zata yi?” A lokacin jama’a da dama sun fara bibiyar shirin a wayoyinsu da rediyoyi. Sun fara rubuce-rubuce a social media: "Shin wannan Maleekh Cashbank mai yake nema ne?" "Wai da gaske yana ƙasƙantar da 'yan Najeriya haka?" "Amal tana da gaskiya! Muryarta tana buɗe mana ido." Maleekh a hankali, ya fara lura da cewa tattaunawarsu ta na fita kai tsaye. Ba shakka wannan sauyi ne da zai fara tayar masa da hankali a fagen da ya raina muryar talakawa..... NEXT NEXT NEXTT *MASU KARATU BANA GANIN ZAFAFAN COMMENT ƊIN KU, IN BAKWA TSOMA BAKI CIKIN RIKICIN AMAL DA MALEEKH TAYA ZAN SAN CEWA CAKWAKIYAR NA TAFIYA YANDA AKA TSARA ? PLEASE A DAGE DA COMMENT, SANNAN INASON GANIN YAWAN ÝAN TEAM ƊIN AMAL DA MALEEKH....* asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE. page 9 to 10 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Maleekh na tsaye gaban Amal, yana ƙoƙarin tursasa nata ra'ayi da tsoran kuɗi, amma ba tare da sanin cewa mic na kunne ba. Amal kuwa a zuciyarta akwai kuzari da jarumtar da ba a iya siye da kuɗi. Amal.ta miƙe cikin nutsuwa, idonta cikin na Maleekh Ta ce: "Ba na buƙatar kuɗin da zai sa inyi shiru akan gaskiya. Ka duba mu a matsayin ƴan ƙasa, sannan ka duba kanku a matsayin sama da dokar ƙasa. To ka sani Allah yana sama da dukanmu, kuma kowanne ran mutum yana ƙidaye." Maleekh ya saki dariyar yaƙe tare da faɗin: "Wai ke da wannan muryar za ki canza duniya? Ke da babu ko rigar kwana guda mai kyau a jikin ki?... Ki tsaya lafiya Amal, domin wannan duniya ba ta talaka ba ce." Amal ta juyo tana kallon mic da wayar laptop ɗin dake kusa ta ce: "To ka tambayi duniya, daga yau... wacece Amal? Kuma wane ne Maleekh?" Kafin Maleekh ya farga, ɗaya daga cikin ma’aikatan Rayuwa FM ya shigo da hanzari yana nuna masa wani bidiyo dake yawo a internet, duk maganganun Maleekh da zagin da yayi sun riga sun bazu.... Ma’aikacin ya ce: "Sir, the whole of Nigeria is listening. Hashtag ‘#AmalTheVoice’ is trending number one. Your brandCashTalk FM is under fire." Maleekh ya tsaya cak! Yana kallon bidiyon kansa da Amal, yana jin yanda jama’a ke commenting: "Wannan ba magana bace daga mai hankali." "Maleekh ya nuna mana irin tsanar da attajirai ke yi wa talaka." "Ina tare da Amal. Muryarta tana wakiltar miliyoyin da ke cikin shiru." Cikin daƙilalliyar zuciya Maleekh ya haɗe tafin hannunsa yana kallon Amal wacce ta zamo wata alama ta ƙarfi da jarumta ba tare da ta buƙaci ƙarfi ko asali ba. Amal ta ce cikin ƙasa da murya... "Mu da kuke gani ba komai bane. Amma idan aka buɗe mana hanya, zamu ɗauki makamai da basira ba bindiga ba, sai ilimi."... Maleekh cikin ƙosawa da fushi yana furta a hankali "This is not over. You will regret this." Amal ta kalle shi kai tsaye cikin idanu sannan ta ce: "To ka dawo lokacin da za ka zama ɗan adam kafin ka zama ɗan siyasa ko ɗan kasuwa." A lokacin da labarin ganawar Maleekh da Amal ya karaɗe gari a karo na biyu, mutane da dama sun fara jin juyayi da mamaki bisa irin rashin mutuncin da Maleekh ya nuna a cikin gidan rediyo. Sai dai shi bai sani ba cewa Amal ta kunna mic ɗin rediyo a ɓoye kafin ya fara magana. Kowane harshensa da ra'ayinsa na ƙasƙantar da 'yan talakawa da ɗaga kai kan kuɗinsa da sunan mahaifinsa da siyasa ya bayyana fili ga jama’a. Jama’a sun ɗauki zafi Mutane sun fara tambaya da zargin cewa "Shin wannan shi ne wanda ake cewa matashin shugaba a Abuja?" "Wai irin wannan mutunci ne zai kawo mana cigaba?" "Ƴar talakawa bata da wani ƙarfi sai muryarta da gaskiyar ta, meyasa za’a ci mutuncinta haka kawai?" Comments sun cika social media suna goyon bayan Amal, suna yabon hikimarta da ladabinta, duk da ƙasƙanci da cin mutuncin da Maleekh ya jefo mata. A Bangaren Maleekh kuma... Bayan ya bar gidan rediyo, ya fara samun rahotanni daga PR ɗinsa cewa abubuwan da ya faɗa an ji su a watsa shirye-shiryen gari, kuma hakan yana janyo rashin kyau ga kamfaninsa CashTalk FM. Amma Maleekh cikin jin isa ya kalle su ya ce: "Ko gwamnati ba za ta iya tambayata ba. Kun san dalili? Saboda sun san wanene mahaifina. Idan tana tunanin zata iya kunyata ni da Muryar ta, zan nuna mata yadda iko ke aiki a Najeriya.".... Kai tsaye Abuja ya wuce... Bayan isar sa cikin ɓacin rai ya zauna a cikin babban falonsa dake Abuja, yana kallo a kan plasma TV, yayin da Amal ke ci gaba da samun goyon bayan jama’a. Sai ya furta: “Na ce miki I’ll crush you. No one messes with Maleekh Cashbank and walks free.” Ƙarfin iko da mulkin kuɗi Gwamnati da hukumomi basu iya tsoma baki ba, domin kowa ya san ƙarfin Maleekh da iyayensa. Ana kallon Amal tamkar ƙaramar yarinya marar mafita. Har wasu 'yan siyasa na Abuja suna cewa: “Yarinyar nan bata san abinda take yi ba. Tana wasa da wuta. Tana jawo hankalin wasu da bazasu iya kareta ba.” Amma Amal, duk da tsoron da ke kewaye da ita, ba ta ja da baya ba. Ta ƙudiri niyyar za ta tsaya da gaskiya, har sai an ji murya ɗaya da ke goyon bayan talakawa... A cikin babban ofishin CashTalk FM dake tsakiyar Abuja, Maleekh ya kalli PA ɗinsa, Idris, da kallo mai cike da ƙorafi. Fuskar Maleekh na nuna gajiya da damuwa, amma har yanzu girman kai yana kansa, yana zaune a babban kujera da kafarsa ɗaya bisa ɗayan, yana motsa kofin coffee a hannunsa. PA Idris sai da ya daidaita nutsuwar sa sannan ya ce: "Mun gwada amfani da ƙarfi amma ya dawo mana da illa. Yanzu mutane suna tausaya wa Amal. Kafafen yaɗa labarai suna juya komai. Amma ina da wata sabuwar dabara...".... Maleek ya ɗago kai da ɗan murɗaɗɗen fuska ya ce: “I’m listening.” PA ya ce: "Mu sauya salon mu. Ba tare da barazana ba, sai da tausasawa. Za mu yi mata tayin da ba za ta iya ƙin karɓa ba. Misali… naira biliyan ɗari. Za mu gana da ita a wani villa mai zaman kansa, ba a gidan rediyo ba, ba a idon jama’a ba. Za mu sayi muryarta, mu sayi hotonta. Za mu mai da ita fuskar sabuwar CashTalk FM, tare da Rikky Blaze da ƙawayenmu na ƙetare. Sir, da zarar ta koma gefenmu, jama’a za su yi shiru." Maleekh ya ɗan juya bakin sa, yana lumshe ido. Ya yi shiru na ƴan dakiku kafin ya ce: “You think she’ll accept the money?” Idris ya ɗan murmusa tare da faɗin "Kowane rai yana da farashi, Sir. Ita ma dai tana kwaɓe ne kawai. Da zarar ta ga yawan kuɗin, za ta manta da duk wannan gwagwarmayar da take yi."... Maleekh ya ɗan kaɗa kai yana murmushi da raɗa a zuciyarsa yana faɗin “Idan ta karɓa, zata zama tamkar ɗan yatsa a hannuna. And if she refuses... then she’ll see the true meaning of regret.” Bangaren Amal A gida Amal na zaune cikin natsuwa, tana rubuta sabon rubutu na shirin rediyo da zai kawo sauyi. Fuskar ta cike damuwa, amma zuciyarta na cike da ƙarfi. Tana jin wata zuciya tana gaya mata kada ki ja da baya. Sai kuwa ta samu saƙon gaggawa a wayarta daga wani lamba marar suna: “We want to offer you a new life. One conversation, one hundred billion naira. No cameras, no mics. Private location. Just you and the future you deserve.” Amal ta kalli saƙon, sannan ta ce cikin zuciyarta: “Wannan shine yunƙurin da ke nuna irin su Maleekh sun fara jin tsoron gaskiya. Amma ni ba zan sayar da murya ta ba.” An shirya komai. Wani babban villa da ke gefen Asokoro, cikin duhun dare, aka kai Amal. Gidajen tsaro a kofar villa sun tabbatar da ba wani na waje da zai iya shigowa. Amal ta iso ne bisa ƙa’ida ba tare da mic ko recording ba, ta zaɓi ta fuskanci wannan ƙalubale kai tsaye, cike da jarumta. Ta shiga cikin babban falon da aka ƙawatar da fitilun da suke ɗaukan hankali. A gaban wata babban glass table ne Maleekh ke zaune, rik’e da cup na red wine, Rikky Blaze yana gefensa, sai wasu turawa biyu daga kamfanin Wave Broadcast International. Maleekh ya yi murmushi mai cike da zafi da mugunta, sannan ya ce: “Miss Amal... welcome. Please sit down. Wannan ba barazana ba ne, kyauta ce. Kina da murya mai haske… da zuciya mai ƙin jin magana...." Amal ta zauna cikin nutsuwa, har yanzu zuciyarta tana da matuƙar ƙarfi. Ta ce da muryarta mai nutsuwa: "Faɗi abin da kake da niyyar faɗa. Na zo nan ne domin gaskiya, ba domin jin daɗi ba." Maleekh ya lumshe ido, ya ɗauki wani babban envelope, ya saka a gabanta yana faɗin: "A cikin wannan akwai takardar check naira biliyan ɗari. Za ki bar wannan Rayuwa FM mai fama da ƙalubale… ki koma CashTalk FM. Muryarki za ta karaɗe duk faɗin Afirka. Ba za ki yi aiki ƙarƙashin kowa ba sai ni. Abin da muke nema kawai shi ne: ki daina sukar gwamnati da 'yan siyasa. Ki mayar da hankalinki kan nishaɗi. Babu sauran ‘gaskiya kuma’." Turawan suka ce: “You’ll also represent us globally. Ambassador of media. All travel expenses covered. No more poverty.” (Za ki wakilce mu a matakin duniya. Jakadiyar kafafen yaɗa labarai. Za mu ɗauki duk kuɗin tafiya da alƙaluma. Ba za ki ƙara sanin talauci ba.") Amal ta kalle su duka. Ta daɗe tana kallon Maleekh cikin idonta. itama cikin nutsuwa ta ce "Bari in fayyace maka abu guda… Muryata baza ta taɓa zama abin sayarwa ba. Ba za a iya sayen raina ba. Ina magana ne domin waɗanda ba su da murya kuma shi ya sa kuke tsorata da ni. Ni ba matalauciya bace, ni mai arziki ce da ƙarfin hali, da manufa mai ƙarfi. Kuma idan kana tunanin zan bar jama’ata saboda check… to, ba ka san komai game da ni ba.... Kana tunanin kai ne kake da Najeriya. Amma ƙarfin gaskiya Shi ne ƙarfin da ya fi komai. Kuma ba za ku iya kashe shi ba, ba da bindiga ba, ba da biliyoyi ba, ba da PA mai surutu ko turawa masu jajayen kunnuwa ba..." Rikky Blaze ya tintsire da dariya, amma Maleekh ya ƙafe ta da ido. Wannan karon, zuciyarsa ta girgiza. Ya ce da ita: "To ki shirya. Kin ƙirƙiri abokan gaba da ba sa mantuwa." Amal ta tashi tsaye. Ta ce: "Ban taɓa roƙon a kare ni ba, abin da na roƙa kawai shi ne in kasance a kan gaskiya. Kuma zan ci gaba da magana… ko da mutanen cikin duniya sun zamo kurmaye."... Ta juya ta bar su da mamaki. Kowa ya yi shiru a falon, turawan sun yi shiru, Rikky ya daina dariya, Maleekh ya kame bakin sa kamar wanda ya rasa hanyar tunani. Washegari da safe. Kafin kowa ya iso ofis, Amal ta riga ta buɗe mic ɗinta a Rayuwa FM. Bata faɗa wa kowa abinda ya faru da ita ba, Tana zaune a cikin studio, kafafunta a ƙasa, hannunta riƙe da mic, idonta a lumshe. Muryarta mai sanyi da natsuwa ta cika dukkanin filin. AMAL: “Assalamu Alaikum 'yan uwa. Ina so ku saurare ni da buɗaɗɗiyar zuciya. Ina magana da ku ba a matsayin mai gabatar da shirye-shirye ba, ina magana ne a matsayin 'yar Najeriya, mace, 'yar talaka, wacce ba ta da komai face gaskiya.” Ta lumshe ido kafin ta cigaba, tana fuskantar mic kamar dai duniya tana kallonta kai tsaye. “A daren jiya na zauna da wani babban ɗan kasuwa, mai girman kai, wanda ya ɗauki duniya da faɗi, kuma zai iya sayen mutunci kamar cin abinci a restaurant. Ya bani kuɗi, ya mun alƙawaruka, ya gaya min zan iya canza rayuwa ta da kuɗi. Amma amsar da na bashi shine "A'a.” Domin rayuwa bata tsaya akan dukiya ba, sai dai akan amana da gaskiya. Na gaya masa: Ni ba zan iya haɗa baki da ƙeta ba. Ba zan iya cin abincin da na san yana zubar da jinin mutane ba. Ba zan yi aiki da waɗanda suka mayar da talaka kamar ƙwari ba.” Ta ɗan dakata tana sauƙe numfashi, daga baya ta ci gaba da cewa "Kafin su akwai waɗanda Suka ce zan iya mutuwa idan ban haɗa baki da su ba. Amma na ce musu: Wanda ya tsani gaskiya, to ya shirya zaman damuwa. Domin gaskiya, ko da an kashe ta, to zata bar ƙura a zuciyar duniya har abada." Ta ƙara yin shiru na daƙiƙu, kafin ta ci gaba da magana "An bani kuɗi. An bani iko. An bani suna. Amma suna da iko ba shine gaskiya ba. Na ga mutanen da suka zauna a kujerun gwamnati suna dariya akan hawayen talaka. Na ji kalmomin da suka ce min, kamar ni ƙura ce da za’a shafe da ƙafa. Kuma zan sake ce musu: NI BA NA SAYAR DA RAI DA RA'AYI NA..... "Sun ce zasu bani biliyoyi, amma a cikin bil’adama, me kake da shi idan ka rasa gaskiya?" Ta lumshe ido tana jiyo sautin numfashinta da sautin zuciyar ta. "Ina magana da duk matasa maza da mata. Kada ku bari a saye ku. Kada ku bar wanda yake da kuɗi yayi muku shiru da kuɗi. Idan munyi shiru yau, gobe su ne za su zagi ƙwaƙwalwarmu." "I met the kind of men that run Nigeria and they are scared of only one thing: THE TRUTH. So let's give it to them. Not with violence… but with courage." A waje, mutane sun fara taruwa a kofar Rayuwa FM. Wasu suna jin kukan Amal a cikin radio, wasu suna kallon live stream ɗinta. AMAL ta cigaba da cewa: "Inna, idan kina jina yanzu, ki sani... jikar ki ba zata tsaya ba. Kuma ba zata ji tsoro ba. Zuciyarki tana cikin zuciyata. Kuma koda wata rana su yi nasara da jikina... maganata zata rayu a kunnuwan mutane!" Muryarta ne ta karye da kuka amma bata daina magana ba: Sai ta cigaba da magana da harshen Turanci domin duka Nigeria da duniya su fahimta: "They wanted to silence me with wealth. They offered me power, fame, billions... But I looked them in the eyes and said, I am not for sale." "Sun so su rufe mun baki da dukiya. Sun miƙa mun iko, suna, da biliyoyi... Amma na kalle su cikin idanu na ce: Ba na sayuwa." Ga dukkan matasa a waje, iyaye maza da mata masu fama, samarin titi, da ’yan mata, ina tsaye a nan saboda ku. Ba domin ina da ƙarfi ba, sai dai domin na san gaskiya ta fi harsashi ƙarfi, ta fi kuɗin jini tsabta." "Ga waɗanda suka sace ni... na yafe muku. Amma ku sani: idan na mutu yau, miliyoyi za su tashi. Domin wannan murya ba tawa ce kaɗai ba, tamu ce." "Kuma ga waɗanda suka sace ni... na ga fuskokinku. Yanzu kuwa, duniya na ganin tawa. Kun ji tsoro ba saboda kalmomina ba, saboda waɗanda ke sauraro na..." Ta dafe mic, tana kallon glass ɗin gaban ta, tana fadin: "This is not just about Amal. This is about every girl that has been told she's too small to speak, too poor to matter, too weak to fight. I speak for them now. And I will never stop." Ta gama jawabi tana hawaye, Sai ta latsa OFF a mic ɗinta da ƙarfin ikon zuciya, sannan ta fita daga studio ba tare da faɗa wa kowa ba. Jawabin Amal ya girgiza Nigeria. Yana nan a YouTube, Twitter, da kafafen duniya. Jama’a sun daina kallon Amal a matsayin karamar yarinya daga gidan talakawa, yanzu tana da murya da muryarta ta girgiza kujerun gwamnati. BBC Hausa ta buƙaci hira da ita. CNN ta wallafa labarinta tare da taken: “The Girl Who Said No to Billions” TVC da NTA sun fara duba yadda zasu kare kanta da shari’a ko rahoton kare hakkin ɗan adam. Youths a duk faɗin Najeriya sun fara wallafa hotonta da taken #AmalVoiceOfTruth Masu adawa da gwamnati sun fara cewa: “A sa Amal cikin tsaro kafin wani abu ya faru da ita.” A Rayuwa FM, ma’aikata sun tsaya kafaɗa da kafaɗa da ita. Hatta wasu da suka fara ganin kamar ba'a cikin hayyacinta take ba, yanzu suna ganin she's the real deal. Maleekh kuwa, da ya koma gida bayan ganawar su, yana jin kalmomin da Amal ta furta a kafafen sada zumunta da rediyo, zuciyarsa ta ɓaci matuƙa. A fusace yake, yana cikin babban ɗakin sa a gidan Abuja, yana cizon yatsa yana kallon screen ɗin laptop ɗinsa tare da faɗin: “She played me? In front of the whole country? Na zo da girmana, na zo da kuɗina, she made me a fool!” PA ɗinsa ya shigo yana ba shi shawara. Ya ce: “Sir, ba za ka iya murƙusheta da girman kai ba. Ka bita a hankali. Ka rinƙa nuna kuɗaɗe. Ka bari ta ga salama. Ka sa ta yi tunanin muna ba ta girma, muna mutuntata da darajata.” Maleekh ya lumshe ido, ya juya daga window, ya furta: "Fine. Za mu bi ta da salo cikin nutsuwa. Amma ka fahimta da kyau, zan mallaki muryar yarinyar nan, ko kuma na kashe ta. Babu wanda ke ran Maleekh Abdul-Majeed a ƙasarsa!".... Sun shirya: Zasu haɗu da wata ƙungiyar kamfani daga ƙasar waje da suka zo kafa sabuwar FM a Abuja. Zasu yi collaboration da Rikky Blaze wanda shima yana da muradin karɓar Amal daga Rayuwa FM. Zasu shirya mata alƙawari da tsarin waje da zata je yi interview, sai su jawo ta da kuɗi, matsayi da haɗa baki da manyan masu ruwa da tsaki. Amma ba su sani ba Amal ta riga ta bar haske a zukatan mutane kuma idan aka ɗan taɓa ta, zasu taɓa wuta mai cin ciyawa a duniya. Bayan jawabin Amal ya karaɗe Nigeria da duniya, Maleekh da PA ɗinsa sun dawo da dabaru masu laushi ba da nuna dama da kwarjini ba, ba da haɗari da bugu kai tsaye ba. Wannan shine shirin da suke ƙira da Soft Power Strategy. "Ba za mu yi faɗa da ita ba. Zamu jawo ta ne. Mu saka ta cikin kwanciyar hankali, mu sa ta gane cewa zama da mu shine mafita." Abubuwan da suka haɗa da shirin: ☆ Sanya mata gayyata daga kamfanin waje: Wani kamfani daga ƙasar Amurka, wanda Maleekh ya haɗa da Rikky Blaze, ya rubuta mata wata gayyata zuwa taron masu ruwa da tsaki akan ‘Freedom of Media in Africa’. Amal na ɗaya daga cikin waɗanda aka zaɓa. Za’a biya duk kuɗin tafiya, hotel, da tsaro. Zasu kuma saka mata alƙawarin idan ta bayyana ra’ayinta a taron, to zata samu damar aiki da Al Jazeera ko BBC. ☆Tura mata saƙo daga sunan wani NGO: Sun kafa wani bogus NGO suna kare ‘yan jarida mata a Afrika. Suna son bayar da grant na miliyan dari (₦100 million) don kafa Gidan Matasa Na Gaskiya. Amma sharaɗin shine dole ta daina sukan gwamnati kai tsaye kuma ta yi “neutral” reporting. Bayan an aikawa Amal wannan saƙon, ta karanta sharuɗɗan kuma ta fara jin cewa wannan ba taimako bane wata hanya ce ta rufe bakinta da kuɗi.... Amal sam ta ƙi yadda da wannan batun, tana shirin watsa musu ƙasa a ido ... An sa wasu fitattun 'yan jarida da take daraja su, da su ƙira ta, su janyo hankalinta... Haka take ganin saƙon wasu daga cikin manyan ƴan jarida su na faɗin: "Kar ki wuce gona da iri. Amal..." "A da akwai irin ki, amma a yanzu sun ɓace, babu labarin su .." "Mu mun daɗe muna fafutuka, amma muna da hikima, ba zafi-zafi ba." Amma Amal ta fahimta: suna ƙoƙarin daƙile zuciyarta da sunan shawara da nasiha ne.. Amal ta ci alwashin babu wanda zai ci nasara akan ta Indai ba ta hanyar Allah ba... A wannan karon ma ta sake bijire musu... Ganin haka yasa maleekh yin amfani da hukumomi ta hanyar barazana.. Maleekh ya yi amfani da ƙarfin mahaifinsa, babban ɗan siyasa mai ƙarfi a Abuja. Ya fara saka kafafen gwamnati su dinga kawo matsalolin Amal ta hanya biyu. Hukumar Bincike (CID) sun fara watsa bayanai akan Amal, sannan suna gayyatar ta... "Tana watsa bayanan ƙarya da ke haddasa rikici.” "Sun ƙirƙiri ƙorafi akan ta bisa wasu hotuna da suke cewa sun wuce gona da iri a social media ta hanyar Editing... Sun tura mata “Notice of Investigation” da barazana. idan ta ƙi halarta, zata fuskanci ɗaukar mataki bisa doka. Gidajen rediyo da ke da alaƙa da gwamnati sun fara ƙin gayyatar ta: An hana ta shiga wasu forums. An daina wallafa labaran da suke ƙara mata daraja. An saka ido akan Rayuwa FM. Haka nan an tura mata barazana ta email cewa: “If you don’t stop, someone else will stop you.” An kafa wasu “fake social media accounts” suna ɓata sunanta: Suna zagin ta da ƙiran ta marar ladabi... Suna yaɗa cewar tana ƙarya da ƙirƙirar labarai. Suna cewa Amal tana da “hidden sponsors” daga jami’an ƙetare.... Amma duk da wannan, Amal tayi amfani da mic ɗin ta Ta ce: “Wannan duk bai game ni ba, domin kowa yasan wace ce Amal Abdulsamaad.... Wannan game da 'yan Nigeria ne. Idan suna ƙoƙarin tsoratar da ni to muryata ƙara volume take wurin faɗan abinda basa son ji... Idan suka yi shiru, haka nan zan cigaba da gudanar da aikina akan tsari na....” Duk da wannan barazanar Amal bata je gayyatar da aka mata ba daga (CID) domin ta san duk shirin Maleekh ne, tana ji a ranta cewa ta gagare shi.... Yau ce ranar da aka fi sauraron Rayuwa FM tun kafuwarta. Mutane daga kowane lungu na Najeriya da ma ƙasashen waje sun sa kunne, domin sun ji labarin cewa Amal zata bayyana a cikin shirin rana na musamman mai taken: "Gaskiya Bata da Tsoro." A cikin studio, Amal na zauna a gaban microphone. Fuskar ta ɗauke da murmushi, idanunta cike suke da ƙarfi da jarumta. Bata buƙatar takarda a gabanta, zuciyarta ita ce 'kundin bayananta. Da Muryar ta mai sanyi ta fara da sallama... “Assalamu alaikum, masu sauraro. Sunana Amal Abdulsamaad, kuma ni ce ke magana da ku a yau daga Rayuwa FM. A yau zan faɗi gaskiya, komai tsanani, domin ina sane da cewa rayuwar gaskiya ta fi rayuwar tsoro tsawo.... A cikin kwanakin baya, na fuskanci abubuwa da ba zan iya karyatawa ba. Na sha wahala, na sha barazana, na sha alƙawari masu laushi da makudan kuɗaɗe. Amma ni ɗaya ce kuma da ikon Allah zan tsaya tsayin daka.” ta numfasa, murya ta ɗan ɗaga.. Sannan ta cigaba “Sun ƙirani da ƴar talakawa eh, hakane. Ni ƴar talakawa ce. Amma ku sani, ƙarfin talaka a Najeriya yana cikin muryarsa. Kuma muryar nan, ku na ƙoƙarin kashe ta ta hanyar tsoro, da kuɗi, da bita-da-'kulli.” “Na karɓi gayyata daga kamfanin waje. Na karɓi ‘offer’ na biliyoyi don inyi shiru. Na fuskanci barazanar kashe ni da kakata. Amma ku sani, ina da abin da ku ba ku da shi, gaskiya da amana ga al’umma. Wanda kuke tsammanin zai saye ni da kuɗin duniya, ku gaya masa wannan: ‘Amal ba tasa ba ce.’ Ni ba za a taɓa saya ta ba. Ni ba zan yi shiru ba. Ni ba zan zuba ido gwamnati ko ɗan siyasa ya ci mutuncin talaka ba."..... ta tsaya kaɗan, sannan cikin rawar murya take faɗin: “Kuma ku sani... Ku da kuke cewa ba zan daɗe ba, ku da kuke cewa za a wayi gari ba labarina yau kuna ji na, duniya tana ji na. Idan na faɗi gobe, tarihin zai tuna da ni.” A lokacin da ta gama jawabin, Facebook, Twitter (X), Instagram da YouTube sun cika da hashtag ɗin: #AmalGaskiyaCe #BabuSiyasarKarya #TalakaNaDaMurya #RayuwaFMForTruth Mutane sun yi ta mayar da martani. Wasu suna kuka da yabon jarumtar ta. Wasu daga cikin ‘yan siyasar da ke biyayya ga Maleekh sun shiga rikicewa da neman hanyar kare kansu. A Ƙarshen Shirin: Rayuwa FM ta ƙara daraja. An ƙira Amal daga kasashen waje domin gabatar da jawabi a UN Women Conference. Wasu daga cikin matasa a Najeriya sun fara kafa #AmalMovement, wata sabuwar fafutuka akan gaskiya, adalci, da kariyar ‘yan jarida.... Bayan jawabin Amal da ya girgiza kasar, gidajen rediyo da kafafen sadarwa suka bazama da labari. Amma wannan ƙwazon da gaskiya bai yiwa manyan masu mulki daɗi ba. A rana ta uku bayan jawabin: An aika wa Rayuwa FM da Takarda daga Hukumar NBC (National Broadcasting Commission) cewa: “Mun lura da yadda gidan rediyonku ke gabatar da shirin da zai iya tayar da ƙayar baya, tunzura jama’a da kuma barazana ga zaman lafiya da ɗorewar tsarin dimokuraɗiyya. Dole ku kare kanku ko a dakatar da lasisin ku na wucin gadi.” Wannan wasiƙar ta rikita shugaban Rayuwa FM. Amal, da sauran ma’aikata, suka shiga damuwa. Amma Amal ta tsaya da kafafunta tana faɗin “Idan muryarmu ce matsala, to me ya rage ga talaka? Idan gaskiya ce laifi, to me ya rage wa ƙasa?” Masu goyon bayan gwamnatin mahaifin Maleekh sun shiga aiki: Wasu kafafen yaɗa labarai da suke da nasaba da gwamnati sun fara ƙirƙirar rahotanni kan cewa Amal tana da alaƙa da wasu foreign agents da ke shirin juyin mulki da tada hankali. Sunce wai “Amal tana amfani da media wajen ɗaga hankali a Najeriya”. Wasu rahotanni na bogi sunce Amal tana karɓar kuɗi daga ‘yan adawa. A hakikanin gaskiya, komai ƙarya ne amma yana da nufin ɓata suna da haddasa tsaiko a karfinta. Wasu Manyan ‘yan siyasa sun shirya ƙulla zargin da zata iya jefa Amal cikin matsala. An fara tattaunawa akan ƙirƙirar Fake Account da za su ɗora mata zargin “Cyber Crime”. Ana shirya “leak” na wasu bayanai na ƙarya don nuna cewa Amal tana amfani da Rayuwa FM wajen tura saƙonnin da suka saɓawa dokokin Najeriya. Suna so su fitar da hujja cewa tana da alaƙa da “Groups of Dissidents”. Shugaban Rayuwa FM ya shiga firgici. Ya kira Amal a office ya ce “Amal… kina so in rasa lasisi? Kina so a kulle ni da iyalai na? Wannan ba yaƙi bane na jarida, yaƙi ne da gwamnatin da ba ta jin tsoron amfani da ƙarfi.” Amal ta kalle shi cike da tausayi, amma bata nuna tsoro ba. Ta ce da shi. “Ina da gaskiya. Idan muka mutu da ita, zamu rayu cikin tarihi. Amma idan muka yi shiru zamu rayu cikin jin kunya ne.”... ★★★ Ƙungiyoyin kare ‘yancin faɗan albarkacin baki daga waje kamar su Amnesty International da Reporters Without Borders sun fara nuna damuwa. Sun fitar da sanarwa suna kare Amal da Rayuwa FM. Sunce. “Ƴancin faɗar gaskiya shine ginshikin demokirad'iyya. Kowane hari akan Amal hari ne akan ‘yan jarida a Afrika.” Reactions daga Jama’a: Matasa sun fara zanga-zangar lumana. Sun ɗauko kwalaye suna rubuta: “Babu Rikon Gaskiya Sai Rayuwa FM” “Amal Voice of the Voiceless” “Kada Ku Kashe Gaskiya” Amal ta tsinci kanta a tsakiyar wani yaƙi wanda ko za ta tsaya ta faɗi gaskiya, ko ta ja baya ta zauna cikin tsoro....... asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 11 to 12 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Bayan kwana biyu, Amal tana zaune tare da Innar ta sai ga ƙira daga wayanta, dubawan da zata yi taga unknown number, cike da mamaki take bin ƙiran da kallo har ya yanke, still ƙiran ne ya sake shigo wa, Inna ta ce "Amal wa yake ta danna miki ƙira haka? ki ɗauka mana..." Amal tana girgiza kai ta ce "Inna ƙiran ba number ba suna, ban san waye bane..." Inna ta ce "Kada ki kuskura ki ɗauka to, kar kije masu shan jini ne, yanzu su zuƙe mun ke, ga shi ba wani auki gare ki ba..." Murmushi Amal tayi tana kallon Inna ta ce "Inna ke ma dai kinsan inada kumari, yanzu ne da matsaloli suka yi yawa ne duk na rarrame..." Har Inna ta buɗe baki zata yi magana suka sake jin wayar tana ringing, still irin ƙiran ɗazu ne, Amal ta ce "Inna bari kawai na ɗaga, ba abin da zai faru da yardar Allah..." Inna ta ce "To! Kiyi Bismillahi. .." Amal tana ɗaga ƙiran tayi shiru, tana sauraron wanda ya ƙira, jin wani irin sassanyar murya ne yasa ta lumshe ido domin har cikin zuciyarta ta ji shauƙin muryar.... Other site. "Amal Abdulsamaad! Da bazaki ɗauki ƙiran bane?..." Amal ta ce "wa ke magana?..." Ya ce "Maƙiyin ki..." Murmushi Amal ta yi sannan ta ce "Maƙiya na suna da yawa, sai dai ban san waye a ciki ba..." "Your big enemy..." in short answer ya bata... Ta ce "Ina sauraronka Maleekh Abdul-Majeed..." "Ina so mu haɗu urgently, wannan karon ba wai siyan gaskiyarki zanyi ba..." Ta ce "ai kaima kasan gaskiyata bazata taɓa sayuwa ba, koda zaka ƙarar da dukiyarka gaba ɗaya. .." Girgiza kai ya yi a bangaren sa, yana Jajanta wa kansa domin Amal tana kashe shi da magana.... Ba tare da ya ƙara furta wani abu ba, ya ce "PA ɗina zai zo ya ɗauke ki, ki shirya..." Daga nan ya katse ƙiran.... Inna ce take kasa kunne taji meke faruwa, tana kallon Amal ta ce "Ke da wa kuma?..." Amal ta ce "inaso zan je ƙiran sa ne, ko ma menene zan je naji, domin naga alamar wasan bai ƙare ba..." Inna ta ce "Kar kuma kije ya cutar da ke..." Amal ta ce "kiyi haƙuri kawai Inna, amma sai na je..." Bayan karɓar ƙira daga Maleekh, Amal ta gyara shigar ta cikin tsari, Duk da cewar tana cikin haɗari, amma zuciyarta na da natsuwa da ƙarfin hali. Inna ta riƙe hannunta tana faɗin “Amal… ki je da addu’a. Kina kare gaskiya, domin Allah baya barin mai gaskiya. Ki kula da kanki.” ●● ● A bakin titi wani mota mai duhu ne ya tsaya. Amal ta shigo cikin motar ba tare da tsoro ba, domin ta gane PA Maleekh ne ke cikin motar. Yayi mata sallama cikin ladabi, yana ƙoƙarin ɓoye wani damuwa a fuskarsa. “Please, ki kwantar da hankalinki. Boss yana so ku fahimci juna ne kawai,” in ji PA Maleekh. Ba tare da Amal ta saurare shi ba haka ya ja motar suka tafi... Sun yi tafiyar da ba ta wuce mintuna 20 ba zuwa wani wuri bayan gari mai cike da sirri da shuke-shuke, inda aka tanada wani ɗan fili da kayan alatu. Maleekh yana zaune a kujerar fata yana zuƙar shisha, idonsa a lulluɓe cikin tunani mai nauyi. Bai ce komai ba lokacin da Amal ta iso, Sai bayan ta zauna, ya ɗago kansa a hankali yana faɗin “Amal… I didn’t call you here to fight. I just want you to see that we can both win, not lose...” Amal ta gyara zama da natsuwa, idonta a kansa ba tare da kamewa ba ta ce “Kayi min tayin da ya ƙunshi yarjejeniyar kuɗi da murd'iya. Amma abinda kake so shine sayen raina ne, ba haɗin gwiwa ba.” Kafin su cigaba da magana, sai ga motoci biyu sun shigo da gudu. Mutane kusan shida suka fara fitowa da gaggawa sanye da baƙin kaya, fuskokinsu a lulluɓe, suna riƙe da manyan bindigogi. PA ya firgita yana duban Maleekh ya ce “Sir! Su waye waɗannan? Wa ya turo su? Kai ne ake nema ko Amal?” Maleekh ya miƙe da sauri yana faɗin: “Wallahi I don’t know them! This is not my doing!” Mutanen sun fara harbin sama, tare da nufar wajen da suke. Amal ta tsaya gaban kujerar da Maleekh yake a da, tana duba ko wani zai yi harin kai tsaye. A gabansa ta tsaya tana masa kallon ƙurilla sannan ta ce “Ka shirya kashe ni ne a gabanka Maleekh? Ko wannan wani sabon shiri ne na buga min drama?” Maleekh bai ce uffan ba. Zuciyarsa ta shiga ruɗani domin bai san da shirin komai ba. Kamar yadda ake gani, wannan farmakin ya danganta da wasu makarkashiyar siyasa da mahaifinsa ke ciki... Amal na dafe da zuciya tana kallon Maleekh da tuhuma ta kuma cewa “Ka zaɓi harkar da zata hallaka ka, ba harkata ba. Zan kare gaskiya har ƙarshen numfashina. Kuma wallahi idan ka shiga sahun Maƙiyan talakawa, na rantse da Allah sai na fallasa ka, kai da duk abinda kake wakilta.” Maleekh ya kasa cewa komai. Wannan shine karon farko da wani ya fuskance shi da irin wannan nauyin magana, ba tare da jin shakkar sa ba... Wurin yayi shiru na ƴan daƙiƙu kafin ƴan daban su kewaye su, ƴan daba fiye da shida, kowanne da bindiga da sanda da wuƙa a hannu. Sun kewaye Amal da Maleekh da PA cikin yanayi na barazana. Maleekh zama ya yi akan kujerarsa tare da ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya, yana ƙoƙarin naɗe hannun rigarsa yana shirin faɗa da su, sai dai kamar wanda bashi da kwarin guiwa sosai. PA yana gefe da baƙin gilashi yana satar kallon waɗanda suka kewaye su.... Amal tana tsaye a tsakiya. Idonta kamar wutar lantarki, zuciyarta kamar karfe. Bata motsa ba sai lokacin da ɗaya daga cikin ɗan daban ya ƙaraso da gaggawa yana son ɗora hannunsa a kanta. “Karka kuskura!” Ta faɗa cikin murya mai ƙarfi. Kafin yayi wani motsi, naushinta ya sauƙa a tsakiyar tsuriyarsa, ihu ya sakar tare da juyawa gefe yana faɗin “Kai! Wace irin mace ce wannan?” Da sauri sauran suka nufi wurinta amma su ma, Amal bata tsaya jira ba. Cikin basira da saurin motsi kamar wacce ta sha horo daga dakarun sojoji, ta fara kai musu naushi, harbin ƙafa da karfi, nan ta kayar da mutum biyu ƙasi... Wurin da tasan dole idan aka daki namiji a wurin zaiji nan take kai harin ta... Maleekh da PA sun tsaya cak! cikin mamaki. Maleekh har yanzu yana sanye da baƙin gilashin idanu, amma zuciyarsa ta fara harbawa da sauri. Ya kasa furta kalma, zuciyarsa na tantama “Wannan yarinyar me take da ita?” Amal ta ɗaga wani ƙarfe a ƙasa, ta fara dukansu da shi, tana buga musu akai, duk da bindigunsu da wuƙake ba abinda suka iya.. Sai dai a gefe guda, wani daga cikin ‘yan daban ya ratsa gefe, ya zagayo bayan Maleekh da wuƙa a hannu kai tsaye yana son ɗora masa wuƙa a wuya, daman wurin shi aka turo su... “Maleekh!” Amal ta furta da ƙarfi, sannan da gudu ta finciko shi daga kujerar da yake har suka faɗa ƙasi... Maleekh ne ya faɗo kan Amal, ya rufe ta da jikinsa. Amma wannan motsi ya sa jikin Maleekh yayi weak, yana kwance a kanta, zuciyarsa na bugawa kamar wacce zata fasa ƙirjinsa. Suna kallon juna. Amal kwance a ƙasa yayin da shi kuma Maleekh yake saman kanta. Haka numfashinsu yake haɗuwa yana bada sabon sautin, kallon juna suka shiga yi ba wanda ya iya ɗagewa, haka suka ji tamkar lokaci ya tsaya cak. Duniya ta daina motsi..... Kamar wani abu mai girma yana shirin faɗowa cikin zukatansu … PA ne ya ƙaraso da sauri, ya yi ƙoƙarin ɗago Maleekh daga saman Amal yana cewa: “Sir! Ka tashi… mutane sun taru… ’yan jaridu sun fara ɗaukar video!” Da sauri Maleekh ya tashi, ya nufi motarsa ba tare da cewa komai ba. Ya shige cikin motarsa, zuciyarsa cike da d'imuwa da ruɗani. PA ya zagaya cikin gaggawa ya ja motar, barin wurin da mutane ke ɗaukar hotuna da bidiyo yayi amma idon Maleekh na kan Amal har suka bar wurin... Amal kuma... Mata biyu daga cikin ma’aikatan gidan rediyo Rayuwa FM suka ƙaraso cikin gaggawa. Sun ɗago da ita suna ƙoƙarin karkaɗe ƙasa daga jikinta, tare da faɗin “Ki daure Amal… ki tsaya mana… kin fi kowa ƙarfin hali!” Amal bata iya magana ba, tana sauƙe numfashi, tana kallon saman sararin sama, kamar me fassara zuciyarta. ●●● An riga an ɗauki video lokacin da Maleekh ya faɗo kan Amal yana kwance, lokacin da ta ceto rayuwarsa, lokacin da kallon idonsu ya haɗu. Duniya bata ji bayani ba tukuna, amma magana ta fara yawo. Kwanaki biyu bidiyon Amal da Maleekh ya karkaɗe duniya, Twitter, TikTok, Instagram da dukkan kafafen labarai sun ƙone da sharhi, faɗa, jin daɗi, mamaki da ruɗani. 🌍 RA'AYIN JAMA'A: “Wannan fa jaruma ce, ba mace ba!” “Wata mace ce ta ceci babban attajiri kamar Maleekh?” “Da alama akwai wani abu a zuciyar Maleekh yanzu…” “Gaskiya Amal tayi bajinta, wannan video yafi duk hoton soyayya da na gani.” JARIDU SUN YI RUBUTU. Vanguard, Premium Times, The Nation da Daily Trust sun buga labarai kamar: “Amal, Matar da ta ceci rayuwar Maleekh a harin ƴan daba” “Ɗiyar Talakawa da ta juyar da hankali a Najeriya, Wacece Amal?” “CashTalk FM ya shiga rikici bayan bidiyon Shugabansu da Amal” RAYUWA FM🎤 Bayan kwana uku, Amal ta koma Rayuwa FM, cikin shiri na musamman da suka yi wa suna: “Soft Power: Lokacin da ƴan talakawa suka dawo da iko.” Tana sanye da doguwar riga abaya, kanta a rufe da gyalen abaya, Tana da kwarin guiwa, da nutsuwa. Ta kunna mic ɗinta, sannan ta ce cikin murya mai ƙarfi da lumana ta fara jawabi “Assalamu Alaikum wa rahmatullah… Sunana Amal Abdulsamaad. Ni jika ce ga Inna, talaka ce, mace ce mai cikakken hankali da imani. A cikin wannan bidiyon da kuka gani, ni ce a ƙasa. Na ceci rayuwar wanda yake da iko, kuɗi, suna da ƙarfafa gwamnati. Na ceci Maleekh. Amma kafin hakan, an yi ƙoƙarin kashe ni, a tsorata ni, a siye ni, a ruɗe ni da maƙudan kuɗaɗe, An nemi in miƙa gaskiyata domin su mallaki zuciyata. Amma ku sani, kuɗi ba gaskiya bane. Iko ba shine girmamawa ba. Gaskiya bata cika da ƙarfin tsiya. Bata jin tsoro. Kuma daga yau zan ci gaba da faɗan gaskiya a kowanne lokaci.” Amal tayi wannan jawabin ne domin ta kawar da wannan maganar video da ake jita-jitar sanar da cewa soyayya ce.. Jama'a a kafafen sada zumunta sun ɗaura taken: #AmalVoice #JarumaAmal #TruthShines Kuma Rayuwa FM ta samu ƙarin masu sauraro fiye da kowane lokaci.... ●●●● Maleekh yana kwance a cikin yacht ɗinsa a cikin swimmingpool dake cikin wantalelen gidan su, yana kallon bidiyon da aka ɗauka lokacin da ya faɗo akan Amal..... A cikin ransa ya furta “Why can't I stop watching this video... Who are you, Amal?” A lokacin ne PA ɗinsa ya shigo, ya ce masa: “Sir… da alama gaskiya ta fara kashe ƙarya. Abinda ka yi da Amal ya fara cin riba.” Maleekh bai ce komai ba. Ya zuba ido cikin bidiyon… ya maimaita kalmarta da murya mai sanyi... “Kuɗi ba gaskiya bane.” RA'AYIN JAMA'A A KAFAFEN SADA ZUMUNTA.. @RealTalkNaija: “Maleekh na kwance akan Amal kamar drama na Nollywood 😭 Abin ya fita a rai!” @QueenLami: “Wannan ba ceto bane kawai. Wannan soyayya ce da basu shirya yarda da ita ba 😍” @VoiceOfKaduna: “Kusan shekara biyar kenan da ba a ga Maleekh da mace a dandalin jama’a ba. Amma yanzu Amal ta jawo shi da zuciya.” #AmLeek #AmalAndMaleek #RayuwarSoyayya A wannan ranar Amal kwana tayi tana juyi ta kasa yin bacci, jin maganganun da mutane ke faɗi tsakanin ta da Maleekh... A ranta ta furta "daga ceto sai a fassara lamarin?..." Inna ce ta shigo ta same ta sai faman juyi take, ta zauna a gefen katifar ta tare da furta "Amal..." Amal ta tafi dogon tunani bata san Inna ta zaune gefenta ba, Inna jin bata cikin hayyacinta ne yasa ta buge ta a baya tare da faɗin "ke Amal..." A ruɗe Amal ta tashi zaune tare da faɗin "Ni ba soyayya nake da Maleekh ba ...." Inna ta zuba mata ido ta ce "too pahh..." Sunkuyar da kai Amal tayi... Inna ta ce "abinda ake faɗa ashe gaskiya ne? daga ƙiyayya sai a fake da soyayya?..." Amal ta ce "wallahi Inna ba gaskiya bane..." Inna ta dankwale ta tana faɗin "Kan jatumarki, munafuka, har gida aka zo aka nuna mun video ke da wancan yaron, ashe bakida hankali Amal? sai yanzu na raina iliminki da tunaninki, to ki sani ke abin magana zai shafa ba shi ba, tinda shi duk abinda yayi ado ne, ki kula da irin yaran nan, tamm...." Inna tana kammalawa ta tashi ta koma wurin kwanciyar ta... Amal ganin ta rasa yanda zata yi ne yasa ta fara marin kanta tana faɗin "Na shiga uku! Na shiga uku!! Na shiga uku!!! Ni Amal ya zanyi..." Itama haka ta gama shawaginta sannan ta kwanta bacci ɓarawo ya ɗauke ta.... Washegari da safe Gidan 📺 TV PROGRAMS DA BLOGGERS sun sake fitar da wani bayani akan Amal da Maleekh... “Gaskiyar Bidiyon Amal da Maleekh...” Wani babban shiri a Channels TV yana nazari akan bidiyon yana ƙiran masanan zamantakewa da kwararrun masu fassarar al’amura... “Is This Power Play or Love Story?” Wani ɗan jarida a Arise News yana tambaya ko akwai wani ɓoyayyen abu da suka kasa faɗa... Bloggers irin su ‘Naija Juice’ da ‘GistMe247’ suna cewa: “Was this attack real or planned to create attention? Yanzu haka Amal ta zama celebrity.” 📻 A RAYUWA FM: Amal ta yi jawabi... Bayan gani da jin abubuwan da ke yawo a dandalin sada zumunta, Amal ta dawo cikin studio ɗin Rayuwa FM, ta zauna tana fuskantar mic kamar yadda ta saba, sai dai wannan karon akwai ɗan fara'a da nutsuwa a fuskarta, ta fara jawabi kamar haka.. “Zan yi magana domin ku sani: Ban san Maleekh daga baya ba har sai wata rana da ya fito da ikonsa ya shiga rayuwata. Amma faɗa ne ya haɗa mu ba soyayya ba. Kuma idan faɗa ne zai haifar da jituwa, toh wannan Allah masani....” Sauraren wannan kalmarta ya sanya mutane sun sake tofa albarkacin baki. Wasu na ganin tayi hikima, wasu kuma sun ɗauka zata iya faɗar gaskiyar zuciyarta... ❤️ A gidan mahaifinsa, Maleekh yana kallon wani ƙaramin talabijin a ɗakinsa ana kan dawo da bidiyon nan akai akai. PA ɗinsa ne ya shigo yace masa: “Sir, Nigeria ta riga ta ɗauka kuna soyayya. Koda ba haka bane, yanzu labarin yana raye.” Maleekh cikin ɗan murmushi mara kwari ya ce “Soyayya? Suna tunanin zuciyata ta buɗe… Amma shin ta karɓe ni kuwa?” Sai ya ɗauki wayarsa, yana kallon hoton Amal da aka ɗauka lokacin da take faɗa, fuskar jarumta da ƙarfi a idonta. Bai ce komai ba, sai kawai yace: “This girl... is ruining me gently.” ● Bayan sati biyu... Rayuwa FM ta shiga labaran duniya da sabbin jita-jita bayan an sanar da cewa an dakatar da Amal daga aiki ba tare da cikakken bayani ba. Jama’a ne suke tambaya "me ya faru?", "wace laifi ta aikata?", amma duk da tambayoyin da ke ci gaba da yawo, hukumar rediyon ta yi gum da baki. Wani babban rikici ya ɓarke ne daga bayan fage, wasu gurɓatattun 'yan siyasa da suka ji tsoron shaharar Amal da yadda kalamanta ke wayar da kan talakawa, sun haɗu suka ba shugaban gidan rediyo Rayuwa FM maƙudan kuɗaɗe kimanin ₦100 Billions domin kawai a kori Amal daga aikin ta. An hana ta dawowa ofis. Bayan mako guda da aka dakatar da ita, wani ƙaramin rubutu kawai aka turo mata: “Rayuwa FM regrets to inform you that your services are no longer required.” Amal ta karanta saƙon da idanuwan da suka saba da jarumta, amma a cikin zuciyarta ta ɗan firgita. Ba saboda aikin ba, sai dai saboda yaudara da cin hanci ya kashe gaskiya a gaban idonta. Yanzu Amal ta dawo gida. Ta cigaba da kula da hidimomin gida, ta watsar da komai, ta ɗauka yanzu komai ba komai bane... Inna ba ƙaramin farin ciki ta shiga ba, domin bata son aikin Amal, kullum a cikin tashin hankali da faɗa da masu kuɗi da ƴan siyasa. Amal ta share hawaye cikin nutsuwa. Tana son kwantar wa Inna da hankali amma zuciyarta ta cika da wata irin murɗaɗɗiyar baƙin ciki da rashin gaskiya da ta gani a duniya. Ta fahimta: gaskiya bata da matsuguni a cikin tsarin da suka sayar da komai. Amal tana zaune da Inna cikin raunanniyar murya ta ce “Inna... na san da yawa za su ce na yi rashin nasara. Amma gaskiya ba ta ƙarewa da aiki. Ta fi haka girma.” Inna ganin yanda Amal take cikin damuwa ne yasa ta fara rarrashinta tare da ƙarfafa mata gwiwa akan haƙuri... A DANDALIN SADA ZUMUNTA... Mutane da yawa sun fara fahimtar cewa dakatar da Amal ba bisa ƙa'ida ba ne. An ƙirƙiri hashtags masu ƙarfi: #JusticeForAmal #RayuwaFMHasFallen #TruthVsBillions Wani shahararren marubuci ya wallafa: “Sun koreta daga Rayuwa FM amma sun kasa koreta daga zukatan talakawa.” 💥 Amal ba zata zauna ba haka nan ba, domin zuciyarta na tafarfasa. Kuma tana da sabbin matakai da zata ɗauka domin cigaba da yaƙi da ƙazantar tsari. Ta yanke hukuncin za ta ƙirƙiri shafinta mai zaman kansa (YouTube ko Podcast) don ci gaba da faɗin gaskiya da wayar da kai.... Amma sai dai dakatarwar da aka mata ba iya wurin aiki ba, har da huld'a da social media gaba ɗaya an hanata.. Tana ƙara fuskantar ƙarin barazana daga ƴan siyasa, domin za su ga cewa ba a iya tsayar da ita da kuɗi ko tsoro. Amal ta fuskanci tozarta daga gwamnatin da ta sayar da hankali da hange da biliyoyi. Amma ita ba ta sayar da murya ba... Amal tana kuka ita kaɗai sai surutai take a ɗaki kamar wacce ta fara haukacewa, tana faɗin “Na rasa aiki. Na rasa tallafi. Amma ban rasa murya ba. Kuma murya ɗaya idan ta faɗi gaskiya na fi biliyan da suka saye shiru.” Kullum a cikin maimaita wannan kalmar take, domin sai da ta kwanta rashin lafiya sosai... Ba ci ba sha kullum a cikin kuka, ga ba kuɗin tafiya hospital, sai dai Inna ta lalla6a zuwa chemist ta siyo mata magani, amma ciwo ƙaruwa yake, Inna har ta rasa kuɗin zuwa chemist ma... Suka cigaba da jinyar gida, sai da Amal ta ɗau sati biyu a kwance, gaba ɗaya ta lalace... A wannan rana Inna tana zaune a tabarma sai Amal dake kwance akan cinyar ta sai faman juye-juye take... Wasu zafafan motoci ne manya baƙaƙe masu tayoyi ta baya kusan guda goma suka Parker a ƙofar gidan su Amal.. Mutanen unguwa kuwa kafin kace me wuri ya cika da mutane, yara da manya yanda kasan a ƙauye tsabar rashin wayewa irin mutanen unguwar...dake unguwar talakawa ne. Wasu manya-manyan bodyguards ne suka fiffito daga cikin motar suna riƙe da manyan bindigu, sun sha black glass gasu baƙaƙe wuluk, yanda kasan sojojin Amurkawa.... Ɗaya daga cikin security ne ya buɗe murfin motar da babu wanda ya fito daga cikinsa, bayan mintuna wanda yake ciki ne ya wurgo da kafarsa ɗaya, kana ganin sawun kasan ɗan manyan mutane ne, shi ɗin ba abin rainawa bane sai wanda bai san shi waye ba, in ba Amal ba babu wanda zai nuna masa yatsa ya zauna lafiya... Lokaci guda Makeekh ya miƙo daga cikin motar yana sanye da baƙin glass, ko kallon mutanen wurin bai tsaya yi ba kai tsaye ya kutsa cikin gidan, domin yau ya kudurta cewa sai yayi maganin Amal, tasa mutuncinsa ya zube a gari, kowa yana masa dariyar cewa ya fara soyayya da ƴar talakawa.... Maleekh da wasu bodyguard biyu ne suka shiga gidan, sauran kuma duk a waje suka tsaya... Inna na ganinsu ta zabga uwar salati tana faɗin "Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un, sojoji kuma a gidan nan? dan Allah ku rufa mana asiri wallahi Amatu ta daina aikin jarida, gata nan rai a hannun Allah, babu lafiya..." Maleekh saida ya bari Inna ta kammala magana kafin ya ce "Assalamu Alaikum warahmatullah..." Inna ta amsa cike da mamaki... Maleekh zare glass ɗin kan dara-daran idanuwansa yayi ganin halin da Amal take ciki, a ruɗe ya ƙarasa wurin da take kwance akan cinyar Inna, shima zama yayi akan taburmar tare da ɗago ta akan cinyar Inna ya kwantar da ita akan tasa cinyar yana faɗin "Amal ce ta dawo haka? me me me meya faru da ita?..." Ganin yanda ya ruɗe ne ya bawa kowa mamaki, haka security suke kallon juna domin tin kafin su taho Ogan nasun ya sanar cewa "zai zo ne akan ya wulakanta Amal, ganin yanda video sa yake yawo tare da ita..." yanzu kuwa labari ya sauya.... Maleekh bai tsaya jiran komai ba ya miƙe da Amal, cikin gaggawa yake faɗin "Please Mama ki sako hijab hospital zan kaita..." Inna da saurin ta jin zasu tafi asibiti, haka Maleekh yayi mata ɗaukan lud'a ya fita da ita. A motarsa ya kwantar da ita sannan ya shige suka miƙe asibiti, ita kuma Inna daga baya aka taho da ita... A babban asibitin Kaduna aka kwantar da Amal, sai da Maleekh yayi jinyar ta na kwana uku kafin yayi sallama da Inna ya koma Abuja, already ya gama biyan kuɗin komai na asibitin, da abinda za'a buƙata duk ya gama biya... Sannan ya sanar wa doctor cewa 'idan da damuwa ya sanar masa a waya' .. Inna tayi matuƙar farin ciki sosai da bajintar da Maleekh yayi musu... Maleekh yana tafiya washegari Amal ta farka, ta samu sauƙi sosai, duk wata damuwa ya yaye mata, domin ba ƙaramin kulawa ta samu a asibitin ba... Bayan an sallame su ne, suna gida Amal take tambayar Inna "Inna! Aina aka samu kuɗin kaini asibiti? bayan bamu da sauran kuɗi, kuma naga babban asibiti muka je..." Inna tayi murmushi sannan ta ce "Ɗan Albarka ne.." Cikin rashin fahimta Amal ta ce "wa kenam?..." Inna ta ce "Maleekh mana..." A zabure Amal ta ce "Wani Maleekh wai?..." Inna ta ce "ke bana son shegen tambaya, Maleekh nawa kika sani..." Amal cike da mamaki take jinjina batun... Har aka ƙare makon nan Maleekh bai ƙira Amal ba sannan Amal bata ƙira shi ba, Inna tayi da ita akan ta ƙira shi tayi masa godiya amma sam Amal ta ƙi, wai ita sai idan shine ya fara ƙira tukun.... Da haka har aka sharar da zancen Maleekh.... ♡♡♡ ○○○ Amal ta shafe wata guda a cikin gida tana juyawa da rayuwa cikin tawali’u da haƙuri. Ta zamo abokiyar tafiya ta Inna daga girki zuwa gyaran gida, sannan kuma ta buɗe ƙaramin kasuwanci na siye da siyarwa a cikin gida. Tana saida kayan kwalliya, kayan miya, da snacks da ta ke sarrafa da kanta. A kullum ana jin dariyarta da sautin walwalarta da Inna.. Amal tayi alkawari wa kanta cewa "Na riga na bar aikin rediyo. Babu komawa. Gaskiya zata rinƙa faɗuwa idan na dawo gurin da aka hana ni murya.".. Wata rana Amal tana zaune kusa da Kakarta, suna shan hira, tare da tura kayan kasuwa cikin leda, sai ga muryar sallama daga bakin ƙofar. "Assalamu Alaikum..." Amal ta ɗago kai tana sakar murmushi cikin mamaki ta ce "A’isha?! Kece a nan gidan mu??" A’isha ta nufo ta da murmushi, suka rungumi juna. Kawarta ta makaranta tin secondary.. A’isha ‘yar gidan wani Minister ce, wacce ta taso cikin alatu, amma bata taɓa manta ƙawarta Amal ba. Bayan sun gaisa da Inna, ta zaro wata ƙaramar takarda mai kyalli daga jaka, ta miƙawa Amal tana faɗin “Katin bikin aurena ne! Na ce bazan bari wani ya kawo miki ba, domin sai da wannan katin ake shiga. Kuma bana so a hanaki shigowa...” Amal ta tsaya daidai. Ta kalli katin tare da murmushin da ke haɗe da dakiya. Amal cikin jin nauyi ta ce “Hmm A’isha, anya kuwa zasu bari na shiga? Na san irin mutanen da zasu taru. Ƴaƴan masu kuɗi ne ke can... kuma ni yanzu dai bana da matsayi...” A’isha ta katse ta da cewa “Kinga Amal, ki manta da komai. Yanzu kowa yana kallonki a social media, kin dai sani, kinyi fice. Kin zama celebrity ba tare da kin nemi hakan ba. Kuma mutane da yawa ciki har da ni muna alfahari da ke. Wannan bikin kuwa, bana so kije a hanaki. Ni da kaina zan karɓe ki a ƙofa.” Amal ta riƙe katin kamar kuɗi, tana kallon shi da ƙwarin gwiwa..... Inna ta yi gyaran murya tare da faɗin “Amal, Allah ne ke kawo mutum da wadata ta hanyoyin da ba ya zato. Ƙila wannan katin ba kawai na biki bane... wataƙila ƙofar sabon fata ne.” Bayan tafiyar A’isha, Amal ta zauna da katin a hannunta tana kallonsa kamar tana karanta sirrin duniya a jikin sa. A gefe kuma Inna ta na harhada kayan miya, amma tana kallonta da ido ɗaya, ta ce "Ke dai Amal... Allah na tare dake. Ki tafi ki je biki, amma da addu’a. Ki sani ba kowanne gayyata ce da nufin sharri ba, wasu ana kawo ta ne don alkhairi." Amal ta kada kai tana murmushi, amma daga ciki zuciyarta tana cike da tunanin tsaro, tsoro da kuma ciwon da zuciya ta sha kwanan nan. Duk da haka, akwai wani saƙo da ya fara janyo hankalinta, zuciyar ta tana ce mata wannan ba biki kaɗai bane… wata alama ce daga sama... Bayan kwana biyu Amal tana zaune tana kallon kayanta cikin akwati, Ba komai mai tsada a ciki, amma akwai wani ƙaton atamfa da ta fi so. Tuni ta zaɓe shi domin tafiye-tafiye na girmamawa... Ta wanke gashin kanta da man shafawa... Ta yi kwalliya sosai, ba ƙaramin kyau tayi ba, ga ta fara ce tass ko bata yi kwalliya sosai ba farin ta zai ƙara mata kyau, ga gashin giran nan ya kwanta luff, komai ya tsaru a jikinta. Yanda kasan ƴar India, amma ita ɗin fulani ce ta asali.. Bayan ta kammala shirinta ta fito tana faɗin "Inna, nayi kyau?.." Inna ta yaba sosai tare da yi mata fatan alkhairi.... Bayan sallar la’asar, motar da A’isha ta turo ta iso a bakin titi. Amal ta fito cikin riga mai launin sky blue, riga da sket sun matse ta sosai, ga ta sha takalmi mai tudu, asalin surar ta ya fito sosai, ba abun rainawa a jikinta masha Allah, fuskar ta kamar ba mutum ba, powder da ta shafa yasa farinta yayi dauuu har ɗaukan ido yake.. Inna ce ta leƙo daga ƙofar gida tana faɗin "Ki tsaya na makj addu’a ƴarnan...." Amal ta tsaya Inna Ta ɗora hannu a kanta, tana karanta ayoyi cikin murya mai raɗa. Bayan haka, ta ce: “Ki je da aminci. Idan alkhairi ne ki dawo da ƙarin daraja. Idan sharri ne, Allah ya 6atar da shi kafin ki isa.” Amal ta amsa da "Amiin".. A cikin motar, Amal tana kallon waje cikin natsuwa. Duk inda suka wuce, mutane suna tafiya da abubuwan rayuwarsu amma zuciyar Amal na tafiya da saƙo.. tana magana a ranta "Zan je, zan tsaya a cikin taron masu daraja. Amma zuciyata za ta zauna cikin ƙasƙanci, domin ni yar gajiya ce, ba ƴar isa ba..." An shirya wajen bikin yayi kyau fiye da yadda Amal ta hango a tunaninta. Babban filin da aka tanadar ya sha kwalliya da furanni, fitilu masu launi, da gilashi masu walkiya. Kowane mutum da yake cikin bikin yana nuna jin daɗi, daraja da kima. Kamar yadda A’isha ta faɗa, sai da katin gayyata ne ake shigowa. A lokacin da Amal ta ƙaraso bakin shiga, jami’an tsaro suka tsaya suna duban ta. Miƙa musu katin tayi a hankali, suna dubawa suka ce: "Welcome, ma’am." Ta shiga.... Kamar wani wutar lantarki da aka kunna, idanuwa da dama suka karkata gareta. Tana tafiya cikin nutsuwa, tafiyarta na ɗauke da tarin tausayi da kima. Wasu daga cikin ƴaƴan masu kuɗi da ke cikin bikin sun ganta ne daga cikin video da ya yaɗu, video ɗin Maleekh yana kwance a kanta. Wasu suka fara magana suna faɗin “Wannan ba ita bace wadda Maleekh ya faɗi a kanta?” “Yar talakawa ce fa… amma tana da kwarjini.” “Kin san sun ce sun kore ta daga aiki saboda politics?” Wasu kuwa sun hau ƙiran sunanta a social media, suna cewa: #QueenOfCourage #AmalOfThePeople #MaceMaiKwarjini A nesa daga cikin VIP section, shigowar Maleekh kenam, ya zauna cikin rigar shadda white color, mai bala'in tsada, domin bazaka taɓa samun irin shaddar a Nigeria ba, ga ya ɗaura white glass ɗan siriri akan golden eyes ɗinsa, yana motsi da ɗan ƙaramin lips ɗinsa da ya sha lip glowin sai sheƙi yake, ga wata farar hula da ya ɗora akan sumar sa da ya sha gyara, shima ba ƙaramin kyau ya yi ba, chocolate handsome guy, ga wani gyara da yayi wa sajensa sai ɗaukan ido yake.... Duk ƴan matan wurin idonsu akan sa yake, farashin Maleekh na da matukar tsada, ga kyau ga kuɗi ga ilimin boko da Arabic, ƙaramin shekaru, bazai wuce 30 ba... Yana tare da wasu manyan baƙi, ciki har da wasu ministoci da mutanen ƙasashen waje, yana duba yanayin taron, dake bikin ƙanwarsa ake, sai dai ita A'isha ba mahaifiyarsu ɗaya da Maleekh ba, A'isha da kannenta mata biyu da mahaifiyarsu suna zaune ana Kaduna. Maleekh kuma da kannensa mata biyu da mahaifiyarsu su kuma suna Abuja... Ɗago kai da zaiyi kwatsam idanunsa suka sauƙa a kan Amal dake zaune ita kaɗai.. Zuba mata ido yayi ko kibtawa babu, a zuciyarsa ya ce "Tana kallon kamar ba ta damu da duniya ba. Amma duniya ce ta damu da ita yanzu..." 🌟 A lokacin da MC ke gab da gabatar da wani ɓangare na shirin, aka sanar da cewa za’a bawa wasu baƙi kujerun VIP saboda "irin jajircewar su a rayuwa." Abin mamaki Amal na daga cikin jerin sunaye! MC ya faɗi suna da ƙarfin murya tare da faɗin "Amal Abdulsamaad, mace mai daraja daga cikin matan ƙasar nan da suka tsaya da gaskiya fiye da kuɗi da ƙarfi!" Kowa ya zaro ido. Amal ta tashi cikin ladabi, amma zuciyarta cike yake da mamaki... Maleekh cikin murmushi yake kallonta domin shi yasa a bata... Bayan ta zauna.. A cikin nutsuwa da salon kwarjini, Maleekh ya tashi daga kujerarsa, yana matsowa kusa da ita. Mutane ne suka zuba ido, domin kowa idonsa akan su yake... Amal jin mutum a gefenta yasa ta kalli wurin, ganin Maleekh ne yasa ta zaro ido waje tana kallon sa.. Maleekh cikin sassanyar murya ya ce "Zan iya magana dake Amal?" Kafin ta amsa, A’isha ta zo yanda suke cikin kayan Amare ta ce: "Let me steal her for a second Yah Maleekh." Ta janyo Amal gefe, sannan ta raɗa mata a kunne: "Duniya tana kallon ku. Ki tsaya da gaskiyar ki, ko ma meye zai biyo baya.".. Maleekh ganin yanda mutane suka zuba masa ido yasa ya koma yaje ya zauna a yanda yake... MC ne ya bayyana a filin wurin. (Jama’a kowa ya nutsu. Fitilu na lilo a sama. Idanun mutane suka koma kan dandalin yayin da MC ya taka gaba cikin kwarjini.) MC cikin fara’a ya ce "‘Yan uwa maza da mata, da fatan za ku tar6i wata baiwar Allah wacce bata buƙatar gabatarwa, jaruma, hazika, muryar matasa Amal Abdulsamaad!” Tafi ya karaɗe wurin. Wasu na tafawa saboda kaunar da suke wa Amal, wasu kuwa domin sha’awa, wasu kuma saboda mamaki.... Amal ce ta miƙe cikin natsuwa, tana tafiyarta cike da nutsuwa ta sa kowa kallonta. Ta isa muryar mic, ta sauƙe numfashi. Ta fara... “Assalamu alaikum warahmatullah. Sunana Amal Abdulsamaad. Ni ƴar asalin Kaduna ce, kuma yanzu haka ina da shekaru 22 da haihuwa. Na rasa iyayena ne tun ina da shekara uku a duniya, sanadiyyar wani hari na siyasa da ya shafi iyayena. Tun daga wannan lokaci, kakata take kula dani wato mahaifiyar mahaifina. Ita ce ta koya min gaskiya. Ita ce ta gina ni akan jarumta. Kuma ta koya min cewa talauci ba laifi ba ne amma rayuwa ba tare da gaskiya ba, tabbas azaba ce.” (Jama’a kowa yayi shiru. Har Maleekh sai da ya ɗan matso gaba daga inda yake zaune.) “Ban taso a cikin dukiya ba. Na tashi a cikin gaskiya. Ban yi makaranta a ƙasashen waje ba. Amma a makarantar mu ta ƙasata na samu abokiya ta gaskiya wato ita ce A’isha.” (Ta kalli amarya A’isha da murmushi wanda ya bayyana zurfin kaunarsu.) “Tun a makaranta A’isha ce ta fara raba abincinta da ni lokacin da ba ni da nawa. Ita ce ta fara tsayawa min idan ana yi min dariya saboda talaucina ko saboda natsuwata. Ta daina kallon banbancin mu. Iyayenta na gwamnati, nawa kuwa na cikin kabari amma mu mun kasance ‘yan mata, abokai, ƴan uwa.... **“Rayuwa ta raba hanyoyin mu, ni na zama mai magana da jama’a, A’isha kuma ta kasance jakada ta ladabi da ilimi. Amma yau ga mu nan kuma komai bai canza ba. Ina alfahari da ita, kuma ina alfahari da kaina.”** (Ta tsaya. Muryarta ta lafa, cikin tausasa murya) “Idan akwai abu ɗaya da nake so kowa ya tuna daga wannan jawabi, shi ne: Ba sai kana da babban suna ba kafin ka zama babban mutum. Ba sai kana da izini ba kafin ka faɗi gaskiya. Kuma ba sai kana da iko ba kafin ka zama mai ƙarfi.” (Matasa suka fara tashi suna tafi. Wasu manya suka bi sahu. A’isha tana goge hawayen farin ciki) Amal ta rufe da cewa: “Gare ki amarya A’isha nagode da kasancewa kamar yadda kika kasance. Gare ku masu saurare nagode da wannan dama. Kuma gare ku ƴan Kaduna daga kowanne gida muryarku na da tasiri.” (Ta sunkuyar da kai cikin girmamawa ta koma kujerarta. Hotuna na ci gaba da ɗauka. Wurin taron ya cika da amo.) MALEEKH yana kallonta Bai tafa hannuwa ba. Yana zaune ne kawai, laɓɓansa a gimtse, zuciyarsa na bugawa da ƙarfi, yana maganar zuci "Ba kawai murya ce ta rediyo ba... juyin juya hali ce a cikin jikin Amal...." asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 13 to 14 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 MC ne ya karɓi mic ɗin daga hannun Amal cikin fara'a, ya juya ya dubi taron, sannan ya kalli Amal wacce take shirin barin wurin. MC ya ce “Eh-eh! Amal bamu gama dake ba fa! Mutane da yawa suna da tambaya, mu ma muna da tambayoyi. Kuma nasan akwai waɗanda suka zo ne saboda ke.” Jama’a ne suka fara dariya da tafi. Amal ta murmusa kaɗan, ta tsaya daidai gefen MC. Ya miƙa mata mic. MC cikin nishadi ya ce “Amal, mun san ki ba kawai a nan ba, har a kafafen watsa labarai na ƙasashen waje. Yanzu idan da ace wani ne ya samu irin shahara da goyon bayan da kika samu, da tuni yana da gida na alfarma, manyan motoci, kudi a account amma meyasa har yanzu kina zaune a irin yanayin da mutane da dama ke ƙira ‘talauci’?” Amal ta ɗan gyara tsayuwarta. Ta ɗago kai cikin natsuwa ta ce “Na gode da tambayar. To gaskiya talauci ba laifi ba ne, kuma arziki ba a tantance mutum da shi. Ni na zaɓi rayuwar gaskiya akan rayuwar ƙaryar kuɗi. Inada ikon in karɓi cin hanci in gina gida na alfarma, in mallaki motocin da mutane ke mafarki amma hakan zai nufe ni da sayar da gaskiyata, na sayar da zuciyata. Rayuwata ta ginu ne bisa gaskiya. Kuma gaskiya ba ta da tsada amma ta fi kuɗi daraja.” (Wani sassa na taron ya fara da tafi. MC ya kalli Amal cikin girmamawa.) Ya ce “Tabbas, abin burgewa ne. To Amal, zamu so ki gaya mana me ya ja hankalinki kika shiga aikin jarida? Kuma me ya sa kika zaɓi ki dinga faɗa da ƴan siyasa maimakon ki nutsu da aikinki?” (Amal ta dafe mic kamar wacce ke maganar zuciya.) Sannan ta ce “Na shiga aikin jarida ne domin rayuwa ba ta bani damar yin shiru ba. Na ga abinda ake yiwa talakawa. Na rasa iyayena saboda tsagwaron karyar siyasa. Su da ba su da laifi an hallaka su kawai don sun tsaya akan gaskiya. Wannan shi ya haifi ƙiyayyata da ƙarya, ya sa na rantse zan yi amfani da muryata wajen ƙwato wa marasa murya haƙkinsu. Ina faɗa da ‘yan siyasa ne domin yawancinsu ba su da gaskiya. Suna cin zarafin al’umma, suna karkatar da dukiyar ƙasa kuma ba wanda ke cewa a’a. Na yarda da Allah, na yarda da mutuncina kuma idan muryata zata mutu saboda gaskiya, to inaso ta mutu cikin daraja.” (Wani sashi na jama’a suka ce “Allah sarki!” Tafi ta kaure.) MC ya gyara murya cikin salo ya ce “To Amal, ba za mu bar ki da duka tambayoyin zuciya ba yanzu me zaki ce: kina soyayya?” Taron ya ƙara kankama. Kowa yana jiran amsa. Amal ta murmusa kaɗan ta sauƙe idonta kafin ta dago ta ce “Bana soyayya.” MC ya ce “A’a kenan, amma akwai wanda ya furta miki soyayya kuwa?” Amal ta ɗan yi dariya sannan ta ce “Eh, akwai su da yawa. Amma ni soyayya ina kallonta a matsayin shashanci ne.. Ina tunanin yawancin waɗanda ke soyayya yanzu suna soyayya da abin da suke gani, ba abin da suke ji ba. Ina buƙatar soyayyar da zata gina ni, ba wacce zata rushe ni ba.” MC yana murmushi ya ce “Toh... toh... toh! Amma akwai jita-jita. Amal da Maleekh Cashbank kuna soyayya ko a’a?” Amal ta ɗan dakata. Taron ya koma cikin natsuwa. Kowa na jiran ta ce “eh” ko “a’a.” Ta juyo cikin natsuwa ta ce “Ban san zancen ba.” MC ya taɓe baki sannan ya ce “To ba zaki mana bayani ba kenan?” Amal ta ce “Na san mutane da yawa na jin labarai, na ga bidiyo, na ji maganganu… Amma a gaskiya, ni kaina har yanzu ban fahimci me Maleekh yake nufi da rayuwata ba. Ni ba na jin kalmomi, na fi karanta hali. Idan ya zo da gaskiya, lokaci zai bayyana. Amma har yanzu, ina da damuwa da tambaya ɗaya: shin yana da gaskiya ko kuma yana wasa da wuta ne?” Taro ya kaure da tafi, wasu ma sai da suka taso tsaye. Haka shafin ya ƙare cikin nishaɗi, lulluɓe da mahangar gaskiya da jarumta.. Amal na ƙoƙarin janye jikinta cikin ladabi domin komawa kujera, tana ƙoƙarin tserewa hasken idon mutane. Sai kwatsam… ƙafarta ta zame! Ta ɗagu sama tana shirin faɗuwa ƙasi amma kafin ta faɗo hannuwan Maleekh suka riƙo ta!... Riƙe shi ta yi da ƙarfi kamar mai neman mafaka. Ta kama wuyansa, idonta cikin nashi. Shi kuwa ya riƙe kunkumin ta da hannunsa ya manne ta sosai a jikinsa, yana kallon ta da idon da babu wata magana da ya fi dacewa da shi sai shiru mai sa bugun zuciya.. Wurin ya ɗau tsit. Kowa ya tsaya, kowa ya zuba musu idanu, daga manyan baki zuwa ƙanana, daga masu kirga numfashinsu zuwa masu ɗaukar bidiyo. Har sai da wani daga cikin manyan bak’i ya katse shiru da faɗin “Soyayya phone storee!!!” Wurin ya kaure da dariya da tafi. Ihu da nishaɗi suka mamaye ɗakin taron. Kamar abin da mutane ke jira kenan. Wasu suna cewa “babu shakka Amal da Maleekh soyayya ce”, wasu suna ɗaukar video suna turawa kai tsaye. Har Amarya A’isha da angonta suna dariya cikin farin ciki da tafawa. Amal jin yanda ya ɗora hannunsa akan boob ɗin ta, sannan mannuwan da suka yi ba ƙaramin mannuwa bane domin tana jin yanda take gogan banana bananansa 🍌🫣. Ƙirjinta ne yake wani irin dukan uku uku.. Ganin yanda ta firgita ne yasa ya ɗaga ta yayi mata ɗaukan lud'a kamar karamar yarinya, yana kallon ta da murmushin da ta rasa fassara. Ya kai ta kujera, ya zaunar da ita a hankali.. Amal cikin jin kunya ta sunkuyar da fuskar ta, miƙa mata mayafinta yayi da ya zame ƙasi, dasauri ta karɓa tare da rufe fuskarta da shi.. Haka hawaye yake gangaro mata tsabar tsananin kunya da baƙin ciki... MC ya kalli Maleekh yana dariya ya ce “Toh toh toh! Toh yanzu daga ‘phone store’ zuwa ‘heart store’… Yallabai, ka iso nan. Kai ma akwai tambayoyi da ke jiran ka!” Tafi da dariya suka sake kaurewa yayin da Maleekh ya ɗan goge gefen rigarsa ya ƙaraso ya tsaya a gaban mic. Ya sauƙe bakinsa yana kallon Amal da har yanzu take kokarin ɓoye kunyar ta. MC cikin murmushi ya ce “Maleekh, kafin mu fara tambayoyi da gaske wannan rikewa ce ta gaggawa, ko kuwa da shiri aka zo da ita?” Jama’a suka yi dariya. Maleekh ya ɗan yi murmushi ya jinjina kai, ya ɗauki mic, murya cike da kwanciyar hankali ya ce “Da ace shiri ne da na tabbata zuciyarta tuni ta bar jikinta. Amal fa ba mace bace da zaka shirya wasa da ita..." MC ya ce "Toh wane hali kake ciki yanzu, ganin yadda duniya ke alakanta ka da Amal, gashi nan kun rungumi juna a bainar jama’a, kana ɗaukar ta kamar amaryarka...” Maleekh ya ɗan yi shiru. Sannan ya ce cikin nutsuwa, yana kallon inda Amal take ya ce “Abin da ke faruwa tsakanin ni da Amal ba ni ke da ikon fassara shi ba, ita ce zata iya fassara shi. Ni dai na san abu ɗaya: duk lokacin da take kusa da ni, nakan ji kamar zan manta da duniya gaba ɗaya. Idan soyayya ne wannan to ban isa na musanta ba. Amma har yanzu, ina jiran zuciyarta ta yarda da ni ba saboda bidiyo ko taro ba sai saboda gaskiya.” Wurin taron ya sake kaurewa da ihu da tafi. Amal ta juyo a hankali ta kalle shi. Ya kalle cikin murmushi mai ƙayatarwa. Cikin shiru suka ci gaba da kallon juna… wanda bai da fassara.. Bayan mutanen wurin sun kaure da dariya, tafi, da ihu, MC ya ƙara miƙa mic ga Maleekh yana faɗin. “Toh yanzu da ka furta cewa ‘ina jiran zuciyarta ta yarda da ni ba saboda bidiyo ko taro ba sai saboda gaskiya’… kana nufin kana sonta ne?” Shiru ya sake ɗaukar wurin. Amal ta ƙara boye fuskarta da mayafi. Har MC ya ɗan cije leɓensa yana jawo kulawa sosai. Maleekh cikin bugawar zuciya, wanda bai san fassara haka ba, ba tare da yasan abunda zai furta ba ya ce “Ina son ta.” Yayi shiru, sannan ya ƙara da wani muryar da ta cika taron kamar ana wasa da zuciya. “Ba saboda kowa ya ce mun dace ba, ba saboda bidiyo ba, ba saboda ta shahara ba... Sai dai saboda wata nutsuwa da nake samu idan ina kallon idonta. Ina son ta kamar yadda ake son zuciya a ɓoye, cikin daɗi da tsoro.” Ya ƙarasa kalaman idonsa akan ta.. Wurin ya ɓarke da ihu. Wasu na cewa "Allah ya kaimu biki!" wasu suna ɗaukar bidiyo suna cewa “Wannan speech ɗin yafi na proposal!” Amal kuwa... hawaye ne kawai ke gangarowa a gefen fuskarta, tana kallon ƙasa amma zuciyarta na motsi da wata sabuwar jin daɗi da tsoro... MC ya ɗauki mic ya ce: “Maleekh, muna godiya da ka tsaya tare da mu a wannan liyafa duk da irin girman matsayin ka. Amma akwai wasu ‘yan tambayoyi daga al’umma, suna so su ƙara tabbatar wa...” Maleekh ya gyara tsayuwa cikin kwanciyar hankali, yana duba inda Amal take zaune, har yanzu tana rufe da fuskarta da mayafinta. MC ya cigaba da cewa “Tambaya ta farko daga jama’a: Maleekh, me ya ja hankalinka zuwa wurin wannan bikin da aka san yana da matuƙar zaman lafiya da mutane masu sauƙi kamar mu?” Maleekh ya murmusa, ya ɗauki mic sannan ya ce “Wannan ba ɓoyayyen al'amari bane, kusan kowa a wurin nan yasan cewa A'isha ƙanwata ce ta jini, wacce muke uba ɗaya..." Amal ta ɗago tana kallonsa bata taɓa tunanin Maleekh da Aisha suna da wata alaƙa ba, ashe ma alaƙa ta kusa ne sosai, ta fara tunanin meyasa A'isha take supporting ɗin ta akan ɗan uwanta..." MC ya katse mata tunani da cewa. “Mun gode. Tambaya ta biyu, shin kai da Amal kuna soyayya ne? Duk da ka sanar cewa kana sonta, amma munaso mu ƙara tabbatar wa...” Maleekh ya fara tunanin cewa ashe dai a fili ya furta cewa 'yana son Amal...' Jama’a suka kaure da dariya da ihu ‘eeeeeeeeh!’ Maleekh ya ɗan yi shiru sannan ya ce: “Ban san inda soyayya take zuwa ba, amma zan iya faɗa da amincewa cewa Amal ita ce mace ta farko da ta sauya min tunani akan duniyar nan. Ita ce mace ta farko da ta bar ni ina tambayar kaina ko ina rayuwa cikin gaskiya ne. Ban san ko soyayya ce ba, amma na san tana da wani ɓangare a zuciyata da ban taɓa bari kowa ya shiga ba.” MC ya ce “Hmmm… gaskiya ka ɓata zukatan mata da yawa yanzu!” (Jama’a suka sake dariya) MC ya kuma cewa “Amal ta tsaya ta faɗi cewa ba ta soyayya, kuma tana ganin soyayya shashanci ne. Shin ka shirya ka gwabza da hakan?” Maleekh ya ce: “Idan wannan shashanci ne, to ni zan zamo babban shashi a gare ta. Saboda rayuwa ba komai bace face gaskiya, da mutunci, da jarumta irin na Amal.” MC ya ce “To Amal... kin ji da kunnen ki. Zaki bashi damar ya gwada miki gaskiyar zuciyarsa, ko dai har yanzu dai soyayya shashanci ce?” Amal ta ɗago a hankali, ta dawo filin wurin ta tsaya tana kallon Maleekh, sannan ta ɗauki mic tana murya ta na ɗan rawa ta ce “Ba wai bana son a so ni bane... Na ƙi soyayya ne saboda ta riga ta ƙone min zuciya tun kafin in gane me take nufi. Na sha wahala da yawa har na rasa iyayena... Har aka ƙi bani aikin da nake so, aka yi ƙoƙarin halaka ni… duk saboda rashin gaskiyar mutane.” Ta kalli Maleekh, idonta cike da ƙwalla ta ce “Amma kai... Kana daga cikin waɗanda suke so su rushe ni. Amma duk da haka ba ka tsaya kallon bidiyo ba, ka tsaya kallon zuciyata. Zan iya cewa: ka na kusa da samun amincewa daga zuciyata… amma ban gama yarda da duniya ba tukuna.” Taro ya sake kaurewa da tafi. Wasu na cewa "Alhamdulillah!" wasu suna ɗaga poster “Amaleekh Forever!” MC kuwa ya ja dogon “Wooooow!”... Bayan jawabin, wurin ya kaure da tafi da dariya, wasu daga cikin mutane sun riga sun fara ɗaukar bidiyon Maleekh suna cewa: "From business to feelings Maleekh in love!" "Amal and Maleekh: Nigeria’s realest power couple." Amal kuwa ta koma gefe bayan jawabinta, tana shaƙar numfashi, zuciyarta na bugawa cikin nauyin kalmomin ta... MC ya ce “To! Bari dai mu bar soyayya mu koma taro…” Yayin da suka koma wurin zama, Maleekh ya zauna gefen Amal. Sai ya ɗago wayarsa yana rubuta.. "A shirye nake na jira shekaru, idan hakan ne zai tabbatar miki da gaskiyata.." Amal ta karanta saƙon daga cikin wayarta. Sai kawai ta saki murmushi. Wannan karon, ba ta ɓoye ba... A lokacin da aka rufe liyafar da addu’a, mutane sun fara watsewa. MC da masu shirya biki suka zo wurin Amal suna ƙara gode mata, suna cewa jawabin da ta yi da kuma jarumtar ta ya sa mutane da yawa sun ji ƙwarin gwiwa.. Amal tana ƙoƙarin fita daga wurin taron ne sai taga PA ɗin Maleekh ya ƙaraso da girmamawa ya ce: “Zaki iya zuwa mu ga oga Maleekh, yana tsaye a garden. Yana son ya ce miki kalma biyu kafin ku watse.” Amal ta ɗan yi shiru, tana jiran amsar da zuciyarta zai bata, sai kawai zuciyarta ya bata cewa “Ki je ki ji abinda zai ce. Idan ba haka ba, zaki dinga rayuwa da tambaya a zuciyarki.” Gyaɗa kai kawai tayi, ta bi bayan PA ɗin Maleekh zuwa waje inda Maleekh ke tsaye, yana kallon sararin sama, ganin Amal yasa ya cire glass ɗin kan idonsa.. Amal ta tsaya daga gefe, sai yace da ita “Na san nayi abubuwa da yawa da suka ɓata miki rai. Kuma ban zo nan saboda izza ba. Na zo ne saboda zuciyata ta buga lokacin da kika ce... ‘soyayya shashanci ne’.” Amal ta ɗan murmusa kaɗan, ba tare da ta ce komai ba.. Ya cigaba da cewa “Zan iya zama duk abinda kika ɗauka na kasancewa mai iko, mai kuɗi, ɗan siyasa... amma a gaban ki, bana da komai face zuciyata. Kuma idan akwai matsayi da zaki iya yarda da ni daga shi, to ina so na tsaya a matsayin wanda zai kare ki, ba wanda zai yi amfani da ke ba.” Amal ta ce da shi a hankali: “Ka san me ya fi komai tsorata ni game da kai?” Maleekh ya ce “Menene?” Ta ce “Kai mai iko ne. kallo ɗaya ya ishe ka ka lalata rayuwar mace ko ka ɗaukaka ta. Kuma ba kai nake tsoro ba... sai zuciyata. Saboda tana iya faɗa maka duk abinda yazo rai, amma a yanzu zuciyata na cewa 'a’a' bazata amince dakai ba...” Maleekh ya kalle ta a hankali sannan ya ce “To bari na tsaya daga nan. Idan zuciyarki ta shirya... sai ki kirani.” Ya miƙa mata wata ƙaramar katin waya: a ciki sunan sa kawai ne da private line number. Bai ce komai ba, ya juya ya bar wurin.... 《☆☆☆☆☆☆》 Bayan Amal ta koma gida, ta sanar wa Inna yanda suka yi da Maleekh a wurin taron bikin, Inna farin ciki ta shiga yi domin kullum addu’ar ta shine Allah ya kawo musu sauyi.. Inna ta ce "To Amal yanzu me kika yanke a ranki? shin kema kina son sa ne?..." Amal ta sauƙe numfashi ta ce "Haba Inna sai kace daman abunda zuciyata take jira kenan? ni ba haka nake ba, ban taɓa jin inason Maleekh ba, kuma wannan al'amarin ban san yanda zan ƙira shi ba, mutane sun riga sun haɗa ni da Maleekh..." Inna cikin jin haushi ta ce "To banda abin ki yaron nan ya dawo bayanki fa, kiyi soyayya da shi mana ko dan kuɗin sa..." Amal yatsina fuska tayi tana kallon Inna. Ta ce "Inna yaushe kika dawo haka?..." Inna a fusace ta ce "Ya bazan zamo haka ba? So kike na mutu cikin talauci? alhalin ga dama yazo mana hannu, to wollahi sai kin so Maleekh..." Amal ba tare da ta furta komai ba, ta shige ɗakin ta... Tana shiga ta zauna a bakin katifar ta tana hawaye, da sauri ta ɗauko jakarta, ta ciro wani ƙaramin hoto, hoton wani yaro ne yana sanye da uniform a jikinsa, ga kuma ita kanta Amal ta rungume da yaron suna dariya aka ɗauki hoton....lokacin bazata wuce shekara biyu zuwa uku ba, tin iyayenta suna raye.... Amal tana hawaye a fili take furta "Maleekh ban sani ba ko kana raye ko ka mutu, ban san aina kake ba, na sanu a kafafen sada zumunta da television da sunana ɗaya Amal Abdulsamaad, sunan da ka sanni dashi tin muna yara amma hakan bai sa ka nemi yanda nake ba, meyasa?, kai ka kasance abokina na musamman sannan me bani shawara, yanzu inaso ka bani shawara akan wani kulallen lamari..." Amal tana kallon yaron jikin hoton ta ce "Akwai wani matashin saurayi mai ji da kansa, mai girman kai amma a yanzu ya sauƙe girman kansa a gabana, yana bayyana mun saƙon zuciyarsa..." Ta ja dogon numfashi sannan ta ce "Kasan wani irin saƙo ne? Saƙon Soyayya, kuma kasan meye sunan sa? to sunansa Maleekh..." Tayi murmushi sannan ta ce "Irin sunanka gare shi, ina matuƙar girmama masu irin sunanka Maleekh, yanzu gaya mun zan amshi saƙon soyayyar sa ko kuma na sharar da shi kawai?...." Ta ɗago hoton saitin kunnenta tana sauraron abinda yaron jikin hoton zai ce mata, ba tare da taji komai ba ta tintsire da dariya tana faɗin "Gaskiya Abokina ka haɗu, wato ka bani shawara mai kyau, kada na nuna masa soyayya yanzu sai ya sha wahala, zan rinƙa juya masa baya, ina wahalar da shi, idan da gaske ne soyayyarsa to zai cigaba da bibiyata, idan kuma bada gaske bane zai ja baya dani, good hakan yayi yanzu wasan zai fara..." Ta mayar da hoton cikin jakarta... 《☆☆☆☆☆》 A Bangaren Maleekh kuwa yana zaune a office ɗinsa, dake nan Kaduna, kamfanin Cashbank....sai ga PA ɗinsa ya shigo, ya ce "Boss! Lamarin ka da Amal yana ta baza duniya akan cewa kuna soyayya, har an fara buga banner hotonka dana Amal, taken banner shine 'AMALEEKH LOVE NEVER END' shin me ka shirya a lamarin, ga shi Amal ta ƙi amince da kai..." Murmushi Maleekh yayi yana zuƙar shisha ya ce "Hakane, ta ƙi amincewa a gaba na amma ta amince a idon duniya, kuskuren ta kenam, bazata taɓa goge wannan ba, yanzu ne zan fara buga ball ɗina, ta nuna mun tsananin taurin kai, tayi amfani da mic wurin tozarta ni, ta wulakanta ni to zan nuna mata cewa Maleekh ba sa'an buga ball ɗinta bane, zanyi amfani da zuciyarta wurin buga wasa na.....zan fito mata a Maleekh mai karyayyen zuciya, zan nuna mata tsananin so da ƙauna, zan bada kulawa na gaskiya, zan shayar da ita ruwan zuma amma duk na wucin gadi ne, idan kanaso ka cika burinka to sai ka sauƙe girman kan ka, zan juri duk wulakancin da zata mu amma da zaran ta kamu da matsanancin sona, wanda idan bata sameni ba zata iya mutuwa, ni kuma a lokacin yi break up da ita, saina tawarwatsa mata zuciya..." PA ne ya jinjina kai sannan ya ce "Boss ni daman nayi mamakin sauyawarka lokaci guda akan yarinyar nan, ashe akwai kullin da kake mata, idan baka ɗauki fansa ba, bazaka taɓa samun kwanciyar hankali ba...." Maleekh ya ce "hakane..." 《☆》 Daga wannan lokacin ne Maleekh ya fara shishige wa Amal, akoda yaushe yana kan bayyana mata zuciyarsa, cikin kalar tausayi yake zuwa mata ya nuna mata cewa 'ta sauyar da shi kuma bazai taɓa mantawa da ita ba..." Yau da misalin ƙarfe 5 na yamma Maleekh ne ya sauƙa a gidan su Amal, bayan ya Parker motarsa a ƙofar gidan, haka yake ƙare gidan da wani irin kallon up and down domin yana tunanin abun tozarci ne ya rinƙa shigowa unguwar balle har cikin gidan... Bayan ya shiga gidan da murmushi akan fuskarsa, yayi sallama cikin ƙwarin gwiwa... Inna tana zaune ganin Maleekh yasa ta fara washe baki, tana masa sannu da zuwa.. A tabarma Maleekh ya zauna suka gaisa da Inna, daga baya sai ga wasu mutane sun fara shigo da buhuhhunan kayan abinci, da wasu kayayyaki na abinci da zannuwa manya a Inna... Sai wani ƙaton akwati wanda yake cike da kayayyakin sakawa masu tsada, ya kawo su a Amal.. Maleekh yana zaune tare da Inna suna shan hirar su akan Amal, Inna tana bashi tarihin rayuwar Amal da irin taurin kai da take da shi tin tana ƙarama, sai jin sallama suka yi... Inna ce ta ɗago tana amsa wa tare da faɗin "Yawwa gata nan ta dawo ƴar albarka ta Amatullah..." Amal tana sanye da dogon hijab har ƙasi da littafin Al'kur'ani mai girma ta dawo daga hadda... Tin a waje ta ga motar Maleekh, a fusace ta shigo gidan fuska a haɗe domin bata son yana zuwa musu gida... Amal haka take bin kayayyakin abinci da aka ajiye su da kallo sannan ta maida kanta kan akwati, still eyes ɗinta suka sake sauƙa akan manyan atamfofi guda biyar... Amal fuska ba annuri ta ce "Wannan fa? wa ya kawo su?..." Inna ta ce "bakya ganin Maleekh a zaune ne?..." Amal ta ce "Na ganshi mana, meye sa ya kawo kayayyakin nan?..." Inna ta ce "saboda soyayya mana, yana son ki shiyasa ya fara miki ihsani, kinsan soyayya da kyautatawa yana ƙara dankon soyayya..." Amal tana kallon Inna ta ce "Ki ai bai samu soyayyan ba tukun, kuma ki sanar masa cewa bazai taɓa samun soyayyata ba..." Inna turo baki tayi tana hararar Amal, sai ji tayi Maleekh ya ce "Inna! Ki sanar mata cewa soyayyarta zai kashe ni, Inna idan bata soni ba zan iya mutuwa..." Amal ta ce "Inna! Ki sanar masa cewa bana son jin wannan tatsuniyarsa, Amal bazata taɓa amincewa da shi ba, sannan ki sanar masa cewa dubu ya shi waɗanda suka mutu a soyayya, don haka idan ya mutu bai dame ni ba..." Maleekh ya ce "Inna meyasa bazaki sanar mata irin matsalar da zan shiga saboda ita ba?..." Amal ta runtse idonta sannan ta ce "Inna ki sanar masa cewa yabar gidan nan..." Maleekh ya ce "Inna kice mata bazan bar gidan nan ba, har sai ta ce tana sona..." Amal a fusace tayi waje ta je ƙiran mutanensa da suka shigo da kayayyakin, sai gasu sun shigo gidan, cikin masifa Amal take nuna su da yatsa tare da sanar musu... "Duk kayayyakin da ku ka shigo dashi inaso yanzu a fitar mun dasu daga gidan nan, bana buƙata..." Inna wacce kanta ya gama ruɗe wa sai yanzu tayi magana tana faɗin "Kina da hankali kuwa Amal? kin san cewa bamu da komai a gidan nan yanzu kuma Allah ya kawo mana kice bakya so? to in bakya so ni inaso..." Amal ta ce "bana ƙaunar ganin kayayyakin nan, a fitar mun dasu ko na cinna musu wuta..." Maleekh ne ya dakatar dasu da cewa. "Bana kyauta sannan a maida mun da kyauta baya, wannan dabi'ar matsiyata ne, amma asalin mai arziki baya karɓan kyautar da ya bayar...don haka bazan maida abinda ya fito daga hannuna ba...." Cikin fushi Amal ta ce "ko ma ina zaka kai, ka kai amma ni bana so..." Ganin Maleekh bashi da niyyar aiwatar da abinda take so ne yasa ta fita ta ƙira matasan ungunwar da mata akan su tattara kayan ta basu kyau, su je su raba, sannan ta ɗauki akwatin ta bayar wa matan cewa su ɗauka ta bar musu, tazo zata tattari zannuwan Inna, da gudu Inna ta durƙusa ta rungumi zannuwan sosai, amma duk da haka sai da Amal ta karɓe su da ƙarfi daga hannun Inna sannan ta bayar da su....Inna tana ihu a bata kayan ta amma tass saida Amal ta rabar... Maleekh yana tsaye ya ji Amal ta ci kwalar rigarsa tare da finciko shi, tana riƙe da kwalar sa ta ja shi zuwa waje, suna fita ta ture shi tana nuna shi da yatsa ta ce "Warning na ƙarshe, kada ka sake kawo mana wani naka domin mu ba mabukata bane, akwai masu neman taimako da yawa meyasa baza kaje ka tallafa musu ba? to bari kaji idan na ƙara ganin ƙafarka a cikin gidan nan saina karya ƙafar..." Daga nan ta shige gida ta barshi a tsaye, daga baya ya girgiza kai shima ya shiga motarsa, sai wani mota daban wannan security sa ne a ciki, haka suka ja mota suka tafi... Amal tana shiga ta tarar da Inna a durƙushe sai kuka take tayi... Amal ta zauna a gabanta ta ce "Kiyi haƙuri Inna, kiyi ta addu'a Allah ya buɗa mun zan miki abinda kike so, har makkah zan kai ki..." Amal bata iddasa maganar ta ba taji Inna ta rufe ta da duka, tana kuka tana faɗin "Ai kekam bazamu taɓa yin abin arziki ba, da talaucin mu zamu cigaba da rayuwa, baki da shi amma kin samu hanyar samu shine baza kiyi amfani da damar ki ba, da haka kike cewa zaki kai ni makkah? ..." Haka Inna take jibgar ta kamar ta samu flawa, Amal miƙe wa tayi tana ƙoƙarin kare kanta... Inna ganin dukan bazaiyi ba yasa ta kafa haƙoran ta a saitin dantsen Amal ta garzaya mata cizo.. Amal wani ƙara tasau tare da ruga wa cikin ɗaki da gudu, tayi saurin rufe ƙofa tare da danna sakata... Inna ci gaba da ihu take kamar wanda aka aiko mata da saƙon mutuwar wani jininta.. Tana cikin ihun idanunta suka sauƙa akan wani ɗan envelope, ɗauka tayi tare da buɗe wa, tayi kici6us da ƴan dubu-dubu sun kai ɗari... Washe baki tayi wanda duk goro ya dafar mata da haƙora...da sauri ta cusa envelope a cikin aljihun rigarta, tana faɗin "Allah sarki yaron kirki, Allah yayi albarka ai daman nasan bazaka bar ni haka ba....wannan hegiyar yarinya nasan idonta na sauƙa akan kuɗin nan zata iya karɓa ta mayar masa, ita da baza'ayi abun alheri da ita ba...." Amal tana zaune a bakin katifa sai mulmula wurin da Inna ta cije ta take, amma hankalin ta na kan Maleekh, ba wai tayi haka don saboda bata sonsa ba, tayi ne saboda ta ja masa aji sannan yana kan gwajin ta ne, in har zai iya jure duk wulancin da zata masa na tsawon wata watanni to zata amince da soyayyarsa, amma in har ya kasa, ya nuna mata zuciya sannan ya daina zuwa yanda take to itama zata sharar da shi, wannan shine gwajin.... Murmushi tasau marar fassara sannan ta kwanta a saman katifa tana kallon ceiling.... A bangaren Maleekh kuwa ya koma GRA unguwar da yake zaune anan Kaduna, yana zaune akan sopa idonsa akan plasman amma hankalinsa na kan Amal, yana tunanin ta yanda zai ja wo hankalinta kansa, ta kamu da matsanancin son sa... A fili ya furta "Amal bazan bari ki sha ba, zan ci gaba da naci har sai kin kamu da soyayyata, bazan taɓa yin ƙasa a gwiwa ba, sai kin so ni, domin babu macen da zan furta soyayya akan ta tayi rejected ɗina, ƴan mata da yawa su suke neman soyayya ta, ban taɓa furta kalmar soyayya akan wata ƴan mace ba, sai akan Amal sannan ta wulakanta ni? wani irin zuciya ne da ita na ƙashi? but I will try my best..." Bayan kwana biyu Maleekh ne ya ziyarci gidan ƴar uwarsa ƙawar Amal wato A'isha... A'isha tayi farin cikin ganin Yayanta Maleekh a gidanta. Ta haɗa masa kayan ciye-ciye da kayan fruits, sun juma suna wasa da dariya kafin daga bisani Maleekh ya yi gyaran murya... Yana kallon A'isha ya ce "Bayan ziyara akwai wani abu mai muhimmanci da ya kawo ni wurin ki..." *NEXT...* asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 15 to 16 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 A'isha ta ƙafe idonta akan Maleekh cike da mamaki ta ce "Ehen! Ina sauraron ka Yaya..." Sai da ya sauƙe numfashi kafin ya ce "maganar akan Amal ne, inaso ki mun wani taimako..." A'isha ta ce "Amal kuma? meya faru?..." Maleekh yana lumshe sexy eyes kamar mai jin bacci ya ce "na kamu da matsanancin ƙaunar ta, amma ita sam ta ƙi yarda da ni, shiyasa nake so ki taya ni kamfe..." A'isha zaro ido tayi lokaci guda ta saki dariya tare da faɗin "Yau kuma Yaya Maleekh ne mai neman kamfe akan mace? very surprised 😮, but abin da nake son sani shine, a lokacin party bikina Amal kamar ta nuna tana supporting ɗin ka why now?..." Maleekh ya sau murmushi shi kaɗai yasan abinda yake shiryawa a ransa, shi kaɗai yasan irin tarkon da yake ɗana wa Amal, amma ya basar yana nuna wa A'isha cewa "Da gaske nake son Amal, ta nuna ba komai a gaban mutane but yanzu tana mun kallon biri I don't know why..." Aisha ta ce "shikenan Yayana ina supporting ɗinka sosai kuma zan yi farin ciki idan soyayyar ku ta 'kullu, insha Allahu zan je gidan su Amal, zan same ta da maganar amma da sharaɗi Yaya..." Maleekh ya jinjina kai sannan ya ce "meye sharaɗin?..." A'isha ta ce "kasan yanda nake ji da Amal, bana son wani abu ya same ta, ka riƙe mun ita da amana, kada ka cutar mun da ita, but wallahi idan kayi broken heart ɗin ta, uhmmm bazan yafe ba Yaya, duk da ka kasance ɗan uwana na jini..." Murmushin gefen baki Maleekh ya yi tare da nuna yardar sa amma a cikin zuciyarsa cewa yake... "Tafiya ɗaya ne da yaro mai ji da kansa, maganin irin su Amal broken heart, anan zasu gane cewa da ruwa ake shayi..." Anan suka yi sallama Maleekh ya yi tafiyarsa... Da daddare misalin ƙarfe 9 Amal tana kwance sai ji tayi wayarta na ringing.. Ɗago wayar tayi tana duban number, ganin sunan da ya bayyana akan Screen ɗin wayar ne yasa zuciyarta bugawa, (Amaleekh) sunan da ya bayyana kenan, murmushi tasau tana riƙe da wayar tana jiran ƙiran ya yanke sai ana biyu ta ɗauka domin tasan nacin sa bazai daina ƙira ba har saita ɗaga... Ƙira na biyu ne ya sake shigo wa nan ma sai da ta kusan yanke wa kafin ta ɗauka tare da karawa a kunne, lumshe golden eyes ɗinta tayi tana jiran sauƙar zazzakar muryarsa... Shima daga can ɓangarensa yana kwance akan katafaren gadonsa, a hankali ya furta "Amincin Allah ya tabbata a gareki sarauniyar kyawawan halittu..." Wani irin farin ciki taji ya ziyarci zuciyarta, sai da ta daidaita kanta tukun cikin rashin mutunci ta ce "Waye akan layi?..." Maleekh ya yi murmushi sannan ya ce "kin manta ba'a gidan rediyo kike ba fa..." Ta ja dogon tsaki sannan ta ce "wai kai wani irin nacaccen mutum ne? wai sau nawa kake so na sanar maka cewa ka fita daga cikin rayuwata? i hate you..." Maleekh ya danne zuciyarsa saboda a rayuwarsa mace bata taɓa tsayawa a gabansa tana gaya masa maganganu haka ba, har ma tace ta tsane shi... Cikin sassanyar murya ya ce "kiyi haƙuri, ba yanda na iya ne, nacin zuciyata akan soyayyarki na so yafi ƙarfin kwakwalwa ta Amal, ki tausaya mun mana..." Cikin fusata ta ce "ka ga malam dakata, da can meyasa ka zamo abokin gaba ta? sai yanzu zaka dawo mun wai soyayya? shin kana cikin hankalinka kuwa? anya baka shaye-shaye? ko dan kana shan shisha ba abinda baza kayi ba, in ance kwakwalwarka ma ta juye ba laifi, gargad'i na ƙarshe kada ka sake ƙiran wayata..." Daga nan ta ƙatsar da ƙiran sannan ta ɗora wayar akan ƙirjinta tana sakin kayataccen murmushi... A hankali ta furta "tafiya ɗaya ne ga yaro mai ji da kansa, wannan girman kan naka saina sauƙe maka shi akan titi Maleekh, rashin mutuncin da ka daɗe kana shukawa yanzu ne daidain girbe wa..." A ɓangaren Maleekh kuwa bayan katsar da waya a take yayi wurgi da wayarsa sai a jikin bangon ɗakin, nan wayarsa ƙirar IPhone 50pro ya tawarwatse, bai shigo Nigeria ba tukun 🙄.. A ruɗe yake faɗin "Ni ne mahaukaci? ni ne nake shaye-shaye? Innalillahi yau mace ce take ƙira na da mahaukaci?..." Nan ya fara wurgi da pilillikan gadon, ya sauƙo yana dukan jikin bango da ƙarfi, wani irin ihu yake na baƙin ciki da tsantsar tsanar Amal, wani irin naushi ya kai wa mirror ɗakin, nan take ya tawarwatse, ya dun'kule hannunsa yana nausar jikin bango tare da furta. "Sai na kashe ki Amal! sai na juya rayuwarki Amal!! sai na ja kanki a tsakiyar titi Amal, na tsane ki Amal, nine mahaukaci? zan nuna miki ni cikakken mahaukaci ne wanda zaiyi raga-raga da rayuwar ki, ƴar matsiyata, ƴar talakawa, ƴar shegiya ..." Da gudu PA ya shigo jin ihun Maleekh, zuwa yayi ya riƙe shi sosai yana ƙoƙarin rungume shi, domin dukan bangon da yake yi yasa hannunsa ya farfashe, ga hannu kalar na hutu bai taɓa ɗaukan abu mai wahala ba, fashewar hannun abu ne mai sauƙi... Da ƙyar PA ya samu damar zaunar da shi a bakin gado yana rarrashinsa.. Maleekh yana huci ya ce "Ta ƙira ni da mahaukaci, sannan ta ƙira ni da mai shaye-shaye, shin wani irin hukunci zan mata ne wanda zai sa na huce? idan ban kashe ta na daina ganinta a duniya ba bana tunanin zan huce..." PA yana bashi haƙuri ya ce "Boss yanzu kana cikin raɗaɗin zuciya, komai ma zaka iya faɗa, idan kanaso ka cimma burinka to ka zama mutum mai juriya, ka daure ka ɗauki duk wasu kalamanta na 6atanci amma kasa a ranka akwai ranar da zata biya, biya mai tsoka, yanzu ka fara tunanin jawo hankalinta kanka, ka rinjayi zuciyarta sannan sai lissafi ya tafi dai-dai, zamu koya mata darasin da ba'a koya mata a school ba, tin da har tasa Boss ɗina ya zubda hawaye to saita biya..." Maleekh jin PA yace ya zubda hawaye ne yasa ya miƙe a ruɗe yana goge hawayen fuskarsa tare da faɗin. "Akan me zan zubda hawaye akan wannan ƙasƙantacciyar yarinya marar class, ƴar talakawa fa'kiriya irin ta, god forbid hawaye na bazasu taɓa zuba akanta ba, tayi kaɗan wallahi..." Da ƙyar PA ya rarrashi Boss ɗinsa....sannan ya ɗauko boxing na magani, yazo ya yi treats ɗin hannunsa da yaji ciwo.... 《☆Bayan kwana biyu☆》 Amal na zaune akan tabarma tana rubutu a wani takarda, sai ga sallamar A'isha, ɗago kai Amal tayi, ganin A'isha yasa ta miƙe ta ruga da gudu ta rungumeta cikin farin ciki take faɗin "Yau Amarya ce a gidan mu? yaushe ma akayi Auren har zaki fara fita yawo?..." A'isha ta ce "ai ke kika fito da ni..." Amal ta ce "ni kuma? taya kenan?.." A'isha ta ce "ta hanyar cutar mun da zuciyar ɗan uwana mana, yana can zai hallaka kansa saboda tunanin ki da damuwar da ya ɗaura wa kansa saboda ke..." Amal tsummm tayi tana kallon A'isha daga bisani ta ja hannunta suka ƙarasa ciki, Amal ce ta leƙa ɗakin Inna tana faɗin "Inna A'isha tazo..." Amal idonta ne ya sauƙa akan kifi baje-baje a gaban Inna sai turawa take tayi... Amal cike da mamaki ta ce "Inna aina kika samu kuɗi har da siyan kifi har haka?..." Inna ta ce "A gidan uwarki.." ta faɗa daidai lokacin da ta ƙara tura kifi bakinta... Amal ta ce "Inna nasan bakida sisin kobo a gidan nan, kuma ba wani ne yazo ba balle kice anyi miki kyauta ne..." Inna tana harararta ta ce "Wato sai inta zama da bushashshen baki kamar naki koh? Allah ne ya kawo mun buɗi lokaci guda, don haka zanyi amfani da damata ce, ke ki je can ki ƙarata..." Amal ta ce "Inna, in baki gaya mun wanda ya baki kifin nan ba, wallahi bazaki ci ba..." Inna a fusace ta ce "Idan kin hana kin ci gwafar ubanki, Maleeku ne ya bani kuɗi na saya ko zaki karɓe ne?..." Amal ta ce "Maleekh kuma?...ina kuɗin da ya baki?.." Inna ba shiri ta zari taɓarya a gefenta tare da miƙe wa tana huci ta ce "In ban ragargaza miki kai anan ba ki canza mun suna, in kin isa zo ki karɓe kuɗin, saboda mugunta irin naki waton kina mun baƙin cikin kyautar da ake mun koh? Ni in banda Maleeku da naci ban ga abinda ya gani a jikin ki ba, kina wulakanta shi, Allah dai ya karkato kansa kaina cikin kwana biyu zance a ɗaura mana Aure, shashashar yarinya..." A'isha ce ta riƙo hannun Amal tana cewa. "Kin ga Amal zo mu shiga ɗakin nakin..." Sannan A'isha ta kalli Inna ta ce "Inna kiyi hakuri ki ci kifinki ki ƙoshi, duk kyautar da ya miki ki karɓe kar ki zauna da babu, Maleekh halattaccen sana'a yake yi balle ace kuɗin jini ne..." Inna tana huci ta ce "ai ko kuɗin ɗiwa ne saina ci ɗin, kuma tayi magana in fiffige mata nonuwa inyi wurgi da su, ai Maleeku idan yaga babu su tinin zai dawo kaina..." Aisha ta kwashe da dariya har da kama ciki.. Amal tana ji ta ce "A wasu shanyayyun kirji da suka gama shekaru a yanƙwane..." Da gudu Inna ta fito da taɓarya zata rausa mata, ai kuwa itama Amal da gudu ta shige ɗakinta ta rufe, haka Inna take doka taɓarya a ƙasi tana ihun ƙauraye... "Ki fito in kin isa, akan Maliku saina sheme ki a gidan nan..." A'isha ce take bawa Inna haƙuri, ganin Inna ta ƙi sauƙowa ne yasa tayi saurin cewa. "Inna kuliya kifinki, ya shiga ɗakin ki..." Ai da gudu Inna ta shiga ɗakin tana faɗin "Yau na shiga uku ni Delu kifina..." haka take tsinewa kuliya, tana kururuwar kifinta kar kuliya ta cinye mata... A'isha kuwa daman ƙarya take itama da sauri ta tura ƙofar Amal ta shige suka sake rufe wa... Saida suka gama shan dariyarsu mai isarwa a cikin ɗaki, kafin suka dawo dai-dai... Sai da suka huta can suna kwance sai Amal ta taɓo A'isha tana faɗin "Yawwa me kike cewa ne akan Maleekh? kika ce yana cikin damuwa?..." A'isha ta harareta sannan ta ce "ban sani ba, ai nasan kema kina sonsa, shine zaki na wulakanta mun da ɗan uwa, Allah bakida kirki Amal..." Amal ta sauƙe numfashi sannan ta ce "wa ya gaya miki ina son sa? shine dai yake nace mun, ni kuma banida lokacin soyayya da shi..." A'isha ta ce "iyeee a gaban nawa kike cewa bakya son sa? to meyasa a wurin taron bikina kika nuna cewa ba komai..." Amal ta kalleta sannan ta ce "Amma nace inasonsa? Ban faɗa ba, kawai dai banaso na tisgashi a gaban mutane shiyasa na nuna masa goyon baya amma bayan haka babu soyayyarsa a zuciyata kuma ba'a soyayya dole, ki gaya masa cewa bazai samu shiga ba, yayi haƙuri ya nemi wata..." Aisha ta ce "Amal meyasa kika koyi wulakanci ne? Ke fa da bakin ki kike cewa 'mutum yaso mai sonsa, kada ka wulakanta wanda ya furta maka kalmar soyayya..' shin duk ƙarya ne bai je zuci ba, wato kinaso ki ɗora mutane akan hanya ke kuma kina tafe a gefen hanya..." Amal ta ce "nace haka amma ba mutum irin Maleekh ba..." Aisha cikin nuna fushi ta ce "shi meye ne? Meye aibunsa?..." Amal ta ce "Ina tsoron mutum irin Maleekh, duba da irin ƙiyayyar da ya nuna mun a baya...bana son na shiga tarkonsa..." A'isha ta ce "shin baki yadda dashi bane, wani irin soyayya zai nuna miki wanda zaki yadda da shi?..." Amal ta ce "Ya fara fita yaje television ya fuskanci mutane ya tsago kalaman soyayya wa Amal, sannan yayi alƙawarin zai riƙe Amal bisa gaskiya. Idan yaci amana kuwa to amana zata ci shi..." A'isha ta ce "inada tabbaci akan ɗan uwana, saboda tinda yake a rayuwarsa bai taɓa kallon idon mace yace yana sonta ba, sai akanki Amal, idan haka kike so yayi miki zaiyi..." A'isha ta miƙe tana riƙe da jakarta ta ce "ni zan wuce, sai ki fara duba television da sauraron rediyo domin jin ƙarin bayani..." Daga nan Aisha ta tafi, amma bisa alamun ranta ya sosu sosai...itama Amal ta fahimci haka, murmushi kawai tayi tana jinjina kai.... Washegari A'isha ne ta je gidan Maleekh da batun.. Maleekh yana zaune a cikin babban falonsa da ke gidansa, yana kallon fuskar ƙanwarsa A’isha wacce ta zuba mishi ido tana jiran amsar da zata fito daga bakinsa. Ita kanta tana mamakin yanda lamarin ya rikice haka tsakanin Amal da ɗan uwanta. A’isha ta girgiza kai tana cewa: "Yaya Maleekh, ga dai sharaɗi Amal, indai kana sonsa da gaske to dole sai kayi abinda ta umarce ka, domin Amal bata da saurin yadda, tanaso ka bayyana hakan a idon duniya kafin ta amince da kai..." Maleekh ya ɗaga hannunsa yana dariyar da ta nuna ba ya ɗaukar maganar da muhimmanci sosai. Ya ce “A’isha, kin san ni ai. Ban taɓa shiga wasan da ba na da tabbacin nasara. Soyayyar Amal kuwa, wata hanya ce kawai ta nuna ikon da nake da shi a gaban jama’a. Zan fito a tv in faɗa wa duniya cewa ita ce masoyiyata… duk duniya zata gane cewa ni Maleekh, wanda babu mai iya tsayar da shi, na ɗauki ƙaramin abu kamar ita na mai da shi sanadin farin ciki na.” Ya tsaya ya ɗan lumshe ido, sai kuma ya ƙara da cewa a cikin ransa... “Idan na bayyana soyayyarmu a fili, za ta zame min hanyar da zan wulakanta ta, ta yadda duk irin darajar da ta tara a idon mutane zata ruguje. Ni dai kawai ina so in nuna wa duniya cewa babu mace da zata guje ni, komai yanda take da suna ko tsarki.” A’isha ta sau murmushi ba tare da sanin shirin ɗan uwanta ba...ta ce “Inaso ka fahimci cewar yaudarar Amal tamkar kana ci gaba da tunkarar raguwar mutuncinka ne, Yaya Maleekh? Amal ba irin sauran matan nan da zaka taɓa ba ne. Wallahi kana da wuya ka shawo kanta da wannan dabara. Kuma ina jin tsoron wata rana ta juya maka da abinda baka zato, saboda haka inma kanada wata manufa a ranka to kayi gaggawar cire wa....” Maleekh ya saki murmushi mai cike da izza, ya matso kusa da ita, a cikin zuciyarsa ya fara da cewa. “Ni Maleekh, na san yadda zan sarrafa komai. Kin ji ni ko, A’isha? Zan fito a tv, na faɗa cewa na fa ɗa soyayya da Amal, duniya ta ji. Bayan haka kuma, ita kanta zata sha mamakin irin sakamakon da zata gani. Wulakanci ne nake nema a kanta, ba soyayya ta gaskiya ba.” A fili kuwa ya furta "Ƴar uwa kenam kema baki yadda dani bane?..." A’isha ta ja dogon numfashi, ta san Yayanta zai iya amfani da soyayya ya ruguza mace, duk da bai taɓa aikatawa ba amma tana da tabbacin zai iya. Ta kalli Maleekh da ido mai cike da damuwa, tana fatan abin da ya tsara kar ya zama sanadin halakar shi da rayuwar Amal gaba ɗaya, amma wata zuciyar ta yadda da shi..kuma ta kudurta taya shi yaƙin neman soyayyarsa.. A’isha bata san meye a zuciyar ɗan’uwanta ba. Ita a tunaninta soyayya ce kawai ta kama shi, sai dai ba ta san irin tsananin shirin da ya ɗaura ba. Wanda yasan ainihin shirin shi kuwa ba kowa ba ne face PA ɗinsa (Personal Assistant), wanda kullum yake tare da shi, yana ɗaukar sirrinsa yana kuma ƙarfafa shi akan wannan tafiyar. PA ɗin nasa kuwa bai tsaya kawai da goyon baya ba, har ma shi ne yake tsara hanyoyin da Maleekh zai bi don cimma manufarsa akan Amal. Shi ke yi masa tunatarwa, “Boss, ba’a samun irin wannan mace sau biyu. Ka nace, ka da ka bari ta kuɓuce maka.” A wannan ranar ne Maleekh ya shirya fitowa television, a cikin shirin da Maleekh ya ƙulla, ya shirya ya fito a talabijin a wani shiri na musamman da kamfaninsa zai gudanar. Ba don komai ba illa ya bayyana soyayyarsa ga Amal a bainar jama’a, ta yadda ba ita kaɗai zata ji ba, duniya ma zata shaida. Wannan matakin kuwa babban rikici zai tayar domin zai kama Amal ba tare da ta shirya ba... Maleekh yana zaune a cikin babban ɗakin taro na kamfaninsa dake nan kaduna, inda aka shiryawa TV interview. Hasken kyamarori yana haskawa, muryar ɗan jaridar da ke tambayarsa tana cika wurin. “Sir Maleekh,” ɗan jaridar ya fara da ladabi, “a kwanakin nan ana ta rade-radin cewa kuna da alaƙar soyayya da wata matashiya mai suna Amal, wacce aka sani da sahihiyar murya wajen magana da gaskiya da adalci. Shin wannan gaskiya ne?” Maleekh ya ɗan murmusa, ya ɗan lankwasar da wuyansa, yayi kalar tausayi ya ce. “Eh, gaskiya ne. Ina sonta da gaske. Amal ce hasken zuciyata. Na yarda cewa in ba tare da ita ba rayuwata ba zata cika ba.” PA ɗinsa yana tsaye gefe yana kallon shi da murmushi mai nuni da cewa shirin nasu yana tafiya yadda suka tsara. A wajen duniya, Maleekh na nuna so mai zurfi kamar ransa zai fita saboda Amal. A'isha kuwa, ƙanwarsa, tana zaune a gidanta tana kallon TV tana murna, zuciyarta cike da alfahari: “Allah ya haɗa kan su, wannan soyayyar gaskiya ce ta zuciya.” Ta ɗauke shi da gaske, bata san cewa a cikin zuciyar ɗan uwanta akwai wani mugun shiri ba. Maleekh a cikin zuciyarsa yana tunani: “Sai na shigar da soyayyata a cikin zuciyarki Amal, sai kin amince. Bayan kin kamu sosai, zan nuna miki cewa ke ba kya da wata daraja a idanuna. Zan nuna miki ƙasar duniya ta banbanci tsakanin mu biyu.” Ya ƙara jefa kalmomin soyayya a cikin amsoshin interview ɗin, wanda hakan ya sa jama’a suka yi ta jinjina masa a matsayin saurayi mai gaskiya da kishi. Duk da cewa Amal ta ji daɗin ganin Maleekh a talabijin yana yabonta, tana ɗaukar taken “ƙarfin murya ta mata masu gaskiya”, bai hana ta ɗaure fuska ba. A idon duniya, bata nuna ta amince da shi ko ta ji daɗin yabon sa ba. Ta yi kamar bata damu ba, domin Amal mace ce mai dauriya, mai son a yabe ta bisa aikinta ba wai saboda wani namiji ba. Amma a cikin zuciyarta? Wani irin farin ciki ya cika mata ƙirji. Kalaman Maleekh sun daɗa ƙarfafa ta, sun bata kwarin gwiwar cigaba da tafiyarta. Sai dai ta yi ƙoƙarin boye wannan farin ciki daga kowa, har ma daga kawarta A’isha. Shi kuwa PA ɗin Maleekh yana gefe yana kallon wannan shirin, yana dariya cikin ransa. Shi ya fi kowa sanin cewa duk wannan shirin Maleekh akan Amal akwai zurfi babu wasa a ciki. Kuma saboda yana goyon bayan shi, ya riga ya ɗauki wannan al’amarin tamkar nasu su biyu ne. A’isha kuwa bata fahimci komai ba. A ganinta Maleekh dai mutum ne mai son fitowa fili yana yabon kowa. Bata san asalin dalilin da yasa yake ƙoƙarin shiga zuciyar Amal ba. Ita dai abin da ta gani shi ne Yayanta yana ƙoƙarin nuna soyayyarsa a bainar jama’a... A ranar kuwa A'isha ta koma gidan su Amal..Suna zaune su biyu, Inna kuwa bata nan.. A’isha tana dariya tana kallon Amal ta ce “Amal, kin ga yadda ya fito a tv saboda ke? Yayana fa ya fito duniya ta sani saboda soyayyarki. Kina da sa’a wallahi.” Amal ta ɗauki remote ta kashe ƙaramin tv dake manne a ɗakinta, ta yi ɗan murmushi ba tare da ta dubi A’isha ba ta ce. “Wannan ba yana nufin zan amince da shi bane. A’isha, kin san halin Yayanki. Ban ga dalilin da zai sa in ɗaura kaina a rayuwarsa ba.” A’isha ta ɗan turo baki sannan ta ce “Ke dai kin fi kowa sani. Amma wallahi ina ganin wannan soyayyar gaskiya ce.” Amal ta ɗauke fuska, amma zuciyarta na cike da farin ciki ta ce “Bari dai lokaci ya nuna gaskiya. Amma ni ban amince ba tukuna.” Suna cikin hira sai ga wayar A'isha na ƙara, tana dubawa taga sunan Yaya Maleekh ya bayyana akan Screen, murmushi tayi tare da ɗaga wa, a bangaren Maleekh kuwa cewa yayi. "Kina tare da Amal ne?..." A'isha ta bada amsar "eh..." Ya ce "Toh! Ki ɗauke ta kuje kiyi mata shopping, ta taya ki zaɓen duk abinda take so a supermarket, Nima zan je wurin zan biya kuɗin..." A'isha ta ce "To ba damuwa..." Ta katsar da wayar tana duban Amal, sannan ta ce. "Yanzu dai tashi ki rakani shopping.." Amal ta dube ta tace "kinga ban fa yi wanka ba, kuma ki bawa Angonki yayi miki mana..." A'isha ta ce "ai ba Angon ne zai sa abinda zan saka ba, kuma inaso ki taya ni zaɓen kayayyaki ne.." Amal ta ce "To jira ni nayi wanka.." A'isha ta jinjina kai, tana jira har Amal ta kammala komai sannan suka tafi..dake A'isha da motarta a cikin motar suka wuce... Bayan sun shiga, suka cika cart da kaya iri-iri. Amal tana taimaka mata ɗaukar kayan da suka burgeta ba tare da ta san a ita ake wa shopping ba. Da suka iso wajen biyan kuɗi, sai Cashier ya sanar dasu cewa. “Madam, ba sai kin biya ba. An riga an biya dukkan kuɗin kayan nan.”.. Amal ta kalli A’isha cikin mamaki ta ce “Waye ya biya kuma?” A'isha ne ta sanar mata cewa "Duk kayayyakin nan nata ne.." Amal ta ce "nawa kuma taya?..." A'isha tana murmushi ta ce. "Yaya Maleekh ne yace na kawo ki shopping, shi ya biya kuɗin...." A’isha ta fara fito waje da kayayyakin, Amal tana tsaye tayi tsumuuu, itama daga baya ta biyo A'isha, suka fito... Cikin mamaki Amal ta hango Maleekh tsaye a wajen motarsa a bakin titi, yana murmushi kamar wanda ya gama nasara, Amal ta tsaya cak, zuciyarta tana bugawa ta ce “Meyasa ku ka yi haka ba tare da kun sanar mun ba?” A'isha ta ce "unsuspecting ne ai..." A fusace Amal ta ɗauki kayayyakin da aka siya, ta nufi inda yake. Tana isa ta watsa kayayyakin a gabansa, wasu suka bugu akan fuskar sa. Cikin fushi, da murya mai ƙarfi take cewa “Ka fita daga rayuwata, Maleekh! Ban sonka, bana kuma son abinda ya fito daga hannunka!” Wurin ya cika da mutane suna kallo. Wasu suna mamaki, wasu suna kwaɗaituwa da magana... A’isha ta ɗaure fuska, zuciyarta na tafarfasa ta ce “Amal! Ki daina wannan rashin mutuncin a bainar jama’a!” Amal ta ce "To dole ne? dole ne sai yayi rayuwa dani?..." Ta kalli Maleekh tana nuna masa yatsa ta ce "Kana ji ba, ka saurare ni, kana tunanin kaci nasara ne akan soyayyata? fitowa television da kayi ba shine yake nuna cewa na amince da kai ba, saboda haka join yourself..." Maleekh ne ya kamo hannunta da ƙarfi yana faɗin. "Wallahi sai kin Aure ni dole..." Yana ƙoƙarin sanya mata wani zoben gold a yatsanta, wanda haka na nufin ƙarfafa soyayya... Kokuwar janye hannunta take tana faɗin "Ka sakar mun hannu nace, Maleekh..." Da ƙarfi ta janye hannunta daga riƙon da yayi mata, cikin ɗaga murya ta ce "I said join yourself..." ta tafka masa wani irin gigitaccen mari.......Har sai da ya karkatar da wuyansa tare da kama wurin marin da hannu, yana mata kallon mamaki...." Amal idonta a cikin nasa tana kuka domin bata so ta mare shi ba.. Kowa ya firgita da ganin wannan al'ajabin... A'isha dake gefe sakin baki tayi tana kallon ikon Allah.. Jama'a kuwa sun daɗe suna ɗaukar video... PA ɗin Maleekh ne ya nufi Amal yana zagin ta da cewa “Ke wace irin yarinya ce? wacece ke har zaki ci mutuncin Boss ɗina haka a gaban mutane? Ke ba kya da hankali ne?” Maleekh ne ya juyo da sauri, ya ɗaga hannu ya zabga wa PA mari yana huci cikin fushi ya ce “Kaɗan ya rage in kore ka! Waye kai da zaka ɗaga mata murya? Ka sani kamar yadda nake a matsayin Boss ɗinka, Amal ita ma Madam ɗinka ce. Ka girmama ta!” PA ya sunkuyar da kai yana bashi haƙuri.... Sannan Maleekh ya maido da idonsa kan Amal, cikin fushi ya dam'ko hannunta cikin ɗaga murya ya ce "Ko ki soni, ko kar ki soni wannan ya rage naki, zan tafi dake dole sai kin soni..." Ya fara jan ta zai shigar da ita mota, a lokacin Amal ta fara ihu tana neman taimako.. "Ka sake ni, ka sakar mun hannu nace bana sonka, ka sake ni Maleekh..." A'isha ce ta buɗi baki ta ce "Ina zaka kaita Yaya?..." Wasu matasa ne ƴan daba su biyar suka sha gaban Maleekh suna faɗin "Ina zaka kaita, a gaban mu zaka sace ta? ashe ma bata sonka har da fitowa gaban tv kana zayyana soyayya?..." Maleekh cikin fushi ya ce "su waye ku? ku matsa mun daga kan hanya..." "Matasan suka ce "Baza ka tafi da ita ba..." Maleekh ya ce "Ku dakatar dani idan kun isa..." Ai kuwa Matasan nan suka afko masa, Maleekh ne ya sakar wa Amal hannu tare da tinkarar su, nan take suka fara gwabzawa, matasa su biyar suka rufu masa, shima Maleekh haka yake kai musu naushi, duk wanda ya samu a cikinsu zai kaiwa naushi.... Ganin haka yasa PA ɗinsa shiga masa, shima PA haka yake kai musu duka, mutum biyu suka haɗu wa PA, mutum uku kuma akan Maleekh... A'isha ba abinda take sai ihu tana faɗin "Wayyo Allah zasu kashe mun Ɗan uwa, taimako jama'aaaa...." Amal kuwa gaba ɗaya ta rikice, ba abinda take sai kuka, tana so ta dakatar da mutanen amma ta kasa... Kafin sai ga motar security Maleekh da ta police, a nan aka raba su, a fusace Maleekh ya ciri bindiga daga aljihun ɗaya daga cikin security sa ya kunna kunamar bindigar yana shirin harbe su... Wani ɗan sanda ya riƙe shi yana bashi haƙuri... Ga yanda suka fasa masa lips ɗin baki, duk da suma matasan sun ji jiki, domin ba ƙaramin naushi suka sha a wurin Maleekh ba, duk da su uku ne amma haka suka kasa kayar da Maleekh, haka shima PA ɗinsa ya nuna jarumta sosai domin duka yayi wa sauran biyun da suka yi kansa... Ƴan sandan ne suka kama matasan duk suka sa musu ankwa, za'a kulle su... Maleekh kuwa Security sa ne suka shigar da shi mota suka tafi... Amal da gudu ta tari napep ta koma gida a tsorace, bata ma lura da zoben da ya sa mata ba, sai sheƙi yake a hannunta.... A'isha kuwa itama motarta ta shiga a tsorace tabi bayan motar su Maleekh... 🌹 Page 15–16 ends here 🌹 asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 17 to 18 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Maleekh yana zaune a motar zuciyarsa na tafasa a yayin da PA ɗin sa yake driving... Ga wasu motocin security a tafe a bayansu.. Maleekh ya lumshe idanu yana faɗi a hankali cikin rawar murya ga lips a fashe sai ɗigar da jini yake.. “Duk abinda tayi min zan rama. Amma sai soyayyata ta mallake ta gaba ɗaya kafin ta san irin azabar da zata fuskanta.” PA ya jinjina kai yana ƙara zuga shi da cewa “Boss, yarinyar nan ba ƙaramin raina ka tayi ba. Lokacin fansa ne kawai ya rage.” Maleekh ya yi murmushi mai cike da takaici da mugunta, yana shirin sabuwar dabarar da zai ɗauka a kan Amal… Tin a napep Amal ta lura da zoben da Amal ya sanya mata da ƙarfi, ɗago hannunta tayi tana kallon zoben sai sheƙi yake, ga wasu zafafan hawaye dake zubo mata... Amal na dawowa gida, zuciyarta ta rikice tamkar an jefa ta cikin ramin da babu mafita. Tana shiga ɗakinta ta rufe da karfi tare da sakale sakata, ta sulale a ƙasa tana kukan da ya huda zuciya. Hannayenta na rufe akan fuska, zuciyarta na bugawa da sauri, tana jin nadamar yadda ta wulakanta Maleekh a gaban duniya. Cikin kuka take faɗin "Me yasa na bari masifar zuciyata ta rinjaye ni? Me yasa na zubar da mutuncinsa haka?” Ta tambayi kanta cikin kuka... Amma duk da haka, wani ɓangare na zuciyarta ya ƙi yarda da cewa kuskure ne, sai cewa tayi a fili “Zan cigaba da gwada shi har sai na tabbatar da gaskiyar soyayyarsa. Idan ya fita daga rayuwata saboda wannan, to shi ba nawa bane.”.... A gefe guda kuwa, Maleekh ya koma cikin duniyar gidansa cikin bacin rai. Zuciyarsa ta ƙone da wuta.. Bayan ya shiga falonsa, ya zauna a kujerarsar falon, sai sauƙe numfashi yake yi tamkar wanda aka ɗora masa wani nauyi... Ya jan yo shisha gabansa, yana zuƙar hayaƙi tamkar yana neman mafita daga rantaƙiyar da ke ci masa zuciya. Idanunshi sun sauya launi, wani yanayi na ɗacin rai yana wanzuwa masa.. A fizge yake faɗin "Amal… wannan wulakanci ba zai tafi a banza ba. sai na nuna miki kuskuren da kika fara tin farko har zuwa yanzu...” Yana raba hayaƙi, fuskarsa kamar wanda aka watsa wa tafashashshen ruwan zafi... 《☆☆☆》 Bayan kwana biyu A Abuja, gidan su Maleekh. Farha tana kwance a kan tsararren gadonta, ta kifa kanta sai sharar kuka take, zuciyarta na ƙuna da kishin da ya kasa boyuwa... Sai ga ƙofar ɗakin ya buɗe a hankali, Hajiyar gidan wanda duk gidan ke ƙiran ta da Ammy, mahaifiyar Maleekh kenam, ta shigo cikin nutsuwa. Tana sanye da kayan alfarma, kyakkyawar mata mai cike da ƙima da isa.. Ta zauna a bakin gadon, ta dafa kafaɗar Farha cikin lallashi... “Meye amfanin kukan nan, Farha?” Ammy ta tambaya cikin murya mai taushi mai cike da iko.. Farha ta ɗago da idanunta da suka yi ja, kuka ya sa sun kumbura, ta ce cikin karyayyen murya. “Haba Ammy! Baki ga abin kunyar da Maleekh ya jawo mana ba? Yana fitowa a television yana yayata soyayyar wata matsiyaciyar yarinya, ƴar talaka marar gata! Wannan ba mutuncinsa bane…” Ta fashe da wani sabon kuka tana girgiza kai, sannan ta cigaba da magana cikin zafin rai. “Ammy, ya zanyi da soyayyarsa? Har yanzu yaƙi kallona a matsayin masoyiyarsa, yaƙi saurarona, kuma nasan saboda waccan yarinyar yaƙi dawowa daga Kaduna. Wallahi idan baki aura mun Maleekh ba, mutuwa zanyi!” Ammy ta sauƙe dogon numfashi, tana kallon Farha da idanun ta cike da wani irin haske na muguwar natsuwa. Ta ɗan yi shiru, sannan ta furta “Ki kwantar da hankalinki, Farha. Bazan taɓa barin Maleekh ya auri wata matsiyaciyar yarinya ba. Na miki alƙawarin Maleekh naki ne, kuma zan aura miki shi.” Farha ta share hawayenta da sauri, tana kallon Ammy da wani irin hope ta ce. “Ammy… amma ba ya sona fa. Ko kallona baya yi…” Ammy ta ɗaga gira, ta murmusa da irin murmushin mace mai cike da shirin da babu wanda ya iya fassara shi, sannan ta ce “Dole zai soki, Farha. Zan sa ya dawo daga can Kaduna, kuma da kansa zaki ga yadda zai fuskanci soyayyarki. Ba zai ƙi umarnina ba.” Farha ta rungume Ammy da sauri, hawaye suna sake zubo mata amma wannan karon hawaye ne na begen cikar burinta.... Farha yarinyar ƙanwar Ammy ce, iyayenta da ita suna zaune a ƙasar London, ita farha ta dawo Nigeria ne saboda Maleekh, tana zaune a gidansu a gaban Ammy.. Suna zaune Ammy da Farha sai ga Arfat ƙanwar Maleekh ta shigo da gudu tana kwallawa Ammy ƙira “Ammy! Ammy!!” Ammy ta zabura ta kalleta, zuciyarta na bugawa cikin firgici ta ce “Meya faruwa ne haka, Arfat? Wannan irin ƙiran fa sai ki tsoratar da mutum!” Arfat ta fitar da numfashi kamar wanda tayi gudun kilo mita hamsin, tana zufa tana huci ta ce “Ammy, zo kiga television… Yaya Maleekh ake nunawa! Budurwa ta mare shi a bainar jama’a, ta wulakanta shi sannan tasa yayi faɗa da wasu matasa. Kamar ya ji ciwo!” Da gudu Ammy ta miƙe, Farha ma ta miƙe duk suka fice zuwa babban falo inda television ke kunne... A can kuwa rahoton yana ci gaba. An nuna video Amal ta ɗaga hannunta, ta zabga mari a fuskar Maleekh a gaban jama’a, da irin wulakancin da ta masa.. Gari ya ɗauki zafi. Kaduna ta kaure da maganganu. Duk inda aka shiga sai a ji ana maganar “Wai Amal ta mari ɗan gidan minister Alhaji Abdul-majeed a bainar jama’a!” Anata posting a social media, hotunan sun bazu fiye da yanda ake tsammani.. Maleekh, a ɗaki ya jingina da kujerarsa, idanunsa sun kaɗa sunyi jaa, yana kallon television. Ganin yadda Amal ta mare shi duba da ƙarancin asalinta, hakan ya sa ya rafka uban harara, zuciyarsa na tafarfasa kamar wuta. Ya riƙe sumar kansa yana cukurkudawa, kamar zai haukace da kunyar da aka jawo masa. Amal kuwa a ɗakinta a Kaduna, ta shagaltu da damuwa. Kuka ne kawai ke tserewa daga idanunta, saboda ta san duniya ta fara kallonta da ido ɗaya, suna tallata wannan abin kunya da ita da Maleekh. A Abuja, Alhaji Abdulmajeed mahaifin Maleekh, yana zaune a ofis ɗinsa, an kawo masa rahoton. Yana ganin hoton yadda mace ta sa hannu ta mari ɗansa a bainar jama’a, ransa ya yi matuƙar ɓaci... Ammy ma ta ji tamkar ta haɗiye ranta saboda takaici. Farha kuwa ta daure ta furta cikin ƙiyayya. “Ammy, yanzu da ni nayi masa haka, kin san ba zan kwana da ƙafafuna ba. Da ya kakkarya ni tun a wurin! Amma ga matsiyaciyar yarinya ta mareshi a bainar jama’a, kuma sannan ya sharar da ita. Har da faɗa saboda ita!” Ammy tana cikin tsananin fushi, hannunta na rawa saboda takaici. Ta kasa furta komai... A ɓangaren Mahaifinsa dake office. A fusace ya ɗauki wayarsa, ya ƙira lambar Maleekh. A ɗayan ɓangaren, Maleekh ya ɗauki ƙiran da muryar da ta sha bamban, kamar wanda ya yi shaye-shaye. Ya ce “Hello, Abba…” Abba bai tsaya gaisawa ba. Da murya mai nauyi ya ce. “Inaso ka dawo Abuja yau ɗinnan. Kada ka ƙara kwana a Kaduna.” Maleekh ya lumshe idanu, ya sauƙe ajiyar zuciya sannan ya ce “Na ji, Abba…” Ya amsa a taƙaice, zuciyarsa na nuni da cewa daga wannan rana lamarin zai ɗauki sabon salo.... Maleekh yana jingine da kujera, hannunsa na riƙe da wayar da ya gama magana da mahaifinsa. Zuciyarsa ta cika da tsananin fushi, amma fuskar sa ta nuna sanyin jiki.. Ya ɗaga shisharsa ya shaƙi iska mai ƙamshi, ya sauƙe ta cikin takaici yana faɗin “Kaduna… ban shirya barin cikinki ba saboda ban gama aiki akan Amal ba. Amma yanzu Abba ya ƙira ni, dole sai na koma Abuja.” Ya juya yana kallon PA ɗinsa, wanda ya tsaya a gefe yana huci shima. Maleekh ya ce “Ka shirya kayana. Ba zan ƙara kwana a nan ba. Abuja na jira.” PA ɗinsa ya yi shiru na ɗan lokaci, sai ya ce cikin ɗan ɗaga murya “Boss, wannan yarinyar ta raina mu sosai. Wallahi ban taɓa ganin mace ta yi maka irin wannan ba… me za ka yi game da ita?” Maleekh ya ɗan yi murmushi, murmushin da ya ƙunshi mugunta da takaici ya ce “Ba yanzu ba. Amma zan nuna wa Amal bana yafiya. Da zarar na koma Abuja, za ku ga yanda zan karkatar da komai zuwa hannuna.” Ya miƙe tsaye, ya nufi bedroom ɗinsa, PA ne yabi bayansa, yana shiga ya nufi wardrobe yana ɗaukar kaya masu tsada yana ajiye wa PA don shirya masa a jakunkuna. Zuciyarsa ta yi nauyi sosai. Amal ta mare shi a bainar jama’a, abin da bai taɓa faruwa da shi ba tun da aka haife shi. Yanzu kuwa duniya ta gani, duniya ta yi sharhi. Kuma mahaifinsa ya ƙira shi da umarni mai zafi... Ya tsaya a gaban madubi, ya kalli fuskar sa, saitin wurin da ta mare shi. Hannunsa ya ɗago a hankali ya taɓa fuskar, zuciyarsa ta cika da tsanar Amal... “Amal…” ya furta cikin sirri. “Kin fara yaƙi, amma ni zan kawo ƙarshensa. Abuja ce matakin farko.” Sai ya juya ya saka agogon hannunsa mai tsada, ya ɗauki wayarsa yana faɗin “PA, ƙira min jirgin Abuja. Na fi son private jet ɗina ya jira ni kafin karfe biyu na rana.” “Yes, Boss.” PA ɗin ya ce, yana bin shi da idanu, zuciyarsa na mamakin irin natsuwar da Boss ɗinsa yake nuna wa duk da irin wutar da yake ƙonewa a cikin zuciyarsa.. ♡ Amal ta zuba wa wayarta ido, tana dubanta, ta kasa natsuwa. Kwana biyu kenan bata ji ƙiran Maleekh ba, bata kuma ga saƙonsa ba. Zuciyarta ta ƙara rikicewa, zuciya na ta bugawa kamar zata fito. Ta jawo wayarta ta sake dubawa. Sai lambar A’isha ta faɗo mata a rai. Cikin tsoro da shakku ta danna ƙira. A can ɓangaren A’isha kuwa, tana zaune taji wayar tana ringing. Takaici ya cika mata zuciya a fili take faɗin “Amal ce? Wacce ta mari Yayana a gaban jama’a? Haka nan kuma duniya ke yi masa ba’a saboda ita?” Ta jinjina kai cikin ɓacin rai, Ta ɗauki lokaci kafin ta ɗaga. A ƙarshe ta ɗauka tare da faɗin. “Assalamu alaikum.” Amal ta runtse idanu, muryarta na rawa ta ce “Dan Allah A’isha kiyi haƙuri da abinda ya faru. Nasan bakiji daɗi ba…” A’isha ta amsa cikin ƙunshi, tana ɗan sauƙe ajiyar zuciya ta ce “Ba komai. Amma yanzu, meya faru ne?” Amal ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta furta cikin rauni. “Maleekh ne… ban ji labarinsa ba, na damu sosai. Shin yana lafiya?” A’isha ta yi dariya sannan ta kaɗa kai kamar tana magana da kanta...Ta ce “Yanzu kuma Yaya Maleekh kike tambaya? Bayan wulakanta shi da kika yi a bainar jama’a? Haba Amal, kin bani mamaki. Kin san irin takaicin da iyayensa zasu ji akan wannan al'amarin? Taya kike tunanin zasu bar shi ya cigaba da zama a Kaduna bayan sun ga abinda kika masa? Ina mai miki fatan kada Allah yasa mahaifiyarsa ta biyo ki har nan kaduna domin tafi wuta ƙuna, saboda bala'inta yasa mahaifin mu ya raba musu gari da mahaifiyata, ita tana can Abuja da iyalanta, mahaifiyata kuma tana nan kaduna da mu, saboda bala'i kinga ko bikina mahaifiyarsa da ƙannensa basu zo ba sai iya Yaya Maleekh ne kawai ya ziyarci bikina, kin yi kuskure Amal .." Zuciyar Amal ce ta karye, hawaye suka fara zubo mata. Tayi ƙasa da murya, tana jin kamar zuciyarta zata fashe ta ce “Maleekh ya koma Abuja kenan…?” A’isha ta lumshe idanu, ta amsa da taƙaice. “Eh.” Ba tare da ƙarin magana ba, ta kashe wayar. Amal ta zube akan gado, kuka mai tsananin raɗaɗi ya kwace mata. Zuciyarta na tsananta da tambayoyi. “Shin hakan me yake nufi kenan? Shin shikenan ya gudu daga gare ni saboda abin da na yi masa? Ko kuwa iyayensa ne suke ƙoƙarin rabani dashi?” Inna ce ta shigo ɗakin, ganin Amal tana kuka yasa tayi ƙwafa ta ce "kaɗan kika gani, indai mutum wulakanci ya iya wata ran zai cusa barkono ne a tsuriyarsa ba tare da saninsa ba..." Inna tayi tsaki bata ma son kallonta. Tun bayan abin da ya faru ta daina kula ta, domin a idanunta Amal ce ta jawo musu ƙasƙanci da tozarci... ABUJA CITY Maleekh ne yake zaune a bakin katafaren gadonsa dake cikin tsararren bedroom ɗin sa... Yana sanye da short 3quarter da rigarsa mai gajeren hannu na shan iska.. shi kaɗai yasan irin tunanin da yake yi.. Bai san an buɗe ƙofar ɗakin bama tsabar yayi nisa a tunanin da yake. Sai ji yayi an rufe ƙofar da ƙarfi, bugun ƙofar da akayi ne yasa ya dawo daga tunanin da ya zurfafa, sleepy eyes ɗinsa ya sauƙe akan mahaifiyarsa, wacce kallo ɗaya zaka mata kasan tana cikin fushi... A tsawa ce ta fara faɗin. "Maleekh! Wannan abinda kayi a Kaduna ai babban abin kunya ne. Haba! kai fa mutum ne babba, ɗan manya, ya za ka bari wata ‘yar talaka ta mare ka a bainar jama’a? A fuska fa? Ka sani kai ba kamar kowa bane.".. Maleekh yana ɗaure da fuska, ya ce "Ammy, ba wai ban san darajata bane. Amma wallahi soyayya ce ta ruɗani. Ban taɓa ɗaukan Amal a matsayin ‘yar talaka ba. A idanuna… ita ce komai." Ammy cikin jin haushi ta ce "Komai? Komai har da wulakantaka a gaban mutane? Ka ji abin da kafafen yaɗa labarai suke ta yayatawa kuwa? Wannan ai abin kunya ne ga iyayenka. Ni fa ban yarda da wannan Amal ba, ba za ta taɓa zama matarka ba! Ga Farha wacce take masifar son ka amma ka ƙi ta gida kana ƙoƙarin jan yo mana magana..." Maleekh yana huci, ya ɗan miƙe yana fuskantar Ammy ya ce "Ammy, me yasa kullum sai Amal kike gani a matsayin barazana? Ta fi kowa gaskiya da amana! Ni dai ba zan iya auran Farha ba, ko da kin tilasta ni." Ammy cikin ɗaga murya ta ce " Farha ai ba irin waccan Amal ɗin bace matsiyaciya. Farha ‘Yar manya ce, ‘yar dattawa, ta girma kuma da tarbiya, za ta kare mutuncinka, ba wai ta zubar maka ba, Kuma duba iyayenta, za ka samu haɗin kai da amfanin ahali, Kai fa dole ne ka auri Farha!".. Maleekh yana kallonta cikin rashin fahimtar abinda take nufi da dole sai ya Auri Farha, haka yake yatsina fuska ya ce "Wallahi ba zan aure ta ba! Ni bana sonta, bana ma jin ko daɗin ganin ta. In har Ammy aure kike so, sai dai ki manta da ni. Soyayyata ta tsaya ne akan Amal, kuma ba zan canza ba!" Daga nan Maleekh ya fice a ɗakin, da sauri yake sauƙa daga upstairs zuwa ƙasin falo, yana sauƙa ya zauna a kujerar falon yana fuskantar plasman... Farha wacce fitowar sa kenam, ganin Maleekh yasa ta huce wurin ƙaton frig ta ɗauko juice da glass cup guda ɗaya, ta nufi cikin tsakiyar falon yanda yake zaune... Farha ta shigo da murmushi, ta kawo masa juice tana faɗin "Sannu Yaya Maleekh, na zo ne saboda Ammy ta ce kana cikin damuwa. Ka sha ruwa, ka huta." Maleekh ya karɓi glass ɗin, ya ajiye shi ba tare da ya sha ba ya ce "Farha, kin dai san bana buƙatar wannan kulawar da kike yi. Me ya sa baza kiyi zuciya ki daina zuwa gidan nan ba? ya kamata ki koma Ƙasar da kika fito, zai fi kyau ki zauna a gaban iyayenki, Ni bana sonki, bana son wannan abokantaka ma."... Farha ranta ne ya ɓaci, amma tana ƙoƙarin yin murmushi domin danne ɓacin ran, ta ce "Ban yi zaton zaka furta haka ba a fili, Yaya Maleekh. Inda kara ai nan gidan ma gidan iyayena ne, tinda Ammy Yayar mahaifiyata ce, maganar soyayya kuma na ɗauka lokaci ne kawai zaka buƙata domin yin tunani akan soyayyata...." Maleekh yana kallonta cikin tsana ya ce "Lokaci? Ko shekara ɗari ne ba zan canza ra’ayina ba. Ni bana sonki Farha. Don Allah ki bar cikin rayuwata. Kar ki takura ni, kar ki takura kanki." Ammy wacce sauƙowar ta daga upstairs kenam ta ce "Maleekh! Yanzu duniya tana magana ne akan wannan Amal ɗin. Me yasa kake ƙara damuwa a kanta? Ka manta da waccan yarinyar, ka zaɓi Farha ka huta.".. Maleekh fuska a ɗaure, yana danna wayarsa ya ce "Ammy, sau nawa kike so na faɗa miki ne? Ba ni da wata mace sai Amal. Ko duk duniya ta tsaneta, ni ba zan ƙi ta ba. Ba zan iya rabuwa da ita ba." Farha tana kallonsa cikin hawaye ta ce "Ni fa ban taɓa jin ciwo irin haka ba, Yaya Maleekh. Amma me Amal ta baka da har ka manta da mutuncin kanka?" Maleekh yana murmushi ya ce "Amal ta bani abin da ba ku fahimta ba, soyayya ta gaskiya. Kuma duk abinda zaku ce, wallahi bazan taɓa sakinta." Ya miƙe cikin fushi ya fita daga falon, yana tafe cikin izza, ya bar su cikin bacin rai, kai tsaye waje yayi ya nufi wurin parking motoci, kafin ya isa ya matsa key ɗin motar da zai shiga nan take ƙofar motar ta buɗe, shiga yayi a ɗari ya bi hanyar da zai kai shi get. Mai gadi ne yayi saurin buɗe masa ya bar gidan gaba ɗaya, cikin ƙananun kaya na shan iska... A Kaduna... Bayan wata guda.. Amal tana juya zuciyarta, tana kai-komo tsakanin tsoro da ƙauna. Duk lokacin da ta tuna da fushin Maleekh da kuma shiru da ya yi mata, sai zuciyarta ta cika da kunci. A ƙarshe ta yanke hukuncin cewa ba zata iya ci gaba da hukunta kanta ba... Ta sanar wa Inna cewa zata je Abuja... Inna a firgice ta dafa kirjinta tana faɗin: "Abuja dai? Uban me zakiyi acan, garin manyan mutane zaki dosa?... Amal kin san garin bana wasa bane..." Amal ta ɗago ido cikin nutsuwa ta ce: "Inna, babu abinda zai faru. Ni addu’arki kawai nake nema. Ba don komai ba, sai don zuciyata ta huta daga wannan azabar shirun." Inna ta juya kai, hawaye suna cika a idonta. Tana kallon jikar tata mai ƙaramin hali da girman zuciya. Cikin taushin murya ta ce: "To Allah ya kare mun ke Amatullah. Ki sani ba ki da wani gata sai addu’ata. Ki kula sosai… Amma nasan Maleekh ɗin zaiji daɗin ganin ki." Amal ta jingina kanta a kafaɗar Inna, tana jin wani irin ƙarfin hali ya mamaye ta... Da Asuba bayan ta idar da sallah, already ta kammala shiryawar ta... Ta shirya tafiya. Ƴan kuɗaɗen da ta daɗe tana ajiye su, ta raba gida biyu. Rabi ta ba Inna, tana faɗin: "Inna, wannan ki riƙe, ko kayan abinci ya ƙare, ko wata buƙata ta taso, za ki samu. Ba daɗewa zan yi ba, iya kwana ɗaya ne kawai." Inna ta karɓa cikin jinƙai, zuciyarta cike da addu’a. Ƙarshen rabin kuɗin kuma Amal ta tanada shi domin kuɗin mota da ƙananan buƙatu. Ta ɗauki jaka ta rataya a kafaɗarta, ta zuba ido tana kallon Inna da murmushin dole. Ta ce "Inna, ni zan tafi..." Inna ta ɗaga hannu tana maimaita: "Allah ya tsare ki Amatullah, Allah ya miki jagora." A haka Amal ta nufi tashar mota, zuciyarta cike da tsoro da bege, kamar mace da ke barin ƙauye zuwa wani sabon duniyar da bata san menene ke jira a ciki ba. A tashar mota mutane suna ta cunkoso, kowa da kayansa, kowa da nufinsa. Amal ta tsaya gefe da jaka ɗaya a hannunta tana jiran direban ya cika mota. Wani irin sanyi na ratsa jikinta... Direba ne ya fara ƙwala ƙira: "Abuja! Abuja! Azo a tafi! Ku shigo mu tafi!" sai ta matso a hankali ta shiga, ta zauna a gefen taga. Motar ta tashi, Amal ta jingina kanta da gilashin taga, idonta na kallon gari da nisan da yake raguwa a bayanta. A zuciyarta kuwa, tunani na kai komo kamar ruwan sama. "Shin Maleekh zai karɓe ni? Shin zai ji daɗin gani na? Ko kuwa fushinsa zai ƙara muni?... Amma duk da haka ba zan iya jure wannan rabuwa ba." Tana rufe ido sai ta ji muryar Inna na sake dawo mata: "Allah ya tsare ki Amatullah…" Wannan kalma ta Inna ta ba ta ƙarfin zuciya, sai ta ɗan yi murmushi da hawaye a idonta. Hanyar Kaduna zuwa Abuja ta yi tsawo a gare ta fiye da yadda ta taɓa yi. A duk lokacin da direban ya taka birki ko motar ta yi tsalle, zuciyarta sai ta buga da ƙarfi, tana addu’ar Allah ya kai ta lafiya. Ƴan mata biyu a motar suna hira da dariya a kusa da ita, amma ita gaba ɗaya zuciyarta nesa take can wurin Maleekh. Tana jin kamar kowane irin abu ne zai iya faruwa da ita muddin ta same shi. Lokacin da suka fara shiga cikin birnin Abuja, hasken manyan fitilun tituna da ginin gine-ginen birnin suka bayyana a gaban Amal. Ta zaro ido tana kallon birnin, cike da bege.. domin zuwan ta Abuja na farko bata tsaya kalle-kalle ba, domin tin lokacin da Rikky Blaze ya gayyato ta zuwa podcast ɗin su, nan ma daga jirgi ne zuwa airport, anan kuma ta shiga mota sai hotel, daga hotel sai podcast, har ta koma bata wani zagaya Abuja ba... A hankali ta furta. "Ashe haka Abuja take... Duniyar manyan mutane, duniyar da zan yi gwagwarmaya domin zuciyata ta huta." Ta dafe kirjinta, tana jin bugun zuciyarta na ƙaruwa. "Maleekh... na iso." Ta furta a hankali... Tana sauƙa daga mota anan Amal ta fara tsorata, domin bata san ina zata je ba, shin idan ta hau napep ina za'a kaita? haka take zuru-zuru da ido... Tambaya ta fara yi tana faɗin. "Dan Allah aina zan samu Maleekh?..." Gaba ɗaya kwakwalwarta ya toshe da inkiyar sunan Maleekh 'Maleekh Cashbank...' sannan ya toshe da sanin shi ɗin ɗan gidan Minister ne, but Minister meye? tinda ba iya Minister guda ɗaya bane... Amma inda tayi kwatance da 'Maleekh ɗan gidan Minister Alhaji Abdul-majeed' zai fi sauƙi... Amma gaba ɗaya sunan mahaifinsa ya kwanta mata a rai, ta rasa yanda zata yi.. Duk wanda tace "Dan Allah ina neman Maleekh..." Sai dai a bata amsar da ba'a san shi ba... Kuma a yankin da take a Abujan ba nan ne yanki masu kuɗin ba, domin yankin unguwar gomnoni da shugaban ƙasa da ministoci da chairmomi da sauran su babu wanda yake shiga yankin sai da izini... Har dare ya fara yi Amal bata samu mafita ba, ga number Maleekh baya shiga kwata-kwata.. Dare yayi sosai. Tana zaune a bakin wani babban supermarket, hannunta na riƙe da ƙaramin jakarta. Ta gaji sosai ga yunwa na neman cinye ta gaba ɗaya, sai dai zuciyarta ta ƙi ba ta damar yin barci. Duk inda ta juyo, babu Maleekh, babu labarinsa. Wayarsa kuwa koda ta ƙira sau nawa, sai dai ta ji muryar machine ɗin waya na cewa “The number you are trying to call is switched off.” Kifa kanta tayi a kan gwiwowinta tana huci da ƙarfin gajiya. Har gari ya waye, motoci suka fara cunkoso, mutane suka fara kai-komo, amma ita nan take zaune, idonta ya kumbura saboda rashin barci ga kukan da take sha... Da ta ga babu wata mafita, sai ta yanke shawarar ta ƙira A’isha. Lalumo lambar A'isha tayi bugu ɗaya kacal A’isha ta ɗauka, kamar daman wayar a hannunta yake.. Amal ta yi sallama cikin raunanniyar murya.. A’isha ta amsa, ta ce: "Amal? Me meya faru kika ƙira da sanyin safiyar nan?" Amal ta gyara zama sannan ta ce cikin rawar murya "Ni yanzu haka ina Abuja A’isha... na zo neman Maleekh tun jiya, amma har yanzu ban same shi ba. Dan Allah ki taimaka ki turo min lambar da yake amfani da ita yanzu." A’isha ta zaro ido kamar za ta fasa wayar, ta ce cikin mamaki: "Abuja kuma Amal? So kike ki ɓatar da kanki? Ni fa wallahi lambar Yaya Maleekh yanzu ba ta shiga kwata-kwata...." Amal ta fashe da kuka, ta ce: "Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un..." A’isha ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta ce: "Sai dai wata hanya ɗaya zan iya turo miki lambar ɗaya daga cikin ƙannensa, zasu iya kwatanta miki gidansu, ki neme shi ki ji ainihin inda yake..." Amal ta girgiza kamar wacce take gabanta, ta ce da sauri: "Gidansu kuma? A’a... ba zan iya zuwa gidansu haka ba." A’isha ta ɗan yi dariya mai ɗaci, sannan ta ce: "To shikenan, idan haka ne ki nufi Kamfaninsa, CashTalk. Ai sananne ne a nan Abuja. Idan kika je, sai ki ce a kai ki can. Wannan shi ne mafi sauƙi." Sai yanzu Amal ta tuna. Ta share hawayenta, ta ce da ƙarfin zuciya: "Eh, I remember... CashTalk. Zan tafi can." Da wannan suka kashe wayar, zuciyar Amal na dukan uku-uku... Bakin hanya ta nufa da ƴar jakarta a hannu, ta tari mai napep, tana cewa 'akai ta kamfanin CashTalk, mai napep ya amsa mata, amma sai wurin yana da nisa sosai, iya kuɗin jikinta kenam ta bashi gaba ɗaya, nan ma saida ta bashi haƙuri akan ya taimaka mata domin kuɗin basu kai ba.... Suna zuwa daga nesa-nesa ta fara ganin tsayin kamfanin, da irin tsaruwar kamfanin, ko wani ƙofa glass ne amma baka iya ganin wanda yake ciki, amma na cikin zai iya ganin abinda ke faruwa a waje... Mai Napep ne ya ajiye ta a wurin... Amal tana kallon bakin get ta ga security sun fi goma suna tsatstsaye dake mashigar get d'in biyu ne, akwai bangaren dama da hagun... Abun da ta lura da tsarin shine.. Idan zaka shiga cikin kamfanin get ɗin shiga da ban yake, kuma akwai security masu duba mai shiga... Sanna ɓangaren ɗayan get kuma idan za'a fito daga cikin kamfanin, nan ma kawai security masu duba waɗanda zasu fita... A tsorace ce Amal ta nufi wurin, gaba ɗaya tayi wujiga-wujiga da ita, tana zuwa suka tare ta... Cikin rawar murya da yunwa yaci ƙarfinta take faɗin "Maleekh nake nema?..." Ɗaga daga cikin security cikin tsawa ya ce "Wani Maleekh?..." Amal kamar zata yi kuka ta ce "Maleekh dai..." Ɗaya daga cikin su ne ya ce "Wannan fa! Boss take magana akai..." Bata ankara ba taji security na gabanta ya ɗauke ta da mari tare da zazzaro mata ido yana cewa. "Baki da hankali ne, cikin rashin respect zaki ambaci sunan sa kai tsaye? to bari kiji shine mai wannan kamfani gaba ɗaya...." Security yayi magana yana nuna girman kamfanin da hannunsa, sannan ya cigaba da cewa "Duk mu ɗin nan da kike gani shi yake mulkan mu, a ƙarƙashin sa muke..." Wani daga cikin security ne ya ce "Haba dallah, har sai ka tsaya kana ɓata yawun bakin ka wurin mata explain... ta je bamu san shi ba..." Amal tana kuka tana riƙe da fuskarta da ta sha mari ta ce "Dan Allah ku taimaka wallahi saboda Maleekh nazo garin nan..." Security cikin tsawa ya ce "In baki gyara wannan sunan ba sai mun karairaya ki a wurin nan..." Cikin kuka ta ce "To Yalla6ai Maleekh..." Wani irin ran'kwashi security gabanta yayi mata a tsakiyar kanta yana faɗin "To dole sai kin furta Maleekh ɗin ne a gaba?...." Amal 6are baki tayi tana kuka hannunta a tsakiyar kai tanashafawa ta ce "Ya Y YA Yalla6aiiiiiiii...." Security ya ce "To bai zo ba, sai ki jira zuwa jumawa, kije can ki zauna ki jira shi..." Amal ta juya tana kuka hannu a tsakiyar kai yana mulmula wurin rankwashin... hannu ɗaya kuma na riƙe da jaka... Amal ta zauna a ƙarƙashin inuwa a wajen nesa da get sosai, jikinta ya yi sanyi saboda yunwa da gajiya, ta zauna a gefe tana kallon yadda ma’aikata ke shige da ficen kamfanin CashTalk... Ta juma sosai, tin safe har yanzu misalin ƙarfe 12 na rana. Tana zaune kawai sai taga wata babbar mota mai haske white color, ta shawo kwana da gudu. Motar ta tsaya a gaban gate, sai ga security suka ruga da gudu, suna buɗe masa get cikin ladabi da girmamawa. Motar ta shige cikin harabar kamfanin, aka rufe gate. Amal ta runtse idanu da sauri, zuciyarta na bugu da ƙarfi: “Shine kenan... Maleekh ɗin da nake nema, Alhamdulillah.” Cikin ƙasaita da izza ya fito daga motar, farin suit ne a jikinsa da gilashi akan dara-daran idanunsa. A mashigar kamfanin ma wasu security ne, yana shiga kai tsaye ya nufi ginin babban office ɗinsa da ke saman bene, ko kallon gefe baya yi, sai kamshin turarensa da ya cika sararin wajen. Duk ma'aikata sai gaishe shi suke, da haka ya nufi can upstairs... Amal ta miƙe a zabure, zuciyarta kamar za ta fito ta hancinta. Ta nufi security da gudu ta ce "Dan Allah naga ya zo, inason ganinsa... ku sanar masa ina nan." Security ɗin suka kalle ta da mamaki, ɗayan ya ce: "Ashe baki tafi ba har yanzu? Mun manta ma kina nan." Sai suka kalli juna, daga bisani ɗaya ya ɗaga wayarsa ya ƙira office ɗin sama... A cikin ofis kuwa, Maleekh yana zaune a kujerarsa mai juyawa, yana duba wasu takardu. Telephone kan table ta fara ringing, ya yi shiru bai ɗauka ba har sai da ta jima tana ruri. Daga ƙarshe ya ɗauka a gajiye... Muryar da ke can ta ce: "Sir, akwai ba'kuwa tana son ganinka a ƙasa." Maleekh ya ɗan yi shiru, bai ma tambaya ko wacece ba, sai kawai ya ce da gajeriyar murya: "Let her in." Bayan ya sauƙe wayar, sai ga knocking. Ya bada izini, wata ma’aikaciyar kamfanin ta shigo da takardu. Bayan ta gaishe shi, ta fara bayani cikin nutsuwa: "Sir, wannan ne jadawalin ribar da muka samu cikin sati, da kuma matsalolin da muke fuskanta a kasuwa..." Suna cikin wannan tattaunawa sai ga wani knocking a ƙofa. Maleekh ya ɗan tsuke fuska, ya ce: "Come in." Security ne ya shigo, sai kuma Amal ce ta biyo bayansa... A hankali Maleekh ya ɗago kai ya kalli bakin ƙofa, sai kawai eyes ɗinsa suka sauƙa akan kaɗaɗden fuskar Amal, wacce ta sha wahala, fuskar tayi fari ƙal kamar ba jini a jikinta... Ji yayi duniyar kamar ta tsaya cak. Ya zazzaro da idanunsa kamar wanda aka fizge shi daga mafarki... "Amal...?!" ya faɗa a zabure, ya miƙe tsaye da sauri daga kujerarsa. Amal ta tsaya a bakin ƙofa, hawaye na zuba daga idonta, zuciyarta cike da farin cikin ganin sa. Shi kuma zuciyarsa ta buga da ƙarfin gaske tsakanin ƙiyayya da soyayya da mamakin zuwanta Abuja... *NEXT NEXT NEXT....* asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 19 to 20 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Ofishin ya yi shiru, sai ƙarar AC da ƙaramin turirin shishan da ya fara fita daga gefe.. Maleekh ya tsaya cike da mamaki, hannayensa a dafe saman tableɗingabansa, yana kallon Amal kamar zai cinye ta. Amal kuwa ta kasa magana, sai hawayen da ke bin kuncinta. Cikin ƙasa da murya ta ce: "Na zo ne... don na ganka." Maleekh kallon ma'aikaciyarsa yayi sannan yayi mata nuni da ta basu wuri, shi kuwa Security yana kawo ta ya juya... Maleekh ya yi dariya mai cike da ciwo, ya dafe ƙirji yana kallonta. "Kin zo Abuja... bayan abinda kika yi mun? Bayan wulakancin da kika yi a bainar jama’a, kike da ƙarfin halin tsayawa a gabana?" Amal ta ɗan runtse ido, zuciyarta na tsananta bugawa ta ce "Ban zo in yi faɗa ba, Maleekh... ban zo in tuna da baya ba. Na zo ne saboda zuciyata bata iya haƙuri da rashin ka ba." Ya matsa kusa da ita, yana hura numfashi mai ƙona zuciya ya ce "Rashi na? Haba Amal! Ni kike faɗa wa haka? Kin manta da marin da kika mun a bainar jama’a? Kin manta da wulakanci? Kin manta da mutuncin da kika zubar mun?" Amal ta share hawayen fuskarta da sauri, tana mayar da ƙarfin hali ta ce "Eh, na tuna da duk abinda ya faru. Amma ni mace ce... zuciyata baza ta taɓa ƙin ka ba. Ina sonka Maleekh, amma ban yarda da kai ba har yanzu. Ina son in ga gaskiyar zuciyarka." Maleekh ya tsaya cak, ya ɗan ja numfashi da ƙarfi, sannan ya yi murmushi mai sauti, murmushin da ya ɓoye muguwar manufa. "Kin zo Abuja don ki tabbatar da zuciyata? To, Amal... zan nuna miki zuciyata. Amma ki shirya... soyayyata ba zata zo miki a sauƙaƙe ba." Ya juya da sauri ya koma kujerarsa, ya zauna yana juyawa da kujerar, ya buga table da ƙarfi sannan ya ce "Amal, ke ce kika sa na zubda hawayen baƙinciki. Zan sa ki biya duk abinda kika yi... ta hanyar soyayya." Amal ta kalle shi da idanu masu cike da fargaba da soyayya a lokaci guda, zuciyarta na bugawa a hankali ta furta “Shin so ne ko fansa yake nufi?” Maleekh ne ya ɗago yana kallonta, lokaci guda ya saki murmushi sannan ya taso ya zo front ɗinta tare da riƙo hannun ta a hankali, yana kallon fuskarta cikin nuna kalar tausayi ya ce "Akwai kalmar da kika faɗa… Amal. Ina son ki maimaita mun." Amal ta runtse idonta, hawaye na tsiyaya a fuskarta, sannan cikin rauni ta furta: "Ina sonka Maleekh…" A hankali ya saki ajiyar zuciya, ya zaro murmushi wanda ya gauraye da jin daɗi da wata muguwar manufa ya ce "Kin san me Amal? Duk soyayyar da za ki nuna mun… bazata kai wanda nake miki ba. Ni na riga na nutse a cikin sonki fiye da yanda kike zato. Kin zo Abuja saboda ni, and I appreciate you for that." Amal ta share hawayenta da hannunta tana kallon shi cikin tsantsar gaskiya ta ce "Ban iya zaman kadaici ba… nayi gwagwarmaya da kaina, amma zuciyata ta kasa daina tunaninka." Ya matso sosai, ya kamo fuskarta da hannunsa, yana shafar gefen kuncinta da yatsa ya ce "Kin tabbatar min da matsayina a zuciyarki… matsayi wanda babu wanda ya isa ya kwace. Ki kwantar da hankalinki Amal, Maleekh bazai taɓa gujenki ba. Na yi nesa da ganin ki, amma a zuciyata… kina kusa da ni kullum." Amal ta yi ɗan dariya mai sauti, cikin hawaye tana jin kamar an sauƙe mata nauyin da take ɗauka tun tsawon lokaci. Ta yi saurin faɗowa jikinsa, ta jingina kanta a faffadar kirjinsa, tana shakar ƙamshin turarensa da ke ƙara narkar da ita. Shi kuwa ya zagaye ta da hannuwansa, yana bubbuga bayanta a hankali tamkar yana rarrashin yaro. a hankali cikin kunnenta ya ce "Shhh… komai zai yi kyau…" Amal ta runtse idonta, ta yi murmushi cikin hawaye, tana jin ɗumin soyayyarsa ya lull6ube ta. Sai dai a cikin zuciyar Maleekh, wani murmushin gefen baki ya bayyana. Wannan farin ciki da yake ji ba wai saboda soyayya ba ne, saboda nasarar matakin farko na ɗaukan fansa ne. Yana maganar zuci "Zan barta ta nutse sosai cikin soyayya… zan barta ta saba da ni har ta daina iya numfashi ba tare da ni ba. Daga baya… sai na karye zuciyarta. Zai fi komai daɗi in ga Amal da kanta tana neman Maleekh, amma Maleekh yana juya mata baya." Sai ya lumshe ido, ya jingina habarsa saman gashinta, yana ci gaba da dariya a zuciyarsa. Ita kuwa Amal tana jin zuciyarta ta samu wurin hutu, tana hawayen farin ciki a kan kirjinsa. Bayan suka gama rungumar juna a office ɗinsa, Maleekh ya ɗan ja Amal da hannunta cikin natsuwa ya ce "Na san yunwa ta galabaita mun da ke… bari mu fita restaurant, kin sha wahala daga jiya har yau." Amal ta yi ƙoƙarin share ragowar hawaye a fuskarta tana ɗan murmushi ta ce "Wallahi gaskiya ne, ban ci komai ba tun jiya…" Maleekh ya ƙara sakin murmushi, yana kallonta da wani irin yanayi da zai sa kowace mace jin daɗi. Ya ce "To shikenan, yau ni zan ciyar da masoyiyata." A haka suka fita yana riƙe da hannunta, suna fita harabar kamfanin wurin parking motoci suka nufa, yana zuwa ya buɗe murfin gaba ta shige, sannan ya zaga yo driver side ya shiga shima, a ɗari suka bar kamfanin.... Security da suka mata wulakanci ganin yanda ta samu matsayi yasa suka shiga mamaki, har suna faɗin "Yarinyar da muka raina wa wayo ashe ba ƙarama bace, cabbb Allah ya taimake mu kada ta sanar wa Boss abinda muka mata..." Haka suka gama mitar su... Maleekh da Amal ne suka nufi wani babban restaurant mai kyau. Amal tana zaune tana dube-duben ƙawataccen wurin. Maleekh kuwa yana ta duba menu yana zaɓa mata abinci da ruwan sha. Bayan sun ci abinci sosai, ya ɗan jingina ya na kallonta da murmushi. Ya ce "Na san kin gaji sosai… bari mu wuce gida ki huta." Amal ta ɗago kai tana kallonsa da sauri ta ce "Gida kuma? Wane gida kake nufi?..." Maleekh ya ce "Gidana da nake hutawa. Ba komai a can sai nutsuwa. Zaki huta, zaki sha iska ki samu kwanciyar hankali." Amal ta girgiza kai da sauri tare da faɗin "A’a, Maleekh… bazan iya zama a gidanka ba. Na san kai mutum ne mai daraja, amma idan mace da namiji suka haɗu a wuri ɗaya da babu kowa, shaidan ne na ukun su. Ka nema mun gidan wata matar aure kawai, zan kwana acan." Maleekh ya tsaya yana kallonta, sai ya yi dariya mai taushi. Ya ce "Amal… kina da imani da tsoron Allah sosai. Wannan shi ya sa nake ƙaunarki. Amma idan hakan ke damunki, to shikenan… zan kai ki gidan mu." Amal ta zaro ido da mamaki. Ta ce "Gidan ku kuma? Kai… ina tsoron iyayenka. Me zasu yi tunani idan suka ganni?..." Maleekh ya ɗan jingina ya na kallonta da ido mai cike da sirri ya ce "Kar ki damu da wannan, masoyiyata. Ni na fi kowa sanin iyayena. Zan gabatar da ke da kwarin gwiwa, domin ni ban zan taɓa ɓoye ki ba." Amal ta kasa ɗauke idonta daga nasa. Zuciyarta ta cika da farin ciki. Ta furta cikin natsuwa.. "Ka tabbata babu matsala?..." Ya jinjina kai cikin tabbaci. Yana faɗin "Ba matsala… ki kwantar da hankalinki." Wannan maganar ta ƙara narkar da Amal, domin a zuciyarta ta tabbatar da cewa Maleekh da gaske yake sonta. "Toh kenan… wannan shi ne soyayya ta gaskiya," ta faɗa a zuciyarta. Shi kuwa a ransa murmushin gefen baki ya sake bayyana. Wani sashe na zuciyarsa yana jin kamar ya ci nasara sosai domin ya san zai fi sauƙi ya karya ta idan ya riga ya gabatar da ita da iyayensa.... Bayan sun kammala gidansu, Maleekh ya nufa da ita.. Arfat da Islam suna zaune a babban falon gidan suna hira da dariya, kowannensu da waya a hannu. Cikin ɗan lokaci sai suka ji ƙarar motar da ta shigo harabar gidan. Da sauri suka leƙa daga window, suka gane motar Yayan su ce. Duk suka koma zaune cikin shirin tarbarshi. Sai ga Maleekh ya shigo cikin falon da sallama mai ƙarfi. Arfat & Islam cikin fara’a suka ce “Sannu da dawowa Yaya!” Maleekh yana amsa musu cikin natsuwa, ya ce “Yawwa, sannu… .” Kafin su sake tambayar wani abu, sai ga Amal a bayansa ta shigo cikin gidan da sallama a ranta, tana sunkuyar da kai saboda jin kunya. Arfat da Islam suka zaro ido suna kallonta da mamaki. Sai ga Farha ta sauƙo daga upstairs, alamar daga ɗakinta ta fito, tana riƙe da glass cup a hannunta mai ɗauke da lemon juice, cikin falon ta shigo ba tare da ta kalli kowa ba, ta zauna tana sha a hankali... ɗago kai tayi zata yi wa Maleekh magana, idonta ne ya sauƙa akan Amal, a zabure ta miƙe da sauri kamar wacce aka mintsina.. Farha cikin ɗaga murya ta ce “Wacece wannan kuma?…” Maleekh ya tsaya cak, fuskarshi babu alamar wasa. Ya ce “Amal ce… matar da zan aura.” Fuskar Farha ta ƙara canzawa, ta ɗaga muryarta cikin kishi da takaici tana faɗin “Amal kuma? A cikin wannan gidan?…” Arfat da Islam ne suka miƙe tsaye Arfat ta ce “Amal wannan matsiyaciyar yarinyar nan?” Islam itama ta ce “Wallahi Yaya, ka rasa macen da zaka so sai wannan ‘yar talaka?” Maleekh ya daka musu tsawa har sai da suka razana, ba iya su kaɗai ba hatta Amal dake bayansa sai da ta tsorata, har suka tsaya cak cikin tsoro.. Maleekh cikin ɗaga murya ya ce “Ku dakata mun! Shin ina wasa da ku ne?…” Arfat da Islam suka yi tsumu, zuciyarsu na harbawa saboda sun san Yayan nasu idan ya ɗaga murya, ba mai iya tankwarar da shi... Farha kuwa ta matse baki cike da kishi, ta kuma furta cikin masifa: “Ƴar talakawa ce mana! Ka rasa mata sai wannan jakar matsiyaciya zaka kawo mana gida? Ni ɗin meye aibu na?…” Maleekh yana zazzaro mata ido cikin tsananin ɓacin rai ya ce “Farha! Gidan ubana ne ko gidan ubanki? Idan kuma baki da amsa, ki yi shiru kafin ki tashi min hankalin da zai sa na kakkarya ki a gidan nan...!” Arfat da gudu ta haura stairs, zuciyarta na ɓari, ta je ta ƙira Ammy da gaggawa. Ba a jima ba sai ga Ammy ta fito daga ɗaki da hanzari ta sauƙo falo, fuskar ta cike da masifa da mamaki. kallo ɗaya tayi wa Amal tayi saurin kawar da kanta tana kallon Maleekh.. cikin ɓacin rai ta ce “ Maleekh saboda ka raina mutane yanzu abun naka har ya kai ka kawo mana wannan matsiyaciya gidan nan? Wato duk duniya ka rasa mace sai wannan jakar marar mutunci?…” Amal ta sunkuyar da kanta, ta kasa cewa komai, hawaye na taruwa a idonta. Maleekh kuwa yana kallon Ammy ya ce “Ammy, ki saurare ni da kyau. Duk masifar da za ki yi, na yanke hukuncina. Dole Amal ta zauna a gidan nan, babu wanda zai hanata. Kuma wanda ya wulakanta ta tamkar ya wulakanta ni ne.” Falon ya ɗauki shiru. Arfat da Islam suka shiga tsoron kallon Yayan nasu, suna taɓa juna da alamun tsoro. Maleekh ya juya ya kalli Islam da idon da yasa ta firgita.. Ya ce “Islam, tashi ki je ki gyara mata ɗaki. Ina so ta samu wurin kwana mai kyau.” Islam ta tsaya cak tana kallon Ammy, amma saboda tsananin tsoron Yayan natan yasa ta juya cikin jin haushi ta tafi ɗakin domin shirya wurin.... Ammy ta cije lebenta, amma babu yanda ta iya domin ta san halin ɗanta idan ya tsaya akan abu mai mai dakatar da shi sai Abbansa... Maleekh ya juyo ya kamo hannun Amal, ya zaunar da ita a kan babban sofa, ya furta cikin natsuwa da izza “Ki zauna a nan, ki kwantar da hankalinki. Ana kammala gyara miki ɗaki sai ki shiga ki huta. Kin ji?” Amal ta ɗaga kai a hankali, zuciyarta cike da tsoro da kunya, amma kuma tana jin wani farin ciki na musamman cewa Maleekh ya tsaya tsayin daka saboda ita. Farha kuwa ta kasa zama. Kishi ya rufe mata ido, tana ta hararar Amal kamar idanunta za su faɗo. Zuciyarta na karyewa, tana jin kamar duniya ta tsaya mata saboda yadda Maleekh ya fito fili ya kare Amal a gaban kowa. Bayan Islam ta gyara ɗakin da ƙyar saboda tsoron Yayan ta, Maleekh ya kai Amal da kansa... Cikin tausasawa ya ce “Kin ga! Ki kwantar da hankalinki, ki huta sosai. Ni zan koma part ɗina. Idan kin buƙaci wani abu, ki sanar.” Amal ta gyaɗa kai cikin kunya, ta ce cikin murya mai rauni “Nagode sosai Yaya Maleekh. Allah ya saka da alheri..” Maleekh ya dafa kanta ya yi mata murmushi, sannan ya fita daga ɗakin ya nufi part ɗinsa. Amal ta rufe ƙofar a hankali, ta kwanta a kan gadon. Da hawayen farin ciki da kuma tsoro, ta rinƙa farta addu’o'i a ranta: “Ya Allah, kai ka san zuciyata da gaskiyata. Kada ka jarabceni da wulakanci. Ka kare min mutuncina, ka tabbatar min da soyayyar da nake gani a fuskar Maleekh…” Ta rufe idonta, hawaye suka fara silalewa akan kuncinta, zuciyarta na tsaka da farin ciki da tsoro a lokaci guda... Ba a jima ba sai ƙofar ɗakin ta buɗe da ƙarfi, Amal dake kwance a firgice ta tashi daga kwancen da take. Farha ce ta shigo, fuska cike da ƙiyayya da kishi, tana tafiya a hankali kamar maciji, tsaya cikin izza tana furta.. “Ke! Tashi ki fuskance ni kafin na tashi miki hankali.” Amal ta tsaya tana kallonta cikin tsoro, ta kasa cewa komai. Farha ta ƙara matsowa ta cigaba da faɗin “Kin ji abin da na faɗa ko? Wannan ɗakin ba naki bane, wannan gidan ba naki bane, wannan namijin da kike mafarki da shi ba naki bane! Ni ce wacce zai aura Farha, cikakkiyar yarinya daga gidan masu kuɗi, mai kima da daraja.” Ta kwaikwayi Amal tana girgiza kai cikin raini ta kuma cewa “Ke kuwa? Babu abin da kike dashi face tsiya! Ƴar talakawa marar gata, ke da kika rasa komai sai kukan banza. Ki fita daga rayuwar Maleekh kafin ki ga tashin hankali a hannuna.” Amal ta runtse idonta, hawaye suka cika mata ido. Ta ce cikin rawar murya “Ni banzo nan domin in karɓe shi daga kowa ba. Soyayya ce ta haɗa mu, kuma shi da kansa ya ce…” Farha ta dakatar da ita da dariyar rainin hankali ta ce “Soyayya? Ke da Yaya Maleekh? Haba! Soyayya ce ta makantar dake har kina tunanin zaki zauna a matsayin Amaryar sa? To bari in gaya miki gaskiya wannan gidan zai zubar miki da mutunci ne, idan baki fice da kanki ba.” Amal ta yi shiru tana kallonta, zuciyarta tana bugawa da sauri. Ba ta so a yi hayaniya ba, amma kalaman Farha sun shiga zuciyarta sosai. Amal cikin rauni ta ce “Me yasa za ki ce haka? Ni ban zo nan da niyyar karɓar wanda ba nawa ba. Idan Maleekh ya yanke shawara akanki, ai ni ba zan taɓa tsaya masa a gaba ba.” Farha ta matso kusa da ita, ta ɗaga gira da isa ta ce “Kin yi kyau wajen wasa da magana, amma ki sani, ni ba zan bari ki tsaya a tsakanin mu ba. Idan baki fita da kanki ba, to zan tabbatar kin fita da kunya.” A part d'in Maleekh kuwa, yana zuwa ya shige bathroom domin watsa ruwa, bai san abinda yake wakana ba acan area Amal. Kunna shower yayi mai ɗauke da ruwan ɗumi...Ruwa na sauƙa akan sa, zuciyarsa na tunanin yadda Amal ta zo Abuja saboda shi.... A hankali ya furta cikin mugun murmushi... “Amal, zaki sha soyayyata sosai… har sai na cika miki zuciya da soyayyata. Amma a ƙarshe zan nuna miki bana taɓa yafewa....” Ya lumshe idanu yana dariyar mugunta, amma a waje yana shirin fito da murmushin soyayya.... Part ɗin Amal... Amal ta yi shiru na ɗan lokaci tana ƙoƙarin ɗaure zuciyarta kada ta fashe da kuka. Ta san cewa idan ta nuna rauni, Farha za ta ɗauka cewa ta yi nasara. Sai ta ɗaga kanta, ta dubi Farha da idanu masu ɗauke da nutsuwa... Ta ce “kin ga, ba ni na gayyaci Maleekh cikin rayuwata ba, shi da kansa ne ya zo. Ni ban zo nan da faɗa ba, kuma ba na buƙatar maƙiyi. Amma ki sani, gaskiya ba ta ɓoye kanta. Wanda Allah ya rubuta miki shi zai kasance naki, to ba makawa zaki mallake shi, amma wanda ba naki ba ne, ba za ki taɓa riƙe shi ba.” Farha ta taɓe baki, ta juya kamar za ta fita, sai kuma ta sake juyowa ta kalle ta... “Kada ki sake ce mun 'Kin ga' sunana Farha, sannan Kina da wayo sosai, amma wayon ki ba zai hana ni zama matar Maleekh ba. Ki dai jira ki gani.” Ta bar ɗakin tana kwaɓe baki.. Amal kuwa tana zaune akan gadon da zuciyarta cike da ƙuna. Ta tashi ta shige bathroom domin dauro alwala, tana fito wa ta zura hijabinta ta rufe jikinta sosai, sannan ta tsada sallah akan sallayar da yake a shimfiɗeyi, bayan ta idar ta fara addu’a a cikin ranta “Ya Allah, ka bani ikon jure wannan jarabawa. Ka kare min mutuncina da amincina.” A bangaren Maleekh kuwa, ruwa ne ya tsaya a bathroom, Maleekh ya fito da tawul yana goge kansa. sai murmushi kawai yake yi, zuciyarsa cike da shirin komawa wajen Amal domin su ci abinci tare... Maleekh ya fito daga bedroom ɗinsa cikin shigar rigar barci, Ya nufi ɗakin da Amal take.. Da ya buɗe ƙofar, ya same ta zaune gefen gado akan sallaya, kanta a sunkuye, hannuwanta cikin hijabi kamar wacce ke cikin tunani mai nauyi... Sai da ya tsaya na ɗan lokaci yana kallonta, fuskar ta nuna cewa tana ɓoye wani abu... Cikin murya mai taushi ya ce "Amal… ya naga fuskar ki haka? Ko dai akwai damuwa ne?" Amal ta ɗago kanta a hankali, ta yi murmushin ƙarya, tana ƙoƙarin ɓoye hawayen da suka taru a idonta. Ta ce "A’a, ba komai… kawai gajiya ce." Maleekh ya matso kusa da ita ya zauna a bakin gado, yana dubanta sosai. Ya ce "Karki ɓoye min wani abu, Amal. Na fi kowa sanin idanuwanki. Idan kina cikin damuwa, zan gane." Amal ta ɗan ja numfashi, ta yi shiru tana kallon hannayenta. Ta yi ƙoƙarin guje wa magana game da Farha saboda kar ta zama dalilin tashin hankali. Ta ce "Wallahi ba komai, Yaya Maleekh. Zan yi ƙoƙari na saba da sabuwar muhalli kawai." Sai ya kama hannunta ya riƙe da ƙarfi, yana kallonta cikin idanu. Ya ce "Kin san ba zan taɓa barin wani ya cutar da ke ba, ko Amal? Na kawo ki gidan mu, kuma wannan gida naki ne. Karki ji tsoro, ina tare dake." Amal ta ɗan murmusa, hawaye suka zubo mata ba tare da ta shirya ba. Ta ce "Nagode, Yaya Maleekh… nagode sosai." Ya share mata hawayen da yatsansa, sannan ya miƙe yana faɗin: "Taso mu je cin abinci..." Amal ta tashi a hankali ta bi shi, zuciyarta tana ƙara tabbatarwa cewa duk da ƙiyayyar da gidan ke nuna mata, Maleekh na tare da ita. Amal da Maleekh suka fito daga ɗakin da aka tanadar mata. Amal na tafiya a hankali gefen Maleekh, kamar wacce take jin nauyin ƙasar da take takawa. Maleekh kuwa ya kama hannunta yana jagoranta har suka ƙarasa dining area. A can kuwa, Ammy tana zaune a kujera tana sanye da eyes glass tana nuna rashin jin daɗi a fuskarta, Farha kuwa ta jingina da kujera, ganin Maleekh da Amal yasa ta kama kugu tana kallon Amal cikin kiyayya. Islam da Arfat suna gefe suna washe baki kamar suna jiran rikici ya tashi. Ammy ganin su yasa ta buɗe baki cikin masifa ta ce "Kai Maleekh, baka da hankali ne? har da ita zaka kawota wajen cin abincin mu? Wannan gidan na talakawa ne? Ko kuwa ka manta gidan uban ka ne?!" Maleekh bai zauna ba, ya tsaya yana duban Ammy da mamaki ya ce "Ammy, ki kula da kalamanki. Ki tuna Amal baƙuwa ce kuma sannan ita ce matar da zan aura. Kuma ban kawo ta nan domin ku wulakanta ta ba." Farha ta tintsire da dariyar baƙin ciki tana tafa hannu ta ce "Matar da zaka aura? Hmmm… da kuwa ka nuna wa duniya cewa iyayenka basu da matsayi! Wannan matsiyaciyar ce zaka zaɓa a matsayin matarka? Wallahi bazan yarda ba!" Amal ta sunkuyar da kanta, zuciyarta na bugawa da ƙarfi. Maleekh ne ya matsa kusa da ita, ya zaro kujerar dining ya zaunar da ita da kansa... Sannan ya juyo yana duban Farha da Ammy ya ce "Ko ku yarda, ko ba ku yarda ba, Amal za ta ci abinci anan, kuma zata zauna a wannan gida cikin mutunci. Na faɗa, kuma na gama." Arfat da Islam suka yi shiru, suka kallon juna, suna jin tsoron yadda fuskar Yayan nasu ta sauya, kamar ba shi ba... Ammy ta daka tsawa, tare da miƙewa tsaye ta ce "Maleekh! Ka raina ni kenan? Ni mahaifiyarka ce! Kuma ba zan taɓa amincewa da wannan abinda kake shiryawa ba. Wannan yarinya ba zata taɓa zama surukata ba, ka ji ni da kyau!" Maleekh ya goya hannuwansa a ƙirji, yana kallonta cike da mamaki.. Ya ce "Ammy, tabbas ke mahaifiyata ce kuma kinada matsayi na musamman a cikin zuciyata, matsayin da ba kowa zai iske shi ba, amma kada ki ɗauke ni a matsayin ƙaramin yaro yanzu. Domin na girma, ina kuma da ra’ayi, kuma ra’ayina shi ne Amal. Na kawo ta cikin wannan gida saboda ina so ta saba da ku, amma idan kun ci gaba da wulakanta ta…" Ya ɗan dakata, ya sauƙe numfashi mai nauyi sannan ya ce "…to wallahi zan ɗauketa mu bar wannan gidan gaba ɗaya." Jikin kowa ya yi sanyi. Amal kuwa ta ji hawaye na tsiyaya a idonta, tana tunanin wannan ƙuduri da Maleekh ya ɗauka saboda ita. Farha kuwa kaɗa kai tayi cikin takaici, zuciyarta na ƙuna saboda rashin nasarar da ta yi wajen dakatar da Maleekh... Farha tana jin maganar Maleekh sai jikinta ya ɗauki rawa saboda takaici. Ta kalli Ammy, ta d'addage gira kamar zata fashe da kuka ta juya da gudu ta nufi ɗakinta cikin fushi... Bayan ta shiga ɗakinta ta rufe ƙofar ɗakin da ƙarfi, ta fashe da wani irin ihu mai cike da tsananin kishi. Ta ɗauki kwalbar turare ta buga a jikin glass mirror ya tarwatse gaba ɗaya... Cikin zafin rai take faɗin "Wallahi Amal! Sai kin gane wacece ni! Kin shiga tsakanina da Maleekh? To kuwa ba za ki taɓa cin nasara a kaina ba!" Ta fara yawo cikin ɗakin tana shirin haɗa plan... Cikin murmushin mugunta ta kuma cewa "Hmm… yanzu dai Maleekh ya ɗauki ta a matsayin mai tsarki, mai gaskiya… Ai babu matsala. Zan nemo hanyar da zan zubar masa da ita, zan nuna masa ainihin Amal da yake so. Sai na jawo masu ƙiyayya ta asali a tsakanin su..." Ta ɗauki wayarta ta fara duba hotunan Amal a shafinta na social media. Tana dariyar mugunta..tare da faɗin "Yar ƙaramar talaka ce kawai, mai kalar da za a iya amfani da ita a jefar da ita. Zan jawo mata mummunar asara, sai Maleekh ya tsane ta da kansa." Ta tsaya a gaban madubin da ya farfashe tana kallo cikin ido da yake yabe wa biyu, tana tafa hannuwa cikin shakku da mugun nufi ta kuma cewa "Zan fara da Ammy, sai ta ƙara tsanar Amal, daga nan zan samu wasu bayanai na karya domin in nuna musu ita ba budurwa ba ce… ko da kuwa karya ce. Wannan ne kawai zai karya Maleekh. Zan ci gaba da amfani da sharrin magana da dabaru. Sai Amal ta gudu da kanta daga gidan nan!" Ta fashe da dariya mai ɗauke da ƙiyayya, tana jin daɗin tunanin yadda zata ɓata sunan Amal a idon iyayensu da mutanen duniya gaba ɗaya... Da dare bayan Maleekh ya koma part ɗinsa, Amal tana kwance a ɗakin da aka gyara mata. Amma zuciyarta ta kasa samun natsuwa. Duk kalaman da Farha ta faɗa mata suna yawo a cikin kunnenta. "Ni ce matar da Maleekh zai aura, ke ba kya da komai sai talauci… ki fita daga rayuwarsa…" Amal ta ɗauki pillow ta rungume shi, hawaye suna sauka daga idonta. A cikin ranta take faɗin "Wayyo Allah na, shin gaskiya ne? Shin da gaske za su ƙi ni saboda halin da nake ciki? Ko kuwa Maleekh zai iya tsayawa dani? Amma idan ya canza ra'ayi fa… idan ya amince da Farha fa…?" Ƙirjinta ya buga da ƙarfi, tana jin tsoron kar soyayyar da take riƙewa da zuciya ɗaya ta zame mata bala’i. Sai ta tuna lokacin da Maleekh ya kamo hannunta a ofis dinsa, lokacin da yace “Maleekh bazai taɓa gujanki ba…” Amal ta ƙara fashewa da kuka. Cikin rawar murya take faɗin "Na biyo shi zuwa Abuja saboda soyayya, amma yanzu na fara jin tsoron makomata. Idan suka wulakanta ni fa? Idan iyayensa suka ƙi karɓata fa? Idan Maleekh ya gaji da ni ya juya mun baya fa…?" Kuka mai ƙarfi ya ci gaba da kwace mata. Ta miƙe tsaye a jikin window tana kallon waje, tana jin daɗin iska mai sanyi. Amal a hankali ta furta "Ya Allah, idan wannan soyayyar ce ƙaddara ta, ka tabbatar mun da ita. Amma idan zata zame min wulakanci da tozarci, ka fitar da ni cikin ruwan sanyi kafin zuciyata ta karye gaba ɗaya…" Ta durƙusa a sallaya, tana roƙon Allah cikin hawaye, zuciyarta na cike da ruɗani da shakku.... ☆☆☆☆ Washegari da safe, tun kafin kowa ya tashi Amal ta farka, ta yi sallah. Amma duk da haka idanunta sun kumbura saboda kuka... Misalin ƙarfe takwas, Farha ta shigo ɗakin Amal da wani ƙamshi na turare. Tana riƙe da cup ɗin coffee a hannu, tana tafe a hankali kamar sarauniya... Tana murmushin raini ta ce "Yar talaka, ina kwana? Kin tashi lafiya kuwa a gidan da bai dace dake ba?" Amal ta sunkuyar da kanta, bata ce komai ba. Farha ta ƙaraso kusa da ita, ta tsaya a gabanta ta ce "Kin ji ko? Wannan gidan ba wurinki zaman ki bane. Maleekh kuwa… Maleekh nawa ne, ba naki ba. Kin ji kuwa? Ni ce matar da zai aura, ba ke ba." Amal cikin sanyin murya ta ce: "Ki daina faɗar haka, don Allah ki barni da masoyina…" Farha ta kyalkyale da dariya mai cike da raini. Ta ce "Masoyinki? Haba Amal. Kina ganin wannan gidan na alfarma, wannan iyalai masu daraja, zasu zaɓi mace irin ki? Matsiyaciya mai lalatacciyar rayuwa? Ki duba kanki, ki duba ni?" Ta ɗaga hannayenta tana nuna rigarta mai tsada, da sarƙa a wuyanta mai kayan da ta sha kwalliya... Farha cikin ɗaga murya ta ce "Ni ce nagarta, ni ce mai kyau, ni ce mai kuɗi, ni ce mai daraja. Ke kuwa… ba kya da komai! Ki fita daga rayuwar Maleekh, ki barshi gare ni kafin ki ga abinda yafi ƙarfin ki!" Amal ta fashe da kuka tana faɗin: "Wallahi ina son Maleekh da gaske, ba wai saboda kuɗinsa ko darajarsa ba…" Farha cikin tsananin kishi, tana zaro ido ta ce "Ke da gaske kike son shi? To bari ki gani. Zan nuna miki wacece ni, zan tabbatar da kin bar rayuwarsa da kanki!" Ta juya cikin masifa ta bar ɗakin, ƙamshin turarenta ya biyo bayanta... Amal kuwa ta durƙusa a ƙasa tana kuka, zuciyarta na cike da tsoro da ruɗani. Jin alamu mutum ta nufo ɗakin ta kuma ƙamshin turaren ya nuna cewa Maleekh ne.. Da sauri ta goggoge hawayen fuskar ta, ta zauna silently.. Maleekh ne ya shigo cikin shirinsa zai tafi Office na tafiya Office... Bayan sun gaisa ta nuna masa ba wani damuwa.. Amal tace dashi "Yaya Maleekh dan Allah inaso zan koma Kaduna, na bar Inna ita kaɗai.." Maleekh yace "bazaki koma yanzu ba Amal, Inna kuwa nasa a kula da ita acan..." Amal tace "sai yaushe to? Nifa da niyyar kwana ɗaya zanyi na koma..." Maleekh ya karkada kai sannan yace. "Taso muje muyi breakfast.." Haka ya ja hannun Amal suka fita. Dinning suka je ana suka tarar da sauran yan gidan. Ammy da Abbah wato mahaifinsu da kannensa biyu Arfat da Islam, sai wacce take masifar sonsa wato Farha... Kowa yana zaune akan kujerun cin abinci. Amal ta shigo a hankali tare da Maleekh, hannunsa riƙe da nata. A zuciyarta tana jin nauyin ganin iyayensa, musamman yadda ta fahimci Ammy ba ta sonta. Amal ce ta durƙusa ƙasi tana gaishe su, Ammy ko kallon yanda take bata yi ba, sai Abba da ya kalleta yana murmushi ya amsa mata....ba tare da ya tambaya ko ita wacece ba ya ci gaba da breakfast ɗinsa, domin duk wanda yazo gidansa yana mai farin ciki, domin masoyinka ne zai zo yanda kake, shiyasa bai wani damu da sanin ko ita wacece ba.... Bayan sun zauna, Ammy ta kalli Abbah da tsananin damuwa. Ta ce da shi "Ka gani ko? Ga shi nan abinda nake ta faɗa maka tun jiya. Maleekh ya kawo mana matsala gida. Wannan matsiyaciyar yarinya ce, wacce ta zubar masa da mutunci a bainar jama’a, ta mare shi, ta wulakanta shi, kuma har yanzu ya kasa kawar da ita daga rayuwarsa. Wannan abin kunya ne gare mu!" Abbah ya juyo yana duban Maleekh. cikin nutsuwa ya ce "Maleekh, me hakan yake nufi?" Maleekh ya riƙe hannun Amal yana kallon mahaifinsa ya ce "Abbah, gaskiya Amal ta zo Abuja ne don ta bani haƙuri akan abin da ya faru a Kaduna. Ba ta da wurin zama anan, shi yasa na kawo ta gida a matsayin mace. Ba zai yiwu in bar ta a waje ba. Kuma gaskiya… ina sonta." Abbah ya gyara zama, yana jin daɗin yadda ɗansa ya faɗi gaskiya... Abbah ya ce "Shikenan, ba komai. Idan kai ka fahimci dalilin ta, na fahimta nima. Ba laifi bane ta zo ta nemi sulhu." Ammy ta buga hannayenta akan tebur cike da mamaki da takaici. Tana masifa "Au, kai ma? Ka ce shikenan? Kana ganin wannan yarinyar, yar matsiyaciya zata shafa mana kashin kaji, kuma ita ka ce shikenan? Yarinyar da zata jawo mutane su ƙi mu? To wallahi, muddin ina da rai, bazan bar ɗana ya aure ta ba. Farha ce ta dace da shi, ita nake so, kuma ita zai aura dole!" Amal ta sunkuyar da kanta, hawaye suna neman zubo mata saboda kalaman Ammy. Abbah ya juyo cikin nutsuwa da karfin murya ya ce "Maryam, ki saurara da kyau. Abinda ɗana yake so shi zan yi. Ba ni zan zauna masa da mata ba, shi ne zai zauna da ita. Idan Farha ya zaɓa, zan yi farin ciki. Idan kuma wannan yarinyar da kike kiran matsiyaciya ce ya zaɓa, to ni na amince. Kin gane?" Ammy ta dafe kirji tana girgiza kai cikin takaici ta ce "Wato kai kake goya masa baya akan raina ni koh? To wallahi ba zan taɓa amincewa da wannan auren ba!" Maleekh ya dubi Ammy yana murmushi ya ce "Ammy, ki sani wannan ba wasa bane. Ni Amal ce nake so, kuma babu wanda zai hana ni. Duk soyayyar da nake nuna mata da gaske ne. Tin da na zaɓe ta, to babu wanda zai hana ni auran ta." Abbah ya ɗaga hannu alamar sulhu ya ce "Shikenan, ku daina ɗaga hankalin ku akan wannan magana. Ku bar shi ya yi abinda zuciyarsa ta zaɓa." Ammy ta yi shiru, tana huci cike da takaici. Farha kuwa ta ɗaure fuska kamar zata fashe da kuka. Maleekh ne shima ya zauna kusa da Amal, yana ƙoƙarin rarrashinta. Suka fara cin breakfast tare, duk da cewa Amal bata iya ɗaga kai sosai saboda kunya da nauyin kalaman da ta ji daga Ammy. Haka suke cin abinci, gidan ya ɗauki shiru, Amma idan aka kalli fuskar Farha, cike take da kishi da takaici. Farha kasa cin komai tayi, ta ɗago tana dariyar mugunta ta ce "Hmm… wallahi mamaki yake bani. Yarinyar da ta mare shi a bainar jama’a, yau ga shi tana nan zaune a gidanmu tana cin abinci da mu. Kenam wannan ce masoyiyar gidan?" Islam ta runtse idanu tana kallon Amal da ta tsinci kanta cikin kunya... Farha ta ɗora da gori tana faɗin "Kin kyauta Amal. Ke da ƙaramar rigar jikinki da tsiyarki, yau kin samu wurin zama a gidan da ba kowace yarinya ke kaiwa ba. Amma ki sani wannan abinci da kike ci, ina ganin ya fi ƙarfin ki. Kuma idan har za a zaɓi wacce za ta zama matar Maleekh, ni ce, ba ke ba!" Abbah yayi kamar bai ji ba ya ci gaba da cin abincin sa... Farha ta kalli Maleekh kai tsaye tana ƙara murya da cewa. "Ya Maleekh, kowa yasan ni ce aka zaɓa maka. Wannan matsiyaciya ba zata tsaya da kai a duk inda ka je ba. Ita yar gari ce kawai, ni ce ta dace da kai. Kai ka duba ka ganni fa, na haɗu sosai..." Amal ta tsaya cak, ta kasa ɗaga cokali. Idanuwanta suka cika da hawaye amma ta nace ta yi shiru saboda kada ta kawo gardama a gaban iyayen Maleekh. Maleekh ya ajiye cokalin hannunsa a fusace, ya yi wani irin tsawar da yasa kowa ya dakata... Maleekh cikin ɗaga murya yake faɗin "Farha! Ki rufe bakinki kafin na nuna miki ina matsayin ki yake. Amal ce zaɓi na, kuma duk wanda ya kuskura ya wulakanta ta to ni ya wulakanta. Ki ji tsoron kalaman ki." Farha ta ɗaga gira tana kallonsa da hawaye cikin fushi, amma bata iya cewa komai ba. Abbah ya ɗan ɗaga kai ya ce cikin natsuwa: "Ku daina wannan hayaniya. Idan aka gama ci kowa sai ya kama abun yi. Amal baƙuwa ce a gidan nan, ku girmamata." Ammy ta yi ƙasa da ido, tana huci da baƙin ciki, Farha kuwa ta share hawayenta da ƙyalle tana jin haushin yanda Maleekh yake nuna kulawarsa a Amal. Maleekh ya jawo Amal kusa da shi yana nuna mata cewa babu ruwanta da wannan masifa, sannan suka ci gaba da breakfast cikin nauyin zuciya da shiru. Bayan sun kammala, Abbah ne yayi wa Ammy sallama cewa zai wuce Kaduna wurin ɗayar matarsa wato uwar su A'isha ƙawar Amal... AMAL jin haka yasa ta sau murmushi tana duban Ammy taga wani irin reaction ne zai bayyana a fuskar ta... A tsawace Ammy ta ce "To ina ruwana, idan ka je kada ka taɓa dawowa gidan nan, tin da zuwa take lasa maka a baki, kada ka ƙara mun sallama in zaka tafi wurin wancan mahaukaciyar matar takan.." Abbah yana duban ta ya ce "To sai bayan kwana biyu kuma..." Ammy tana huci ta ce "Kayi shekara ɗari idan ka ga dama..." Da haka Abbah ya tafi tare da Maleekh suka fice... Amal tana zaune akan sopa tana fuskarta plasman da dariyar Ammy akan fuskarta... Arfat ganin yanda Amal take da murmushi kamar bata da wani damuwa, yasa ta je gabanta tana faɗin "Ke wai kin manta inda kika fito ne? Ƴar talaka kawai, kin samu damar shigowa gidan mu shine kina ji da kai... In ba don Yaya bane ya kawo ki, da tunin an kore ki daga nan!" Amal ta kalle ta cikin nutsuwa ta ce: "Arfat, ban zo nan don mu yi takaddama ba. Ban kuma zo neman girma ba. Allah ne ya kawo ni, kuma duk wanda Allah ya ɗaukaka, babu wanda zai iya wulakanta shi." Islam kuwa, tana zaune gefen kujera, ta ce a hankali cikin taushin murya: "Ku daina mana....." Islam tana kallon Arfat ta ce "Amma fa, ba haka ake yi ba. Tinda Yaya Maleekh ne ya kawo ta gidan nan, to akwai dalili, kuma bai dace a wulaƙanta ta ba." Ammy ta ɗan zaro ido tana kallon Islam, dake itace mai ɗan sauƙi ta ce "Ke ma kin fara nuna wa wannan matsiyaciya goyon baya kenan? To ki kalle ni da kyau, ba zan taɓa yarda ta zama surukata ba!" Farha ta sake matsowa kusa da Amal cikin harara ta ce "Kin ji dai? Ni ce matar da Maleekh zai aura. Ki fita daga gaban mu, ki daina ƙoƙarin shiga tsakaninmu... Kafin ki gane da ruwa ake shayi, ki duba yadda gidan nan yake buƙatata, ba ke ba!" Amal ta ɗan murmusa cikin taurin zuciya, ta dubi Farha idon cikin ido sannan ta ce "Farha, mijin da Allah bai rubuta miki ba, ba ki isa ki riƙe shi ba. Kuma mijin da Allah ya rubuta miki, babu wanda zai iya kwace shi daga gare ki. Don haka ki daina jin tsoro ko ƙiyayya a kaina." Farha ta ƙara tunzura tana huci... Ammy ta daka mata tsawa tana faɗin. "Ni ba zan ɗauki wannan abun kunya ba! Ki jira Maleekh ya dawo, yau sai dai ya zaɓa, ni ko ke, wato har kin samu bakin mayar wa koh?!" Farha cikin jin nasara ta tsaya a gefe tana dariya tana tafa hannuwa, tana faɗin "Amal, ki shirya tafiya, domin nan ba wurinki bane!" Ammy cikin fushi ta wurga wa Amal harara tare da faɗin "Wai tsaya,, Ke ɗin wacece?..." Amal tayi murmushi sannan tace "ni ƙawar A'isha ce, ƴar kishiyarki dake kaduna..." Ammy cikin fushi ta zabga wa Amal mari tare da faɗin "Aikin banza kawai, to uwar A'isha ma dan buro ubanta ba komai ne a wurina ba balle A'isha, balle ke ƙawar Aisha, saboda kin raina mun wayo shine zaki bani wannan amsar koh?..." Farha tana dariya tace "ƙawar ƴar kishiyar Ammy? Lallai da kalan dangi kike kam, kenam Aisha ce ta haɗa ki da Maleekh koh?.." Amal ta ce "Allah ne ya haɗa ni da Maleekh..." Farha ce ta kawo hannu zata mari Amal, Amal tayi saurin riƙe hannunta tare da faɗin "Kada ki kuskura ki mare ni, koda wasa...idan ita Ammy ta mare ni tasha to ke baki isa ba..." Ammy cikin tsawa tace "to ko nima zaki rama ne?..." Amal tace "ke Mahaifiyar Maleekh ne, Mahaifiyarsa kuma tamkar Mahaifiyata ce, ina girmama ki..." Kafin Amal ta ƙarasa Ammy tayi saurin dakatar da ita, tana faɗin "kull....Kada ki kuskura ki ɗauke ni a matsayin mahaifiyarki domin ni ban haifi matsiyaci ba..." Farha ta ce "saboda rashin kunya har da riƙe mun hannu na kawo miki mari koh? To bari kiji nafi karfinki, kuma ko kasheki nayi a gidan nan babu abinda za'a mun...Sai dai ƙarin matsayi..." Arfat itama ta fara mata, tana mata wulakanci, tare da kwatanta ta da "yar kasuwa marar galihu...". Islam, wacce tunda farko bata ce komai ba, ta shiga tsakaninsu tana faɗin "Don Allah ku daina. Wannan da kuke yi babu amfani, sai dai ku ɓata wa Yayana Maleekh rai." Ammy ta ɗaga hannu tana girgiza kai cikin tsawa: "Wallahi yau sai Maleekh ya zaɓa a tsakani ni da ke! Ni ba zan zauna da ke a matsayin suruka ba!" Farha ta yi dariya tana tafa hannuwa ta ce "Ki shirya tafiya Amal. Wannan gida ba naki bane, ni ce uwargida a nan!" Amal ta kalle ta cikin bacin rai, ta ce: "Farha, mijin da Allah bai rubuta miki ba, ba zaki taɓa samu ba. Kuma mijin da Allah ya rubuta a gare ki, babu wanda zai iya kwace shi. Zan jira Maleekh ya dawo domin bazan cigaba da zama a gidan nan ba, ku kwantar da hankalin ku..." Daga nan ta wuce ɗakin da aka ajiye ta..... asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 21 to 22 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 A cikin babban office nasa mai yalwa da haske, Maleekh yana zaune akan kujerarsa ta Executive, yana juyawa a hankali tare da zuƙar shisha, yana wani mugun murmushi ta gefen baki. A gabansa kuwa akwai manyan screens guda biyu, ɗaya yana nuna masa graphs na business ɗinsa, ɗaya kuma live CCTV footage na gidan su. Sai ga PA ɗinsa ya shigo da takardu a hannu. Yana kallon boss ɗinsa cikin mamaki, saboda murmushin da yake yi. PA Ya ce “Boss, yau naga kamar kana cikin farin ciki… ko akwai wani sabon deal?” Maleekh yana jinjina kai, ya ɗan ja shisha sannan ya ce “Eh, akwai deal mafi girma fiye da kowanne. Amal ta zo Abuja, ta nemi sulhu, ta kuma amince da soyayyata. Yanzu haka tana gidan mu.” PA cike da damuwa ya ce “Amma Boss, kasan fa cewa Hajiya da Farha da sauran ’yan gidan basa ƙaunar ta. Za su iya yi mata duka ko wulakanci. Ka tabbatar da hakan?” Maleekh yana dariya marar sauti, ya ɗan zazzaro ido ya ce “Na tabbatar. Shi yasa na kaita gidan. Inaso suyi kaca-kaca da ita. Hajiyata fa ba kanwar lasa bace, Farha kuma ta fi kowa kishin banza. Arfat kuwa, rashin kunya ne sunanta. Sai dai Islam… ita kaɗai ce mai tausayin abin da nake so. Amma da tasan abinda ke cikin raina na tsanar Amal, da ita ma zata tsane ta.” Ya ɗan matsar da kujerarsa gaba, ya danno wani button, footage na Amal tana tsaye a falon gida tare da Arfat da Farha suka bayyana akan screen. Ana jiyo su suna mata masifa. Maleekh ya kalli PA yana murmushi ya ce “Ka gani? Wannan shi nake so. Ina so su gasa ta da wulakanci, sai dai ni in fito a gabanta a matsayin mai kare ta. A haka zata ƙara manne mun ɗari bisa ɗari. Daga baya kuma in jefa ta cikin wuta, in buga wasan ball ɗina da ita. Wannan shine plan ɗina.” PA ya lumshe ido yana jinjina kai tare da faɗin “Boss… wallahi ka fi kowa wayo. Amma fa ta yi babban kuskure da ta dawo wurinka. Yanzu dole ne ta gane babu gudu babu ja da baya.” Maleekh yana kallonsa tare da jan kunne ya ce “Karka manta, babu wanda yasan wannan game sai ni da kai. Idan wani ya ji wannan sirri daga bakinka… uhmm! zaka iya tuna yadda na gama da abokin nan nawa wancan shekarar?” PA ya girgiza kai da sauri, jikin sa har ya ɗan ɗauki karkarwa ya ce “A’a Boss! Babu wanda zai ji daga bakina. Kai kaɗai ne boss ɗina har abada.” Maleekh ya sake yin la’anannen murmushi, yana juyi akan kujerarsa, shisha a hannu, footage na Amal a gaban sa. Maleekh a hankali, kamar yana magana da kansa ya furta “Amal zata ji soyayyata a fili… amma a ɓoye, zan jefa ta cikin wuta har sai ta zama abinda nake so.” ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Amal in her Room Amal tana zaune a ɗakin da aka tanadar mata. Ɗakin kuwa ba wani mai yalwa ba ne idan aka kwatanta da sauran d'akunan gidan, amma ya fi mata komai tunda tana cikin ƙasaitaccen gida.... Tana zaune akan gadonta ta jingina kanta jikin bango, idanunta sun kumbura saboda kuka. Hannunta na riƙe da hijab ɗinta domin bata fiye cire shi ba, kullum yana jikinta, tana murza gefensa kamar zata samu nutsuwa daga hakan... Amal muryarta a hankali, tana magana da kanta... “Me yasa kowa a gidan nan baya sona? Ko Ammy bata tausaya mun… Farha kuma sai kishi dani. Arfat kuma sai rashin kunya. Wayyo Allah na, na shiga gidan da ba kowa ke so na ba.” Ta ɗan ɗaga ido tana kallon sama, hawaye na zubo mata ta ci gaba da faɗin . “Amma ban da Maleekh. Shi kaɗai ne ya tsaya mun, yake kare ni. Duk da abinda ya faru a baya, yanzu nake tabbatarwa cewa yana sona da gaske. Da babu shi a gefena, da tuni zuciyata ta fashe da baƙin ciki.” Ta ɗan kwantar da kanta bisa filo, tana tuna lokacin da Maleekh ya rungume ta a falon ofishinsa, ya ce ba zai gujeta ba. Wani ɗan murmushi ya bayyana a fuskar Amal duk da cewa tana cikin hawaye. “Zan jure komai saboda shi. Ko wane irin wulakanci suka min, ina da tabbacin Maleekh zai tsaya a bayana. Shi ne hasken zuciyata.” A haka ta lumshe ido tana kuka a hankali, zuciyarta cike da soyayya da amincewa ba tare da ta san cewa wanda take ganin mai tsaronta ne babban mai jefa ta cikin ramin wulakanci ba. In the Corridor A waje kusa da ƙofar ɗakin Amal, Farha tana jingine da bango hannunta riƙe da glass cup ɗin drink, tana sauraron maganganun Amal da take yin su a fili cikin kuka... Farha ta lumshe ido tana saurare, wani mungun murmushi ya bayyana a fuskarta. A hankali, tana magana da kanta ta ce “Haka nake so… ki fara jin zafin da gidan nan zai miki. Wannan ba wai farkon ba ne, Amal! nan ne asalin azabarki. Ni kuwa sai na tabbatar kin gudu kin bar min Maleekh gaba ɗaya.” Ta ɗan ja numfashi, sannan ta juya da isa da gadara kamar wata sarauniya, ta nufi sashen ta... Bayan dawowar Maleekh daga Office da yamma, ya ƙaraso gidan cikin nutsuwa. Ganin bai tarar da kowa a falo ba yasa ya nufi sashen Amal, knocking yayi tare da tura ƙofar a lokaci guda, bai tsaya jiran bada izini ba, yana shiga ya tarar da ita zaune a kan gado, kanta lullube da pillow tana sharar kuka kamar ƙaramar yarinya... Cikin dabara ya ɗan tsaya a bakin ƙofa yana kallonta, murmushin mugunta ya wuce a zuciyarsa kafin ya daidaita fuskar sa ya saka annuri. Ya shiga a hankali yana faɗin: “Amal… kina kuka kuma? Waye ya taɓa min ke a gidan nan?” Amal ta ɗago da idonta da suka yi jawur saboda kuka, ta share hawayenta da sauri... Cikin raunanniyar muryar ta ce “Ban iya jurewa ba, Maleekh. Gaba ɗaya suna kallona da mungun nufi, suna nuna min cewa ban dace da kai ba. Har suna ƙira na da matsiyaciya…” Sai hawaye suka sake zubo mata. Maleekh ya ƙaraso kusa da ita ya zauna, ya ɗauki hannunta ya riƙe sosai, yana kallonta ya ce “Kin san abinda zan faɗa miki? Bazan bar kowa ya hana ni soyayyata ba. Ki daina sauraren su, ki tsaya a kan kalmar da kika faɗa min jiya cewa kina sona. Idan har kina sona Amal, babu wanda zai iya raba mu.” Amal ta girgiza kai tana hawaye ta ce “Ina sonka, Maleekh… amma tsoron iyayenka nake ji. Tsoron kar su raba ni da kai.” Maleekh ya ɗan murmusa, ya matso da ita sosai har ta jingina da ƙirjinsa ya ce “Babu wanda zai iya rabani dake. Ki tabbatar da wannan. Ki ɗauki zuciyata tamkar garkuwarki. Har abada, ni ne zan kare ki.” Ya ɗora hannunsa a kanta yana bubbuga bayanta cikin rarrashi. Amal kuwa ta sake fashewa da kuka na farin ciki, tana jin kamar wannan kalaman sun share mata duk wata damuwa... A zuciyar Maleekh kuwa, yana wani irin dariyar mugunta tare da maganar zuci. “Haka nake so, Amal. Ki miƙa min zuciyarki gaba ɗaya. Lokaci yana zuwa da zaki gane ni ba abin da kike zato ba.” Sai ya share fuskar da murmushi mai taushi, yana ci gaba da rarrashin ta kamar masoyin gaskiya. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Washegari da safe, Maleekh ya shirya cikin shigar alfarma mai kyau. Yana tare da Amal a room ɗinta, cikin sassanyar murya ya ce da ita. “Amal, yau ba na so ki zauna a gida. Zamu fita tare, mu sha iska, mu ci abinci mai daɗi a waje.” Amal da farko ta yi shiru tana tunanin ko hakan ba zai fusata iyayensa ba. Amma ganin irin rarrashi da tsananin kulawa a fuskarsa, sai ta amince. Sun fita da wata motarsa mai kyan gaske, suka je wani babban restaurant mai ɗauke da haske da kiɗa mai laushi. A wajen Amal ta ji daɗin kasancewa tare da shi. Har ta manta da tsangwamar iyayensa. Maleekh yana murmushi, yana saka ta dariya. Yana tsokanar ta da kalmomi masu daɗi, har sai da zuciyar Amal ta sake gaba ɗaya. Maleekh cikin murmushi yake faɗin “Kin ga yadda dariya yake bala'in miki kyau? Wannan dariyar ce ta ɗauke mun hankali. Idan kina kusa da ni, babu wani abu da zai dame ni.” Amal tana dariya cikin jin kunya ta ce “Ni dai ina jin daɗin kasancewa tare da kai. Amma gaskiya ban saba irin wannan wuri ba.” Maleekh ya dafa hannunta akan teburin restaurant, yana kallon ta ido cikin ido ya ce “Wannan rayuwa tamu ce. Zan koya miki komai a hankali. Ki daina jin tsoro.” Amal ta yi murmushi cikin hawaye na farin ciki... Bayan nan suka nufi babban supermarket yayi mata siyayya kala-kala, da dogwayen riguna, da takalma da kayan kwalliya, har da su pants da breziyass da komai abinda ya shafi mata.. Maleekh ganin Amal ta ɗauki sinƙin wani abu kamar dozen ne a ninninke ya sa hannu yana taɓa wa cike da mamaki ya ce. "Amal ke ɗin me zaki yi da sinƙin bread haka..?.." Amal tayi dariya tare da faɗin "Ba fa bread bane, mata ne kawai masu amfani dashi..." Ya ce. "Kamar ya? Shi ɗin meye ne kenam?.." Amal ganin yana so ya takurata da wannan question ne yasa ta miƙa masa ba tare da ta furta komai ba... Ya karɓa yana faɗin "Yawwa ban na duba koma menene..." Karanta rubutun jikin yayi sannan ya saki murmushi yana faɗin. "O hoooo, sai ki ce mun abun ku na taran makwararin jini ne..." Amal da sauri ta karɓe cikin jin kunya tayi saurin yin gaba, domin akwai wasu matasa har sun juyo suna dariya... Da haka suka kammala siyayya, Maleekh ya biya duk kayan da suka ɗauka... Bayan sun dawo gida, Amal ta ji nutsuwa sosai saboda kulawar Maleekh. Amma tun da suka shigo gidan taji wani bugun zuciya... Ita kaɗai ta shigo falo ta tarar da mutanen gidan a falo... Ammy wani irin harara ta wurga mata cike da baƙin ciki ta ce “Kin yi ta yawon banza da shi ko? Wannan dai shine aikin ki, jan ɗana ya manta da iyayensa...” Farha, wacce zuciyarta ke cike da kishi, ta miƙe tsaye tana kallon Amal da tsantsar tsanarta ta ce “Ni kam ban san wace irin jaraba ce ke da Maleekh ba. Kin ɗauka soyayyar da yake miki za ta kare ki ne? Ki sani, ni ce wacce za ta zama matar Maleekh, ba ke ba. Ke dai matsiyaciya ce kawai, marar gata.” Arfat ta ɗan goyi bayan su tana cewa: “Amal, kin san wannan gidan ba naku bane. Ki shirya komawa inda kika fito, kafin mu kore ki da kanmu.” Amal ta yi shiru tana sauraronsu. Amma zuciyarta tana karfafa mata da cewa “Ina da Maleekh. Shi kaɗai zan dogara da shi.” Islam dai ta tsaya gefe tana tausayawa Amal, amma bata ce komai ba saboda tana tsoron ɓacin ran mahaifiyarta... ♡ Maleekh ne ya shigo yana riƙe da jakunkuna na siyayya masu alfarma, waɗanda duk wanda ya gansu ya san ba a ƙaramin kasafi aka saya ba. Har lokacin murmushi yake yi, zuciyarsa cike da nishaɗin yadda zai faranta wa Amal rai da sabbin kayayyakin da ya siya mata. Da ya taka cikin babban falon, abin da idonsa ya tarar da shi ya karyar da farin cikinsa. Amal ce tsaye a tsakiyar falo, Ammy da Farha sun zagaye ta da kalaman wulakanci, yayin da Arfat kanwarsa ke ɗaga hannu cikin tsananin bacin rai, alamar ta kusa kaima Amal duka. Amal kuwa tana tsaye, hannunta a gefe tana ƙoƙarin tattara ƙarfin guiwa, kodayake idanunta sun kaɗa saboda tsananin zafin cin fuska. Islam ce kaɗai ke gefe, shiru kamar wacce ba ta da ikon magana. Maleekh ya dakata da sauri, idanunsa suka sauya kala. A fusace ya isa tsakiyar falon yana ɗaga murya cikin faɗa: “What the hell is going on here?!” Dukansu suka kalle shi. Amal ta juya idanunta suka haɗu da na Maleekh, sai ta sauƙe numfashi mai nauyi, alamun jin daɗin ganin shi. Farha ce ta fara tsaki tana turo baki ta ce “Oh, har mata siyayyar kayayyaki koh? Wato wannan ce yanzu har ta zama special?…” Ammy ta tsunduma cikin magana tana kallon jakunkunan hannunsa cikin ɓacin rai ta ce “Kai Maleekh, Kana da hankali kuwa? Ka dawo gida da wannan ‘yar banza, har da mata siyayyar kaya masu tsada? Ka manta kai ɗan gidan masu kuɗi ne, ba ɗan gidan talauci ba? Wataƙila ta shirya maka wani laya ne da take shirin mallake ka, to wallahi bokanta bazai taɓa yin aiki a gidan nan ba…” Amal ta kasa jurewa, zuciyarta ta buga da ƙarfi jin an kwatanta ta da boka, amma kafin ta buɗe baki Maleekh yayi saurin faɗin: “Enough, Mom! Enough! bazan bari ku wulakanta min ita ba. Amal ba matsiyaciya bace kamar yadda kuke ƙiran ta. Duk wani abu da nake mata daga zuciyata yake fitowa. Kuma ki sani Mom, duk wanda ya ɗaga mata hannu, tamkar ya ɗaga mun hannu ne!” Ammy ta ce "And so what idan an ɗaga maka hannun? Ubanka ma ai bai fi ƙarfin a ɗaga masa hannu ba balle kai, to ka kiyaye ni..." Maleekh ya kawar da fuska gefe ba tare da ya furta komai ba, Ya kama hannun Amal yana ƙoƙarin jan ta ya nufi saman upstairs da ita... Arfat ce tayi dariya tana faɗin “Wow, lallai Amal, kin yi nasara! Amma ki sani ba wannan ke nufin za ki ji daɗin zama a gidan nan ba. Ki jira ki gani…” Maleekh ne ya juyo a fusace ya zabga mata mari daman a gefensa take... Arfat tinin ta riƙe fuska tana zunduma ihu... Farha ce ta riƙe ta tana shafa mata wurin marin, tare da faɗin "Yanzu saboda wannan matsiyaciyar zaka raunana ƙanwarka?..." Islam kuwa hannu tasa ta toshe baki tana gusar da dariyar marin da Arfat ta sha... Ammy kuwa dariya ta yi cikin tsaki tana girgiza kai ta ce “Maleekh, wallahi baka da hankali. Ka je sama ka ci gaba da wawantarka, amma ka sani wannan ƴar jarida ba zata taɓa zama ‘yar gidan nan da daraja ba. Ni ce mahaifiyarka, na fi sanin abin da ya fi dacewa da kai.” Maleekh ya juyo yana ƙoƙarin haɗiye zuciyarsa ya ce “Mom, idan kina son darajata, to ki fara daraja ni ta hanyar daraja wacce nake so. Wannan shine karshen raini da cin fuska akan Amal a gidan nan. I won’t take it anymore.” Ya ɗauki jakunkunan siyayya, sannan ya ja hannun Amal da ƙarfin gaske ba tare da ya sake kallon kowa ba, Maleekh ya ja Amal suka nufi sama, a wannan lokacin part ɗinsa suka nufa tare... matakan gilashin beni mai walƙiya suna bayyana tsantsar tsadar gidan. Amal idonta akan glass ɗin benin, gani take kamar zai fashe, just a tsorace take takawa... Kowa yana kallonsu cike da bacin rai da tsananin kishi, musamman Farha da idonta ya kaɗa saboda tsananin baƙin ciki. ✨ Part ɗin Maleekh’s Area Bayan sun haura upstairs, Amal ta tarar da wani sashe mai faɗi wanda ya bambanta da sauran wurare na gidan. Wannan part ɗin na Maleekh yana da private sitting room (falo na musamman), wanda aka yi wa ado da farin paint da fitilun chandelier masu launin haske. A gefen falon akwai glass table mai ƙyalli, sofas masu launin grey da cushions masu taushi. Daga gefen hagu, akwai ƙofar da ke kaiwa master bedroom ɗinsa, wanda shima ke da king-sized bed, bedsheet ɗinsa mai launin fari da launin navy blue mai kyan gaske.. A cikin bedroom ɗin akwai side ɗin walk-in closet mai cikakken shelves na tufafi da takalma da dabam.. A gefen dama kuma akwai ƙofa da ke kaiwa private bathroom, wanda aka gina da tiles masu sheƙi, jacuzzi mai faɗi, da gilashin shower room mai tsada. AC ɗin ɗakin yana busar da sanyi mai ɗaukar hankali, yana haifar da kwanciyar hankali da nishaɗi... Da suka shigo cikin falon nasa, Maleekh ya ajiye jakunkunan akan glass table, Amal kuwa ta zauna a gefen sofa cikin nutsuwa. Duk da kukan zuciyarta da takaicin wulakancin da ta sha daga Ammy da Farha, sai ta yi murmushi mai rauni tana kallon Maleekh. Shi kuma ya nufi bedroom ɗinsa domin rage kayan jikinsa. Tunaninsa ya cika da damuwa da fushi, amma ya daddage domin kar Amal ta ji wani tashin hankali. Yana cikin bedroom ɗin yana sauya kaya, sai ya fito da t-shirt mai sauƙi da trouser. Amma da ya fito, sai ya tsaya cak. Amal ce akan sofa, tana kwance idanunta a rufe gaba ɗaya. Ta miƙe akan kujera tana sharar bacci cikin nutsuwa, gashin kanta ya warware duk ya zubo akan kafaɗarta... Maleekh ya tsaya yana kallonta, Sanyin AC ɗakin ya lulluɓe ta gaba ɗaya, har take bacci cikin nutsuwa, ba tare da ta damu da komai ba... Ajiyar zuciya ya sauƙe, ya sunkuya ya ɗauke ta a hankali cikin hannayensa kamar jaririya. Numfashinta mai sanyi yana bugan wuyansa...motsi ta fara yi tana ƙoƙarin gyara kanta a saman kafaɗarsa. A hankali ya shiga cikin bedroom ɗinsa... Maleekh ya isa kusa da gadon ya kwantar da Amal a hankali, tamkar bai son ta tashi daga baccinta. Ya ja blanket mai laushi ya lulluɓe jikinta gaba ɗaya. Duk da haka, idanunsa ba su iya barin fuskarta ba. Ya tsaya a tsaye gefen gadon, hannuwansa a aljihunsa, yana kallonta da irin kallon da mutum ke yi wa abu mai daraja wanda bai taɓa tsammanin zai mallaka ba. A zuciyarsa akwai tarin ƙiyayya, amma a wannan lokacin wani sabon abu ya taso masa, abin da bai iya fahimta ba. Idanunsa suna biye da kowanne ɓangare na fuskarta: Farar fatar ta mai ɗaukar ido, wacce take da laushi kamar auduga. Idanunta duk da a rufe suke, girman su da tsawon gashinsu na sa mutum ya ji tamkar za su yi magana koda ba ta buɗe su ba. Ƙaramin bakinta, tare da launin lips ɗinta mai color ja tamkar sabuwar pomegranate, suna yi masa wani irin kallo koda ba ta motsa su ba. Gashin girarta mai kauri mai siffar natural, wanda ya yi kyau daidai da surar fuskarta. Tsayin hancinta madaidaiciya.. Idanunsa suka sauƙa ƙasa, suka tsaya a kan kirjin ta. Breast ɗinta a cike masu girma suna lulluɓe da blanket, amma shaid'an ya shiga masa rai. Da sauri ya ɗauke kansa cikin ƙarfin hali, zuciyarsa tana wani mummunan bugawa... Shape ɗin hips ɗinta da ya bayyana cikin lulluɓin blanket ya sa shi ƙara yin shiru yana danne zuciyarsa. Kyakkyawar surarta ta zarce misali, irin kyan da yake haɗe da na Indian beauty... Maleekh ya ja numfashi mai nauyi. Ƙila zuciyarsa ta fara karkata gareta....girgiza kai yayi tare da matsawa daga jikin gadon, yana jin kamar idan ya ƙara tsayawa kusa da ita, zai rasa ikon kansa... “Ba yanzu ba… fansa ta fi wannan muhimmanci.” Ya furta a zuciyarsa. Sai dai, idanunsa sun ƙi barin jikinta... Maleekh ya tsaya gefen gadon, yana kallon Amal da ta yi nisa a baccin ta. Numfashinta mai sauƙi yana fita cikin nutsuwa, tamkar ba ta taɓa shiga cikin wahala ko tashin hankali ba. A zuciyarsa ya fara magana da kansa: “Amal… ke ce mace ta farko da ta taɓa tsallake iyakokina, ta mare ni, ta wulakanta ni a bainar jama’a. Na rantse cewa ranar fansa ta ba zata wuce ba. Amma yau… ga shi kina kwance a kan gadona, kina baccin nutsuwa kamar wata sarauniya.” Ya lumshe ido, ya haɗa hannuwansa ya goya akan kirjinsa..Ya ci gaba da faɗin “Kina da kyau fiye da misali… farin fatarki, idanuwan nan masu girma, bakin ki mai ɗaukar hankali… komai naki abin sha’awa ne. Amma, Amal… wannan kyau ba zai hana ki biyan fansar da kika jarabtar da ni da ita ba.” Ya ƙara matsawa kusa, idanunsa suka tsaya kan blanket ɗin da ya lulluɓeta, yana iya hango siffar jikinta a ƙarƙashin sa. “Na san duk wani namiji da zai ganki a wannan yanayi zai ruɗu ya manta da komai, amma ni… Maleekh… ban saba barin mace ta ci karfina ba. Sai dai gaskiya Amal, yau na kasa ɗauke idona daga gare ki. Kamar wanda kika mun sihiri?.” Ya jinjina kai, ya yi murmushin gefen baki, mai ɗauke da duhu da alamar mugun shiri... “Zan nuna miki soyayya, zan lulluɓe ki da alheri da kariya… amma duk a fuska ne. A ɓoye kuwa, zan jefa ki cikin wuta. Ki ɗanɗana wahalar da ta fi marin da kika yi min sau dubu.” Ya yi shiru na ɗan lokaci, yana lumshe idanuwansa cikin nutsuwa, sai daga baya ya furta a hankali, tamkar yana magana da ita amma ba ta jin sa: “Amal… kiyi bacci, ki huta a kan gadona… domin wannan hutu zai zama farkon hanyarki zuwa cikin azabar da nake shiryawa a zuciya ta.” Ya ja blanket ɗin da ta ɗan zame, ya rufe ta sosai, sannan ya juya ya fice daga ɗakin da wani irin nauyi a zuciyarsa, nauyin soyayya da yake ƙoƙarin hana shigar sa cikin zuciyarsa, da kuma nauyin mungun fansa da yake ran sa... Yanayin tsarin bedroom ɗin gwanin burgewa, domin bedroom ɗin ba kawai ɗaki bane, mazauni ne na sarki... Katafaren gadon king size bed ne, mai frame ɗin Italian mahogany wood wanda aka yi masa zane a gefuna. Headboard ɗinsa an yi shi da leather quilted design mai taushi, wanda fitilar gefen gado (bedside lamp) ke haskawa yana fitar da walwali. Blanket ɗin farar fata ce mai ɗauke da silk embroidery, pillows kuwa sun cika gadon, manya-manyan masu taushi da ƙananun masu launi daban-daban, suna sa gadon yayi kamar wani gado na princess.. Bangon ɗakin an yi masa marble wall panels na farin dutse, sannan a tsakiyar bangon da gadon ya jingina aka saka babban frame mai ɗauke da painting na art ɗin ocean view. An yi hidden lighting a saman bangon (ceiling) wanda yake bada hasken mai laushi, yana sa ɗakin yayi romantic. Ƙasa kuwa Persian carpet ce mai launin ruwan haske, ta rufe tsakiyar ɗakin, yayin da sauran ƙasan Italian marble tiles ne masu kyalli. An saka manyan windows masu gilashin tempered glass, sai dai an rufe da long curtains na velvet wine color da aka ja daga sama har ƙasa, suna bada yanayin royalty. Sofas biyu masu launin fari, Italian leather da aka saka a gefe... Ga akwatin glass center table wanda yake kan carpet. Wardrobe ɗin walk-in closet ne a gefe, sai bathroom mai ƙyalli da aka yi da marble tiles da kuma jacuzzi bathtub a ciki. Hancinki zai ji ƙamshin oudh perfume mai haɗe da vanilla da sandalwood, da zaran kin shiga ciki.... sai wani dim light wanda yake bada nutsuwa da ɗan “romantic tension”. Amal tana kwance akan gadon nan mai girma, blanket ɗin silk ya rufe jikinta, gashinta ya bazu a kan farin pillow kamar sarauniya da aka kwantar. Fitilar gefen gado tana haskawa a saman fuskarta, ta sa farin fatarta da kyan idanuwanta sun ƙara walwali. Baccin da take yi ya haɗu da luxury ambience ɗakin, tamkar wata Indian princess da aka kwantar a masarauta... Maleekh kuwa yana tsaye a gefen gado, idanunsa suna kai-kawo tsakanin kyawunta da kuma tunanin mungun shirin da yake yi. Idan aka koma kan Bathroom ɗinsa...bathroom ɗin yana da sliding glass door mai gilashin frosted wanda ba’a iya ganin ciki sosai. Idan ka shiga ciki iska mai sanyi na air freshener ne zai bugi hancinki da ƙamshin oudh & lavender. An yi bangon bathroom da Italian white marble mai ƙyalli, an zana masa gold streaks kamar layukan zinare.. Ƙasan kuwa heated floor tiles ne wato tiles ɗin suna bada ɗumi a ƙasa duk lokacin da ka taka, ko da a lokacin sanyi ne. Babban abu da ya ɗauke ido shine Jacuzzi bathtub ɗin da aka saka a kusurwar hagun.. An yi shi da porcelain white finish mai sheƙi.. Yana da hydro-massage system wato ruwa na fitowa a jikin bangon tub ɗin yana yi maka tausa yayin da kake ciki. Sannan aka zagaye gefen tub ɗin da small LED lights masu launin blue, suna bada wani romantic glow. A gefen bathtub aka ajiye wine glass holder da kuma scented candles masu ƙamshi... Shower area.. A gefe guda akwai walk-in glass shower, frameless transparent glass. Shower ɗin rainfall shower head ne, idan an kunna, ruwan yana sauƙa kamar ruwan sama.. A gefe an saka hand shower don tausa da goge jiki. Fuskokin bangon an yi musu waterproof golden mosaic tiles. Mirror & Sink Area A tsakiyar bathroom akwai double sink vanity wato basin biyu masu ceramic finish da golden faucets. A sama akwai huge mirror mai ɗauke da backlit LED frame wanda yake bada haske mai kyau idan mutum na duban kansa. A gefen sink aka jera designer perfumes, aftershaves, da kuma expensive skincare products (Versace, Dior, Tom Ford). Towels Arrangement... Towels masu taushi (Egyptian cotton) aka nannad'e su a cikin golden towel rack. An jera manya (bath towels), ƙanana (hand towels), da robe mai alama da sunan Maleekh da aka yi da embroidery. Other Luxury Touches.. An saka sound system speakers a cikin ceiling, don haka mutum zai iya kunna kiɗa yayin da yake wanka. A gefen jikin mirror akwai automatic soap dispenser da kuma flower vase mai ɗauke da fresh white roses. Fitilun bathroom ɗin ba su da tsanani an yi su dim light option domin ya bada nutsuwa yayin da mutum ke hutawa cikin Jacuzzi. Amal tana kwance kan katafaren king-sized bed ɗinsa har bacci ya fara kaurace mata, a hankali ta fara motsi daga baya ta farka gaba ɗaya.... Idanunta suka ɗan lumshe saboda AC mai sanyin daɗi da ƙamshin turaren da ke tashi a ɗakin... A hankali ta miƙe daga gadon, tana bin ƙyallin fitilun LED lights da ke gefen bangon bedroom ɗin. Ganin wata ƙofa mai frosted glass da haske ke fita daga ciki yasa ta je wurin... Da ta buɗe ƙofar, sai iska mai daɗi da ƙamshin lavender & oudh ya buge mata hanci. Gabanta ya ɗan faɗi rass, wannan shine bathroom ɗin Maleekh... 👣 Ta taka cikin marble tiles masu ɗumi a ƙasa, idanunta suka lumshe saboda nutsuwar da ta shige ta. A gabanta, huge backlit mirror ne ya bayyana mata. Tana kallon kanta cikin madubin, tana ganin irin yadda gajeriyar tafiyar da ta sha wahala ta haggard ɗin fuskarta, amma kyawunta bai gushe ba. Hannunta ya sauƙa a kan golden faucet, ta kunna ruwa sai crystal clear water ya fara gudu da ƙamshi. Ta ɗan wanke fuskarta tana shaƙar nutsuwa... Idonta ya sauƙa kan Jacuzzi bathtub a gefen kusurwa, da LED lights masu launin blue suna kyalli kamar taurari a ƙarƙashin ruwa. Sai ta ɗan yi murmushi kaɗan tana faɗin a ranta: "Kai wannan rayuwar alatu... ni ce na tsinci kaina a ciki yau? Har cikin gidan su Maleekh, cikin ɗakin sa... Sai ta ji jikinta yana rawa da tsoro da kunya lokaci guda. Amal ta juya zuwa gefen towel rack, ta ɗauki ƙaramar towel mai laushi, ta ɗora akan kafaɗarta. Idanunta suka sake komawa kan madubi, inda ta tsaya tana duban kanta. Kyawunta ya bayyana fiye da ko yaushe.. farar fatar ta ta haske ƙarƙashin hasken LED. gashin girarta masu kauri da kyau suna rufe manyan idanunta masu launin hazel. ƙaramin bakinta mai launin pink natural lips ya yi laushi... tsayin hancinta madaidaici, ga surar fuskarta mai kama da Indiyawa. Kayan dake jikinta ya lulluɓe jikinta sosai amma duk da hakan perfect body curves ɗinta sun fito: hips ɗinta masu shape, ƙirjinta da ya yi kyau daidai gwargwado. Ta lumshe ido tana rufe fuska da towel ɗin kamar tana ɓoye kunya. Sai kawai ta ji ƙarar ƙofar bedroom ta buɗe, Maleekh ya dawo daga falon ɗakin nasa. Yana riƙe da wayarsa a hannu, amma da ya hango ƙyallin hasken bathroom ɗinsa, sai ya tsaya cak. A hankali ya je bakin ƙofar bathroom ya tsaya.. Knowing ya fara yi tare da furta. "Kin fara ne ko na shigo?..." Jin shiru yasa ya ɗan tura ƙofar, ganin ta yayi a tsaye a jikin mirror... Tsaya kallonta yake, Kallo mai haɗe da soyayya da ƙiyayya a zuciyarsa lokaci guda. Amal kuwa tana tsaye gaban madubi tana share fuskarta da towel, sai gashinta mai tsawo da ya zubo kan kafaɗunta... Maleekh a hankali ya busar da slow deep breath, sai murmushin gefen baki ya bayyana a fuskarsa, yana faɗin a ransa: "Kin shiga ragar da na kafa miki da kanki, Amal." Ya ɗan jinjina kai, idanunsa suna sauƙa a kan kowace siffarta, kafin ya furta da murya mai nutsuwa da kuma izza.. "Amal… me kike yi cikin bathroom haka? Kina son kaɗa mun zuciya ne?" Amal ta juyo da sauri, idonta ya haɗu da nasa. Towel ɗin da ta ɗora a kafaɗarta ya zame ƙasa. Ta matsa baya kaɗan, zuciyarta na bugawa da sauri... Amal cikin jin kunya ta ce "Ni… ba haka bane. Ban san bathroom bane, kawai… na ga ƙofa na haskawa, sai na shigo." Maleekh ya ɗan yi murmushi sannan ya matsa kusa da ita, Amal ta ja baya tare da yin saurin ɗaukar towel ta rungume a ƙirjinta.. Cikin rawar murya take faɗin "Maleekh, dan Allah ka daina irin wannan kallon. Ka sani… ni ba irin ‘yan matan da kake gani ba ne." Maleekh ya tsaya yana kallonta cikin madubin sannan ya ce "Kuma wannan shi ne dalilin da yasa na kasa samun natsuwa, Amal. Kin bambanta. Kina da wani abu da sauran basu da shi. Idan kina tsaye a nan, cikin bathroom ɗina… me kike tsammani zan yi?" Amal ta yi shiru, idanunta suka cika da hawaye. Ta ƙi kallonsa kai tsaye, sai ta ce da sanyin murya "Abin da nake tsammani shine… ka barni da mutuncina. Ka bari na fita daga nan cikin kwanciyar hankali. Ban zo duniya don in kasance abin wasa ba, Maleekh." Bayan ta furta hakan, sai bathroom ɗin ya yi shiru na ɗan lokaci. Maleekh ya zuba mata ido kamar zai cinye ta da kallo. Sai kuma ya matsa kusa, yana ɗan lumshe ido ya ce: "Mutunci…? Ni ma mutuncin ki ne, Amal. Amma ki sani… kin shiga rayuwata, kuma babu fita. Ko da kina so ko baki so." Amal ta ji jikinta ya mutu da tsoro da wani abu da ta kasa fassara. Ta ƙara matse towel ɗin, zuciyarta na bugawa kamar zata fito... Maleekh ya matsa sosai dab da ita, har numfashinsa yana busawa a fuskarta. Hannunsa ya kai ya kama gashinta mai taushi, ya shafa shi a hankali tare da murzawa.... Amal ta rufe idonta tana jin jikinta ya mutu gaba ɗaya, babu kuzari sai na zuciya da take bugawa da sauri. Maleekh cikin murya mai taushi, yana shafa gashinta ya ce "Amal… kina sane da irin abin da kike haddasa min? Kin taɓa sanin yadda kike da iko a kaina?" Amal bata iya magana ba, sai shiru da rawar numfashi. Idanunsa suka sauƙa kan fuskarta gaba ɗaya, yana bin girarta da kallon sha’awa. Ya zame hannunsa daga gashi ya kai gefen fuskarta, ya shafa ƙuncinta da yatsunsa cikin taushi. Amal ta buɗe idanunta a hankali, idonsu suka haɗu. Sai suka tsaya kallon juna na wasu daƙiƙu da suka ji kamar lokaci ya tsaya cak. Numfashinsu ya gauraya, ƙamshin jikinsa yana gauraya da nata. Maleekh ya kai yatsarsa kan lips ɗinta, ya shafa a hankali kamar yana karanta wani sirri a ciki. Amal ta lumshe ido, zuciyarta tana wanzuwa cikin wani irin shauƙin da bata taɓa jin makamancin sa ba. Maleekh yana raɗawa a hankali.. "Bakinki… ya fi kowanne abu da na gani kyau. Na kasa hana kaina kallo, Amal." A lokacin, Amal ta kasa motsawa. Jikinta ya yi sanyi gaba ɗaya, zuciyarta ta cika da ƙaunar Maleekh, soyayyar da ta ɗauke mata hankali. Hannunta ya motsa kaɗan kamar tana son ta riƙe hannunsa da ke shafawa a lips ɗinta. Sai shiru ya mamaye su. sai numfashinsu da bugun zuciyoyinsu ke cika bathroom ɗin. Maleekh ya matsa gaba ɗaya kusa da ita, har Amal ta ji ƙirjinsa yana gogan nata. Hannunsa guda ya sauƙa kan kafaɗarta, ɗayan kuma yana bin gashin kanta yana yawo.. Amal ta buɗe idanunta da sauƙin numfashi, ta haɗa kallo da shi. Idanun su sun zamo kamar maganarsa da maganarta na haɗuwa a wuri ɗaya, babu kalma, babu magana sai soyayya mai kauri. A hankali Maleekh ya sauƙe hannunsa daga kafaɗarta zuwa bayanta, yana jan ta zuwa jikinsa. Amal ta kasa motsa wa, Sai ma jikinta da ya sake, Idonta a rufe, tana jin wani irin nutsuwa da ƙauna... Maleekh har ya kusan rungumar ta gaba ɗaya. Sai dai a wannan lokacin zuciyarsa ta yi wani irin harbawa. Wani murya a ransa ta tunasar da shi: "Ka manta da fansarka ne Maleekh? Ita ce za ta biya maka laifin da ta aikata, ka manta? Kada ka bari soyayya ta mamaye ka..." Ya runtse idonsa da ƙarfi, yana ƙoƙarin danne abinda zuciyarsa ke hura masa. A hankali ya janye hannunsa daga bayanta, ya ɗan matsa gefe kaɗan. Yayi kamar bai so ya janye ba, amma zuciyarsa ta tilasta shi. Amal ta buɗe idanunta a hankali, tana kallonsa cikin rashin fahimta. Ta ji kamar akwai wani abu da ya kusan faruwa amma ya tsaya cak. Ta ji daɗi da kuma ɗan haushi lokaci guda... Maleekh ya ɗan yi murmushi mai rikitarwa, wanda babu wanda zai iya gane ma’anarsa, baƙin ciki ne ko jin daɗi? Sai dai murmushin ya nuna ɓoyayyen abu a ransa... Maleekh cikin murya mai rauni, kamar yana danne zuciya ya ce "Amal… na kasa fahimtar yadda nake ji a kanki. Amma lokaci zai nuna." Sai ya juya, yana sakin numfashi mai zurfi, ya bar ta a wajen tana kallonsa cike da mamaki.. Fita yayi daga bathroom ɗin... Bayan ya fita ne Amal ta nufi ƙofa ta sa key, sannan ta shigo ciki ta shire kayan jikinta gaba ɗaya ta nufi bathtub.. Sai da ta ɗau mintuna kafin ta fito daga bathroom ɗin, tana ɗaure da towel har zuwa kirji. Tana fitowa idonta ya faɗa kan rigar da suka siya a supermarket, Maleekh ne m ya zaɓa mata a cikin sauran rigunan ya ajiye a kan gadon... Cike da murmushi ta ɗauki doguwar riga mai siririyar shape, riga ce milk-white mai ɗauke da ɗan glitter a gefe, cike da zumud'i ta sanya rigar.. Rigar ta rufe jikinta tsaf, amma ta fito da siffar hips ɗinta, shape ɗin ƙirjinta, da siririn kugunta. A gaban madubi ta tsaya, tana gyara rigar da kanta, tana taɓa gashin kanta wanda ya bazu har gadon baya... Amal ta tsaya gaban mirror tana gyara rigar jikinta, rigar ta kama jikinta har sai da ta fito da dukkanin surar da Allah ya yi mata. Hannunta na kan sumar kanta tana janye shi gefe, idonta kuma na ƙafe akan hoton kanta da yake cikin glass... Maleekh ne ya shigo falo da sallama a bakinsa yana ɗauke da kulolin abinci, ya ajiye a kan dinning dake falon, sannan ya ɗauko drinks a frig ya ajiye su... Cikin bedroom ya nufa.. Yana shiga ya tsaya a bakin ƙofa kamar an dasa shi. idonsa na kan Amal... Numfashinsa ya tsaya na ɗan lokaci. Ya ji kamar duk wani tunanin tsanar Amal da ke ransa ya ɓace a wannan mintuna.. Ita kuwa tana tsaye a jikin mirror ta kasa ɗago idonta ta kalli ƙofar, duk da tasan Maleekh ya shigo. Idonsa ya zame mata kamar camerar da ta makale akan kyanta. Yana kallonta tana kallon kanta a madubi. Amal ta fito da wani irin kyau da har haske na mirror ɗin ya ninka mata kyau ɗin da take dashi.. Shima fa Maleekh ba'a barshi a baya ba.. Kyansa ya sha bamban. Kyakyawa ne irin wanda idan ya shigo taro, kai tsaye idanun kowa yake sauƙa kansa. Tsayinsa ya zarce, cikakke ne da girman da ya dace da namiji... Jikinsa faffad'a ne, broad chest ɗin da yake nuna ƙarfinsa, amma bai yi nauyi da yawa ba. Launin fatarsa chocolate mai haske, irin wanda yake kama hasken rana da ɗan sheƙi. Fuskar sa mai ɗan faɗi ce mai ɗaukar ido, ga dogon hanci madaidaici, ga girar da ta cika masa saman ido kamar an zana.. Ga ƙaramin bakin sa mai laushi da pink lips ɗinsa da kallo ɗaya kaɗai ya isa ya rikitar da mace. Ga sumar sa mai ɗan tsayi, baƙi mai sheƙi, da siririn waves kamar sabon aski..sajen nan ya kwanta kamar wanda yayi masa shampoo...ma sha Allah.. Sai ka rantse Maleekh ba ɗan Nigeria ba ne, sai ka ce hoton wani ɗan jarumin Bollywood actor da aka hado da cikakken tsari na asali.. Maleekh ya tsaya yana kallon Amal, idonsa bai motsa daga kanta ba. Sai dai Amal duk da ta san yana kallonta ta ci gaba da shafa rigar tana kallon kanta a madubi. Zuciyarta na bugawa da sauri, amma ta kasa juyawa ta kalli idanunsa saboda jin nauyin wannan kallo da yake mata. Numfashin Maleekh ya ɗan canza. Zuciyarsa na rawa, kyan Amal a cikin wannan riga ya rikita shi. Ya sha ganin mata masu kyau a duniya, amma kyanta na yau ya bambanta. Sai ya matso da takunsa a hankali, kamar wanda yake jan kansa zuwa wani abu da bai shirya ba… A hankali ya ƙarasa kusa da ita, ya tsaya a bayanta idanunsa suna kallon hotonta a cikin mirror. Amal ta lura da shi ta cikin reflection ɗin, sai zuciyarta ta buga da ƙarfi. Amma ta kasa juyowa ta kalle shi kai tsaye. Sai dai jikin ta ya bayyana gaskiyar zuciyarta: numfashinta ya fara hargitsewa, launin fuskarta ya ɗan sauya, jikinta ya yi sanyi. Maleekh ya matso sosai tare da ɗago tafin hannunsa ya sauƙar akan gashin kanta... Ya shafa gashin nata a hankali, yana kallon idonta cikin madubi. “Amal…” ya furta da muryar da ta raɗaɗa zuciya, mai nauyin so da tsananin shauƙi. Amal kuwa ta rufe idonta na ɗan lokaci, tamkar tana jin wani abu ya taso daga ƙasan zuciyarta har ya shige dukkanin jinin jikinta. Duk da tana so ta guje masa, amma sai ta kasa. Maleekh a sannu a hankali ya sauƙe yatsunsa daga gashin kanta zuwa gefen fuskarta, ya bi layin lips ɗinta ta cikin reflection ɗin, yana shafa a hankali. Numfashinsu na fita a hankali, glass ɗin mirror ɗin ya kama hucin zafin numfashinsu. Wani irin shiru ne ya lulluɓe ɗakin, sai bugun zuciyoyinsu kawai suke ji. A wannan lokacin, soyayyar da suke ɓoye tana bayyana cikin sauƙin shauƙi, kamar wani fim ɗin soyayya na Indiya inda idanu da jiki suke magana ba tare da kalma ba... Maleekh ya ci gaba da kallon Amal ta cikin mirror, numfashinsa yana sauƙa akan wuyanta. Yatsunsa har yanzu na kan lips ɗinta, yana shafawa a hankali.. Amal ta lumshe idonta gaba ɗaya, jikin ta ya mutu tamkar ba nata ba. Wani irin sanyi mai daɗi ya lulluɓe ta, zuciyarta ta shiga wata sabuwar duniyar soyayya da bata taɓa tsammani ba. A hankali Maleekh ya manno jikinsa a nata ta baya. Zafin numfashinsa yana sauƙa a saman wuyanta, hakan yasa jikinta ya ɗauki rawar shauƙi. “Amal…” ya ƙira sunanta a hankali, muryarsa kamar ƙarar raɗa daga zuciya. Tayi shiru, amma shiru da ya fi kowanne magana. Idonta na rufe, hancinta yana shaƙar ƙamshin jikinsa wanda ya cika ɗakin. Maleekh ya ɗora hannunsa ɗaya a kan kafaɗarta, ɗayan kuma yana biye da gefen kuncinta har zuwa ƙaramin bakinta. Sannu a hankali ya sunkuyo sosai har fuskokinsu suka haɗu ta cikin reflection. Lips ɗinsa yana gogan nata a hankali, ba tare da sun haɗu gaba ɗaya ba. Wannan kusanci ya rikita Amal fiye da duk wani abu da ta taɓa ji a rayuwarta. Sai ta buɗe idonta a hankali ta kalle shi ta cikin madubi. A can cikin reflection ɗin, ta hango soyayya da shauƙi, amma a zurfin idonsa akwai wani abu da bata iya fassara ba. Hannunta ne ya fara karkarwa, da sauri ta ɗora shi a kan hannunsa da yake riƙe da fuskarta. A hankali tace da muryar da ta cika da rawar zuciya: “Maleekh…” Shi kuwa ya ƙara kusantar fuskarsa sosai, har numfashinsu yana gaurayuwa. Ya ɗan murmusa cikin wani irin salo, sannan yace: “Ke ce abinda zuciyata ta daɗe tana jira… na tabbata, bazan taɓa barin wani ya rabani dake ba…” Sai ya lumshe idonsa ya ɗan goga dogon hancinsa a kan wuyanta cikin shauƙi, ba tare da ya janye jikinsa ba. Amal kuwa ta kasa motsawa, ta shiga duniyar da soyayya ta mamaye ta baki ɗaya. Lokacin da numfashin Maleekh ya gauraye da nata, zuciyar Amal ta yi wata irin tsalle. Ta ji tamkar wani abu ya fashe a cikinta, shauƙi ya mamaye ta har ta kasa jurewa. Ba tare da wani tunani ba, ta juyo da sauri daga inda take tsaye a gaban madubi, ta faɗa cikin ƙirjinsa da ƙarfi. Hannayenta biyu ta zagaye masa wuya tana rungumarsa da tsananin ƙarfin zuciya. “Maleekh…” ta ƙira sunansa cikin rawar murya, hawaye na zubo mata ba na bakin ciki ba, sai dai na farin ciki da nutsuwar da ta tsinci kanta a ciki. Shi kuwa ya tsaya sumamme, bai taɓa tsammanin Amal zata nuna irin wannan kuzarin ba. Zuciyarsa ta yi wani irin bugu, a lokaci guda soyayya da fansa suka fara gwabza wa a ransa. Ya ɗora hannayensa biyu a bayanta, ya matse ta a jikinsa sosai. Numfashinsa ya yi nauyi, zuciyarsa tana son zaucewa gaba ɗaya. “Amal…” ya ƙira cikin murya mai zurfi, yana ɗora habarsa a kanta. “Kin sani a matsayin da babu wanda ya taɓa kai ni…” Amal ta ɗago kanta tana kallonsa, jikinta har rawa yake saboda ƙarfi da zafin da zuciyarta ta ɗauka. “Saboda kai nake rayuwa yanzu… idan ba kai ba, to waye?” Ta faɗa tana ƙura masa ido.. Maganarta ta ratsa shi kamar wuƙa, sai ya ɗan runtse idonsa. Ya ɗora ɗan yatsansa a kan lips ɗinta yana share hawaye a hankali. Sai suka tsaya a haka, jikin ta ya lulluɓe ƙirjinsa, zuciyarsu biyu suna bugawa cikin daidaito, tamkar ana kunna kiɗan soyayya da ba a iya ji sai da rai. A hankali Maleekh ya ɗora bakinsa a saman goshinta, ya yi kissing mai daɗi da tsawo. Wannan ya saka Amal ta sake ƙara matse shi da ƙarfi, tamkar zata shige jikinsa gaba ɗaya. Amal ta kasa jurewa irin yadda zuciyarta take harbawa, ta ɗaga hannuwanta a hankali kamar mai jin tsoro, sai kuma ta jingina jikinta a kirjin Maleekh, ta rungume shi da ƙarfi tamkar mai neman mafaka. Numfashin su biyu ya haɗu, shi kuwa ya runtse idanu yana jin zafin sha’awa da sanyi na soyayya ya lulluɓe shi. Cikin wannan yanayi ne, muryar mace ta katse su: Farha cikin tsawa da rawar murya ta ce “Na shiga uku! Mai zan gani haka? Amal… kina da hankali kuwa zaki rungume mun miji?” A razane Amal ta yi saurin janyewa daga jikin Maleekh, jikinta har rawa yake. Ta juyo da kallon bakin ƙofa, ta hango Farha tsaye bakin ƙofa, hannunta a ƙirji, tana zazzaro da ido waje.. Maleekh ya ƙanƙance ido yana kallonta da mamaki da fushi lokaci guda. Ya matsa gaba kaɗan, yana faɗin “What nonsense is this? Waye ya baki damar shigo mun ɗaki haka ba knocking, ba excuse? Haba Farha!” Farha cikin hararar Amal, tana yatsina fuska ta ce “Ni fa matar gidan nan ce. Ko dole sai na nemi izini in shiga bedroom ɗin mijina?” Maleekh yana daga murya ya ce “Matar gidan nan? Kin manta wannan ɗaki ba naki bane? Kin wuce gona da iri Farha! Kin sa kanki inda bai dace ba.” Farha ta matso gaba tana huci ta ce “Ai kuwa sai ka shaida a yau, domin bazan yarda da wannan abu ba! Ni a gabana wani abu irin wannan ya faru, ka kuma ce ba ni da hurumin magana?” Amal ta sunkuyar da kai kamar wata tsohuwar munafuka tana tsoron kallon Farha. Ta matso gefe, jikinta kamar zai faɗin tsabar kakkarwa... Maleekh ya kalle ta tare da riƙo hannunta yana matsawa alamar ta kwantar da hankalin ta,... lokaci guda ya mayar da hankalinsa ga Farha, yana tsananta fushinsa: “Farha, ki fita kafin nayi wurgi dake. Ki fita yanzu kafin na sa ranki ya ɓaci fiye da haka.” Farha ta yi dariyar raini mai ɗaci, sannan ta juyar da idanu, tana faɗin: “Lallai yau na tabbatar soyayyar da kake yiwa Amal ta wuce tunani… Amma wallahi, ka fara shiryawa, domin ni ba zan bari ta cinye mun zuciya a gidan da nake da hakki ba!” Ta juya da sauri ta fice daga ɗakin tana harba ƙafafu kamar mai fareti.. Dakin ya ɗauki shiru, numfashin Amal da Maleekh kawai ke cike da sararin bedroom ɗin.... NEXT NEXT NEXT.... asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 23 to 24 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Bayan Farha ta fice tana bubbuga ƙafafu, sai bedroom ɗin ya koma shiru. Maleekh ya tsaya hannunsa a ƙugu, tsabar tsananin fushi haka yake bin ƙofarda Farha ta tsaya da kallo. Numfashinsa na fita da sauri... Amal kuwa tana tsaye a gefe tana riƙe da hannun rigarta, zuciyarta na dukan uku-uku. Bata iya ɗaga ido ta kalle shi ba, saboda tsoron abinda zai faru. Cikin rawar murya ta furta: “Ka ga irin abinda ya faru koh?… ka ga abin da ta gani…” Sai kawai Maleekh ya juya da sauri ya ƙaraso inda take. Ya ɗora tafin hannunsa a kan hannunta da take riƙe da rigarta, ya sa ta sake a hankali. Yana kallon idonta kai tsaye, yana furta “Stop it, Amal. Don’t blame yourself. Ba ke kika karya ƙa’ida ba… ita ce ta karya. Ke baki da laifi.” Ya matso kusa sosai har tana iya jin zafin numfashinsa a fuskarta. Idanunsa suka cika da wani irin tsananin kulawa da ƙauna. A hankali ya kuma cewa “Na tsani ganin kin shiga damuwa saboda wani. Na tsani ganin kin firgita. Ki kwantar da hankalinki, ba zan taɓa bari Farha ko wata ta cutar dake ba. You’re mine, Amal.” Yana faɗin haka ya kamo hannayenta biyu ya ɗaure su da nasa, ya ɗaga sama ya jingina su da ƙirjinsa. Amal cikin hawaye ta ce “Amma Maleekh… maganganunta suna da zafi sosai. Ni kam tsoron rikici nake ji…” Maleekh yana girgiza kai cikin ƙarfi ya ce “Rikici? To let her dare. Let her dare, Amal. Wallahi babu wanda zai iya rabani dake. In na faɗi abu, sai ya tabbata. Babu mai tsayawa tsakanina da ke.” Ya ɗora hannunsa ɗaya a bayan kanta, ya jawo ta jikinsa sosai. Yana faɗin “Ki saurara da kyau, Amal… babu wata mace a rayuwata da zata iya mamaye zuciyata kamar ke. Ko da me zata yi, ko da me zata faɗa… you’re the only one.” Sai ya ji jikinta ya yi sanyi a jikinsa, tana ɗan fashewa da kuka a hankali, zuciyarta na narkewa da kalaman nasa. Bayan shiru mai ɗaukar lokaci, Maleekh ya saki ajiyar zuciya sannan ya ɗan raba jikinsa da nata, yana kallonta cikin lumsasshen ido. Ya ce “Come on… zo mu je falo. Kina buƙatar kwanciyar hankali, sannan kuma kina buƙatar cin abinci.” Ya kama hannunta a tausashe ya ja ta zuwa falo, kai tsaye zuwa dinning area ɗinsa da ya jera kulolin abinci a kai. Amal tana tafiya a hankali, tana jin yadda hannunsa ke riƙe da nata tamkar kada ya sake. Bayan suka isa, ya zame kujerar dinning ɗaya ya ja ya zaunar da ita, sannan ya zauna a gefenta. Kulolin abinci masu ƙanshi ya buɗe, ƙamshi ya gauraye wajen. Sai ya ɗauki cokali ya zuba mata cikin faranti, yana murmushin da bai saba yi ba. Idonsa na lumshewa kamar na wanda ya shafe dare bai huta ba. Amal tana kallon sa ta ce “Maleekh… ka dai bari ni zan ci da kaina.” Ya girgiza kai cikin izza da taushin murya ya ce “No, Amal… tonight ba zan bari ki yi komai da kanki ba. Ki huta kawai, ni zan kula dake.” Ya ɗauki spoon ɗin ya ɗebo abinci ya kai mata baki. Amal ta tsaya kallonsa, zuciyarta na rawa da wani irin zafi mai daɗi. A hankali ta buɗe baki ta karɓa. Maleekh ya kasa cire idonsa daga fuskarta yayin da take taunawa. Hannunsa da ya riƙe spoon ɗin ya tsaya cak, yana jin tamkar lokaci ya tsaya a wurin. Maleekh a hankali kamar yana furta a ransa ya ce “Allah ya sani… kina da wani abu a jikinki da ke rikita ni…” Amal ta ɗaga ido ta kalle shi, idanuwansu suka haɗu, suka tsaya suna kallon juna cikin nutsuwa. Sai ya sake ɗaukar wani ya sake bata, yana murmushin da ya fi na baya taushi. Amal cikin ƙanƙanin murya ta ce “Na gode… Maleekh.” Sai kawai ya sa hannunsa ɗaya ya dafa ƙaramar fuskarta, yana shafa gefen kumatunta mai taushi, sannan ya kai spoon ɗin gaba cikin kulawa. Har abincin ya ƙare, suka ci cikin natsuwa. Duk da kulawar da Maleekh ya nuna mata, Amal zuciyarta na karyewa... Maleekh ya sanar mata cewa su shiga cikin ta kwanta... Ta san idan har ta kwana a part ɗinsa, idanun gidan gaba ɗaya za su sauƙa akan ta da wata mummunar fahimta. Amma a lokaci guda, ta kasa faɗa masa kai tsaye... Bayan sunci abinci ya ja hannunta zuwa bedroom ɗinsa. Katafaren gadon yana shimfiɗe da blanket mai laushi, sannan ya jawo ta a hankali ya kwantar da ita.. Maleekh da saukin murya, yana kallonta daga tsaye ya ce “Amal… ki kwantar da hankalinki. Babu wanda zai cutar dake a nan… babu wanda zan bari ya tsawata miki. Ki huta kawai.” Ya gyara mata lulluɓa da hannunsa, har ta ji sanyin girmamawa fiye da yadda ta zata. Ya ɗan tsaya kallonta kamar zai sake magana, amma sai ya sauƙe ajiyar zuciya, ya juya.. A zuciyar Amal, soyyaya da tsoro suna rikici. Soyayyar da take jin tana ratsa zuciyarta saboda Maleekh, da kuma tsoron abin da zai biyo baya idan gidan ya sake samun labarin kasancewar ta a ɗakinsa. Maleekh kuwa fita daga bedroom ɗin yayi ya nufi falonsa. Sofas ɗin falon ya shimfiɗa blanket, ya kwanta yana kallon ceiling ɗin falon.. Zuciyarsa cike da tunanin abin da ya ji a lokacin da ya rungume Amal, yadda numfashinta ya rikita shi, yadda idanunta suka ja shi tamkar ruhi. Amma duk da haka, bai bari ya kauce daga burinsa ba. A zuciyarsa yana nan da niyyar fansar da zai ɗauka akan Amal, duk da cewa wani sabon yanayi na soyayya yana rarrafe shi ba tare da saninsa ba. Amal ta juyar da kanta a kan gadon, tana kallon hasken ɗakin da ya rage a kunne. Ta zuba ido a jikin kofar bedroom ɗin da Maleekh ya fita, zuciyarta na ta faman bugawa. A ranta take faɗin “Allah ka kare ni daga wannan soyayyar da zan iya rasa rayuwata a dalilinta…” Sai ta runtse ido cikin damuwa, tana jin ƙamshinsa ya gauraye har cikin gadon da take kwance. Amal tana kwance a kan katafaren gadon Maleekh, zuciyarta ta kasa samun nutsuwa. Sai ta rufe idanu tana ƙoƙarin yin bacci, amma tunanin ya fi karfin zuciyarta. A zuciyarta kalmomin da Maleekh ya faɗa mata na ci gaba da maimaituwa: “Ki kwantar da hankalinki… babu wanda zai cutar dake a nan.” Sai ta sau ƙanƙanin murmushi mai ɗaci. “Taya zan kwantar da hankali, alhalin idanu da yawa na kallona da ƙiyayya? Kuma ina jin tsananin ƙaunarsa tana ƙara ɗaure mun zuciya…” Ta jawo pillow ta rungume shi kamar shi ne Maleekh ɗin, tana jin daɗin ƙamshin turarensa da ya gauraye gadon. Sai wani irin shauƙi ya taso mata, da wata shakka mai haɗawa da tsoro. Lokaci guda bacci mai nauyi ya ɗauke ta, sai kuma ta fara mafarki... mafarkin kanta a matsayin matar auren Maleekh, tana tafiya da shi cikin taro cikin farin ciki, kowa yana kallonsu da girmamawa. Tana sanye cikin fararen kaya na Aure, Maleekh kuma yana riƙe da hannunta, yana nuna ta ga kowa a matsayin “matata”. Ta ji daɗi fiye da kowane lokaci. Amma kafin ta gama jin daɗin mafarkin, sai hoto ya sauya, Ammy da Farha sun shigo cikin mafarkin, suna tura ta daga jikin Maleekh, suna ƙiran ta “wawiya, matsiyaciya, ƴar tasha da ba ta cancanci zama matar mai daraja ba.” Haka suka riƙa caccakarta, suna dariya, suna ƙasƙantar da ita. A lokacin ta farka da tsananin firgici, tana jin hawayenta na zubo mata ba tare da saninta ba. Sai ta lumshe ido ta sake yin wani irin mafarki. A wannan karon, ta ga Maleekh ya rungume ta sosai, yana shaƙar ƙamshinta, yana furta kalmomi da suka daɗe suna ɓuya a zuciyarta: “Amal… kin zama nawa gaba ɗaya. Babu wanda zai rabani dake.” Sai numfashinta ya rikice har cikin baccinta. Ta miƙe a hankali ta zauna akan gadon, ta dafe kirjinta, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa kamar zai tsage mata ƙirji. Amal a ranta ta ce “Ko wannan soyayyar zata hallaka ni… amma wallahi ba zan iya tserewa daga gare shi ba. Kamar an ɗaure ni da Maleekh tamkar igiyar da ba zata taɓa yankewa ba.” Sai ta sake kwanciya, tana rufe fuska da bargo, tana jin kuka da dariya suna haɗuwa mata lokaci guda. A falon waje kuwa, Maleekh ya kwanta amma bacci ya gagare shi. Duk da cewa ya ɗaura kan fansa, yana jin wani sashi na zuciyarsa na tura shi ga ƙaunar Amal fiye da kowane lokaci. Ƙarar ƙiran sallar asuba ta ne ya daki dodon kunnensa, sautin muryar mai ƙiran sallah yana ratsa zuciya cikin nutsuwa. Maleekh ne ya fara tashi, ya buɗe idonsa a hankali yana kallon hasken fitilar ɗakin da bai mutu gaba ɗaya ba. Ya miƙe daga kan sofas ɗin falonsa, ya nufi bedroom ɗinsa domin duban Amal. Da ya buɗe ƙofar, sai ya ganta a kwance, idonta a lumshe kamar wacce bacci ya yi nisa. Amma a zahiri ba bacci take ba tana jin shigowarsa sosai, zuciyarta kuwa haka yake tsalle-tsalle tamkar zata ƙwace daga kirjinta. Maleekh bai nuna ya gane hakan ba, sai kawai ya wuce kai tsaye cikin bathroom domin ɗauro alwala. Murmushin ƙaramin ƙarfi ne ya bayyana a fuskarsa, wanda shi kaɗai yasan ma’anarsa. Bayan ƴan mintuna ya fito, tare da zura farar jallabiyarsa, ya matsa kusa da Amal, ya bubbuga kanta a hankali da tafin hannunsa cikin natsuwa. “Ki tashi, lokaci yayi na yin sallah.” Amal ta buɗe idonta a hankali, ta ɗaga kanta daga kan pillow tana kallonsa. Ba tare da wata magana ba ta miƙe, ta shiga bathroom don yin alwala. Ita kanta zuciyarta ta cika da mamaki tausayin irin nutsuwar da ta gani a fuskar Maleekh lokacin da yake cikin fararen kaya ya tsunduma mata a rai sosai. Shi kuwa, bayan ya kammala shirinsa, ya fice gaba ɗaya daga part ɗinsa. Kai tsaye masallaci ya nufa tare da wasu daga cikin maza masu aiki a gidan. Amal ta fito daga bathroom ɗin, ta shimfiɗa dadduma a tsakiyar bedroom. Ta tsai da sallah, zuciyarta cike da nauyi da addu’o’i. Duk da yanayin da take ciki, ta ji sallar ta mata daɗi sosai, zuciyarta ta ji wani irin sauƙi kamar an wanke mata damuwa da tsoron da ya rufe ta tun jiya. Da ta idar, ta zauna akan daddumar tana jera tasbihi. Numfashinta ya sauya zuwa na kwanciyar hankali. Sai dai duk da haka, a zuciyarta tana maimaita addu’a guda ɗaya: “Ya Allah, idan soyayyarsa alheri ne gare ni, ka daɗa mana kusanci. Idan kuwa sharri ne, ka raba ni da shi cikin sauƙi kafin zuciyata ta hallaka da ƙauna.” Bayan an idar da sallah a masallaci, Maleekh ya dawo cikin natsuwa...kafin ya haura part ɗinsa sai da ya bi da ɗakin Ammy ya yi mata knock kamar yandq ya saba kullum, yakan je ya tashe ta idan Abbansu baya nan, koda kuwa ta tashi, bayan ta buɗe sai da ya durƙusa sannan ya gaisheta kamar kullum, Ammy a sama sama ta amsa masa sannan ta juya ba tare da ta ce mishi komai ba, Amal ganin ba haka Ammy take masa ba idan yazo da asuba yasa hankalinsa tashi, amma haka ya daure ya bar part ɗinta, sai da yabi ɗakin ƙannensa sannan ya tayar dasu suma, sannan ya sanar musu akan su je ɗakin Farha su tashe ta itama... daga nan ya nufi part ɗinsa... Bayan ya shi ga falonsa kai tsaye buɗe ƙofar bedroom ɗinsa yayi, sai idonsa ya sauƙa akan Amal da take zaune har yanzu a kan daddumar sallah.. hannunta kuma na riƙe da sibha tana jera tasbihi cikin kwanciyar hankali. Ya tsaya cak yana kallonta. A zuciyarsa wani abu ya motsa, ba wai ƙauna ba ce kai tsaye, amma akwai wani irin nutsuwa da ya gani a cikin yanayinta da ya ɗan ɗaga masa hankali. Amal kuwa, da ta lura da shigowarsa, ta ɗan saki murmushi, ta ajiye sibha a gefe sannan ta ce cikin muryar kasaita. “Ina kwana, fatan antashi lafiya..” Maleekh ya ƙaraso a hankali, ya tsuguna a gabanta tare da faɗin “Lafiya klau Alhamdulillah. Amma wannan nutsuwar da nake gani a fuskarki, yau kin bambanta. Kin fi jiya kwanciyar hankali.” Amal ta ɗan sunkuyar da kanta, tana wasa da yatsun hannunta a kan dadduma. “Ka san dalili? Addu’a ce ta ba ni wannan sauƙin zuciya. Na roƙi Allah ya yanke hukuncin da ya fi alheri a tsakaninmu.” Kalmar “a tsakaninmu” ta ɗauki zuciyar Maleekh. Ya danne murmushin gefen baki da yazo masa, ya zauna kusa da ita, yana ɗaga gira yana dubanta. Ya ce “To me kike nufa da wannan addu’ar? Kina son ki tabbatar da soyayyata ce alheri gare ki ne, ko kina addu’ar Allah ya cire ni a zuciyarki gaba ɗaya?” Amal ta ɗan yi shiru, sannan ta ce cikin nutsuwa: “Na barwa Allah komai. Ni dai na fi ƙarfi wajen sanin wanda ya fi dacewa da ni. Amma ka sani Maleekh, soyayya ba abin wasa ba ce. Bata wuce zuciya ba, amma zata iya ruguza zuciya idan ta tafi kan hanya marar kyau.” Maleekh ya ɗan jinjina kai, yana ɗaga hannunsa ya shafi gashin kansa cikin yanayin mai nazari. A zuciyarsa kuwa ya yi dariya, yana cewa: “Ki kwantar da hankalinki Amal. Wutar da na fara kunna miki ba zata mutu ba. Sai na tabbatar kin kamu gaba ɗaya kafin wasan ya fara.” Amma a fili ya nuna mata kulawa, ya ce: “Na fahimta. Amma kin san wani abu? Bana son ki yi tunani mai wahalar da ke. Duk wani abu da kike ji, ki faɗa mun kai tsaye. Ni ina tare da ke.” Ya miƙa mata hannu kamar yana son ya ɗaga ta daga kan daddumar. “Taso, ki je ki ɗan kwanta. Kin yi salla, kin yi tasbihi, yanzu lokaci ne na hutu kafin kowa a gidan ya farka...” Amal ta kalle shi na ɗan lokaci, zuciyarta tana tsalle, sannan ta miƙa hannu ta miƙe tare da shi. Har lokacin ta kasa fahimtar dalilin da yasa idan tana kusa da Maleekh take rasa ƙarfin taurin zuciyarta gaba ɗaya. Knocking mai ƙarfi aka fara yi a ƙofar part ɗin Maleekh, har Amal ta firgita tana kallon hanyar ƙofar. Maleekh ya fito daga bedroom ɗinsa cikin nutsuwa, ya nufi ƙofar falon ya buɗe, sai ga Islam tsaye fuskarta ɗauke da alamar damuwa. Islam ta rusuna da ladabi, tana cewa: “Yaya, Ammy na kiranka… kai da Amal… a babban falo.” Maleekh ya ɗan taƙaita fuska ya ce: “Lafiya kuwa da sassafen nan take ƙiran mu?…” Islam ta ɗan kame baki kafin ta ce cikin siririyar murya: “Ni ma ban san menene ba, amma naga kamar ranta a ɓace yake… bana wasa ba.” Maleekh ya yi ɗan murmushi yana girgiza kai: “Ita ai koda yaushe cikin ɓacin rai take. Kije kice muna zuwa.” Islam ta jinjina kai ta juya ta tafi. Da ƙyar Maleekh ya shawo kan Amal suka fito daga part ɗinsa. Kamar yadda ake tafiya zuwa kotu haka zuciyar Amal ke bugawa, ita kanta bata san me zata fuskanta ba...tsoron fuskantar su take, tana tunanin yau dole tabar gidan nan koda Maleekh baya so, domin a takure take, kuma sam bai dace ta zauna a gidansu ba kuma haka ma a ɗakin sa, hakan yasa take jin kunyar fuskantar mahaifiyarsa.. Da suka shigo babban falon gidan, suka tarar da Ammy zaune kan babban kujerar ta daidai tsakiyar falo, fuskarta ta cika da ɓacin rai. Farha tana gefenta cikin shegen kishi, yayin da Arfat ke jingine da kujera tana taɗa nails ɗinta, Islam kuma tana gefen su cikin natsuwa... Amal tana isa ta durƙusa ta ce "ina kwana Mama..." Ammy a fusace ta juyo tana mata wani irin kallo sannan ta ce "Da ban kwana ba zaki ganni ne? wato ke marar kunya iskancin nakin har ya kai ki kwana a ɗakin sa? idan aka ce miki gantalalliya yanzu sai kiji haushi ko? To bari kiji baza kizo ki koya wa ɗana iskanci ba, yarona baya neman mata, yau ne na farko da yarona ya kusanci mace, ɗana bai taɓa aikata zina ba sai yau ata sanadiyyar ki..." A ruɗe Amal ta ɗago tana kallonta ƙirjinta na wani irin bugawa da ƙarfi, bata san lokacin da ta furta "INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN..." Amal ta fashe da kuka tana faɗin "Wallahi ba haka bane, kar kuyi irin wannan mummunan zargi a kaina, wallahi babu abinda ya faru..." Ammy ta darara mata tsawa tare da faɗin "Yi mun shiru karuwar banza, gantalalliya marar tarbiyya, ƴar tasha, kenan haka iyayenki suka ɗora ki akan wannan turba? cewa ki rinƙa bin saurayi yanda yake har kina kwana a ɗakinsa? tirrr da halin ki, wannan sam rashin kunya ne da tarbiyya, alamar ke jahila ce, Allah ya kiyaye na bar ɗana ya Aure ki, ban san maza nawa kika rabar wa kanki ba, haka kawai bazaki zo ki dasa wa ɗana cutar da bazai taɓa warkewa ba sai dai mutuwa, ɗana namiji ɗaya a duniya, wannan ya nuna cewa haka iyayenki suke ba tarbiyya balle su baki..." Amal tana kuka ta ce. "Kiyi haƙuri Mama iyayena suna kabari, basa raye..." Ammy ta ce "Au saboda basa raye sai akace ki rinƙa jawo musu zagi a kabari? Haka ya kamata ki saka musu? mai makon ki zauna ki nutsu kiyita musu addu'a sai ki fake da bin maza? Ke wata iriyar shashasha ne?..." Amal ta ce "Mama ki yi h....." Ammy ta katseta da cewa. "Kada ki sake ƙirana da Mama, domin ban haifi ƴar tasha ba kuma insha Allahu bazan taɓa haifan gantalallu kamar ke ba..." Amal ta ce "Yau zan tafi..." Ammy ta ce "Kada ma ki tafi kiga rashin mutuncin da zan miki, wallahi sawa zanyi karnukan gidan nan suyi fata-fata da naman jikinki, ba yau ba yanzu ma zaki bar gidan nan dan kutumar ubanki..." Maleekh gaba ɗaya bai ji daɗin abinda Ammy tayi wa Amal ba... Ya kalli Ammy sannan ya ce "Mom laifi nane dana kawo ta..." Ammy ta wurga masa hararar da yasa ya dakata.. Sannan ta ce. "Ita kuma mahaukaciya ce da ta biyoka koh? ko kwaya ka bata ne ka kawo ta gidan nan ba tare da saninta ba?..." Maleekh bai ma zauna ba yana tsaye a tsakiyar falon, Amal kuwa tana durƙushe a gefe kusa da shi tana kuka.. Ammy ce ta kuma yin magana tana kallon Maleekh ta ce “Yanzu inaso ka zaɓa, Maleekh. Ni ko wannan yarinyar? Domin a yanzu nake so tabar gidan nan, ba zan lamunta a cigaba da zama a nan ba!” Kalmar ta ratsa falon gaba ɗaya, ta cika kunne da nauyin da ya tsaya cak. Amal sai da jikinta ya ɗauki rawa, zuciyarta ta shiga bugu kamar ana buga ganga. Hankalin Maleekh ya tashi matuƙa, duk da irin taurin zuciyar da yake da shi, wannan maganar Ammy ta bambanta da sauran kwanakin. Ya san halin mahaifiyarsa tana da ƙarfin mulki a gidan, kuma idan ta ɗauki mataki, lallai zai zame masa babban ƙalubale... Ya yi ƙoƙarin buɗe baki cikin ladabi, ya fara cewa: “Ammy ki kwantar da hankalinki, zan—” Ammy tayi saurin katse shi da tsawa, ta ɗaga hannu tana huci: “Ba lallashi nake so ba! Ina jiranka yanzu, ni da na haife ka, na kuma raine ka, inaso ka zaɓa ni… ko wannan matsiyaciyar yarinya da kuka haɗu a titi!” Kalmar “haɗuwar titi” ta buga zuciyar Amal da ƙarfi, ta sunkuyar da kai hawaye na zubo mata.... Maleekh ya tsu'ke baki ya tsaya kamar gunki, ya kasa amsawa nan take. Fushin Ammy ya ƙara zafi, idanunta har sun canza launi tsabar ɓacin rai... Maleekh ya jinjina kai cikin ladabi kamar ɗan da bai saba yin gardama da iyayensa ba, sai dai a zuciyarsa akwai tsananin ɓacin rai. Ya furta cikin sanyayyen murya.. "Shikenan zata tafi a yau, kar ki damu Mom… bana so na cigaba da ganin ɓacin ranki akaina. Idan hakan zai kawo miki nutsuwa, to na amince. Amma kiyi haƙuri, bana jin daɗin ganin ki cikin wannan yanayin." A wannan lokacin zuciyar Farha ta cika da farin ciki, har wani ƙaramin murmushi ta saki tana jin nasara. Sai ya juyo ya kalli Amal, idonsa ya cika da wani irin abu mai wuyar fassara, ƙauna da tsananin tausayinta a lokaci guda. Kamar yana so ya furta kalmomin da zuciyarsa ke ɓoyewa, amma sai ya jure ya maida numfashinsa. Ya kama hannunta a hankali, ya ɗago ta muryarsa na rawa ya furta. "Mu je, Amal. Mu shirya kayanki… bana son na ƙara ganin mahaifiyata cikin ƙunci saboda mu." Amal ta zuba masa ido, zuciyarta na tafasa da zafi. Duk da ba ta ce komai ba, hawaye suka cicciko a idanunta. Ta ji hannunsa yana da dumi a nata hannun, amma zuciyarta ta karye da tunanin cewa wannan kusancin da suka gina cikin dare ɗaya zai rushe haka kawai, ta wani ɓangare tana farin cikin barin ta gidan.. A haka suka fice daga babban falon, inda dukkan idanu suka bi bayansu kamar suna musu kallon karshe. Sun nufi part ɗin Maleekh, shiru ya lulluɓe su gaba ɗaya, babu wanda ya iya furta wata kalma. A can cikin zuciyarsa, Maleekh yana tunanin: "Taya zan sa6awa uwata akan matar da nake so na ɗauki fansa akan ta?..." Bayan sun shiga ɗakin, Amal a iya falo ta zauna akan sofas, yayinda shi kuma Maleekh ya wuce cikin bedroom domin haɗa mata kayan da yayi mata siyayya, ya jera kayan a cikin akwatin da ya siya mata.. Amal tana sharar hawaye tana jiran fitowarsa, sai idonta ya sauƙa akan wani glass photo a jikin bango, an kewaye shi da kyawawan flowers. Ta tsaya cak, zuciyarta ta yi wani irin tsalle kamar an danna mata wuta. hoton da bata lura dashi ba sai yanzu.. Kirjinta ne ya buga lokaci guda ganin hoton yara biyu mace da namiji sanye da kayan makaranta.. Amma namijin kana ganinsa kasan ya girmi macen sosai sannan ya fita da class sosai.. Amal a ruɗe ta nufi wurin idonta akai, ganin hotonta tana ƙarama da abokinta wanda a halin yanzu bata san a yanda yake ba, domin tin suna yara suka rabu... A hankali ta furta sunan yaron dake jikin hoton "My Leekh💝.. Maleekh wanda fitowarsa kenam daga bedroom yana jan akwatin ta jin kamar ta ambaci sunan da babu wanda yake ƙiran sa da shi sai fiance ɗin ta... Da sauri ya ɗago, zuciyarsa ta tsaya cak. Kalmar da ya ji daga bakinta “My Leekh” ita ce kalmar da tin yana yaro babu wanda ya sake ƙiransa da ita sai abokiyar ƙuruciyarsa... Ya juyo a rikice yana kallonta, idonsa ya sauya launi da mamaki. Da sauri ya furta “Me kika ce?…” Amal ta yi saurin gyara kanta, tana son ɓoye damuwarta, tana nuna kamar hoton kawai ya burge ta ne ta ce “Na ce naga hoton nan ya burge ni… su waye waɗannan yara?” Ta nuna da yatsanta cikin rawar jiki, idonta na kan hoton amma zuciyarta na dukan tara-tara. Maleekh ya tsaya kallon hoton na wasu daƙiƙu, sannan ya murmusa da wani irin murmushin da ke ɗauke da zafi da sirri. Ya ce “Wannan ita ce fiancée ɗina… tun muna yara muka rabu. Ban san a ina zan sake samunta ba. Na sha nemanta, domin ita ce ƙaunata ta farko, amma har yanzu ina riƙe da wannan hoton a zuciya.” Sai kuma yayi shiru, ya ɗauki numfashi mai nauyi yana dubanta da ido kai tsaye, yana ji zuciyarsa na son faɗa mata gaskiya amma kalmomi sun makale... Dakatawa yayi saboda kada taji haushi akan ya bayyana irin ƙaunar da yake yiwa fiancée ɗinsa... Amal lumshe idonta tayi zuciyarta na bugawa, ganin Maleekh yana ƙoƙarin sanar mata cewa shine 'Leekh ɗinta..." Sai ta ɗago idanunta a hankali, ta tsaya kallon shi, zuciyarta na cewa: “Shin zan iya furta masa cewa nine Fiancée ɗinka?…” Muryar Maleekh ne ya katse ta da cewa. "Yanzu zamu iya tafiya, amma ki sani… bazan taɓa barin ki ba, ko da duniyar nan ta ɗauka cewa mun rabu. Ki adana wannan magana a zuciyarki." Amal ta kasa cewa komai, zuciyarta na bugawa da ƙarfi. Sai kawai ta ɗan girgiza kai, idonta cike da hawayen farin ciki da tsoro lokaci guda. Ya kamo hannunta, suka nufi falo tare. Bayan sun shiga babban falo, sun tarar da su Ammy, Farha, Arfat da Islam. Wani murmushi mai cike da fifiko da kishi ya bayyana a fuskar Farha.. Farha ta haɗe fuska, tana tsaki sannan ta ce.. " Tafiya zakiyi Amal?, to ai kuwa gwara ki tafi domin nan ba wurinki bane. Allah ya raka taki gona, sannan Allah ya baki miji ɗan tasha kamar ke, kuyi rayuwar ƙasƙanci irin na ƴan tasha, ya kuma baku ƴaƴa masu irin tarbiyyarku na ƴan tasha…" Amal ta juyo tana kallon ta sannan tayi murmushi tare da mayar mata da amsar cewa.. "Amin ya Allah tinda gashi nan a gabana..." Tayi maganar tana nuna Maleekh.. Farha ta wurga mata harara tare da haɗiye maganarta..ganin zata raina mata hankali... Ammy idonta akan Maleekh cikin isa da gadara ta ce "Na gode da ka fahimce ni, Maleekh. Wannan ce dama ɗaya da zan tabbatar da kai ɗana ne nagari. Amal… Allah ya raka ki lafiya." Amal ta sunkuyar da kai cikin kunya, zuciyarta na bugawa domin Ammy na mata gwarjini, amma sai taji hannun Maleekh ya ƙara matse nata da ƙarfi... Har zasu juya sai ga Arfar ta wurgo mata jakar kayanta da tazo dashi, tana faɗin "Tsaya ki ɗauki tsiyarki nan, shin awa zaki bar wannan kazantar kayan ki?..." Amal sunkuyawa tayi ta ɗauki jakar.. Maleekh kuwa nuni yayi wa Arfat cewa "Zai dawo zata shiga hannunsa..." Arfat kukan shagwaɓa ta fara yi tana kallon Ammy, da sauri taje ta faɗa jikin Ammy tana shishshige mata kamar zata koma ciki, dake ita ce ƙarama..kuma ƴar auta a wurin Ammy, domin a wurin Abbah akwai ƙaramar Arfat ƙanwar A'isha... Ba tare da wani ƙarin magana ba, suka fita. Maleekh ya ja Amal da kansa har zuwa mota. Ya buɗe mata ƙofa cikin kulawa, ta shiga, sannan shima ya zagaya ya zauna a kujerar driver. A nan security ya buɗe musu gate, suka fita a ɗari daga gidan... Sunyi tafiya sosai kafin su fita daga unguwar Maitama.. Suna tafiya akan titunan Abuja cikin nutsuwa. Dukansu babu wanda ya ce komai, amma zuciyoyinsu suna ta magana, kowannensu yana ji kamar ana rura musu wutar soyayya.. Doguwar tafiya suka yi, sai dai ba su fita daga Abuja ba. Amal na sa ran tashar mota zai nufa, domin ta koma Kaduna. Amma sai taga ya tsaya a bakin wani tsararren gida mai katanga babba, cike da tsaro, ya fara hon da mota. Bai ɗauki lokaci ba maigadi ya buɗe musu gate. Maleekh ya shiga ciki da mota cikin nutsuwa.. Amal ta zaro ido, zuciyarta ta tsaya cak. Wannan gida ya bambanta da duk wanda ta taɓa gani. Tsari ne na alfarma, gininsa na zamani, duk an zagaye gidan da tsararrun tiles, da manyan trees masu kyau da burgewa a cikin harabar. Tana dafe da kirji, ta juya tana kallonsa da mamaki: Cikin rawar murya ta ce "Nan ɗin wani gida ne? Nifa so nake na koma Kaduna… nabar Inna ita kaɗai. Ka kuma ce za ka kai ni tashar mota…" Maleekh bai ce mata komai ba, sai ya kashe motar, ya fito. Ya zagaya ya buɗe mata ƙofar jikinsa cike da ƙarfi da izza, sannan ya riƙe hannunta. Tana tsaye a inda take kamar an dasa ta, ya ja ta cikin ƙarfin ikon da yake da shi a kanta. Maleekh da muryarsa da na cika da iko ya ce "Ki tsayar da tambayoyin ki..." Ya shigar da ita ciki. Gidan ya cika da tsari irin na masu kuɗi. Dogayen glass windows suna kyalli da hasken, lambu mai kyau ya zagaye shi, flowers masu launi suna ta kaɗawa da iska, sai kamshin fresh roses da ya gauraye da iska. Amal ta tsaya tana kallon kowane ɓangare, zuciyarta na wani irin bugawa... Da haka ya shigar da ita ciki, wani tsararren falo ne mai girma, ya tsaru sosai.. Maleekh ne ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun falon, Amal cikin ɓacin rai take kallon Maleekh kamar zata yi kuka ta ce "Wai me kake shirin aikata wa haka? na ce ina buƙatar komawa Kaduna, shine ka kawo ni wannan gidan? me kake nufi dani Maleekh? kana so aita zargi nane? baka ji abinda mahaifiyarka take faɗi akaina ba?.." Tana cikin wannan masifar ne sai ga sautin takun ƙafafu daga sama. Amal ta ɗago ido tana kallon stairs ɗin dake zagaye da golden railing. A hankali wata dattijuwa ta bayyana daga upstairs, Tana sanye da dankararren less mai launin shuɗi da silver, an yi mata ɗaurin ɗan kwali mai kyau wanda ya ƙara mata ƙima, duk da tsufarta. Amal ta tsaya cak. Zuciyarta ta buga. Ido ya sauƙa kan fuskarta da ta shafe shekaru tana gani, amma a yanzu ta canza ganinta a irin wannan gidan... Cikin rawar murya ta furta: "Inna?... Innaaaaaa!" Ta ruga da gudu kamar yarinya, ta rungumi Inna gam a jikinta, hawayenta na zuba kamar fanfo... Amal cike da mamaki da kuka take faɗin "Inna! Taya kika zo nan Abuja? me yasa kika baro Kaduna?..." Inna ta shafa kanta da hannunta mai sanyi. Ta yi murmushi, sai kawai ta ce: "Ki tambayi Maliku mana..." Amal ta janye jikinta kaɗan tana kallon Inna cikin mamaki. Inna ta ci gaba da magana cikin natsuwa: "Kin dai san tsufa baya barin mutum yayi surutu sosai. Amma ki sani wannan Maliku ɗin mutumin kirki ne. Tunda kika tafi Abuja, yasa can Kaduna ana kula dani: abinci mai kyau, ruwan sha mai kyau, sutura masu tsada. Jiya Jiya yasa aka kawo ni nan Abuja aka ajiye ni a cikin wannan gida. Yace gidan nan na mu ne…" Amal ta juya a ruɗe tana kallon Maleekh da hawaye a idonta... Maleekh ya miƙe daga kujerar da yake zaune, ya matso kusa da ita cikin natsuwa. Ya ce "Amal… ba wai na ajiye ki a gidan mu ba ne kawai. Na yi haka ne saboda gidan da nake gina muku bai kammalu ba sai jiya. Aka kammala shi. Shi yasa na sa aka kawo Inna nan gidan domin nan gidan sadaukarwa ne. Hallak mallak naku ne. Ko da a misali mun rabu, kada ki taɓa tunanin za ki mayar mun da gidan nan." Ya saka hannu cikin aljihunsa, ya fitar da wasu takardu. Ya miƙa mata da hannunsa cikin kulawa. Sannan ya ci gaba da faɗin "Ga takardun gidan. An rubuta shi da sunanki, Amal Abdulsamaad." Amal kamar zata haɗiyi ranta tsabar farin ciki, haka take tsalle tana farin ciki haɗe da kukan farin ciki, kamar zata rungume shi domin sauran kaɗan ta rungume shi sai kawo ta juya ta sake rungumar Inna... Tana faɗin "Ya Allah! Na gode, na gode..! Inna! Inna! Wannan duk ya faru saboda soyayya ne?!..." Inna ta shafa kanta tana murmushi. A wannan lokacin suka ji motsin mutane. Sai ga wasu dattijan mata biyu sun bayyana daga cikin corridor. Suna sanye da uniform masu tsabta, kowannensu da nutsuwa a fuska. Maleekh ya nuna su da hannu. Yana faɗin "Waɗannan su ne masu aikin gidan gaba ɗaya. Su zasu kasance tare da ku, ki ɗauke su kamar uwaye." Amal ta kalle su cikin mamaki da farin ciki. Idonta ya sake cicciko da hawaye. A zuciyarta ta ce: "Wannan Maleekh… ni kaina ban san me zan ce game dashi ba. Allah ya sani…" Da sallama da girmamawa, dattijan mata biyun masu aikin gidan suka ƙaraso kusa da Amal. Dukansu suna ɗauke da murmushi irin na masu hidima masu gaskiya. Ɗaya daga cikinsu mai ƙiba kaɗan ta yi gaisuwa cikin ladabi: "Sannu da zuwa, Hajiya Amal. Munji daɗin zuwan ki. Daga yau za ki ɗauke mu tamkar ‘yan uwa. Ba aikin gidan kawai muke ba, muna nan ne don mu kula da ku da gaskiya da zuciya ɗaya." Ɗayar itama ta ɗora da cewa: "Ni sunana Goggo Rabi, ita kuwa wannan ita ce Goggo Hauwa. Mun daɗe muna hidima a gidajen manyan masu kuɗi a Abuja, amma yau wannan shi ne karon farko da muke jin daɗin zama gidan da ya dace sosai. Zamu kula da ke da Inna kamar iyayen mu. Ki kwantar da hankalinki." Amal ta kasa boye farin cikinta. hawayenta na zuba cikin murmushi. Amal ta ce "Na gode sosai, Allah ya saka muku da alheri. Wallahi ban san yaya zan nuna godiyata ba… Amma zan ɗauke ku kamar iyaye na..." Maleekh da ya tsaya gefe yana kallon ikon Allah, murmushi kawai ya yi. Bai ce komai ba sai ya ƙara jin daɗin ganin Amal cikin farin ciki. Bayan sun zauna na ɗan wani lokaci, Amal ta fara nuna sha’awar ta ga dukkan tsararren gidan. Maleekh ya lura da hakan, ya miƙa hannu yana kallonta cikin kulawa: "Zo, Amal. Bari na nuna miki gidan ki daga yau." Ta yi dariya mai cike da kunya, ta miƙe ta kama hannunsa cikin nutsuwa. Suka fara zagaye cikin gidan. → Babban Falon Gida: Babban falo ne mai faɗi da tsayi. An ƙawata shi da luxury Italian sofas, an jera su a geometric design. Babban chandelier mai sheƙi yana rataye a rufin sama mai tsawo, yana haskawa tamkar rana ta sauƙo. TV mai faɗin bango yana manne a gaban su tare da sound system mai cike da ƙarfi. Amal ta tsaya tana girgiza kai cikin mamaki. Amal cikin zuciyarta ta ce "Wannan gidan da kaɗan gidan su Maleekh ya fishi tsaruwa..." → Kitchen: Kitchen ɗin kuma tsararre ne irin na zamani. Granite countertops, microwave, oven, coffee machine da duk wasu kayan girki na zamani suna cikin tsafta da tsari. Goggo Hauwa ta nuna mata kowanne bangare, tana cewa: “Nan ne gidan ki, duk abinda kike buƙata yana nan.” → Upstairs: Suka haura bene, Amal tana jin ƙamshin flowers da aka tanadar a cikin hallway. A gefen hagu akwai guest rooms guda uku, kowanne da toilet. A dama kuwa akwai library mai ɗauke da littattafai daga turai har da na larabci, sai ɗakin hutawa da ya sha kayan alatu.. → Bedroom ɗinta da aka tanadar. A ƙarshe suka isa wani ɗaki mai kama da ɗakin sarauta. Bed ɗin king-size ne, an yi masa canopy da curtains masu siliki. Ɗakin ya sha kyawawan paintings, sai wardrobe na glass da aka shirya mata kayan da aka siya daga supermarket... Amal ta tsaya tana rufe da fuska cikin farin ciki, hawaye na bin kuncinta cikin murmushi. Ta ce "Wannan duk saboda ni ne, ya Allah!..." Inna ta shigo daga baya tana dariya, ta ce: "Ki gode wa Allah, ki gode wa Maliku. Wannan duk bai yi miki komai ba idan kika cigaba da kasancewa mai kirki da biyayya." Amal ta juya tana kallon Maleekh. Idonsu suka haɗu. Numfashinta ya tsaya cak. Taji kamar ta ce masa: “Kai ne Leekh ɗina.” Amma ta daure, ta janye idonta cikin kunya. Maleekh kuwa ya juya da murmushi mai cike da ɓoyayyen nufi. A zuciyarsa ya ce: "Kada ki manta, Amal… duk wannan kyautar, akwai fansa a bayan sa.".... NEXT NEXT NEXT... asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 25 to 26 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Bayan ya tabbatar da cewa Amal da Inna sun zauna lafiya a cikin sabon gidan da ya mallaka musu, Maleekh ya juya ya koma gida. Zuciyar Ammy har yanzu cike take da nauyin bacin rai. Da ya shiga falo ya tarar da ita zaune akan sofas tana fuskantar plasman. Sai da ya zauna a gefenta ya kama hannunta cikin ladabi sannan ya furta: “Mom, ki yafe mun. Na ga halin da kika shiga saboda Amal, amma na tabbatar da cewa daga yau ba zan sake sa ki cikin kunci saboda ita ba..” Ammy ta ɗago ido ta kalle shi, tana nazarin maganarsa. “Kana nufin ba za ka sake ɗora ta a kan zuciyarka ba, Maleekh?” Ya jinjina kai cikin nutsuwa, muryarsa na fita da yanayin rarrashi. “Ina bada mahimmanci a soyayyarki Mom, wannan karon na yi abin da ya dace. Amma ki fahimce ni, ba zan iya rabuwa da ita ba. Ko da me zai faru, zuciyata ta amince da ita.” Shiru ya ratsa tsakanin su. A zuciyar Ammy, akwai sassaucin rai, amma tunanin alƙawarin da tayi wa Farha na Aura mata shi sun riga sun yi katutu. Duk da haka ta ce da ƙasa-ƙasa: “To shikenan, Allah Ya kyauta. Amma ka sani, idan ta ci amanarka… ba zan taɓa yafewa ba, tin da ka nuna ban isa na rabaka da Amal ba amma inaso ka sani cewa bazaka ƙi Auran Farha ba..." Maleekh ba yanda ya iya haka ya tashi ya nufi part ɗinsa... 🌹 Tun daga wannan rana, soyayya mai zafi ta shiga tsakanin Amal da Maleekh. Amal ta fara samun kwanciyar hankali, zuciyarta ta ji sabuwar rayuwa ta buɗe gare ta. Idan Maleekh bai zo ba, to tabbas za su yi waya har zuwa ƙarfe sha biyu na dare... Sai dai… duk da wannan kulawa da gaskiyar soyayya da yake nuna mata, a zuciyar Maleekh akwai wani abu da ba ya iya fadar wa kowa. Duk lokacin da ya rungumu Amal cikin ƙauna, sai wani muryar zuciya ta yi masa ƙira: “Ka tuna, wannan soyayya ba ta kawar da manufarka ba. Fansar ka har yanzu tana nan.”.. Bayan cika wata guda da zamansu a Abuja, soyayya ta fara ƙara ƙarfi tsakanin Amal da Maleekh. Duk da cewa akwai sirrin gida da bai bayyana ba, har yanzu babu wanda yasan Maleekh ya siya wa Amal gida... A yau kuwa, Maleekh yana cikin ofishinsa, yana jingina da kujerar executive, yana kallon files a gaban laptop ɗinsa. Da Bluetooth a kunnensa yana waya da Amal, muryarsa cike da kasala ya ce: “Amal, yau kam na wuni ofishin nan. Tun safe har yanzu ban motsa ba. Kuma fa yunwa kamar zata kashe ni.” Amal ta yi dariya a ɗayan ɓangaren wayar, ta furta cikin shagwaɓar soyayya: “Tin da kai baka iya jiran girkin wata mace sai nawa. To ka kwantar da hankalinka, bari na haɗa maka delicious food da hannuna, zan kawo maka yanzu.” Maleekh ya rufe ido da murmushi, zuciyarsa na bugawa da farin ciki. Daman haka yake son ji domin yana son cin girkin Amal mai daɗin gaske... “Yawwa tawan wallahi wannan shi ne burina. Ina jiran ki.” Wayar ta yanke, shi kuma ya cigaba da kallon agogo, yana jiran zuwanta kamar wani yaro mai jiran a sauƙe abinci... Bayan lokaci mai tsawo, sai yaji knocking a ƙofar office ɗin. Da kasala ya ce: “Yes, come in.” Ƙofar ta buɗe a hankali, sai ga Farha ta shigo cikin shigar riga da wandon jeans na kanty, ta sha kwalliya tana ɗauke da basket ɗin kulolin abinci. Ta yi kyau matuƙa, sai ƙamshin turare take... Maleekh da ganinta sai ya miƙe tsaye, fuskarsa cike da mamaki da rashin jin daɗi. “Farha? Me ya kawo ki nan?” Farha ta ɗan bubbuga ƙafafunta, kamar wata yarinya mai jin daɗin shagwaɓa, sannan ta ce: “Kai Ya Maleekh, kenam ba zan iya zuwa inda kake ba? Naga tun safe baka dawo gida ba, na ƙira PA ɗinka yace har yanzu kana office. Na san yunwa kake ji, shiyasa na haɗo maka girki na kawo.” Ta miƙa basket ɗin tana murmushi. Maleekh ya kawar da fuska gefe, zuciyarsa na tafarfasa ya ce “Farha, ki koma da abincinki. Ni dai na ƙoshi. Kuma ban ce ki kawo min girki ba. Wane irin abu ne haka?” Farha ta matso kusa, idonta cike da hawaye na shagwaɓa ta ce “Haba Ya Maleekh, kasan ina sonka sosai. Ba zan bari ka zauna da yunwa ba.” Maleekh ya dafe kansa da ɓacin rai ya ce “Na ce ki koma da abincin nan! Ko yau na saba kaiwa wannan lokacin ban koma gida ba? Don Allah Farha ki daina tada mun hankali. Please join yourself.” Ya ƙarasa yana ɗaga muryarsa... Kafin rigimar ta lafa, sai suka ji ƙofa ta turo da sauri. Security ɗin ofishin ya shigo cikin ladabi ya ce “Sir, akwai baƙuwa a waje. Ta ce tana da appointment da kai.” Da zarar Maleekh ya ji haka, zuciyarsa ta yi tsalle, ya san Amal ce. Ya ɗaga hannu yana nuna Farha da basket ɗinta. “Daga yau ku daina bari kowa ya shigo mun office haka ba tare da izini ba. Ko wannan (ya nuna Farha), ko kuma waccan. Idan na ce ku bari ne za ku bari. Otherwise, kar ku sake.” Security ya gyaɗa kai cikin girmamawa, sannan ya juya. Sai ga Amal ta bayyana a ƙofar ofishin, hannunta ɗauke da kulolin abinci, da murmushi a fuskarta. “Assalamu alaikum.” Cikin nutsuwa ta shigo, amma tana ɗaga kai ta kalli Farha tsaye, tana riƙe da basket ɗinta. Amal ta dakata cak, zuciyarta ta ɗan buga, tana kallon Farha da mamaki da tsoro a lokaci guda. Farha ta haɗiye miyau, ta furta cikin ƙiyayya: “Kai kai kai! Ashe wannan yarinyar bata koma inda ta fito ba? Wannan matsiyaciyar ƴar gari, ubanta me take a Abuja? Kenan Ya Maleekh har gida ka kama mata a nan Abuja?” Amal ta runtse ido da ƙarfi, kafin ta buɗe baki, Maleekh ya furta. “Farha, wannan bai shafe ki ba. Don Allah ki fita daga ofishina yanzu.” Ya nufi Amal da murmushi, yana karɓar basket ɗin hannunta. “You’re welcome abar ƙauna. Fatan kin haɗa min wannan girkin da ɗanɗanon ki.” Amal ta yi murmushi a hankali, muryarta cike da soyayya: “Na kawo maka irin wanda kafi so. Fatan zaka ci da ɗanɗano.” Farha ta ƙara haɗiye zuciya, idonta cike da ƙiyayya. Amal kuma ta juya tana kallonta da tsananin kishi, ganin yanda Farha take ta harararta yasa itama ta mayar mata da martanin hararar sannan ta ce “Ki sani, yanzu ba a gidan ku nake zaune ba. Ki kama kanki, domin Amal bata rasa abin faɗi. Tambayi kowa ki ji wacece Amal Voice.” Farha ta yi ƙoƙarin danne fushinta, a hargitse tazo wuce ta bugi kafaɗar Amal da ƙarfin tsiya sannan ta buɗe ƙofar da ƙarfi ta fice. Ƙamshin turarenta ya bi bayanta.. Amal ta juya tana kallon Maleekh, da murmushi a fuskarta, duk da cewa zuciyarta tana tsalle-tsalle da kishi. Shi kuma ya tsaya yana kallonta, zuciyarsa ta ji daɗin ganin yadda ta tsaya kai tsaye ta kare kanta a gaban Farha. Bayan Farha ta fice daga ofishin cikin ƙiyayya, wurin ya dawo da nutsuwa. Maleekh ya saki ajiyar zuciya, sannan ya ɗauki basket ɗin abincin da Amal ta kawo, yana murmushi yana kallonta ya ce “Na saba da irin fitinun Farha. Amma yau na ji daɗin yadda kika tsaya ki ka bata amsa. Amal, kin burge ni sosai.” Amal ta lumshe ido, fuskarta cike da jin kunya da farin ciki ta ce. “Ni dai bana son ta ci gaba da shiga tsakanina da kai. Na san kai mutum ne da kowa ke so, amma ni bazan yarda a raina ni ba..” Maleekh ya ɗan matsa kusa da ita, yana kallon idonta kai tsaye. Hannunsa yasa yana buɗe kulolin abinci ɗaya bayan ɗaya. Ƙamshin miyan taushe ya cika ɗakin... Maleekh ya ce “Masha Allah… girkin nan da kanki kika haɗa shi? Na rantse, wannan shi ne mafi daɗin gift da aka taɓa kawo mun.” Ya ɗauki spoon, ya ɗan ɗibo tuwo da miyar taushe mai kyau, ya miƙa mata kai tsaye yana faɗin “Come on, open your mouth. I want to be the first to taste this with you.” Amal ta yi murmushi tana girgiza kai. Ta ce “A’a, kai dai ka fara. Ni ba zan iya cin abinci haka a ofishinka ba, idan wani ya shigo fa?” Maleekh ya yi dariya, yana ɗan danna spoon ɗin a gaban bakinta. Yana faɗin “Ba wanda zai shigo. Kuma idan suka shigo, sai su ga yadda masoyiyata ta fi kowacce mace a duniya.” Cikin jin kunya da sanyi, Amal ta buɗe baki a hankali, ya saka mata spoon ɗin. Yana kallonta sosai har sai da ta haɗiye. Lumshe ido tayi tana faɗin “Hmmm… ai na ce maka zaka ji daɗin sa. Amma ya Maleekh, ka dena irin wannan magana da kake yi, zuciyata tana tsalle kamar zata fito daga kirjina.” Maleekh ya yi dariya cikin tsantsar shauƙi, sannan shi ma ya ɗauki spoon ya ci. Ya lumshe ido yana jin ɗanɗanon abincin. “Wallahi Amal, da za a bani damar zaɓen abincin duniya, sai dai na zaɓi wanda kika girka. This is heavenly.” Ya furta yana santy.. Amal ta ɗan sunkuyar da kanta, tana murmushi. Ta ji wani irin ƙarfi a zuciyarta, tana jin soyayyar Maleekh ta wuce dukkan tunaninta. Suka ci gaba da cin abincin tare. Wani lokaci shi ke feeding ɗinta, wani lokaci kuma ita ke ɗaukar spoon ta miƙa masa. Suna hira mai daɗi da tsokanan junansu... A ƙarshe, bayan sun gama, Maleekh ya jingina da kujera yana kallonta. Ya furta “Amal, kin san me yasa nake so in kasance kusa da ke kullum? Domin idan na kasance tare da ke, komai na duniya ya zama kamar baya da muhimmanci. Ni da ke kaɗai nake gani.” Idon Amal ya kaɗa da hawaye, ta ji kamar ta rungume shi a nan take, amma ta danne kanta. Ta ce cikin murya mai sanyi: “Ni ma haka nake ji. Ina jin kamar duk duniya babu abinda nake so face kasancewa tare da kai.” Shiru ya ratsa tsakaninsu, sai kukan zuciya da bugun numfashi. Amma dukansu biyu sun san cewa soyayyar da ke tsakaninsu ta fara shiga wani sabon matsayi da ba zata taɓa komawa baya ba… Cikin wannan lokaci zuciyar Maleekh ta fara sauya salo. Duk da akwai wani sirri a boye a ƙirjinsa, sai dai soyayya ta fara hura wutar da bai taɓa zato ba. Ya fahimci cewa kasancewar Amal kusa da shi na sa zuciyarsa ta huce, duk da cewa har yanzu yana da wani ƙuduri na ɓoye a cikin ransa. Amal kuwa ta fara jin wani irin nishaɗi da kwanciyar hankali fiye da da. A lokuta da bai samu ya zo gidan nata ba, sai wayar su ta ɗauki dare suna hira da dariya kamar sabbin masoya da suka yi asarar shekaru da dama ba tare da sanin juna ba... Da safe idan Amal ta farka, zuciyarta kan cika da farin ciki, ta ji kamar komai na duniyar ya tsaya cak domin jin muryar Maleekh. Haka shi ma idan ya shige cikin aiki, bai da sukuni har sai ya ji labarinta. Wannan kusanci ya zama tamkar sabon babi a rayuwarsu. Amma akwai wani zazzafan ƙuduri da Maleekh ke ɓoyewa, wanda shi kaɗai ya san yadda zai bayyana nan gaba. Farha tana komawa gida ta fara ihu, tayi wurgi da basket ɗin kulolin abincin da ta kawo, suka watse a ƙasa. Ammy ce ta fito da gaggawa tana tambayarta cikin tashin hankali: “Farha meya faru haka? Me yasa kike ihu kamar wacce aka ci zarafi?” Farha tana kuka tana sheshsheka tace: “Ya Maleekh bai yi mun adalci ba Ammy, ya fifita wata a kaina? To wallahi bazan yadda ba!” Ammy ta ɗan runtsa idanu kafin tace: “Wace yarinya ya fifita a kanki? Ki faɗa min gaskiya.” Farha tana huci tana share hawaye ta ce “Wacece inba wancan matsiyaciya ba?” Ammy ta ɗaga gira a rikice ta ce “Wa kuma?!” Farha ta tura baki cikin jin haushi tace: “Amal ƴar jarida. Ya nema mata gida anan Abuja Ammy! Kuma kullum take kai masa abinci office…” Ammy ta dafa ƙirjinta da hannu biyu, fuskarta ta nuna firgici, ta furta da ƙarfi: “Meeeeee? Ya nema mata gida? Shi Maleekh ɗin? Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Abun da zai yi mun kenan? Yau sai ya dawo ya same ni, sai nayi maganinsa!” A wancan ɓangaren kuma, Maleekh bayan sun gama lunch da Amal, sun sha soyayyarsu cikin annashuwa, sai suka fita tare. Shi ya kaita har gida da motarsa. Sai da ya shiga ya gaishe da Inna cikin ladabi kafin ya juya gida da daddare, misalin ƙarfe 8 na dare lokacin da bai saba komawa ba... A falo kuwa Ammy ce take zaman jiran dawowarsa, zuciyarta da ƙuna.. Da ya shigo da motarsa ya ajiye a wurin parking, sannan ya nufi compound ɗin gidan, ya shiga falo da sallama yana riƙe da jakar office ɗinsa... Ammy tana jin sallamar tasa, tayi saurin miƙewa, ta tsaya cak tana kallonsa kafin ta fara masifa: “Wato Maleekh ban isa na faɗa maka ba kenan? Ashe duk ladabin da kake nuna min ƙarya ne? Meye ya zaunar da Amal a garin nan? Har tana kai maka abinci? Shikenan ta zamo dadironka?” Maleekh ya ja numfashi, daman yasan dole Farha zata sanar mata. Ya dubeta a hankali yace: “Mom, ba zaman dadiro nake da ita ba. Kin fi kowa sanin ɗanki, ba manemin mata bane. Kar ki ɗora min wannan shaidar, dan Allah.” Ammy ta girgiza kai cikin tsawa: “Oh to me yasa ka nema mata gida anan Abuja?!” Maleekh ya sauƙe numfashi mai nauyi sannan yace: “Na siya musu gida ne ita da kakarta.” A ruɗe Ammy ta ɗaga murya: “Ka siya musu gida? Maleekh kasan me kake faɗi kuwa? Anan Abuja har kayi kyautar gida?” Maleekh ya kalli gefen bango kafin ya mayar da kallonshi gareta: “To Ammy, meye amfanin dukiyar da bazaka kyautar da ita ba, sannan bazaka sadakar da ita ba? Amal marainiya ce, bata da iyaye. Daga ita sai kakarta. Gidan da suke ciki a Kaduna gidan haya ne. Please Mom, ki bar ni na taimaki waɗanda basu da ƙarfi.” Ammy ta tafa hannu cikin huci: “To idan kana son kyautar gida, sai a nan Abuja? Meyasa bazata cigaba da zama a Kaduna ba? Ko dole sai ita zaka yiwa kyautar?” Maleekh ya girgiza kai da sanyin murya ya ce “Ina kyautata ga duk wanda na ga dama Mom. Kafin Amal, nayi kyautar dukiya fiye da adadi. Ba abinda ya ragu a hannuna. Allah bai bani arziki don in sa a gaba naita kallo ba. Ki yi haƙuri, biyayya zan ci gaba da yi miki a matsayin mahaifiyata. Amma kada ki shiga hurumin abinda zan kyautar da shi cikin dukiyata. Ni ba bin mata nake da dukiyata ba. Ba shaye-shaye nake ba. Ba gidan club nake zuwa ba. Ba safarar miyagun kwayoyi nake yi ba. Shiyasa kullum Allah bai hanani ba. Kuma dukiyata kullum ƙaruwa suke, ba raguwa ba.” Sai ya ɗan ɗaga murya cikin ƙarfin hali: “Zan yi kyauta, zan yi sadaka, zan yi zakka. Duk garin da na zagaya naga basuda masallaci zan gina musu. Zan tono rijiya ko in saka fanfoo. Lokacin layya waɗanda basu da hali zan raba musu. Duk ba saboda riya ba. Kuma ba kowa yasan irin abubuwan da nake yi ba, ko ke baki sani ba sai yanzu da nake gaya miki. Gida kuwa, ba Amal kaɗai ba, duk wanda nayi niyyar taimaka masa da gida zan yi. Ko a England ne, indai inada hali zan yi. Saboda haka ku gani kawai ku yi shiru.” Ammy tana huci kamar zata yi kuka tace: “Uhmmm! Amma Amal dai saboda soyayya kayi mata.” Maleekh ya murmusa cikin ƙarfin hali: “Kusan haka. Abinda nake so dole na kyautata masa. And so what idan ina sonta? Ra’ayina ne. Tinda ba wanda zai zauna mun da ita. Kuma duk munafikin da yazo ya sanar miki wallahi sai nayi maganinsa.” Ammy ta yi tsaki sannan ta miƙa masa hannu: “Bani wayarka nan.” Ba tare da musu ba, Maleekh ya ciro wayarsa ya bata. Ammy ta kalle shi sannan tace: “Wannan wayar nayi sizing ɗinta!” Maleekh ya yi dariya kawai, ya ratsa ta gefenta, ya wuce sama kai tsaye zuwa part ɗinsa. Ammy tana tsaye da wayar a hannunta cikin huci. Sai ga Farha ta shigo tana laɓe, ta tsaya ta ji duk hirar su. Da ta ƙaraso kusa da Ammy tace cikin lallashi: “Ammy, don Allah ki bani wayar. Nasan Amal zata ƙira shi. Ina so in caccaki durun uwarta a daren nan.” Ammy ta yi murmushin mugunta, ta miƙa mata wayar sannan ta wuce part ɗinta. Farha kuwa ta riƙe wayar tana murna, ta fice zuwa ɗakinta. Ta zauna tana jiran ƙira daga Amal, zuciyarta cike da shirin tada rikici... Misalin ƙarfe goma da rabi na dare, Amal ta gama shiryawa cikin nutsuwa. Ta ɗauki wayarta, zuciyarta cike da ƙaunar Maleekh, ta ƙira lambar shi domin ta yi masa magana kafin ta kwanta. A ɓangaren Maleekh kuwa, wayar tana hannun Farha da ke zaune a ɗakinta tana jiran wannan lokacin. Da taga sunan Amaleekh a jikin screen ɗin, ta danne dariya, sai ta ɗaga da sauri, ta kai kunne tana shirin caccakar ta, ta ce “Hello matsiyaciya, wani irin rashin mutunci ne zaki ƙira wayar mijin Aure na. Ke waca iriyar marar zuciya ce?” Farha ta yi magana da kakkausar murya. Amal ta yi shiru na ƴan daƙiƙu, ta ɗan yi murmushi sannan ta ce cikin lafazi mai tsauri... “Ke yarinya, kina sauraron kanki kuwa? Kin san da wa kike magana? Ni ce Amal Voice, wacce idan ta yi magana ana sauraro a jihohi da dama, ba wai don ina son a ji ni ba, a’a, don kalamaina suna da nauyi.” Farha ta yi tsaki sannan ta ce “Kina yi min ihu da wannan sunan banza naki? To wallahi ba zan taɓa barinki ba. Ni ce matar Maleekh, na fi ki komai, daga asali har ƙarshe.” Amal ta yi dariya mai sauti, sannan ta mayar mata da martani . “Farha, ki ji tsoron Allah. Soyayya ba da ƙarfi ake jantaba. Ni da Maleekh mutu-karaba ne, babu wanda zai iya tsayawa tsakanin mu. Ke ana soyayya dole ne? yace baya so, please ki rabu dashi ba, ko har sai kin masa fyade kafin hankalinki ya kwanta? kawai ki sa a ranki zuciyar shi ta riga ta zaɓe ni. Kuma idan zuciya ta zaɓi abu, babu sarauta, babu iko, babu kuɗi da zai iya hana hakan.”... Farha ta yi rau-rau da ido tana cizon yatsa saboda takaicin yanda Amal ke gasa mata magana cikin natsuwa... Amal ta ƙara da cewa: “Ke ki bi hanyarki daban, amma wallahi idan kika cigaba da shigowa tsakanin mu, sai kin gane cewa bana wasa da yara irinku. Karki manta ni ƴar jarida ce, na san kalmar da zata zame miki tukunyar zafi. Ina da harshen da zai iya tsinewa mutuncin duk wanda ya tsaya mun a gaba. Amma ban zo yin faɗa da ke ba, kawai ina sanar miki gaskiya ne. Ke da Maleekh ba wani abu bane, haɗin bai yi ba sammm, ni kuma da shi, kalmar da ke tsakanin mu: shine Mutu-karaba.” Ta kashe ƙiran a nan, ta bar Farha sai huci take tayi... Farha ta cije baki, hawaye suka cika mata ido saboda takaici. Ta furta cikin tsawa: “Wallahi Amal, sai na ga bayan ki. Ko da zai zame min mutuwa, ba zan bar ki ki more wannan soyayya ba. Sai dai mutuwa ta rabaki da Maleekh.” Amma zuciyarta ta tabbatar mata da abu guda ɗaya, Amal ta fita iya magana, ta fita iya nuna ƙarfin zuciya. Wannan ne abinda yafi mata ciwo fiye da komai... Farha tana gama wayar da Amal, zuciyarta ta cika da wutar haushi. Tayi saurin miƙewa, da sauri ta sauƙa falo, zuciyarta cike da muguwar manufa. Ba tare da wani tunani ba, ta nufi part ɗin Maleekh... A hankali ta zuƙo key ɗin da aka ɗaura a jikin ƙofa. Ta tsaya jim kaɗan tana runtse ido, tana jin zuciyarta na bugawa kamar ana wasan doki. Sai ta janyo ƙofar ta saka key ɗin, ta jiyo “Klik!” alamar ta kulle shi daga waje... Tayi murmushin mugunta, tana jin kamar ta yi nasara. Da sauri ta janye key ɗin daga ƙofar, ta riƙe shi a hannunta sannan ta juya ta nufi nata part ɗin. Tana tafiya tana maganar zuci... “Wallahi Amal, ni Farha ba zan bari soyayyarku tayi kwari ba. Tinda har kika raina ni zaki gane kuranki. Sai Maleekh yayi sati a kulle a ɗakinsa, ba zai ga fuskarki ba. Wallahi sai na hana shi fita, sai naga yadda soyayyarku zata dawwama a kulle.” Ta ɗan tsaya a tsakiyar falon babban gida tana dafa ƙirji, hawaye na cika idonta saboda tsananin kishi. Sannan ta ƙara cewa a zuciya: “Ke Amal, ba zaki taɓa cin nasara akaina ba. Idan da gaske ne ‘Mutu-karaba’ ne tsakaninki da Maleekh, to bari mu gani ko kulle ba zai iya raba ku ba. Wannan shi ne farkon shirin da zan ɗauka akan ki. Na rantse da rantsuwa, daga yau soyayyarki zata fara ruguje wa a idonki.” Tana gama wannan tunanin ta nufi ɗakinta da murmushin mugunta a fuskarta, key ɗin na hannunta tamkar tayi wata gagarumar nasara. Da asuba, Maleekh ne ya miƙe daga gado cikin nutsuwa. Ya ɗauro alwala a bathroom, sannan ya saka farin jallabiyarsa tare da riƙo misbaharsa, zuciyarsa cike da natsuwa da niyyar nufar masallaci... Sai dai, da ya isa ƙofar falonsa ya murɗa handle ɗin ƙofar, ya juya da nufin buɗewa… “Klik!” Ya ɗan tsaya, ya ƙara juyawa da ƙarfin gaske… amma sai yaji ƙofar tamau! Wani irin yanayi ya ratsashi lokaci guda. Ya janye hannunsa ya matsa gefe, ya ƙara gwadawa. Amma ƙofar sai juyawa take, ba buɗewa! Ya tsuguna ƙasa yana kallon ƙofar da kyau. Glass door ce, mai ƙyalli da ƙarfinsa, wacce idan aka kulle daga waje ba mutum da zai iya buɗewa daga ciki. Zuciyarsa ta buga. Ya miƙe ya ɗan bubbuga ƙofar, sai dai babu wanda zai jiyo shi domin part ɗin nasa yana nesa da inda masu aikin gidan suke. Numfashinsa ya ɗan rikice, sai ya dafe kansa. “Me ke faruwa haka?..” Daurewa ya yi, ya koma ɗaki, ya shimfiɗa sallaya, ya yi sallar Asuba cikin ɗaki da zuciyar da ta cika da damuwa. Bayan ya iddar.. Sai ya zauna a gefen gado, ya haɗe hannuwa guri ɗaya, yana girgiza kai cikin ɗan murya: “Wannan ya nuna akwai wani shiri da ake kullawa a kaina..." A Ranar ya kwana cikin ɗaki, babu fita, babu ganawa da kowa. Abinci ma ba wanda ya kawo masa, sai ruwa kawai da ya ɗauko daga fridge ɗin ɗakin. Yayin da yake zaune, zuciyarsa kullum na yawo wajen Amal. Tunani yake, ko dai ita ma an hana ta ganinsa? Ko kuwa har yanzu tana zaune cikin kwanciyar hankali ba tare da ta san halin da yake ciki ba? A wancan gefen kuma, Amal ta tashi da safe cikin shauƙi. Tun kafin gari ya waye, zuciyarta na ta ɗokin jin muryar Maleekh kamar yadda suka saba. Tana ɗaukar wayarta ta ƙira shi, sai dai shiru. Kiran na shiga, amma babu mai ɗauka. Ta sake ƙira sau biyu, uku… har ta ƙara a karo na biyar, amma babu amsa. Zuciyarta ta fara bugawa da sauri. Cikin ranta ta ce: "Ko dai yana barci ne? Amma ko barci yake, da ya ji ƙiran wayata yake ɗaga wa. Me yasa yanzu shiru?" Cikin rikicewa ta jefa wayar gefe, ta ɗan jingina da gado tana mai lumshe ido da tunani. Amma zuciyarta ta kasa samun natsuwa. Ta sake ɗaukar wayar ta ƙira, amma har yanzu babu amsa. A gefe guda, Farha ce ke riƙe da wayar Maleekh tun daren jiya bayan ta kulle shi a ɗaki. Da ta ga ƙira daga Amal, zuciyarta ta ƙara ƙone wa da haushi. Ta ɗan bushe da dariyar mugunta, ta ajiye wayar gefe tana mai faɗin cikin zuciya: "Kin yi fatan jin muryarsa ko? Wallahi yau sai kin shiga ruɗani, zaki sha mamaki. Zan koya miki how to respect someone." Haka Amal ta wuni cikin damuwa, tana ɗaukar waya tana ƙiransa lokaci zuwa lokaci, amma babu alamar amsa. Zuciyarta ta shiga kullewa da tunani iri-iri. 🌹🌹🌹🌹 A gefe guda kuwa, Maleekh a ɗaki yana zaune kamar mai zaman kurkuku. Sai dai yayi sallarsa a ɗaki yayi wanka ya cigaba da zama, ya zauna yana ta nazari. Ga wayarsa kuwa bata kusa da shi, saboda tana wurin Ammy. Wannan yasa shi bai san cewa Amal na ƙiran shi ba... Maleekh yana zaune a bakin gado, zuciyarsa cike da tunani mai nauyi. Wayarsa Samsung Galaxy Z Fold 6, wacce kuɗinsa ya kai miliyoyi, bata wurinsa balle ya yi ƙira... Ga ɗayar wayarsa iPhone 17 Pro Max ɗinsa wanda ya bar wa Amal saboda ya fi son ita ta riƙe shi... Ya yi ƙasa da kai ya ɗan dafe goshinsa, sai ya tuna da laptop ɗinsa da yake a cikin jakar office. Da sauri ya buɗe jakar, sai ya tarar wayam. A ransa ya ce: "Kai! Ashe na manta na bar laptop a office… da shi zan iya yin ƙira ko tura saƙo…" Yayi firgit yana ɗan cakud'a sumar kansa, zuciyarsa ta shiga wani irin yanayi na tsarguwa... Yana cikin wannan halin ne ya miƙe zuwa bathroom don yin wanka da alwala. Sai da ya fito ya tarar da kulolin abinci an jera masa tsaf a kan teburin ɗakin. Abin da ya ba shi mamaki shi ne—ba a kawo masa abincin ba lokacin yana zaune, sai lokacin da ya shiga bathroom kawai aka yi amfani da damar aka shigo aka ajiye masa... Kafin ya kai hannunsa ga kulolin, sai ya ji motsin ƙofa. Da ya ƙarasa, sai ya lura an ƙara saka masa key daga waje. Zuciyarsa ta dinga harbawa. Cikin ransa ya furta: "Wannan wanne irin iskanci ne? Farha, nasan babu wanda zai mun wannan aika aika sai ke, ki tabbatar duk sanda na fito zamanki a gidan nan ya ƙare...." A kwana a tashi yau an wayi gari, sati uku kenam Maleekh yana kulle, sai dai yaga an kai masa flask ɗin abinci...already yana da kayan drinks a frig dasu milk.. Cikin wannan lokaci, Farha ta fahimci yadda Amal ta shiga damuwa saboda ƙiransa da take ba ya ɗauka. Da mugun haushi ta ɗauki wayar Maleekh ta yi blocking ɗin lambar Amal, domin ta tsananta mata damuwa... Amal kuwa… Hankalinta ya tashi matuƙa. Sau da dama ta ƙira wayarsa, amma kullum babu amsa, yanzu kuma wayar bata shiga kwata-kwata... Har ta kai ta kwana tana kuka da fargaba. Har ma ta saba zuwa kamfaninsa, tana tambaya ko ya zo. Amma kullum amsar da take samu ɗaya ce: "Bai zo ba." Ranar wata monday da ta sake zuwa, sai ta tarar da PA ɗinsa a bakin office. Bayan sun gaisa, Amal ta dubi fuskar sa da ta nuna alamar damuwa, ta ce: "Don Allah, ina Maleekh ne? Kwanan nan wayarsa bata shiga, kuma ba ya zuwa kamfani. Na damu sosai." PA ɗin ya kalli Amal cikin tausayi, sannan ya ce da ita "Wallahi nima ban san inda yake ba. Na je har gidansu na tambaya, amma sai suka ce min bai da lafiya. Amma gaskiyar magana, ba wani bayani suka yi ba sosai." Jikin Amal ya ɗauki rawa. Tana jin wani abu ya soke zuciyarta. Tace cikin firgici: "Ina so na je gidansu yanzu, ko da zan ganshi daga nesa ne kawai." Sai PA ya ɗaga mata hannu a natsuwa, yana faɗin: "Kada ki je, Amal. Idan har kina son kwanciyar hankalinki, ki yi haƙuri ki jira. Ki bar shi, zai bayyana da kansa. Idan kika tura kanki can yanzu, zai iya rikitar da al’amura fiye da haka." Amal ta yi shiru, hawaye na sauƙowa daga idonta. Ta jinjina kai a hankali, ta ce: "Toh shikenan… zan jira. Amma wallahi zuciyata ta kasa natsuwa." Da haka ta juya ta koma gida, jikinta babu ƙarfi, zuciyarta kuma na cike da ruɗani. Tun daga ranar da ta ji labarin cewa Maleekh “ba shi da lafiya” hankalinta ya ƙara tashi. Cikin kwanaki biyu kacal, jikinta ya fara sauyawa, idanunta sun ƙara faɗuwa, fuskarta ta rame, har kasa cin abinci take sosai. A daren wata Juma’a, tana zaune a falo tana ta kallon wayarta da ba ta daina ƙiran Maleekh ba, sai Inna ta shigo da hijab a jikinta. ta zauna kusa da ita, sai ta ce cikin tausasawa: "Amal… me ke damunki haka? Kullum nakan ganki cikin tunani, abinci ba kya ci sosai, sai kuka da ƙiran waya… ke ɗin ba haka kike ba tun farko." Amal ta runtse idonta, hawayenta na zuba, ta ce: "Inna… zuciyata ta kasa natsuwa. Maleekh ya ɓace min gaba ɗaya, babu waya, babu saƙo. Aka ce ma wai ba shi da lafiya… wallahi ina ji kamar rayuwata ta tsaya cak. Ban san me ke faruwa da shi ba." Inna ta kama hannunta da natsuwa, ta ce: "Ki saurare ni, Amal. Ki tuna Allah ne ke da ikon rayuwa da mutuwa. Idan Maleekh naki ne, wallahi babu mai iya rabaku. Amma idan Allah ya rubuta wata jarabawa gare ki, sai dai ki ɗauke ta da haƙuri da addu’a. Ke dai kar ki bari zuciyarki ta ɓaci har ki sa kanki cikin rashin lafiya." Amal ta share hawayenta, tana faɗin: "Inna, kin san shi da kyau. Mutum ne mai son gaskiya, mai adalci, mai taimako. Ni da shi babu wanda zai iya rabamu, sai dai mutuwa kawai. Amma ganin shi bai ƙira ba, bai zo ba, ko ɗaya daga cikin ma'aikatansa ban ji wani sanar wa daga gare su ba… wallahi hakan na mun ciwo sosai." Inna ta girgiza kai, ta yi murmushi sannan ta ce "Ƴar jikalle na, ki yi tawakkali. Ki dage da sallah da addu’a. Kar ki bari wannan jarabawa ta karya miki zuciya. Zuciyar mace abar daraja ce idan ta kasance da haƙuri. Ki bari Allah ya fitar miki da gaskiya da hannunsa." Amal ta jinjina kai, ta ce: "Na gode Inna… zan yi ƙoƙarin jurewa. Amma Inna wallahi bana jin zan iya jurewa idan na rasa shi." Inna ta lumshe ido ta ce: "Allah ba zai bar ki ba, yarinyata. Idan har Maleekh naki ne, zai dawo hannunki da ikon Allah, babu makawa." (Su Hajiya Inna kuɗi ya gyara tsohuwa 🤣🤣) A Ɓangare guda kuwaa Farha ta kwana da tunani mai nauyi, zuciyarta ta cika da hassada da ƙiyayya. Da daddare ta ɗauki wayar Maleekh ta shiga yin tracking inda Amal take. A zahiri kuwa, sai taga Amal na zaune da Kakarta a cikin wani gida mai kyau a Gwarinpa Estate... Cikin jin haushin abin, ta ɗauki makiƙiyar shawara tana faɗin “Wallahi zan je da kaina na same ta, zan sanar mata cewa......!." tasau murmushin mugunta sannan ta ce "ya bar ta da mummunan kunya.”.. Washegari, ta nufi Gwarinpa da motarta, bayan ta parked a gefen titi, ta sauƙa cikin izza kamar wata sarauniya. Tana tafe tana gyagygyara ɗan ƙaramin mayafinta sai kamshin perfume take... Ta iso bakin get, ta fara knocking da ƙarfi... Mai gadi ya fito cikin alfarma yana tambaya: “Madam, daga ina? Waye kike nema?” A gadarance Farha ta watsa masa wani irin kallo tare da ɗaga gira ta ce: “Ka buɗe mun kawai, ban son surutu. Gidan masoyina ne, ni baƙuwa ce ta musamman.” Mai gadi ya harare ta, ya ce: “To ai bazan bar ki shiga haka kawai ba. Sai na je na sanar wa masu gidan. Idan sun ce a shigo dake, sai ki shigo.” Ya juya da sauri ya nufi cikin gidan, ya sanar da Amal cewa akwai wata “baƙuwa mai tsiyar tsiya” tana wajen get. Amal, wacce ke zaune a falonta cikin tsananin tunani, ta ce a shigo da ita. Ba a jima ba, sai ga Farha ta shigo cikin izza tana tauna chiwgum, tana wani irin taku kamar wata sarauniya. Amal kuwa ta miƙe tsaye cikin jin haushinta, tana harararta da idanun da ke huci kamar wuta... Amal ta ce da ita cikin tsawa: “Ke kuma fa? Me ya kawo ki gidana?” Farha ta kyalkyale da dariya ta ce: “Gidanki? Kin tabbata gidanki ne? Ko gidan Maleekh? Ki sani ina da cikakken right in shigo nan domin nan gidan masoyina ne.” Amal ta taka zuwa gabanta cikin izza ta ce: “Ki tambayi kowa! Wannan gida nawa ne, ba na kowa ba. Ni ce mai shi!” Farha ta runtse ido tana dariya ta ce: “Gidan da ya gina da kuɗinsa kike ce wa naki? Kina da hankali kuwa?” Amal ta girgiza kai ta ce cikin karfin hali: “Duk da haka dai, nawa ne! Tunda takardun gidan da sunana a jiki. Kar ki raina mun hankali.” Farha ta yi tsaki, ta ciro wata takarda daga jakarta ta miƙa mata. Invitation card ce... A jikin card ɗin kuwa, sunan Maleekh ne da nata aka rubuta a matsayin ango da amarya. Cikin izza ta ce: “Ga shaida! Muna gayyatarki zuwa party bikin mu a mako mai zuwa. Ki tabbatar kin halarci wurin.. saboda kuwa idan ‘yar jarida ta zo, bikin zai ɗauki armashi sosai.” Amal ta zaro ido, zuciyarta ta fara bugawa da ƙarfi, hawaye suka taru a idanunta. Amma kafin ta yi magana, Farha ta yi murmushi mai cike da mugunta, tana jin daɗin ganin halin da Amal ta shiga. Amal tana hawaye ta ce cikin rawar murya: “Ƙarya kike yi, munafikar banza! Maleekh ba zai taɓa cin amanata ba. Kin yi ƙarya matsiyaciya, ƙarya kike makaryaciya!” Farha ta ce tana ɗaga hannu: “Ƙarya kuma? To ga shaida a hannunki! Idan ba gaskiya ba ne, wannan meye?” Amal ta riƙe card ɗin tana huci, tana kuka har fuskarta ta fara yin jawur abinka da farar mace. A fusace ta zabura, ta hankad'a Farha da ƙarfi. Farha ta faɗi ƙasa ta ɗan yi ihu... Amal kuma cikin tsawa ta ce: “Ƙarya ne! Ke munafuka ce!” Farha ta tashi tana huci kamar wata zakanya, ta kai wa Amal mari da ƙarfi... Amal itama bata tsaya ba. Cikin hargowa ta ɗaga hannu ta maida mata da mari ta hagun, ta ƙara zabga mata wani marin a gefen fuska ta dama, ta ƙara zabga mata mari sau uku a jere. A take Farha ta riƙe kumatunta, ta yi ƙara, sannan ta zube ƙasa sumammiya! Amal ta tsaya tana haki, zuciyarta na bugawa, tana kallon Farha da mamaki da takaici a lokaci guda... Amal ta tsaya tana haki, zuciyarta kamar zata fito ta bugi ƙirjinta. Idonta ya sauƙa kan Farha wacce ta zube ƙasa ba motsi.. Amal ta yi saurin dafe kai, tana furta cikin rawar murya: “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un… me nayi haka? Na kashe mutum? Ya Allah ka tsare ni da jarabarnan!” Ta durƙusa kusa da ita tana jijjigan ta, amma Farha ko motsi bata yi ba. Amal ta yi saurin ɗauko bottle ruwan sanyi a frig tana zuba mata amma Farha ko motsi...kuka ne yaci karfinta kamar ruwan sama... Tana faɗin “Farha! Ki tashi don Allah. Ni ban nufin kashe ki ba. Na yi fushi ne kawai. Don Allah ki buɗe idonki, ki tashi ki yi min bala'i kamar yadda kika saba yi… ki ce munafuka kamar yadda kika saba faɗa. Ki tashi ki faɗa min cewa Maleekh naki ne! Don Allah kar ki barni cikin wannan hali…” Amal ta fara jijjiga hannayenta, zuciyarta na harbawa da tsoro. A zuciyarta ta fara jin cewa lallai ta jefa kanta cikin babban haɗari. “Idan har ta mutu fa? Za su ce ni na kashe ta saboda soyayya da Maleekh! To shin wace kotu zata yarda da ni?” Cikin tsananin fargaba ta miƙe tsaye tana tafiya a falo tana ƙiran: “Inna! Inna ki zo ki taimake ni! Na shiga uku… Innaaa!” Sai ta dawo kusa da Farha tana kallonta, zuciyarta ta kasa yanke shawara: ta ƙira ‘yan sanda ko kuma ta ƙira Maleekh kai tsaye? Amal ta ɗauki wayarta da sauri, hannunta na rawa. Tana danna lambar Maleekh, sai ta tuna cewa wayarsa tana hannun Ammy ko Farha, kuma tuni an yi blocking ɗinta. Wannan tunanin ya ƙara girgiza ta. Ta kalli Farha da idanuwanta da suka cika da hawaye, ta furta cikin muryar kuka: “Wallahi ba nufin kashe ki nayi ba. Ni ‘yar jarida ce, ba azzaluma ba. Amma wannan haɗin baki da ƙaryar da kika kawo, sai kika jefa ni cikin jarabawa.” Amal tana cikin wannan halin sai ga Inna ta dawo.. Inna ta dawo daga kasuwa tayo siyayya, ta tarar da Amal a cikin wannan halin ga Farha a sume a ƙasin carpet, nan masu aikin gidan su biyu duk suka shigo falon jin ihun Amal, kowa hankalinsa yayi matuƙar tashi... Ana ta watsa wa Farha ruwa amma bata motsa ba, Amal tana ta jijjiga ta amma ko motsi... Anan ta ƙara fashewa da kuka tana faɗin "Farha ta mutu na shiga uku. Wazai taimake ni, ni Amal marainiyar Allah. Tazo ta sanar mun cewa wani sati bikinta da Maleekh, kenam Maleekh yaudara ta yayi? Maleekh ya ci amana taaa, ga na shiga tsaka mai wuya nayi kisan kaiii..." Har zuwa dare Farha tana kwance ko motsi... Maleekh yana can ɓangarensa a kulle shima ya shiga damuwa matuƙa ganin sa a halin da bai taɓa shiga ba, na kullen da ya ga kansa a ciki, tsawon sati uku yana kulle... Ammy ganin dare yayi bata ga Farha ta dawo ba yasa ta fara ƙiran wayanta... Wayar Farha ne ya fara ringing. Amal tana dubawa taga Ammy ta bayyana a screen ɗin wayar. Amal ta ƙara ɗora hannu akai tana kuka tana faɗin "Na shiga uku naaaa..." Amal tana kallon wayar da ke ringing, sunan Ammy a jikin screen ɗin yana yi mata haske kamar an saka mata wuta a kai. Hannunta haka yake rawa, idanuwanta sun yi jajir saboda kuka. Masu aikin gidan suka tsaya a gefe suna kallo cikin firgici, ba su san abin da za su yi ba. Inna kuwa ta tsaya cak tana rike da ledar siyayyar ta, ta kasa motsawa. “Amal, ki ɗaga mana ƙiran nan! Koma dai menene, ki bari gidansu su san halin da ake ciki...” Inna ta furta cikin rawar murya. “Ban isa ba Innaaa! Ban isa na ɗaga ba! Na shiga uku... wallahi na kashe ta, na kashe Farhaaa... idan Ammy ta sani fa? Wane ido zan sake duban duniya?” Amal ta ƙara fashewa da kuka tana bubbugan Farha, ta rufe fuskarta da hannuwa... Wayar sai ringing take yi, ƙiran bai yanke ba. A ƙarshe ɗaya daga cikin masu aikin gidan ta ƙaraso ta ɗaga, cikin murya mai rawa ta ce: “Assalamu alaikum Hajiya...” Ammy ta ɗaga da sauri, cike da damuwa ta ce “Wa alaikumus salam, ina Farha take? Tun da rana ban ganta ba, yanzu kuwa wayarta ba ta ɗauka ba... me ke faruwa ne?” Mata mai aikin gidan ta kalli Amal, tana jiran amsarta. Ita kuwa ta soma girgiza kai tana kuka, tana faɗin: “Kada ku gaya mataaa... don Allah ku ce tana lafiyaaa...” Ammy ta sake cewa da ƙarfin murya: “Ku gaya mun gaskiya! Ku gaya mun inda Farha take yanzu!” Amal ta ƙara ɗora hannu akai tana kuka tana faɗin, "Na shiga uku naaaa..." Inna dake tsaye ta zabura da sauri ta karɓi wayar daga hannun mai aiki zuciyarta na bugawa da ƙarfi. Batare da wata-wata ba ta ɗaga ƙiran.... Ammy ta kuma cewa.. "Hello… Farha! Ina kika shiga tun safe baki dawo ba?" Cewar Ammy daga can ɓangaren muryarta cike da damuwa. Inna ta ɗan kalli Amal wacce take rawar jiki tana kuka, sai ta ce cikin ɗan ɓatar murya "Uhmm… ehh… wai don Allah ku zo yanzu da gaggawa… an samu matsala ne… kiyi sauri ku taho kafin mu rasa rai a hannun mu." Cikin firgici Ammy ta jefa tambaya, "Wai me ke faruwa? Lafiya dai? Ki faɗa min gaskiya, lafiya Farha ce?!" Hannu Inna ta ɗora akai, ta kalli Farha da ke shimfiɗe ƙasa kamar gawa, babu motsi. Sai tace cikin rawar murya... Inna tsabar ta rikice cikin rawar murya ta ce "Lafiya ba ta da kyau… kiyi sauri ki taho yanzu, don Allah…" Cikin razana Amal ta sake fashewa da kuka tana faɗin, "Wannan masifar da ta same ni ina zan saka kaina? Ni Amal na shiga uku, Allah ka cece ni…"... NEXT NEXT NEXT.... asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 27 to 28 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Ammy tana so ta tambayi ina Farha take zata zo sai kawai taji wayar ta katse. Ta sake ƙira, ta sake ƙira, amma babu wanda ya ɗauka… duk ƙiraye-ƙirayenta suka ci tura. Misalin ƙarfe biyu na dare Farha ta fara motsawa a hankali daga suman da ta tafi. Idonta ya fara motsawa cikin rauni, numfashinta na fita sama-sama.. Kowa a gidan ya kasa bacci. Amal ta kasa runtsa ido, kuka kawai take yi tana durƙushe a gaban Farha da ke shimfiɗe a ƙasan carpet. Inna kuwa ta zauna gefe cike da fargaba, zuciyarta na bugawa da sauri, haka ma masu aikin gidan suna ta kai komo, kowa hankalinsa a tashe. A dai-dai lokacin, suka ji jiniyar motoci na tsaya wa a bakin get ɗin gidan. Saƙon firgici ya ratsar da Amal, ta zabura ta ɗago tana kallon Inna da ido zuru-zuru, muryarta na rawa ta ce: "Innaaa… taya ƴan sanda suka sani?..." Inna ma jikinta ya ɗauki rawa, ciki ya tsure, ta kasa bawa Amal amsa. A bakin get kuwa, ƴan sanda ne tare da Ammy suka iso, domin Ammy ta samu damar gano inda Farha take ta hanyar tracking ɗin wayarta. Ƴan sandan suka fara knocking da ƙarfi, ƙarar ƙwanƙwasa get ɗin ya razana mai gadi wanda ya taso a tsorace. Cikin zuciyarsa yana tunanin ko ƴan fashi ne suka iso a wannan daren. Sai dai kafin ya yi wani yunƙuri, ƴan sandan suka tsawatar masa da ƙarfi, suka nuna masa hasken torchlight ɗinsu tare da rera sunansa. A firgice ya buɗe musu get ɗin. Kai tsaye cikin gidan suka nufa da sauri. Ammy kuwa bata ma san gidan waye bane, kawai dai ta bi ƴan sandan da zuciya cike da tashin hankali. Sai suka kutsa cikin falon gidan ba tare da bata lokaci ba… Ƴan sandan da suka shigo falon sun tsaya cak ganin wata yarinya a kwance a ƙasan carpet, fuska kumbure, jiki a sake. Amal na kuka tana jijjiga ta. Inna kuma na tsaye gefe jikinta na rawa. Masu aikin gidan suma suna gefe da rawar jiki, kamar wanda aka kama da laifi. Ammy ce ta fara zabura, ta nufi wurin da Farha take kwance tana ihu tana ƙiran sunanta: “Farha! Farhataaa! Kece nan?! Me aka miki haka?!” Ta durƙusa tana jijjigata, idonta cike da hawaye. Ganin Farha ba ta motsi sosai sai ƙaramin numfashi kawai take yi yasa zuciyarta ta ji wani irin sanyi mai sosa rai. Ƴan sanda suka matsa, suka rarrabe su Amal da Inna da masu aikin. Ɗaya daga cikin su ya kalli Amal cikin tsattsauran ido yace: “Ke ce kika yi wannan laifin?” Amal ta ɗora hannaye a kai tana kuka tana girgiza kai: “Wallahi ba ni na kashe ta ba… ni ma ban san ta faɗi haka ba. Na shiga uku, Allah ya sani ban yi niyyar kashe ta ba…” Inna da sauri ta durƙusa tana roƙon ƴan sandan: “Don Allah kuyi hak’uri, ku barta, komai ne ya faru dai matsala ce ta afku, kar ku ɗauki ƴar matashiyar yarinya ku jefa ta cikin kurkuku…” Ammy ce ta miƙe tsaye cike da haushi, fuska a ɗaure, tana kallon Amal ta wutsiryar ido tana huci tace: “Wallahi ba zan lamunta ba. Wannan matsiyaciyar yarinya ba zata kashe min ɗiya ba ta ce zata tsira. Sai dai ku kama ta, ku tafi da ita yanzu! Ni da kaina zan tabbatar ta ɗanɗani ɗaci irin wanda ta jefa ni a yanzu.” Ƴan sandan suka yi wa Amal dirar mikiya, suka kama hannunta da ƙarfi. Amal ta fashe da kuka mai ban tausayi, tana faɗin: “Don Allah ku yi hak’uri, ban kashe ta ba. Ku tambayi Allah! Ku tambayi zuciyar ku. Na shiga uku, ni Amal, babu kokai a wannan rayuwar sai sharri?!” Ammy ta ƙara tunkarar ta da magana marar daɗi, tana harara tana faɗin: “Ke matsiyaciya! Kina tunanin Maleekh zai aureki? To idan mafarki kike ki tashi kiyi sadaka, domin bazan taɓa aurawa yarona tsiya ba....kina burin zama matarsa ko? Sai dai ki lalace a kurkuku wallahi...” Ƙirjinta ya buga, zuciyarta ta narke da baƙin ciki. Amma saboda tsoron abin da zai biyo baya, Amal tayi shiru da sauran ƴan gidan. Jigum-jigum suke kallon yadda ƴan sandan ke jan Amal kamar wata barauniya. Hankalin Amal ya ƙara tashi ganin suna shirin ficewa da ita. Ta zube a ƙasa tana roƙo cikin kuka: “Don Allah kuyi hak’uri, ku kyaleni, ba ni na kashe ta ba… wallahi ba ni ba ce!” Sai dai Ammy ta ɗaga hannu ta tsawatar musu da cewa: “Ku ɗauke ta! Sai ta ɗanɗani ɗakin kurkuku, sai ta gane shiga rayuwarmu ba abu ne mai sauƙi ba...” Ƴan sandan suka ja Amal suka nufi ƙofar fita da ita, kukan Amal yana cika ko'ina, idonta cike da hawaye, zuciyarta cike da tsoro da baƙin cikin zargi… Inna zama tayi tare da fashewa da kuka... Maleekh yana nan a ɗakinsa, yana zaune a gefen gado, idonsa jajur saboda kwanaki yaƙi bacci. Zuciyarsa cike da ɓacin rai da ruɗani, bai san meke faruwa ba a waje. Kamar kullum sai juyi yake yi a kan gado, yana tunanin yanda zai kuɓuta daga wannan kulle da Farha ta tsare shi. Bai ma san cewa a wannan daren rayuwar Amal za ta sauya ba. A can waje kuwa, ƴan sanda sun ja Amal kamar wata 6arauniya, kuka take tsaye tana roƙo amma babu mai sauraro. A cikin mota suka sata, suka kaita police station, suna isa suka jefa ta cikin cell mai ƙunci da wari, tare da wasu mata masu laifuffuka daban-daban. Hawaye ke zuba mata ba tare da tsayawa ba, zuciyarta na tsinke-tsinke da baƙin ciki. Amal ta kwana daren nan cikin kuka, cikin tsananin tsoro da fargaba. Bata taɓa tunanin rayuwa zata jefa ta irin haka ba. Tana zaune a tsugunne, hannayenta riƙe da ƙafafunta, idonta a rufe, zuciyarta cike da addu’a: “Ya Allah! Ka tsare ni daga sharri. Ka kawo gaskiya fili. Ka tabbatar da cewa ban taɓa kisan kai ba, Allah kai ka san ni marainiya ce. Kada ka bar ni a wulakance a duniya.” A gefe guda kuma, Farha wacce ta fara motsawa daga sumar da ta kwashe lokaci mai tsawo, sai ranta a ɗaure da ciwo da wani irin kasala. Numfashinta na fita a wahalce, idanunta a lumshe, jikinta kamar wanda ya sha miyagun ƙwayoyi. Ammy na tsaye a kanta tana kuka tana girgiza ta: “Farhata, ki buɗe idonki, ki dubeni. Don Allah kar ki barni, idan kika mutu me zance wa iyayenki?!” Sai da ta ji Farha ta motsa da ƙyar ta ɗaga hannu, ta sake faɗowa gefe kamar zata sake suma. Da gaggawa Ammy ta ƙira direba, ta ɗauke ta da hannunta ta saka ta cikin mota. “Hospital za mu nufa yanzu! Na rantse sai wannan yarinyar Amal ta biya kuɗin halin da Farha ta shiga,” ta faɗa tana kuka tana riƙe da hannun Farha... Motar ta nufo babban titi da gudu, yayin da zuciyar Ammy take huci da haushin Amal. Ita kuwa Farha sai sauƙe numfashi take yi kamar wacce take kan shan wahala mai tsanani. A haka suka nufi asibiti, yayinda Amal kuwa ta kwana cikin ƙunci a ɗakin kulle na ƴan sanda… Washegari gari na wayewa, ƙarar ƴan ƙiran sallah daga masallatai daban-daban ke ratsa kunnuwan mutane. Amma Amal ta buɗe idanu a cikin ɗakin kulle, babu wani hasken rana face ɗan ƙaramin wutar lantarki mai walƙiya a sama. Tana juyi a ƙasa, ƙasa mai sanyi ga duhu da wari, duk jikinta ya kankame saboda sanyi. Idonta ya kumbura saboda kuka, zuciyarta cike da tsoro da damuwa. Ƴan sanda biyu suka shigo suna mata ihu a kai. “Ke! Tashi ki fito..." Amal tayi tsitt kamar bada ita ake ba sai rawar sanyi take.. Ɗaya ne ya sake daka mata tsawa.. "Ki fito mana! Kin yi shiru kamar gawa.” Amal ta ɗago a tsorace, ta daidaita kanta. Aka ja ta zuwa ofishin DPO, inda aka fara yi mata tambayoyi cikin tsawa: “Wacece ke? Me kika yiwa Farha? Kin bada guba ta sha, sannan kin shaƙe ta, har ta faɗi. Shin kisan mai kike shirin yi ne?” Hawayen Amal suka zubo tana cewa: “Wallahi ban bata komai ba. Gaskiya nake faɗi, mun yi faɗa ne kawai saboda ta zo gidana ta ci mun mutunci. Ni ban san tasha wani abu ba. Don Allah kuyi adalci.” Ƴan sandan suka kalli juna suna dariyar rainin wayo: “Ke yarinya, kin yi laifi kin kawo kanki. Idan ba kin sami wanda zai tsaya miki ba, za ki cigaba da kwana a nan. Kuma idan aka tabbatar ta mutu, to lallai kin shiga uku.” Amal ta fashe da kuka, zuciyarta na karyewa... Sannan aka maida ta cikin cell.. A gefe guda kuma, Maleekh yana zaune a ɗakinsa a kulle, fuskar sa cike da gajiya. Yana zaune a bakin gado, hannunsa na tallafe da kansa, yana tunanin: “Me yasa Mom za ta ɗaure ni haka? Wani hali Amal ke ciki yanzu? Shin tana lafiya? Ko kuwa ta ɗauka na watsar da ita ne?” Ya ɗago yana kallon saman ceiling, zuciyarsa na wani irin bugawa da tashin hankali. Ya tuna da wayarsa da aka kwace masa... “Idan dai suna ƙiran wayata, to nasan zasu yi tunanin na gudu ko na guje su. Ya Allah! Ka fito da ni daga wannan halin.” Ya miƙe a tsorace, ya ɗauki kwalbar ruwa ya sha sannan ya nufi bathroom, ya ɗauroalwala. A cikin ɗakinsa ya tsaya ya tayar da sallah... Bayan ya idar da sallah. Idonsa ya rufe yana jin wani irin zafi a zuciya, zuciyarsa ta cika da tsanar Farha.. Maleekh yana zaune a daddumar sa, sai yaji budar ƙofar ɗakin sa, a zabure ya miƙe tare da nufan falonsa da gudu, Islam ya gani a tsaye da key a hannunta... Haka yayo kanta kamar zai rufe ta da duka.. Islam a tsorace ta ce "Yaya ka tsaya kaji.." Maleekh yana tambaya "waya rufe ni? Meyasa aka rufe ni har tsawon sati uku?.." Islam ta ce "Yaya Wallahi Aunty Farha ce ta kulle ka, sannan ta hana kowa zuwa yanda kake, ita take ɓoye da key ɗin ka sannan wayarka ma a hannunta yake....yanzu ma tin jiya da safe Aunty Farha ta fita bata dawo ba, har dare Ammy ta fita neman ta, nayi waya da Ammy da safen nan take sanar mun wai suna hospital, Farha bata cikin hayyacinta sakamakon shaƙar da Amal tayi mata a gidanta, yanzu haka Amal tana police station a kulle..." Maleekh jin haka hankalinsa ba ƙaramin tashi yayi ba, jin Amal tana police station, cikin fushi yake cewa "Tin da Farha tayi mun wannan danyen aiki sai na wulakantata, ko tana gadon asibiti sai naci mutuncinta, har tana da kwarin gwiwar rufe ni a ɗaki har tsawon kwanaki? Sannan meya kaita gidan Amal?..." Islam ta ce "wallahi ban sani ba Yaya, yanzu ma ɗakin ta naje na dubo yanda ta ɓoye key ɗin ɗakin ka, nazo na buɗe maka, kasan ina kaunarka Yayana..." Maleekh ya rungumi Islam yana jin daɗin yanda jininsu yazo ɗaya da ƙanwarsa Islam...Yana ji da ita sosai sa6anin Arfat marar kunya... Maleekh ko tsaya gyara kansa baiyi ba ya fita... Yana fita harabar gidan ya nufi wurin parker motoci, ya shiga motarsa sabuwar Mercedes-Benz CLE 450 4MATIC Coupé mai sheƙi, wanda ko a Abuja da Lagos ba a cika ganinsa ba. Duk da yana cikin tashin hankali bai tsaya gyara kansa ba, ko kallon gilashin motar. Zuciyarsa na tafasa kamar wuta, yana maimaita a zuciyarsa: “Amal a kulle? Kuma saboda wannan wautar da Farha tayi? Wallahi sai ta gane ni ba yaro bane.” Kai tsaye ya nufi gidan Amal, ba tare da tsayawa ko’ina ba. Yana tafe da gudu, yana jin kamar hanya ta yi masa kaɗan saboda tsananin fushinsa. Da isarsa gidan Amal, bai tsaya daƙile hayaniyar zuciyarsa ba, ya sauƙa daga motar da sauri, ya nufi ƙofar gidan... Knocking yake da ƙarfi, mai gadi yana tambaya amma Maleekh bai tsaya bashi amsa ba, ganin buga get ɗin yaƙi ƙarewa ne yasa Mai gadin buɗe wa, yana buɗe get Maleekh ya hankad'a shi tare da shige wa... A falo ya tarar da Inna zaune sai hawaye take tayi, Maleekh ne ya rarrashe ta tare da tambayarta "shin wani police station aka kaita?.." Inna cikin kuka tace "Ni ina zan sa ni..." Sai da ɗaya daga cikin masu aikin gidan ta shigo ta sanar masa.. Maleekh bai tsaya jiran komai ba ya miƙe tare da fice wa... A gefe guda kuwa, Amal tana cikin azabar duka a hannun wata ‘yar sanda mace. Ta na ƙoƙarin kare kanta da kuka da magiya, amma taurin zuciyar wacce ke dukan nata ya fi ƙarfin tausayawa. Kowane dukan sanda yana ratsar da ita yana kuma hura mata ƙarin zafi. Duk abin da suke nema daga gareta shi ne ta faɗi cewa wani abu ta ba Farha tasha domin ta mutu. Amal tana kuka cikin wahala tana cewa: “Wallahi ban ba ta komai ba! Na rantse da Allah, babu wani abu a hannuna. Don Allah ku yi adalci!” Amma babu wanda ya saurareta. Sai dai a lokacin, ƙarar motar Maleekh da ya tsaya a gaban police station ɗin ya jawo hankalin kowa, ciki har da wacce ke dukan Amal... Da ƙarfi Maleekh ya tura ƙofar police station ɗin ya shiga, zuciyarsa a hargitse, fuskarsa cike da bacin rai. Ƙarar takalminsa da ke ƙaraso wa da gudu-gudu ta sanya jami’an da ke tsaye kallon sa, wasu daga cikinsu ma suka ɗan ja da baya ganin irin hankoron da ya shigo da shi. Da sauri idanunsa suka sauƙa kan Amal da ke cell, jikinta ya kumbura, hancinta yana zubar da jini. Wata ‘yar sanda mace na tsaye da sanda a hannunta, alamar ba ta kammala dukanta ba.. A zabure Maleekh ya nufe ta yana huci kamar zaki, da sauri ya fisge sandar hannunta ya wurgar gefe, yana ɗaga muryarsa: “Ke wacce irin rashin imani kike yi ne? Wace ƙa’ida ce ta ce ku ci zarafin mace a hannunku? saboda Amal ce shiyasa kuka yi mata haka?” ‘Yar sandar ta ja da baya tana rawar jiki, amma kafin ta ce komai, Maleekh ya wuce wurin Amal. Ya zauna a gefenta, zuciyarsa na tsananta da tausayinta. Ya kamo hannunta cikin tausayi, idonsa cike da hawaye da fushi lokaci ɗaya: “Amal… me suka yi miki haka? duk saboda ni kika shiga wannan hali? Ki kalle ni, wallahi duk abinda ya same ki Farha ce ta jawo amma zanyi maganinta..!” Amal ta ɗago da ƙyar, muryarta a raunane, idanunta sun kumbura da hawaye ta ce “Maleekh… wallahi ban aikata komai ba… suna zargina da wani abu… amma na rantse da Allah ban ba Farha komai ba.” Maleekh ya ɗaga kansa ya kalli jami’an da ke tsaye da ƙarfi, muryarsa na girgiza ɗakin ya ce “Duk wanda ya sa hannu aka ci zarafin ta, sai na sa a bincike shi! Wallahi sai kun gane illar zubar da mutuncinta da ku ka yi...” Yayin da yake magana, manyan jami’an station ɗin suka fito daga ofis ɗin su saboda hayaniyar. Gani Maleekh yasa ɗaya daga cikinsu ya ce cikin ladabi: “Sir Maleekh, kayi haƙuri. Wata matsala ce ta biyo baya, amma za mu warware komai yanzu…” Maleekh ya miƙe tsaye, yana huci, ya dube su da idanun da suka cika da fushi: “Ba ku isa ku ci zarafin ta ba! Da izinin wa kuka yi haka? Amal zata fita tare da ni yanzu, kuma sai na san duk wanda ya bayar da umarnin a daketa.” Ya juya ya dubi Amal, ya kama hannunta da tausayi yana cewa: “Tashi mu tafi, Amal. Wannan wulakanci ba zai sake faruwa ba.” Duk jami’an suka shiga rikicewa, wasu suna ƙoƙarin kwantar da hayaniyar domin sun san halinsa idan yaga ba daidai ba zai iya sawa a cire su a aikin, duk station kowa ya san Maleekh ya shigo, kuma an karya masa zuciya saboda abinda aka yi wa Amal... Police station ɗin ya ɗauki shiru, sai kukan zuciya da Amal ke yi a raunane, tana zaune kamar marar ƙarfi. Dukkan jami’an da suka taru suna sunkuyar da kai suna ba da haƙuri. Wani babban officer ma ya matso da ladabi yana faɗin: “Sir Maleekh, wallahi ba mu yi haka da kanmu ba. Hajiyarku ce ta bayar da umarnin a hukuntata… mu dai umarnin ta muka bi…” Maleekh ya ɗaga hannunsa ya dakatar da shi, idonsa jajir cikin fushi, ya ce da ƙarfi: “Ba ni zaku bawa haƙuri ba! A Amal za ku bada haƙuri! Ita kuka wulaƙanta, ita kuka ci zarafi! Ku tsaya ku nemi afuwarta…” Nan da nan suka ƙarasa wurin Amal ɗaya bayan ɗaya, suna ƙoƙarin lallashinta cikin ladabi: “Ki yafe mana Hajiya, wallahi ba mu san ƙarya akayi miki ba…” “Ki yi haƙuri, hakan ba zai sake faruwa ba.” Amal kuwa hawaye kawai take zubarwa tana jin ɗacin abinda aka yi mata. Maleekh ya kalli jami’an, muryarsa ta sake yin nauyi: “Ku sani, daga yau, ba wanda ya isa ya ɗaga mata yatsa a gabana. Ita ce matar da zan aura, kuma duk wanda ya kuskura ya sake tabata… sai na nuna masa babu wanda ya isa ya tauye mata daraja a wannan ƙasa.” Kowa ya sunkuyar da kai.. Da haka Maleekh ya kamo hannun Amal, ya taimaka mata ta miƙe da ƙyar, sannan ya ja ta har zuwa motarsa. Ya buɗe mata ƙofa da kansa ya tabbatar ta shiga, sai ya zagaya ya shiga driver’s seat. Ya kunna motar, zuciyarsa na cike da fushi da tausayinta lokaci guda. Ba tare da ɓata lokaci ba ya nufi hospital domin a duba jikinta, ganin yanda bakinta da hancinta suka fashe suna ɗigar da jini... Bayan sun isa hospital ɗin, motar Maleekh ta tsaya da ƙarfi har sai da mai gadin wurin ya zabura. Ba tare da ya tsaya ɓata lokaci ba ya fito ya buɗe ƙofar Amal, ya ɗaga ta kamar karamar yarinya ya shigar da ita cikin babban reception na hospital ɗin. “Doctor! Doctor!!” Ya ƙwalla ƙira, muryarsa na ɗaukar hankalin kowa. Ma’aikatan asibitin kamar ba su damu ba, suna ta dube-dube suna tambayar “card” da “payment” kafin su shiga aiki. Wani doctor ya ƙaraso da nutsuwa, yana faɗin: “Sir, please calm down, mu a nan muna bin order ne, dole sai an rubuta file kafin—” “Ka tsaya nan!” Maleekh ya katse shi da ƙarfi, idonsa ya ɗan firgita shi. “Kana ganin wannan yarinyar a wannan hali, baka da hankali ne, kace za a fara rubuce-rubuce kafin a taimaka mata? Wane irin rashin imani ne wannan?!” Nurse ɗin dake gefe ta ce a hankali: “Sir, rules ne, dole mu cike bayanai kafin—” “Rules ɗin ku ku watsar dasu!” Maleekh ya ɗaga hannu yana nuna Amal da hannunsa yana jijjiga. “Idan wani abu ya same ta saboda sakarci da rashin gaggawar ku, wallahi sai na rufe muku wannan hospital ɗin gaba ɗaya! Kun san ni da kyau! Ba zan bari wani ya ƙara wulaƙanta ta ba!” Dukan reception ɗin ya shiga ruɗewa, nurses da doctors suka fara ƙoƙarin haɗawa da sauri. Wani likita ya fito daga Emergency room, ya ga tashin hankalin, nan take ya umarci su: “Quick! Take her inside, emergency ward now!” Suka karɓi Amal daga hannun Maleekh a hankali suka ɗora ta kan gurneti. Duk da haka, Maleekh ya ci gaba da bin su har cikin hallway, yana rera musu magana da ƙarfi: “Kada wani ya kuskura ya yi wasa da rayuwar Amal! Duk wani abu da take buƙata, ku kawo yanzu! Ku tuna, idan wani abu ya same ta… kai ne na farko zan hukunta!” Doctors suka shiga yin gaggawa fiye da yadda suka saba, saboda kowa ya san irin tasirin Maleekh a ƙasar, babu wanda zai so ya shiga cikin fushinsa. Maleekh bai tsaya sauraron kowa ba. Duk wata nurse da ta ce masa ya tsaya a waje sai ya ɗaga hannu yana tsawatarwa. “Na ce bana son ji! Wannan hannunta zan riƙe har sai ta samu ƙarfin jiki! Ku dai kuyi aikin ku kawai!” Nurse ɗin da ke kusa da shi ta girgiza kai, tana faɗin: “Sir, please, ka tsaya a waje mana, ai ba manyan ciwuka bane—” “Ki yi mun shiru anan!” Maleekh ya dakatar da ita da murya mai cike da izza. “Kin ce ba ciwo bane? To kina ganin wannan jinin da yake fita a hancinta da lebenta wasa ne? Wannan ita ce rayuwata! Ki shiga ki kula da ita kafin na maka ƙarar ki cewa kina sakarci da aikinki..!” Likitan da yake tsaye ya kasa ɗaga kai ya kalle shi kawai, zuciyarsa na cewa: “Ai wannan fa ƙaramin rauni ne, amma yana wani rikicewa kamar wacce tayi accident da ya tawarwatsa ta.” Amal kuwa tana kwance tana ɗan motsa idanu. Tana jin yadda Maleekh yake ƙara tada hankalin kowa a asibitin saboda ita. Duk da zafin da take ji a hancinta da lebenta, dariya na ƙoƙarin ƙwace mata saboda irin yadda yake nuna tsantsar ƙauna... Sai dai ita ta kasa furta komai, sai ta matse hannunsa wanda yake riƙe da nata. “Amal,” ya faɗa cikin rawar murya, yana lumshe ido, “wallahi babu wani da zai sake cutar da ke a gabana. Ko ƙwayar jini ɗaya naga ya zubo, sai na tabbatar da an biya mun kuɗin ta da rayuwarsa.” Nurses suka kalli juna da murmushi marar sauti, ɗaya tana faɗi a ƙasan baki: “Wannan ai soyayyar da ta wuce ƙa’ida ce. Don lips da hanci sun ɗan fashe, sai kamar za'a tashi duniya...” Amal bata san lokacin da dariya ya kuɓce mata ba. Duk ciwon da take ji, sai ta kasa daurewa ganin yadda Maleekh yake ta surutai yana korafi ga doctors da nurses tamkar an kawo mace da tayi mummunan accident. Ɗaya daga cikin nurses ta kalli Amal tana murmushi tace: “Kin ga dole kiyi dariya, wannan ciwon naki fa bai wuce aje chemist a ɗauko maganin hanci da lips balm ba. Amma gashi an tada mana hankali.” Doctors ma suka murmusa, suka shiga kallon Maleekh da mamaki. Maleekh ya yi saurin hararar Amal yana faɗin: “Au, dariya ma kike yi ko? To ki ci gaba, amma wallahi idan baki warke ba, sai nayi wa dukkan likitocin nan rigima.” Amal ta cigaba da dariyar cikin hawaye, zuciyarta na ƙara narkewa da yadda yake nuna tsantsar damuwa da ƙauna. Bayan sun goge mata jinin hanci da lips ɗinta da auduga, aka ɗora mata maganin ointment kaɗan, suka ce shikenan. Maleekh ya zuba musu ido yana faɗin: “Shikenan fa ku ka ce? Wannan kawai kuka iya yiwa matar da zuciyata take kanta? Wallahi bana jin daɗin yadda kuke sakaci da aikin ku.” Doctors suka yi shiru suka cigaba da rubuta prescription ɗin magungunan da za a siya. Amal kuwa ta tashi tana dariya tana riƙe da hannunsa. Haka suka fita daga ɗakin emergency kamar wacce aka yiwa babban tiyata. 😅 Maleekh da Amal suna fita daga emergency suka hangi Ammy tana nufar wani side na marasa lafiya, women ward. Suka zuba mata ido, tare da bin bayanta, domin sun tabbatar Farha tana kwance a cikin wannan hospital. Bayan Ammy ta shiga room ɗin da aka kwantar da Farha, sai ga Maleekh da Amal suma suka shigo. Farha a wannan lokacin tana zaune akan gado, jikinta ya ɗan warware sosai. Ganin Maleekh ya sa ta tsure, jikinta ya fara rawa, zuciyarta ta faɗi rasss. Tasan ba ƙaramin hukunci zai yi mata ba kan laifin kulle shi da tayi har tsawon sati uku. Ammy kuwa ganin Amal yasa ta tunzura, ta ɗaga murya cikin fushi tana faɗin: “Waye ya bada izinin sako ki daga police station?..” Maleekh ya yi saurin cewa cikin tsawa: “Nine!” Ammy ta zuba masa ido cike da mamaki, zuciyarta cike da takaici. Ba ta taɓa tsammanin ɗanta zai tsaya a gaban idonta ya kare wata mace irin haka ba. Sai kuma ya juyo da hancin fushinsa kan Farha. Kallo ɗaya ya yi mata, sai jikinta ya fara rawa. A tsawace ya ce. “Wa ya baki izinin kulle ni a ɗaki?” Shiru tayi, tana sunkuyar da kai. Maleekh ya darara mata tsawa, har Ammy da Amal suka zabura da tsoro. “Magana nake miki! Ko baki da kunne?!” Cikin rawar murya, Farha ta ce da kyar: “Babu…” Maleekh ya ci gaba da magana, zuciyarsa kamar wuta: “Amma ban taɓa sanin ke daƙiƙiya, jahila, banza jaka marar class ba, sai yau. Wacce kwakwalwarta datti ya cika. Shin a tunaninki, a haka zan aure ki? To wallahi ko mata sun ƙare a duniya, bazan taɓa aure ballagaza irinki ba. Na tsane ki Farha, na tsane ki da zuciya ta gaba ɗaya! Kuma ki tabbata, daga yau zaki tattara ki koma can gaban iyayenki. Bazaki cigaba da zama a gidan mu ba!” Farha ta riƙe ƙirjinta tana rawar jiki, hawaye suka fara sauƙa a idonta. Ammy ta tsaya dafe da goshinta, tana mamakin irin kalaman da ɗanta ya zuba wa Farha a gaban Amal.. Amal kuwa tana tsaye a gefe tana kallon Maleekh, zuciyarta na tafarfasa da soyayya da alfahari da irin yadda yake tsaya mata. Farha ta riƙe kirjinta tana rawar jiki, hawaye na zuba kamar ruwan sama. Tana faɗin cikin kuka: “Don Allah kayi haƙuri Ya Maleekh… Na yi kuskure ne saboda sonka… Wallahi sonka ya rufe mun ido… Na rasa tunani saboda kai…” Maleekh ya yi wani tsaki mai ƙarfi, idonsa jajir kamar wuta. “Sonka fa kike cewa? Wannan abin kunya da kika yi ne soyayya? Kulle ni cikin ɗaki kamar zakin da aka saka a keji? Ki hana ni zuwa masallaci? Ki hana ni aiki? Ki hana ni zuwa ga masoyiyata? Wannan ba soyayya bace, hauka ce, haukar banza!” Farha ta fara matsawa baya tana girgiza kai, hawaye na kwaranya. “Wallahi ban yi nufin cutar da kai ba…” Maleekh ya katseta da cewa “Karya kike! Ba wai cutar da ni ba kawai kika yi ba, kin cutar da Amal! Kin je gidanta, kin je kin tada mata hankali, kin saka mata fargaba, har kin sa aka ɗauke ta zuwa police station saboda sharrinki! Yanzu ki gaya min, menene laifinta? Menene kuskurenta da za ki wahalar da ita haka?!” Farha ta kasa magana, tana kallonsa da idanuwanta da suka kumbura da kuka. Maleekh ya matso kusa da ita, muryarsa ta sake kaɗawa cikin ɗaki: “Na rantse da Allah Farha, kin gama da ni. Kada ki sake furta sunana, kada ki sake bibiyata, ka da ki sake kusantar Amal. Wallahi idan kika sake kusantar ta ko da a mafarki ne zan sa kiyi kuka na gaske. Na gama da ke, kuma kema kin gama da ni!” Farha tana kwance a gado, tana ɗaure da drip. Maleekh yana tsaye da fuskar ɓacin rai, yana ɗaga murya: Ya ci gaba da faɗin “Farha! Yanzu na gane baki da hankali ne ko kaɗan, Wannan wautar takin tasa kin zubar da mutuncina. Kin raina ni saboda me?” Yana nuna ta da yatsa cikin hargowa. Farha ta runtse idonta, ta kasa magana.. Ammy ta katse shi a fusace “Maleekhhh!!!” Ɗakin ya ɗan ɗauki shiru. Kafin ya ankara Ammy ta zabga masa mari mai ƙarfi. Ammy tana faɗin “Kada ka sake ɗaga mata murya haka! Ka manta marar lafiya ce? Ka manta asibiti muke? Maleekh bana son wulakanci irin wannan!” Ta tsaya tana huci. Maleekh ya dafe kuncinsa yana kallonta da mamaki. Ammy ta cigaba da cewa “Ka sani yau, auranka da Farha ba fashi! Babu wata Amal da za ka aura! Wannan yarinya ta kulle ka ne saboda soyayya, ba saboda ƙiyayya ba!” Farha ta fara kuka cikin rauni. Sai a nan Doctor ya shigo da file a hannunsa, ya tsaya daga bakin ƙofa, yana kallon hayaniyar. Doctor a tausashe ya ce “Excuse me… kuyi hak’uri. Wannan asibiti ne, akwai majinyata da basa son hayaniya..” Suka yi shiru. Sai Doctor ya juya ya kalli Farha, sannan ya buɗe file ɗin. Doctor cikin girmamawa da muhimmanci ya ce “Yanzu dai za mu faɗa muku ainihin matsalar. Dalilin da yasa Farha ta faɗi dogon suma saboda ƙaramin abu shi ne, jikinta ya raunana… saboda tana amfani da wasu miyagun kwayoyi na maye.” Ya ɗan ja numfashi. Sannan Doctor ya cigaba da faɗin “Mun gano tana shaye-shaye kafin rikicin ya faru. Wannan shi ne ya jawo suma, kuma idan ba’a kula ba, yana iya fara taɓar mata kwakwalwa. Don haka ku sani, matsalar tana da girma sosai.” Ɗakin ya ɗauki shiru. Ammy ta yi diri-diri tana kallon Farha. Maleekh ya zaro ido, ya kasa magana. Farha ta rufe fuska da hannunta tana kuka. Maleekh a firgice ya tsaya cak sannan ya ce “Shaye–shaye??” Ya runtse ido yana jin tamkar asibitin ya juye akansa. Ammy ta ce “Wannan ba gaskiya bane! Ba zai yiwu Farha ke shan miyagun kwayoyi ba! Doctor, ka tabbatar da abinda kake cewa kuwa?!” Doctor cikin nutsuwa ya ce “Mun tabbatar, ta sha kafin rikicin ya faru kuma ta daɗe tana sha. Wannan dalilin ne yasa jikinta ya raunana da sauri, kuma suma ta tsawon lokaci fiye da yadda ake tsammani.” Farha ta fashe da kuka tana girgiza kai: Fcikin kuka take faɗin “Wallahi ba da son raina nake sha ba… wallahi! Na shiga cikin wannan abu ne saboda matsin rayuwa… saboda… saboda nake jin bana da kowa sai soyayyar Maleekh. Amma na kasa daina…” Ammy ta dafe kirjinta cikin tashin hankali ta ce “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un! Farha… shaye–shaye kuma?!” Ta matso kusa da Farha tana riƙeta, amma a fili tana jin kunya da takaicin halin da Farha take ciki...sannan tana tunanin idan iyayenta suka san da wannan maganar ya zata yi.. Maleekh ya nuna ta cikin fushi da zafi ya ce “Shiyasa kika kulle ni a ɗaki? Shiyasa kika jefa ni cikin tashin hankali? wannan itace ‘soyayyar’ da kike ikirari? Wauta da lalaci!” Ya juya kamar zai fita. Ammy da ƙarfi tana tsawatar masa ta ce “Maleekh! Idan baka amince da auren ta ba, ka sani ka karya mini zuciya. Wannan yarinya zata zama matar ka, ko da kuwa kana so ko baka so. Ka taimaka mata, ka gyara ta, ka ceci rayuwarta. Wannan shine nauyin ka a kanta.” Farha tana kuka sosai tana girgiza kai. Cikin kuka mai nauyi “Ban cancanci ka taimake ni ba Maleekh… amma wallahi bana so in rasa ka. Kai kaɗai nake da kai a duniya.” Doctor ya kalle su duka da tausayi, ya ja numfashi sannan ya ce “Idan har kuna so ku ceci rayuwarta, sai an saka ta a rehabilitation program. Idan ba haka ba… wannan al’ada zata ƙara tsananta, kuma tana iya zama tabin hankali gaba ɗaya.” Ɗakin ya sake yin shiru. Amal ta tsaya gefe tana kallon komai da idanu cike da hawaye, zuciyarta cike da tausayi da kuma rikici. Maleekh ya fice daga ɗakin cikin fushi, yana riƙe da kansa kamar zai fashe da kuka. Zuciyarsa cike da fushi, takaici, da ruɗani. Maleekh yana furta a ransa cikin zafi. “Ni aure da mai shaye–shaye? Wannan abin kunya ne, wulakanci ne! Ammy har ta mare ni saboda ta kare ta?!” Amal ta bi shi a baya da sauri tana ƙiran sunansa: Amal cikin tsoro da tausayawa ta ce “Maleekh… please, ka tsaya… don Allah ka saurare ni.” Ya tsaya cak, ya juya da hanzari, idonsa jawur saboda fushi da takaici. Cikin tsawa ya ce “Me kike so in saurara Amal? Ba ki ga halin da ake ciki ba?! Saboda an raina ni, a gaban mutane ake cewa in auri wacce take shaye–shaye! Za'a naɗa min ballagaza mai dattin shaye-shaye?!” Ya dafe bango, zuciyarsa tana tafarfasa. Amal ta matso kusa da shi da nutsuwa, ta ɗora hannunta a kan kafadarsa ta ce. “Na san wannan abu ya girgiza ka… amma ka kwantar da hankalinka. Idan kana son yin hukunci a yanzu, zai iya zama a cikin fushi. Ka bari ka nutsu kafin ka ɗauki mataki.” Maleekh ya kalleta sosai, kamar idanunsa za su cinye ta ya ce “Amal… ba ki gane bane. Ammy ta ce dole ne in aure ta. Ke fa? Kina nufin ke za ki zama a gefe…? laifin me kika yi da aka sa ki cikin wannan azabar?!” Hawaye ya taru a idon Amal, ta runtse ido tana jin nauyin kalmarsa. Amal a hankali, cikin murya mai rauni ta ce “Ban san dalilin da yasa duniya ta ɗora min wannan nauyin ba… Amma duk da haka, ina nan tare da kai. Ka tuna ka ce min ni matar da zaka aura ce. Wannan magana taka tana bani ƙwarin gwiwa, duk da abinda nake fuskanta.” Maleekh ya yi shiru. Numfashinsa yana nauyi, yana kallonta tamkar yana son ya rungumeta amma zuciyarsa tana cikin rikici saboda maganar Ammy. Sai ya ɗan matsa gefe, ya furta da ƙarfi: “Na rantse da Allah Amal, ko da meye, ba zan taɓa yarda a tilasta min auren Farha ba! Ko da hakan zai sa na yi gaba da mahaifiyata.” Ya ja numfashi ya wuce gaba yana tafiya cikin hanzari. Amal ta tsaya a wurin, idonta cike da hawaye...itama ta bi bayansa Maleekh ya shiga mota cikin hanzari, ya tada engine da ƙarfin zuciya. Fuskar sa cike da fushi, numfashinsa yana tsananta. Amal ta shige a gefensa, ta dafa ƙafarsa a hankali tana kallonsa. Shiru ne ya mamaye motar, sai karar AC da numfashinsu kawai ake ji. Amal ta juyo da nutsuwa tana kallon Maleekh. A hankali cikin murya mai rauni da ƙarfi a zuciya ta ce “Maleekh… akwai kalmar da ka furta ta yi nauyi a zuciyata.” Maleekh ya ɗan kalleta cikin mamaki, ya ce da ita. “Me na ce? Na fa yi magana ne cikin fushi Amal.” Amal ta ce “Ka ce koda hakan zai sa ka yi gaba da mahaifiyarka.” Ta ɗan sauƙe ajiyar zuciya, hawaye ya taru a idonta saboda nauyin kalmar. Amal ta ci gaba da cewa. “Maleekh, mahaifiya darajarta babba ce a rayuwarmu. Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce: ‘Ku bi uwa! Ku bi uwa!! Ku bi uwa!!! Har sau uku, sannan ya ce ku bi uba.’ Wannan ya nuna mana uwa ita ce ginshiƙin rayuwa, ita ce hanyar rahamar Allah gare mu. Allah Maɗaukakin Sarki ma ya umarce mu a cikin Alkur’ani: ‘Mu yi wa iyaye biyayya da kyautatawa, musamman uwa da ta ɗauki ciki da wahala, ta haife ka da zafi, ta shayar da kai da ƙauna.’ (Suratul Luqman: 14).” Ta ɗan kama hannunsa da ƙarfi. “Wallahi Maleekh, ko da mahaifiyarka ta yi kuskure, bai kamata ka furta kalmar gaba da ita ba. Ka yi haƙuri, ka nemi hanyar da zaka yi magana cikin hikima da ladabi. Wannan shi ne darajar da musulunci ya ɗora mana akan uwa.” Maleekh ya yi shiru. Hannunsa a kan sitiyari ya ɗan yi sanyi, zuciyarsa ta fara raguwa daga zafin da take. Ya kalli Amal cikin mamaki, yana ji kalmarta tana shiga zuciyarsa kamar ruwa mai sanyaya wuta. Maleekh a hankali ya furta. “Amal… kin yi gaskiya, Kin tuna min darajar uwa, na ji a raina… Wallahi bana nufin in yi gaba da ita. Fushin ne kawai ya rinjaye ni.” Amal ta yi murmushi mai taushi, ta share hawayenta sannan ta ce “Haka nake so na ji daga gare ka. Fushi baya ƙara mana komai sai haɗari. Amma idan ka daidaita kalmomin ka da addini ya koyar mana, zaka kasance cikin nasara. Ka roƙi Allah ya yi maka jagora wajen kyautatawa uwa da yin adalci tsakanin soyayyata da ita.” Maleekh ya ɗan kai mata hannu ya kama nata da ƙarfi, yana jin zuciyarsa ta yi sanyi sosai. Ya ce “Na gode Amal. Zan kiyaye kalamaina. Kuma zan nemi hanyar da ba zata cutar da ke ba, ba kuma zata ɓata wa uwa zuciya ba.” Suka cigaba da tafiya, kowannensu yana jin wani irin salama a zuciya. A ƙarshe motar ta tsaya a kofar gidan Amal. Amal ta sauƙa cikin nutsuwa, ta juya ta sake kallon Maleekh. Ta ce cikin sanyin murya “Ka tuna… uwa ita ce aljannah ko wuta a gare mu...” Maleekh ya gyaɗa kai da ladabi, zuciyarsa cike da tunani mai zurfi... Maleekh ya dawo gida da dare, fuskar sa cike da nutsuwa duk da zuciyarsa tana ɗauke da zafi. Ya shigo falon da sallama cikin ladabi. Ammy tana zaune a kan kujera mai faɗi, tana jiran dawowarsa. Fuskar ta a ɗaure, ta ɗago kai ta kalleshi cikin tsananin fushi ta ce. “Maleekh! Kaje asibiti ka yi hayaniya, ka rufe wa mutane ido, ka ɓata mana suna. To yanzu, a nan gidan, ka gaya min gaskiya. Wannan miskilar yarinyar Amal ce ta rufe maka ido har ka yi min tawaye?!” Maleekh ya durƙusa a gabanta, ya dafa ƙafafunta cikin ladabi, yana kallonta da idanu masu cike da hawaye. “Ammy… bana son ɓata miki rai. Uwa ke ce ginshiƙina, ina girmamaki sama da komai. Amma wallahi Ammy, akan batun Farha, ina roƙonki ki fahimce ni. Bazan iya aurenta ba.” Ammy ta fizgi ƙafarta daga hannunsa cikin bacin rai tana ɗaga murya ta ce “Ka yi mun shiru! Kai ɗana ne, kuma kai ne farin cikina. Amma idan ka yi tawaye a kaina, kai da kanka zaka yi asarar wannan uwar takan. Aure ne da Farha, kuma dole ne! Ka ji ni kuwa?!” Maleekh ya haɗiye yawu, cikin ladabi ya ce “Ammy, ki gafarta mun. Ni ɗanki ne tabbas, ban isa in yi musayar yawu dake ba. Amma ki duba gaskiya da adalci, ki duba irin halayen Farha. Kin ga abinda ya faru a asibiti, kin ji da kanki likita ya ce tana shaye-shaye. Ina jin tsoron aure da mace irin wannan, Ammy. Wannan ba ƙiyayya ba ce, gaskiya ce.” Ammy ta yi shiru na ɗan lokaci, zuciyarta na tafasa. Sai ta juya ido gefe, tana jin kalamansa amma ta ƙi sassauta wa, ta ce “Ko shaye-shaye take, ni ce na ɗora ta a kanka. Kuma ni mahaifiyarka ce. Idan kana son ka nuna kana mun biyayya, to ka ɗauke ta da halinta. Idan ba haka ba… to ka sani, bana goyon bayanka akan Amal!” Maleekh ya lumshe ido, zuciyarsa na tsananin girgiza. Ya share hawayen da ya taru a idanunsa. “Ammy, zan yi biyayya a kanki akan duk wani abu. Zan baki girmanki da darajarki. Amma akan wannan aure… zan yi addu’a Allah ya sa ki fahimce ni. Bazan iya ɗaukar Farha a matsayin mata ba. Ki yi hakuri.” Ya durƙusa har kasa, ya gaisheta da kyau sannan ya miƙe cikin nutsuwa ya fice daga falon, zuciyarsa cike da nauyin kalmomin ta, kai tsaye part ɗinsa ya wuce.. Hospital – ɗakin da Farha take.. Washegari Ammy ta dawo hospital, ta shigo ɗakin da Farha take kwance, ta barta da Arfat ne akan ta taya ta kwana, bayan sun gaishe da Ammy, Ammy zama tayi a kujerar gefen gadon tana ɗauke da saƙon da zai girgiza zuciyar Farha.... Farha ta zaro ido tana jiran jin abinda Maleekh ya ce. Farha da rawar murya ta ce “Ammy… Yaya Maleekh fa? Yanzu ya yarda da aurenmu ko?” Ammy ta zauna kusa da gadon, ta dafa hannunta tana sauƙe numfashi ta ce “Farha, ki kwantar da hankalinki. Na yi magana da Maleekh. Yana girmama ni sosai, amma… akan aure… sai dai na ce miki, ya ƙi.” Farha ta zaro ido, zuciyarta ta buga da ƙarfi. Ta ce “Ya ƙi?! Ammy kina gaya min da bakinki cewa shi da kansa ya ce ba zai aure ni ba?! To wai ni waye zan Aura idan ba Maleekh ba? Me yasa ya raina ni haka bayan duk irin ƙoƙarin da nayi?!” Ta fashe da kuka tana bugun ƙirji, tana murɗa hannayenta. Ammy cikin lallashi ta ce “Ki natsu Farha. Na rantse, zan tilasta masa. Aure ba fashi. Kin ji na rantse. Maleekh ɗana ne, bai isa ya ƙi mun biyayya ba. Ki daina kuka.” Farha cike da tsananin fushi ta ce “Ammy ki saurara! Idan Maleekh ya ci gaba da bijirewa, sai na ɗauki fansa akan shi da waccan matsiyaciyar yarinyar Amal! Wallahi sai na nuna musu babu wanda zai yi min wulakanci a duniya!” Ta share hawayenta da hannun rigarta, idanuwanta suka canza launi kamar wacce take cikin hauka, tana ta huci da kishi da tsanar Amal... Ammy ta ɗan ja da baya tana kallonta da mamaki, zuciyarta na tunanin “Ko dai shaye-shayen nan ya fara shafar kwakwalwarta?” Arfat itama bakin ƙofa taje ta tsaya ganin yanda Farha take wani irin huci kamar mayunwacin kare... NEXT NEXT NEXT.... asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 29 to 30 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Ɓangaren Amal kuwa bayan ta koma gida.. Tana shiga cikin falon gidan da sallama, zuciyarta cike da gajiyawar rai, sai ga Inna da ke zaune tayi tagumi, idonta cike da hawaye. Da jin muryar Amal ta firgita, ta miƙe da sauri kamar za ta faɗi. Inna da kuka, ta rungumi Amal da ƙarfi tana faɗin “Alhamdulillahi, Alhamdulillahi! Na san ai dole Maliku ya karɓo ki daga hannun waɗancan ƴan sandan nan. Allah ya tsare ki, Amal na… Wallahi ina tsoron kada wani abu ya same ki!” Amal ta ji jikinta ya ɗan yi sanyi, ta rungumi Inna sosai kamar ƙaramar yarinya da ta dawo jikin uwa. Hawaye suna zuba daga idonta, tana goge wa Inna hawaye.. Ƴan aikin gidan da ke cikin kitchen suka fito da gudu, kowacce ta rungumi Amal, suka ce cikin farin ciki “Alhamdulillah! Mun yi kewarki Hajiya Amal! Kin dawo lafiya, mun gode wa Allah!” Falon ya cika da hawaye na farin ciki da godiya wa Allah, kamar ba su da abin da zasu ce sai “Alhamdulillah”. Amal ta zauna a kujerar falon, tana goge hawaye, ta dubi kowa da murmushi cikin kuka, ta ce: “Ku daina damuwa, ku kwantar da hankalinku. Ni dai Allah ya ceto ni, wallahi idan ba saboda Maleekh ba, da yanzu ban san halin da nake ciki ba…” Kowa ya jinjina kai, falon ya koma cikin shiru na tausayawa, amma a zuciyar Amal akwai wani irin nauyi da ƙuduri na cewa dole ta fuskanci wannan ƙalubalen da karfin imani. A can hospital kuwa.. An sallami Farha daga asibiti, an dawo da ita gida. ta shiga ɗakinta ta zauna Ammy itama ta shigo tare da zama a kusa da ita... Fuskar Farha cike take da damuwa, koda yake har yanzu akwai ɗan murmushi saboda farin cikin samun kulawar Ammy.. Farha ta ɗago ta dubi Ammy cikin raunin murya ta ce "Ammy, dan Allah yanzu ya zanyi in shawo kan Maleekh zuwa gare ni..? Kullum sai gudu na yake..." Ammy ta kalleta da idanu masu cike da ƙauna da kuma tsananin ƙuduri, ta kama hannun Farha tana shafa shi ta ce: "Ina so ne, Farha, nasa ranar baikon ku. Ba zan wani ɓata lokaci ba." Idon Farha ya cika da walƙiya na farin ciki, ta sau murmushi na jin daɗi, ta rungumi pillow tana jin kamar mafarki take, ta ce "Ammy, idan har da gaske haka ne, ai yana da kyau mu haɗa ranar baiko da ranar birthday ɗinsa. Kin manta kuwa? Jibi ne birthday ɗinsa..." Ammy ta yi dariya cikin jin daɗi, ta girgiza kai: "Taya zan manta shekarun yarona? Tabbas jibi zai cika shekara talatin cifff. A ranar birthday ɗin, bayan kowa ya taru, zan mayar da ita rana ta musamman ranar baikon ku ke da shi. Zan ƙira dangi, abokan arziki, har da iyayenki daga London." Farha ta zaro ido cike da murna, ta riƙe hannun Ammy tana murza shi tare da faɗin "Ammy, wannan fa bazai zama abin alfahari ba kawai, zai zama mafarkin rayuwata! Amma shi zai yadda da wannan baikon? Kinsan fa Ya Maleekh baya ƙaunata kamar yanda yake faɗa..." Ammy ta danne murmushi, ta yi ƙwafa, sannan ta jinjina kai cikin girmamawa da girman kai irin na uwa mai iko ta ce "Farha, ki bar wannan damuwar a hannuna. Zan tilasta shi. Daga yau za a fara shirye-shiryen birthday ɗinsa. Zan sanar masa ya fara gayyatar abokansa da sauran jama’a. Amma maganar baiko? Wannan sirrinmu ne. Ba za mu sanar masa ba sai a ranar birthday ɗin. A lokacin, babu yanda zai yi domin bazai iya bijirewa ba, saboda kowa zai taru, sai dai ya amince dole." Farha ta sake dariya cikin farin ciki, ta jingina kanta a kafaɗar Ammy tana furta cikin sirri: "Ammy… kina da hikima sosai. Wallahi ina sonki da zuciyata dukkaninta." Ammy ta shafa gashinta a hankali, tana murmushi mai cike da annashuwa ta ce "Ni ma ina sonki, ƴata. Ki kwantar da hankalinki. Jibi rana ce da ba za ki taɓa mantawa da ita ba." A haka Farha ta kwanta saman gado tana ta tunanin yadda wannan ranar zata zame mata babban nasara, zuciyarta na cike da mafarki da buri. Ita kam Ammy kuwa, zuciyarta na daɗa ƙarfafa cewa zata cimma burinta na ganin ɗanta ya auri Farha, ko da kuwa hakan ba da yardarsa ba. Bayan Ammy ta bar ɗakin Farha, part ɗin Maleekh ta nufa... Tana zuwa ta fara knocking, a hankali yazo ya buɗe mata... Ta shiga sannan ta zauna akan sofas falonsa, ta bashi umarnin ya zauna kusa da ita, shima zama yayi, Ammy ta riƙe hannunsa tana murmushi ta ce "Suprise my son.." Maleekh yace "Suprise ɗin me?.." Ammy ta ce "Jibi birthday ɗinka, za'a haɗa dinner party na musamman, zan sa a shirya mana hall mai girman gaske, a shirya komai zuwa jibi.." Maleekh ya ce "congratulation to me.." Ammy ta ce "Inaso ka gayyato abokanka na kasashen waje dana nan Nigeria....sannan iyayen Farha zasu zo daga London.." Maleekh ya ce "Shikenan idan sun zo, sai su ɗauki ƴarsu su tafi da ita, domin bazata lalace da shaye-shaye anan gaban mu ba, mutane zasu ce don ba ke kika haifeta ba shiyasa kika barta ta lalace, kinga daga shaye-shaye zata fara bin maza..." Ammy ta ce "Ya isa haka Maleekh, dan Allah kada idan iyayenta sun zo ka nuna musu ƙiyayyar da kake yiwa ƴarsu.." Maleekh ya jinjina kai yana kallon gefe.. Daga nan Ammy ta fice a ɗakin ba tare da ta sanar masa maganar baikonsa da Farha ba... Washegari Ammy ta sa an fara shirye-shiryen party birthday ɗin Maleekh... RANAR BIRTHDAY DINNER, PARTY NA MALEEKH An kai ga ranar da Ammy ta sha alwashin ta zamarwa ɗanta suprise. Tun daga safe gidan ya cika da hayaniya da shirye-shirye. Ana shiga ana fita, an ɗauko masu kwalliya, decorators, caterers, DJs, da security. An zaɓi Hilton Event Center a cikin Abuja, hall ɗin da aka san shi da girma da walwala. Aka kawata wurin da gold da white. Daga ƙofar shiga har zuwa ciki, aka shimfiɗa red carpet, tare da golden lights da balloons masu kyau. A tsakiya an kafa manyan LED Screens suna nuna hotunan Maleekh tun yana ƙarami har zuwa girmansa. A gefe kuma aka kafa photo booth da aka rubuta: ✨ “Maleekh @30 – The King’s Birthday Dinner” ✨ An shirya teburori masu kyau da gilashi mai ƙyalli, aka sa fresh roses da candles a tsakiyarsu. Kowa da aka gayyata yana samun invitation card mai golden foil, saboda VIP event ne. Lokacin da manyan baƙi suka zauna, aka kunna background music. Aka kashe wutar hall ɗin gaba ɗaya, sai fitilu masu colour suka fara haskawa. Sai jin ƙarar horn ɗin motor daga wajen hall, alamar cewa Lamborghini Urus mai launin black-gold ta iso. Security masu baƙin suits suka buɗe masa hanya.. Cameramen ne suke ta ɗaukar hotuna, dron ɗin sama yana capturing cinematic entry ɗinsa. Maleekh ya fito cikin royal tuxedo mai launin navy blue da golden tie, yana tafiya a kan red carpet kamar sarkin da ake masa coronation. Duk hall ɗin ya tashi da tafi da murna. PROGRAM ENTERTAINMENT MC (AY) ya ɗauki mic yana yiwa kowa barkwanci cikin annashuwa... Sai kuma DJ mai suna DJ Neptune ya saka kiɗa mai armashi. Live Band suka fara rera waƙa domin Maleekh, suna cewa “Happy Birthday, The King @30”. An yi special dance presentation daga ƙungiyar rawa cikin uniform mai kyau. Wani celebrity singer, Davido, ya rera waƙa ta musamman domin bikin birthday... Bayan shagalin farko, aka buɗe buffet. An kawo abinci kala-kala: Nigerian Dishes: jollof rice, fried rice, tuwo da miya. Intercontinental: Chinese noodles, pizza, pasta. Seafood section: prawns, shrimps, lobsters. Dessert corner: ice cream, chocolate fountain, cake slices, da fruits carving. Drinks kuma kala-kala: mocktails, cocktails, champagne popping, har da tiger nuts da zobo ga masu avoiding alcohol. (Kan bala'iiii har da ni a wurin cin Abinci domin mu acici ba'a barin mu a baya🤣🤣) BIRTHDAY CAKE An shigo da cake mai layers 7, mai launin gold da white, wanda aka kawata shi da diamonds designs. A kan cake aka rubuta 🎂 “Happy 30th Birthday, Maleekh The King” 🎂 Maleekh ya yanka cake tare da Ammy da Farha a ɗayan gefensa, aka kunna fireworks a cikin hall... Bayan an gama didimar Birthday sai kuma SURPRISE ANNOUNCEMENT 😳😳 Bayan kowa ya zauna cikin farin ciki, Ammy ta miƙe tsaye da mic a hannunta. Tana murmushi cikin nishaɗi, ta ce: “Alhamdulillah. Yau rana ce ta farin ciki a gareni da iyalaina. Na ga ɗana ya kai shekara 30, kuma Allah ya yi masa arziki, lafiya, da daraja. Amma wannan ba kawai birthday bane…” Kowa a hall ɗin ya ɗaga kai cikin mamaki. “…bayan birthday sai kuma ranar baiko a yau. Ina farin cikin sanar da ku cewa yau ɗana, Maleekh, zai ɗaura baiko da Farha.” Hall ɗin ya ɗauki ihu da mamaki. Wasu suka tashi tsaye suna tafi, wasu kuma suka dubi Maleekh da ido domin ganin yanda zai yi, shin da son ransa ne ko kuma Suprise ne kamar yanda aka sanar.. Maleekh ya tsaya cak kamar wanda aka yi masa sihiri. Bai taɓa tsammani wannan ba... Amal tana zaune a falonta, falon da aka kawata cikin nutsuwa da kyan gida na zamani. Wani ƙaramin flower vase ke tsakiyar table, TV ɗin da ke manne a bango kuwa na nuna live cinema broadcast na taron da Ammy ta shirya domin ɗanta. Amal na zaune ne gefen sofa tana cin abinci a hankali, sai kawai ta ji jawabin Ammy....zaro ido tayi tana kallon TV daga baya MC a hall ɗin ya nanata da cewa: “Ladies and Gentlemen, please rise and welcome… Farha & Maleekh the couple-to-be tonight!” Amal ta zabura! Abincin hannunta ya zube ƙasi, kofin drink ɗinta ya biyo baya ya zube a tiles. Hannayenta suka fara rawa, zuciyarta na bugawa kamar zata fito daga kirjinta. Ta miƙe da sauri, idanunta sun cika da hawaye tana faɗin: “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un… baiko? Baiko kuma Maleekh da Farha? Maleekh ya yaudare ni?” Ta kai hannu kan zuciyarta tana jin wani irin bugawa da ciwo. TV ɗin na nuna Farha cikin wata farar riga mai tsada, rigar da aka kawata da diamonds stones masu walƙiya. An zaunar da ita kusa da Maleekh a kujerar da aka tanadar musu. Farha ta yi kyau sosai, tana murmushin alfahari, kamar wacce ta ci nasara. Iyayenta daga London suma suna zaune a gaba cikin kujera ta musamman, suna ta tafa hannu cike da jin daɗi da alfahari. A gefe kuma aka nuna A’isha ƙawar Amal daga Kaduna tare da mahaifiyarta wato kishiyar Ammy, da ƙannenta mata biyu. Sai camera ya nuna Ammy na nuna rashin jin daɗinta, ta ƙarasa wurinsu Mahaifiyar A'isha tana habaici tana cewa: “Meya kawo ku wannan shagali? Ai ban gayyace ku ba, kuma ku ka zo. Amma dai ku zauna ku gani, wannan baiko ne da ba ku isa ku hana ba.” Amal ta ɗan ja da baya, tana tari sakamakon kwaruwar da tayi, ta ɗauki ruwa ta kora, hawaye na silalowa. Tana faɗi da ƙarfi: “Wallahi ba haka ba ne! Taya Maleekh zai mun haka? Kenan yasan da maganar baiko shine ya bani card ɗin gayyata da hannunsa...kuma ya zauna tare da ita?” Ta fashe da kuka, zuciyarta na tafarfasa. Sai ta ji ƙarfin zuciya ya shige ta. Ta fice daga gidan ba tare da ta shirya ba. Babu gyaran kai, babu kwalliya, babu mayafi mai kyau. Kawai ta ɗauki jakarta ta rataya a kafadarta..Ta riƙe wayarta da ƙarfi a hannu ɗaya, ta zura takalmin slippers, ta fita da gudu kamar wacce zuciya take tura ta. A HALL ƊIN TARON Maleekh kuwa, duk da cewa yana zaune kusa da Farha, gaba ɗaya jikinsa a takure yake. Idanunsa na yawo cikin hall ɗin yana kallon ko'ina domin duba ko Amal tazo.. Ya roƙe ta akan tazo, yana zaune sai kuma ya tuna lokacin da ya bata VIP invitation card yana ce mata: “Amal, koda duniya zata yi gaba dani, kin zama wata ta musamman a rayuwata. Kawai ki kasance tare da ni ranar, zan gabatar dake a matsayin masoyiyata..." Amma yanzu babu ita, babu kamshinta, babu murmushinta. Zuciyarsa ta cika da baƙin ciki. Abokan sa na gefe suna ta murna, suna tura masa cup na wine suna cewa: “Happy Birthday King Maleekh!” Amma kwata-kwata baya jin daɗin wannan ranar. A ransa yana cewa: “Ina Amal? Me yasa bata zo ba? Ko kuwa an dakatar da ita ne? Ko… bata ɗauki rayuwata da mahimmanci ba?” Ya ji ransa yana tafarfasa, amma bai nuna wa kowa ba... ☆☆☆☆ A wannan lokacin Amal na ta gudu tana ƙiran taxi. Taxi ɗin ya tsaya, ta shige ciki tana hawaye. Ta ce “Driver, please… Hilton Event Center… yanzu yanzu, kayi gudu!” Driver ya dubeta ta madubi, ya ga fuskarta cike da hawaye. Ya ɗaga kai kawai ya ce: “Okay madam.” Motar ta yi saurin tafiya cikin titunan Abuja da fitilun titin ke walƙiya. Amal ta jingina kanta jikin glass, hawayenta na gudu tana faɗin a hankali: “Ya Allah ka bani ƙarfin zuciya. Wallahi idan na shiga hall ɗin, Allah kada ka bawa Maleekh damar da zai amince da baikon nan....” Wurin nada nisa da gidan Amal, hakan yasa har yanzu bata iso wurin ba. A hall kuwa ana kan gudanar da wani wasa. An tayar da Maleekh tsakar filin, aka ɗaura masa farin kyalle a idonsa. Wani wasa ne irin na masu kuɗi, sunan wasan dumi-dumi tsakanin ƙawayen Farha, manyan ’ya’yan masu kuɗi... Ka’ida: Maleekh zai rinƙa tafiya a hankali, ido a rufe, hannunsa a miƙe. Duk wacce hannunsa ya sauƙa a kanta, ita ce za suyi rawa tare a gaban jama’a. Shi kuma Maleekh ya tsare fuskarsa da ɗan murmushin dole. A ransa kuwa ba ma wasa yake so ba, ba kuma baiko da Farha yake muradi ba.... Sai dai abokansa da suka fahimci akwai damuwa a tattare dashi sai suka fara lallamin shi akan kada ya nuna rashin jin daɗinsa a bainar jama’a, kada ya kunyata iyaye, kada ya lalata yanayin shagalin. “Ka bari komai ya wuce, daga baya sai kayi komai,” suka shawarce shi... Sai ya yarda da haka, ya fara tafiya a filin, ido a rufe, yana miƙa hannu, yana neman wanda zai kama. ’Yan matan a gefe kuwa suna tsalle-tsalle da dariya, suna ɓuya suna ƙara motsa nishaɗi. Jama’a suna ta tafi suna dariya. A gefe kuwa mahaifin Maleekh na zaune, fuskar sa cike da farin ciki da alfahari da ɗansa, yana ta jinjinawa taron. A wannan lokaci ne Amal ta iso. Ta nuna card ɗin da Maleekh ya bata tun farko, security suka dubeta, duk da shigar ta ba ta masu kuɗi bace, sai suka barta ta shiga. Tana sanye da doguwar riga, kanta babu gyaran salo irin na taro, ƙafarta sanye da slippers. Hasken fuskarta da kamalarta sun bambanta ta a cikin jama’a. Da ta shiga, idonta ya sauƙa kan Maleekh da aka ɗaura masa farin kyalle a idonsa. Yana yawo cikin filin, yana wurga hannu yana neman kama wata. Zuciyarta ta buga. Bata tsaya tunani ba ta ruga da gudu ta nufi tsakiyar filin, zuciyarta na tafasa da niyyar kada a aikata abinda zuciyarta zai buga... Kafin ta yi wani abu, sai ga hannun Maleekh ya cabke ta!.. Lokaci guda ya ji wurin yayi tsittt, ba dariya, ba ihu, ba tafi....ganin haka yasa ɗayan hannunsa ya cire kyallen da aka ɗaura masa, ɗayan hannun kuma yana riƙe da kafaɗar Amal... A nan idonsa suka haɗu da nata. Tsitttt! Wurin ya yi shiru! Kowa ya dakata da numfashi, idanun kowa ya sauƙa kan kyakkyawar fuskar Amal wacce bata daga cikin ’yan matan masu kuɗin.... Wata nutsuwa ta bayyana a idanun Maleekh lokacin da ya gane yana riƙe da hannun Amal ne.. A gefe kuwa Farha da aka zaunar da ita a kujera ta miƙe da zafin rai, fuskarta ta canza daga farin ciki zuwa baƙin ciki, zuciyarta tana tafasa da haushin wannan yarinyar da ta kutsa musu wasa... Ammy kuwa ta kaɗa kai a fusace, tana hararar Amal, zuciyarta cike da ɓacin rai, tana jin kamar Amal ta zo ta ɓata musu shiri a gaban iyayen Farha da kowa da kowa... Sai dai A’isha, ƙawar Amal, na cikin jama’a. Ganin Amal ya sanya ta tashi da farin ciki, tayi dariya da tafi tana goyon bayan abokiyar tata...A fusace Ammy ta juyo ta kalle ta tana hararar ta kamar idanu zasu faɗo, ai ba shiri A'isha ta zauna tare da nutsuwa, domin a wurin iya tafin ta ne kawai ya ratsa kunnuwan kowa... (Ina Amaleekh fan's readers, shin ya ku ka a wannan lokacin?😅😅🫣) MC, wanda bai san komai game da Amal da Maleekh ba, ya ɗauka wannan al’ada ce ta wasa. Shi ma sai ya nufi mic ɗin ya ce da murya mai ƙarfi: “Alhamdulillah! An samu wacce aka kama. Yanzu kuwa babu sassauci tare zasu yi rawa!” Sai ya ƙira DJ ya kunna kiɗan rawa.. Kafin a sake DJ, Farha ta daka uban tsawa cikin zafin rai, ta ɗaga hannu faɗin “Ku dakata! Ba wani rawar da za a yi a nan. Wannan yarinya ai ba kowa bace face wata matsiyaciya ballagaza! Bata daga cikin mu, wai ita a dole son Ya Maleekh take. ta ƙuduri aniyar cewa sai ta mallake shi!” Jama’a suka ɗaga kai, wasu suka yi tsit suna kallon abin da zai biyo baya. Amma kawayen Farha da ’yan uwanta kuwa, sai suka kwashe da dariya, suna nuna Amal da hannu, suna yi mata kallon ƙasƙanci da raini... “Shine zata shigo cikin mu? Ni kam ba zan taɓa yarda ba!” wata daga cikinsu ta faɗa tana harararta. Sai dai abokan Maleekh ba duka suka ji daidai da wannan kalaman ba. Wasu daga cikinsu suna kallo suna murmushi, suna ganin Amal da gaske ta dace da Maleekh. A idanunsu, kyawunta ya wuce kima, kyakkyawa ce mai tsarin halitta, idan dai ta samu kuɗi kamar nasu, to ba ƙaramin daraja za ta samu ba. Amma kuma wasu daga cikinsu sun fi son ganin auren ɗan mai kuɗi da ’yar masu kuɗi kawai. A ransu suna faɗin: mai kuɗi sai mai kuɗi, talaka kuma sai talaka... A lokacin ne Maleekh ya ɗaga hannunsa ya nufi jama’ar wurin da murya mai ƙarfi, yana kallonsu da idanu masu ɗauke da ƙarfin gwiwa, yana faɗin “Wannan itace zaɓi na. Ita zan aura! Baikon da aka yi mini da Farha na soke shi yanzu nan a gaban kowa, domin bana ƙaunar ta. Abin da nake so shi nake faɗa a nan gaban duniya. Kuma wacce kuka gani a gabana, Amal itace tarihin rayuwata.” Ya juyo yana duban MC kai tsaye, fuskarsa babu annuri sai da ƙuduri ya ce “Kada mu ɓata lokaci. DJ, saka mana waƙa irin ta masoya. Yanzu haka, wannan ita ce rawar zuciyata.” MC ya tsaya kallonsa cikin razana, amma ganin ƙarfin da kalaman suka ɗauka sai ya ɗaga hannu ya bada izini. DJ ya kunna waƙa, kiɗa ya cika hall ɗin. Maleekh ya matso kusa da Amal, ya kama hannunta cikin girmamawa, sannan ya fara jujjuya ta cikin kiɗan... Jama’a suka yi shiru na ɗan lokaci, kafin wasu daga cikin abokansa suka kwad'a uban tafi suna ihu cikin farin ciki. “Ya dace da ita wallahi! Su biyu sun yi kyau sosai!” wani daga cikinsu ya furta cikin jin daɗi. Amma daga bangaren ’yan uwan Maleekh kuwa, babu wanda ya nuna goyon baya. Fuskar su tamkar an sassaka ta cikin dutse, babu murmushi, babu farin ciki. Ammy kuwa ta zauna cak, zuciyarta kamar zata fashe. Wani irin baƙin ciki ya lulluɓe ta, har kowa ya lura da fuskarta ta kumbura sosai.. Abbah, mahaifin Maleekh, ya miƙe ya fice daga hall ɗin da wayarsa a kunne, kamar yana yin waya. Ba wai saboda bai goyi bayan ɗansa ba, a’a, kawai ya fita ne saboda gudun zargin jama’a. Bai son mutane su yi tunanin shi ne ya sa Maleekh ya nuna adawa da Farha. Amma a ransa ya yi murmushi, domin shi ya fi son ɗansa ya zaɓi wacce yake so. Iyayen Farha kuwa, fuskar su ta canza gaba ɗaya. Zuciyoyinsu sun cika da haushi da ƙasƙanci, suna ganin an tozarta ’yarsu a bainar jama’a. Amal kuwa, duk da cewa tana tsaye a hannun Maleekh tana rawa da shi, gaba ɗaya jikinta ya mutu da tsananin kunya. Bata saba irin wannan ba, musamman a gaban jama’a da suka zuba mata ido. Tana jin kamar ƙasa ta buɗe ta shige tsabar kunya.. Amma Maleekh ya riƙe ta da ƙarfi, yana jujjuya ta da murmushi tamkar yana so ya tabbatar wa duniya cewa babu mai iya rabasu.. Maleekh ya ɗauki Amal da hannunsa biyu kamar wani gwani a rawa, ya juyo da ita cikin natsuwa, idanunsa suna ƙafe a nata. Kowa ya gane ba wai rawa ce kawai yake yi ba, kamar yana furta wata soyayya ce ta cikin zuciyarsa, yana sauƙar da ita cikin tafin Amal... Kiɗan ya ƙara ɗagawa, MC na ihu da dariya yana ƙarfafa jama’a: “Ladies and gentlemen, ga masoya a gaban ku! Let’s give them a big round of applause!” Sai kuma aka ji wani irin sautin tafi daga cikin abokan Maleekh, wasu daga cikinsu har ihu suka fara yi suna kwatanta irin soyayyar nan da suke gani.. “Amal and Maleekh forever!” wani ya faɗa yana dariya. Amma a gefe guda kuwa, ’yan uwa da dangin Maleekh suka ƙara jinjina kai da kaɗa hannaye. “Wannan abin kunya ne a bainar jama’a ɗan hamsha'kin mai kuɗi yana rawa da matsiyaciya ƙasƙantacciyar talaka, wacce take sanye da slippers a ƙafarta..,” wata daga cikin dangin Ammy ta furta a hankali tana huci... Ammy kuwa ta kasa ɓoye haushinta, tana zaune a kujerarta tana jijjiga ƙafafunta da sauri kamar wacce zuciyarta ke ƙoƙarin tsallewa daga kirjinta. Wani lokaci tana kallon Farha, wacce ta tsaya tana huci kamar za ta cinna wa kanta wuta. Idanunta sun cika da hawaye.. Abbah a wajen da ya fita, ya tsaya a bakin kofar hall yana kallon cikin gilashin babban tagar hall ɗin. A zuciyarsa ya furta: “Da gaske yarona ya yi abin da zuciyarsa take so.” Sai ya yi murmushi a hankali, sannan ya ɗaga wayarsa ya ci gaba da maganar da yake yi da wani abokin business ɗinsa, kamar ba shi da wata damuwa... A gefe kuwa, iyayen Farha sun kasa ɓoye fushinsu. Mahaifinta ya miƙe yana kallon Ammy cikin ɓacin rai, ya ce cikin harshen turanci mai ɗauke da fushi: “This is a total disgrace! How could you allow this in public? My daughter deserves respect, not humiliation!” Ammy bata samu damar ba shi amsa ba, domin hankalinta gaba ɗaya ya tattaru wajen ganin yadda Maleekh ya ci gaba da juyawa da Amal kamar sarautar rawa ta dogara da su... Amal kuwa jikinta gaba ɗaya ya yi sanyi. Hannunta na cikin na Maleekh, zuciyarta na cike da nauyi. Idanunta sun rufe da hawaye masu kauri, amma tana ƙoƙarin ɓoye su domin kada duniya ta ga raunin da take ciki. Duk da haka, a zuciyarta tana jin soyayyar Maleekh na sauƙa gareta.. Sai ga wani irin danna haske da akayi a hoton bidiyon da ake nuna wa a babban screen, an ɗauki Amal da Maleekh suna rawa, aka ƙara slow-motion, inda Maleekh ya juyo yana kallonta da murmushi mai cike da alamar “na mallake ki.” Jama’a suka sake ɗagawa da ihu, wasu cikin sha’awa, wasu cikin mamaki, wasu kuwa cikin takaici. Wani daga cikin abokan Maleekh ya yi ihu: “Wallahi wannan shine birthday gift ɗin shekara! Baiko ya zama soyayya ta gaskiya!” Farha ta kasa jurewa, ta fice daga hall ɗin da gudu tana riƙe da rigarta, tana kukan kuka mai sauti... (Ai da nine Farha da tin farkon abun zan fice don kada zuciyata ta buga 🤣🤣)... MC kuwa ya rufe maganar da dariya yana faɗin: “Ladies and gentlemen, wannan shine soyayya! Ko dai a so aure, ko a mutu da ƙiyayya. Tonight, we have witnessed the beginning of a new chapter.” Maleekh ya matso kusa da kunnen Amal, ya yi mata raɗa cikin murya mai sanyi: “Na bayyana ki a gaban duniya, ko kina jin tsoron hakan?” Amal ta kasa amsawa. Sai kawai hawaye suka sauƙo daga idanunta, tana jin ƙaunarsa ta ƙara shige mata jiki. Live Broadcast Ba kawai hall ɗin da ke cike da hayaniya ba, hatta duk gidajen masu kallo a gida da wajen ƙasar nan suna kallon shagalin birthday ɗin Maleekh Live on Cinema. Gidan su Amal kuwa.. A falo, Inna tana zaune da masu aikin gida, su ma kallon suka kafa a babban TV plasma. Da suka ga Amal a hannun Maleekh, suna rawa a gaban kowa, gaba ɗaya gidan ya ɗauki ihun farin ciki. “Innalillahi! Amal ce a hannun Maleekh?!” Inna ta zabura tana dariya tana tafa hannuwa... Masu aikin gida suka kwashe da ihu: “Lallai wannan soyayyar ce ta gaskiya! Tab yau Farha zata haɗiyi ranta..!” Inna ta jinjina kai, tana murmushi ta ce “Allah ya albarkaci dangantakar ku, Amal… ai tunda duniya ta ga haka, babu mai iya raba ku...Sai dai tsorona kada su cutar mun da Amal..” ☆☆☆ Bayan DJ ya rage kiɗa, jama’a suka fara watsewa da surutai kala-kala. Wasu suna ta jinjinawa rawar soyayya. Wasu kuwa suna ɗaga ƙafa cikin fushi, musamman dangin Ammy. Abokan Maleekh na dariya suna jin daɗi, suna ɗaga wayoyinsu suna ɗaukar hotuna da bidiyo suna sakawa a social media. Bayan an dawo gida.. Farha ta rufe kanta a ɗaki tana zabga ihu tana wurgi da pillows. Mahaifiyarta tana buga ƙofar tana kuka tare da faɗin “Farha please open this door! Ki bari mu yi magana! Don’t kill yourself because of this boy!” Mahaifinta shima haka yake buga ƙofar da ƙarfi yana cewa “Open the door now Farha! Stop disgracing us more than this!” Sai kawai aka ji muryarta daga ciki tana tana faɗin “Na tsane shi! Na tsani Amal!! Wallahi bazan yarda da wannan wulakanci ba!” Tayi maganar cikin kuka.. Sunyi akan Farha ta buɗe amma taƙi, haka suka hak'ura suka koma falo.. Ammy tana zaune a sofas, Mahaifin Farha yana tsaye yana huci, ya juya ya kalli Ammy a fusace ya ce: “This is nonsense! Absolute nonsense, Maryam!” ya ce cikin ƙarfi... “You humiliated my daughter in front of the whole world! Do you know who I am in London? Do you know how many businesses I control? And today my only daughter was disgraced like this?” Mahaifiyar Farha ta karɓa da kuka tana faɗin: “Maleekh bai yi wa yarinyarmu adalci ba! Yaudarar mu kika yi, Ammy! Kin ce za su yi baiko, amma ki kalli yadda ya tozarta ta a gaban kowa. Wannan abun ba zai taɓa wucewa haka kawai ba!” Ammy ta riƙe kanta tana huci, zuciyarta cike da kunya..ta ce “Dan Allah kuyi haƙuri. Ni kaina ban san hakan zai faru ba… ni na shirya komai domin ku, amma ga shi abin ya juya.” Dake duk ƴan uwan juna ne, su a danginsu basa Auran na waje sai haɗin gida.. Abbah da Ammy haɗin gida ne domin su ɗin ƴaƴan baffanu suke.. Mahaifiyar Farha da Mahaifin Farha suma ƴan uwan juna ne, su kuma ƴaƴan kawunai ne.. Amma Ammy da Mahaifiyar Farha Yaya da Ƙanwa ne.. Hakan yasa suke yiwa ƴaƴansu Auren haɗin gida kamar yanda aka musu.. Abbah ne kawai da zai ƙara Aure na biyu yaje ya auro ta waje wato mahaifiyarsu A'isha, nan ma ansha rikici sosai, shiyasa Abbah bai wani takura Maleekh akan wacce yake so ba.. ☆☆☆ Abokan Maleekh kuwa duk Hotel suka kama kafin washegari su wuce.. Maleekh ne ya kai Amal har gida, sai da suka taɓa soyayya kafin yayi mata sallama... A wannan ranar Maleekh bai koma gidansu ba saboda yasan idan ya koma komai zai iya faruwa.. Kai tsaye hotel ɗin da abokansa suke nan yaje zai kwana dasu.. A hotel.. Suna cikin babban suite ɗinsu, ƙamshin shisha ya gauraye ɗakin. Ga ƙamshin turare ya cika ko'ina, duk suna kwance suna tafka dariya kan labarin da suka gani a TV. Maleekh yana zaune akan katifa yana pressing phone ɗin sa alamar chat yake.. Abokin sa Samir ya ce yana dariya: “Guy, wallahi kai ka bada show na shekara. Duk social media fa labarinka ne yanzu. Wallahi trending number one!” Wani daga cikinsu, Khalid, ya ɗaga glass yana dariya: “Bro, forget about Farha. Duk wanda baya son ku, ya mutu da haushi. Amal ce take da soyayyar gaske a idanunka, kuma ita za ta baka natsuwa. Kai dai ka tsaya kan maganarka, kada kowa ya juya maka zuciya.” Sauran abokai suka kwashe da dariya suna shan shisha, suna furta kalamai: “Wallahi Amal ce ta dace da kai, ba Farha ba. Ga ta da hankali, ga ta da ladabi. Kuma gaskiya soyayyarta ta fito karara a wurin rawa.” Maleekh ya lumshe idanu yana murmushi a hankali ya furta “Wallahi ban san me yasa amma idan Amal na kusa da ni, zuciyata tana samun kwanciyar hankali… Na yanke hukunci, ita ce zaɓina.” Abokansa suka ce gaba ɗaya: “Cheers to love! Cheers to Amal!” suka ɗaga cups ɗin lemon juice suna dariya, ƙamshin shisha da kamshin turarensu yana tashi.. ☆☆☆ Amal tana kwance a gida zuciyarta cike da farin ciki da tsoro lokaci guda... NEXT NEXT NEXTTT.... asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 31 to 32 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Washegari bayan shagali… Gidansu Maleekh bai taɓa yin shiru irin wannan ba, gida ya koma gidan makoki, Tun da gari ya waye nan ma ta ƙi buɗe ƙofa.. Mahaifinta sai kai kawo yake yana ta masifa. Cikin bacin rai, tinda gari ya waye yake yiwa Ammy bala'i tare da faɗin “This is nonsense! Absolute nonsense! How could your son, Maryam humiliate my daughter in public like that? In front of thousands… and even on live TV?! This is unacceptable!” Yana jujjuya kai cikin tsawa, duk falon sai rawar muryarsa ne yake tashi.. Ammy dai zaune kan kujera, idonta a ƙasa, zuciyarta cike da nadama. Ta kasa amsa wa, sai hawaye da ke makalewa a idanunta. Mahaifiyar Farha ta sa baki cikin haushin ta ce “Wallahi wannan rashin adalci ne! Ƴa ta da aka yiwa alƙawarin aure da ɗanki, amma gashi ya tozarta ta da wata a gaban duniya. Me kike tunanin mutane za su ce mana?!” Falon ya cika da hayaniya, baƙi masu kwana a gidan suna jinjina kai. Duk wanda ya ɗago tv ɗin da ke gefe, sai ya ga replay na Amal da Maleekh suna rawa tare, suna murmushi kamar an haɗa jini da jini. Ammy ta runtse ido da nauyin kunya, tana maida numfashi... Ammy cikin murya ƙasa ƙasa ta ce “I… I didn’t expect this. I only wanted peace between our families. But… things fell apart.” Mahaifin Farha ya daka tsawa tare da faɗin “Peace?! You call this peace? You call public disgrace peace?! No, Maryam, you failed us!” Ɗakin ya ɗauki shiru, sai kukan Farha da ke cikin ɗaki yana fitowa, tana ƙoƙarin karya zuciyar iyayenta gaba ɗaya. Scene ɗin Maleekh da Abokansa🥳 A babban hotel mai tsadar gaske a tsakiyar birni, an kunna AC, cikin walwala abokan Maleekh suna zaune suna ta yi masa barkwanci. Maleekh ya kwanta luf kan kujera, yana danna wayarsa da murmushi — hotunan Amal da suka yi tare kenan ke yawo a kafafen sada zumunta... Aboki na 1 yana dariya, yana busa hayaƙin shisha y ce “Kai Maleekh, you kill it yesterday, bro! That dance, that kiss, damn… you trended more than the president himself. Wallahi the whole country dey talk about you and Amal.” Suka kwashe da dariya gaba ɗaya. Aboki na 2 yana zuba juice a glass cup ya ce “Bro, forget that Farha matter. You don’t love her, and everybody knows. Amal is the vibe. She’s natural, classy, she completes your energy. Don’t let anyone force you into what you don’t feel.” Maleekh ya kalli gilashin ruwan lemo a hannunsa, ya ɗan murmusa sannan ya ce “Amal… wallahi she’s different. For the first time in my life, I feel alive. The way she looked at me yesterday… it was real. Not fame, not money, just… me.” Aboki na 3 yana dariya, yana tafa masa hannu ya ce “That’s it! Follow your heart, man. We got your back. Marry the one you love. Forget family politics.” Maleekh yana jin daɗin shawarwarin da abokansa suke bashi hakan yasa koda yaushe yake tare da su... Suka ci gaba da shan shisha, suna dariya, suna bada shawarar “ba’a ɗaure zuciya a soyayya.” PA ɗin Maleekh na zaune shima a gefe, sai ya kalli Maleekh da wani irin murmushi, da sigar dariya, ya kalli Maleekh yana cewa “Boss! What about your ɗaukan fansa akan Amal na marin da ta yi maka in public.....?..” Sai yayi shiru yana dariya ganin irin kallon da Maleekh ya wurga masa.. Zuciyar Maleekh ta buga dimmm! Wani zafi ya tsaya a ƙirjinsa. Maleekh ya ɗan harari PA sannan ya ce “What the hell are you talking about?..” Abokansa suka ji, suka ɗaga kai gaba ɗaya. Aboki na 1 da mamaki ya ce “Kamar ya ɗaukan fansa? Wani fansa?..” PA ya yi dariya, ya ɗan zaro wayarsa. Yana murmushi da tsokana ya ce “Hehehe… lemme show you something, guys.” Ya kunna screen ya nuna musu tsohon bidiyo lokacin a Kaduna inda Amal ta mare Maleekh a bainar jama’a tana faɗin: “Join yourself, I said: join yourself Maleekh!” Sai kuma ta zabga masa mari a fuska, mutane suka yi ihun mamaki a wajen. Ɗakin hotel ɗin ya kaure da dariya. Abokansa duk suna ta tsalle da dariya, ɗaya daga ciki ya ce “What?! Hahahaha! Oh my God! So this love started with a hot slap?!” Aboki na 2 yana tintsirewa da dariya sosai ya ce “Waiii, bro, you got slapped in public by your queen! And now you’re dancing with her on live TV! Epic storyline!” Suka kwashe gaba ɗaya da dariya kamar ba za su daina ba. Maleekh ya ɗaga pillow da sauri, ya wurga wa PA a fusace. Yana ɗaga murya cikin bacin rai “You are stupid! I told you it was a secret, dumb ass! How dare you show them that video?!” PA ya ƙara yin dariya, yana bashi haƙuri. Yana kare jikinsa tare da faɗin “Sorry boss, just vibes… wallahi sorry…” Amma dariyar abokansa ta ƙara tunzura shi. Aboki na 3 yana bugun tebur cikin dariya yake faɗin “Oh my God, the almighty Maleekh got slapped! Bro, she tamed you from day one!” Maleekh ya ɗaga pillow ya wurga musu, ya ɗauki wani pillow ya kwad'a wa wani. Suka fara dariya suna guje-guje a cikin ɗakin kamar yara. Ya dinga kwad'a musu pillow, wani ma sai da ya sha naushi a baya... Maleekh yana tsawa cikin dariya ya ce “Shut up all of you! Crazy idiots!” Abokansa duk da dariya, suna tsokanar shi.. “Boss, boss, take it easy! Don’t be mad… we love you!” Ɗakin ya cika da annashuwa da dariya, ƙamshin shisha, wasan pillow fight da tsokana. Bayan sun gama wannan shagalin suka watse kan kujeru, suka fara sauƙar numfashi. Sai ɗaya daga cikin abokan ya ɗauki gilashin cup ya ɗago sama yana faɗin: “Listen bro, forget about revenge. Love is not about ego. Amal loves you, you love her… end of story. Don’t spoil it with nonsense.” Aboki na 2 yana gyaɗa kai ya ce “Wallahi. A true man doesn’t take revenge on the woman he loves. He protects her. That’s the real game.” Maleekh ya jingina, ya lumshe ido. Cikin zuciyarsa, kalmomin sun dake shi. Har yanzu yana tuna marin Amal, amma kalmar soyayyarta da murmushinta ta sha fiye da duk wani rauni. Maleekh a ransa ya ce “Revenge? No… she’s worth more than that.” Sai ya ɗago kai ya kalli abokansa da murmushi a fili ya furta “You’re right. Amal is my peace now… no more revenge.” Ɗakin ya sake kaurewa da dariya, amma wannan karon dariyar ta soyayya ce, ba ta tsokana ba. 🌹🌹🌹 Farha ta killace kanta a ɗaki. Bayan ta gama shan kuka, ta buɗe drawer ɗinta ta ciro kwayoyi da allurai irin na masu shaye-shaye. Hannunta sai rawa yake yi amma zuciyarta ta cika da baƙin ciki da kunya. Ta zauna ta huda hannunta, ta zuba wa kanta allura. Ta ɗauki ƙwayoyi ta sha over dose. Cikin ɗan lokaci maye ya mamaye ta. Idanuwanta suka fara juyawa, ta zube a ƙasa tana dariya ita kaɗai. Ƙarar dariyarta ta ɗan tsaya.. Bayan mintuna babu motsinta. Iyaye da masu aiki suka taru a bakin ƙofa suna ƙoƙarin shiga amma ta ƙulle ƙofar. Da ƙarfi aka buɗe ƙofar, sai ga Farha kwance a ƙasa tamkar gawa. A kusa da ita allurai da kwayoyi a wajen, hannunta cike da jini. Mahaifiyarta ta durƙusa tare da rungumar ta da kuka “Ya Allah, ƴata shaye-shaye? Farhaaa wake up, please wake up!…” Mahaifinta da mamaki, yana girgiza kai ya ce “My daughter? Drugs? Injection? How… how did this happen under our roof?” Ammy na tsaye a gefe, jikinta na rawa. Idanuwanta cike da tsoro da damuwa. Da sauri aka ɗauki Farha zuwa asibiti. A Falo Ammy ta zauna ita kaɗai a falo, tana riƙe da kanta cikin damuwa. Ga Maleekh yaƙi dawowa gida saboda ya san abin da zai tarar. Sai ga Mahaifiyar A’isha (kishiyarta), ta shigo falo a hankali tare da murmushin taushin zuciya. Mahaifiyar A’isha cikin rarrashi ta ce “Don’t worry Hajiya… abin da ya faru ya faru, komai zai wuce. Allah zai ɗauki. Kiyi hakuri, komai zai dai-daita.” Ammy ta ɗago kanta, idanuwanta sun sauya. Ta miƙe a fusace, ta shaƙe mata wuya a tsawa ce take faɗin “Waye ya gayyace ki shagalin ɗana? Hm? Da akayi bikin ƴarki A’isha kin ganni na je? To me yasa bazaki fita daga rayuwata ba?! Ki zauna a yankin ki da ƴaƴanki ki barni!” A’isha da ta fito ta tarar da abin da ke faruwa ta ruga cikin tashin hankali, ta riƙe hannun Ammy tana kuka... Cikin sigar lallashi take faɗin “Please Ammy ki saki Mamata! Don Allah ki sake ta, kiyi hakuri!” Arfat da Islam ‘ya’yan Ammy suka nufo wurin suna kare mahaifiyarsu. Arfat cikin fushi ta ce “Wannan ya wuce gona da iri! Ke A’isha, baki isa ki shiga rayuwar Ammynmu ba!”.. Salma da Ummi ‘ya’yan mahaifiyar A’isha suma suka fito, suka ruga suka tsaya a gefen uwarsu. Salma ta furta da ƙarfi cewa “Baza mu bari ku ci zarafin Mamarmu ba! Duk da gidanku ne, amma itama tana da hakki akan gidan...tin da gidan mahaifin mu ne muma!” Sai kawai lokaci guda aka kaure da faɗa a falon. Arfat da Salma suka cafke juna, suka hau damben faɗa, da zage-zage... Islam da Ummi suma suka rikice, suka fara wurgi da juna... Ammy da kishiyarta kuma sun rungume suna kai wa juna duka da zagi iri-iri.. A’isha tana kuka tana ƙoƙarin raba su amma babu wanda ke sauraronta.. Ƙarar ihu, naushi, da zage-zage suka cika gidan gaba ɗaya. Falon ya rikide tamkar kasuwa... Sai kawai ƙarar buɗe ƙofa ta ɗaki kunnen kowa... Gaba ɗaya suka tsaya cak suna numfashi da huci jin irin tsawar da Abbah ya daka musu... Abbah ya shigo, cikin shigar manyan mutane, wayarsa a hannu, fuskarsa a ɗaure kamar dutse... Da kallo guda ya tsayar da rikicin. Kowa ya ja jikinsa gefe yana jan numfashi. Abbah cikin muryar tsawa yake faɗin “Subhanallah… me nake gani haka? Wannan gidan ku ka rikide kamar kasuwa? Ƴaƴa kuna dambe? Ku ma iyaye kuna shaƙe juna? Me yasa baku da kunya? Wani irin jahilci ne wannan?!".. Ammy ta na huci ta ja baya, tana share gumin fuskarta. Kishiyarta ma ta gyara mayafinta cikin hawaye domin ko kaɗan bata taɓa tunanin zasu aiwatar da haka ba a gaban ƴaƴanta.. Arfat da Islam suka saki kwalayen rigunan juna suna ja da baya, Salma da Ummi suma suka ja gefe suna huci. Abbah kamar zai haɗiyi ransa yana nuna su da yatsa tare da faɗin “Dukanku! Waye ya kawo wannan tashin hankali a gidana?.." Ammy ta sunkuyar da kai tana rawar baki, tana son yin magana amma Abbah ya katse ta da cewa “Shiru! Ba na son magana yanzu. Kowa ya natsu. Wallahi wannan gidana ne, ba zan lamunci ku mai da shi dandalin zagi da ashar ba!” Abbah ya kuma cewa “Wallahi wannan tashin hankali da na gani yau… Maryam (yana kallo Ammy), ke kika jawo shi. Domin na fuskanci bakya son zaman lafiya da ƙanwarki...” Ammy ta yi saurin mayar da martani da cewa “Ai dama kai kafi son ta fiye da ni! Ka fifita ta akaina tun farko, to shikenan ka ja mata kunne kada ta sake takowa gidana nan Abuja. Wannan gidana ne, ban yarda da ita ba.” Abbah ya ɗaga hannunsa da yatsa yana nuna Ammy, fuskarsa a cunkushe da fushi ya ce “Ki saurare ni da kyau, Maryam. Wannan gida na ne ba gidanki ba. Kuma duk matana suna da hakkinsu a kaina. Itama matata ce kamar yadda ke kike matata. Wallahi ki kiyaye ni! Ban yarda da wannan shirmen da kike yi ba.” Ammy ta harare shi, ta ɗaga hannu tana nuna Maman A’isha, ta ce: “To ai saboda kana son ta ne kake cewa haka. Ni kuwa wallahi yau sai naci babban buro uban ta a gidan nan!” Kafin ta ƙarasa, Abbah ya tako da ƙarfi zuwa gabanta. Idanunsa sun canza, ya girgiza kai yana furta cewa “Ni kika zaga ko ita?! Ni kike nuna wa rashin kunya a gaban iyalaina?” Wanne irin jahilci ne wannan? Maryam, ke kullum zaman lafiya baya yi miki. Uwargida ce ke, amma baki da haƙuri. Ki kalli kishiyarki, tana da haƙuri, ke kika jawo rikici.” Ammy cikin fushi ta mayar masa da magana: “Ai daman ita ka fi so, shine kake fifitata a kanta! To wallahi kar ta sake zuwa gidana! Taje ta zauna a Kaduna can.” Abbah ya katse ta da tsawa yana faɗi “Enough! Idan ba za ku iya zaman lafiya ba, kowacce ta koma gidanta. Ni ban kawo ku don nayi sulhu da mace ba, an gudanar da shagalin ɗana. Kuma yanzu shagalin ya zama abun kunya, kuma duk saboda ke Maryam, kin jawo cece kuce akan ɗana, masu zaginsa su suka fi yawa, to wallahi ki sani duk wanda ya zagi ɗana a bayan idona ban yafe ba, idan kuma naji a gabana to kotu ce zata rabamu, domin bazan lamunta ba, sannan kinzo kin ta da rigima a cikin gida ke da abokiyar zamanki m, shin akan ki aka fara ƙara aure ne? kina so ki koyawa yarana rashin kunya da ƙin mutane, to wallahi ki kiyaye ni..." Kowa ya yi shiru, falo ya koma tamkar an zuba ruwa. Sai Abbah ya zauna a babban kujera ya dafe kansa, a hankali, cikin takaici ya kuma furta. “Wannan abin da ke faruwa yana ƙara tabbatar min… wannan gidan zai tarwatse idan babu wanda ya tsaya masa...” Maman A’isha cikin nutsuwa ta ce: “Ka yi haƙuri Alhaji, ba komai. Don zaman lafiya, ni da ƴaƴana za mu koma Kaduna.” Ammy ta saki tsaki ta ce: “kar ma ki koma dan uban ku daga ke har ƴaƴan nakin, gaba ɗaya saina hallaka ku idan kuka cigaba da zama mun...!” Abbah miƙe wa yayi a fusace ya nufi Ammy cikin fushi: “Ni kike zagi ko ita?” Shiru ya ratsa falon. Kowa ya tsaya kallon ikon Allah. Sai Maman A’isha ta share hawaye, ta dubi Abbah cikin ladabi ta ce: “Yi haƙuri Alhaji… Ni dai yau zan bar mata gida, zan koma Kaduna da ƴaƴana, kada abun ya sake rikidewa.” Abbah ya girgiza kai, ya tsaya tsayin daka sannan ya ce: “Ba zaki tafi ko’ina ba. Wannan gidana ne, ba gidanta ba. Kinada ‘yancin hutunki a nan Abuja, kamar yadda itama take da ‘yanci ta je gidanki Kaduna. Amma wallahi bana son in sake jin hayaniya irin wannan a gidan nan. In na sake… sai na ɗauki mataki a kanku.” Maman A’isha ta sunkuyar da kai, ta ce da siririyar murya: “Na ji Alhaji… Zan yi haƙuri.” Abbah ya sauƙe numfashi mai nauyi, ya dafa kafaɗarta cikin tausayi ya ce “Allah ya saka da alheri. Ki zauna ki nutsu, ki sani duk matana ɗaya suke a wurina. Abin da ya sa na raba gidanku tun farko kenan saboda rashin zaman lafiya. Ke ki zauna a Kaduna, ita ta zauna nan Abuja. Amma ki tabbata, wannan gidan nawa ne, ku duk kuna da hakki akansa.” Ammy ta ce "Ai wallahi ba'a isa a wulakanta ni a gidan nan ba..." Abbah nuna ta ya yi da yatsa yana faɗin "Wallahi zan kwad'a miki mari yanzu idan baki kiyaye ni ba.." Da sauri Ammy ta ja tsaki ta bar falon, tana ganin Abbah ya fusata. Abbah ya kalli Maman A’isha yana faɗin: “Kije ki zauna, kiyi haƙuri. Wannan gidana ne, duk kuna da hakki a kai. Amma wallahi kada na ƙara jin hayaniya a nan.” Maman A’isha ta juya tare da iyalainta.. Su ma iyalain Ammy barin wurin suka yi suna taya uwarsu kishi.. Shima Abbah haura saman part ɗinsa ya yi... Dalilinda yasa Abbah ya raba musu gida kenam saboda rikici basa zaman lafiya, Ammy take zaune a Abuja, Maman A'isha kuma a Kaduna... Bayan washegari, Farha tana kwance akan gadon asibiti ɗaure da drip a hannunta, ga Mommynta a gefen gado suna so su tafi da ƴarsu.. A zabure Farha ta tashi zaune tana faɗin.. "Wallahi sai nayi maganin ku, tin da ni zaku wulakanta a gaban mutane, nima sai na tozarta ku..." Mahaifiyarta dake kusa da ita ne ta rungumeta tare da rarrashinta.. Sai yanzu Farha ta dawo cikin hayyacin ta tana bin asibiti da kallo kamar wata baƙuwa.. Tana cijan leɓe ta ce "Wa ya kawo ni hospital? ku ma kun san cewa ina shaye-shaye ko?.." Mommynta ta ce "ki kwantar da hankalinki zamu tafi dake London a yau, daman jiran tashinki muke.." Farha tasa hannu ta fincike drip ɗin hannunta tare da miƙe wa tana faɗin "I will not go anywhere, burina bazai taɓa cika ba in har Maleekh bai aure ni ba, inhar ya auri wata bani ba..." ta jinjina kai sannan ta ce "Kashe kaina zanyi domin banida wani amfani, na tsani rashin nasara..." Mommynta gaba ɗaya ta tsorata ta ce "Baza ma ki mutu ba insha Allahu, kuma sai kin cika burinki....ina supporting ɗinki my daughter, amma kafin ki ci nasara sai kin bi wata hanya guda..." Farha ta tsaya tana sauraron mommynta.. Uwar ta ci gaba da faɗin "Inaso ki shiga jikin Amal yanda zata yadda dake sannan ki tarwatsa mata rayuwa, inason Maleekh ya tsane ta lokaci guda, ke Daughter kin san hanyar da zaki bi..." Farha ta jinjina cike da murmushin mugunta... Daga wannan lokacin aka sallame su, bayan sun koma gida Ammy tayi farin cikin ganin Farha.. Ammy ta ɗau alƙawari wa iyayen Farha cewa saita aura wa Maleekh Farha, ko yana so ko bayaso, domin duk suna son farin cikin ta, Ammy duk da itace babba da mahaifiyar Farha tana matuƙar tsoronta da mahaifin Farha, shiyasa take son faranta musu da ƴar su... A wannan ranar suka koma London, gida dai kowa ya watse ya dawo yanda yake.. Yau kwana uku da gudanar da Birthday amma Maleekh bai koma gida ba... A wannan ranar Farha ta nemi Islam da ta rakata gidan Amal... Ba musu Islam ta biye ta suka shirya tare da jan mota suka tafi.... Bayan sun isa gwarinpa estate a layin gidan suka Parker motarsu a bakin titi, sannan suka ƙarasa bakin get tare da knocking... Maigadi ne ya buɗe musu, ganin farha yasa shi faɗin "Ke kika ƙara dawowa kuma.." Farha ta ce "Ka ga ba wurinka muka zo ba, ka ci gaba da aikin ka kawai.." Maigadi ne ya ƙira wayan cikin gidan, bugu ɗaya aka ɗauka ya sanar musu cewa sunyi baƙuwa, jinjina kai maigadi yayi sakamakon bada izinin shiga.. Kallonsu yayi sannan yayi musu iso... A falo Suka tarar da Inna a zaune Bayan Maigadi ya barsu sun shiga. Inna da ganinta ta zabura ta miƙe tare da faɗin "Meya sake kawo ki gidan nan Fara? Kinzo ne ki ƙara saka jikata a matsala? Kinaso ta ƙara komawa wurin folin tetion ne? (Police station).. Sai ga Amal ta sauƙo daga upstairs, fuskar ta cike da annuri. Makeup ɗinta ya haskaka fuskarta domin ba ƙaramin kyau tayi ba, inda tayi foundation da launin ruwan pawder, kalar gyalen kayan . Gashinta an ɗaure shi a tsakiyar kai cikin salon da ya bazu da kyau, sannan an yi masa styles a gaban gashi da ya kwanta yayi kyau. Sanye take da dankareren less wanda ya yi daidai da jacket ɗin wayarta iPhone 17 dake hannunta, da kuma plate shoes da suka yi daidai da kayan da ta saka. Ta zauna a kan sofas, tare da ɗora ƙafa ɗaya a kan ɗaya, sai da ta ja ajinta kafin ta faɗi cikin murmushi: "Sannun ku da zuwa, meke tafe daku..?" Farha ta murmusa, zuciyarta cike da shiri, ta ce cikin nutsuwa: "Kiyi haƙuri, Amal. Banzo da niyyar faɗa ba, sulhu nazo nema. Naga kamar yanda kika faɗa ke da Yaya Maleekh, mutu karaba, na gane hakan. Shiyasa na tako nazo yanda kike, domin baki haƙuri, sannan ina mai sanar miki cewa nabar miki Yaya Maleekh." Islam cike da mamaki take kallon Farha, tana tunanin shin har zuciyarta take faɗin haka kodai akwai abinda take shiryawa. Amal ta jinjina kai sannan ta ce "Allah yasa da gaske kike" Inna ta ce "Ke Fara ba abin yadda bane, kinzo da salon ki ko?.." Farha ta ce "wallahi ku yadda dani, bazan iya juran cin mutunci ba shiyasa na haƙura da soyayyarsa.." Suna cikin wannan sai suka ji sallama an shigo falon.. Duk kallon bakin ƙofar falon suka yi, Maleekh ne da abokansa sun zo ganin Amal kafin su wuce garuruwansu, daman shagalin birthday ne ya kawo su kuma yanzu angama zasu tafi sun gama shirinsu.. Maleekh ganin Farha yasa shi nuna ta da yatsa "Keee meya kawo ki wurinta again?.." Farha kamar zatayi kuka ta ce "Nazo bata haƙuri ne da neman sulhu.." Amal ta miƙe tana murmushi ta ce "Rabin raina kar ka damu, Farha tazo ne bawai da neman rigima ba.." Maleekh yana hararar Farha domin bai gama yadda da ita ba. Amal ta kalli abokan Maleekh tayi musu sannu da zuwa, duk zama suka yi suna yabonta tare da faɗin "Wannan dacewar yayi kyau tsakanin Maleekh da Amal..." Masu aiki ne suka kawo musu kayan drinks da delicious food da aka dafa musu daman Maleekh ya sanar mata cewa zasu zo.. Amal ta gayyaci Farha da Islam su zauna su ci abinci tare. Farha ta yi murmushi, amma zuciyarta cike da shiri da takaici. Haka suka sha hirarsu har da Inna.. Daga baya Maleekh ya sanar wa abokansa cewa zaiyi wa masoyiyarsa babbar kyauta.. Maleekh ya miƙe tare da kamo hannun Amal ya miƙar da ita sannan ya damka mata makullin mota mai tsada. Jeep mai ƙira ta musamman Jeep Wrangler Rubicon 2025, kalar Black Steel. Farha da Islam suka zaro ido suna kallonsu da mamaki. Farha ta yi tunanin ta rausa ihu, sai kawai ta jure. Abokansa duk sun tafi cikin farin ciki, Inna ta yi dariya tana tafa hannu, Amal kuma ta rufe bakinta da hannaye biyu, tana mamakin wannan surprise. Maleekh ya ƙara da cewa: "Na ba wa masoyiyata Amal appointment a kamfanina mai suna CashTalk, ita zata maye gurbin Assistant ɗina, wacce a halin yanzu tayi aure ne a ƙasar waje. Na bawa Amal miƙamin ta." Duk farin ciki ya cika falon, abokansa, Inna, masu aikin gidan, da ita Amal. Farha kuwa, zuciyarta cike da rashin jin daɗi, tana kallon wannan nasara da Maleekh ya yiwa Amal. Maleekh ya ƙara da cewa: "Ba wai nayi hakan da kaina bane, sai da na nemi shawarar mahaifina sannan yayi supporting ɗina akan Amal." Bayan an gama ƙaramin shagali a gidan su Amal daga baya Farha da Islam suka bar gidan cike da takaicin abinda suka tarar.. Suna daga cikin motarsu Farha take faɗin... “Dole ne in mayar da martani… in nuna masa cewa ni ce haƙiƙanin zaɓinsa, ba wai Amal ba…” Islam tana zaune kusa da ita, tana kallonta cikin damuwa ta ce "Aunty Farha, kina nufin zaki zo a gaba da Amal? Kina sane da cewa Yaya Maleekh har yanzu bai amince da zuciyarki ba?" Farha ta jinjina kai, da murmushi a fuska ta ce: "Ina sane da haka, amma duk wani sirri yana da hanyarsa. Zan yi hankali, duk da haka zan samu damar nuna masa cewa ni ce mafi dacewa. Zan yi amfani da hankali na, ba rigima ba. Dole Maleekh ya gani cewa ni ce wacce zata iya zama mata mai hankali da daraja,” Islam ta ce "Ki tuna, Aunty Farha, komai bazai zo da sauƙi ba. Amma idan kika yi hankali, Yaya Maleekh zai fara lura da canji a jikin ki." Farha ta ce. “Dole ne in yi shiri sosai, in nuna masa darajata. Wannan lokaci ne na nuni da hankali, ba rigima ba. Komai zai fara nan gaba…” Ammy tana kan jiran dawowar Maleekh yau kwana uku bata ganshi ba, Bayan sun dawo gida, a falo suka tarar da Ammy.. Farha ta zauna a kan kujera, tana kallon Ammy cikin nutsuwa sannan ta ce: "Ammy, Maleekh yayiwa Amal kyautar mota..." Ammy ta girgiza da jin wannan batun, a fusace ta miƙe da sauri: "Me kike faɗin Farha?!" Farha ta ci gaba da faɗin "Tabbas kuwa, sannan ya ba ta aiki a kamfaninsa, a matsayin mataimakiyarsa ma." Ammy ta tsaya cike da tsananin fushi, tana ƙoƙarin jurewa, sai kawai ta fara jin hajijiya tana shirin faɗuwa a gefen ta Islam ta riƙe ta, tana ƙoƙarin kwantar da hankalinta: "Sorry Ammy…" Islam ta zaunar da ita. Ammy ta ce "Wato Maleekh ya raina ni koh? Sai ga Maleekh ya turo ƙofar falon da sallama a bakinsa, tsabar damuwa basu ji shigowar motarsa ba har yayi parking ya fito ya shigo falon... Ammy na ganinsa tayi saurin miƙe wa ta nufe shi da sauri, tana zuwa ta zabga masa mari a fuska, kafin ya ankara har ta ƙara zabga masa wani marin tana kuka... Ammy ta juyar da fuskarta cike da fushi tana faɗi "Wato Maleekh ka raina ni ko? Bayan abinda ka aikata a gaban al'umma, ka rushe baikon dana saka maka da Farha, sannan kayi rawa da wacce na tsana a rayuwata, still yanzu kayi mata kyautar mota da aiki a kamfaninka? MALEEKH!" Maleekh bai ce komai ba, ya tsaya tsaye kamar dutse, idonsa na kallon Ammy da nutsuwa, ba tare da ya nuna fushi ko tsoro ba. Farha da Islam suna kallon abin da ke faruwa cikin mamaki. Farha tana murmushi a ranta, tana jin yadda shirin da ta fara tunanin zai fara aiki a hankali. Ammy kuwa, tana tsaye, har yanzu tana riƙe da ɗan damuwar fushi, ta ce "Ka san dai, Maleekh, ba zan iya yarda da wannan ba. Duk abinda ka aikata ba daidai bane… Ya kamata ka san inda yake maka ciwo!" Maleekh ya ja numfashi mai zurfi, ya matsa zuwa ga Ammy, yana ƙoƙarin ɗan sassauta lamarin ya ce: "Ammy… kada kiyi haka, ina son ki… amma wannan lokacin bai dace da faɗa ba. Zan yi bayani, amma ki saurara min." Ammy ta ja kai gefe, har yanzu tana cike da fushi da rashin yarda.. Farha ta kalli Islam cikin sirri, tana murmushi a ranta ta ce "Nan gaba, Maleekh zai fara lura da ni. Wannan farkon shirin ne kawai…haɗa shi da mahaifiyarsa" Ammy ta ce “Ka san irin yadda nake ji kuwa? ka san irin rainin da ka ja wo mun kuwa? To kaima yanzu ka raina ni Maleekh!” Islam ta matsa kusa da Ammy, tana riƙe da hannunta, tana faɗin: “Ammy, ki yi haƙuri, kada ki fusata da shi yanzu, mu saurari abinda zai aiwatar.” Maleekh ya juya hannunsa ya riƙe Ammy a hankali, cikin sanyin jiki, yana murmushi mai ɗan tsananin sanyi. Ya ce a hankali: “Ammy… ni ban raina ki ba. Na san kina jin haushin abin da na yi, amma abin da na aikata ga Amal… ba wai don bana son farin cikin ki ba ne, ko don na fi son ta a kanki… ba haka bane. Na aikata shi ne saboda zuciyata ta amince da hakan, kuma nayi tunani, kuma mahaifina ya goyi bayan hakan.” Ammy cikin tsawa take faɗin “Na yi haƙuri? Ka aikata laifi a gaban kowa sannan kace na yadda da kai?! Ka yi rawa da wacce bata da wani amfani a wurina! Ka ɓata Farha a gaban kowa, yanzu kuma ka yi wa Amal kyautar mota! Menene a zuciyarka Maleekh? Kodai duk wannan Mahaifinka ne ya umarce ka da kayi mun haka?..." Maleekh ya ɗan saki hannunta, yana kallonta ya ce “Ammy… ku yi haƙuri da ni. Amma ki saurare ni, ki yi ƙoƙarin fahimta ta… Zuciyata yanzu ta fahimci gaskiya, kuma ba zan sake yin abinda zai raina ki ba. Ina so ki gane cewa ni da Amal… akwai soyayya tsakaninmu, amma hakan ba yana rage hakkin ki a zuciyata ba.” Ammy ta gyaɗa kai cikin rashin gamsuwa, hawaye na zuba daga idonta. Islam kuwa ta matsa kusa da ita, tana ƙara kwantar mata hankali. Maleekh ya ja numfashi, ya miƙa hannu ga Ammy yana faɗin “Ki amince da ni, ki yarda dani Ammy, bazan so ganin hawaye a fuskarki ba..." Ammy ta ce "Idan kana son ganin farin cikina Maleekh to ka amince da auren Farha.." Ya share guntun hawayen da ya zubo masa sannan ya ce "Shikenan zan yi yanda kike so ɗin..." Ammy ta tsaya a tsaka-tsaki, tana kallon Maleekh, zuciyarta na bugawa cikin haɗi da damuwa. Hawaye na ci gaba da zuba amma sai ta yi ƙoƙarin ƙara daidaituwa, ta ce: “Maleekh… wannan ba abu ne mai sauƙi ba na sani. Abinda ka aikata… bazan manta ba. Amma… zan saurare ka. Zan saurare ka har sai na ga gaskiya.” Maleekh ya lallashi Mahaifiyarsa ta sigar lallami ba tare da ta haƙura akan batun Amal ba, ya wuce part ɗinsa... Daga baya Farha ta nufi part ɗinsa da kwalliya a fuska tana tafiya tana rangwad'a... Farha ta tsaya a bakin ƙofar falon Maleekh, zuciyarta na bugawa cikin sauri. Tana knocking, tana jan numfashi, tana tunanin yadda zata iya shawo kansa. Maleekh, yana zaune a kan kujera, ya ɗaga kai ya kalli ƙofar. "Come in," ya faɗa murya cike da fushi. Farha ta turo ƙofa a hankali, ta shigo falon, idonta na ƙasa, durƙusa wa ta yi tana gaishe shi irin na nutsuwa, fuska cike da murmushi, Duk da akwai wani shiri a cikin ranta, ta shirya tarko domin Amal, ta sa Maleekh ya ji zuciyarsa ta tsani Amal sosai. Maleekh ya harare ta da idanunsa masu tsanani, sannan ya ce cikin murya mai kaifi: "Bana son wannan shirme, kar ki raina mun hankali na, Farha. Kuma kada ki yi tunanin zan yadda dake. Idan na tsani mutum, to bana taɓa sonsa." Farha, tana ƙoƙarin riƙe hawaye, ta tambaya cikin kuka: "To, me na maka? Me yasa ka tsaneni, Yaya Maleekh?" Maleekh, cike da fushi, ya ce: "Rashin nutsuwa da naci. Na ce bana sonki, amma kin nace. Har kina haɗa ni da mahaifiyata, mahaifiyata tana yawan fushi dani. Taya zan so ki? Kuma yanzu kin nuna halinki na shaye-shaye. Babu mace mai tarbiyya da zata rinƙa shaye-shaye, babu kuma mutum mai hankali da zai auri ƴar shaye-shaye, koda mata sun ƙare a duniya..." Farha tana kuka, tana ɗaga murya ta ce "Zan daina, wallahi zan daina..." Maleekh ya girgiza kai tare da faɗin: "Da ki daina, da kar ki daina wannan ya rage naki. Kuma kada ki sake zuwa gidansu Amal. Idan na ji wani abu ya faru da ita, ki yi kuka da kanki." Ya ɗaga kai ya kalleta, sannan ya tambaya: "Wai me yasa iyayenki basu ɗauke ki sun tafi dake ba?" Farha, cikin kuka, ta ce: "Ya Maleekh, kayi haƙuri. Wallahi ina sonka. Ni na yarda ka haɗa mu ni da Amal ka aura..." Maleekh ya girgiza kai, fuskarsa cike da tsanani, ya ce: "God forbid. Please leave my room. I don’t want to see your face." Farha ta buɗe baki zata ƙara magana, amma Maleekh ya riƙo hannunta, ya ja ta waje, ya wurgata kamar kayan wanki, ya rufe ƙofar falonsa da key. Kai tsaye ya nufi bedroom ɗinsa, yana cire kayan jikinsa ya shiga bathroom domin yin wanka. Farha kuwa, cikin kuka da damuwa, ta miƙe da gudu, ta sauƙa zuwa ƙasa, kai tsaye ta nufi ɗakinta. A falon, Islam ce kawai take zaune, ta jingina kai, da murmushi a fuska mai cike da tausayi... "Kin haɗu da aiki, ƴar wahala… Nidai, Yayana Maleekh nake supported akan Amal. Bana goyon bayan ya aure ki," Islam ta faɗa a cikin ranta.. NEXT NEXT NEXT.... asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 33 to 34 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Weekend Driving Lesson Ranar Asabar ce, rana mai haske, iska na kaɗa wa a garin Abuja. Maleekh ya ɗauki Amal da mota zuwa wani driving school mai suna “Skyline Driving Academy”, wuri mai faɗi da filin parking mai kyau, da alamomin hanya sosai, cike da tsaro da tsari, wanda ya dace da masu koyon tuƙi.. Amal ta shiga mota da ɗan tsoro a zuciya, tana kallon Maleekh da ido mai cike da sha’awa da jin tsoro a lokaci guda. Maleekh cikin nutsuwa yake zaune gefen ta, yana zaune a driver's seat. “Ok, Amal, yau zan koya miki yadda za ki iya *_tuƙi_* a hankali. Kada ki ji tsoro, ni a gefen ki zan kasance.” Amal ta ɗaga kai, idanunta suna haske da ƙarfin soyayya da bege ya ce “Yaya Maleekh, ni dai ban taɓa tuƙin mota ba, amma zan yi ƙoƙari.” Maleekh ya murmusa, ya ce: “Ni zan tabbatar kin koya cikin sauƙi, amma ina so ki mai da hankali sosai. Wannan ba wasa ba ne.” Ya fara koya mata yadda ake adjusting seat, mirrors, da kuma starting the engine. Amal tana bin dukkan umarninsa cikin natsuwa, duk da tana ɗan tsoro. “Yanzu danna clutch da hannun dama, sannan ki kunna gear ɗin farko. Kada ki yi gaggawa,” Maleekh ya faɗa. Amal ta yi daidai, sai dai tana ɗan razane saboda jin zuciyarta na bugawa da sauri. Maleekh ya riƙe hannunta dake kusa da gear, yana murmushi: “Kar ki ɗaga hankali, Amal. Kada ki damu. Ni zan kasance tare da ke.” A hankali suka fara tuƙi a open parking lot, jere da alamomin tsayuwa, juye, da canza gear. Amal tana farin ciki, idanunta na kallon Maleekh lokaci zuwa lokaci. Maleekh yana kallonta yana murmushi: “Kin ga, ba ruwan ki da tsoro ko matsala, abin da kike buƙata shine nutsuwa.” Amal ta ɗaga kai, idonta cike da farin ciki da ɗan ban tsoro ta ce: “Yaya Maleekh… wannan yana da wahala, amma ina jin daɗin kasancewa tare da kai.” Maleekh ya motsa gefenta, ya ɗan matsa kusa da ita yayin da suke tuƙi a hankali, cikin murya mai laushi ya ce: “Amal, ina son ganin murmushin ki yayin da kike jin tsoro. Wannan shi ne abin da nake so.” Amal ta yi murmushi mai ɗan kunya, hannunta na ɗauke da clutch, amma zuciyarta na bugawa cikin sauri saboda ƙarfin soyayya da take ji.. Maleekh ya ɗaga hannunsa, ya taɓa hannunta a hankali: “Kin san, ba na son kina jin tsoro. Ina son ki amince da ni.” Amal ta danna brakes ɗin hannu kaɗan, tana kallon fuskar sa ta ce: “Na amince, Yaya Maleekh. Na amince.” Suka tsaya kaɗan a gefen filin, suna kallon juna. Rana ta haske su sosai, iska na busa wa, kuma zuciyarsu tana bugawa da sauri saboda soyayya... Maleekh ya ce, da murmushi a fuskarsa: “Yau ne farkon zamaninmu tare, a matsayin malaminki Amal. Zan koya miki tuƙi, amma zan koya miki yadda za ki kula da zuciyarki ma.” Amal ta ɗan yi murmushi, sannan ta yi murmushi mai ɗauke da ɓoyayyen tsoro da sha’awa.... “Yaya Maleekh… kai ne mutum na musamman.” Suka cigaba da tuƙi a hankali a filin Skyline Driving Academy, suna dariyar farin ciki, suna jin farin ciki a zuciyarsu, har rana ta fara sauƙa, hasken rana ta sauya launi, alamu a saman filin tuƙi alamun yamma tayi sosai... Sun tsaya bayan wani lokaci, Maleekh ya kalli Amal, sannan ya ce: “Kin yi kyau sosai a yau. Ina alfahari da ke.” Amal ta kalli Maleekh, idonta na cike da farin ciki ta ce: “Na gode, Yaya Maleekh… Kai ne malamina na musamman.” A wannan lokacin, zuciyarsu ta haɗu cikin wani irin romance mai ɗumi, soyayya da kulawa, a tsakiyar filin Skyline Driving Academy, inda sun fara wani sabon babi na rayuwarsu... Evening Return Home Rana ta fara raguwa, hasken duhu na sauƙa, Amal da Maleekh sun gama driving session ɗinsu, duka cike da nishaɗi da dariya. Maleekh ya tsaya gefen mota, ya juya fuska ya kalli Amal: sannan ya kuma cewa: “Amal, yau kin yi kyau sosai. Ina alfahari da ke.” Amal ta kuma yin murmushi ta ce: “Na gode, Yaya Maleekh. Ban taba jin nishaɗi haka ba a driving lesson kafin yanzu.” Maleekh ya miƙe hannunsa ya taimaka mata ta fita daga mota. Sun tsaya kaɗan suna kallon junansu a ƙarƙashin hasken rana mai raguwa. “Kin shirya mu tafi gida?” Maleekh ya tambaya, fuska cike da kulawa. “Eh, ina shirye,” Amal ta amsa, tana ɗan jin kunya amma zuciyarta na cike da farin ciki. Maleekh ya tuƙa su zuwa gidan Amal.. hanya cike da nishaɗi da light conversation: “Yau na ga kin koya sosai, Amma ki tuna kada ki manta da nutsuwa idan kina tuƙin ki kada ki yi sauri kuma tinda farko ne.” Amal ta yi dariya sannan ta ce: “Ni mai hankali ce yanzu, Yaya Maleekh. Zan tuna duk abin da ka koya min.” A gidan Amal, Maleekh ya tsaya a bakin ƙofar. Ya fito sannan ya zagaya ya buɗe mata, Ya miƙa hannunsa, ya sauƙe ta daga motar yana faɗin “Sai da safe, Amal. Na gode da kasancewa tare da ni yau.” Amal ta yi murmushi, murmushi mai ɓoyayyen shauƙi ta ce: “Na gode, Yaya Maleekh. Sai da Safe, Allah ya kai ka gida lafiya.” Maleekh ya ƙara murmushi, yana kallon ta: “Zan jira gobe Sunday mu sake haɗuwa, domin weekend ba za ta ƙare ba har sai mun ci gaba da wannan nishaɗi.” Amal ta ɗaga kai, idonta cike da farin ciki: “Zan kasance a shirye, Yaya Maleekh.” Maleekh ya juya baya, ya shiga mota ya wuce gida. Zuciyarsa cike da happiness da nishaɗi, yana tunanin yanda ya fi jin daɗi lokacin da Amal ke tare da shi. Amal ta shiga gida, ta shiga falonta tana murmushi mai ɓoyayyen farin ciki da soyayya. Ta zauna a kan sofa ta duba wayarta, tana ƙaunar tunanin ranar da suka yi driving lesson tare, zuciyarta na bugawa da sauri saboda soyayya da kulawa daga Maleekh. A gefen Maleekh kuwa, ya isa gida cikin residence, ya shiga falonsa cike da nishaɗi da contentment, yana tunanin Amal, yana jin farin ciki cewa yana da wani wanda zai raba lokacinsa da shi cikin nishaɗi da soyayya. _Washegari da safe_ Sunday Morning Driving Lesson.. Rana ta fara haskakawa alamun gari ya waye sosai. Gidan su Maleekh duk sun hallaru a dining area cike da murmushi da haɗin kan iyalai, kowa ya hallaru, Abbah, Ammy, Maleekh, Arfat, Islam, da Farha duk sun zauna suna breakfast... Maleekh yana tafiyar da breakfast cikin sauri, yana duba lokaci lokaci, yana tabbatar komai na tafiya lafiya. Abbah ya kalle shi, fuska cike da mamaki ya ce: "Ina zakaje ne my son da safen nan, yau weekend ne ba aiki amma naga kanata sauri.." Maleekh ya ɗaga kai, yayi murmushi kaɗan sannan ya ce: "Wallahi Abbah, na fara koya wa Amal mota ne tun jiya, shiyasa nakeso muna fita da sassafe. Inaso ta koya sosai cikin satin nan." Ammy ta wurga masa harara tare da jan dogon tsaki, fuskarta cike da rashin jin daɗi. Maleekh kuwa bai ce komai ba, ya san halin mahaifiyarsa bazata taɓa son Amal ba. Farha kuwa tana zaune, fuska cike da raunin kishi, zuciyarta kamar ana hura wuta, amma ba ta nuna komai ba.. Bayan sun kammala breakfast, Maleekh ne ya ɗauki wayarsa ya fice daga gidan, ba tare da ya tsaya ba sai a kofar gidan Amal. Amal tana tsaye a ƙofar gidan tana jiran shi. Yana ganin ta ya sau murmushi tare da faɗin "Sorry Beb, na ɓata miki lokaci koh?" Amal ta murmushi, idonta na shining ta ce "Ai kai baka laifi, saboda kar na ɓata maka lokaci ne yasa na kammala shirina tun sallar asuba." Maleekh ya murmusa, ya buɗe motarsa, suka shiga cikin nishaɗi. Hanya ta kasance shiru amma cike da yanayin soyayya kowa jin kansa yake cikin farin ciki, dake motar Amal acan school ake barin ta, su na zuwa zasu fara.. Bayan sun isa Skyline Driving Academy, babban fili mai faɗi a Abuja, Maleekh ya tsayar da motarsa a gefen filin. Sai Motar Amal da aka fito da ita na zamani, Mercedes-Benz GLE 2025, kyakkyawa, mai amfani sosai ga sabon mai koyan tuƙi... Maleekh ya juya fuska ya ce: "Amal, yau za mu fara da basic. Zan fara nuna miki yadda ake jan motar da kanki, sannan daga nan sai mu shiga real driving." Amal ta yi murmushi mai cike da nishaɗi, ta ce "Na shirya, Yaya Maleekh. Zan koya sosai, kada ka damu." Maleekh ya fara shiryawa, ya tabbatar da seat, mirrors da steering wheel sun yi daidai. Ya tsaya a gefe yana kallonta ya ce "Ki da ki ji tsoro, sannan ki yi a hankali sosai. Nayi miki wannan kyauta saboda ina son ki koya yadda ake tuƙi lafiya da kuma zuwa yanda kike so ba tare da kin sha wahala ba, ba wai kawai nishaɗi ba." Amal ta ɗora hannunta a steering wheel, zuciyarta cike da farin ciki da jin daɗi.. "Ina godiya sosai, Yaya Maleekh. Zan yi iya ƙoƙarina." Maleekh ya tsaya a gefe, idonsa na kallonta, yana tabbatar da cewa tana fahimta. A hankali ya barta ta ja motar da kanta a filin, suna dariya da tsokanar junansu lokaci-lokaci, soyayyar su na bayyana a cikin kowane murmushi, kowane dariya da ƙaramar kulawa. Skyline Driving Academy ta cika da nishaɗi da jin daɗi a tsakanin su, har lokacin da rana ta fara sauƙa, suna cikin jin daɗi da soyayya, suna ci gaba da lesson ɗinsu... Bayan sati guda na koyarwa a Skyline Driving Academy, Amal ta koyi motar sosai, har yanzu duk wani mota zata iya ja ba tare da jin tsoro ko shakka ba. Kowace rana Maleekh da Amal suna fita da safe, suna tuƙi a filin driving academy, har sai da Amal ta koyi basics sosai, daga ja da kanta, gear changes, parking, har zuwa driving cikin traffic simulation a cikin academy. Maleekh ya tsaya gefenta, yana kallonta, idonsa na haske da alfahari ya ce: "Amal, kin yi kokarin sosai, kin koyi abin da ya kawo mu cikin mako guda... Ina matukar alfahari da ke. Ba kowa ke iya jan mota haka a wannan lokaci kaɗan ba." Amal ta yi murmushi, zuciyarta na cike da farin ciki ta ce: "Na gode sosai Yaya Maleekh. Ba zan taɓa manta wannan lesson ɗin ba. Ina jin kamar yanzu ko wacce mota zan iya ja da kaina." Maleekh ya yi dariya kaɗan, ya ja ta kusa da motar, ya nuna mata kyautar da ya shirya mata, yana faɗin "Don nuna min girmamawa akan yadda kika yi ƙoƙari, na bawa masoyiyata kyauta ta musamman certificate na iya mota, award ɗin ‘Best Driver of the Week’ a Skyline Academy." Amal ta ɗaga ido, mamaki ya bayyana a fuska: "Seriously? Wannan nawa ne? Ina matukar farin ciki Yaya Maleekh!" Maleekh ya miƙa mata award ɗin, ya ɗaga hannu, yana murmushi: "Na san wannan ba kawai kyauta bane, amma shaida ce cewa kina iya jan mota ba tare da tsoro ba. Ina alfahari da ke sosai." Amal ta ɗauki award ɗin da hannu biyu, tana jinjina masa da murmushi ta ce: "Na gode sosai, Yaya Maleekh. Wannan zai zama tunawa mai kyau ga zuciyata." Maleekh ya yi murmushi, ya ce: "Kuma ki sani, wannan bai tsaya nan ba, yau kin koyi mota sosai, kuma na san kina iya tuƙi sosai a kowane lokaci, koda a real traffic na Abuja. Ina matuƙar alfahari da ke." Amal ta ji wani irin nishaɗi, zuciyarta cike da farin ciki, yayin da Maleekh ya rungume ta kaɗan, suna dariya tare. A cikin driving academy, sauran instructors da students sun jinjina mata saboda yadda ta koyi driving a cikin sati guda, kuma award ɗin ya ƙara mata kwarin gwiwa sosai... Daga wannan rana, Amal ta zama cikakkiyar mai iya tuƙi ba tare da jin tsoro ko shakka ba, kuma soyayyar Maleekh da ita na karfi, suna cikin nishaɗi da jin daɗi, suna shirya tarurruka na driving sessions.. Bayan Amal ta samu cikakken kwarin gwiwa a Skyline Driving Academy, Maleekh ya yanke shawarar yau ita za ta tuƙa motarsu. Sun fita daga gidan da safe, rana tana haskakawa cikin annashuwa. Maleekh ya miƙe hannunsa a kan seat na passenger, yana kallon Amal da idanuwan cike da alfahari ya ce: "Amal, yau ke za ki tuƙa mu, ba zan shiga driving ba. Ina son ganin yadda kika koya, zamu zagaya cikin gari har wajen gari shiyasa na fito da safe..." Amal ta yi murmushi mai cike da jin daɗi, ta sa hannu a kan gear, ta kunna motar, sannan ta fara ja a hankali. Motar ta motsa cikin santsi, Maleekh yana kallonta yana murmushi: "Wow… ki kalli wannan smooth driving! Ina alfahari da ke sosai." Amal ta juya kanta kaɗan, tana dariya ta ce: "To fa, Yaya Maleekh, yanzu ka tsaya a gefena kana son ganin kwarewa ta kenam." Duk dariya suka yi tare da jan mota suka tafi a slow... Sun fara zagaye Lugbe Road, suna hawa zuwa Jabi Lake Mall da Central Business District na Abuja. Amal tana tuƙi cikin hankali, tana canza gears ba tare da wata tsoro ba. Maleekh yana ta dariya, yana tsokanar ta: "Ba zan taɓa mantawa da ranar da kika fara koyon driving ba… yanzu ga ki, kamar gogaggen driver..!" Amal ta yi dariya tare da tsokanar shi da cewa: "Eh! Kada kayi tunanin zan zauna haka kana driving ɗina. Domin na fi ka ƙwarewa yanzu." Maleekh ya yi dariya, ya riƙe hannun ta kaɗan: "Eh… wannan gaskiya ne. Ina ganin zan bari ki zama official driver ɗina." Suka wuce Millennium Park... motarsu tana tafiya a hankali, suna jin iska mai sanyaya jiki. Amal ta yi parking na ɗan lokaci a gefen titi, suka fito daga motar, suna kallon shimfidar birnin Abuja daga saman titi, Maleekh yana kallon Amal cike da soyayya ya ce "Amal, kina da kyau sosai a kowace rana, amma a yau, ganin ki kina tuƙi, na ga kin samu cikakken iko da komai… Ina matuƙar son ki." Amal ta yi murmushi tana riƙe da hannun shi ta ce: "Yau na ga soyayya cikin motsin mota da nishaɗin birni, Yaya Maleekh.".. Bayan sun gama hutawa.. Suka koma cikin motar, Amal ta ci gaba da driving zuwa Wuse Market da Garki, suna yawon shakatawa, suna hira da dariya a kan titi. Maleekh yana ta godewa Amal a zuciyarsa, yana ganin yadda ta koyi motar da kyau, yana jin ƙaunar ta ta ƙaru da kowace rana. Daga karshe, suka dawo gida bayan zagaye birni, Maleekh yana jinjina kai cikin alfahari ya ce "Na san yau kina jin daɗin driving sosai, kuma na ga kin cancanci duk girmamawa da kyaututtuka. Ina matuƙar alfahari da ke." Amal ta yi murmushi mai cike da jin daɗi, zuciyarta na cike da farin ciki, tana jin cewa soyayya da Maleekh ta girma sosai yayin da suke cikin nishaɗi a kan titi. Cikin begen juna suka yi sallama Maleekh ya koma gida, yanzu burinsa ya cika Amal ta iya mota yanzu sauran fara aiki a kamfaninsa.... _Bayan Sati, ranar Monday_ .. Amal Starts Work at CashTalk Yau da safe Amal ta fito daga gidan ta cikin sabuwar motarta, jeep mai kyau, wacce Maleekh ya bata, tana tuƙi kamar gogaggen driver. Hasken safe na yi mata kyalli, kowa a unguwar yana kallonta kamar tauraruwa. Yanzu itama ta shigo sahun masu kuɗi, dake unguwar da take duk masu kuɗi ne.. Tana zuwa CashTalk FM, gate security suka hango motarta. Sai da suka buɗe gate tare da gaishe ta cikin ladabi: "Good morning, Madam Amal," ɗaya daga cikin masu tsaro yace, idanuwansu na cike da mamaki. Duk ma’aikatan da suka hango Amal, sun tsaya cike da mamaki. Yarinyar da suka daɗe suna ganin a matsayin talaka matsiyaciya yanzu ta bayyana cikin ƙyakkyawan tsari da ƙwarewa: Black glass yana rufe akan golden eyes ɗinta, yana ƙara mata sirri da kwarjini. Tana sanye da Abaya mai milk color da stones a gaba, gyalen rigar ya ɗan yi masa highlights, yana bayyana kyan ta... Handbag ɗinta da wayarta a hannunta guda. Takalmanta mai tsini yana ƙara mata kwarjini a kowace mataki. Kowanne ma’aikaci yana kallonta, zuciyoyinsu cike da sha’awa da mamaki. Mata da maza, duka suna mamakin wannan canji: daga ƙaramar matsiyaciya zuwa mataimakiyar babban attajiri. Maleekh kuwa daga ofishinsa dake saman building stairs yana tsaye a glass office da ke zagaye da windows, yana kallonta yayin da yake shan coffee daga glass cup ɗinsa: "Ahh… wannan ita ce nawa… babu shakka, ta cancanci duk wani yabo," ya ce cikin ransa, yana murmushi. Amal tana motsi a hankali cikin compound ɗin kamfanin, tana lura da kowace matsala da takalmanta mai tudu zai iya janyo... tunani ta fara yi shin wata hanya zata bi don haura wa sama yanda Offince ɗin Maleekh yake... Tunani tayi gwara kawai ta shiga elevator ya kaita har sama ba tare da ta sha wahala ba.. Wani ma'aikacin saurayi ne ya nuna mata hanyar elevator, domin ta kauce wa stairs ɗin da zai kawo mata cikass da takalminta... Tana shiga elevator, ta tsaya cikin kwarjini, zuciyarta cike da farin ciki da ɗan tsoro. Ta san wannan rana zata fara aiki a CashTalk, a matsayin mataimakiyar Maleekh, wanda hakan zai ƙara mata ƙwarewa da girmamawa a gaba... Maleekh ya dan yi murmushi, zuciyarsa cike da alfahari yake faɗin "Yau za ta fara aikinta… ina fatan zata ba da kyakkyawan hoto ga kamfanin." Elevator ya tsaya a floor na 18 na ƙarshe ƙarshe... Amal ta fito cikin nutsuwa, tana shirya handbag ɗinta, tana duba ma’aikata da murmushi. Duk wanda ya hango wannan sabon fuskarta, sai zuciyarsa ta narke, domin Amal ba karamar kyakkyawa bace ta asali.. "Good morning, everyone," Amal ta ce cikin ladabi da nutsuwa, kowa ya miƙe ya amsa gaisuwa, suna kallonta cike da mamaki da yabon kwarjinta... Kai tsaye Office ɗin Maleekh ta nufa, tana zuwa tayi knocking, daga ciki ya ce: "come in." Ta shiga da Murmushin ta, bayan sun gaisa ta zauna akan kujerar dake facing ɗinsa.. Maleekh ya ɗan ɗaga kofi ɗinsa yana zuƙar juice, yana murmushi ya ce: "Amal… I knew you would shine today," ya faɗi a ransa, cike da jin daɗin ganin yadda yarinyarsa ta girma cikin kwarjini... A wannan lokacin yasa aka ƙira masa duk ma'aikacin dake aiki a wannan kamfani, za'a gudanar da meeting a office ɗin taro na musamman.. First Official Meeting at CashTalk FM Kowa ya hallaru a babban ofishin CashTalk FM, babban ɗakin taro wanda yake na zamani, da dogon table a tsakiyar room, gefen table an jera kujeru masu yawa ga ma’aikata. Hawa hawan bene na wannan kamfani sun kai goma sha takwas, kuma babu wanda zai iya zuwa floor na sama sai da elevator ko escalator. Gida ne na kamfani mai girma a Abuja, wanda babu wanda bai san shi ba. Maleekh ya tsaya a ƙarshen dogon table, kujerarsa tafi ta kowa girma, yana fuskantar dukkan ma’aikata da suka zauna a jerin kujeru a gefen table, ciki har da Amal. Ofishin yana cike da haske, tare da kyawawan kayan ofis da technology na zamani. Maleekh ya ɗaga hannu, dukkan ma’aikata suka nutsu, suna sauraren shugaban su. Maleekh ya fara magana: "Good morning everyone, I hope you all had a productive week. Today, we are here not only to discuss our weekly operations but also to welcome a new member to our team." Duk tafi suka fara yi.. Daga nan sai ya juya fuska zuwa ga Amal ya furta: "Amal Abdulsamaad will be joining us as my Assistant. I trust she will bring fresh energy and perspective to CashTalk.".. Nan ma aka kaure da tafi.. Amal ta miƙe, tana murmushi, tana gaisawa da dukkan ma’aikata, ta ce: "Good morning everyone. I’m very honored to be here. My name is Amal Abdulsamaad. Many of you may know me from my work as a journalist across different states, but today, I’m here to serve as Assistant to the CEO, Maleekh Abdul-Majeed, and I hope to contribute positively to the success of this company." Duk ma’aikata suka fara tashi tsaye suna gabatar da kansu, suna nuna ladabi da professional attitude: "I’m Ahmed, Head of Marketing." "I’m Fatima, Finance Department." "I’m Chike, IT Coordinator." PA ɗinsa shima yana daga ciki ya miƙe tare da gabatar da kansa da cewa: "I'm Ibrahim, The Manager." Bayan kowa ya gabatar da kansa, Maleekh ya ɗaga hannu tare da faɗin: "Thank you all. I’m proud of the team we’ve built here. CashTalk is not just a company; it’s a family. Every week we achieve milestones, but we also face challenges. Our goal is to continue expanding, innovate in broadcasting, and maintain our position as the leading media company in Abuja." Ya ɗan ɗauki lokaci yana kallon dukkan ma’aikata, sannan ya ƙara: "I encourage open communication, professionalism, and teamwork. Amal will be assisting me directly, so I expect everyone to support her as she transitions into this role." Amal ta zauna bayan wannan jawabi, tana jin ɗan tsoro amma kuma cikin fargaba da excitement saboda wannan shine babban mataki a rayuwarta. Duk wanda ya kalli Maleekh da Amal a wannan babban ofishin, ya gane cewa abu mai girma zai faru a CashTalk FM, kuma kowa yana ɗokin ganin irin canjin da Amal za ta kawo. Meeting ɗin ya cigaba da tattaunawa akan projects, schedules, da objectives na kamfanin, dukkan ma’aikata suna nuna professional attitude, suna sha’awar sabuwar mataimakiya ta Maleekh. Amal ta tsaya a bakin office ɗin Maleekh, tana kallon babban room ɗin, dukkan na’urorin zamani suna nan, computers, monitors, da smart boards. Ta ɗauki ajanda da pen a hannu, tana jin ɗan tsoro amma a lokaci guda cikin excitement. Maleekh ya ce: "Alright, Amal, yau zaki fara da tasks ɗin yau da safe. Zan nuna miki workflow ɗin kamfani, sannan zamu duba schedules, emails, da projects ɗin da muke yi." Amal ta yi murmushi: "Yes, Sir. I’m ready." Maleekh ya ɗauki tablet ɗinsa ya fara nuna mata: "CashTalk FM is structured in departments. Marketing, Finance, HR, IT, and Content Production. I expect you to assist me directly, manage appointments, and also liaise with department heads when needed." Amal ta rubuta kowanne word a ajandanta. Daga nan suka fara zagaye office, suna zuwa departments ɗin daban-daban: Marketing: Amal ta gaisa da Ahmed, ya nuna mata ongoing campaigns. Finance: Fatima ta yi mata briefing akan budget reports. IT: Chike ya nuna mata dashboard na live broadcast da recordings. Manager: Ibrahim ya gaisa da Amal, sannan ya bayyana mata aikinsa: Yace shi ne ke da alhakin tsara ayyukan sassan daban-daban da tabbatar da cewa kowanne yana aiki bisa manufa. Ya nuna mata yadda yake tracking progress ta weekly reports daga kowane department. Ya kuma gaya mata cewa duk lokacin da akwai matsala ko shawarwari, shi ne first point of contact kafin su kai wa CEO. Amma tinda ta bayyana a matsayin assistant of CEO yanzu ita za'ana sanar wa komai kafin ta kai wa CEO.. Daga ƙarshe ya nuna mata wani project board da yake amfani da shi wajen saka deadlines da monitoring... Maleekh ya kalle ta cike da murmushi ya ɗora da cewa: Assistant COE tana taimaka wa shugaban kai tsaye. Ita ce hannun damarsa wajen kula da abubuwa na yau da kullum, tana sauƙe masa nauyi da yin follow-up akan departments. Manager kuma suya kula da departments (Marketing, Finance, IT, HR, da sauransu)... Maleekh ya cigaba da sanar mata cewa: Tana karɓar rahotanni daga Managers, ta tace su kafin su je wurin COE. Tana iya jagorantar meeting idan COE baya nan. Tana taimaka wajen tsara strategies da implementation, musamman idan COE ya fi kula da babban vision. Ita ke sa ido akan discipline da compliance kafin rahoto ya kai ga babban boss. Wato Manager → ya kula da department. Assistant CEO → ta haɗa rahotanni daga Managers, ta tace, ta duba, sannan ta kai wa COE. COE → ya yanke manyan hukunci da policies... ⚖️ Idan babu Assistant CEO, to duk Managers za su rinƙa damun CEO da ƙananan bayanai, hakan zai cika mun kai da workload..... Maleekh yana lura da Amal, yanda take ta zabga murmushi, cikin dariya ya ce: "You’re catching up fast, Amal. I knew you’d be able to handle this." Amal ta yi murmushi sannan ta ce "Thank you, Sir. I’ll do my best." Bayan zagaye, suka koma office tare da hutawa a babban office na Maleekh, inda Amal zata fara handling emails, scheduling meetings, da drafting reports. Yayin da take aiki, wasu ma’aikata suka zo suna tambayar ta: "Amal, how are you finding your first day?" Amal ta ce: "It’s exciting! Everyone is so professional, and I feel welcomed." Maleekh yana kallonta, yana murmushi ya ce "Good. That’s exactly what I like to see. Confidence, poise, and professionalism." Daga bisani, Maleekh ya ce: "Amal, today is just an introduction. By tomorrow, I want you to handle your first mini project, liaise with HR, and prepare a short report for me." Amal ta amsa da kwarin gwiwa: "I’ll make sure it’s done, Sir." Cikin wannan first day, Amal ta fara samun gaskiyar ƙwarewa akan aiki, tana ganin yadda take iya organizing schedules, communicating da manyan ma’aikata, da handling tasks efficiently. Maleekh yana kallonta daga ɗaya gefe na office, yana jin alfahari da yadda take sarrafa aiki, sannan yana shirin ganin yadda zata ƙara bunkasa a CashTalk FM. Meeting ɗin farko da Amal ta jagoranta (kodayake ƙaramin program ne) ya nuna cewa kowa ya fara yaba mata da kwarewarta, har ma da ma’aikatan da suka fara kallonta da mamaki. By the end of the day, Amal ta gama dukkan tasks nata da kyau, Maleekh ya yi mata brief: "Well done, Amal. I’m impressed. Keep this momentum, and soon you’ll be fully managing executive tasks on your own." Amal ta yi murmushi, tana jin confidence da excitement: wannan shine farkon babban tafiyarta a CashTalk FM. An tashi daga aiki ƙarfe 6 na yamma, tun safe karfe 7 ake fara aiki. Amal ta ɗauki jakanta ta fita daga CashTalk FM cikin nishaɗi, tana jan motarta zuwa gida, zuciyarta cike da farin ciki da excitement; tana tunanin yadda ma’aikatan suka karɓe ta hannu bibbiyu, kuma yadda Maleekh yake lura da ita a office. Da ta isa gida, ta tarar da Inna a falo tana shan tea. Amal ta sauri ta rungumi Inna tana faɗin "Inna! Today was amazing! Kowa a office ya yaba da ni, da aiki na, har Maleekh ya nuna jin daɗinsa sosai." Inna ta yi rawar hannu, ta girgiza jikinta, sannan ta ce cikin farin ciki: "Allah! Ashe ya tabbata aikin, ya kamata kiyi farin ciki, yarinya ta. Ina ta tunanin yanda zaki je wurin aikin nan ki burge su duka." Amal ta yi dariya tare da faɗin: "Yes Inna! Duk suna kallona da mamaki, sun yaba min sosai. Amma Maleekh… Inna, Maleekh yana kallona ne har a office da yanda nake gudanar da aiki, yana lura da ni sosai." Inna ta rungume ta da dariya: "Ai yarinya, ki more wannan lokacin, ki nuna kwarewa sosai." Maleekh ma ya koma gida cikin annashuwa da farin ciki... Abu ɗaya ne yake ɗaga masa hankali da zaran ya koma gida shine.. Kullum batun mahaifiyarsa Ammy akan Auren Farha ne, damuwarta Maleekh ya amince da Auren Farha in yana son farin cikinta.. Shi kuwa ya dage akan baya sonta, baya kaunarta....ƙalubalen dake damunsa kenam.. Bayan ya koma gida, ya wuce part ɗinsa..zama yayi yana kallon wayarsa, yana rubuta wasu notes game da projects na Amal da CashTalk, amma a zuciyarsa har yanzu akwai damuwa akan Farha da mahaifiyarsa... Maleekh ya ɗaga kai ya yi murmushi sannan ya furta "Amal… yanzu ke ce zaki cike min office da farin ciki. Kullum ina son ganin irin wannan ƙwarewa a tattare da ke." A gefe guda, Amal tana gida tana ta shaƙe da labaran aikin nata, tana jin confidence da motivation, wannan shine farkon babban tafiyarta a CashTalk FM, kuma ranar Monday ya kasance mai cike da nishaɗi da farin ciki ga dukkan su biyu. 🌹🌹🌹 Ammy ce ta fara knocking a ƙofar Maleekh jin dawowarsa.. Ba jumawa yazo ya buɗe mata, ta shigo tana yatsine ta zauna cikin izzah sannan tace da Maleekh shima ya zauna.. Ya zauna yana fuskantar Ammy yasan batun ta baya wuce akan Farha... Ammy ta ce cikin tsanani.. "Ya batun maganar mu akan auren?.." Maleekh ya ce "Auren wa Ammy?.." "Ammy ta ce "Kar ka raina mun wayo mana, ka manta maganar mu akan Farha ne?.." Maleekh ya ce "Na riga da na sanar mik, kullum batun ki ɗaya kuma nima amsar da nake baki ɗaya ne Ammy, bana sonta taya zan aure ta?.." Ammy tana harararsa ta ce "Maleekh! Ka saurara da kyau. Ka fahimci cewa dole ne ka auri Farha, idan har kana son ganin farin cikina. Bazan zauna lafiya ba har sai ka yarda da wannan!" Maleekh ya ɗaga kai, fuskar sa tana nuna ƙwarin guiwa da natsuwa, cikin murya mai ƙarfi ya ce: "Ammy… na fahimci damuwarki, kuma ina son farin cikinki sosai. Amma ki saurara da kyau: bazan taɓa auran Farha ba, ko mata sun ƙare a duniya. Ko zata mutu… ba zan yi hakan ba." Ammy ta wurga masa wani kallo ta taja numfashi mai ƙarfi, tana ƙoƙarin ɗaukar hankali daga fushin da take ciki ta ce "Maleekh! Kai kasan me kike yi ne kuwa? Kai ba yaro bane, amma kana wasa da rayuwata! Ni ina son ganin Farha a gidanka. Kuma dole sai ka aure ta!" Maleekh ya yi murmushi mai sanyi, ya matsa kusa da ita, amma bai bari ya nuna fushi ba ya ce: "Ammy… Ina sonki. Amma ba zan auri matar da ba na ƙauna ba.… Farha bata da wani wuri a rayuwata. Ki fahimta cewa ni ba mutum ne mai yin wasa da soyayya ba." Ammy ta ɗaga kai tana ƙoƙarin faɗar wani abu..kafin ta furta Maleekh ya ɗaga hannunsa da sauri ya toshe mata baki yana girgiza kai, cikin raunin murya kamar zaiyi kuka ya ce "Ki yi haƙuri, mahaifiyata… Wannan shine gaskiya, kuma ba zan taɓa boye miki ba. Ina sonki, amma na san inda zuciyata take." Ammy ta yi shiru, idonta cike da hawaye, amma zuciyarta ta fahimci cewa Maleekh yana da nufinsa. Duk da haka, fushinta da damuwa basu sauƙa ba gaba ɗaya. Ammy kiyi haƙuri da abin da zance.. "Ni yanzu zan huta. Amma ki san cewa zuciyata ba zata canza ba, kuma Farha ba zata shiga gidan nan a matsayin matar Maleekh ba." Ammy ta tsaya kallon sa, zuciyarta cike da rikici da rashin jin daɗi... A fusace Ammy ta miƙe tare da barin ɗakin... A wannan rana, duk da nishaɗin da Maleekh ya samu daga Amal da fara gudanar da aikin, gidan ya kasance cike da damuwa da tashin hankali saboda batun Farha da tsananin kishi da damuwar Ammy... Yana zaune ya kifar da kansa akan gwiwarsa lokaci guda yaji wani irin zafaffen hawaye yana zubo masa... Haka ya kwana a zaune bai runtsa ba, yana tunanin kalmar da zata fito daga bakin Ammy ya haka, a hankali ya furta.. "Zan tsi.....!." Wannan kalmar ce ta tsaya nasa a rai, yana mamakin Ammy zata iya tsine masa akan Farha...? _Washegari da safe,_ Amal ta fito daga gidansu cikin tsararren motarta, Kalar motar ta saje da kayan jikinta: brown colored abaya mai bubu ya sha kwalliya, da golden eyeglasses akan dara-daran idanuwanta, da takalmi mai tudu. Handbag da wayarta a hannu ɗaya, lokaci da ta iso company kowa yana bata girmanta da gaisuwa na musamman... Security a mashigar kamfanin suka buɗe mata ƙofofi tare da miƙa gaisuwa: "Good morning, Miss Abdulsamaad," suka ce, suna nuna girmamawa. Amal ta murmusa cikin ladabi: "Good morning, sir. Thank you." Tayi parking motar ta a wurin parked.. Ta shiga cikin babban lobby, tayi amfani da elevator zuwa office floor inda Maleekh yake, dake ta wurin Office ɗinsa yake, amma sai ta fara shiga office ɗin Maleekh kafin ta shiga nata.... Bayan ta isa office, ta gaishe shi cikin girmamawa. Maleekh ya fita daga corner office ɗinsa tare da murmushi ya ce "Beb, ready for your first executive tasks?" Amal ta amsa cikin ladabi da nishaɗi: "Yes, Yaya Maleekh. Ina so in tabbatar da zan yi aiki kamar yadda aka sa ran." Maleekh ya ce: "Good. Zan fara da showing you the operations, sannan za ki fara handling some executive emails da scheduling." Fita suka yi zuwa office ɗinta.. Ma’aikatan kamfanin suna kallonta, suna murmushi da mamaki saboda yadda take tsaye da ladabi, da yadda take professional a kowa da kowa. Bayan sun shiga office ɗinta. Maleekh ya nuna mata babban conference table: "Ga kujerunka a nan, ga computer ɗinki, sannan ga dukkan files da za ki fara aiki da su." Amal ta zauna, ta fara sorting emails, scheduling meetings, da drafting documents. Maleekh yana tsaye kusa da ita, yana bayar da guidance: "Always respond professionally, and ensure no detail is missed. This is how we maintain CashTalk’s standards." Amal ta ɗauki notes, tana fahimtar kowanne abu da kyau. duk ma’aikata sun lura da yadda take indispensable assistant, wani daga cikin ma'aikata sun shigo office ya ce "Wow, Miss Amal, you are very organized. I can see why CEO appointed you," wani ma’aikaci ya faɗa. Maleekh ya miƙe, ya yi murmushi sannan ya ce "I told you she’s talented. And you’ll see… she’s going to make life much easier for all of us." Amal ta murmusa cikin nutsuwa, tana jin ƙwarin guiwa saboda support daga Maleekh da yarda daga ma’aikata. A ƙarshen ranar, Maleekh ya yi mata private discussion a his office, suna zaune kusa da glass window ya ce "Beb, I am impressed with your performance today. You really understood the flow fast." Amal ta murmusa, tana jin daɗi: "Thank you, Yaya Maleekh. Na yi ƙoƙari sosai koh?." Maleekh ya faɗa da nishaɗi: "Keep this up, and soon everyone will know you as my indispensable assistant." Amal ta kalle shi da murmushi, tana jin cewa ya amince da ita sosai. Bayan wannan, Amal ta fita daga office, tana jin nishaɗi da ƙwarin guiwa saboda first successful day a CashTalk. _Washegari_ Bayan ta iso cikin girmamawa.. Amal ta shiga office ɗinta a CashTalk. Tana duba emails, schedules, da reports da Maleekh ya tura mata. Ta fara tsara appointments, ta yi organize client meetings, kuma ta fara ƙirga budgets da spreadsheets cikin sauri da kyau. Maleekh ya shigo office ɗinta, yana murmushi ya ce "Beb, yau zamu fara strategy meeting ɗin mu, kafin ma’aikatan su iso." Amal ta miƙe, ta ɗaga kai, ta ce: "Shiryashi nake, Yaya Maleekh. Duk wani task da kake buƙata, zan tsara shi yadda kowa zai fahimta." Maleekh ya dubeta, yana murmushi. "Kin tabbata zaki iya komai da kanki. Ina jin daɗin hakan.".. (In aka zo office ba batun soyayya domin daga CEO har assistant ba lokaci😅😅) Suna zaune, suna tattauna private projects da clients, suna shirya budgets, da deadlines. Maleekh yana dariya, yana cewa: "Tin da kina matsayin assistant, babu wani project da zai tsaya a CashTalk.".. Amal ta yi murmushi ta ce "Ko shakka babu, Yaya Maleekh, za mu tabbatar da cewa duk clients da tasks suna tafiya smoothly." Bayan wasu lokaci, ma’aikatan sun shiga office don team briefing. Amal ta jagoranci wasu questions, tana bayar da guidance ga staff. Duk wanda ya tambaye ta, tana ba da amsa cikin nutsuwa da fahimta, har ma wasu staff suka yi dariya da nishaɗi akan irin attitude ɗinta da professionalism. Maleekh ya tsaya a gefe yana kallonta, yana jin nishaɗi sosai ya ce "Yau Beb ta tabbatar min, ita ba kawai assistant ba, har da driving force ga kamfanin mu." Daga nan, ma’aikatan suka jinjina mata. Amal ta yi musu murmurshi, tare da cewa: "Ku yi aiki da ni kamar team ɗaya, insha Allah zamu samu nasarori da yawa." Washegari da safe, Amal ta dawo CashTalk cikin tsararren motarta... Ta isa office ɗin kamfanin, tana shiryawa don babban show broadcast da za ta jagoranta a TV, domin ta nuna cigaba da nasarorin kamfani. A TV studio ɗin kamfanin, Amal ta shige, ta duba lighting, cameras da microphones tare da technical team. Ta tabbatar komai na aiki lafiya kafin ta fara jawabi. Daidai lokacin broadcast ya fara. Amal ta tsaya a gaban camera, murmushi tayi, sai ta fara jawabi: "Assalamu alaikum, masu kallo. Ni ce Amal Abdulsamaad, mataimakiyar shugaban kamfani CashTalk, CEO Maleekh Abdul-Majeed. Yau zamu kawo muku labarin cigaba da nasarorin kamfanin mu, tare da gabatar da sabbin ayyuka da muka fara." Voice ɗinta ya cika da kwarjini da natsuwa, kamar yadda take jarida, kowa a TV yana sauraro da kulawa. Ta fara gabatar da wasu statistics, projects, da sabbin initiatives na kamfani. Duk lokacin da take magana, ma’aikatan da ke kusa da ita suna kallonta da mamaki, suna dariya da jinjina mata. Maleekh daga office ɗinsa na kallo a TV, yana sipping coffee, yana murmushi, yana cewa: "Beb na, yanzu duk duniya suna ganin iya aikinki. Wannan shine voice ɗin da nake son ji a kamfani na." A gida kuwa, Ammy da Farha suna zaune a falon gidan su, suna kallon TV. Gaba ɗaya fuskokinsu cike da haushi da kishi. Ammy ta ce: "Maleekh, wannan yarinya ta kama ka sosai, tana aiki a kamfaninka, kuma yanzu duk duniya suna ganin ta, wani irin asiri tayi wa yarona? Domin na tabbata ba haka kawai ta barshi ba, gaba ɗaya ta haukatar mun da yaro, yaron da baya kula ko wace mace, wanda zaman sa yafi yinsa a England amma yanzu saboda ita yaƙi komawa sannan saboda ita yake bijire mun..." Farha tana tafa hannu da ƙarfi, tana cewa: "Ya Allah! Wannan ya fi ƙarfin zuciyata! Haka Female ɗan talaka ke cin nasara a cikin rayuwar matashin mai kuɗi!? Bazata taɓa kyale shi ba daman, ta gama da shi..." Amal kuwa a TV tana ci gaba da jawabi, tana gabatar da sabbin projects, tana nuna professionalism da charisma. Voice ɗinta ta cika da kwarjini, tana ba da labarin kamfani da sabbin initiatives. Kowa da kowa a CashTalk ya shaida cewa Amal ta zama indispensable assistant. A ƙarshen broadcast, Amal ta yi murmushi, ta ce: "Na gode sosai, kuma insha Allah za mu ci gaba da kawo cigaba da nasara ga kamfanin mu." Maleekh daga office ɗinsa ya tura hannu yana yi mata thumbs up, murmushi yayi, yana jin nishaɗi sosai... Ammy da Farha sun ci gaba da kallon TV, zuciyarsu cike da kishi da haushi, yayin da Amal take haskakawa a matsayin tauraruwa a kamfanin Maleekh.... *TO PAH ZAN YI WANI ƊAN COMMENT NIMA....* *A YANZU ZA'A FAHIMCI CEWA KWAKWALWAR MACE DA NAMIJI SUN BANBANTA, KAMAR YANDA AKE CEWA TUNANIN MACE DA NAMIJI BA ƊAYA BANE, TABBAS HAKANE NAMIJI YAFI MACE ZURFIN TUNANI DA WAYO...* *MEYASA NACE HAKA?..* *SABODA A LOKACIN DA AMAL TAKE TASHEN TA A GIDAN RADIO KOWA DA KOWA YANA YINTA, A LOKACIN MALEEKH YAKE TA NACI AKAN JAWO TA KAMFANINSA DA TAYIN MAKUDAN KU'DADE, YA BADA CHECK NA BILLIONS DOMIN TA DAWO AIKI KARKASHINSA TAƘI, AMMA GASHI A RUWAN SANYI YA SHIGE JIKINTA, TA HANYAR SOYAYYA YA JAWOTA KAMFANIN BA TARE DA CHECK BA😢😢* *KUƊIN DA ZATA IYA GUDANAR DA RAYUWARTA DA SHI AMMA TAYI LOSING, DUK DA MUTUMIN BA BUTULU BANE TANA CIN MORIYARSA DUK DA HAKA 😅😅😅* asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 35 to 36 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Inna Ta Ziyarci Amal a CashTalk Ranar yau ta kasance ta musamman ga Amal, domin Inna ta zo kamfanin CashTalk domin ta ga inda jikarta ke aiki. Daga bakin get ɗin kamfanin aka shigo da ita, security suka yi mata iso cike da girmamawa, suka nuna ma ta hanya har zuwa cikin compound. Amal da Maleekh suna tsaye a tsakiya suka tare ta. Inna tana ƙare kamfanin da kallo, idanunta suna yawo daga sama har ƙasa, sai ta ce cikin mamaki: “Oh ikon Allah… yo dubi wuri kamar aljanna…!” Ganin tagogi da ƙofofi duk na glass mai ƙarfi, ginin kuwa tsaye sama sama, har sai da ta ɗaga kanta sosai kafin ta hango ƙarshen sa. Tsayin ginin ya wuce misali, hawa goma sha takwas kacal ga office na Maleekh, sai kuma hawan biyu da aka ƙara a saman wanda aka tanada domin ma’ajiyar kuɗaɗe. Wurin ma’ajiyar kuwa an kafa masa tsaro na musamman – security na ko’ina, ga ƙofar shiga da sai an danna code sannan ta buɗe. Idan kuma aka sa wrong code, nan take robot zai zabura da ƙarar jiniya kamar karar wuta, robot ɗin kofar tsaron zai ɗauka duk wanda ya yi kuskure number to ya shigo a matsayin ɓarawo ne... Inna sai kallo take yi tana faɗin: “Subhanallah… wallahi duniya ta lalace, yanzu haka aka zubar da kuɗaɗe tamkar a bola ake d'ibar su...!” Maleekh da Amal suka saka Inna a tsakiya suka nufi stairs ɗin escalator. Da suka iso wajen, Inna ta tsaya cak tana kallon matakala yana motsi da kansa kamar maciji. Da sauri ta zaro ido tana faɗin: “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Amal, wannan menene kuma? Matakala ne ko maciji ne yake tafiya da kansa haka?” Amal dariya take yi, tana ce mata: “Inna wannan ba komai bane, escalator ake ƙiransa. Zai tafi da mu sama da kansa.” Da ƙyar ta ɗora ƙafar Inna kan stairs ɗin, Maleekh kuma ya tallafe ta tare da ɗago ta kan benin. Suka taka nan da nan escalator ya fara tafiya. Inna ta firgita! Ta daka ihu tana faɗin “Wayyo Allah na! Mutuwa ta iso! Amatu, Maliku ku kama ni, ku riƙe ni!”... Tana rawar jiki ta tsuguna, daga nan ta kwanta bisa escalator ɗin, ta rungume shi tamkar zai tafi da ita. Escalator kuwa bai tsaya ba sai tafiya yake da ita a kwance, tana zunduma ihu, yayin da Amal da Maleekh suke tsaye suna dariya kamar ba za su tsaya ba. Sauran mutane da ke hawa da sauƙa suna ta kallonta suna dariya.. Escalator dai an yi shi biyu bangaren hawa sama, da bangaren sauƙa ƙasa amma hankalin kowa ya koma kan Inna... Da suka sauƙa daga saman escalator, Inna ta fara sauƙe ajiyar zuciya tana jijjiga kanta ta ce: “Amal! Wallahi na gaji da wannan kamfanin nakun. Ni ba zan iya shiga sama ba, ku sauƙar da ni ƙasa, na koma gida tun yanzu.” Amal ta tsaya tana kallonta, ganin Inna ba wani nutsuwa zata yi ba yasa ta ce cikin lallashi.. “Inna mu je na saka ki taxi ya maidar da ke gida. Kada ki damu.” Inna kuwa ta ce cikin rawar murya: “Amatu, ki yi wa Allah da Annabi, kar ki ƙara saka ni kan wannan matakala mai tafiya da kansa. Wannan ai ba na mutane bane, na aljanu ne. Na rantse idan na koma gida yau, in kin ƙara ganina a nan ki yanke mun ƙafa.” Amal ta buɗe baki da mamaki ta ce “Haba Inna, wannan wane irin kauyanci ne kuma?” Maleekh yana gefe ya kasa riƙe dariyarsa, yana ce mata: “Amal, ku bar escalator, sai ku bi ta elevator. Wannan ya fi sauƙi gareta.” Amal ta yi murmushi, ta ce: “To shikenan Inna, muje.” Suka nufi elevator. Amal ta danna, ƙofar ta buɗe. Inna ta yi baya da sauri tana zaro ido ta ce: “Ikon Allah! To nan kuma wane irin duniya ne za ku saka ni ciki? Wallahi Amal wannan ai kurkuku ne.” Amal ta kwashe da dariya ta ce: “Inna, ba kurkuku bane. Elevator ne ake ƙiransa. Shi ne zai sauƙar da mu ƙasa.” Da ƙyar ta ja hannun Inna suka shiga ciki. Da ƙofar ta rufe, Inna ta fara zabga salati da addu’o’i, tana kankame Amal da hannunta na rawar jiki. Da elevator ya fara motsi ƙasa, Inna ta fashe da kuka. “Wayyo mutuwa! Amal wannan ina yake kai ni!? Na rantse yau dai na shiga tarkon aljanu!” Har sai da suka isa ƙasa, suka fita daga ciki. Inna tana share hawayenta, ta tsaya cak ta ce: “Amatu, idan kin ƙara ganina a wannan shegen kamfanin naku, ki yanke mun kafafu! Allah ya haneni dawowa, wuri kamar gidan sihiri.” Amal ta girgiza kai cikin dariya, sannan ta ƙira wani security ya taimaka ya saka Inna a taxi ta koma gida. Amal kuwa ta juya cikin kamfanin, tana ɗan murmushi, tana tunanin irin abun dariyar da Inna ta nuna yau. ☆☆☆☆☆☆ Bayan Amal ta raka Inna har ta fita daga kamfanin, sai ta juya ta dawo ciki. Amma kafin ta shiga office ɗinta, zuciyarta ta ja ta kai kai tsaye wurin Maleekh. Ta ɗan tura ƙofar office ɗinsa a hankali, sai ta shiga da murmushi a fuskarta. Maleekh kuwa yana zaune a kan kujerarsa mai juyawa, yana kallonta cikin sanyi, kamar ya san ita ce zata shigo. Amal ta zauna a kusa da shi tana lumshe ido, kafin ta buɗe baki ta ce cikin shagwaɓa: “Yaya Maleekh…” Da sauri ya katse ta, ya ɗaga yatsarsa yana dariya kaɗan ya ce “Kada ki sake ƙirana da haka, haba kamar wata bakauyiya. Kin manta muna soyayya? Ga sunayen soyayya kala-kala, amma sai ki kirani Yaya Maleekh…” Amal ta yi shagwaɓar gyara murya, ta ce: “To my love…” Ya girgiza kai yana murmushi ya ce “Tsohon suna kenan. Ba zan amince da shi ba.” Ta yi dariya, tana gyara zama a kujerar da ta matsa kusa da shi sannan ta ce “To my chocolate…” Sai ya dafe goshinsa, yana yin kamar ya ji haushi ya ce “A’a, wannan ma bai yi mun ba. Chocolate kuma ai zai iya narke wa.” Amal ta kwaɓe baki, tana kallonsa da shagwaɓa ta ce “To Baby…” Maleekh ya yi dariya yana girgiza kai ya ce “Wannan sunan ya fi dacewa da ni in kiraki da shi, ba ke da ni ba. Kenan kin ɗauke ni jariri kenam?” Ta ce cikin dariya: “To Shalele…” Ya turo baki kamar mace, ya ce: “Ni ɗin mace ce?…Za ki sa ayi mun dariya wallahi.” Amal ta ɗaure fuska tana dariya a hankali ta ce “To Bee Heart…” Maleekh ya zaro ido, yana kallonta da mamaki ya ce “Meye Bee Heart kuma? Wani sabon kalma kika ƙirƙira ke kaɗai?.” Amal ta tintsire da dariya tana ce wa “Ƙudan zuman zuciya mana, ai soyayya ce…” Ya yi dariya sosai, yana kallonta da ƙauna ya ce “To a’a fa, ba zuciyar ƙudan zuma za ki ce, wannan sunan ko armashi babu....” Amal ta cije lips ɗinta, tana kallonsa da shagwaɓa ta ce: “Wayyo Allah, to kai ka zaɓa sunan da kake so. Honeybee, Sweet Bee, My Bee…” Kafin Maleekh ya ba da amsa, ƙofar ta buɗe. PA (manager ɗin kamfanin) ya shigo da gaggawa, amma da ya ga irin hirar soyayyar da suke yi, sai ya saki murmushi ya ce: “Na zaɓa masa! My Bee → tamkar ace masoyina, kai ne ƙudan zumana. Boss ɗina tamkar ƙuda ne mai addabar zuciyarki…” Amal ta tafa hannu da shewa, tana dariya sosai ta ce “Yeeeeeee! Gaskiya ne wallahi. You are my Bee 🩷🩷🩷” PA ya kunna kiɗa a ƙaramin speaker ɗinsa, ya ce: “Yau mu yi rawa mu sha soyayya!” Nan take Amal ta miƙe tsaye tana juyawa cikin nishaɗi, ita da PA suka hau rawa suna tikar rawa sosai, suna dariya suna zagaye ofishin. Maleekh kuwa ya zauna a kujerarsa yana kallonsu da murmushi, sai ya girgiza kai yana ce wa. “All of you are just childish.” Amal ta tsaya cak tana kallonsa cikin shagwaɓa, ta ce: “Mu ne yarinta ke damu, my Bee?..” Ya kalli idonta ya ce: “Eh mana! You’re all behaving like kids.” Amal ta yi tsalle tana dariya, ta koma ta ci gaba da rawa tare da PA. Maleekh kuwa ya juya yana duba computer ɗinsa, yana murmushi a ransa, zuciyarsa cike da ƙaunar Amal duk da shagwaɓarta. PA yana rawa yana ɗaga hannu sama, yana cewa: "Amal, ki ga yadda nake rawa saboda boss ɗina ya zama ƙudan zumanki. Ai yau zan yi mishi gasa a kan soyayyarki!" Amal tana dariya sosai har tana riƙe ciki, ta ce: "Ka shiga uku, ka isa kayi wa Yaya Maleekh ɗina gasa?" PA ya ɗan karkata kai yana kwad'a rawa, ya ce: "Ba Yaya Maleekh ba, My bee fa! Daga yau shi My bee, ni kuma zan zama your sugar manager." Amal ta fashe da dariya tana tafa hannu ta ce "Wayyo Allah! Sugar manager fa!" Maleekh wanda yake zaune yana bin su da kallo ya yi murmushin ƙarfin hali, amma a zuciyarsa sai yake ji kamar kada Amal ta dinga taɓa shi da barkwanci haka, saboda tsantsar soyayyar da yake ji gareta. Ya ɗan yi ƙasa da muryarsa yana cewa cikin zuciya: "Ta ina zan fara nuna mata yadda nake jin soyayyarta ya cika min zuciya? Ta ina zan bayyana mata cewa ban taɓa yin soyayya irin wannan ba?" Sai kuma ya ga PA ya kama hannun Amal suna juyawa cikin rawa. Nan fa Maleekh ya hargitso cikin tsananin kishi ya yi saurin tashi ya isa wajensu, ya ce da ɗan tsawa mai taushi: "Enough Amal!" Amal ta tsaya cak, tana dariya, tana kuma kallonsa cikin shagwaɓa ta ce "My bee… me kuma? Mu dai muna nishaɗi ne kawai fa…" Maleekh ya ja hannunta a hankali, ya sa Amal ta zube a jikinsa. Ya rungumeta sosai kamar ba zai sake ta ba, sannan ya lumshe ido ya ce a hankali cikin wayincewa: "Amal… ba nishaɗi kawai ba ne. Kin zama zuciyata gaba ɗaya. Kin zama numfashina. Kin zama dalilin farin cikina." Dariya ta tsaya a bakin Amal, idonta ya cika da hawayen farin ciki, Ta ce a shagwaɓe: "My bee… da gaske ka ke?" Ya ɗan haɗe goshinsa da nata, yana furta: "Eh Amal, da gaske nake. Na faɗa a karon farko, ki sani… ina sonki fiye da komai." PA kuwa ya ja bakinsa gefe yana kallon su da shagwaɓa ya ce: "To ai yanzu kun bani kunya. Na bar muku fagen soyayya… amma ku tuna dai ni sugar manager ɗin ku ne!" Suka kwashe da dariya gaba ɗaya. Bayan wannan ɗan nishaɗin soyayya, Amal ta yi murmushi ta kwace kanta daga jikin Maleekh, ta ce: "My bee, yanzu dai bari na wuce zuwa office ɗina kafin jama’a su fara ganin kamar ni ban da aiki sai soyayya kawai…" Maleekh ya ɗan kwaɓe fuska, cikin shagwaɓa ya ce: "To ai ni ne aikinki, ki zauna nan kawai." Amal ta yi dariya sosai har ta rufe baki da tafin hannu ta ce "Wayyo Allah, kai wallahi My bee kana da wasa. Amma bari na wuce, akwai report da nake son duba kafin broadcast ɗin yau." Ta kama hannunsa a shagwaɓe ta ce: "Za ka zo mu ci lunch tare da rana?" Ya kalli idonta yana murmushi mai zurfi, sannan ya ce: "Idan baki ƙira ni ba, bazan zauna da kowa ba. Dole Lunch ɗin yau ya zama tare da ke." Suka yi murmushi da juna, sai Amal ta juyo ta nufi office ɗinta... Shi kuma Maleekh yana shirin barin campany zai koma gida.. Da ta shiga, sai taga komai ya gyaru, an shirya mata sabuwar kujera, sabbin system, da flowers masu ƙamshi a gefen teburinta. Amal ta tsaya cak tana kallon komai da mamaki, sai ta ce cikin muryar da take rawa: "Subhanallah… wa ya shirya min haka?" PA wanda ya leƙo daga ƙofa ya ce: "Ni ne sugar manager, amma Boss ɗin ki ne ya bayar da umarni. Ya ce office ɗinki ya dace da irin darajar ki a matsayin Amal Voice." Amal ta runtse ido da murmushi, zuciyarta cike da daɗi, ta furta a hankali: "My bee… kai kaine komai nawa." Bayan Amal ta zauna a sabon office ɗinta, ta duba system ɗinta, sai ta ga an shirya mata speech ɗin da zata gabatar a yau a matsayin mataimakiyar shugaban kamfanin CashTalk FM. PA ya shigo da sauri, yana ɗauke da mic da camera crew. Ya ce cikin annashuwa: "Madam Amal, lokaci yayi, kowa ya shirya don broadcast ɗin yau a CashTalk TV. Jama’a dubun-dubata za su kalli muryarki." Amal ta ɗan ɗaga kanta da murmushi mai cike da kima, ta ce: "Alhamdulillah… wannan rana ce da bana tsammanin zata zo haka da wuri. Amma yanzu na shirya." Da aka kunna camera, aka fara live, Amal ta miƙe tsaye cikin kyan suturarta da kyakkyawar kwalliya ta manyan mata. Ta fara da cewa: "Assalamu alaikum wa rahmatullah. Ni ce Amal Abdulsamaad, a yau ina tare da ku a matsayin Executive Assistant to the CEO of CashTalk Group. Wannan rana ce ta musamman, domin ina mai sanar da ku sabbin shirye-shirye, manufofi, da tsare-tsare da kamfaninmu ya kawo domin ƙara haɗin kai, ƙarfafa ɗabi’ar gaskiya, da kuma bayar da damar fitar da muryar talakawa." Muryarta mai daɗi ta cika ɗakin, kowa ya tsaya kallonta, daga ma’aikata har zuwa masu kallo a gidajen su. An kawo camera kusa da fuskarta, sai ta ɗan murmusa ta ce: "CashTalk ba wai kamfani bane kawai, CashTalk Voice ce muryar ku, muryarmu, muryar gaskiya!" Bayan Maleekh ya koma gida, yana zaune a babban parlour ɗin su tare da Ammy da Farha. Da suka ga Amal a television cikin wannan kyan jawabi, sai Ammy ta yi tsaki mai ƙarfi ta ce: "Wallahi Maleekh ka bani kunya, har wannan yarinyar zaka sa a ranka haka? Har ta samu damar fitowa a TV tana magana a matsayin assistant ɗinka? Ka ji kunya wallahi" Farha kuwa ta buga ƙafa ƙasa ta ce cikin haushi: "Ba zan lamunta ba! Amal ce zata zama assistant ɗin mijina a gaban duniya? Wallahi bazan yarda ba!" Maleekh kuwa, maimakon damuwa, sai murmushi ya yi cikin nutsuwa ya ce: "Kuna iya jin haushi, amma ba za ku iya hana gaskiya fitowa fili ba. Amal is my choice, kuma duniya zata shaida hakan." Da Amal ta gama jawabi aka rufe shirin, nan take kowa a cikin kamfanin ya yi mata ihu da tafi. Wasu suka ce "Amal Voice is back! Amal ta dawo!" Social media kuwa ya hargitse. Hashtag ɗin #AmalVoiceReturns ya bazu. Kowa na posting hotonta, yadda take tsaye cikin nutsuwa, tana jawabi da murya mai ƙarfi da girmamawa. ☆☆☆☆ Kaduna Gidan rediyon Rayuwa FM (tsohon gurinta) Ma’aikata da tsoffin abokan aikinta suna kallo, suka tsaya da mamaki. Wata kawarta Maryam ta ce cikin hawaye: "Alhamdulillah! G Amal ɗin da aka zalunta aka kora ta hanyar cin hanci, Gashi yanzu ta koma babban matsayi a Abuja, assistant CEO!" Wani tsohon producer ya ce cikin jin kunya: "Rayuwa da gaske juyi-juyi ce. Mun ga Amal ta fāɗi fururu, yanzu kuma mun ga ta tashi tsaye. Yanzu mun ga ta zarce mu gaba ɗaya." Makotansu a Kaduna sun taru suna kallo a TV. Kowa sai mamaki da tafi. Wata tsohuwa ta ce: "Allah ya ɗaga darajarta. Yarinya mai gaskiya ba ta taɓa faɗi ƙasa har abada. Ga shi yanzu ta fi duk wanda ya zalunce ta." ☆☆Jawabin rayuwa Voiceover☆☆ Ana nuna hotunan Amal tun daga lokacin tana ɗan ƙaramin table a gidan rediyon Rayuwa FM, tana ɗauke da littafi tana rubutu da paper. Ana kuma nuna lokacin da aka koreta... Sai kuma a juya hoton zuwa lokacin yanzu tana tsaye a gaban camera a babban kamfani, tana jawabi cikin nutsuwa... Muryar narrator ta shiga: "Rayuwa tafiya ce mai cike da darussa. Wani lokaci tana jefa mutum ƙasa, wani lokaci tana ɗaga shi sama. Amal Abdulsamaad ta sha wahala, ta fuskanci zalunci, ta shaida cin hanci da rashin adalci. Amma ta ƙi fāɗuwa ƙasa. Yau, ga shi daga ƙaramin matsayi a Kaduna, zuwa babban matsayi a Abuja. Wannan shi ne rayuwa daga ƙananan ƙalubale, mutum na iya tsayawa ya ɗaga kansa har ya zama abin koyi ga duniya.".. Inna dake nan Abuja har da hawayenta ganin yanda ake ta yabon Amal.. daga talauci yanzu sun dawo masu dukiya.... Yau ranar weekend babu aiki Amal tana tare da Inna... Soyayya a tsakanin Amal da CEO Maleekh ya zurfafa sosai... A can gidan su Maleekh kuwa.. Saboda tsananin tsanar Amal da kuma ganin tana samun ɗaukaka ta sanadiyar Maleekh yasa Ammy ta fāɗi ƙasa ta tayar da bori... Ammy ta tayar da aljanun ƙarya sai ihu take tayi a gidan, ga Abbansu baya Nigeria.. Gaba ɗaya Ammy ta rikice gidanta da ihu.. Ammy ta na burgima a ƙasa tana ihu, tana zabura tana jifa maganganu irin kamar aljanu ne suke magana, tana faɗin "Zamu haukatar da mahaifiyarku! Indai Maleekh bai rabu da Amal ba! Indai Maleekh bai auri Farha ba! Zamu shiga duniyar mahaifiyar ku, mu hallaka taaa!" Arfat da Islam suka zube da kuka, zuciyarsu cike da tsoro da ruɗani. Suka kamo hannun yayansu Maleekh suna roƙonsa: "Dan Allah Yaya, ka amince da auren Farha. Kaga idan ba haka ba, Ammy zata mutu wallahi!" Farha ma ta haɗe hannu da hawaye tana matsowa kusa: "Yaya Maleekh, dan Allah ka amince ka aure ni. Nasan baka son mahaifiyarka ta hallaka ko?.." Maleekh ya rasa yanda zai yi. Zuciyarsa na ci masa gaba ɗaya. Wani ɓangare na zuciyarsa na bugawa da ƙarfi saboda soyayyar Amal, wani kuma na rikicewa saboda ganin mahaifiyarsa a kwance tana bori. Nan take ya yi saurin ɗaukar wayarsa, ya ƙira wani babban malamin addini da yake girmamawa, yana masa bayanin abin da yake faruwa... Nan malamin ya sanar cewa yana zuwa.. Bai jima ba, malamin ya iso gidan cikin nutsuwa da salati a bakinsa. Yasa a shigar da Ammy wani ɗaki.. Farha da Islam ne suka ɗaga Ammy suka kaita ɗakin ta, sannan suka dawo falo, duk suka zauna a falon.. Malamin ne ya shiga ɗakin, ya tarar da ita tana burgima a kan carpet, tana ihu tana nanata kalmomi masu tayar da hankali: "Maleekh dole ya rabu da Amal! Dole ya auri Farha!!" Malamin ya tsaya ya na kallonta cike da shakku. Sai zuciyarsa ta ce: "Wannan ba aljanu bane gaskiya, wannan shiri ne." Ya matso da nutsuwa, ya ce mata da murya mai cike da iko: "Ki daina wannan kwaɗayin yaudara, ba aljanu bane na sani. Ki tashi ki faɗa min gaskiya, me ya sa kike wannan abu a matsayinki na uwa?!" Ammy ta yi shiru na ɗan lokaci. Sai daga baya ta tashi zaune ta fara rawar murya cikin hawaye ta ce "Idan ban yi haka ba, Maleekh bazai taɓa jin maganata ba! Na tsani Amal a zuciyata! Na tsani ganin ta tare da ɗana! Saboda haka nayi wannan shirin bori don ya ji tsoro ya rabu da ita!" Malamin ya girgiza kai, ya ce: "To, wai saboda ɗanki ya ƙi auren wacce kike so, ya zaɓi wacce zuciyarsa take so, shiyasa kika kai kanki ga irin wannan ƙarya? To idan ya auri Farha, shin ke ce zaki zauna masa da ita? Ko kuwa kai tsaye zai zauna da ita a matsayin matarsa?" Ammy ta ce cikin kuka: "Don Allah Malam, ka yi masa magana. Ka ce ya yi abinda nake so. Ban yarda Amal ta cigaba da zama cikin rayuwarsa ba, wallahi ba zan taɓa yarda ba!" Malamin ya yi shiru na ɗan lokaci. Daga nan ya ce: "To shikenan. Zan yi masa magana. Zai yi abinda kike so, zai auri Farha insha Allah. Amma ki ji tsoron Allah ki daina yin wannan bori na ƙarya. Ba kyau, ba daraja ga mace mai mutunci bane." Bayan wannan tattaunawar, malamin ya fito tare da Ammy daga ɗakin. Duk yaran da Farha suka yi shiru suna jiran amsa... Ammy ta fito tana share hawaye, amma idonta na cike da murmushin farin ciki. Malamin kuwa ya ɓoye gaskiyar da ya gano, bai gaya musu cewa bori ne na ƙarya ba, saboda ya ja mata girma a wajen ‘ya’yanta. Ya ce musu cikin nutsuwa: "Ku kwantar da hankalinku. Zancen ya ƙare, komai zai yi daidai. Ku cigaba da addu’a kawai." Arfat da Islam suka natsu suka yi godiya. Farha kuwa ta yi dariya cikin sirri, zuciyarta ta ce: "Yanzu dai dole sai na zama matar Maleekh." Maleekh dai ya tsaya can gefe zuciyarsa na tafarfasa. Yasan akwai wani abu.. Malam da Maleekh ne suka yi waje, zama suka yi domin akwai maganar da malam yake son sanar da shi.. Malam ya zauna gaban Maleekh, Ya dubi Maleekh da ido mai cike da natsuwa, ya ce da shi: "Maleekh, kai ɗa ne mai biyayya. Na san yadda kake ƙaunar mahaifiyarka. Kuma na san yadda take ƙaunar ka. Duk tsanarta ga Amal saboda ƙaunarka ne. Yanzu ina roƙonka da ka yi wa mahaifiyarka biyayya. Cika mata buri. Ka auri Farha. Wannan ne zai sanyaya ranta." Maleekh ya girgiza kai, zuciyarsa na harbawa da ƙarfi. Ya kalli Malam cikin tsananin ɓacin rai amma ya tare harshensa saboda girmama shi. Maleekh ya ce "Ni auren Farha? Kenan dole sai na rasa Amal? Kenan dole sai na hallakar zuciyata saboda farin cikin mahaifiyata? Wayyo Allah." Malam ya zauna cikin nutsuwa yana duban Maleekh da damuwa sannan ya ce "Maleekh, ka sani uba da uwa su ne ginshiƙin ɗa. Ka kuma sani, mahaifiyarka tana da buri babba a kanka. Ka san yadda ta dage wajen ganin kai ne abin alfahari ga wannan gida. Don Allah ka yi haƙuri ka bi abinda take so. Aure da Farha ba zai cutar da kai ba, sai dai ya cika mata burinta. Ka yi tunani, ba dukkan lokaci muke samun damar girmama iyaye da rai ba." Maleekh ya lumshe ido yana jin zafin zuciya, yana ta harbawa da ciwo ya ce "Malam… na sani. Na san girman iyaye. Na san darajar uwa. Amma zuciyata kamar tana so ta fasa kirjina ta fito. Ban taɓa jin tsanar aure irin wannan ba a rayuwata. Amma saboda kai, saboda maganarka, malam… ba komai." ya furta cikin murya mai rauni.. Malam ya dafa kafaɗarsa da tausayi ya ce "Ka yi Haƙuri. Wannan rayuwa ce, wani lokaci tana ɗauke da abu da zuciya ba ta so amma tilas ka rungume shi. Allah ya sauƙaƙa maka." Maleekh bai iya cewa komai ba sai ya yi shiru, yana jin kamar yana shirin nutsewa a cikin baƙin ciki. Ya sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi, sannan ya ce a fili cikin ladabi: "Ba komai Malam. Zan yi duk abinda ku ka ce." Malam ya ɗan yi murmushi cikin gamsuwa ya ce.. "Allah ya saka da alheri. Wannan ne alheri a gareka." Tun daga wannan rana Maleekh ya rikid'e. Bai sake zama cikin dariya ko annashuwa ba. Ko a company an lura da shi baya cikin nishaɗi, baya yin dariya kamar da. Amal kuwa a matsayin mataimakiyarsa tana lura sosai da halinsa. Ita ce tafi kusa da shi a ofis, ita ce take tare da shi a ayyuka, amma yanzu kullum tana ganin damuwarsa... A ofishinsa suka zauna. Amal ta matso kusa da shi tana kallon fuskarsa. Ta ce "My Bee… me ke faruwa da kai? Kwanan nan kana canzawa sosai. Ba ka cikin annashuwa, baka cikin wargi da dariya kamar da. Ka fara bani tsoro wallahi." Maleekh ya ɗago ya kalleta, idonsa cike da damuwa. Ya so ya faɗa mata, amma ya kasa. Hannunsa ya ɗora akan nata, yana jin zafin soyayyarta a jikinsa.. A ransa yake faɗin "Taya zan gaya mata cewa dole ne in auri Farha? Taya zan hallaka zuciyarta? In fa ta ji wannan maganar cewa zata rasa ni, shin wane hali zata shiga?" Sai kawai ya danne zancen ya ce a fili: "Ba komai Amal… kawai damuwar aiki ne. Ki kwantar da hankalinki." Amal ta runtse ido, zuciyarta na tsananin damuwa ta ce "Kai kaɗai ne farin cikina yanzu, bana son ganin ka cikin damuwa. Don Allah ka gaya min gaskiya, ni fa zan iya jurewa komai muddin kana lafiya." Maleekh ya kalleta, idonsa ya kaɗa ja saboda yawan tunani. Sai ya saki hannunta a hankali, ya juya kansa gefe ya ce. "Na gode, amma ki kwantar da hankali. Komai zai yi daidai." 📍 Amal ta koma ofis ɗinta cike da tambayoyi. Zuciyarta tana bugawa: "Me ke damun Maleekh haka? Shin wani abu ya same shi ne? Ko wani abu yake ɓoye min? Ya Allah, kada wannan soyayya ta lalace." Daga wannan ranar Maleekh ya ɗauke ƙafarsa da zuwa wurin aiki... Saboda tsananin damuwa yanzu Maleekh ya daina zuwa company, kullum yana ɗaki daga masallaci sai ɗakinsa...zazzabi da ciwon kai da damuwa sun sako shi a gaba... Amal tana company a office ɗin ta.. Ta kifar da kanta akan table, ta shiga damuwa sosai ganin halin da Maleekh yake ciki, gashi yanzu ya daina zuwa wurin aiki, tana ƙiransa a waya, amma wayar switch up, kuma ta kasa zuwa gidan su... Hakan yasa washegari da safe kafin Amal ta wuce wurin aiki, sai da ta biyo ta unguwar Maitama layin gidan su Maleekh, tayi parking motarta a gefe guda tana cikin motar tana tunanin Taya zata samu Maleekh. Ga wayarsa ba ta shiga... Tana cikin wannan tunanin ne ta hango shi daga nesa nesa ya fito daga wani tsararren masallaci wanda yake gefe da gidansu.. Da sauri ta fita tana ambatar sunan sa.. Cike da mamaki yake bin ta da kallo, ya ce "Amal lafiya kuwa?..." Amal bata san komai ba. A wurinta Maleekh yana cikin shiru ne saboda damuwar aiki. Ita kam tana ta fama da tambayarsa: Ta tsaya a gabansa tana faɗin "Maleekh, me yake damunka ne? Na lura ka canza sosai. Ba kamar da ba, ko a wajen company. Koda nake tare da kai, ba na ganin murmushinka kamar da." Maleekh ya kasa magana. Sai ya kalli fuskarta cikin tausayawa, zuciyarsa na karyewa. A ransa: "Taya zan faɗa miki, Amal? Taya zan gaya miki cewa Ammy ta ɗaura mun alƙawarin aure da Farha? Idan na faɗa, halinki fa? Karyewar zuciyarki fa? Ba zan iya ba." Sai kawai ya ɗauke kansa, ya ce da ita da cikin rauni: "Amal, babu komai… kawai gajiya ce." Amal ta ce "Shikenan, kai dai kana ɓoye mun ne amma nasan baka da lafiya ne, shiyasa na kasa jure wa nazo duba jikinka, yanzu zan wuce wurin aiki, zan kula da komai in sha Allah, Allah ya baka lafiya _AMALEEKH_...." Sai da Maleekh ya ji wani sabon bugun zuciya jin ta furta wannan sunan... Ba tare da ya furta komai ba ya juya daidai lokacin da hawaye yake zubo masa... Amal kuwa ta ji damuwa sosai, zuciyarta ta soma yin nauyi, tana ta tunanin meke faruwa da shi... Haka ta juya itama cike da damuwa ta shige motarta, kai tsaye Campany ta nufa... _Bayan Sati Uku_ Amal’s office, CashTalk HQ Amal ta kifar da kanta a kan table ɗinta, zuciyarta na tafarfasa. Wayarta ta sake dubawa, amma har yanzu wayar Maleekh switch off. Hawayen damuwa sun cika idonta. Bata san yadda zata isa gidansu Maleekh ba, ba kuma zata iya boye wa kanta irin damuwar da take ciki ba. Sai kawai ta ji ƙarar buɗar ƙofa. Da sauri ta ɗago kai. Amal a firgice ta furta “Innalillahi… Farha?!” Farha ta shigo da kwarjini, tana sanye da kaya masu tsada, murmushi cike da izza a fuskarta _ta ce_ “Ina miki sannu da rashin cin nasara, Amal.” Amal ta miƙe a zabure, zuciyarta na tsalle ta ce “Subhanallah! Rashin nasara kuma? God forbid! Ni kullum a cikin nasara nake. Nasara ce ma ta kawo ni inda nake yanzu!” Farha ta yi dariya cikin raini sannan ta ce “Nasara? Rashin nasararki ta farko shi ne rasa Maleekh a rayuwarki. Na zo jan kunne ne kawai, ki fita daga rayuwar mijina. Kin ji ko? Abbah na dawowa daga ƙasar waje za'a saka mana ranar biki.” Amal ta ji ƙirjinta ya buga. Wani irin shock ya rufe jikinta gaba ɗaya. Amma ta daure ta yi shiru, ta ƙuduri cewa baza ta bata martani ba.. Sai ta buɗe ƙofar office ta window side yanda take hutawa tana kallon kowa dake ƙasin building..Tana kallon ƙasan compound ɗin daga sama, zuciyarta na yi mata nauyi. Kawai sai ga Farha ta biyo ta, ta tsaya a ta bayanta, tana murmushin mugunta ta ce “Me ya faru Amal? Allah yasa yau ba zuciyarki ce za ta buga ba, sai kin ga bikina da Maleekh” Amal ta ji hawaye sun fara gangaro mata. Ta juya da tsananin kishi da zafin zuciya ta ce cikin rawar murya. “Irin ranar da kike mafarki kenam? To bazata taɓa zuwa ba. Shiyasa kike addu’ar kar na mutu. Amma ki sani, Maleekh bazai taɓa auranki ba!” Farha ta yi tsaki tare da faɗin “Hmm, to mu gani! Shin umarnin mahaifiyarsa zai bi ne ko umarninki? Wacce matsayi kike da shi a rayuwarsa?!” Amal cikin tsawa ta furta: “Ƙarya neeeee!!!” Cikin hargowa suka shaƙi juna, suka fara tururuwar dambe a saman bene, wuri mai cike da haɗari. Daga ƙasa, mutanen company da security suka taru suna kallonsu da firgici. A nan ne sai aka ga wata mota ta shigo cikin harabar company, motar Maleekh! Ya fito cikin hanzari, yana ɗaga kansa sama. Ganin Amal da Farha a tsaka da dambe a wuri mai haɗari, zuciyarsa ta tsinke! Maleekh yana ɗaga murya, zuciyarsa na harbawa ya ce “Amal!!! Farha!!! Ku dakata da wannan shirmen! Wane hauka ne wannan?!” Amma basu tsaya ba. Amal da Farha suna faman turje-turje, saboda hayaniya ba sa jin komai. Maleekh ya riƙe kansa, yana kallon inda suke, zuciyarsa kamar zata tarwatse. Idanunsa suka kaɗa da ja, jin tsoron kada wani abu mai muni ya faru.. Farha ce ta yi turus ta tura Amal baya da ƙarfi! Amal cikin razana ta yi figici, bayanta ya bugu da ƙarfen da ke zagaye bakin tsalalleku. Sai kawai jikinta ya kife, ta tsallake ƙarfen da baya, ta kai ga faɗuwa ƙasa. Sai dai cikin azama, Amal ta yi saurin riƙe ƙarfen wurin da hannunta ɗaya. Amma jikinta gaba ɗaya na ƙasa, yana kaɗawa cikin iska. Da zarar ta sake wannan ƙarfen, tana faɗowa kai tsaye mutuwa ce kawai, domin tsakanin su da ƙasa akwai tazara sosai.. Maleekh wanda yake kallon sama yanda suke, zuciyarsa ta yi wani irin tsalle. Cikin razana ya shiga kururuwa: “Amal!!! Amal!!! Kada ki sake! Ki riƙe! Zan iso gareki yanzu… zan iso…!” Amal kuwa cikin tsananin fargaba da hawayen tsoro, ta riƙe ƙarfen da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma ta kama ƙafar Farha da take tsaye a sama. Amal tana kuka tana faɗin “Farha… don Allah… kada ki bari na faɗi…!” Sai dai, saboda mugunta da hassada, Farha ta fara dukan hannun Amal da ta riƙe ƙafarta. Tana take hannun da ƙafarta, tana yakushin hannunta da ƙarfi domin ta sake ta faɗi ƙasa. Farha ta na ihu cikin mugunta tana faɗin “Ki sake ni Amal! Ki faɗi ɗin mana! Duniya ta huta da ke! Maleekh zai zama nawa ni kaɗai!” Ƙasa kuwa jama’a sun taru suna kallon tashin hankalin da ake ciki, kowa addu’arsa kada Amal ta gaji ta sake ƙarfen.. Maleekh yana ganin haka, zuciyarsa ta yi wata irin guguwa. Ya ruga da gudu cikin gaggawa zuwa elevator, zuciyarsa na bugu kamar ta tsinke ƙirji. Maleekh a ransa yake faɗin “Ya Allah, kar ka ɗauke min Amal a haka! Kar in rasa ta a idanuna…!” Elevator ya kai shi kai tsaye hawa na goma sha takwas. Bai tsaya ko da dakika ɗaya ba, ya fito da gudu kamar mahaukaci. Kai tsaye ya nufi ofishin Amal. Da ya shigo, ya nufi window sides ya hango Amal a kasalance tana riƙe da ƙarfen da hannu ɗaya, ɗayan hannun nata ta riƙe da ƙafar Farha, yayin da Farha ke ta dukanta da ƙarfi. A lokaci guda, tsananin ciwon da Farha ta jefa hannun yasa Amal ta sake ƙafar, saboda tsananin gajiya yasa ta sake ƙarfen da take riƙe da shi gaba ɗaya.. Tayi wani irin ihu, cikin kuka ta ce “Maaaaleeeeekhhh!!!” A nan ne Maleekh ya yi wani irin tsalle mai ban mamaki ya kama hannun Amal kafin ta yi ƙasi gaba ɗaya... Maleekh cikin rawar murya yake faɗin “Amal! Bazan bar ki ba! Bazan taɓa barin ki ba! Ki riƙe ni sosai!” Amal cikin kuka da firgici ta riƙe hannunsa, jikinta na lumshewa saboda gajiya. Farha kuwa, ganin Maleekh ya riƙe Amal, ta fara ture shi da ƙarfi tana ihu: “Ka saketa ta faɗa! Ka barni na huta da ita! Ka saketa, so nake ta mutu ta bar rayuwarka har abada!” Cikin ɗacin rai, Maleekh ya kasa jurewa. Ya zabga mata mari da hannunsa na hagu...yayinda yake riƙe da hannun Amal da ɗayan hannunsa.. Maleekh cikin tsawa ya ce “Ke wace irin marar imani ne!? Ke wace iriyar marar tausayin ɗan adam ne!? Ki ture ƴar uwarki haka bayan kinsan ba cigaba da rayuwa zata yi ba, da zaran ta faɗa?!” Da hannu ɗaya ya ƙara tura Farha gefe, sannan ya ɗaga Amal da ƙarfin zuciya. Ya yi ƙoƙari sosai har sai da ya jan yo ta sama da hannaye biyu, ya rungume ta sosai a jikinsa. Amal ta saka ihu tana kuka, tana riƙe Maleekh da ƙarfi kamar zata shige jikinsa. Tana kuka ta ce “Wayyo Maleekh… na shiga uku…Sauran kaɗan na mutu..!” Maleekh kuwa yana huci, zuciyarsa kamar zata fashe, yana fitar da numfashi cikin tsananin tashin hankali. A gefe, Farha cikin tashin hankali, Ta riƙo Amal tana ƙoƙarin janye ta daga jikin Maleekh. Farha cikin hauka take faɗin “Na ce maka sai ta mutu! Sai ta tafi yanda ba'a dawowa! Ni kaɗai ce za ta zauna da kai!!!” A wannan lokacin, Maleekh ya ɗauki kwalbar ruwa mai kauri da ke kan window side table, ya fasa kwalbar da jikin bango, ƙasan kwalbar ta zama makami mai kaifi. Ya riƙe Farha da ƙarfi, ya manna ta da bango. Idanunsa sun kaɗa da ja, yana shirin caka mata kwalbar a kirjinta. Maleekh cikin kakkauran murya ya ce “Kafin ki kashe ta ni zan fara kashe ki Farha! Na rantse da Allah, idan kika sake kusantar Amal zan caka miki wannan kwalbar yanzu yanzu!!!” Farha ta zaro idanu, jikinta ya fara rawa, zuciyarta ta nuna tsoro karara. Amal kuwa cikin tsananin firgici da kuka, ta ruga da sauri ta riƙe hannun Maleekh. Cikin kuka da roƙo take faɗin “A’a Maleekh… Dan Allah… kada ka aikata haka! Ka dube ni, ni kake son karewa, ni kake so, amma…! Kada ka zubar da jinin mutum saboda ni… Dan Allah ka janye wannan hannun!” Amal ta sake ihu tana faɗin “Ka tuna Maleekh, idan ka kashe ta, za ka zama mai kisan kai… Ni ba zan iya rayuwa da hakan ba! Ka ajiye kwalbar, Dan Allah…!” Maleekh yana rawar hannu, idanunsa na tsananin huci, zuciyarsa na girgiza tsakanin ƙaunar Amal da kuma mugun fushin da yake ji. Maleekh yana tsaye yana riƙe da kwalbar da aka fasa, idanunsa sun ƙanƙance, jikinsa na rawa. Wani irin huci yake yi kamar zaki da aka tsokane. Amal kuwa tana kuka tana roƙonsa, tana riƙe hannunsa da ƙarfin hali. Amal ganin ya ƙi ajiye kwalbar sai za'kami yake tayi ga yana shaƙe da wuyan Farha, ba ƙaramin shaƙa kuma yayi mata ba domin har ta fara firfito da eyes, Amal ta ce da shi.. “Maleekh… ka duba idanuna… ka ga soyayyata gare ka… kada ka yi hakan. Idan ka kashe ta, kai da kanka ka hallaka ni, saboda ni ba zan iya rayuwa da mai kisan kai ba… Dan Allah, ka ajiye wannan kwalbar…” Wannan kalmomin Amal ne suka shiga zuciyar Maleekh kamar ruwan sama da aka zuba wa wuta. Numfashinsa ya sake nauyi, amma zuciyarsa cike da raɗaɗi da fushi. Ya ɗaga kwalbar da sauri, sannan da ƙarfi ya jefa ta ƙasa! Tsssssshhhhh! Ƙarar fashewar kwalbar ta cika wurin, sassan gilash suka watse a ko’ina. Amal ta runtse idanu tana riƙe da kunnenta saboda tsoro. Maleekh ya janye daga bangon da ya manne Farha, yana huci da ƙarfi. Hannunsa na rawa, idanunsa sun cika da ƙwallah. Maleekh da murya mai sanyi da ƙarfi ya ce “Farha… wallahi kin kusa hallaka ni yau...Amma kin san meye? Idan ba saboda Amal ba… da yau kin daina numfashi. Ki fita a rayuwata, ki fita a raina, ki fita a zuciyata! Na tsane ki!” Amal ta riƙe hannunsa tana kuka, tana ƙoƙarin kwantar masa da hankali. Amal ta ce: “Shhhh… ya isa haka, my bee… don Allah, ka kwantar da zuciyarka. Ka bar komai a hannun Allah…” Maleekh ya dafe kansa yana huci, sannan ya durƙusa a ƙasa, yana maida numfashi da ƙyar. Amal ta durƙusa a gabansa, ta rungume shi tana hawaye... A gefe kuwa, Farha tana tsaye tana jijjiga jikinta cikin tsoro, tana mamakin ganin yanda Maleekh ya kusan hallaka ta saboda Amal.... Cikin takaici ta ɗauki kwalbar da ya dagargaje a ƙasi ta yi masa kyakkyawan riƙo kamar zata yanka wani, sai kawai ta saita tsakiyar tafin hannunta ta yanka da ƙarfi...tayi haka ko zata fi samun sauƙin raɗaɗin da take ji a zuciyarta..... _*NEXT NEXT NEXT*_ asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 37 to 38 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Ma’aikatan company da security ne suka ruga da gudu cikin tashin hankali. Wasu suka tsaya a bakin ƙofa suna leƙowa, wasu kuma suka kutsa ciki. Suka tarar da Amal tana durƙushe tana rungume da Maleekh tana kuka, shi kuma yana riƙe da kanta yana huci kamar zakin da ya ga nama. A gefe kuwa Farha ce take riƙe da hannunta da jini ya ɗan zubo mata sakamakon gilashin da ta yage fatar tafin hannunta da shi.. Gaba ɗaya ofishin ya hau hayaniya, kowa sai tambayar: “Me ke faruwa haka?!” “Lafiya dai CEO?!” Sai kuwa suka jiyo muryar Maleekh, mai ƙarfi cike da fushi, har sai da ofishin ya amsa: “Ku saurara mun haka..." Ya maida kallonsa kan Farha cikin fushi.. Ofishin ya ɗauki shiru daga ɗaruruwan idanu da ke kallonsa. Kowa sai ya juya kai yana kallon Farha... Maleekh ya ce yana nuna ta da yatsa: “Kin kusan kashe Amal yau! Idan ba saboda Allah ya tsare ta ba, da yanzu tana gadon asibiti ko kuma kabari. Amma ki sani, inda ace wani rauni ya same ta uhmmm! Wallahi wallahi wallahi da sai na kashe ki...Sai dai na ƙare rayuwata a gidan prison ko kuma nima a kashe ni. Kuma last warning da zan miki shine daga yau bana son ganin ki a cikin wannan kamfani! Babu inda kika dace a rayuwata, babu inda kika dace dani..! Fita! Fitaaa daga nan kafin na manta da cewa ke mace ce!”.. Wannan kalmomin sun soki zuciyar Farha fiye da kowanne mari. Ta ji kamar ƙasa ta buɗe ta shige. Idanunta suka cika da hawaye, tana rawar jiki ta fara ja da baya. Mutanen company suna kallonta da mamakin rashin zuciyarta... Farha ta dafe ƙirji tana kuka ta fita da gudu daga ofishin, tana rera kuka tare da faɗin “Zan rama! Zan rama wannan wulakanci!” Ta shige cikin motarta a harabar company tana huci, sai kawai ta yi ƙwafa da gudu ta bar wajen. A ciki kuwa, Amal har yanzu tana kuka tana riƙe da Maleekh. Maleekh ya tallafo fuskarta da hannuwansa biyu, yana share mata hawaye, yana furta cikin tausayi: “Beb… shhh… ki kwantar da hankalinki. Na yi miki alƙawari, a duniyan nan bazan bari wani ya cutar dake ba. Ki bar komai a hannuna.” Security da sauran ma’aikata suka tsaya kallonsu cikin nutsuwa, suka ga irin soyayyar da Maleekh yake nunawa Amal, sai su kaɗai suka fahimci asalin darajar Amal a zuciyar CEO. Farha ta isa gida cikin rawar jiki, idonta jawur tsabar kuka, tana ihu kamar wacce ta rasa iyayenta. Ta buge ƙofar falon da ƙarfi, cikin ƙyarma ta na ihu:.. Ammy tana zaune a kujerar falo ita da yaranta Islam da Arfat. Ammy hankali a tashe ta ce "Lafiya kuwa?.." Farha tana kuka ta ce: “Ammy! Yaya Maleekh ne ya mun duka a kan Amal! Yayi mun wulakanci a gaban mutane!” Ta nuna hannunta da ta yanka da kwalba, jini ya ɗan zube kadan a gefen yatsun hannunta. “Kinga! Ya yi min haka saboda ita! Ya yi min haka saboda Amal!”.. Ammy ta yi saurin tashi daga kujerar falon, idonta cike da takaici. Ta kalli Arfat da Islam sannan ta ɗaga muryarta, tana faɗin: “Kada ku tsaya ɓata lokaci! Ku tafi ku je gidan su Amal ku murkushe ta, kuyi mata dukan da sai an kwantar ta a gadon asibiti...!” Ta kalli Farha sannan ta ce "Wa ta ƙila ki rage raɗaɗin da kike ji yanzu haka..." Arfat da Islam suke yiwa Ammy kallon kama-da-wane; sun san halin mahaifiyarsu, sun san ba sauƙi ne da ita, kuma abin magana bata gudunsa... Islam ce ta buɗe baki zata yi magana Ammy ta katse ta da tsawa mai nuni da umarni: “Na ce ku tafi! Wannan umarni ne ba shawara ba!” Farha, tana kuka cikin rawar murya, ta ce: “Ni ma zan tafi! Zan rama! Zan nuna mata cewa ba za a wulakanta ni a haka ba!” Daga nan ta fice daga falon. Arfat da Islam duk suka bi bayan Farha cikin sauri, suna ƙara shirya kansu da mugun nufi. A zuciyarsu dai akwai haɗuwa tsakanin kishin ɗan uwa da kishin gida... ✦ A gidan Amal.. Amal ta bar company cikin halin damuwa sosai. Ta yi kuka sosai a cikin motarta, a zuciyarta tana godewa Maleekh saboda yadda ya tsaya mata; hakan ya ƙara bata tabbacin: akwai wanda yake kula da ita sosai.. Ta isa gidan su, bayan ta shiga parlour, ganin ba kowa a falon yasa ta jingina da bango sannan ta sauƙe nannauyar numfashi.... Inna, itama shigo wa tayi alamun daga unguwa take, ganin Amal yasa ta yi turuss tana kallonta, ta ƙaraso wurin ta da tsananin mamakin ganin halin da jikarta take ciki, Inna riƙo hannun Amal tayi tare da zaunar da ita akan sofas, itama ta zauna kusa da Amal, ta riƙe hannunta cikin tausaya wa ta ce: “Amatu… me ya faru? Ki gaya mini komai.” Amal ta share hawaye, rai-rai ta fara ba da labari, ta faɗa wa Inna yadda abubuwa suka faru, yadda Farha ta zo ofis da irin maganganun ta, yadda rikici ya tashi har Maleekh ya zo ya ceci ta. Inna ta rufe bakinta hannayenta nata zazzaro ido tare da faɗin "Ki ce yau ina zaune sai dai a kawo mun gawarki Amatu, wannan yarinya Fara Allah dai ya kwashe mata wallahi..." Inna ta gama surutan ta sannan ta fara yi wa Maleekh addu’ar fatan alkhairi... ✦ A CashTalk. A company kuma, Maleekh ya tsaya ƙarasa aikin da ya taru masa. Bayan tashin hankali, ya tsaya a ofishinsa yana ƙoƙarin tsara abin da bai kammala ba; kansa yana cike da damuwa. PA da wasu ma’aikata suka tsaya wajen, suna ta dubansa cikin kulawa kowa na gani ya san wani abu ya faru, amma babu wanda ya san cikakken abun da ke faruwa sai PA... PA ya kawo masa wasu takardu, ya ɗan yi magana cikin natsuwa: “Boss, kana lafiya? Na ga ka kusan kammala wa duk da iya na yau ne, Madam Amal duk tayi maka sauran ayyukan, abu ɗaya ne ya rage. Zan kawo maka summary ɗin meeting ɗin yau da safe.” Maleekh ya ɗan miƙe, ya ɗaga kansa ya kalli taga inda gilashin building yayi hasken yamma... Ya ce: “Na gode. Ku ci gaba, ku shirya komai kamar kullum.” Ya juyo, idonsa ya tsunduma cikin duhu na tunani; ya yi alƙawarin in Allah ya yarda, zai ɗauki mataki akan duk wanda ya cutar da masoyiyarsa ya kuma sani, ya zama dole ya natsu yanzu, ya dawo daga wannan tashin hankali don kada ya yi abin da zai yi nadama. Zama ya yi tare da kifar da kansa akan table ɗin office, yana ta tunani da dama... A zuciyarsa akwai ƙauna mai zurfi ga Amal, amma akwai kuma rashin sulhu da mahaifiyarsa da bukatar girmamawa ga Malam. Yana jin nauyin zaɓin, amma a zuwansa yanzu akwai abu ɗaya: kare Amal, dawo da kwanciyar hankalinta, da gyara duk irin barnar da rikici zai iya haifarwa. ✦ Misalin ƙarfe 6 na yamma... Babban falo ya cika da shiru, sai ƙarar plasman da yake haske yana nuna wani shirin fim. Amal da Inna tare da mata masu aikin gidan guda biyu suna zaune suna kallo, kowannensu cikin nutsuwa. Sai kuma kwatsam! Suka ji an turo ƙofar falon da ƙarfi, Farha ta shigo a gaba tana huci, a bayanta Arfat da Islam. Fuskar Farha ta cika da tsananin fushi, idanunta sunyi jawur alamar ta sha kuka sosai.. Amal ta miƙe tsaye da gaggawa, idonta na kallon Farha da tambaya: “Me kuke nema a gidana, zaku wani shigo wa ba sallama kamar wanda aka muku sata?” Farha ta yi tsaki, ta kalli Amal daga sama zuwa ƙasa: “Ai satar kika yi, baki sani bane? kin sace mun abu mafi girma a cikin zuciyata, yanzu shi nazo karɓa..." Amal tayi murmushi sannan ta ce: "Ai abin da ya fito daga cikin zuciya ba ya koma wa gurbinsa, sai dai kawai ki haƙura..." Farha ta harare ta tare da faɗin: "Kina mun abubuwa da yawa, Amal! Ke ce kika jawo min wulakanci a company, kika sa Yaya Maleekh ya wulaƙanta ni a gaban jama’a! To yau sai kin sha ɗan buro uban duka, domin ban zo da niyar koma wa haka nan ba...” Inna ta miƙe cikin mamaki, ta ɗauki gyalenta ta ɗaura a kunkumi, ta kalli Farha da mugun kallo ta ce: “Ke yarinya! Wani dalili ne zai sa ki shigo gidanmu kina wasu surutan banza? Waye ya turo ku?” Arfat ta sa dariya, tana duban Inna cikin raini sannan ta ce: “Kowa ya turo mu, mu ne za mu koya muku hankali yau.” Islam dai tana tsaye gefe, zuciyarta na bugawa. Tana ganin tashin hankali yana ƙaruwa, amma ta kasa shiga tsakaninsu. Nan take cacar baki ta 6arke, Amal da Inna suna mayar da martani cikin rashin mutunci. Sa’annan rikici ya tashi!. Farha ta rufe Amal da duka lokaci guda, Arfat itama ta rufu kanta, haka suka kai mata duka da hannaye.. Amal tana ƙoƙarin kare kanta da ƙarfi, amma sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi. Duk da ƙoƙarin ta, haka suka kayar da ita ƙasa, suka ci gaba da dukan ta ba ƙaƙautawa. Inna kuwa da ta ga haka, ta sa karfi ta shiga tsakani, tana kai musu duka itama duk da tsufarta. Ganin ba sa bi ta kanta ne yasa ta cafke Farha ta garzaya mata uban cizo akan nonuwanta.. 🤣🤣 Lokaci guda Farha ta saki ihu cikin zama ta ture Inna da ƙarfi, har sai da tsohuwar ta kife a kan kujera. Masu aikin gidan ne suka yi saurin ɗaga Inna cikin tashin hankali, suna ƙiran Amal da ta tashi ta karɓi ƴancin ta.. Amal kuwa tana ƙoƙarin miƙewa, tana mayar da martani amma duk da haka suka ci galaba. Farha da Arfat suka yi mata duka har sai da ta kasa tashi... Islam dai tana tsaye gefe, zuciyarta ta riga ta ɓaci da tunanin: “Idan Yaya Maleekh ya ji labari, shin wane hukunci zai ɗauka akanmu?” Bayan sun gama dukan Amal, sai Farha ta ɗauki ƙarfen flower stand ɗin falon, tare da Arfat suka fara bugun plasman. Sai da suka farfasa gilashin nan baki ɗaya, suka bar shi a wargaje a ƙasa. Daga nan suka kama hanyar fita cikin dariyar mugunta. Amal kuwa ta kwanta a ƙasa tana kuka, tana ihu cikin rauni... Inna da zuciyarta ta ƙone saboda zafin ganin yadda aka rufe jikarta da duka, ta nufi kitchen da gudu, ta ɗauko wuƙa mai kaifi, ta fito da gudu tana bin Farha da Arfat tana faɗin: “Sai na yanke muku wuyan ku yau! Ku tsaya in kun isa, dabbobin yara kawai, marasa hankali..” Da ganin haka Farha, Arfat da Islam suka ruɗe da tsoro, da gudu suka fice daga gidan. Motarsu suka shiga cikin sauri, suna dariya mai cike da mugunta da rashin imani. Inna ta tsaya a bakin get tana huci, ga wuƙar a hannu, tana faɗin: “Wallahi sai Allah Ya isa tsakanina da ku!” Falon ta koma cikin ruɗani plasman a wargaje, Amal a ƙasa tana kuka cikin jin raɗaɗin abin da suka mata, masu aiki suna ta duban ta cikin tashin hankali... Inna tana huci, tana zazzaro ido da ƙarfi ta ce wa masu aikin gidan: “Ku ƙira mun Maliku yanzu-nan! Yazo ya ga irin tashin hankalin da ‘yan uwansa suka kawo mana cikin gida.” Ba tare da ɓata lokaci ba suka ɗauki waya suka ƙira Maleekh. A lokacin kuwa Maleekh yana mota, yana kan hanyar komawa gida... Amma da jin ƙiran gaggawa daga gidan Amal, zuciyarsa ta bada saƙo mai nauyi. Nan take ya juyar da motarsa cikin sauri ya nufi gidan Amal. Da isarsa, ya tarar da tashin hankali! Ga Amal a ƙasan carpet tana kuka, jikinta cike da raunukan yakushi da duka, jikinta ya yi jawur abin ka da farar fata ga duk sun yayyaga mata kayan jikinta da ƙarfi.. Ga plasma falon a farfashe, wargajjen gilashi ya bazu a ko’ina... Zuciyar Maleekh ta tsaya cak, ya zaburo yana tambaya cikin tashin hankali: “Meya faru haka? Shin 6arayi ne suka shigo muku?..” Inna, wacce ranta yake har yanzu tana huci, ta zaburo ta dubi Maleekh tana faɗin da tsawa: “Ɓarayin ƙannenka marasa mutunci baaa! Sun zo nan suka yi wa Amatu dukan tsiya, sannan suka farfasa mana tv muna kallo! Wannan marar mutunci, yarinyar nan Fara, ta hankad’e ni da ƙarfi har sai da na kifu a kujera, da ba ƙaramin sa’a na yi ba, da karyewar wuyana kenan! To wallahi, Maliku, ko ka dakatar da su yanzu, ko kuma na ɗauki hukunci da kaina!” Zuciyar Maleekh ta buga sosai. Ya sauƙe dogon numfashi, zuciyarsa ta yi nauyi. Ya rasa kalma da zai furta a daidai lokacin, domin wutar tashin hankali ta yi yawa sosai. Sai ya durƙusa a gaban Amal, yana riƙe da hannunta, yana share mata hawaye cikin sanyin murya ya ce: “Yi haƙuri Amal… ki yi haƙuri dan Allah.” Hannunsa ya yi sanyi kamar ruwan sanyi a zuciyarta, duk da hawayenta basu tsaya ba. Ya juya ya kalli Inna, shi ma a sanyaye ya ce: “Inna, ki yi haƙuri… Ni zan gyara komai, ki bar komai a hannuna. Dan Allah ki kwantar da hankalinki.” Sai da ya rarrashe su sosai, kafin Inna ta samu ta zauna tana huci tana girgiza kai. A daren nan kuwa, Maleekh ya tabbatar da an kawo musu sabon plasma wanda ya fi wanda aka farfasa girma da tsada, domin ya gamsar da Inna da Amal, ya kuma dawo da nutsuwa a gidan. Bayan ya tabbatar sun samu natsuwa, da kansa ya ɗauki motarsa, ya fita daga gidan Amal cikin damuwa. Kai tsaye ya nufi gidansu, zuciyarsa cike da tunani marar daɗi... ☆☆☆▪︎☆☆☆ Arfat, Islam da Farha suna zaune suna dariyar abin da ya faru, suna ta hira akan irin dukan da suka yi wa Amal. Har Arfat tana ɗaga hannu tana nuna yadda Amal ta faɗi, suna dariya kamar masu hauka.. Sai ga ƙarar motar Maleekh ya shigo cikin compound da ƙarfi. Zuciyarsa cike da fushi, fuskar nan ta kumbura kamar an hura wuta a cikinta. Ko sallama bai yi ba, ya shigo falon da gaggawa. Kafin kowa ya yi wani motsi, sai ya rufo kan Arfat ya ɗago ta da ƙarfi ya zabga mata mari har sau biyar a jere! “PAT! PATT! PATTT! PATTTT! PATTTTT!” Arfat ta fasa wani irin ihu tana riƙe da kunci tana karkarwa... Bai tsaya ba, ya juyo ga Islam, ya ɗago ta da mugun fuska. Da sauri Islam ta durƙusa tana kuka: “Dan Allah Yaya kayi haƙuri! Wallahi banda ni… su Aunty Farha ne suka ce muje…” Maleekh ya tsayar da hannun nasa yana huci, idonsa jawur, ta wani ɓangare baya son taɓa Islam domin kaf yafi ji da ita, jininsu yafi haɗuwa... Farha da take zaune a gefe ta ga abin da ke faruwa, da sauri ta miƙe da niyyar guduwa. A fusace Maleekh ya kai mata harbi da ƙafarshi, ya canke ta kamar kwallo. Sai da tayi sama ta doki a ƙasa da ƙarfi... Kafin ta samu daidaita kanta, ya ɗago ta a fusace tare da yin wurgi da ita da ƙarfi har sai da goshinta ya bugi a jikin bango, nan goshin ya fashe sai jinin da yake zubo wa nan take... Arfat kuwa tana durƙushe sai ihu take, Maleekh ne ya ƙara ɗagota ya ɗaga ta sama kafin ya buga ta da ƙasa. Ihun ta ɗaya ya tsaya cak – ta sume! Islam ta sulale ta shiga bayan kujera tana kukan razana, jikinta sai rawa yake kamar zata mutu.. Maleekh ya sake rufa kan Farha, ya ɗago ta ya ƙara buga kanta da jikin bango a karo na biyu. Jinin na ƙara zuba, ta saki ihu tana neman taimako... A nan ne Ammy ta fito daga part ɗinta cikin razana, ta tsayar da kallon ta kan Maleekh! A tsawace ta ce: “Subhanallah! Maleekh!!! Wannan wanne irin hauka ne ka shigo da shi gidan nan?! Zaka kashe su ne saboda sun je sun taɓo ƴar gold? To ni na tura su, eh! Ni na ce su je suyi wa yarinyar can dukan tsiya, shine yanzu zaka zo ka kashe mun ‘ya’yana?!” Ta nuna Arfat dake sume a ƙasa ta ce; “Ka kashe mun yarinya saboda waccan matsiyaciyar ƴar talaka?! Ashe haka ƙiyayyarka ta kai?!” Ta dubi Farha da jini ke kwarara daga goshinta tana kuka. Nan ma Ammy ta ce: “Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Matar da zaka aura kayi mata irin wannan mummunan duka na wulakanci? To wallahi, na rantse da Allah, gobe za a yi taron aurenka da ita! Ba wani shiri tinda kai ɗan banza ne! Kai ba ɗa bane da zan tsaya kallon abin da kake aikatawa!...” Maleekh ya juyo a fusace, yana huci kamar wuta zata fito daga bakinsa ya ce: “Ammy, ki saurare ni da kyau…! Wallahi sai dai a ɗaura auren da gawa ta! Ki je ki shirya jana’iza, amma ba aure da ni da Farha! Na tsani wannan yarinyar fiye da mutuwata..!!!” Ammy ta zaburo, idonta cikin nashi, a tsawace ta ce: “Kai Maleekh, Saboda wata ‘yar matsiyaciya ka juyawa mahaifiyarka baya? Ɗan banzan yaro kawai, sai ka auri Farha, ko da kuwa ta sanadiyyar haka zaka rasa rayuwarka! A gabana sai an ɗaura wannan auren..!” Islam ta miƙe da sauri tana kallon Ammy jin furucin da tayi.. Maleekh jinjina kai ya yi yana murmushin dole ya ce: “A gabanki da duniya gaba ɗaya, ba za a taɓa ɗaura auren nan ba! Wallahi Farha bata da wata nasaba da ni, domin ita ɗin maƙiyata ce! Duk inda Amal take, ita ce ƙauna ta, ita ce zuciyata ni da ita zan zauna har ƙarshen rayuwata..!” Ya juyo yana kallon Farha wacce ke kuka ga jini duk ya ɓata mata fuska, ya ce: “Ke kuma, ki ci gaba da shirinki, Amma wallahi zan nuna miki cewa ni ɗan halak ne, sannan ni ba ragon namijin da zaki raina bane, ki ci gaba da shishshige mun rayuwata wata rana wallahi sai kin rasa numfashinki ta sanadiyya ta...." Har ya juya zai nufi part ɗinsa...Sai ya ji an ƙira wayar gida (telephone).. Maleekh da sauri ya nufi wurin ya ɗaga ƙiran, jin ana ta ambatar. "Hello Hajiya, Hajiya kina ji na?...idan kina ji na aikin Maleekh zai tabbata.." Maleekh kallon Ammy ya yi tare da saka wayar a speaker.. Kowa yana ji, domin yana mamaki ne ta yanda aka nemi Ammy ta wannan wayar gida, ya ɗauka wani sanarwa ne, tin da shine namiji yanzu a gidan, Abbah baya ƙasar....Sannan ya ji an furta sunansa... Ammy zaro ido tayi jin muryar Salamatu... Salamatu ta ci gaba da cewa. "Hajiya ni bana jin ki, idan kina ji na to na ƙira wayarki baki ɗauka ba shiyasa na ƙira wayar gidan nakin, nasan yanzu ke kaɗai ce shiyasa....na je na samu malamin nan akan batun haɗa Maleekh da Farha sannan na bashi sunan Amal ɗin da photonta, insha Allahu ba za ta kai next week a raye ba, domin sai ta sha mungun jinya kafin ta mutu....." Maleekh zaro ido waje ya yi yana kallon Ammy.. Islam buɗe baki tayi tare da toshe wa da hannayenta biyu.. Arfat kuwa tana kwance a sume bata san halin da ake ciki ba.... Ita kuwa Farha dake bakinsu ɗaya da Ammy saita sunkuyar da kanta ƙasi... Ammy kuwa kasa motsi ta yi, haka zuciyarta ke bugawa ta kasa cewa komai... Maleekh da yake riƙe da wayar sai ya ci gaba da sauraron matar tana faɗin... "Malamin ya mun lissafin cewa, kuɗin kawar da Amal zai kai kimanin 1.5...Sannan kuɗin haɗa soyayyar Maleekh da Farha 2.5 ne domin yace zasu rayu ne har karshen rayuwa...domin Maleekh zai rinƙa bin Farha kamar raƙumi da akala, soyayya kuma mai ɗore wa, amma ya ce dole sai kin je ke da kan ki, abu ne mai muhimmanci idan har kina son burinki ya cika, jibi da asuba ki shirya zamu tafi, kafin nan ya gama haɗa mana komai...." Ammy a fusace ta je ta fisge wayar daga hannun Maleekh... A tsawa ce take magana da matar cikin wayar.. "Ke wata iriyar jahila ce, jaka! Dabbiya, ai ko meye kya bari muyi waya ata wayata tin da private secret ne, ko kuma ki zo ki sameni a gida, amma saboda ke jaka ce shine za ki ƙira ni a public phone? ni kaɗai ce a gidan? ina da yara fa, shin kin san waye zai ɗauka a cikin su? ko kuma a misali idan mijina ya ɗauka fa?..." Matar ta ce "Kiyi haƙuri Hajiya ai nasan Alhaji baya Nigeria shiyasa na ƙira a wannan wayar gida..." Ammy ta daka tsawa da cewa: "Yi mun shiru dallah, ko ma menene ai kya bari mu haɗu kafin muyi wannan maganar.." Matar ta ce "Au kina nufin ki ce yanzu ba ke kaɗai kika ji wannan sirrin ba?.." Ammy ta ja dogon tsaki tare da kashe wayar... Ammy a wayen ce ta kalli Maleekh tana huci ta ce: "Maleekh! Na ga alamar shaidan ya rufe maka ido koh? Kan ‘yan uwanka zaka yi musu irin wannan duka kamar dabbobi? Wlh yau ka wuce gona da iri! Kai ɗan banza ne, kai mara mutunci ne!!" Maleekh idonsa Kan ta ya ce: "Ni ɗan banza ne saboda na kare mutuncin matata? Ko saboda na hana su cin zarafin yarinyar da nake so? Ke kika ƙulla komai Ammy! Ke kika sa su zuwa gidansu Amal su yi mata dukan tsiya? Har kika kai ga haɗa baki da boka wajen zubar da jinin marainiya?! Wlh ki sani, a wannan karon baza ki taɓa cin nasara a kaina ba! Boka? Boka Ammy?..." Ammy tana nuna shi da yatsa ta ce: "Maleekh, ka saurareni da kyau, ni ce mahaifiyarka, ni ce na haife ka, ni ce na raine ka! Amma saboda wata ƙaramar yarinya matsiyaciyar ‘yar jarida zaka zubar da mutuncin ‘yan uwanka da ni kaina? Ka duba Arfat nan! Ka buga ta har ta suma! Farha nan jini ke zuba daga goshinta! Sannan ka tsaya a gabana kana faɗa mun maganganu son ranka, wai wannan shi ne mutumin da nake ƙira ɗana?!" Maleekh ya matso kusa da ita, muryarsa na rawa da fushi ya ce: "Idan kina so ki sani Ammy, kina gab da zubar da mutuncin mahaifiya a idona in har kika ci gaba da zuwa wurin waɗancan dabbobin bokaye, wallahi ban taɓa jin haushin ki irin yau ba. Kin yi amfani ta hanyar boka wurin niyyar zubar da jinin mutum, zaki biya boka akan ya cutar da rayuwar yarinya, sannan kike so in auri wacce take son jefa rayuwarki cikin haɗari? Ta sanadiyyar wannan ballagazar ƴar shaye-shaye kike son ki tarwatsa rayuwarki saboda ita, Ammy?...To wallahi sai dai ranar mutuwata na ƙarshe zan bar Amal ta shiga cikin sharrin ku...!" Ammy ta buge ƙirjinsa da hannuwa, tana ihun takaici tare da faɗin; "Wayyo Allah! Kai ne kaɗai ɗan da na haifa zai zama abin kunya a duniya? kai ne kaɗai ka bijire mun, ka zubar da darajata saboda wata zabiyar yarinya? To ka ji da kyau, wallahi tallahi gobe za’a ɗaura aurenka da Farha, ko ka so ko kar ka so. Wannan magana ta ƙare!" Maleekh ya ce: "Wallahi sai dai a ɗaura auren da gawa ta!! Ke da Farha da kowa duka ku ji da kyau, wallahi bazan aure ta ba! Bana son ta, bana son ta, bana buƙatar ta! Idan kin nace, to ki shirya zaman makoki!!" Ammy ta girgiza kai, tana hawaye na fushi ta ce: "Ka faɗi haka ko Maleekh? To ka sani, daga yau kai ba ɗana bane! Kai ba daga cikina ka fito ba! Nayi Allah wadai da haihuwarka, wlh sai na nuna maka babu wanda zai fi ƙarfina! Amal zata zama gawa a hannuna, kuma zaka dawo hannuna ciki kuka!!".. Maleekh girgiza kai ya yi cikin kuka ya ce: “Ki ci gaba da shirinki, Ammy! Ban yi mamaki dan kin ce ni ba ɗanki bane, sannan kin yi Allah wadai da haihuwana, zuciyarki ta riga da ta dusashe, boka ya ɓata miki imanin ki, tausayina ya dusashe a ranki, kin nuna cewa Allah bashi da ikon komai sai boka, kin nuna cewa boka yafi Allah wanda ya halicce ki, a duniya kika tarar da boka, Allah kuma baki ma san yanayinsa ba, baki taɓa ganinsa ba ko a mafarki, ƙarfin ikonsa kawai kike ji da kuma abubuwan da yake aiwatar wa ba tare da ganinsa ba, amma duk da hakan baki ɗauki hakan a matsayin darasi ba....gaskiya ne, saboda Allah ya baki lafiya, wadata, dukiya shiyasa zaki saka masa ta hanyar yin shirka da kuma tsine wa ɗanki wanda ya halitta a cikin cikinki, ni ɗin fa kyauta ne wanda Allah ya baki Ammy..." Haka yake kuka yana magana, gaba ɗaya ya fita hayyacinsa, idanuwansa kamar jini tsabar jan da suka yi.. Ya ci gaba da cewa: "Ammy! Wasu fa haka suke neman haihuwa amma Allah bai basu ba, sun nemi magani har sun gaji, sun roƙi Allah amma saboda ba wannan a cikin kaddararsu basu samu ba, amma ke Allah ya baki ni kuma iya nine namijin da Allah ya baki shine zaki yi watsi dani?... Soyayyata da Amal kaddara ce ta Ubangiji, Allah ne ya ɗora mun sonta... Idan na zaɓi matar aure bisa halal, ba tare da sa6a wa dokokin Musulunci ba, ba laifi nayi ba. Idan uwa ta tsine saboda haka, wannan tsinuwa bata da tushe, kuma zata iya dawo wa gare ta kamar yadda hadisi ya nuna... Manzon Allah ﷺ ya ce: “Ku guji tsinuwar iyaye, domin tsinuwarsu tana komawa ga wanda aka tsinewa kamar yadda kibiyar da aka harba take komawa ga mai harbawa.”.. Wannan yana nuna cewa, idan uwa ta tsine wa ɗa ba bisa hujja ba, Allah na iya karɓa saboda girman matsayin iyaye, amma kuma hakan na iya jawo mata alhakin da ba zata iya ɗauka ba.. Allah baya karɓar addu’a ta zalunci. Kuma wannan tsinuwa ba zata hana ƙaddarar Allah ba, domin aure da wanda ake so hukuncin Allah ne, ba wanda zai canza shi... Ayar Qur’ani, Allah yana cewa: “Babu wata masifar da za ta same ku face da izinin Allah. Kuma wanda ya yi imani da Allah, Allah zai shiryar da zuciyarsa. Kuma Allah ne Masani akan dukkan abubuwa.” (Surat At-Taghabun: 11) A Hadisi Manzon Allah ﷺ ya ce: “Ka yi imani cewa abin da ya same ka, ba zai wuce ka ba, kuma abin da ya wuce ka, ba zai same ka ba. Alkalami ya riga ya bushe da abin da aka rubuta.” (Tirmidhi Sahih) Maleekh yana kai wannan kalaman, ya juya cikin sanyin rai, Ya bar falon, ya wuce part ɗinsa ba tare da ya waiwayi kowa ba. Ammy, kama kanta tayi tare da dokuwa akan kujera tana kuka... ☆ Maleekh ya shige ɗakinsa. Zuciyarsa tana bugawa kamar zata fito. Kalaman Ammy suna maimaituwa a kunnensa.. Voice echo a cikin kwakwalwarsa: "Kai ba ɗana bane… Kai ba daga cikin jikina ka fito ba… Nayi Allah wadai da haihuwarka!".. Maleekh dafe kansa ya yi yana girgiza shi da ƙarfi. Murya na rawa yake faɗin: "Why Ammy…? 😭 Why Ammy!! Why Ammy!!!" (Ciwon kai ya tsananta, a ruɗe ya miƙe tare da ɗaukar ƙarfen flower vase ya fasa babban mirror ɗinsa.. Glass ya tarwatse a ƙasa. Ya ci gaba da farfasa duk wani abu na glass a ɗakin, yana ihu kamar mahaukaci.) Maleekh yana ihu, yana zubar da hawayen da ba zai iya hanawa ba, yana faɗin: "Idan ban kasance ɗanki ba, to ɗan wa nake?? Me yasa kika ce haka a kaina, mahaifiyata?? Wane ne ni yanzu…?!" Ƙarar fashewar glass da ihunsa suka kai ga falon ƙasa. Ammy ta tsaya tana kallon Arfat da Farha, ko ta saurari yanda ihun yake fitowa, ta nuna kamar bata ji ba, sai ɗaukan ruwan sanyi da tayi a frig tana yayyafawa Arfat.. Islam kuwa ba ta iya jurewa ba, da gudu ta haura upstairs... Cikin ɗakin Maleekh ta shige... Islam ta shigo cikin razana, ta tarar da ɗakin a hargitse. Maleekh yana tsaye cikin kuka, hannunsa sai ɗigar da jini yake yanda glass ɗin mirror ya tsatstsaga masa fata... haka yake cakurkud'e sumar kansa yana ihu... Ganin Islam yasa ya fara gurnanin cewa: "Ammy ta kore ni daga zuciyarta, ta ce ni ba ɗanta bane… Islam, to ni ɗan wa ne in ba ɗanta ba?! Ina zan dosa yanzu??" Islam ta ƙaraso cikin kuka, ta rungume shi da ƙarfi.. Itama kukan take tana faɗin: "Dan Allah Yaya ka dakata haka. Ka yi haƙuri. Wallahi kai ɗan Ammy ne, kai ɗan gidanmu ne! Kada ka bari kalamanta su hallaka maka zuciya. Ka yi haƙuri dan Allah!" Maleekh yana sakin nannauyar zuciya cikin kuka ya durƙusa ƙasa, ya jingina da bangon ɗaki, Islam itama zama tayi a tare da shi, ta rungume shi sosai. Dukansu suna kuka... Maleekh a raunane cikin rawar murya ya ce: "Islam… zuciyata ta karye. Na fi jin zafin wannan kalaman fiye da duk abinda aka taɓa mun a rayuwa. Ni ɗan waye yanzu, idan ba ɗan mahaifiyata ba?" Islam ta share masa hawaye ta ce: "Yaya, kai ɗan daraja ne. Kai ɗan halak ne. Kai ɗan da Allah ya ba a wannan gidan ne. Kada ka taɓa mantawa da hakan." Maleekh ya rungumi Islam da ƙarfi, hawayensa na digowa a kafaɗarta, suna kuka tare. Ɗakin ya cika da ƙarar hargitsewar zuciya.... Suna zaune a wannan lokacin har dare yayi sosai, suna zaune rungume da juna, haka Islam take jin yanda jikin Yayanta Maleekh yake kakkarwa kamar wanda yake jin tsananin sanyi... ga jikinsa ya yi mungun ɗaukan zafi, alamun tsananin zazzabi ne ke damunsa.. Ga wani irin fitar da deep breathing da yake kamar last breathing ɗinsa kenam.. A tsorace ce Islam ta kokarta ɗaga shi, ta tallafa masa zuwa kan gadonsa ta kwantar da shi... Da gudu ta fita daga ɗakin ta nufi down stairs, ba kowa a falon domin a lokacin misalin ƙarfe 12 na dare ne.. Kai tsaye medicines room ta nufa domin ɗauko first aid box.. Tana ɗauka ta koma part ɗin Maleekh dake itama Islam ɗin ɓangare likitanci ta karanta.. Tana aiki a wani babban hospital... Tana zuwa tayi saurin masa allurar zazzabi sannan ta ɗaura masa drip a ɗakin, dake suna da komai da komai na emergency... Sannan ta jiko ƙaramin towel da ruwan ɗumi tana matsa masa jiki da kan goshinsa gaba ɗaya... A wannan ranar Islam bata samu yin bacci ba har asuba... Da jin ƙiran sallah Maleekh ya buɗe ido, a hankali ya tashi zaune yana bin Islam da kallo wanda bacci bai daɗe da ɗaukar ta ba, tana zaune akan ƙarami chair a bakin gado, ta kwantar da kanta a bakin gadon.. Murmushi ya yi ganin yanda ta bashi kulawa, ɗaga kansa ya yi yaga drip na ruwa har leda uku duk ya ƙarar, ya samu an cire masa, ga alluran da ta masa ciki har da na Anxiety (damuwa).. Yana ƙoƙarin tashi a zabure Islam ta buɗe ido tare da ɗago wa tana kallonsa, ta ce "Yaya ya jikin dai? Yanzu me kake ji a jikinka?..." Maleekh ya ce "Ba komai Sweet Sis, normal.." Murmushi tayi tare da faɗin "To bari naje na haɗa maka breakfast sai na kawo maka ko?..." Ta fice, shi kuwa ya bita da kallon Murmushi, daga bisani ya miƙe ya shiga toilet domin ɗauro alwala... ☆ _This Morning_ ☆ Gida gaba ɗaya ya yi shiru, kamar gidan da aka gudanar da jana’iza. Ba kowa ya yi bacci da kyau ba. Farha na zaune a kujera tana duba wayanta.. Arfat kuwa har yanzu tana jin ciwon marin da Maleekh ya riƙa mata jiya, tana zaune itama tana game a wayarta... Islam ce ta sauƙo daga part ɗin Maleekh zata wuce kitchen baya yi wa kowa magana ba.. Farha ta tsayar da ita da cewa. "Kin ga Islam, zo ki taya ni zaɓan kayan ɗakin da aka turo mun daga Malaysian, kin san yau ne auren kuma a yau za'a kawo mun kayan.... Islam harararta tayi tare da faɗin. "Wai ke kin ɗauka da gaske za'ayi auren yau ne?..." Ammy wacce shigowar ta kenam falon ta ce: "Ku saurara da kyau. Wallahi ban ga dalilin da zai hana a ɗaura auren Maleekh da Farha yau ba. A shirye nake. Ni uwa ba zan ƙi ganin auren ɗana ba. Idan kuwa shi yaron ya raina ni, to sai dai ya kashe kansa da ƙiyayya. Ba zan canja ra’ayina ba!" Islam tana tsaye ta kasa magana, zuciyarta cike da tausayi. Ta tuna halin da ta ga Maleekh a ɗakinsa jiya. Ta kalli Ammy tana hawaye ta ce: "Ammy… ki ji tausayin Yaya. Kalamanki sun yi masa ciwo sosai jiya. Wallahi ban taɓa ganin shi cikin wannan hali ba. Don Allah ki yi haƙuri da shi, kar ki tilasta masa wannan aure…" Ammy ta kalli Islam da idanunta masu zafi..ta ce: "Ke ma ko? To yanzu kin fara goyon bayan waccan yarinyar kenam? Ki saurara mun sosai Islam, ni ce mahaifiyar ku! Duk abin da zan ce kuyi, dole kuyi shi! Kuma wallahi sai na ga auren nan ya tabbata, ko Maleekh ya so, ko kar ya so wannan ya rage nasa.!" Farha tana yatsina fuska ta ce: "Ya yanzu Ya Maleekh ya soni ne?..." Ammy ta ce da ita: "Ke dai kiyi shiru! ki bar ni da shi. Idan har ya zama mijinki, to dole ya koyi yanda zai zauna dake. Ba son zuciyarsa nake nema ba, abin da nake nema shi ne buri na ya cika. Kuma sai ya cika, wallahi sai ya cika!" Arfat ta turo baki tana shafar kumcinta ta ce: "Ammy, gaskiya Yaya Maleekh ya yi mun tsauri sosai. Zai iya kasheni wallahi, jiya ya kusan hallaka ni da duka…dan Allah a haƙura da auren nan, wallahi tsoro nake ji..." Ammy ta wurga mata ido cikin tsawa ta ce: "Ke wato kin ji tsoro saboda ɗan marin da aka yi miki kenan? Idan ba ki shirya ba, sai ki fita daga harkata kema! Wallahi ba zan bar Farha ta zauna haka babu aure ba. Ko da duniya zata guje ni auren nan sai ya tabbata!".. Tana faɗin haka ta miƙe tsaye ta bar falon.. Zuciyarta cike da tsananin fushi... Bayan ya idar da sallah. Idanunsa sun kumbura saboda kuka. Ya tuna da kalaman Ammy na jiya: “Kai ba ɗana bane… Ba daga cikin jikina ka fito ba!” Sai zuciyarsa ta sake karyewa. Ya dafe kansa da hannaye biyu... Yana magana shi kaɗai, da murya mai sanyi: "Ammy… yau kike son ɗaura auren da Farha? To wallahi… idan wannan aure ya tabbata, sai dai a ɗaura shi ne da gawa ta…Domin nasan zuciyata ne zata buga, ga nauyin kalamanki ga nauyin ƙiyayyar Farha.." Ya nufi window yana kallon rana wacce ta fito da haske, amma a zuciyarsa babu haske. Zuciyarsa ta cika da ƙiyayya, ciwo, da rashin bege... Anata shirye-shiryen ɗaurin aure. An kawata falo da flowers da ƙananan kayan ado. Farha tana zaune cikin wani sabon gown mai tsada, tana cike da ƙyashi da girman kai. Arfat da Islam da wasu ƙawaye suna kusa da ita... Sai ga Amal ta shigo cikin ruɗani, idanunta a kumbure da kuka. Ta shigo falon kamar wacce take neman mafaka, tana ƙiran suna da rawar murya... "Maleeeekh! Maleeeekh!! Ina Yaya Maleekh ɗi naaa??" ƴan mata a falon suka tsaya kallonta. Farha kuwa ta tashi da sauri, ta sha gabanta kafin ta nufi stairs ɗin... A tsawace, tana hararar ta ta ce: "Ke tsaya nan! Yau ranar aurensa da ni, ba zaki taɓa ganinsa ba. Domin mijina mai tsada ne, ba kowace kucaka bace zata iya ganinsa..." Amal ta fashe da kuka, tana ƙoƙarin turata ta wuce tare da faɗin: "Don Allah ki barni, ki barni na ganshi, ki barni kawai na ganshi…" Da ƙyar Amal ke tura hannun Farha, sai kuma suka ji muryar Ammy daga sama, muryar da ta tsinke zuciya da ƙarfi kamar tsawa... "KEEEE!! Dakata nan nace!!" Amal ta tsaya cak! Ta juya a zabure tana kallon Ammy wacce ta sauƙo daga stairs ɗin part ɗinsa, fuskarta cike da ɗaci da fushi...ta ce: "Me ya kawo ki gidan nan?!" Amal tana kuka sosai ta ce: "Ammy… wallahi ni Yaya Maleekh nake nema…" Ammy ta katseta da tsawa cewa: "Kin ji labarin aurensa kenam!? Ko shi ya gaya miki? To Da ke da Maleekh ɗin kunci kutumar buro uban ku! Kina jina kooo?!! Maza kama hanya ki barmun gida kafin in sa gadawa su fita mun dake..!!" Amal ta gudu ta ƙaraso gabanta, ta durƙusa, ta riƙe ƙafar Ammy tana kuka da rawar murya. "Dan Allah Ammy! Dan Allah kar ki rabani da shi! Wallahi inasonsa da zuciyata gaba ɗaya. Ki taimake mu, ki ji tausayinmu Ammy. Idan ma zaki aura masa Farha, to don Allah ki saka sunana a matsayin mata ta biyu. Ki haɗa aurenmu gaba ɗaya, dan Allah! Zan iya jure komai domin kawai na kasance da Maleekh…" Ammy ta zare ƙafarta daga hannunta, ta ɗaga Amal da ƙarfi ta zabga mata mari! Mari har sau biyar a jere, tana huci. Ta ce: "Ke! Ki rabu da yarona. Kin hallaka shi da hauka saboda soyayyarki marar mutunci. Wace irin mayyar yarinya ce ke? Jarababbiya mara zuciya!" Amal tana kuka tana riƙe da kumcinta ta ce: "Ammy, idan auren ne… wallahi na yarda ki yi mun duk wani hukunci. Ki saka ni a cikin masu gasar shad'i idan haka ne. Zan iya jure bulala ɗari biyu kawai don na auri Maleekh…" Ammy ta ja dogon tsaki tare da faɗin: "Ni bani da lokacinki! Kafin minti biyu, ki bar min gida, kafin na ƙira maza su fitar dake da ƙarfin tsiya!" Daga nan Ammy ta juya a fusace.. Amal ta juya zata tafi. Farha ta sha gabanta, tana dariya cikin kyashi ta ce: "Na gaya miki hanyar da zaki samu Maleekh? To ki tafi gidan club. Ki je can zaki same shi, kuyi bankwana na ƙarshe." Farha ta ci gaba da yi mata dariya tana faɗin address ɗin wani club sananne a Abuja, inda aka fi cusa mata ƴan iska da masu shaye-shaye. Amal ba tare da ta yi tunani ba ta ɗauka da gaske ne. Da gudu ta fita daga gidan, ta shiga mota kai tsaye ta nufi wurin da aka faɗa mata... Maleekh kuwa a wannan lokacin yana ɗakinsa, yana kwance cikin damuwa, bai san komai daga abin da ke faruwa a ƙasa ba. Islam tana falo, zuciyarta na tafasa da tausayin Amal da Yayan nata, amma ta kasa yin komai.... Kafin Amal ta isa. Farha ta ƙira wasu kawayenta a waya tana sanar da su cewa: “Ku saurara da kyau! Amal za ta shigo club, ka da ku bata damar shan iska. Ku dabaibayeta, ku tilastata ta shan kwayar maye. Idan ta fara rikicewa, sai ku mata injection, da zaran ta fara maye sai ku kaita toilet na maza, ku kwantar da ita, ku yayyaga mata kayan jikinta. Ku zuba mata jini a ƙasan wandonta, ku tabbatar ya gangaro har ƙafarta. Za a ɗauka cikin da take da shi ta zubar ne. Bayan nan, ku ajiye kwayoyin zubar da ciki kusa da ita don a tabbatar da sharrin. Sai ku gudu ku bar ta can… Zan tabbatar duniya ta tsane ta!”.. Dariyar mugunta suka yi kowacce ta ɗauki nata aikin da za ta yi. Farha kuwa ta ci gaba da zaman jiran saƙon kammala aiki...ɗaurin aure kuwa an ɗan taru a gidan ana jiran isowar Abbah kafin a shafa Fatiha.... Amal ta isa Club Amal ta shigo club ɗin a ruɗe, tana duba ko za ta hangi Maleekh. Idonta ya rufe saboda tashin hankali da ruɗewa. Cikin mintuna, kawayen Farha suka iso kanta. Ɗaya daga cikinsu ta yi kamar tana yi mata sannu da zuwa.. Amal kallonsu tayi tare da faɗin "Ku ɗin su waye ne?.." Suka sanar da ita cewa, su ɗin ƙawayen Maleekh ne.. Suka zaunar da ita tare da bata juice wanda suka sanya kwaya a ciki, sun sanar mata cewa. "Ta jira Maleekh yana nan zuwa.." Amal bata zargi komai ba, ta karɓi drink ɗin. Da ta sha, jikinta ya fara sanyi. Idonta ya fara juyawa, zuciyarta na bugawa da sauri. “Me ke faruwa da ni haka…?” Ta furta da rawar murya. Wata daga cikinsu ne ta watsa masa ruwan lemo ta nuna rashin sani ne, Amal ta zabura ta miƙe tana karkade ruwan jikinta, anan suka tura ta toilet akan ta je ta gyara jikinta, suka mata kwatancen toilet ɗin maza, ai kuwa nan Amal ta je.. Tana zuwa kuwa kanta yayi wani irin sarawa, maganin ya fara mata aiki.. Anan ta faɗi... A cikin male’s toilet suka tarar da ita, suka kulle ƙofa. Wata ta riƙe hannunta, wata ta cire mata hijab ɗinta. Suka buɗe mata jiki da karfi, suka yi mata injection. Amal ta fara rawar jiki, idanunta sun yi nauyi, numfashinta na sauƙa a wahale. Suka yayyaga rigarta da ƙarfin tsiya, sannan ɗaya ta zuba mata jini da suka riga suka tanada a cikin kwalban roba. Jinin ya biyo ƙafafunta ya watse a tiles ɗin toilet. “Hahaha yanzu duniya zata ɗauka ciki ta zubar. Muna da tabbaci wannan yarinyar ta lalace!” Suka ajiye kwayoyin zubar da ciki kusa da ita, suka gama mata video sannan suka fice da gudu suna dariya, suka tura wa Farha video yanda suka yi mata daga farko har ƙarshe.. Misalin ƙarfe 10 na dare aka samu Amal a kwance a cikin male’s toilet. Tana kwance a cikin jini, idonta a rufe, numfashinta ya tsaya.. Mutane suka taru, suka fara ihu. Wani ya ɗauki hoton ta, ya saka a social media... Aka ƙira an jarida.. Ƴan jarida suka isa, suna video da cewa: “Abun mamaki, Amal Abdulsamaad shahararriyar ƴar jaridar nan, ga ta a gidan club a male's toilet kwance cikin jini, abin da bamu sani ba shine 'shin wani ne ya mata fyade ko kuwa?' Amma bisa alamun ciki ta zubar, domin ga kwayoyin zubda ciki a gefenta...." Ƴan sanda suka shiga cikin hayaniya suna ƙoƙarin ƙiran motar asibiti, amma kafin hakan hotunan da bidiyon suka baza a duniya. Maleekh yana kwance yana tunani. Wayarsa ta yi ting. Ya duba WhatsApp ya ga hoton Amal kwance a jini! Message ya biyo baya: “Idan baka yarda ba, kunna TV.” Zuciyarsa ta buga, jini ya hau kai. Ya kunna TV sai ya ga rahoton kai tsaye na club ɗin, Amal kwance a jini, mutane suna ta kallonta, ƴan jarida suna ta yayata zancen “Amal!!” Ya furta sunan a ruɗe.. Ya fice da gudu daga ɗakin sanye da farar jallabiya. Bai tsaya sauraron kowa a falon ba. Farha ta bishi da kallo tana tauna lebenta cikin shauƙin mugunta. A wannan rana kuma, daidai da lokacin bikin Maleekh da Farha, Abbah ya dawo daga Amurka. Cikin fushi ya dawo zuciyarsa na harzuka, yana zuwa daman ya wargaza taron bikin, ya kori kowa a gidansa sannan ya ƙira iyayen su Farha ya sanar da su cewa kada su zo, an fasa bikin... A wannan ranar wuni Abbah ya yi yana balbale Ammy da masifa.. "Akan me zaki yanke bikin ɗana ba tare da sanina ba? Saboda kin mayar ni mahaukaci bansan me nake yi ba?..." A falon akwai wata tsohuwa wato mahaifiyar Abbah da Mahaifiyar Ammy duk suna zaune har da Mahaifin Ammy... Jin wannan al'amari yasa duk suka zo... Wannan bikin an soke shi a wannan ranar. Maleekh bai san meke faruwa ba dake ya kulle ƙofarsa ya hana koma shigo masa.. Sai a yanzu da ya fita a ruɗe... Kuma har wannan lokacin kowa yana falo, sai dai su ɗin ma kallon television suke, kan labarin Amal... Wannan ya ƙara ɓacin rai ga Farha, amma duk da haka tana jin daɗin sharri da ta kitsa wa Amal. Maleekh ya isa club ɗin da gudu, zuciyarsa kamar za ta faso ƙirjinsa. Ya shiga cikin cunkoson mutane. Ƴan sanda na son dakatar da shi amma ya ture su gefe. Ya ga Amal kwance, ga jini a jikinta, ga wayoyi a sama suna ɗaukar hotuna. Idanunsa suka cika da hawaye. Ya faɗi a kanta ya riƙe hannunta: “Amal! Ki tashi, ki dubeni, don Allah kar ki barni haka. Ba zan bari su lalata miki suna ba. Zan gano wanda ya yi wannan sharri, kuma sai na ɗauki mataki akan hakan..!” Ƴan jarida suka yi wuf da kyamarori suna ɗaukar hotonsa da ita... “Amal! Amal! Open your eyes, please! Don’t leave me… Wallahi ba zan bari ki tafi ba!” Haka Maleekh yake ta jijjiga ta amma ko motsi.. Mutane suka tsaya kallonsa, ƴan jarida suka ɗauki hoton shi yana kuka a kan Amal. Ɗaya daga cikinsu ya ce da sauti: “Shin wannan ba shi ne Maleekh, babban ɗanbusiness, wanda a yau aka shirya aurensa da wata ba?” Kowa ya fara raɗa: “To yaya ake ciki kenan? Ai Amal ita ce budurwarsa ta asali...” Zuciyarsa ce ta fara masa wani irin zogi. Yana tuna kalaman Ammy da cewa ba ɗanta ba ne, yanzu kuma Amal tana shan mugun zargi.. Ya riƙo haɓarta da rawar hannu yana faɗin: “Na rantse da Allah, zan binciko gaskiya. Zan wanke ki daga wannan sharri! Duk wanda ya yi miki wannan sharrin zai biya kuɗinsa da rayuwarsa…” A lokacin, ƴan sanda suka nufe shi da nufin ɗaukar Amal. Amma Maleekh ya ɗaga Amal ya nufi ƙofar waje... A wannan daren, duniya ta tsaya ga Amal da Maleekh. Cikin hanzari Maleekh ya ɗauke Amal a hannuwansa, yana daka tsawa ga ƴan jarida: “Kafin safe duk posting ɗin da kuka yi game da Amal ku share shi! Duk hotunan da kuka saka ku cire su yanzu! Idan kuwa wani ɗan jarida ya sake taɓa wannan magana, sai na tabbatar an kamashi, kuma bai sake ganin hasken waje ba sai ya mutu a prison!” Ƴan jarida suka tsaya a tsorace, wasu suka fara sharewa nan take. Ƴan sanda suka matsa kusa, amma Maleekh ya ɗaga musu hannu da cewa: “Ku kuma! Ba ruwanku da wannan case. Ku ja baya ku barta a hannuna!” Ya fito da Amal cikin karfi, yana riƙe da ita kamar zai cinye duk wanda ya kusance ta... Haka ya nufi hospital da ita... A asibiti Amal an kwantar da ita a kan gado, da drip a hannunta. Maleekh ya zauna kusa da ita har dare, bai runtsa ba. Idonsa cike da hawaye, zuciyarsa cike da tsoro da damuwa. Anan duk suka kwana.... _Washegari_ Da safe, Inna ta shigo tana kuka, tana riƙe da mayafi tana jijjiga kai. Cikin rawar murya take cewa: “Na ji labarin… Amal tana asibiti? Amma me ya faru da ita ne? Me aka yi mata haka?” Maleekh bai ce komai ba, ya riƙe hannun Amal yana kallon fuskar ta da hawaye. Doctor’s Office Doctor yana zaune a office ya gama rubuta result akan Amal.. Knocking aka yi masa, ya bada izinin shigo wa... Farha ce ta shigo. Ta zauna tana facing Doctor, ta zaro wata babbar jaka mai cike da kuɗi. Tayi murmushi mai cike da mugunta sannan ta ce “Kasan nan ɗin nawa ne?” Doctor ya kalli jakar yana firfito da ido waje, a ruɗe ya ce: “A’a… gaskiya ban sani ba.” Farha ta ce “Kimani ne 2 billion dollars ne. Kuma duk naka ne idan ka yi min abu ɗaya kawai.” Doctor ya miƙe a zabure, zuciyarsa ta rikice. Cikin rawar murya ya ce: “Subhanallah! Hajiya, me kike so ayi?” Farha tayi dariyar mugunta sannan ta ce: “Yarinyar da aka kawo jiya da daddare Amal. Nasani result ya nuna ba ciki a jikinta, kuma bata sha maganin zubar da ciki ba, kawai maye ne ya yi mata. Dama haka ne ko?” Doctor da sauri, yana jinjina kai ya ce “Hakane, wallahi kuwa.” Farha ta ce “Toh, ina so ka canza result ɗin. Ka rubuta cewa Amal ta zubar da cikin wata huɗu. Ka tabbatar labarin ya zama ainihi, babu wanda zai iya ƙaryatawa.” Doctor ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya dubi jakar kuɗin da idanuwansa suka ciko da jarumta na ɗanɗano kuɗi ya ce “Indai wannan ne aikin, ki tafi lafiya. Zan shirya result ɗin yanzu.” Farha ta miƙe da murmushin mugunta, ta bar masa kuɗin sannan ta fice daga office ba tare da kowa ya lura ba... A ɗakin Amal, Maleekh da Inna suna zaune kusa da ita. Amal har yanzu bata farfaɗo ba. Doctor ya shigo da takardu a hannunsa. Maleekh ya miƙe da sauri, zuciyarsa na bugawa. Maleekh a tsanake, cikin tashin hankali ya ce: “Doctor… meke damun Amal? Ka faɗa min gaskiya.” Doctor ya ɗan gyara tsayuwarsa, sannan ya ce da nutsuwa: “Result ɗin ya nuna cewa Amal ta zubar da ciki… cikin wata huɗu ne ya fita.” Wani irin shock ya shaƙe jikin Maleekh. Ya riƙe takardar, idanuwansa suka ciko da hawaye. Ya kalli Amal da hawaye suna zuba a fuskarsa. A hankali ya furta “Ciki… Amal?? Har na wata huɗu? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un…” Inna ta zabura ta miƙe a tsorace. Ta ce “Meeeee?? Amal ta yi ciki??” Girgiza kai Maleekh ya yi tare da faɗin: “Amal ta cuce ni. Amal ta gama da rayuwata. Ta rusa soyayyata. Ta bani kunya. Fuska biyu gare ta? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” Inna ta fashe da kuka, tana jijjiga kai. Cikin baƙin ciki ta ce: “Ko da ta zubar da cikin, ta riga ta zubar da tarbiyyarta! Ta zubar da mutuncinta! Iyayenta suna kwance a kabari, ita kuma ta janyo musu abun kunya. Jikata ce ita, amma ta janyo mun abun kunya!” Maleekh ya miƙa wa Inna result ɗin da hannunsa na rawa, ya fita daga ɗakin cikin baƙin ciki. Doctor ma ya fice, zuciyarsa cike da natsuwa cewa ya gama da aikinsa da aka saka shi. Amal kuwa, tana kwance cikin rashin sani, bata san halin da ake ciki ba...... *_NEXT! NEXT!! NEXT!!!_* asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 domin samun akai-akai har zuwa complete. https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 39 to 40 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Farfaɗowar Amal. Ta buɗe idanunta a hankali, tana jin nauyin kanta. Sai ta yi mamakin ganin kanta a asibiti. Idonta ya sauka kan Inna wacce ke zaune gefe tana juya mata baya, idonta cike da hawaye, murya na rawa ta ce: "Inna… me ya kawo ni asibiti? Me ya same ni haka? Ni dai ban gane komai ba. Na manta… na manta yanda na shigo nan…" Inna ta juyo da huci ta ce: "Ke baki da kunya wallahi Amatu! Ashe haka kika lalace? Ashe ashe cikin shege kike ɗauke dashi, har ya zube a gidan rawa na ‘yan iska?!" Amal ta zabura, ta riƙe kanta sakamakon ciwon da yake tana girgiza kai a ruɗe ta ce: "Ciki kuma Inna? A jikina? Inna shin ana iya ɗaukar ciki haka kawai? Kodai a ruwa ake sha? Wallahi ban taɓa sanin haka ba…!" Inna ta daka tsawa, ta miƙe a fusace tare da faɗin "Kar ki raina mun hankali Amatu! Ba abinda zaki ce mun yanzu! Me ya kaiki club ɗin ‘yan iska? Me kike nema a can? Sai dai ki karɓi sakamakon sharrin ki!" Amal ta fashe da kuka, tana jin kamar duniya ta juya mata.. _Gidansu Maleekh_ A falo kuwa, Abbah yana zaune da Ammy da iyayenta (Grands). Fuskokinsu cike da baƙin ciki. Grandmother (na bangaren Ammy) ta daka tsawa tana faɗi "Ke Maryam! (Ammy) Ashe har yanzu baki canza ba? Tun kina yarinya kike ɗaga kai, baki taɓa bin umarninmu ba. Shi yasa yau ɗanki ya koma haka! Duk sakamakon halinki ne!" Grandfather shima ya ce: "Mun ja miki kunne a baya! Mun gaya miki rashin biyayya ga iyaye bala’i ne. Yanzu kin ga sakamakon! Ki kalli yaronki, ya koma halin da ba’a taɓa tsammani ba." Islam cikin kuka ta ce: "Ammy ta tsine wa Ya Maleekh jiya. Ta ce shi ba ɗanta bane! Ta ce ba daga jikinta ya fito ba!" Abbah ya girgiza kai da tsananin takaici ya ce: "Maryam, wannan wane irin rashin hankali ne? Wane irin baki ne ya fita daga bakinki? Kin shirya Auren ɗana ba tare da sanar da ni ba, hakan ma kin tsine masa?!" Ammy ta fashe da kuka tana kare kanta da cewa: "To ku gani fa a TV jiya! Yarinyar da yake so, ta zubar da ciki a gidan rawa! Ni zan aura masa irin wannan ‘yar iskar?!" Abbah a fusace ya daka tsawa yana faɗin "Duk abinda ɗana yake so shi za’ayi! Ba za ki kashe min yaro da damuwa ba!" Cikin wannan hayaniya ne sai ga Maleekh ya shigo daga waje, yana jan ƙafa da ƙyar, kamar ba jini a jikinsa. Fuskarshi ba annuri, idonsa sun ƙanƙance kamar wanda yake shirin mutuwa. Bai kalli kowa ba, ya nufi sama. Abbah da sauri ya miƙe tare da zuwa ya riƙe shi, yana faɗin: "Yaron kirki, an soke maganar auren da baka so. Ka kwantar da hankalinka. Yanzu ka gaya min, mu je mu nema maka auren Amal ne?" Maleekh ya tsaya yana kallonsa da idanu masu cike da hawaye, daga bisani ya furta cikin sanyin murya: "Bana ƙaunar kowace mace yanzu! Na tsani mata gaba ɗaya! Gaba gaba gaba gaba ɗayaaaa…!" A lokacin ya yi luuu, zai faɗi ƙasa. Abbah ya yi saurin tare shi a rikice, cikin ɗaga murya ya ƙira sunansa: "Maleekh!!" Ammy ta nufo da gudu tana kuka tana faɗin: "Maleekh ɗana, don Allah ka tashi! Wallahi ina sonka, wallahi kai ɗana ne, taya mahaifiya zata ƙi ɗanta?!" Islam da Arfat suka ruga suna kuka, suna riƙe da hannun Maleekh. Tsofin suka miƙe tsaye a firgice suna cewa: "Akai shi asibiti yanzu! Kada lokaci ya kure!" Abbah ya ɗaga ɗansa ya rungume shi da ƙarfi, su Islam suka riƙe ɗayan ɓangaren suka nufi waje, suka fice cikin hanzari. Farha da gudu ta bi bayansu... Security suna ganin haka suka yi saurin karɓar Maleekh tare da shigar da shi motar, kai tsaye sai hospital... _Asibiti – Emergency Room_ An shigar da Maleekh cikin emergency room. Nurses da likitoci suka zagaye shi da hanzari. Doctor cikin tsawa yake faɗin: "Quick! Prepare oxygen mask! Bring the defibrillator, now!" Nurse ta ɗaura masa oxygen, wani ya saka drip a hannunsa. Domin numfashinsa ne ya tsaya cak... Doctor yana ɗaga murya a gaggauce ya ce: "We’re losing him! Start CPR, now!" Wani likita ya fara bugun ƙirjinsa da hannu (chest compression), wani kuma ya saka oxygen da karfi.. Babban Doctor ya ce: "Charge defibrillator to 200! Everyone clear!" Suka ɗaga hannuwa daga jikinsa, aka kwantar da shi. Aka buga shock na farko, jikinsa ya motsa ya tashi, amma monitor ɗin ya nuna flatline. Doctor ya kuma cewa: "Again! 300! Everyone clear!" Aka sake bugawa, monitor ɗin ya yi tsalle ɗaya ya dawo flat... Nurses suna kallon juna da hawaye a idonsu. Islam tana waje tana ihu tare da faɗin: "Yaya Maleekh, don Allah kada ka mutu! Ka dawo mana…!" Doctor ne ya sake ɗaga murya ya ce: "Increase to 360! This is our last chance! Clear!" Aka buga na uku sai beep beep beep ya dawo kan monitor. Numfashinsa ya fara dawowa a hankali. Doctor ya sauƙe numfashi mai nauyi: "Alhamdulillah! We got him back. Keep monitoring his vitals!" Nurses suka fara farin ciki, suka fara jona masa magunguna da drip.. Waje kuwa, Abbah ya jingina da bango yana hawaye. Ammy tana kuka tana faɗin: "Allah na tuba, kar ka ɗauke mun ɗana! Kar ka ɗauke mun Maleekh…" Islam ta durƙusa tana addu’a da roƙon addu’a, tana kuka kamar za ta mutu.. (Ikon Allah, masu kuɗi kenam, da zarar Allah ya jarabce su da jinya sai su ɗauka mutum mutuwa zai yi🤔 amma mu ƴaƴan talakawa da zaran babu lafiya muna langwa6ewa sai ace lalaci ne, a baka kaje chemist ka haɗo magani 🫩🫩🫩)... Doctor bayan ya fito daga Emergency room, ya tadda Abbah da Ammy da Grandma da sauran iyali a tsaye cikin tashin hankali. Doctor ya kalli Abbah a hankali sannan ya ce da murya mai sanyi: "Alhaji... ba zan ɓoye muku ba. Yaronku yana cikin matsananciyar halin gaggawa. Heartbeat ɗinsa na tafiya da sauƙi sosai, a wasu lokutan har yana tsaya wa cak. Mun sha wahala wajen dawo da numfashinsa… yanzu haka injin na taimaka masa. Idan har ya tsira daga wannan, zai buƙaci kulawa sosai da kuma kwantar da hankali domin zuciyarsa tana da rauni mai tsanani." Ammy ta fashe da kuka, Grandma ta dafe kirji tana ambaton "Innalillahi wa inna ilaihirraji’un." Doctor ya ɗauki numfashi kafin ya ƙara cewa: "Alhaji, ya kamata ku sani, damuwar da yaron nan yake ciki tafi ƙarfin jikinsa. Duk wani raɗaɗi da kuke ji a jiki, shi zuciyar sa take ɗauka kai tsaye. Idan ba'a yi hankali ba, Allah kadai yasan yadda zai kasance." ☆☆☆☆☆ An kwana biyu babu motsi daga Maleekh. Yana kwance a gadon asibiti, komai na'ura ce ke yi masa. Abbah kullum yana zaune kusa da shi, Islam ta kasa barin asibitin tin da aka kawo shi, kullum tana kuka tana riƙe da hannunsa tana faɗin: "Yaya, dan Allah ka tashi ka duba ni. Ka tuna kace baza ka taɓa barina ni kaɗai ba… don Allah ka tashi." Ammy kuwa ta rikice gaba ɗaya, kullum sai dai ta yi kuka tana tunanin kalaman da ta faɗa masa, ta tsinewa ɗan da ta haifa da kanta. A gefe guda kuma Amal… An sallame ta daga asibiti, sun dawo gida. Amma Inna ta ƙi kulata gaba ɗaya. Ko zama kusa da ita Inna bata yi, balle ta duba yanayin jikinta.. Ko wani lokaci Amal na tambayarta tana hawaye: "Inna… don Allah ki gaya min, me ya faru da ni? Me yasa na tashi a asibiti? Taya aka ce ina da ciki…?" Inna ta daka mata tsawa cikin tsananin fushi: "Kar ki raina min hankali Amatu! Ke baki san me kika aikata ba? Kina can gidan rawa na ƴan iska kina tozarta kanki! Doctor ne ya ce kin zubar da ciki sakamakon iskanci! Har kike cewa baki sani ba?" Amal ta zaro ido tana mamaki sosai, ta fara shafa cikinta tana girgiza kai da kuka ta ce: "Inna wai haka kawai mace zata iya samun ciki ne? Ko a ruwa ake sha ne? Inna don Allah ki yarda dani, ban san komai ba, ban taɓa yin wannan abun ba!" Inna ta yi tsaki, ta juya mata baya cike da ƙiyayya ta ce: "Ni dai ban san komai ba, Amatu. Duk abinda kika aikata, ki ɗauki alhakin kanki. Ni ba ruwana! Na gaji da wahalar ki, na gaji da tozarci da kunyar ki. Idan kika ga dama ki je ki nemi uban cikin nan ki kawo mun shi a gabana. Ni ba zan raba miki shimfiɗa da shi ba!" Amal ta fashe da kuka tana dafe da cikinta da mamaki da tsoro, gaba ɗaya ta shiga cikin tashin hankali mai tsanani.... *_Day 1_* Duk daren nan Abbah bai runtsa ba. Ya zauna a gefen gadon ɗan nasa, ya riƙe hannunsa da karfi yana ta ambaton: "Allah ka dawo min da ɗana…kada ka raba ni da shi. Ya Allah ka dawo da shi cikin rayuwa." Islam kuwa ta kwanta a ƙasa kusa da gadon, ta ƙi tafiya ko da minti ɗaya. Idonta ya kumbura saboda kuka. Duk lokacin da injin ɗin da ke jona numfashin Maleekh ya yi sautin gargaɗi, sai ta firgita ta nufi ƙofar ta ƙira nurse. Ammy ta kasa shigowa ɗakin. Duk lokacin da ta kawo ƙafafunta wajen ƙofar, sai ta tuna kalamanta: “Kai ba ɗana bane.” Sai ta ja da baya ta fashe da kuka. Grandma ta riƙe ta sosai tana faɗin: "Kije ki riƙe hannun ɗanki, shin ba addu’ar nakin bane zai dawo da shi ba?" Ammy ta fashe da kuka tana girgiza kai ta ce: "Na tsine masa da bakina, ke kina so in ƙarasa kashe shi kenan?…" *_Day 2_* Doctor ya ƙira Abbah da Ammy ofis ɗinsa. Ya ce da su: "Alhaji, gaskiya mu dai likitoci mun yi iya bakin ƙoƙarin mu. Wannan na'ura ce kawai ke riƙe da shi yanzu. Amma ku sani, yaron nan yana cikin koma mai tsanani. Sai dai Allah ya ɗora masa rayuwa." Ya ɗan yi shiru, ya kalli Abbah cikin tausayawa: "Kar ku daina addu’a, saboda zuciyarsa tana fama da nauyin damuwa da tashin hankali. Idan ba’a cire masa wannan nauyi daga zuciya ba, duk magunguna ba zasu wadatar ba." Abbah ya dafe kansa yana hawayen maza... Ammy ta durƙusa a gaban Doctor tana kuka sosai tana faɗin: "Doctor, akwai wata hanya da za ku iya yi? Ko zaku cire mun zuciya ku saka masa, wallahi ku yi!" Doctor ya girgiza kai ya ce cikin tausayawa: "Allah ne kaɗai zai iya yin hakan, Hajiya." Islam dake zaune da Maleekh a ɗakin..sai kuka take tayi tana faɗin: "Yaya, wallahi ba zaka mutu ba. Ka tashi ka duba ni don Allah…" Waje daban kuma… Amal a gida. Amal ta kasa cin abinci, ta kasa runtsawa. Inna ta ƙi kulata, ko da tambayarta abu zata yi sai dai ta yi mata tsawa. Amal tana zaune ita kaɗai cikin ɗaki tana shafa cikinta da hawaye tana cewa: "Allah ka sani ban san komai ba… Na tashi a asibiti ne kawai. Shin ni ƴar iska ce? Da wannan rayuwar gwara mutuwa ta, Allah ka bani gaskiya…" ☆Daren kwana na uku☆ Injin numfashin yana ta bugawa a hankali. Abbah yana zaune a gefensa kamar yadda ya saba, ya riƙe hannunsa yana karanta Qur’ani. Islam ta kwantar da kanta a gefen gado tana bacci da kuka a idonta. Ammy kuwa ta jingina da bango tana hawaye cikin shiru... Iya su uku ne a zaune da Maleekh.. Sai a hankali yatsun hannun Maleekh suka motsa... Abbah ya ji motsin ya kalli hannun cikin sauri, zuciyarsa tana bugawa. Ya matsa kusa ya ƙira cikin rawar murya: "Maleekh… ɗana, kana jin Abbah?" Kamar wanda aka ɗago daga zurfin rami, Maleekh ya ɗan motsa bakinsa a wahalce... Bai iya magana sosai ba, sai dai wani irin numfashi mai nauyi ya fito daga bakinsa. Islam ta farka da sauri ta ce: "Yaya! Yaya ya motsa! Abbah, Yaya ya motsa wallahi!" Ammy itama taso wa tayi daga jikin bango cikin rawar jiki ta durƙusa a kusa da shi, tana riƙe da hannunsa cikin hawaye ta ce: "Maleekh ɗana… don Allah ka tashi ka kalle ni, na rantse ban tsaneka ba, na yi kuskure. Nasan ni ce na jefa ka a wannan hali, ni ce na cutar da kai… Amma ina ƙaunarka fiye da komai." Likitan da nurse suka shigo da gudu, suka fara duba injin. Likitan ya ce cikin farin ciki: "Alhamdulillah, yana nuna alamun farkawa. Ku ci gaba da ƙiran sunansa, wannan yana taimaka masa sosai." Maleekh ya yi wani irin gunji kamar yana ƙoƙarin magana. Abbah ya sunkuya sosai ya ce: "Ka yi ƙoƙari ɗana. Ka dawo mana, muna jiranka. Babu aure da za a tilasta maka, babu wanda zai cutar da kai, ka kwantar da hankalinka." Sai a hankali idanuwan Maleekh suka fara ƙoƙarin buɗewa, dishi-dishi kamar mai ganin haske bayan dogon duhu. Islam ta yi ihu da murna tana cewa: "Ya buɗe ido! Wallahi ya buɗe ido!" Ammy ta fashe da kuka tana rungume da hannunsa ta ce: "Na gode Allah, na gode! Maleekh ɗana, sakacina ne ya jawo haka, amma wallahi ina sonka. Ka gafarta mini…" Likitan ya yi murmushi ya ce: "Alhamdulillah, hakan yana nuna zuciyarsa tana dawowa a hankali. Amma kada ku dame shi da surutu mai yawa yanzu. Yana bukatar nutsuwa." bayan ya buɗe ido a karo na farko Ɗakin ya ɗau shiru, sai ƙarar injin numfashi da ɗan motsin nurse dake gyara drip. Abbah da Ammy sun zuba ido suna jiran wani kalami daga gare shi. Islam kuwa tana riƙe hannunsa tana kuka da murmushi lokaci guda. Maleekh ya buɗe bakinsa a wahalce, muryarsa na fita ƙasa-ƙasa kamar fitar rai ya ce: "Ab…bah…" Abbah ya matsa kusa cikin sauri ya ce: "Na’am ɗana, ina nan, ina jinka. Kar ka damu, Abbah naka yana nan a tare da kai." Sai ya ɗau dogon numfashi a wahalce, ya sake cewa: "Am…my…" Ammy ta sunkuya tana hawaye, zuciyarta kamar zata tarwatse ta ce: "Eh Maleekh, Ammy ce, ɗana. Na’am… ka faɗi abinda kake ji." Idanuwansa suka cicciko da hawaye, ya ɗago da ƙyar yana kallon fuskarta ya ce: "Me… yasa… kika ce… ni..ba ɗanki… bane…?" Ammy ta fashe da kuka tana girgiza kai: "Na yi kuskure, wallahi ba da nufin zuciyata ba. Na ce haka a cikin fushi ne, amma kai jinin jikina ne, Maleekh ɗana. Don Allah ka yafe min…" Maleekh ya runtse idanu yana sauƙe numfashi da ƙyar. Sai ya buɗe su a hankali, muryarsa ta sake yin rauni ya ce: "Na gaji… da rayuwa… Na gaji… da soyayya… Ba na son kowa… sai ku…" Islam ta rushe da kuka ta rungume hannunsa tare da faɗin: "Dan Allah kar ka sake faɗin haka Yaya. Kana da mu, kai rayuwarmu ne…" Abbah ya share hawayensa ya ce: "Ka kwantar da hankalinka, ɗana. Zamu tsaya a tare da kai har sai ka farfaɗo gaba ɗaya. Babu wanda zai sake cutar da kai." Maleekh ya lumshe idanu, hawaye na sauƙa daga gefen kumatunsa, sannan ya furta cikin rauni: "Ina… so… na huta…" Sai ya sake lumshe idanu yana shaƙar numfashi a hankali, ya koma shiru. Doctor ya matsa kusa da Abbah da Ammy. Ya da fa kafaɗar Abbah cikin girmamawa, sannan ya dubi Ammy da ido mai cike da gargaɗi. Sannan ya ce: "Don Allah ku kula da kalamanku a gabansa. Zuciyarsa tana da rauni sosai yanzu, duk wata magana da zata tada masa hankali na iya sake rikita bugun zuciyarsa. Wannan halin da yake ciki ya samo asali ne daga tashin hankali da damuwa mai tsanani. Idan kuna so ya warke, to ku tabbatar komai da yake ji daga gareku yana da sauƙi, babu zafi, babu fushi." Abbah ya jinjina kai cikin nauyi ya ce: "Insha Allah, zamu kiyaye. Wannan yaron mu ne gaba ɗaya." Ammy ta share hawayenta da sauri ta ce: "Doctor, wallahi zan riƙe alƙawari. Ba zan ƙara masa ciwo ba, sai dai farin ciki." Doctor ya dube ta yana faɗin: "Ki tabbata kin aikata hakan. Wannan ba wai maganin asibiti kaɗai bane, soyayya da kwantar da hankali suna cikin maganin sa." Scene ɗin Amal... Tun daga daren da ta dawo daga asibiti, kullum ƙoƙari take ta ƙira Maleekh amma wayarsa a switch off. Hankalinta ya fara tashi. A daren nan ta ɗauki wayarta ta ƙira PA ɗin Maleekh, wanda shine manager ɗinsa a campany. Amal cikin damuwa ta kara wayar a kunne bayan ya ɗaga ta ce: "Hello… don Allah, ina Yaya Maleekh ne? Na kirashi tun kwanaki amma wayarsa a kashe. Ko yana lafiya ne?" Manager ɗin ya yi shiru na wasu sakanni kafin ya amsa da wata murya mai nauyi: "Eh… Madam Amal, gaskiya akwai wani hali da yake ciki. Yana asibiti yanzu, tun kwanaki biyu kenan yana kwance." Amal a firgice ta ce: "Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Hospital kuma? Amma me ya same shi?!" Manager ya ce: "Ni ma ban san cikakkun bayanai ba. Amma dai likitoci suna ƙoƙarin ganin ya warke. Ki kwantar da hankalinki…" A ruɗe ta kashe wayar tare da rufe baki da tafin hannunta, hawaye suna zubo mata ta ce: "Ya Allah… Maleekh a asibiti kuma ni ban sani ba…!" Sai zuciyarta ta ƙara tsinkewa lokacin da ta ga results ɗin asibiti nata da aka kawo mata a envelop. Ta buɗe da hannu mai rawa… idonta ya sauƙa akan rubutu: “Evidence of miscarriage, 4 months pregnancy.” Amal ta zaro ido tana kallon saƙon, jikinta ya ɗau rawa. Sai ta riƙe cikinta a gigice tana magana da kanta: "Ciki kuma? Wai a jikina? Na rasa gane komai amma ina aka ɗauko wannan sakamakon? Shin Maleekh ya sani?.." Sai ta rushe da kuka tana riƙe da ƙirjinta. Bayan ta gama shan kukan ta. A ruɗe ta ɗauki gyale ta yafa, ta sauƙa down stairs a falo ta tarar da Inna.. Wani irin kallo Inna ta yi mata.. Amal a ruɗe take faɗin "Inna Maleekh yana hospital ba lafiya inaso zanje na dubo shi.." Inna ta kawar da kai ko kallonta bata yi ba. Amal har zata tafi ta juyo tana kallo Inna, tace "Inna anyi auren Maleekh kuwa?.." Nan ma Inna bata kula ta ba. Ganin inna bazata kulata ba yasa ta girgiza kai zata tafi... Inna ta daka mata tsawa da cewa "Bayan ke kikayi silar kwanciyarsa jinya shine yanzu zakije ki ƙarasa kashe shi koh?.." A firgice Amal ta juya tana kallo Inna. Muryarta na rawa tace "inna ni kuma?.." Inna ta ce "Mutumin da yake burin aurenki, yazo yaji cewa kin zubar da cikin wata huɗu ya kenam? Kowa ya sani, an tallata ki a tv da ko ina, ke ko kunyar fita bazaki ji ba?..." Amal ta ja dogon numfashi sannan ta ce "Koma menene tinda ina da gaskiya, zanje, zan tabbatar shin Maleekh baya sona yanzu ko kuma har yanzu yana sona.." Inna taja tsaki tare da kawar da kai.. Amal ta fice, kai tsaye motarta ta shiga tare da fita daga gidan... Amal ta hau mota jikinta yana kyarma, zuciyarta kamar zata fito daga ƙirji. Hannunta a kan sitiyari sai rawar sanyi yake, idanuwanta sun cika da hawaye amma ta share su da bayan hannunta tana faɗin: "Ya Allah, idan da gaske Maleekh yana sona, ka haɗa ni da shi cikin alheri… kar ma'kiya su rabamu da ƙiyayya. Kar cutar zuciyata ta zama gaskiya..." Yayin da ta ƙarasa bakin asibitin, motarta ta tsaya cak a bakin gate. Security ya matsa kusa yana tambaya, kafin ta ce komai sai ta nuna musu sunanta da sunan Maleekh. Nan take aka buɗe mata hanya. Cikin tsoro da ruɗu ta shige cikin babban building ɗin, ƙafafunta kamar ba ya jikinta. Tana shiga cikin reception ta ce da rawar murya: "Excuse me… ina wajen da aka kwantar da patient ɗin nan, Mr. Maleekh?" Nurse ɗin ta dube ta da mamaki tace: "Kin shigo da ɗan ɗaukar rai ne… ke ce Amal?" Amal ta kasa amsa sai da ta ɗaga kai kawai, zuciyarta ta cika da tsoro. Nurse ɗin ta nuna mata hanyar ward. A hankali Amal ta nufi hanyar, ƙafafuwanta suna jijjiga, hawaye suna tsiyaya a fuskarta. A zuciyarta kalmomi ɗaya ke maimaituwa: "Ya Allah kar ya ƙi ni… kar ya ƙi ni…" Da ta isa bakin ƙofar ɗakin, sai zuciyarta ta tsinke kamar zata tsaya. Hannunta ya tsaya cak a kan handle ɗin ƙofar. Ta ɗauki numfashi tana kuka a ranta: "Ko zai ƙi ni, zan sani yau… zan ji da bakinsa. Tinda Inna ta ce ni ne silar ciwonsa, bari ya gaya min da kansa…" A hankali ta murɗa ƙofar ta shiga... Sai idonta ya sauƙa a kan Maleekh, kwance a gadon asibiti, gaba ɗaya ya rame, yana sanye da oxygen pipe a hancinsa. Amal ta dafe ƙirji tana sauƙe kuka mai ƙarfi. Cikin zuciya ta ce: "Wayyo Allah na, ciwon har ya kai haka? Innalillahiwa’innailaihirraji’un, Ya Maleekh dan Allah kada kace nine silar rashin lafiyarka.." Ta ƙarasa kusa da shi da rawar jiki, ta durƙusa a gefen gadon, ta riƙe hannunsa. Hannu mai sanyi da rauni.. A hankali, kamar wanda yake jin muryar da zuciyarsa ta fi so fiye da komai, Maleekh ya motsa idanunsa. Suka buɗe a hankali, yana lumshe su a slow, sannan suka tsaya kan Amal... Shiru ya cika ɗakin. Na’urar heartbeat yana beep beep beep a hankali. Sai Maleekh ya ɗan motsa leɓensa. Muryarsa ƙasa sosai, amma kalmomin suna ɗan fitowa... "Amal… kina nan?" Amal ta fashe da kuka mai ƙarfi tana faɗin: "Eh, ni ce… ni ce My bee. Na zo… na zo duba ka…" Sai Maleekh ya ƙara lumshe idanuwansa, yana ƙoƙarin yin murmushi mai rauni, ya ce "Ban taɓa daina sonki ba…" Amal ta durƙusa tana riƙe da hannunsa, idanuwanta na cike da hawaye, ta ce: "Ka daina kuka Ya Maleekh, don Allah… ka tsaya ka dubeni, ni ce… ban taɓa daina sonka ba nima..." Sai dai Maleekh ya lumshe idanunsa gaba ɗaya, zuciyarsa na bugawa da sauri. A ƙwaƙwalwarsa sai muryar Doctor ta dawo yanda yake faɗin: "Mr. Maleekh, result ɗin ya nuna cewa Amal ta zubar da cikin wata huɗu…" Zuciyarsa ta ƙara karye wa! Wani irin raɗaɗi ya shige shi fiye da duk wani ciwon jiki da yake ji. Numfashinsa ya ƙara sarkewa, idanunsa suka ƙumbura da hawaye masu zafi.. A cikin ransa ya ke faɗin: “Na yarda da ita… na amince da ita… yanzu kuwa?” Sai hawaye suka kwaranyo masa, ya girgiza kai yana ta faman zubar su. Amal ta firgita, ta miƙe tana share masa fuska tare da faɗin: "Wayyo Allah! Me yasa kake kuka haka? Na baka tsoro ne? Ko jikinka ne ke maka zafi?!" Maleekh ya zame hannunsa daga nata da ƙarfin da ba’a zata zai iya ba. Idanunsa suka canza, suka cika da huci da tsanar da take neman cinye shi. Ya ɗan motsa bakinsa da ƙarfi ya ce: "Ke… me kika yi min? Ke wacece Amal?!" Amal ta tsaya cak, jikinta ya ɗauki rawa ta ce: "Ni? Ni na yi maka me, Maleekh?" Ya lumshe idanuwansa yana ƙoƙarin tattara ƙarfin magana.. "Na ji… na sani… asibiti… result ɗin ki… kin zubar da ciki na wata huɗu! Me kike nufi da wannan? Wane namiji kika aura da har kika yi masa ciki, kika zubar?!" Amal ta durƙusa tana rikicewa ta ce: "Subhanallah! Maleekh, ni fa ba haka bane! Wallahi ba haka bane! Ka yarda da ni… ba gaskiya bane wannan…" Amma Maleekh ya juyo da fuskarsa gefe, hawaye na zuba, zuciyarsa ta cika da haushi da kishi mai ban tsoro. A cikin ransa kalma ɗaya ce ke maimaituwa: "Ta ci amanata… ta ci amanata…" Sai muryarsa mai rauni da tsawa a lokaci guda yana cewa: "Ki fita! Ki fita daga ɗakin nan kafin ki kashe ni da ƙaryar da kike zubawa! KI FITA!!!" Amal ta fashe da kuka, ta juyo da rawar murya tana faɗin: "Na rantse da Allah, ni ba haka bane! Ka yarda da ni Maleekh, wallahi ban ci amanarka ba!..." Ta miƙe da kuka, amma zuciyarta ta kasa barin ɗakin. Ta tsaya a gefen gadon tana kallon shi yana cigaba da zubar da hawaye cikin raɗaɗi, zuciyarta ta karye fiye da tunanin kowa. A daidai lokacin da muryar Maleekh ke ƙara ɗaga ɗaki yana tsawatawa da ƙarfin da bai kamata ba, ƙofar emergency ɗin ta buɗe da sauri. Doctor ɗin ya shigo da nurses biyu a ruɗe. Doctor ya daka-tsawa tare da faɗin: "What is going on here?! Waye ya saka shi magana haka?!" Ya matsa kusa da gadon da sauri, yana riƙe da stethoscope ɗinsa, ya duba hancin Maleekh da kirjinshi. Sai ya juyo yana hararar Amal da fushi ya ce: "Young lady, baki fahimci halin da marar lafiya yake ciki bane?! Zuciyarsa tana a critical stage! Koda kaɗan ba zai iya ɗaukar tashin hankali ba. Idan kika cigaba da tayar masa da hankali, zai iya mutu nan take! Kina son hakan ya faru?!" Amal ta zabura da rawar jiki, ta saki kuka tana girgiza kai ta ce: "Wallahi ban nufin cutar da shi ba, Doctor… ban nufin haka ba…" Doctor ya tsawata mata da ƙarfi cewa: "Sai dai ke kika jawo wannan! Ki fita daga ɗakin nan yanzu! Lafiyar marar lafiya ce a gaba, ba damuwar zuciyarki ba!" Nurses suka matsa kusa da Amal, suka riƙe hannunta cikin tausayawa, suka fitar da ita.. Amal tana cewa cikin kuka mai ƙarfi: "Na rantse da Allah, ban ci amanarka ba Maleekh… Wallahi sai gaskiya ta tabbata, sai Allah ya saka min…!" Ta juya da gudu cikin kuka, ta bar wurin, ƙafafuwanta na jijjiga kamar zata faɗi. Doctor ya kalli Maleekh da idanu masu ƙarfi ya ce da shi: "Ka saurare ni, Mr. Maleekh. Idan baka kwantar da hankalinka ba, zuciyarka zata iya tsaya maka. Ka tuna kai babban mutum ne da rayuwarka take da daraja a gaban iyayenka da jama’a. Idan kana son mutum to ka kiyaye lafiyar ka, idan kuma baka so, ka kwantar da zuciyarka..... Idan baka so ka rayu saboda kanka, to ka rayu saboda waɗanda suke ƙaunarka." Ya nuna nurse ɗaya ya ce da ita: "Ku saka masa oxygen sosai, sannan ku duba ECG. Na ce babu wanda zai sake shiga ɗakin nan sai na bayar da izini!" Nurses suka amsa: "Yes Doctor." Doctor ya sake kallon Maleekh cikin tausayawa ya ce: "Don’t waste your life on anger. Heart is too delicate for that." Ya juya ya fice daga ɗakin, nurses suka cigaba da gyara masa kayan da aka jona. Maleekh ya lumshe idanu yana sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi, amma hawaye na ci gaba da gudana. A zuciyarsa kalma ɗaya ce ke murɗawa: "Na so ta fiye da komai… amma ta ci amanata…". _NEXT! NEXT!! NEXT!!!_ asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 41 to 42 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 A corridor ɗin hospital Amal ke tafiya tana kuka, hawaye na sauƙa kamar ruwan sama. Gyalen jikinta ta ɗora akan fuska gaba ɗaya, ta kasa ganin inda take nufa. Sakamakon hakan ta buge wani babban mutum da ke tsaye yana waya, takardun da ke hannunsa suka watse ƙasa. Amal a firgice ta dafa ƙirji, ta durƙusa da sauri tana tattara takardun: "Innalillahi! Na shiga uku, don Allah ranka ya daɗe kayi haƙuri wallahi ban lura ba…" Hannunta na rawar sanyi tana miƙa masa takardun cikin ladabi. Shi kuwa mutumin, Abbansu Maleekh ya ɗago yana dubanta. Yana kallon yadda take kuka kamar mara galihu, fuska cike da hawaye, zuciyarsa ta ji tausayinta duk da bai san wacece ba... Abba ya karɓi takardunsa, sannan ya sa hannunsa ya ɗagota a tausashe: "Tashi ki tsaya yarinya, babu laifi. Amma meyasa kike kuka haka?. Me ya same ki haka?.." Amal ta share hawaye cikin ƙaryar ƙarfin hali, tayi murmushi mai ciwo tare da faɗin: "Ba komai wallahi… wata ƙaddara ce kawai. Na gode sosai." Abba ya girgiza kai yana kallonta cikin tausayawa ya ce: "Kada ki yarda damuwa ta raunana miki zuciya. Rayuwa ba ta wuce gwaji ba. Ki roƙi Allah ya kawo miki mafita, domin shi ne mai iko akan zuciya da ƙaddara." Kalamansa sun shige jikin Amal kamar wutar lantarki. Ta ɗan lumshe ido tana jin sanyi a ranta, kamar an shafa mata magani. Ta kasa cewa komai sai dai ta yi masa godiya tana murmushi cikin hawaye: "Na gode ranka ya daɗe, Allah ya saka da alheri." Ta yi gaba tana fita daga corridor ɗin. Abba ya bita da kallo, zuciyarsa na tambaya “Wacece wannan yarinya mai ɗauke da baƙin ciki haka?” Sai ya juya ya nufi ɗakin da Maleekh yake. A harabar hospital, Amal na tafiya a hanzari zuwa motarta. Amma kafin ta isa, sai ta yi kucuɓus da Ammy, Farha, Arfat, da Islam waɗanda yanzu suka shigo asibitin. Ammy ta tsaya cak tana harararta, muryarta cike da izza ta ce: "Me ya kawo ki asibiti? Shin baki ji na yi muku iyaka ba? Ko kina so ki kashe ɗana da hannunki?!" Farha ta haɗe fuska, ta turo baki cikin raini ta ce: "Eh mana! Ai yanzu Yaya Maleekh ya daina ƙaunarki. Ba zai taɓa mu’amala da karuwa ba, don karuwai kawai suke zubar da ciki a club!" Amal ta tsaya kyam, sai ta saki murmushin takaici. Ta juya kai a hankali ta dubi Farha da idanu masu ƙarfi sannan ta ce: "Haka kuma ba zai taɓa mu’amala da yar shaye-shaye ba." Farha ta ɗaga hannu cikin hargowa za ta mari Amal. Cikin zafin nama Amal ta cafke hannunta da sauri, tana murɗawa kaɗan har sai da Farha ta ji zafi. Idanunta sun canza launi zuwa ƙiyayya, muryarta a tsanake take faɗin: "Kada ki sake taɓa ni Farha. Idan kika kuskura, sai nayi gutsi-gutsi da yatsun ki nan take." Arfat ta ɗan ja da baya tana kallon Amal da mamaki. Islam kuwa ta runtse baki tana ƙoƙarin boye murmushinta. Ammy ta katse su da tsawa: "Enough! Warning na ƙarshe nake baki Amal, ki fita daga rayuwar ɗana. Bana son sake ganin ki kusa da shi!" Amal ta ja dogon numfashi, ta ɗan yi shiru kamar wacce ke tunani. Sannan ta ɗaga ƙafa ta taka gaba, ta tsaya a gabansu cikin ƙarfin hali, muryarta na rawar zuciya cike da tabbaci take faɗin: "Ammy, sai dai idan Maleekh ne ya mutu, ko ni na mutu, amma ƙaddara ta riga ta haɗa mu. Kuma ƙaddara ba a goge ta da kalma, a rubuce take a littafin Ubangiji." Ta wuce su kai tsaye, ta buɗe motarta, ta shiga. Ta kunna engine, a ɗari ta bar hospital ɗin ba tare da ta sake waiwayen su ba. Ammy ta tsaya kallonta da tsananin haushi, har sai da motar ta ɓace daga gani. Farha ta harare Amal cikin ƙiyayya tana turo baki, tana huci ta ce: "Tabbas dole mu kawar da wannan yarinya daga rayuwar Ya Maleekh, kafin ta kashe shi da hannunta." Islam kuwa ta kasa ɓoye murmushi, ta yi gaba ta bar su a tsaye. ☆☆☆☆ Abba yana shiga cikin hospital, zuciyarsa na tunani akan yarinyar da ya gani a corridor. Ya ji kamar akwai wani abu a tattare da ita, baƙin cikin da yake ɗauke da shi ya ratsa shi sosai. Yana shigowa ɗakin Maleekh ya tarar da shi kwance, har yanzu bai farfaɗo da kyau ba, idanu a lumshe, numfashi a sarƙe. Likitoci sun fito daga emergency room sun ce a barshi ya samu hutu. Abba ya zauna a gefen gadonsa, ya riƙe hannunsa da ɗumin ƙauna. Idanunsa suka kaɗa da hawaye, sai ya ce cikin sanyi: "Yaro na… Maleekh. Ka tashi ka ga yadda kake jefa mu cikin tashin hankali. Ni mahaifinka ne, kuma na rantse da Allah, ba zan taɓa bari a tilasta maka abin da ba ka so ba. Duk yarinyar da kake so, zan tsaya a bayanka." Ya yi shiru, ya goge idonsa. Sai kuma ya sake magana cikin tausayi: "Ka san meye ɗana? yanzu na haɗu da wata yarinya a corridor. Na ji tausayinta. Amma ban san wacece ba. Sai kawai zuciyata ta ce, wannan yarinyar akwai wani abu mai girma a ranta. Kamar ƙaddarar rayuwarka tana haɗe da ita… Amma Allah ne masani..." Maleekh ya motsa a hankali, kamar yana jin maganganun. Ya ɗan buɗe ido kaɗan, hawaye suka gangaro masa, amma bai iya magana ba. Abba ya matse hannunsa da ƙarfi ya ce: "Ka kwantar da hankalinka ɗana, Allah zai baka mafita. Na fasa, babu wata yarinyar da zan saka ka aura. Babu tilas. Zan tsaya a bayanka da gaskiya." Ya ji motsin ƙofa. Sai ga Ammy ta shigo tare da iyalanta. Ammy ta tsaya cak, ta hango Abba yana riƙe da hannun Maleekh. Fuskar Abba ta nuna rashin jituwa. Abba ya dubeta da ido cike da gargaɗi ya ce: "Kina ji ko? Na ce babu tilas ga ɗana. Na gaji da wannan mulkin da kike yi na rashin hankali. Ki bar wannan doka taki, saboda wannan ɗan ba naki bane ke kaɗai. Shi ɗana ne, kuma rayuwarsa ba abar wasa ba ce." Ammy ta fashe da kuka tana cewa: "Kana gani ko? Kana gani fa? Wannan yarinya karuwa ce, ta zubar da ciki a club! Shin wannan ce kake so ta zama matar ɗanmu?.." Abba ya daka mata tsawa cikin bacin rai ya ce: "Shiru!! Ba ki da ikon yanke hukunci akan rayuwar ɗana. Ni ne uba, kuma na yarda da abin da zai zaɓa. Duk abinda ya so, shi ne za’ayi. Kuma wallahi, bana son sake jin ki da sunan karuwanci ko zubar da ciki a gaban ɗana! Idan kin kasa gane magana, zan tabbatar iyayenki sun koya miki darasi." Tsofaffin iyayen Ammy wanda shigowarsu kenam, basu koma garin da suke ba suna jiran tashin Maleekh, jin tattaunawarsu yasa suka gyaɗa kai, suka ce da ita cikin tsawa: "Ai ke kika ja wannan bala’in da rashin biyayya da bijirewa tunda kina yarinya. Ki ci gaba da ganin sakamakon dabi’arki yanzu." Ammy ta saki kuka tana girgiza kai, amma babu wanda ya tausaya mata. Maleekh a gefe yana sauraron wannan maganganu, hawaye na fita daga idonsa. Zuciyarsa ta ƙara rikicewa, ƙaunar Amal, tsanar Amal, da soyayyar iyayensa da kuma tsanar Farha duk sun gauraye cikin zuciyarsa. A ɗakin, shiru ya mamaye bayan hayaniyar Ammy da iyayenta ta lafa. Kowa ya fita, aka bar Maleekh a kan gadonsa, da Farha a gefen gado tana kuka. Farha ta tsuguna ƙasa, tana riƙe da hannayensa cikin rawar jiki. Idonta ya cicciko da hawaye, muryarta na rawa tace: “Yaya Maleekh… wallahi ina matuƙar kaunarka. Ka sani ko? Shi ya sa kake ganin ina abubuwa marasa kyau. Ni ba wai saboda mugunta nake ba, kawai burina shi ne na mallake ka a matsayin mijina.” Ta kalli fuskarsa, amma ba amsa. Sai ta ƙara fashewa da kuka mai ƙarfi: “Amma tinda baka sona… shikenan. Ni ba zan tilasta kaina a gareka ba. Ka huta kawai, ka manta da ni.” Ta saki hannuwansa ta rufe fuskarta a cikin tafin hannunta tana kuka sosai. Maleekh ya juyo da kyar, idanunsa sun cika da hawaye, ya dube ta na ɗan lokaci. Sai zuciyarsa ta motsa da tausayin kalmarta. Wani abu ya shige shi, ƙaunar, soyayya duk ya watsar da su gaba ɗaya, amma jinin ɗan’uwantaka ya motsa... Cikin rauni, muryarsa ƙasa ƙasa sosai, ya furta “Farha… kin cancanci a so ki… amma ni… na haƙura da soyayya gaba ɗaya. Na haƙura da ita har abada. Ke, ko Amal… babu wanda zai sake samun zuciyata.” Ya lumshe idonsa, hawaye suka zubo daga gefe yana ƙara cewa cikin rauni: “Zan rayu ba tare da mace ba… tunda babu komai a soyayya sai ciwo kawai.” Farha ta yi ƙara cikin kuka ta riƙe gadon, tana faɗin: “Wayyo Allah naaa! Yaya Maleekh kada ka ce haka. Ni bazan iya jurewa ba.” Ya rufe ido gaba ɗaya, bai sake magana ba.. Farha tana kuka tana jingina da gefen gadon, sai taga Maleekh ya rufe idonsa gaba ɗaya. Kafin ta sake magana sai ga ƙarar buɗe ƙofa. Doctor ya shigo da file a hannunsa, yana takowa har kusa da gadon. Idonsa ya sauƙa kan Farha da ke tsugunne a ƙasa, sannan ya duba fuskar Maleekh da ke lumshe ido, hawaye na zuba masa a gefe. Doctor ya ɗan tsaya yana nazari kafin ya yi magana da tausasawa da ƙarfi ya ce: “Hajiya, kiyi hakuri, amma yanzu dole ne ki bar ɗakin. Yana cikin damuwa sosai. Idan kina ƙara saka shi cikin kuka ko tashin hankali, hakan na iya cutar da lafiyarsa fiye da jinyar da muke yi masa.” Farha ta ɗago kai cikin kuka, ta dubi Doctor da idanunta jawur ta ce: “Ni ba wai son tashin hankalinshi nake so ba Doctor… wallahi ni ina ƙoƙarin kwantar masa da hankali ne.” Doctor ya girgiza kai cikin ladabi, ya ɗan sauƙe numfashi sannan yace: “Na fahimta, amma yanzu ba wannan lokacin bane. Lafiyarsa tafi buƙatar kwanciyar hankali. Ki bari ki fita ki barshi ya huta. Zaki iya dawowa daga baya idan ya samu sauƙi.” Sai ya matsa kusa da ita cikin tausayawa, yana nuna mata ƙofa da hannu. Farha ta share hawayenta, zuciyarta na karyewa, ta dubi Maleekh da bai buɗe ido ba. Ta miƙe a hankali, tana jin jikinta ya yi nauyi, kafin ta fice daga ɗakin cike da ƙunci. Doctor ya juya ya duba Maleekh, ya ɗan murmusa da tausayawa a gefen baki, yana rubuta wani abu a takarda. ☆☆☆ Amal ta shigo gida da hawayen da ta kasa dakatawa, duk jikinta yana rawa saboda nauyin damuwa da tashin hankali. Hannunta a rufe akan fuska da gyale, ta shige falo ba tare da ta wa Inna kallon kirki ba. Inna tana zaune a kujerar falo, tana zare ido tana haɗa rai. Da sauri ta daga murya cikin yanayin tsawa: “Can miki dai! Ki ƙarata sama ki zauna. Wawiya kawai! Kin tsaya kina rawar jiki saboda wani namiji da ya watsar dake? Taya kike tunanin Maliku zai sake kallonki bayan wannan abun kunyar da kika aikata? Kin tozarta kanki kin tozarta mu gaba ɗaya!” Kalmar “tozarta” ta shiga kunne Amal kamar wuƙa, ta ƙara ratsa zuciyarta da raɗaɗi. Bata tsaya sauraren ƙarin magana ba, ta wuce da gudu zuwa sama. Da ta shiga ɗaki, ta rufe ƙofa da ƙarfi, sannan ta faɗa akan gadonta. Ta dunƙule jikinta kamar ƙaramar yarinya, hawaye suna tsiyaya tamkar ruwan sama. “Ya Allah… me yasa zuciyata ke son shi haka? Me yasa Maleekh ya zame min kamar rai na? Duk inda na juya, shi kawai nake gani…” ta furta cikin shessheƙar kuka. Tsanannin kaunar Maleekh ya yi mata nauyi kamar dutse mai murƙushe zuciya. Zuciyarta na neman hallaka, jikinta gaba ɗaya na rawa da sanyi. Ta matse pillow tana goge hawayen da basu daina zuba ba. Duk da kalaman Inna sun ɗora mata raɗaɗi, amma ƙaunar Maleekh ta mamaye duk wani tunani nata. A zuciyarta, ta yi addu’a cikin rawar murya: “Ya Allah, idan wannan soyayya zata zama abun da zai hallaka ni, ka bani ƙarfin zuciya in jure. Amma idan ƙaddara ce ta haɗa mu, to ka sauƙaƙa min… ka dawo min da shi…” Darenta ya yi tsawo kamar shekara. Amal ta juya ta baya, ta juya ta gaba, amma idanunta sun ƙi rufuwa. Kallon ceiling ɗakin kawai take yi, amma abin da zuciyarta ke gani daban ne – fuskar Maleekh ce kawai a cikin idanunta. Hawayen da suka gama bushewa sai suka sake sabunta. Duk lokacin da ta lumshe idanu, sai zuciyarta ta cika da muryarsa, yadda yake kiranta “Amal” cikin salo na musamman da babu wanda zai iya kwaikwayo. Sai a hankali barci mai nauyin damuwa ya ɗauke ta. A cikin mafarki ta tsinci kanta a cikin wani fili mai yalwa, duk wurin fari ne kamar ƙasar hazo. A can gaba kuwa, ta hangi Maleekh tsaye cikin farin kaya, yana mata murmushi irin na da. Da gudu ta nufi wurinsa tana cewa: “Ya Maleekh! Ka dawo gare ni, ka ce baza ka barni ba…” Amma kafin ta kai shi, sai fili ya fara rikicewa. Maleekh ya fara ja da baya, kamar wani ƙarfin duhu ke jansa daga gareta. “Amal… bazan iya zuwa gare ki ba… kin ci amanata…” muryarsa ta fito kamar wuƙa, tana yankan zuciyarta... Amal ta durƙusa cikin kuka tana ƙiran sunansa, tana miƙa masa hannaye amma ya ƙi kamo su. Hazo ya lulluɓe shi gaba ɗaya, ya ɓace daga ganinta “A’a! Maleekh, wallahi ban ci amanarka ba! Ka saurare ni, ka dawo! Don Allah ka dawo!” A firgice ta farka daga barcin, tana tsalle daga gadon kamar wacce aka jefa a wuta. Kafafunta suna rawa, jikinta duk ya jike da zufa. Ta dafe ƙirji tana kuka mai tsanani, zuciyarta kamar zata tarwatse. “Wayyo Allah! Har mafarki ya koma azaba saboda Maleekh… Ni me nayi ne haka? Ina ruwana da wannan ƙaddara? Wayyo Allah …” A daren, Amal bata sake iya rufe ido ba. Ta zauna tana kallo cikin duhun ɗakin, tana jin soyayyar Maleekh na hura mata wuta a ƙirji tamkar ana zuba gishiri cikin raunannen zuciyarta. Washegari bayan sallar asuba, Amal ta zauna a kan sallaya, idanuwanta sun kumbura saboda kukan daren jiya. Kafin ta miƙe, wayarta ta fara ringing. Ta ɗauka cikin sanyin murya. “Hello…” Manager ya ce: “Madam Amal, mun jiki shiru daga gare ki. Kema baki zo company ba. A matsayinki na assistant CEO, yanzu da oga Maleekh ba shi da lafiya, ya kamata ki tsaya ki wakilce shi. Ayyuka sun yi mana yawa sosai…” Amal ta rufe idanunta tana jan numfashi mai nauyi. Kalaman sun bugi zuciyarta domin har yanzu tana cikin baƙin ciki, amma bata so ta nuna raunin ta.. Ta ce: “Kar ku damu. Zan dawo aiki yau.” Suka yi sallama, ta kashe wayar. Ta shiga bathroom ta watsa ruwa, sannan ta sha kwalliya kamar wata sarauniya. Ta shafe fuskarta da makeup, ta sanya Atamfa riga da skirt da suka matse jikinta sosai, sun fito da surar jikinta. Ta sanya takalmi masu tudu a ƙafarta, ta ɗan yafa gyale a kafaɗa gefe guda, sannan ta ɗauki farin glass siriri ta ɗora a idonta. Sai ƙamshin turare masu sanyi da daɗi suka mamaye jikinta. Ta ɗauki handbag da wayarta ta fito. A falo ta tarar da Inna zaune. Ta yi mata sallama cikin ladabi, amma Inna ta kawar da kai kamar bata ji ba. Ta kuma cewa: “Ni zan tafi wurin aiki.” Inna ta kalleta da ido mai cike da tsana ta ce: “Ai idan kin ga dama ki wuce wurin club ɗin ma. Domin na tabbata nan ne wurin samarinki.” Amal ta tsaya cak, sai murmushin da ta yi sannan cikin takaici ta ce: *“Inna, idan har tunaninki bai gushe ba, gaya min. Da wa kika taɓa ganina tunda kike? Eh, gaya mun? Idan ciki ne ai Maleekh za a zarga, domin ban taɓa kula wani ba sai shi. To wallahi ya isheki, Inna.... Kuma shi Maleekh ɗin, idan akwai hukunci a kaina, ya rage nasa, tunda shi ya san gaskiyar Amal ɗinsa.” Inna ta miƙe cikin masifa tana zaginta, itama Amal ta ƙara ƙarfafa murya cikin zafi ta ce: “Inna, ko tsine mun kikayi, wallahi bazai kamfani ba. Domin ba ke kika haifeni ba. Mahaifina kika haifa, ba ni ba. Shi ya mutu balle… Ni jikarki ce, amma ba ƴarki ba!” Kalmar ta girgiza Inna, ta tsaya tana haki tana kallonta da mamaki da fushi. Amal kuwa bata tsaya ba, ta juya cikin isa ta bar falon... Tana fita ta shiga motarta kai tsaye ta nufi company, zuciyarta cike da haushin rayuwa amma ta daure ta sanya fuskar izza domin ta san yanzu dole ta tsaya ta kare matsayin da Maleekh ya bari a hannunta. Motar Amal ta tsaya a bakin harabar CashTalk Empire. Security da receptionists suka yi saurin tashi da girmamawa, kowannensu na zuba mata ido. Sun ji tsoro da mamakin irin labarin da ya bazu akan Amal cewa ta zubar da ciki a gidan rawa. Amma babu wanda ya furta komai, saboda sun san matsayin ta: Assistant CEO. Amal ta fito daga motarta a hankali, dogayen takalmin da ta saka na ɗaukar hankali. Gyalen da ta ɗora ya ɗan zame gefe yana ƙara fito da tsantsar kamalarta. Idanuwanta da farin glass ya lullube suka bada wani irin izza da basira. Kowa da yake kallonta ya ɗan sunkuyar da kai, suna yin gaisuwa cikin ladabi. Ma’aikata suka miƙa gaisuwa da cewa: “Good morning, Madam Amal.” Amal ta ɗan ɗaga hannu a hankali, muryarta a nutse ta ce: “Morning.” Ta wuce kai tsaye zuwa elevator, kafafuwanta na yin taka-tsantsan kamar sarauniya. Duk inda ta bi sai kallonta ake yi, amma babu wanda ya ƙara magana. Wasu ma’aikatan mata suka yi shiru suna bin ta da ido cike da hassada da kuma mamaki. Bayan ta shiga office ɗinta, ta rufe ƙofar da ƙarfi ta jingina da ita. Ta runtse idanuwanta tana jan numfashi mai nauyi. Zuciyarta tana tuna zagin Inna, kalaman Ammy, da kuma yanda Maleekh ya nuna mata baya son ta. Sai dai ta girgiza kai, ta tafi ta zauna a kan kujerar executive chair mai juyawa. A gabanta akwai takardun contracts, files masu yawa da suke jiran signature ɗin Maleekh. A hankali ta fara ɗauka ɗaya bayan ɗaya, tana nazari sosai. Amal a cikin zuciyarta ta ce: “Ba zan bari mutanen nan su raina ni ba saboda abinda suka ji. Ni Amal ce Assistant CEO. Kuma na san kowa a nan da yake aiki yana jiran ganin ikon da zan nuna.” Ta ɗaga wayarta ta ƙira secretary. Amal ta ce: “Kawo min dukkan reports na kwana biyun nan da na yau. Ina son ganin komai kafin ƙarfe goma. Kuma ka sanar da managers ɗin departments su shigo da briefing yanzu.” Secretary ya bada amsa da cewa: “Yes, Madam.” Bayan ‘yan mintoci kaɗan, manyan ma’aikata da managers suka shiga office ɗinta cikin ladabi. Sun tarar da ita zaune, ta cire glasses tana kallon files a gabanta. Amal ta ɗago da idanu masu kaifi ta ce: “Ku zauna. Ina so in ji matsayin kowane department yanzu. Maleekh baya nan, amma aiki bai tsaya ba. Ku tuna, company ba ta tsaya wa akan mutum guda sai dai akan tsarin aiki da jajircewa.” Managers suka kalli juna, kowanne yana girmama ƙarfin halinta. Duk da ƙazafin da ake mata, ta zauna a matsayin shugaba mai cikakken iko. A lokacin, ɗaya daga cikin managers ɗin ya ɗan gyara murya cikin girmamawa ya ce: “Madam, gaskiya muna mamakin yadda kika zo da ƙarfi haka. Mun san komai da ake magana a waje, amma yanzu mun ga da idonmu kin fi ƙarfin duk wata jita-jita. Zamu ba ki haɗin kai.” Amal ta ɗan murmusa, murmushin da ya cika da takaici da izza a lokaci guda.....ta ce: “Kyakkyawan aiki shine amsar da zan bawa maƙiyi. Babu wanda zai ce Amal ba ta da daraja. Ni zan tabbatar da haka.” Sai ta ɗora hannunta akan files ɗin gaban ta ta fara briefing, tana ƙiran department ɗaya bayan ɗaya. Duk da zuciyarta na ta ƙuna da zafin kaunar Maleekh, a wajen aiki ta bayyana kamar wadda babu wata damuwa da ta taɓa zuciyarta. Bayan ta kammala meeting ɗin managers, Amal ta koma office ɗinta. Duk wani aikin da aka kawo mata ta duba shi da tsantsar hankali, ta sanya signature inda ya dace. Duk da gajiyar zuciya da ke cin jikinta, ta tsaya daram ta tabbatar da babu wani abu da zai tsaya a gaba saboda rashin Maleekh. Sai dai lokacin da ta kalli agogo ta ga ƙarfe 3:30 na rana. Zuciyarta ta fara bugu da ƙarfi. Ta san akwai wurin da zuciyarta ke jan ta: Office ɗin Maleekh. Da sauri ta miƙe, ta ɗauki glass ɗinta ta ɗora, ta ɗauki jakarta ta fita daga office ɗinta. Bata tsaya sauraron kallon da ma’aikata ke mata ba, ta nufi babban office ɗin CEO.... (Oh ko ina dai sai ka samu magulmata..). Bayan ta isa bakin ƙofar, zuciyarta ta buga sau uku kamar zata fito. Ta jingina da ƙofar tana jan numfashi mai nauyi. A hankali ta murɗa handle ɗin ta shiga ciki. Office ɗin na Maleekh ba kowa a ciki. Sai duhu, sai shiru, sai kuma ƙamshin turarensa da ya lulluɓe ɗakin gaba ɗaya. Amal ta tsaya cak a bakin ƙofa. Idanuwanta suka rufe, zuciyarta ta fara rawa. Kamar Maleekh yana zaune a kan kujerarsa yana mata kallon ƙauna. Ta ja ƙafar ta a hankali ta ƙarasa zuwa kujerar executive chair ɗinsa. Ta taɓa bayan kujerar da hannunta, hawaye suka zubo mata. Amal a cikin ranta ta ce: “Oh Maleekh… har yanzu ƙamshinka yana nan. Har yanzu zuciyata ta ƙi yarda da cewa baka sona. Me yasa kake min haka bayan dukkan so da ka nuna mun?…” Ta zauna a kujerarsa, ta jingina da kujerar tana runtse idanu. Hannunta ta ɗora akan teburinsa tana shafa wani pen da yake ɗauke da rubutunsa. A hankali ta ɗauki hotonsa da ke kan teburin wanda aka ɗauka lokacin award ɗinsa na CEO of the Year. Ta ɗauki hoton ta kalle shi sosai, hawaye na zuba. Amal a hankali da murya mai rawa ta ce: “Ko da duniya ta juya mun baya, ko da iyayenka basu fahimce ni ba, na rantse ba zan taɓa daina sonka ba. Koda kuwa ka tsane ni…” Sai ta ɗora hoton akan ƙirjinta, ta rufe idanu tana jin tsantsar ƙauna da zafi a zuciyarta. A waje kuwa, wasu daga cikin staff sun hango Amal na fita daga office ɗin CEO ɗin daga baya, suka kalli juna cikin mamaki. Wata daga cikinsu ta ce da sannu-sannu: “Lallai wannan yarinyar akwai ƙarfin hali… Da ace ni ce a irin halinta, wallahi ba zan iya zuwa ko kusa da wannan campany ba. Amma ita, har tana iya shiga ta zauna.” Staff ɗin namiji ya ce: “Shi ne bambancin mace mai kishin zuciya da ƙuduri. Ko da kuwa duniyar bata yinta, sai ta tsaya tsayin daka akan abinda take so.” Amal ta fito daga cikin office ɗin Maleekh, ta nufi ƙofar fita daga campany. Sai dai a tsakar corridor ta hangi wasu ma’aikata mata biyu suna ta magana da dariya, suna kallonta a ɓoye. Da ta matsa kusa ta ji da kunnenta suna faɗin: “Ko kunya bata da ita wallahi. Kin manta irin yadda aka ɗauke ta a cikin jini daga gidan club? Ai magungunan zubar da ciki ta sha...” Ɗayar ta ce: “Haka fa. Amma yanzu gashi tana tafe da wani isa kamar ba ita ake nunawa a TV ba. Wallahi akwai wauta a rayuwa.” Amal ta tsaya cak! Ta ja numfashi ta juyo a hankali. Da glass a idonta, fuska cike da izza, ta taka cikin tafiya mai natsuwa zuwa wajen reception. Sai ta tsaya a tsakiyar hall ɗin inda ma’aikata suke cike. Ta ɗaga hannunta sama ta ce da murya mai ƙarfi: “Ina son waɗanda na jiyo suna gulmata su fito nan yanzu. A gaban kowa. Ku fito!” Sai aka yi shiru, kowa ya kalli juna. Su biyun da suka yi maganar suka fara rawar jiki suka fito a kunyace. Amal ta juya da kafaɗarta, ta cire glass ɗin daga idonta a hankali, ta dafa tebur ta ɗan jingina, sannan ta ce da murya mai kaushi: “Kun ce bani da kunya? Kun ce an ɗauke ni cikin jini daga club? Kun ce magungunan zubar da ciki ne suka kaini can? To ku saurara! Ƙaddara bata san gidan kowa ba. Wallahi idan wata rana irin wannan ta same ku, da kun san babu abinda ya fi shiru da adalci a rayuwa. Amma saboda ƙarancin tunani, ku kaɗai kun fake kuna munafurci, wawaye kawai, marasa kishin kai...” Sai ta kalli sauran ma’aikata gaba ɗaya, ta ɗaga hannu tana girgiza musu yatsa ta ce: “Ina so a san wannan a matsayin gargaɗi. Duk wanda na sake jin ya tsoma baki cikin rayuwata ko kuma ya kuskura ya sake ambaton wannan batu a bakin sa, wallahi zan rubuta masa takardar kora a nan take. Na rantse da ikon Allah zan tabbatar da ya bar wannan campany ba tare da second chance ba!” Ta ɗan ɗaga kai cikin izza ta ƙara da cewa: “Kar ku manta, ko da ban mallaki kujerar CEO ba, yanzu ni ce assistant CEO. Kuma ikon ɗaukar hukunci a hannuna yake. Don haka kowa ya kashe wutar gabansa, ya kula da aikinsa. Ku tuna..." Ta maida kallonta kan matan da ta kama tana cewa: "Mata ne ku, ba ku san irin makomar da Allah ya tanadar ba. Kada ku yi min hukunci da sharri, domin yau ni ce, gobe wata ce.” Ta ɗora glass ɗinta a idonta, ta juyo cikin izza ta nufi ƙofar fita. Takunta na ƙara amo a cikin shiru da kowa ya yi. Sai ta ce kafin ta fita: “Na gama magana. Ku tuna da abinda na faɗa.” Ta fice ta nufi motarta. Gaba ɗaya ma’aikatan suka tsaya shiru, suna kallonta cike da mamaki. Wasu suka lumshe ido suna cewa: “Wallahi wannan yarinya ƙarfin hali gareta sosai. Duk da kuwa an yi mata sharri, sai ta tsaya ta kare kanta.” Wani ya ce: “Eh… wannan izza da kwarin gwiwa ba kowa ke da shi ba.” Bayan Amal ta fice daga cikin campany cikin izza, harabar ofishin ta yi shiru kamar wuta ta mutu. Duk ma’aikatan kowa da abinda yake tunani, babu wanda ya iya sake yin magana. Sai PA ɗin Maleekh, ya fito daga cikin corridor. Shi ya shaida komai tun lokacin da Amal ta tsaya ta tara ma’aikatan. Ya tsaya yana kallon fuskar ma’aikatan da suka yi ƙasa da kai cikin kunya. Ya ɗan gyara murya ya ce: “Kun ga wannan abin da ya faru yau? Wannan yarinya ta nuna muku cewa bata da rauni a zuciyarta. Duk wani sharri da za ku ƙirƙira mata, wallahi za ta iya fuskantarsa da ƙarfin hali. Idan har tana iya tsaya ta kare kanta haka, to ta cancanci a ƙira ta shugaba.” Sai ya ɗan yi shiru ya kalli su biyun da Amal ta fallasa a gaban kowa. Ya ce: “Kuma ku, ku ji tsoron Allah. Wannan abu da kuka yi ba magana bace ta office. Aikin ku ne ya kawo ku nan, ba rayuwar wani ba. Ku ma ku iya tunanin kanku, me zai faru idan wata rana aka yi muku sharri irin wannan? Kada ku kuskura ku kuma.” Daga nan ya ɗan juya yana kallon sauran ma’aikatan gaba ɗaya: PA ɗin Maleekh ya ce: “Na ga yawanku kunyi shiru, kun girgiza kai. Wannan darasi ne. Kar ku manta duk wanda ya ƙi yin aiki da hankali da mutunci, wallahi Amal ba zata taɓa bari ya lalata campany ba. Kuma ni kaina zan tsaya a bayanta.” Ya jinjina kai ya ce a hankali: “Ko da kuwa Maleekh baya nan, Amal ta riga ta tabbatar da kanta a matsayin mai ikon ɗaukar hukunci. Ku kiyaye.” Sai ya juya ya koma cikin office ɗinsa, barin ma’aikatan da ke jinjina da cewa Amal ta nuna ƙarfin hali da cikakken iko. Da dare bayan kowa ya watse daga campany, PA ɗin Maleekh ya ɗauki waya ya ƙira ɗakin asibitin da yake kwance. Bayan sallama da gaisuwa, aka miƙa masa wayar zuwa Maleekh... PA ya ce: “Boss, ina fatan jikinka ya ɗan sauƙa?” Maleekh Ya ɗan murmusa da rauni sannan ya ce: “Muna nan, Allah na tare damu… Amma ka fadamin gaskiya, me yake faruwa a campany? Na ga har yanzu baku kawo mun daily report ba.” PA Ya yi gyaran murya, zuciyarsa cike da damuwa ya ce: “Hakane Boss… Amma akwai abu da na ga ya kamata ka sani kai tsaye. Yau bayan Madam Amal ta kammala aikinta, ta fito ta iske wasu daga cikin ma’aikatan suna gulmarta… suna cewa wai ‘yar club ce, da kuma zancen zubar da ciki. Boss, wallahi duk ma’aikata sun tsaya suna ji.” Maleekh ya runtse ido, zuciyarsa ta sake raɗaɗi, amma ya ce a hankali: “To, me tayi?” PA ya ce: “Wallahi, ta tsaya a gabansu cikin izza. Ta tara su gaba ɗaya, ta fallasa waɗanda suka fara gulmar, ta wulakanta su a gaban jama’a, sannan ta gargaɗi dukkanin ma’aikata cewa idan har wani ya sake taɓo wannan batun, zai fuskanci takardar kora. Boss, komai ta yi cikin natsuwa da ƙarfin hali.” Shiru ya cika ɗakin, Maleekh yana maida numfashi da nauyi. Duk da jin haushin Amal da yake yi tun daga asibiti, zuciyarsa ta girgiza da jin irin tsayuwar da ta yi a kan mutuncinta... Ya ɗago kai yana kallon PA ɗin da yake cikin call ya ce: “Duk wanda ya sake gulmar Amal a campany, kai da kanka zaka rubuta mun sunansa. Ba zan yarda wani ma ya wulakanta ta a ofishin nan ba. Kowane mutum yana da kurakurai, amma wannan ba dalili bane da zai sa a raina assistant CEO. Kaji ko?” PA da murmushi cikin girmamawa ya ce: “Na ji sir. Zan tabbatar babu wanda ya kuma.” Maleekh ya lumshe ido, zuciyarsa ta kumbura da abubuwa biyu: haushin Amal saboda sakamakon zubar da ciki da yake tunani, da kuma ƙarfin hali da ta nuna a bainar jama’a. Ya ja numfashi a hankali ya furta: “Amal… kin zame min raɗaɗi...” Bayan PA ya katse wayar, Maleekh ya jingina da filo yana rufe idanuwansa. Zuciyarsa na juyawa tsakanin soyayya da ƙiyayya. Sai ga Ammy ta shigo ɗakin da tray a hannu, ta kawo masa tea. Ta zauna kusa da shi tana tambayar: “Ya jikinka ɗana? Har yanzu kana ɗauke da damuwa ne?” Maleekh da murmushi ya ce: “Alhamdulillah Ammy, jikina ya ɗan sauƙa sosai.” Ammy ta ce: “Toh Allah ya ƙara lafiya. Campany fa? Ban ji kana magana akai ba yau. Wane irin labari kake samu daga can?” Maleekh ya buɗe ido ya dubeta, ya ɗan yi shiru kamar yana tunani. Sai ya ƙara gyara kwanciya, ya ɗan yi murmushi ya ce: “Komai lafiya. Ayyuka suna tafiya yadda ya dace. PA yana kula da komai, babu wani rikici.” Ammy ta gyaɗa kai cike da gamsuwa ta ce: “Toh madallah. Kar ka damu da komai sai lafiyar ka. Ni dai har yanzu bana jin daɗin ganin waccan yarinyar (Amal) tana zagaye ofis ɗinka. Amma dai idan har kana bukatar hakan, zan tsaya a gefe tunda Doctor ya ce a bar ka cikin natsuwa.” Maleekh ya ɗan saki murmushi marar sauti, zuciyarsa na motsi. Bai ce komai ba sai cewa da yayi: “Na gode Ammy… komai zai zo daidai da iznin Allah.” Ya rufe maganar da wannan, bai taɓa bari ta ji labarin abinda Amal ta fuskanta a ofishinsa ba. Ya ƙuduri aniyar boye komai daga iyayensa, saboda baya so wani ya ƙara wulakanta Amal a gabansa even da yake shi ma yana jin haushinta a zuciyarsa. Sai dai zuciyarsa ta furta a ransa: “Amal… duk da na tsane ki, bana son wani ya tauye mutuncinki.”.... _NEXT! NEXT!! NEXT!!!_ asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 43 to 44 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Bayan tattaunawar da yayi da Ammy, an bar shi shi kaɗai a ɗakin. Ya jingina da filo yana sauƙe ajiyar zuciya. Kalaman PA suna yawo a kunnensa: “Madam Amal ta tsayar da ma’aikata gaba ɗaya, ta nuna musu ƙarfi da izza… ta gargaɗe su cewa idan aka sake maganar ta, zata kori kowa.” Maleekh ya lumshe ido, zuciyarsa ta haɗu da soyayya da haushi. Ya tuna result ɗin Amal, ya tuna rashin gaskiyar da yake zargin ta da shi, sannan kuma sai ya tuna irin ƙarfin zuciyar da ta nuna a campany, tana kare mutuncinta da mutuncin sa kai tsaye. Hawayen takaici suka tsaya masa a ido, ya furta cikin zuciyarsa: “Amal… me yasa kika zama min tamkar dafin da nake sha kullum? Duk da ina zargin ki, ban so wani ya kalle ki a matsayin marar mutunci.” Sai ya runtse ido, yana jin ciwon zuciya da soyayya suna rikici a ransa. Amal kuwa ta dawo da mota gida, ta shiga falon. Inna na zaune tana duba TV, tana kallonta da idon da ya cika da zargi. Amal da sallama cikin ladabi ta ce: “Inna sannu da hutawa…” Inna ta kawar da kai, da dariyar raini ta ce: “Kin dawo kenan? Ko daga aiki kike, ko daga club ɗinki! Domin ai ban ga bambanci ba.” Amal ta tsaya cak tana kallonta. Ta ji kamar zuciyarta zata fashe, amma ta daure cikin nutsuwa ta ce “Inna, na dawo daga aiki ne, ina wakiltar Maleekh a campany. Ni ba ‘yar club bace.” Inna ta buga hannu a kujera cikin tsawa ta ce: “Ke da aka ɗauke ki cikin jini daga club, da likitoci suka tabbatar kin zubar da ciki… kina da bakin cewa ba ‘yar club bace? Ke ce bala’in rayuwar Maliku!” Amal ta matse hawayenta, tana girgiza kai. Sai ta taka kusa da Inna, ta ce da murya mai rauni mai cike da gaskiya: “Inna, wallahi ban taɓa bin wani namiji ba banda Maleekh. Kaddara ce kawai ta jawo abin da ya faru, amma da zuciya ta zan shaida miki ni ba ‘yar iska bace. Ni masoyiyarsa ce, shi kuma masoyina ne. Komai ya faru, Allah zai fitar da gaskiya.” Inna ta ja tsaki tare da faɗin: “Sai dai ki ci gaba da mafarki, domin Maliku yanzu ba ya son ki! Kuma bana so ki kara zancen shi a gabana.” Amal ta kalli Inna da idanuwan da suka cika da hawaye, amma ta ƙara murya da ƙarfin hali cewa: “Inna, ko da duniya ta ƙi ni, zan ci gaba da tsayawa da gaskiya. Domin soyayya tsakanina da Maleekh, ƙaddara ce. Ba wanda zai iya goge abin da aka rubuta.” Ta juya tana hawaye, ta haura sama kai tsaye ɗakinta, ta faɗi kan gado tana kuka... Bata ankara ba ta ji an turo ƙofar ɗaki da ƙarfi.. Inna ta shigo ɗakin Amal da masifa, tana huci kamar wuta.. Ta dafa bango tare da faɗin: “Ni dai wallahi Amal, baki isa ki tozarta ni ba. Ke kika jawo abin kunyar nan, yanzu za ki zo kina min gadara a gidan nan? Wacece ke a nan gidan?” Amal ta miƙe a fusace, idonta akan Inna tana zazzaro ido ta ce: “Inna kin wuce gona da iri! Me na yi miki da kike ta zagina kullum? Ko kin manta ni jikarki ce? Idan kika ci gaba da mun haka wallahi zan wurgar da ke daga wannan gidan, sai dai ki koma can Kaduna ki ci gaba da masifa a can! Wannan gidan gida na ne, da sunana a rubuce a jikin takardun gidan nan..!” Inna ta zaburo, ta kama ƙugu tana jijjiga kamar wacce zata yi dambe ta ce: “Au? Gidanki? To sai naga ‘yar iskar da zata bani umarni a gidan nan. Kina so in koma Kaduna saboda ki kawo tsinannun samarin club ɗinki gidan nan koh? To ki ji tsoron Allah Amal, bazan taɓa barin gidan nan ba wallahi, kuma zan nuna miki ni na fi ki bariki, karuwa kawai!”.. Amal ta sau murmushin takaici sannan ta ce: “Inna, na ga baki ɗauke ni a mazannin jika ba, meyasa bazaki kyale ni naji da abin da ke da mu na ba? Can ba sauƙi, nan ma ba sauƙi shin ya ku ke so nayi da raina? Ko kina so na mutu ne?..." Inna cikin ɗaga murya ta ce: "To ki mutu manaaaa, da wannan abun kunyar da kika jawo mana ai gwara mutuwar ki..." Amal ta ɗaga muryarta sosai, tana cewa: “Kafin ki ga mutuwata bari na wurgar dake tukun! Ki ji! Jarababbiyar tsohuwa kawai, kin mayar da gidannan gidan masifa! Daga yau, babu ruwanki da ni, babu ruwanki da Maleekh!” Amal ta riƙo hannun Inna da ƙarfi ta jawo ta. Inna tana ihu tana cewa: “Ki sakeni munafuka! Ke ba kya ji tsoron Allah?! Ni kike ja kamar yarinya?!” Amal bata saurare ta ba, ta ja ta har bakin ƙofa. Sai da ta ture ta waje gaba ɗaya, ta rufe ƙofa da ƙarfi “paahhhtttt!!” sannan ta saka key tana huci... Amal ta jingina da ƙofar tana huci, zuciyarta na bugawa da ƙarfi, Inna kuma tana waje tana ci gaba da tsinewa da masifa kamar zata tarwatse... Zuwa ta yi ta kwanta kib da ciki tare da lumshe ido...tana tunani har bacci ɓarawo ya ɗauke ta.. 🤦‍♀️🧞‍♀️ Amal tana zaune a kan kujerarta, biro a hannu amma gaba ɗaya zuciyarta ta tattare ne da damuwar Maleekh. Zuciyarta ta tsinke, idonta ya rinƙa lumshewa da nauyin tunani. Kwatsam krrriiiin ta ji an turo ƙofar office ɗinta a hankali. Bata san lokacin da ta ɗago kai ba, sai idonta ya sauƙa akan Maleekh!.. Sanye da fararen suit, farar riga, farin wando, farin tie duk ya haɗu tamkar mala’ika ya sauƙo. Fuskar sa cike da annuri, murmushi ya mamaye kyakkyawar fuskarsa, idanuwansa masu tsananin haske suka zuba kai tsaye cikin nata. Amal ta tsaya cak! Jikinta ya ɗauki rawa. “Ya Maleekh…” ta furta a hankali cikin ruɗani. Shi kuwa ya ɗan daga hannu alamar “zo nan”. Amal ta tsaya naƙe-naƙe kamar mai mafarki, amma ƙarshe ta miƙe, da sauri ta nufi inda yake. Da zarar ta isa ƙofar office ɗinta sai ya juyar da kai ya fita. Ita kuwa tana biye dashi a guje. Ƙafafuwansu suna ɗaukar sauti a kan tsalelakun bene suna hawa beni can sama-sama har sai da suka kai top floor na company, beni mafi tsayi wanda daga nan idan ka leƙo ƙasa za ka ga mutane kamar ƙwari. Sai da zuciyar Amal ta tsaya lokacin da ta ga inda Maleekh ya tsaya, bakin gefen building, inda babu komai sai sararin sama a samansa da kuma tsalelakun ƙasa a gaban sa. Ya juyo yana murmushi mai cike da annuri akan fuskarsa. Ya ɗaga hannayensa biyu yana buɗewa kamar yana ce mata “shigo ki faɗa jikina”. Amal ta furta cikin kuka: “Ya Maleekh… wallahi na yi kewarka… wallahi ina sonka!” Tayi gudu da karfi ta nufi inda yake domin rungume shi. Sai dai kafin hannunta ya rufe kirjinsa - battt!- ya ɓace kamar hayaki. Amal kuwa ta yi gaba! Hannayenta suna a buɗe, ƙafafunta suka zame ta faɗa cikin sararin ƙasa daga tsayin beni! Ta ware hannaye tana kukan tsoro cikin iska ta ce: “Yaaa Maleeeekh…!!!” Iskar sama na kaɗawa a kunnenta, zuciyarta ta riga ta amince cewa mutuwa ta iso. Idanunta sun kulle suna jiran ƙarshen faɗuwa... Sai kawai Amal ta farka a razane! 😱 Tana kan gadonta, jikinta na rawa, zufa ya wanke fuskarta. Numfashinta na fita da ƙyar kamar wacce ta yi tsere. Ta dafe kirjinta tana hawaye tare da faɗin: “Ya Allah… ashe mafarki ne… Ya Maleekh! Me yasa kake min haka a mafarki?…” Ta kwanta ta sake lumshe ido amma tsoron da ya mamaye ta bai bari ta sake samun nutsuwa ba... Amal tana kan gadonta amma har yanzu hawayen mafarkin na gangarowa. Hannunta na rikicewa akan kirjinta tana ji kamar zuciyarta zata tsage. Ta ce cikin rawar murya: “Ya Allah… me yasa mafarkina kullum akan Maleekh ne? Me yasa zuciyata ta kasa kwanciya sai na ganshi? Shin wannan ƙauna zata hallaka ni ne?…” Ta rufe fuska da hannuwanta, numfashinta na fita da ƙarfi. Cikin zuciyarta ta fara addu’a, tana roƙon Allah ya yaye mata wannan ƙunci. Amma ko da take addu’a, hoton Maleekh ɗin nan da murmushinsa mai ɗauke da annuri bai fita daga ranta ba. 🕊️ Kwatsam, ƙarar ƙofar ɗaki ta turo. Amal ta yi saurin jan gyale ta rufe kanta, tana share hawayenta... Inna har ta buɗe baki zata zazzago masifarta sai kawai ta ga wanin irin kallon da Amal take mata, abin da yafi tsoratar da ita shine ganin yanda kwayoyin idanuwanta suka ƙara girma ga sun yi jawur kamar gobara... Inna a tsorace ta saki murmushin dole tana faɗin: “Amatu… har yanzu baki tashi ba? Ko baki shirya zuwa campany ɗin bane yau?” Amal ta girgiza kai a hankali, ta ce da muryar da ta yi rauni sosai: “Inna… nayi mafarki, kuma sai yanzu zuciyata ta tsaya. Naga Ya Maleekh… naga kamar zai tafi ya barni har abada…” Inna ta tsura mata ido, ta sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi. Sai ta ce da ƙarfin hali: “Kin dai san mafarki ba komai bane. Amma Amal, idan kina son kwanciyar hankali to ki guji abin da zai sa ki zama zance a idon mutane. Kiyi tunani sosai, duniya ba ta da tabbas.” Amal ta miƙe a hankali ta tako gaban Inna, ta manta da ƙiyayyar da Inna ke mata...Kuma Innan ma ganin halin da Amal ke ciki yasa ta tsure... Amal ta dafa hannun Inna a tausashe ta ce: “Inna ki yi min addu’a kawai. Domin zuciyata bata yarda da kowa sai shi, kuma idan na rasa shi… na rasa komai a rayuwata.” Inna ta girgiza kai, bata iya cewa komai ba. Ta fita a hankali, ta bar Amal cikin tunani mai nauyi. Bayan Inna ta fita, Amal ta sake fashewa da kuka. Tace: “Ya Maleekh… idan da gaske baka sona, me yasa zuciyata ba zata iya barinka ba? Me yasa ko a mafarki sai ka dawo kana rikitar da ni?…” Sai ta ɗauki wayarta ta sake ƙiran lambar Maleekh, amma kamar kullum switched off. Bayan tayi kuka ta wanke fuska, Amal ta ɗaura gyale ta fito da nufin zuwa hospital...Domin sake ganawa da Maleekh, zuciyarta tana bugawa da sauri, kamar zata faɗi. A zuciyarta tana faɗin: “Zan je domin tabbatar da Ya Maleekh ko yana raye, zan duba idan har yanzu yana raye… Allah yasa yana numfashi, domin mafarkin da nayi ya nuna cewa ya mutu...” Ta shiga motarta a gaggauce, ta tafi ba tare da tsayawa ko’ina ba har ta iso gate ɗin hospital.. 🏥 Tana shiga ciki da sauri ta tambayi nurse: “Please, ɗakin da aka kwantar da patient Maleekh pag?” Nurse ɗin ta kalleta a tausashe sannan ta ce: “Sorry Madam… an sallame su jiya da yamma. Sun koma gida.” Amal ta tsaya cak! Numfashinta ya tsaya na wasu daƙiƙu.. “Me… me kika ce? An sallame su?” Nurse ɗin ta gyada kai: “Eh, family ɗinsa sun zo sun ɗauke shi. Ba a nan yake yanzu ba.” Amal ta riƙe handbag ɗinta da ƙarfi. Idonta ya cika da hawaye, ta juya a hankali ta fice daga hospital ɗin... Bayan ta fita harabar hospital ta jingina da motarta tana girgiza kai cikin kuka.. “Ya Allah… har yanzu ina cikin duhu. Ba zan iya ganin shi ba, ba zan iya jin muryarsa ba… Shin wannan alama ce daga gareka ka nuna mun cewa ba shi ne rabona ba?…” Sai ta buɗe mota ta shiga, tana kuka tana ƙiran sunan Maleekh a zuciyarta. Duk da haka zuciyarta ta ƙi yarda da cewa Maleekh na raye. Amal kai tsaye zata shahada ta nufi gidansu Maleekh duk da tasan gidan da ake wulakantata ne amma burinta shine taga Maleekh... Tana zuwa bakin get ɗin gidan ta sauƙa daga mota. Security suka tareta dake babban gida ne, gidan minister ne dole sai da matakan tsaro.. Ta ce da su: "Na zo duba jikin Maleekh ne.." Ɗaya daga cikine ya ƙira wayan gidan ya sanar dasu cewa anyi baƙuwa.. Aka bada izinin ta shigo ba tare da an san wacece ba. Amal ta tsaya cak a harabar gidan bayan security sun buɗe mata. Hannunta na rawa, zuciyarta na bugawa kamar zata tsage ƙirji.. Amma ta ɗaura niyya ko wulakanci ne, sai ta ga Maleekh.. Bayan ta taka ƙafar ta zuwa babban falon... Tana shiga gaba ɗaya idanun kowa ya koma kanta... Maleekh yana zaune a gefe, farin riga mai laushi a jikin shi, har yanzu yanayin mara ƙarfi na jinya yana tare da shi. Abba yana gefensa da murmushin tausayi a fuska. Ammy kuwa ta ɗaga gira cikin ɓacin rai. Farha ta ƙafe Amal da idon da yake haɗe da kishi da tsanar da ba’a iya ɓoyewa. Islam ta kalleta da tausayi, tana jin wani abu na motsawa a zuciyarta. Arfat kuwa ta ɗauke ido tana ta wasa da phone ɗinta... Falonnan mai yalwa ya cika da shiru na tsawon wasu sakanni. Har kowa yaji kamar iska ta tsaya. Amal ta yi shahada a ranta sannan ta tsaya tana kallon Maleekh kai tsaye. Idonta ya cika da hawaye, muryarta ta karye tana cewa: “Na zo… don na ga halin da kake ciki Ya Maleekh. Na kasa jurewa na zauna a gida ban san ya kake ba, ban damu da me za ku faɗa ba. Ka yafe mun, idan ka tsane ni, to ka tsane ni da gaskiya, amma kar ka barni cikin duhu ina ƙiran sunanka babu amsa…” Hawayenta ya zubo, ta durƙusa a ƙasa...Tana kuka. ⚡ Reaction in the Room Ammy ta miƙe da sauri ta ce cikin ɗaga murya: “Subhanallah! Daman wannan ce aka bari ta shigo cikin falona? Wane irin sakaci ne wannan? Amal! Kina da bakin dawowa nan bayan abinda kika aikata?!” Farha ta ɗora da muryar kuka da nufin jin tausayinta: “Yaya Maleekh, ka ga dai ni da gaske nake tare da kai, amma wannan yarinyar da kake biye mata har yanzu tana neman ta zame maka illah!” Abba ya ɗaga hannunsa yana cewa: “Ku nutsu! Bari muji dalilin zuwanta.” Maleekh bai iya magana ba, ya lumshe ido hawaye suna taruwa, yana jin zuciyarsa na bugawa cikin ciwo da rauni. Islam ce ta kalli Amal da idon tausayi,sannan ta miƙe ta je yanda take, ta ɗago tare da shigo da ita ciki, ta zaunar da ita, ta ce a hankali: “Ki zauna, Amal… ki faɗi abinda ya kawo ki.” Abba ya ɗago ido da mamaki yana kallon Amal. Ya yi ƙoƙarin tuna inda ya taɓa ganin wannan fuskar sai nan da nan ya tuna. Da mamaki, cikin muryarsa mai cike da natsuwa ya ce: “Daman kece yarinyar da ake ta cece-ku-ce akai? Ba ke bace muka haɗu a asibiti lokacin da kika buge min takardu?..” Amal ta share hawayenta tana girgiza kai cikin rawar murya ta ce: “Ni ce… ni ce...” Ita ma tayi mamakin ganin cewa wannan mutumin kirki da ya ba ta shawara a asibiti, shi ne mahaifin Maleekh! Islam ta ji jikinta ya motsa da tausayi... Ammy da Farha kuwa, kamar za su fashe da kuka tsabar takaici. Farha ta ƙame tana cije leɓenta, idonta na kan Amal kamar zata huda ta da kallo. Ammy kuwa buge cinyarta tayi tana huci a zuciya, amma ta yi shiru don ganin halin da Maleekh yake... Arfat kuwa ta maida hankali kan wayarta, zuciyarta cike da ƙin shiga rigimar nan. Tunaninta ya dawo lokacin da Maleekh ya mareta ya kuma sumar da ita, alkawarin da ta ɗauka a ranta: “ba zan sake tsoma baki a wannan shirgi ba.” Falonnan ya ɗauki wani irin nauyi na shiru kafin Maleekh, wanda yake jingine da kujera ya juyo cikin baƙin ciki, muryarsa cike da rauni a fusace ya ce: “Me ya kawo ki nan?” Amal ta durƙusa a gaban shi, hawaye na zuba, zuciyarta na rawa ta ce: “Na zo ne don na roƙe ka. Ka yafe min Ya Maleekh. Wallahi ba ni da masaniya akan abinda ake zargina da shi. Don Allah ka daina zargina da abinda ban sani ba!” Maleekh ya ɗaga murya cikin tsawa mai ƙarfi har kowa a falo ya tsaya suna tsoron kada ciwon ya motsa. “Wani irin zargi Amal?! Doctor ya tabbatar da komai da idona! Kuma kina ce magana akan zargi?!” Abba ya ɗan motsa da damuwa, zuciyarsa na tsoro kada wannan tashin hankali ya ƙara jefa ɗansa cikin ciwon zuciya, musamman da Doctor ya ja musu kunne akan kada su tada hankalinsa. Amal cikin kuka, jikinta na rawa, ta ce: “To kazo muje a ƙara gwadawa… wallahi zaka tabbatar da gaskiyata!” Maleekh ya girgiza kai, muryarsa mai tsanani ta sauya zuwa takaici: “Ban da lokacin ki, Amal. Ki fita daga cikin rayuwata!” Amal ta zuba masa ido, zuciyarta na tafarfasa ta ce: “Yanzu kana nufin baka sona?…” A fusace ya ce: “Bana sonki, Amal!” Hawayenta ya zubo sosai. Ta matso kusa da shi da rawar murya: “Ka taimaki rayuwata, kada ka faɗi wannan kalmar, Ya Maleekh…” A nan kuwa, Maleekh ya miƙe tsaye da hanzari, zuciyarsa na tafasa. Ya kamo hannun Farha ya ɗaga ta tsaye, ya dafa kafaɗarta yana kallon Amal da idanu masu cike da hawaye ya ce: “Kin ga Farhat? Ita ce wacce zan aura! Ita nake so yanzu. Ke, ki fita daga rayuwata!” Amal ta yi ƙoƙarin miƙewa amma ta kasa, ta durƙusa tana kuka mai ƙarfi. Maleekh ne ya ɗaga murya cikin tsawa ya ce: “I SAID GET OUT!” Amal ta ɗaga idonta cikin hawaye ta ce da ƙarfi: “I will not go anywhere, my bee!” Zuciyarsa ta ƙara karye wa, a fusace ya ce: “I’m not your bee! Sunana Maleekh. Kuma daga yau bana son jin sunanki!” Ya ɗago Amal da ƙarfi, ya ja ta da hanzari zuwa bakin ƙofar falo. Kowa na kallo cikin razana amma babu wanda ya iya yin magana. Har suka fito bakin get, ya tura ta waje da ƙarfi sannan ya juya ya bar ta a can, ya koma ciki da numfashi mai nauyi. Ya shige falon ba tare da ya yi magana da kowa ba, ya haura sama zuwa ɗakinsa. Falon ya dawo da wani irin shiru. Farha kuwa, zuciyarta ta cika da farin ciki yau dai Maleekh ya bayyana ta a matsayin wacce yake so. Abba ya sauƙe ajiyar zuciya, Islam ta ji zuciyarta na karyewa saboda tausayin Amal. Ammy kuwa ta sake haɗe fuska cikin jin daɗin ganin abin da ta jima tana jira ya faru.... Abbah shima tashi ya yi tare da haurawa saman ɗakin Maleekh.... TO PAH AUNTY HABIBA ABIN DA KIKE JIRA YA FARU, FATANKI MALEEKH YA ƊAUKI FANSA AKAN ABIN DA AMAL TAYI MASA A KADUNA TO GA SHI.... AUNTY KHADIJA AFUWAN FA, DAUGHTER KI TA SHIGA TSAKA DA SOYAYYA, HAR TANA SHIRIN MAKANCE WA...SAI KIN TAYA TA DA ADDU'A.... asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 45 to 46 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Bayan Maleekh ya haura sama, falon ya ɗauki wani irin shiru. Kowa na jin sautin bugun zuciyarsa. Ammy ce ta fara sauƙe ajiyar zuciya tana murmushi cikin jin nasara. Ammy ta juyo tana kallon Farha, murmushi mai nuna ƙwarin gwiwa na yawo a fuskarta: “Kin gani ko Farha? Kin gani yadda ɗana ya nuna a fili cewa ke ce ƙaunarsa? Wannan ita ce amsawar addu’ata, yau Amal ta sha kashi.” Farha tana jin daɗi sosai har hawaye suka cika idonta, ta ce cikin shagwaɓa: “Ammy, wallahi burina ya cika yau. Ganin yanda ya ɗaga hannuna a gabanta ya ce ni zai aura, na ji kamar zuciyata ta gama samun natsuwa. Yaya Maleekh ya zama nawa.” Islam kuwa ta ɗan zura musu ido, sai ta girgiza kai kawai ta juya gefe tana murmushi mai zurfi. Ba don farin ciki da su ba, sai don ta san labarin zai ɗauki sabon salo. Ammy ta sake cewa da farin ciki: “Kina ji ba, ki ƙara samun nutsuwa yanzu. Ki kula da shi sosai. Ki nuna masa soyayya da kulawa. Amal ta gama, ta fita daga jerin waɗanda za su taɓa rayuwarsa.” Farha ta yi dariya mai sauƙi, ta jingina da kujera tana share hawayen farin ciki. Arfat kuwa ta ci gaba da latsa waya kamar ba komai ya faru ba, tana jin haushin wulakancin da Maleekh ya mata kwanaki, shiyasa ta fi son zaman shiru ba tare da ta nuna tausayin Amal ba. 🕊 A gefe guda kuma, Abba ya bi bayan ɗansa kai tsaye zuwa part ɗinsa. Yana tafiya a hankali, cikin tunanin yadda zai rarrashe shi ba tare da ya sake tada masa hankalin da zai iya shafar lafiyarsa ba. Da ya shiga ɗakin, ya tarar da Maleekh zaune a gefen gado, kansa a jingine, hannunsa na rufe da fuska. Idanuwansa sun cika da hawaye amma ya daure ya maida su ciki. Abba ya ƙarasa a hankali ya zauna kusa da shi, ya dafa kafaɗarsa cikin lallashi kamar yadda ake yi wa jariri: “Maleekh ɗana… ka kwantar da hankalinka. Kada ka bari wannan abun ya shafi lafiyarka. Na ji zafin abinda ya faru, amma dole ka tuna da nasihohin likita.” Maleekh ya ɗago idonsa da suka yi ja saboda hawaye, ya ce cikin murya mai cike da raɗaɗi: “Abba, ta ya zan iya? Na ba Amal zuciyata gaba ɗaya, amma ga sakamakon da ta bani. Abun da ya fi mutuwa ciwo, shi ne a ce wanda kake so ya ci amanarka…” Abba ya yi shiru, ya dafa hannunsa yana girgiza kai cikin tausayi. “Na fahimta, ɗana. Amma rayuwa haka take. Wani lokacin abin da muke buri ba shi ne ƙaddarar mu ba. Idan har Amal ba ta dace da kai ba, Allah zai baka wacce ta fi zama alheri gare ka.” Maleekh ya sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi, ya jingina da gado yana ƙoƙarin danne kukan da ke son subucewa. A bakin get ɗin gidan, Amal ta tsaya cak, idonta cike da hawaye, zuciyarta na bugawa kamar za ta faso kirjinta. Kamar yadda aka jefo ta haka ta tsaya kamar gawa a tsaye. Motarta na tsaye a gefen titi, amma ƙafafunta sun kasa motsi. Hannayenta biyu ta dafe kirjinta tana kuka mai ciwo: “Ya Allah… me yasa Ya Maleekh zai furta haka? Bana da wani laifi… me yasa duniya ta haɗa kai akaina haka?” Jikinta ya gama yin sanyi da haka ta ƙarisa bakin titi, ƙafafunta sun karye, ta sulale ta zauna a ƙasa, tana kuka cikin karyewar zuciya.. Wani security ne ya matsa kusa yana ce mata cikin muryar tausayi: “Haba Madam, ki shiga mota, kar ki zauna haka a titi…” Amal ta ɗago ido cikin hawaye ta ce da murya mai rauni: “Shi ne rayuwata… idan ya ce baya sona, wace riba zan samu da wannan rayuwar?” Girgiza kai Security yayi cikin tausayawa sannan ya koma bakin aikinsa... Zama ta ci gaba da yi a bakin titi ta haɗe kai da gwiwa tana kuka mai cin rai... Ta ɗau lokaci tana zaune ita kaɗai tasan mai yake mata ciwo a ranta, tana cikin wannan halin sai ta ga an miƙo mata farin handkerchief, ba tare da ta ɗago ta ga waye ba ta karɓa tana goge fuskarta da ya ji'ke da hawaye, sannan ta saita hancinta ta faco majina tana dunƙule handkerchief a hannunta, jin wani irin bugun turaren da yake dukan hancinta ne yasa ta ɗago a slow tana kallon gefen da aka miƙo mata handkerchief, a zabure ta ja gefe tana kallon fuskar mutumin cikin rashin sanin waye... Durƙusa wa ya yi a gabanta yana ƙare ta da kallo, sannan ya ce "Sannu koh.." Amal dai ba tare da tayi magana sai idon da take binsa da shi.. A hankali ya furta: "Sunana Zayd, ni ba'ko ne a wannan ƙasar duk da ƙasata ce amma tsawon shekaru domin tin ina ƙaramin yaro na bar ƙasar... yanzun ma na zo gudanar da wani aiki ne, ina tunanin na dawo domin ci gaba da aiki a nan ƙasar, fatan za ku karɓe ni hannu bibbiyu..." Amal dai ga abin da yake damun ta amma yazo yana cikata da surutu, a hankali ta juyar da eyes ɗinta gefe alamun 'bai shafe ta ba...' Zayd ya ci gaba da cewa "Kiyi haƙuri na ga kina cikin damuwa, shin zan iya sanin damuwar ki, ko zan iya taimaka miki?..' Sai a lokacin Amal tayi magana tare da faɗin "A'a damuwata bai shafeka ba, sirrin zuciya na ne..." Zayd ya ja numfashi sannan ya ce: "Amma bana jin daɗin ganin kyawawan mata irin ku suna kuka, shin daman ana sanya kyawawan mata kuka anan Nigeria ne? mu a can kyawawan mata lalla6a su muke..." Amal tana kallonsa ta ce "Munanan mata fa?..." Ɗan sosa sumar kansa yayi cikin murmushi ya ce "I means duk mata, ina daraja mata gaba ɗaya...domin mata iyayenmu ne.." Amal ta sake juyar da eyes ɗinta gefe tare da faɗin "Da kyauuu..." Zayd ya lumshe eyes ɗinsa sannan ya ce "Amm dan Allah ki daina sa damuwa a ranki, yanzu ba wani wadataccen lafiya muke da shi ba, abu kaɗan sai ki ji ciwo ya shige mu..bazan so wani abu ya same ki ba.." Amal ta ce "Meyasa?..." Ya ce "No domin bama son mu rinƙa rasa kyawawan mata a duniya.." Amal ta miƙe tare da faɗin "OK thanks..." Ya dube ta da kyau sannan ya ce "Kamar ba kiyi farin cikin ganina ba.." Amal tayi dariyar da ya kawatar da fuskarta har sai da Zayd ya lumshe ido yana kallon kyakkyawan fuskarta duk da yayi ja tsabar kuka....Wani irin lotsatstsen dimples ne yake lotse wa akan fuskarta tana kallon Zayd ta ce "Shin wurina kazo ne da kake batun kamar banji daɗin zuwanka ba..." Zayd yana murmushi shima ya ce "Nigeria na zo kuma kina cikinta.." Amal ta ce "OK thanks ni zan wuce.." Zayd ne ya miƙa mata hannu akan suyi musabaha.. Amal hararar hannun tayi ta kuma cewa. "Thanks..." Ta buɗe murfin motarta ta shige tana ƙoƙarin ta da engine motar... Jikinta gaba ɗaya ya haɗe da gumi saboda tashin hankali. Idanunta sun kumbura, muryarta ta dusashe a cikin ranta take faɗin. “Ya Maleekh… ko da ka kore ni… wallahi sai na ci gaba da addu’a don ka dawo cikin rayuwata. Ina sonka fiye da yadda nake son numfashina…” Ta jingina kanta da sitiyari, tana kuka mai ban tausayi. Tayi ƙoƙarin tada motar amma hannunta na rawa. Sai ta runtse ido tana roƙon Allah: “Allah, kar ka barni cikin wannan ƙunci. Ka ba ni haƙuri da ƙarfin zuciya… idan kuwa ƙaddarata ce in rayu da shi, to ka dawo da shi cikin rayuwata.” Bata ankara ba ta ji ana knocking ɗin glass ɗin motar, a zabure ta kalle shi ita har ta manta da yana wurin... Zayd ya tsaya a glass ɗin motar da cewa. "Na ga kamar you are so weak, shin zan iya kai ki yanda zaki je?..." Amal ta dube shi sannan ta ce "Thanks.." daidai lokacin da ta tada motar, a ɗari tabar wurin... Motar ta fara tafiya amma zuciyar Amal ta rage masa nisan tafiya domin kalaman Maleekh suna maimaituwa a kunnen ta kamar ana kunna waƙa mai ciwo. Shi kuwa tsaya bin bayan motar ya yi da kallo yana murmushi...daga bisani ya shiga ƙaton motarsa ya nufi get ɗin gidansu Maleekh... Yana zuwa security suka dube shi sannan suka buɗe masa ya shige ciki already sun san da zuwansa.... A falo ya tarar da iyalan gidan... Ammy, Islam, Arfat, da Farha.. Yana tarar da su ya ce "Hellooo my families..." Wani irin tsalle Farha ta buga tare da nufansa da gudun gaske tana faɗin: "Ya'yaanaaaaaa...." Tayi tsalle ta kamo wuyansa ta d'ale shi cikin farin ciki.. Shima rungumarta ya yi yana ɗauke da ita, yana faɗin. "Oyoyo my beautiful lady sister.." Duk sauran miƙe wa suka yi cikin farin ciki.. Islam da Arfat su ma zuwa suka yi suka rungume shi su na masa "your welcome.." Zayd ya nufi Ammy ya gaisheta. Cikin farin ciki ta amsa masa tare da faɗin "Sannu da zuwa Zayd, tin ɗazu muke ta duban ka sai yanzu..." Zayd ya ce: "Wallahi Ammy kaya ne suka tsayar da ni.." Ammy ta ce "Ayyah ai da kayi waya, ai da anje an taryeka a Airport ai..." Zayd ya ce "Kawai bana son wahalar da ku ne..." Daga baya Zayd ya tambayi Ammy cewa: "Ina mutumin ne kam?.." Ammy ta ce. "Yana ciki can part ɗinsa..." Zayd yana dariya ya ce "Ni gaba ɗaya gidan ya rikice mun, bana gane ko ina.." Ammy itama dariya tayi tare da faɗin. "Ai dole rabonka da nan Nigeria tin kana shekara goma fa, lokacin ba'a yaye Islam daga nono ba..." Islam kawar da kai tayi gefe cikin jin kunya..." Ga Arfat Auta ba'a haifeta bama... Zayd yana murmushi ya ce. "OK wani yamun escort zuwa part ɗinsa kar na ɓata..." Duk suka yi dariya. Farha ta ce: "To mu je na rakaka Yaya.." Ammy tayi saurin cewa: "A'a ki bar shi, bari Islam ta raka shi..." Farha dakatawa tayi tana kallon Ammy da murmushi daman wannan rana Ammy take jira, Allah ya kawo Zayd ta daidaita soyayya tsakaninsa da Islam... Islam kallon Ammy tayi tana shirin yin magana, Ammy ta hankad’a ta gaba tana faɗin. "Je ki! Je ki!!..." Islam ba yanda ta iya haka ta sa Zayd a gaba zata kai shi part ɗin Maleekh.... Farha cikin shagwaɓa ta ce. "Ammy nima dai ina son ganin Ya Maleekh ne dai..." Ammy ta ce "Ki bari daga baya kya gan shi, tin da kuna tare yanzu..." ☆☆☆☆ Abbah yana zaune a bakin gadon da Maleekh yake zaune shima, sun jeru kamar masu hira... Abba ne yake ta bashi haƙuri akan ya daina sa damuwa a ransa yanzu, sannan ya daina gaggawar ɗaukan hukunci.... Abbah ya ce "Maleekh na ga tsantsar soyayya a idon wannan yarinya, dan Allah ka tsaya kayi bincike sosai kafin ka yanke hukunci, kallo ɗaya nayi wa wannan yarinyar na fahimci cewa bazata taɓa aikata abinda ake zarginta akai ba, naga nutsuwa a tattare da ita..." Maleekh ya ce "Abbah please ni yanzu bana son jin maganarta, zan yi abin da ya kamata idan na nutsu..." Su na cikin wannan halin sai suka ji knocking... Abbah ne ya bata izinin shigo wa.. A falon ɗakin suka ji sallamar Islam.. Abbah ne ya yi magana da cewa: "Ya akayi ne shigo ciki mana.." Islam ta ƙara yin sallama sannan ta buɗe ƙofar bedroom ta shigo, a bayanta kuwa Zayd ne yake biye da ita... Abbah ganin Zayd yasa shi faɗin. "Ha'a yau babban ba'ko muka yi ne?.." Zayd yana dariya ya durƙusa yana gaishe da Abbah.. Abbah ya amsa cikin nutsuwa sannan ya tashi ya yabar musu ɗakin...domin yasan Maleekh da Zayd manyan abokai ne... Maleekh miƙe wa yayi yana murmushi suka rungumi juna....Zayd ya bubbuga bayansa tare da faɗin: "Man ya jikin nakan, naji ance ka haɗu da break heart..." Maleekh jin haka yasa ya harare shi ya zauna a bakin gadon.. Islam kuwa sallama tayi musu sannan itama ta fita... Idon Zayd ne ya sauƙa akan wani glass pictures na yara biyu suna rungume da juna.. Murmushi ya yi tare da ɗauka yana duba wa... "Har yanzu ka kasa cire Baby a ranka..." Maleekh ya ce yana kallon hoton hannun Zayd. "Da ba dan rasata da nayi ba, da babu wani heart break da zan fiskanta...A yanzu zan ci gaba da jiran fiance ɗina..." Zayd ya ce "Idan kuma ta mutu fa?.." A zabure Maleekh ya kalle shi tare da girgiza kai yana faɗin "Kar ka sake faɗin haka..." Zayd ya ce. "Kana hauka ne? amma kowa yasan cewa ita da iyayenta sun mutu sakamakon gobarar wuta da aka dasa musu.." Maleekh a hankali ya furta. "Idan iyayenta sun mutu to ita tana raye kuma zan ci gaba da jiranta.."... ☆☆☆☆ Da ƙyar Amal take tuƙi, hawaye na zuba kamar ruwan sama. Gaba ɗaya titin da take bi sai ya rikice mata a ido. Sau biyu tana kusan yin karo da mota saboda tsananin tunanin da ya mamaye ta. “Ya Allah… me yasa rayuwata ta zama haka? Na rasa wanda zuciyata take so… Na rasa farin cikina gaba ɗaya…” Ta dafe kirjinta, tana jin kamar zuciyarta ta tsinke gida biyu. Duk inda ta dubi gilashin mota, a madubin gaba sai ta hango fuskar Maleekh. Idanunsa masu ƙarfi, muryarsa mai dukan zuciya, da kalmomin da suka fi kowane makami ciwo: _*“Bana sonki, Amal… bana sonki.”*_ “Ya Maleekh…” ta furta da rawar murya. “Wallahi ban aikata laifin da ake zargina ba. Na rantse da Allah kai kaɗai nake so. Na rantse da Allah kai ne numfashina. Ka yarda da ni, My Bee… kada ka ƙi ni haka.” Sai hawaye suka sake zuba sosai. Ta tsaya gefe da hanya ta jingina kanta da sitiyari tana kuka kamar wata ƙaramar yarinya... A zuciyarta tana addu’a: “Ya Allah, idan ina tare da gaskiya, idan ina son shi da zuciya ɗaya, ka dawo min da shi. Kada ka bar soyayyarmu ta mutu haka kawai. Ka tsare shi da cuta, ka tsare shi da mugunta… ka shiryar da zuciyarsa gare ni.” Numfashinta ya yi nauyi, amma har yanzu zuciyarta na ambaton sunansa: _“Maleekh… Ya Maleekh…”_ ______________________________________ Maleekh yana zaune a gadon sa yana jingine da pillow, idanunsa na kallon Zayd wanda ke zaune a gefen gado da murmushin nishaɗi a fuska. Zayd ya gyara zama ya ce: “Bros, wallahi yau a zuwana gidan nan na haɗu da wata pretty yarinya… gaskiya ta kwanto min a rai sosai. Amma fa tana da ɗan jiji da kai, duk da haka babu matsala, soyayyata zata sauƙe mata wannan girman kan.” Maleekh ya ɗan ɗago ido ya kalle shi, sai kawai ya yi murmushi mai rauni sannan ya ce: “So cute, na tayaka murna.” Zayd ya girgiza kai yana dariya: “Hmm, Bros, kai da kanka ka san idan Zayd ya fara, to babu gudu babu ja da baya.” Maleekh ya ce cikin dariyar dole: “Ni dai ina fatan kada ta kawo maka wahala.” Zayd ya lumshe ido ya ce cikin salo: “Amma ka san wani abu? Na yi big mistake wallahi. Ban tambayi sunanta ba, ban kuma karɓi address ɗinta ba. Kuma a lokacin ma she is so weak… kamar mai ciwo.” Maleekh ya yi dariya kaɗan, yana kallon shi da murmushin tausayi: “To sai ka yi searching ɗinta a zuciya, ko? In ka ci gaba da yi mata addu’a za ku haɗu da ita in Allah ya so.” Suka yi dariya duka. Sai Zayd ya matsa kusa da shi ya ce: “Amma fa Bros, sai ka daure. Na san kana da wani abu a zuciya, amma ina maka addu’a zaka samu nutsuwa. Kai fa ba kawai yayana ba ne kai ne abokin rayuwata. Duk ciwonka, duk damuwarka, ina tare da kai har ƙarshe.” Maleekh ya ɗan rufe ido, zuciyarsa ta yi nauyi. Amma saboda ƙoƙarin kada ya nuna raɗaɗinsa, ya ce cikin murmushi: “Na gode, Zayd. Allah ya saka da alheri. Kai kaɗai ne kake bani nishaɗi a wannan lokacin.” Zayd ya bubbuga kafaɗarsa yana dariya: “To ai ba komai ba. Ni dai na ce maka ka shirya, very soon zan zo maka da labarin soyayya irin ta film. Ka ga na fi ka nasara kenan.” Duka suka sa dariya.... dariya mai saurin yankewa daga gefen zuciyar Maleekh saboda ciwon da yake boyewa. Bayan dariyar ta ɗan lafa, Zayd ya tashi daga gefen gadon ya ce: “Ni dai zan je in huta. Amma Bros, ka kwanta ka cire damuwa daga ranka. Komai zai daidaita da izinin Allah.” Maleekh ya yi ƙoƙarin mayar da murmushi: “Na gode sosai, Zayd. Allah ya sa ka samu farin cikin da kake nema.” Zayd ya yi masa _thumbs up_ ya fice daga ɗakin cikin nishaɗi. Maleekh ya zauna a gefen gadon na ɗan lokaci, hannunsa yana shafa hoton da yake a gefen bedside table. Wani irin numfashi ya sauƙe, ya kwanta da baya ya rufe idanunsa. Amma duk da ƙoƙarinsa, hoton Amal ya bayyana cikin zuciyarsa kamar tana tsaye a gabansa. Kukan da ya ji daga gare ta a falon gida, hawaye a fuskarta, da muryarta tana ƙiran sunansa duk suka sake dawo masa. Ya rufe fuska da hannayensa yana ambaton: “Ya Allah… me yasa har yanzu zuciyata ta kasa daina ji da ita?..” Wani irin raɗaɗi ya shige shi, amma duk da haka ya danne shi, yana son ya nuna ƙarfin hali gaban kowa. Sai dai a zuciya, ya san ciwon Amal ba zai bace masa da sauƙi ba. ____________________________________ A wannan daren... Amal tana kwance kan gadonta, ƙwance cikin duhu, idanunta suna kallo ceiling ɗin ɗakin amma zuciyarta ta kasa samun nutsuwa. Ta juyo gefe tana riƙe da pillow kamar zata matse shi. Hawaye suka zubo a kuncinta tana faɗin cikin rauni: “Maleekh… duk duniya babu wanda na so kamar kai. Ko da baka yarda dani ba, ni nasan gaskiya zata bayyana wata rana…” Ta runtse idanu tana ƙoƙarin yin bacci, amma duk lokacin da ta lumshe ido, hoton Maleekh ne yake bayyana, yana mata tsawa da maganarsa mai ciwo. Sai kawai ta yi shahada a hankali, tana roƙon Allah ya ba ta ƙarfin zuciya: “Allah ka bani haƙuri da ƙarfin zuciya akan wannan jarabawa…” Ta zauna bakin gado tana kallon taga, tana jin wani irin ƙarfi a zuciyarta cewa ko da Maleekh ya ƙi ta, ta tabbata ba haka zuciyarsa take ji ba. _WASHEGARI_ Da safe suna zaune tare a dining area, an shirya breakfast. Zayd yana cin toast yana kallon Maleekh cikin annashuwa ya ce: “Bros, shin wani matsayi za’a bani a cikin company ɗinka?..” Maleekh ya ɗan ɗaga kai daga coffee cup ɗinsa, ya girgiza kai tare da faɗin: “Zan iya faɗa maka Zayd, amma ka bari mu je muji daga bakin board kafin a sanar maka matsayi.” Zayd ya lumshe idanu yana murmushi ya ce: “Gaskiya fa, ina so ace an bani matsayin assistant ɗinka. Ka san muna tare a koda yaushe.” Ƙaramin murmushi ya bayyana saman fuskar Maleekh sannan ya ce: “Akwai wacce take kan wannan matsayi. Ban yarda da cire wanda yake kan mukaminsa kawai don wani ya shigo ba. Abin da ya dace shine, zan baka matsayin da ya yi daidai da kwarewarka. Duk wanda yake matsayin assistant burinsa shine ya haura gaba, ba ya tsaya nan ba.” Zayd ya ɗan saki baki cikin rashin fahimta ya ce: “Oh, kenan ban dace da matsayin ba?..” Maleekh ya ɗago idonsa ya kalle shi da nutsuwa ya ce: “Ba haka nake nufi ba. Zayd, adalci ne yafi komai. Idan na sauƙe wacce take assistant ɗina kawai saboda kai, ai na zalunce ta. Ina fatan zaka fahimce ni.” Zayd ya lumshe ido cikin murmushi ya ce: “Shikenan, no problem. Na yarda da kai.” A haka suka gama breakfast ɗin suka nufi company ɗin tare... _Campany_ Yayin da suka shigo cikin babban reception ɗin, ma’aikata suka fara gaishe da Maleekh da girmamawa. A nan suka tsaya kafin su nufi sama, sai kawai ƙofar glass ta buɗe. Amal ce ta shigo cikin tsararren kaya, tayi dressing cikin class, high heels ɗinta na danna tiles ɗin ƙasa tana tafiya cikin ƙasaita. Duk wajen ya ɗan tsaya cak. Zayd ne ya fara hangen ta, ya yi ido huɗu da ita. Ya buɗe baki yana cewa cikin farin ciki: “Wowww… Allah ya sake haɗa mu, my beautiful pretty!” Duk reception suka juyo da kallon mamaki, suna kallon Amal da Zayd. A hankali Maleekh ya juya kansa saboda jin yanda Zayd ya ƙira pretty. Idonsa ya sauƙa kan Amal, zuciyarsa ta buga da ƙarfi! Ya dunƙule hannunsa da ƙarfi tare da haɗiyar yawu... Amal ta tsaya cak, idonta akan Maleekh, jikinta yana rawa da tsoro. Maleekh ya ɗan jinjina kai da ƙarfi, yana murza yatsansa cikin tafin hannu, sannan cikin nutsuwa ya ce da karfin zuciya: “Fatan alkhairi…” Ya nufi escalator..Yana zuwa ya ɗaga ƙafarsa ya hau escalator, amma idanunsa suna kan Amal har sai da ya haura. Amal itama idonta akan sa har sai da ya ɓacewa gani. Zayd yana nan tsaye kamar wanda ya ci jackpot, yana murmushi ya ce da Amal: “Pretty, ke ma a nan company kike aiki? Alhamdulillah! Wannan babban alheri ne. Ni ma yau zan fara aiki anan. Kinga yanzu za mu zama ɗaya kullum…” Amal bata ko kalleshi ba, kawai ta ratsa gefensa cikin isa, ta nufi elevator. PA ɗin Maleekh dake tsaye a reception ya yi murmushi ya ce wa Zayd: “Your welcome sir. Waccan ce assistant CEO ɗin company.” Idon Zayd ya buɗe da mamaki ya ce: “What! Assistant CEO? She?…” Kafin ya gama, Amal ta shige elevator. Da sauri Zayd ya nufi wurin yana cewa: “Wait, pretty! Ki jira mana please!” Amma elevator ɗin ya rufe a gabansa, Amal ta tafi sama ta barshi tsaye a ƙasa yana ƙoƙarin numfasawa da murmushi marar dalili... A wannan rana haka Zayd yake ta shishshige wa Amal. Zayd ya ci gaba da zagaye Amal a cikin company... Ko da break-time sai ka ganshi ya shigo office ɗinta da excuse: “Pretty, kin ci lunch kuwa?..." Anjuma kaɗan sai ya dawo ya ce "Pretty, kin huta kuwa?.." Bayan wasu ƴan mintuna sai ya sake dawowa Ya ce "Pretty, kin sha ruwa kuwa?”.. Duk da Amal tana ƙoƙarin sharar da shi da kakkaucewa, Zayd ya kasa nisanta daga gare ta... Ba yanda ta iya haka take biye shi suna fita tare da sauran staff, yana yi mata hira da dariya. Duk wanda ya gansu zai ce soyayya ce mai tasowa... Amma Amal a ranta tana jin nauyi, tana jin ba komai bane idan ba da Maleekh ba…. A gefe kuwa, Maleekh shiru yake. Duk lokacin da ya hango Zayd yana yi wa Amal hira, idonsa na canzawa. Yana jin zafi a zuciyarsa amma baya nuna komai. Kishi na cin ransa, amma sai ya dake, yana bawa kansa hujja: “Ba ni da masoyiya, na sallame ta, so… me yasa kike jin zafi Maleekh?” ☆☆☆☆☆ Two days after Zayd started working at the company…. Wata rana, bayan aiki, Amal ce ta ɗauki babban fayil ɗin takardu. Su ne takardun da Maleekh bai samu damar dubawa ba lokacin da yake jinya. Ita ce assistant, dole ta kai masa domin ya sanya hannu kafin ranar ƙarshe. Tana shiga cikin office ɗin sa. Ƙamshin turarensa ya buga mata kai. Maleekh yana zaune shi kaɗai, ya jingina a kujerarsa, hannunsa riƙe da pen yana rubuce-rubuce. “Excuse me, sir…” Amal ta furta a hankali, zuciyarta na tsalle-tsalle. Ya ɗago idonsa, suka yi ido huɗu. Zuciyarsa ta buga, amma bai nuna ba. “Zo,” kawai ya ce da muryar kasaita. Ta matsa kusa da desk ɗinsa, ta aje fayil ɗin. “Wannan su ne takardun da ba a duba ba lokacin da kake jinya. Na yi reviewing, sai ka sanya hannu.” Ya ɗauki pen ɗinsa, ya fara dubawa. Amal ta tsaya a tsaye tana kallon gefe, zuciyarta na rawa. Duk da ita ce assistant ɗinsa yanzu, ba zai taɓa sauƙin kasancewa da shi cikin ɗaki guda ba. Shiru ya mamaye office ɗin, sai ƙarar bugun zuciyoyinsu da suke jin shi su kaɗai. Bayan ɗan lokaci ya ɗago ya ce da muryar nutsuwa: “Na gode da kula da company lokacin da ban samu dama ba.” Amal ta ɗan runtse ido, ta ce cikin sanyin murya: “It’s my duty, sir.” Suka yi shiru. Takardun suka koma magana tsakanin su. Babu wata hirar soyayya. Babu wata rigima. Sai dai ƙirji biyu suna bugawa cikin ciwo da sha’awar da suke ɓoyewa. Amal tana tsaye a gaban desk, tana nuna wa Maleekh inda zai sanya hannu a cikin fayil. Shi kuma yana kallon takardu, sai lokaci-lokaci idanunsa su kai kanta, sannan ya ɗan janye kai kamar bai kula ba. Shiru ya rufe office ɗin, bugun zuciyoyinsu na ci gaba da daɗa karfi. Kawai aka buɗe ƙofa, Zayd ya shigo da murmushi a fuskarsa.. “Prettyyy! Ashe kina nan…” ya faɗa yana matsowa cikin sanyi. Amal ta juyo da sauri, idanunta suka firgita. “Zayd… kai fa…” Maleekh kuwa ya ɗago daga rubutunsa, ya kalle shi da idon da ba a iya fassara ba. Idonsa cike da kishi da takaici, amma fuskarsa na ɗauke da ɗan murmushin da ya fi zafi fiye da faɗa. Zayd bai damu ba, ya ƙarasa gaban Amal, har yana ƙoƙarin kai hannu zai ɗauki fayil daga hannunta..Yana cewa “Kin wahala fa Pretty. Ina gaya miki, idan kin gaji da yawa sai ki bar sauran a hannuna.” Amal ta janye hannunta da sauri, ta ɗan ɗaure fuska sannan ta ce: “Ba sai haka ba, Zayd. Ina yi ne saboda aikin company.” Maleekh ya jingina da kujerarsa baya, ya ɗau pen ya fara jujjuyawa a yatsansa.. Da wata muryar ƙasaita mai sanyi amma mai tsanani, ya ce: “Mr. Zayd… wannan office ba wajen hira bane. Idan akwai aikin da ya shafe ka, zaka iya aiko da secretary ɗinka.” Shiru ya ɗan ɗauki ɗakin. Zayd ya murmusa, yana son nuna bai damu da tsawar ba ya ce: “Sorry, sir. Ni dai kawai na zo in ga Pretty—ehm… Amal ko ta gama da waɗannan takardu.” Amal ta ji kunya sosai, zuciyarta na buga wa... Maleekh kuwa idanunsa sun ƙanƙance, ya dafa desk ɗin da hannu ɗaya. Cikin natsuwa amma muryarsa ta sauya, ya ce: “From now on… babu wanda zai ƙira assistant ɗina da wani suna daban a nan cikin office.” Zayd ya ji an kulle masa baki. Amal ta kasa ɗaga kai saboda kunya da bugun zuciya. Amal jan jikinta tayi ta bar Office, Zayd ganin haka yasa shi bin bayanta yana faɗin "Ya za ki tafi ki bar ni ehhh pretty tsaya manaa..." Bayan antashi daga wurin aiki.. Amal ta fito daga building tana riƙe da jaka a hannu. Zayd ya biyo bayanta da sauri, yana ɗan tafiya da wani irin sanyi da yanga. “Pretty,” ya ƙira ta da fara’a, “nasani kin gaji sosai yau. Ki bari ni na kai ki gida da kaina a mota.” Amal ta tsaya, ta kalle shi da ɗan murmushin ladabi, sannan ta girgiza kai. “A’a, ka barshi. Zan tafi da motata. Sai gobe ka fito da wuri kar ka makara.” Zayd ya yi dariya yana jingina da jikinsa kamar wanda ya ci nasara... “To my pretty, ai ko ba komai … saboda naga wannan kyakkyawan fuskar taki zan fito da safe.” Amal ta yi shiru kawai, ta buɗe motarta ta shiga. Ta ja motarta ta tafi cikin nutsuwa. A gefe kuma… Maleekh yana cikin motarsa, hannunsa yana ta matsa sitiyarin kamar yana son ya murƙushe shi. Fuskar tasa ɗauke da murmushi marar annuri, idanunsa sun cika da wani irin haske na kishi da haushi. Ya kalli hanyar da motar Amal ta bi, zuciyarsa na karyewa da tunanin: “Tana iya yin dariya da shi… ta kyale shi yana ƙiran ta da suna da ni kaɗai na san darajarsa… amma ni na rasa komai. Na bar komai.” Bayan mintuna kaɗan, Zayd ya ƙaraso motar Maleekh da murmushi a fuskarsa. Ya buɗe ƙofar ya shiga cikin nishaɗi tare da faɗin. “Bros Maleekh! Wallahi wannan assistant ɗinka…ehm sorry—Amal—she’s so wonderful! Ka ga irin yadda take da nutsuwa? Kuma gaskiya she’s different, ba kamar sauran mata ba…” Maleekh ya ɗauke kansa daga kallonsa, ya mayar da hankalinsa kan hanya. Zayd yana ta zuba maganganu yana yaba Amal kamar wanda ya gano wani abu na musamman. Shi kuma Maleekh ba ya cewa komai. Sai dai idanunsa suna ƙara yin ja saboda haushin maganganun Zayd, zuciyarsa na ƙonewa cikin silent fire. Sai kawai ya murɗa accelerator, motar ta yi wani irin gudu kamar yana zubar da ɓacin rai cikin gudun... Zayd ya ɗan tsaya yana kallonsa, ya ce da dariya: “Bros… wai kai ba ka ganin irin yadda Amal take kyakkyawa ne? Ai ba a barta haka kawai ba.” Maleekh ya ɗan yi murmushi mai sanyi, wanda bai nuna farin ciki ba. Ya ce cikin wata murya mai sanyi da raɗa: “Ka cigaba da yaba ta, Zayd… kai dai ka tabbatar baka makara a aiki gobe ba.” Shiru ya rufe motar. Zayd bai fahimci nauyin kalaman ba, ya cigaba da hira, yayin da Maleekh zuciyarsa ke tafasa cikin silent jealousy... _AMAL_ Ta riƙe sitiyarin da hannayenta biyu kamar mai gudun kada zuciyarta ta tsinke. Tun lokacin da ta hango Maleekh a reception, har lokacin da ya haura saman escalator ba tare da ya yi mata magana ba, zuciyarta ta kasa natsuwa. “Ya kalle ni… amma ya ɗauke kai. Ya jinjina kai kamar wanda ya gama da ni. Amma shin da gaske ya gama da ni? Har yanzu idanunsa sun cika da soyayya ta… na gani, na ji. Zuciyata ta ce haka. Amma me ya sa yake ƙoƙarin nuna babu ni a ransa?” Ta hura iska mai zafi, idonta ya ɗan kaɗa da hawaye. “Wannan sabon ma'aikacin fa?, Zayd… yana ƙirana da pretty kamar yana wasa... Bai san darajar sunan pretty a zuciyar Maleekh ba. Sunan da nake adanawa cikin zuciyata a matsayin sirri na soyayya. Amma yanzu? Zai zama abin dariya ne? Maleekh ya ji? Ya ji ana ƙirana da pretty? Ya ji, na san ya ji… amma bai ce komai ba. Shiru ya fi komai ciwo.” Ta girgiza kanta da sauri tana ƙoƙarin daurewa...zuciyarta ne ya fara magana da cewa: “Amal, ki nutsu. Wannan company aikin ki ne, ba wurin soyayya ba. Ki bar komai ga Allah.” Sai ta ɗaga idonta, ta share hawayen da ya fito. Sai dai duk da haka, zuciyarta na ci gaba da bugawa da irin ƙarfi da ta fi jurewa… saboda har yanzu Maleekh ne kaɗai burinta da farin cikinta... Suna shigowa bakin ƙofar falo Farha ta nufo su da murmushi a fuskarta. Tana sanye cikin doguwar riga mai walƙiya, ta riƙe jakarta kamar wacce ta fito daga party. Da zarar ta hango Maleekh, ta miƙe da sauri ta tareshi, tana gyara gaban rigarsa tana cewa: "Sannu da dawowa Ya Maleekh, Allah ya ƙara lafiya." Maleekh ya ɗan ja gefe yana ƙoƙarin kaucewa hannunta, cikin dannewar takaicin da ke cinsa. Duk da haka, ya daure fuskarsa saboda yana jin nauyin yayanta Zayd, wanda ke tsaye a gefensa yana kallon komai. Zayd ya zaro ido tare da dariya ya ce: "Uhmm, soyayya kenan fa ta tashi. To Yaya Maleekh, kai dai ka ce zaka jira fiancé ɗinka?.." Sai ya ɗan buga kafaɗar Maleekh cikin zolaya. Farha ta yi wani irin kallo, idonta ya ƙanƙance kamar za ta cinye shi. Ta ce cikin tsawa: "Haba Yaya! Wace fiancé kuma? Karka yi wasa da irin wannan magana a gabana fa!" Zayd ya yi dariya ya ɗaga hannunsa: "Ooops, sorry sorry sorry my sweet sis. Na manta baki son irin wannan zolayar… Amma albishirinki.." Farha ta ɗan sassauta fuska, tana jinjina kai cikin jin daɗi: "Goro fari tasss, albishir ɗin me?" Zayd ya zaro idanu tare da murmushi mai ɗauke da annashuwa: "Nayi gamo da wata pretty, Farha! Wallahi in kin ganta kamar aljana tsabar kyau. Kin san irin kyawun ‘yan India? To, ta wuce su gaba ɗaya." Ya yi ƙaramar shiru kamar yana sake jin yadda Amal ta tsaya a gabansa a reception. Maleekh kuwa ya tsaya daga gefe yana kallonsa da idon da ke iya fashewa da wuta, amma ya danne komai, ya wuce da sauri ya haura sama part ɗinsa bayan ya yi gaisuwa da Ammy. Ƙannensa suka taru da murmushi suna yi masa sannu da zuwa, amma zuciyar Maleekh babu inda take sai a wajen Amal da kalaman Zayd. Ammy kuwa, jin daɗin hirar ya ɓace mata, zuciyarta ta tsinke da sauri. Ta kalli Islam da ke gefenta, tana murmushi amma a zuciyarta tana tunanin: "Wayyo Allah, wannan labarin 'pretty' bai yi min daɗi ba. Ni dai burina Islam ta zauna da Zayd, amma idan aka ce ya kama wata daban fa?.. Hmm…" A gefe kuma, Farha ta tattara baƙin cikin rashin jin daɗi, ta kalli Zayd da harara: "Yaya, wai ka haɗu da wata kuma?.." Zayd ya ɗan yi dariya mai sauti yana ɗaga hannunsa sama kamar mai rantsuwa: "Eh mana, ba wasa nake ba. In kin ganta kin ga kamar aljanar gaske ce ta bayyana.. Wallahi pretty ce, Farha." Farha ta ce tana haɗa rai: "Kai dai kawai, zan ga yadda wannan maganar ka zata ƙare."... Farha ta juyo tana kallon Ammy domin suna son haɗa soyayyar Zayd da Islam. Duk da Islam bata jin wani soyayya a ranta kuma bata san ana wannan haɗin ba... (To pah Farha, kema yaushe soyayyarki ta settling balle ku seta soyayyar wasu 🤣🤣, Su Hajiya Ammy da duk kan alamu fa Zayd ya fiki bariki..😅😅..).. To masu karatu sai NEXTTT... asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 47 to 48 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Maleekh ne ya rufe ƙofar ɗakinsa a hankali, ya jingina bayansa da ƙofar yana riƙe da kirjinsa da hannayensa biyu. Numfashinsa ya ɗauki nauyi, zuciyarsa na bugawa kamar ƙarar gangar yaƙi. Ya taka a hankali zuwa jikin gilasan window, ya zuba ido waje yana kallon sararin sama. Fitilun gari suna walƙiya amma idanunsa sun rufe da hazo na baƙin ciki. A zuciyarsa ya ce: "Zayd… pretty… Amal. Wannan sunan har yanzu ba ya barin kunnena. Ashe ita ce wacce ya haɗu da ita? Ita ce yake cewa kamar aljana tsabar kyau?.." Ya girgiza kai da ƙarfi, yana ƙoƙarin danne hawayen da suka cika idanuwansa. "Ni na furta mata bana sonta, na koreta daga rayuwata… Amma yau zuciyata ta tabbatar min ban taɓa son kowa irin ta ba. Duk da na yi ƙoƙari in kore ta daga zuciyata, amma ganin Zayd yana kiranta da pretty… Ya Allah, yaushe wannan ciwon zai daina cin raina?.." Ya tafi ya zauna a gefen gado, ya jingina kansa da tafukan hannunsa, yana ƙoƙarin hana hawayen sauƙa. Amma hawayen ya ƙi tsayawa, ya gangaro yana shigar masa da zafi kamar wuta. A wancan lokacin, ƙarar dariyar Zayd daga ƙasa ta sake taso masa a kunne, kamar an kunna masa kaset. Wannan dariyar ta cika masa zuciya da kishi da ɓacin rai. Sai kawai ya daki tebur da ƙarfi, ya furta a hankali cikin rawar murya: "Amal… pretty ɗin Zayd… wallahi wannan abu ba zai yiwu ba." Washe gari tun safe, babban harabar CashTalk Empire Holdings ta cika da ɗaukakar jama’a. An kawata wurin da flowers masu kyau, ana kunna kiɗa mai laushi a gefe. Fitilun gilasa na haskawa suna ba da hoton kamfani mai ƙima da daraja. Manyan baƙi daga ƙasashen waje sun iso cikin manyan motoci masu sheƙi. Ana tare su da farin cikin manyan jami’an company. Maleekh ya fito cikin suit baƙi da red tie da ya kara masa ƙwarin girmamawa. Fuskarshi cike take da kalar nutsuwa, ko da zuciyarsa na tafasa, bai bari kowa ya hango hakan ba. A gefe kuwa Amal ce ta biyo shi, sanye da skirt suit navy blue mai matuƙar kyau. A daidai wannan rana dukkan ma’aikata sun tabbatar da cewa ta cancanci matsayinta na assistant CEO. Duk da kalar gajiya a idanunta, kwarjini da kyan tafiyarta ya zame musu abin sha’awa. Zayd kuma cikin farin ciki yake ta shawagi a wajen, yana ɗan tsokanar Amal cikin sirrin murya: “Pretty, idan kika tsaya gefe, to kowa zai ce kina ɗauke da kyakkyawar kwalliya fiye da CEO ɗin kansa. Kar ki barni na rikice.” Amal ta dube shi da idanu masu sanyi, ta ɗan harare shi a hankali, sannan ta matsa gefe. Amma duk wanda ya kalla ya fahimci ba ta ɗaukar abin da yake cewa da muhimmanci. Maleekh da kansa ya gabatar da su a gaban baƙi: “Wannan ita ce Assistant CEO, Amal Abdulsamaad, tana kula da aikace-aikacen da ke hannun shugabanci... Wannan kuwa shine younger brother ɗina, Zayd, wanda ya dawo domin cigaba da aiki tare da mu a nan company. .” Baƙin suka yi mamaki da yabawa. Wani daga cikin su ya ce: “Wannan company tana da hazikan matasa. It’s a pride to invest here.” Ana haka aka shiga babban hall ɗin taro. Tables sun jera, projectors suna nuna hotuna da bayanan nasarorin company. Maleekh ya tsaya yana gabatar da jawabi cikin harshen Turanci, yana nuna sabbin shirye-shiryen da zasu ƙara bunƙasa hannun jari. A yayin da yake magana, idanunsa na kai ga Amal a gefe ba tare da kowa ya lura ba. Sai dai kowane lokaci idan ya hango Zayd yana yi mata magana ko murmushi, zuciyarsa ta sake yi masa raɗaɗin kishi. A ƙarshe bayan an gama taro, baƙin sun tsaya suna tattaunawa da ma’aikata daban-daban. Wani babban baƙo ya matso ya kalli Amal da murmushi sannan ya ce: “Young lady, you really impressed me. You have a bright future in this industry.” Amal ta yi murmushi cikin ladabi ta ce: “Thank you, sir.” Zayd kuwa yana tsaye a gefenta yana faɗin: “Of course sir, she is more than just impressive… she is my pretty.” Baƙon ya yi dariya, ya ɗauki abin a wasa. Amma Maleekh da ke gefe sai ya matse yatsunsa da ƙarfi, yana ɓoye zafin zuciya cikin annashuwa. An jera baƙi a babban hall, manyan keken Turawa da wasu manyan ‘yan kasuwa daga ƙasar waje suna zaune cikin nutsuwa. An yi musu hidima sosai aka jera musu juice da snacks a kan teburori masu sheƙi. Sai ga Farha ta shigo. Ta sha kwalliya fiye da yadda aka saba ganin ta, fuska ta cika da powder, jan baki ya ƙara mata ɗaukar ido, riga da siket masu sheƙi sun matse jikinta kamar yadda ta saba. Da sallama ta gaisa da baƙin, ta yi murmushin ƙarfin hali. Bata tsaya ko ina ba sai ta nufi wurin Maleekh kai tsaye ta zauna a gefensa, har ta riƙe hannunsa a gaban kowa, tana faɗin: “Na zo duba angona… Ashe kunyi manyan baƙi.” Maleekh ransa ya yi wani irin mummunan ɓaci.. Fuskarshi ta ɗan canza amma sai ya daure saboda girman taron da kuma irin mutanen da ke wajen. Ya ƙanƙance idanu yana tambayarta da ƙarfi cikin nutsuwa: “Me yasa zaki zauna kusa da ni a gaban mutane?…” Farha ta ƙyalƙyale da dariya ta ce: “Oh… kana so mu zauna kusa da juna a bayan fage ne? Don mutane kada su ganmu?” Sai ya yi mata duba mai cike da haushi, ya ce cikin jin zafi: “Wannan wani irin rashin hankali ne?” Sai wani ɗan kasuwa Bature ya dube su, ya ce da farin ciki cikin Turanci: “Wow! This must be your wife-to-be. Congratulations, Mr. Maleekh!” Farha ta yi murmushi tana washe haƙora, ta ce cikin harshen Turanci da ɗan izza: “Yes… yes, I am his wife-to-be. Don’t we look perfect together?” Kowa ya ɗan yi dariyar siyasa kawai, amma Amal da ke gefe zuciyarta kamar za ta fashe saboda kishi. Ta ji kamar ta miƙe ta gudu, amma ta daure ta cigaba da zama da kyan halinta. Sai ga Farha ta juya tana nuna Amal da yatsa a gaban baƙi: “Please… kawo mana coffee ni da mijina.” Maleekh ya dubeta da tsananin takaici. Sai ya ce: “Farha, wannan fa assistant ɗina ce, ba ‘yar aiki ba.” Farha ta kankance ido ta ce cikin raini: “Assistant ɗinka ce to… ai mai yi maka aiki ce. Don haka ita taje ta haɗa.” Baƙin suka kalli juna cikin ɗan mamaki. Maleekh ya yi shiru, zuciyarsa cike da tsawa amma saboda girman taron sai ya ce a hankali: “Ki je, tana son coffee.” Amal ta yi masa kallon da ya haɗa da zafi da kishi, ta ɗan harare shi kafin ta miƙe. Tana fita can kitchen na company ɗin, sai ga Zayd ya biyo bayanta da murmushi, yana ƙara tsokanar ta: “Pretty… ke za ki haɗa coffee? Wani kamfani na duniya zai yi sa’a idan ya samu irin assistant kamar ki. Bari na taimaka miki…” Duk da ta ƙi kula shi, sai ya rinƙa ɗan taya ta surutun ban dariya har suka haɗa coffee ɗin... Bayan Amal ta dawo, tana riƙe da tray ɗin tana tafiya a hankali ta miƙa kofin farko ga Maleekh. Shi kansa sai ya yi shiru yana kallonta kafin ya ɗauka. Sai ta miƙa na biyu ga Farha. Cikin mugunta Farha ta ɗauki kofin da zafi sosai da ta girgiza shi, sannan ta watsa tafasasshen ruwan coffee a kan hannun Amal! Amal ta saki wani irin ƙara mai tsuma rai, ta jefar da tray ɗin a ƙasi.. A zabure Maleekh ya miƙe daga kujera kamar wanda aka cusa masa wuta. Zuciyarsa ta tsaya cak. Yana faɗin: “Amallll!” Ya riƙo hannunta da sauri, ya shiga hura mata iska daga bakinsa, yana shasshafa hannun cikin firgici kamar shi aka zuba wa ruwan zafi. Gaba ɗaya ya manta wurin cike yake da mutane! Amal ma ta tsaya kallonsa, zuciyarta na bugu kamar za ta fito daga kirjinta. Sai bayan ya dawo cikin hankalinsa ya ga irin kallon da kowa ya yi musu, ya ja dogon numfashi. Nan take ya kalli Farha da fuska a haɗe, ya ce cikin tsawa: “Tashi ki koma gida… PLEASE, ki tafi!” Farha ta yi wani ɗan murmushi mai cike da raini, ta ɗan harare Amal, amma ganin fushin Maleekh sai ta turo baki ta miƙe. Sai wani daga cikin manyan baƙi ya tashi ya ce cikin Turanci: “This is a big mistake… An assistant CEO is not a servant. She should never be humiliated like this. She is equally important in this company.” Wani Bature ma ya ƙara da cewa: “If this company respects professionalism, then treat her with dignity. That’s how we trust our investment.” Gaba ɗaya hall ɗin ya yi shiru. Kowa ya san a ranar Farha ta kunyata kanta, amma Amal ta ƙara girma a idon jama’a. Maleekh ya dafe kansa da hannunsa ɗaya, yana jin tsantsar kunya da haushi. Amma zuciyarsa na yi masa magana ɗaya: “Ba zan taɓa bari a ci zarafinki ba, Amal…” Bayan taron company Ana waje suna yi wa baƙi bankwana. Zayd yana gefe da Amal, sai ya rinƙa ƙoƙarin jan hirarta. Zayd yana dariya ya ce: “Kin ga yau dai kin tabbatar da ni cewa ke pretty ce. Ko mai kika yi, kina da wani irin shine da mutane ke gani. Koda bak’i daga ƙasar waje, sun ga darajar ki. Kin ga kuwa? CEO ma bai iya kare kansa ba, sai dai ya kare ki.” Amal ta ɗan yi murmushi, ta sunkuyar da kanta cikin kunya sannan ta ce: “Zayd, don Allah ka daina irin wannan magana. Ai aikinmu ne kawai. Bana son a yi min wata fassara daban.” Sai Zayd ya girgiza kai da nishadi ya ce: “Toh ai ni gaskiya nake faɗa miki, kinga CEO Maleekh ya yi break-up da wata, shi ya faɗa min da kansa... " Amal ta ji maganar kamar an caka mata wuƙa a zuciya. Sai ta yi shiru, ta ƙara ɗauke kai gefe... Zayd ya ƙara da cewa: “Kin ga ke kuwa, ke assistant ɗinsa ce kawai, ba komai a tsakaninku, kuma hakan ya fi kyau. Amma gaskiya, wallahi ina son ki san… bana jin zan iya daurewa ba tare da na nuna miki yadda nake ji a raina.” Ya kalleta da ido. Amal zuciyarta na bugawa, ta ɗauke kai, ta ce cikin rawar murya: “Zayd, don Allah ka daina irin wannan magana yanzu. Ba lokacin wannan maganar bane, kuma bana son wani abu da zai kawo matsala a wajen aiki.” Zayd ya yi dariya kaɗan sannan ya ce: “Shikenan, pretty. Amma ki sani akwai lokacin da zuciyata zata kasa ɓoyewa. Amma a yanzu zan tsaya a gefe, kawai in ta kallonki, in kuma taimakeki. Kin cancanci hakan.” Ya bar wurin, Amal ta tsaya da wani irin nauyi a ranta, zuciyarta cike da ruɗani. A gefe kuwa, Maleekh yana tsaye yana kallon su, idonsa cike da wuta, zuciyarsa tana tafarfasa, amma ya ci gaba da riƙe bakinsa.. __________________________________________ Ana zaune a babban parlour na part ɗin Maleekh, Zayd ya zauna a kan kujerar opposite ɗin Maleekh. Maleekh yana ta duba wasu takardu, yana ƙoƙarin shagala da aiki don kada zuciyarsa ta bayyana. Zayd yana dariya, hannunsa a kirjinsa ya ce “Wallahi Bros, kullum idan na ga pretty sai zuciyata ta yi wani irin tsalle. Amma fa akwai ɗan jiji da kai a tare da ita, tana ganin ta fi kowa. Amma ni, Zayd, na san hanyar da zan lallabeta. Just ka tayani jan hankalinta kawai, shege ne ni, ba zata kauce min ba.” Maleekh ya ɗago kai daga takardunsa, ya kalle shi da ido masu sanyi amma cike da haushi ya ce “She is my assistant, Zayd. Kaji assistant. Kana so ka nuna mun ban da iko akan assistant ɗina ne? Kana son ta rainani ne a gabanka da kuma a gaban company?” Zayd ya yi murmushi yana girgiza kai ya ce: “Oh bros, kai ba ka fahimta ba. Na sanka da son girma. Ni ba wai ina ganin ta raine ka bane, a’a. Ai kai babba ne, CEO ne zata ji maganarka. Amma na rantse maka, pretty zata zama tawa. Ni ba na rasa nasara a rayuwa.” Ya jingina a kujerar yana nishaɗi. Maleekh kuwa ya ɗaure fuska, ya jingina da kujerar yana haɗiye zuciyarsa. Idanunsa sun kaɗa sunyi ja saboda ɓacin rai da kishi, amma bai ce komai ba sai kawai ya ce: “Do whatever you want, Zayd. Amma ka sani… ba kowace hanya ce zata kai ka inda kake son zuwa ba.” Sai ya miƙe ya nufi ɗaki, ya bar Zayd yana dariya cikin rashin fahimta.. Zayd yana kallon bayansa, yana ɗan ɗaga gira cikin ransa ya ce: “Hmm… Bross da gaske yana ɗaukar wannan abun da wasa. Amma zan nuna masa cewa pretty ba za ta ƙi Zayd ba.”.... A company, ranar aiki Amal ta fito daga office ɗinta tana riƙe da takardu, tana tafiya zuwa wajen meeting. Zayd ya hangota daga nesa, da sauri ya taho yana sanye da farin suit, yana riƙe da jakar hannunsa yana murmushi. Yana ɗan gyara murya ya ce: “Pretty, ki bari in taimaka miki, kada ki wahalar da kanki da ɗaukar takardu masu nauyi haka.” Ba tare da ta tsaya ba, Amal ta ce cikin ladabi. “Thanks, but zan iya kaiwa da kaina.” Kafin ta ƙarasa maganar, Zayd ya kwace takardun yana cewa: “Don Allah ki barni, ai wannan aikin ne na wanda yake tare da ke kullum. Kin san ni na rantse sai na sa murmushi a fuskar pretty.” Ya yi mata wani irin lallausan murmushi, ma’aikatan wurin duk suna kallon su suna jin daɗi, wasu har suna ɗan faɗin: “Kai wannan sabon ɗan uwan CEO yana da barkwanci.” Amal ta ɗan yi shiru, tana so ta kaucewa abun, amma ta kasa nuna masa fushi saboda yadda yake ta nuna kulawa da barkwanci.. Bayan meeting Zayd ya sake shigowa office ɗin Amal. Yana riƙe da wani ƙaramin gift box da aka nannade da ribbon. “Pretty, this is for you. Ba komai bane, just a little something da na gani kuma na ji ya dace da ke. Ki buɗe ki gani.” Amal ta girgiza kai tare da faɗin: “Ba sai kayi wannan ba, ni ba na son ɗaukar kyauta haka.” Zayd ya ce: “C’mon, don Allah. Ba soyayya ba ce, appreciation ne kawai. Kin cancanci a yaba miki. Kowa yana cewa kina aiki sosai. Please ki karɓa.” Ya saka ƙarfin halinsa ya sa box ɗin a kan tebur ɗinta. Amal ta kalle shi cikin tausayawa amma bata ce komai ba.... Ba yanda ta iya haka ta karɓi gift ɗin. Shi kuwa bayan ya gama surutansa ya fice daga office dake lokacin tashi yayi.... _____________________________________☆ Part ɗin Maleekh, a daren yau.. Maleekh yana zaune yana nazarin files, amma zuciyarsa gaba ɗaya tana rikicewa. Zayd yana kwance a kan kujera ya gama waya da wani abokinsa dake London.. Ya dubi Maleekh cikin dariya ya ce: “Bros, ai yanzu I’m in love, wallahi. Pretty ta fara sakin jiki dani a hankali, har na fara yi mata kyaututtuka. Na siyo mata wani ƙananan diamond pen today – ai da kanta zata gane Zayd ba mutum bane, prince ne.”.. Maleekh ya runtse idanu yana jin kamar zuciyarsa zata fashe. Bai ce komai ba, kawai ya riƙe biro yana danna shi da ƙarfi, sai kuma ya miƙe ya ce da ƙarfi cikin sanyin murya: “Zayd, remember she is my assistant. Don’t cross limits.” Zayd ya ɗaga hannayensa yana dariya tare da faɗin “Hahahaha! Ai ba na crossing limits, bros. Ina dai bin hanyar soyayya ne kawai. Kuma ban taɓa yin soyayya da wadda ba ta cancanta ba.” Maleekh ya juya ya bar ɗakin cikin takaici, zuciyarsa na ƙonewa, amma yana riƙe komai a silence... ☆☆☆☆☆☆ Ending weekend. Monday morning... Amal ta shiga office ɗin Maleekh da files... Bayan ta gaishe shi cikin ladabi ta ce: “Sir, ga reports ɗin da aka nema. Na tabbatar da dukkan bayanai.” Maleekh ya karɓa ba tare da ya duba files ɗin ba. Ya jingina da kujera yana kallonta da idanu masu zurfi. Amal ta saki hannunta tana jin bugun zuciya. A sanyaye ya ce: “Amal… kina jin daɗin wannan kyaututtukan da ake kawo miki kullum?” Amal ta yi shiru, zuciyarta ta tsinke. Ta san yana magana ne akan Zayd. Ta sauƙe kai sannan ta ce: “Ni ba na buƙatar su… amma na kasa hana shi.” Maleekh cikin taushin da ya haɗu da haushi ya ce: “Kina iya hana shi, idan kina so.” Ta ɗago idonta tana kallonsa kai tsaye, sannan ta ce: “Kai kace bani da matsayi a zuciyarka. So why ka damu?” Maganar ta bugi zuciyar Maleekh. Ya riƙe biro yana murɗawa da ƙarfi, kafin ya ce: “Because… you’re still my assistant. Kuma ban yarda wani ya raina ni ta sanadiyyarki ba.” Amal ta yi murmushi mai cike da baƙin ciki. Ta tattara takardunta ta fita ba tare da ta ce komai ba. Maleekh ya biyo ta da kallo, zuciyarsa na ƙonewa da soyayya da kishi, amma yana riƙe komai a silence. A rana ya ta yau ana gudanar da Big Event na campany.. An hallara a babban taro. Manyan baƙi da Ma'aikata sun hallaru, ana gabatar da company achievements. Amal tana tsaye a gefe cikin kyau da nutsuwa, da files a hannunta. Zayd ya kasa ɗauke idonsa daga kanta. Kafin kowa ya ankara, sai kawai ya yi magana cikin fara’a: Da ƙarfi, yana dariya ya ce: “Ladies and gentlemen, allow me to appreciate someone special to me… my Pretty! Amal.”.. Duk aka juya a lokaci guda. Amal ta tsaya cak, zuciyarta ta tsaya, ganin abinda bata zata ba.. Zayd ya tsaya a gefenta tare da zagayo da hannunsa ta bayanta, ya jawo ta kusa da shi ya riƙe kunkuminta... Zayd yana kallon jama’a ya ce: “She’s so amazing, ba zan gaji da jin daɗin kasancewa kusa da ita ba.” 😳 REACTIONS Maleekh: A inda yake zaune gaba ɗaya idonsa ya kaɗa ya yi jawur. Zuciyarsa na narke wa kamar wuta. Hannunsa ya matse glass cup da yake riƙe da shi har kusan tsage wa. Ya so ya miƙe ya tunkare su amma ya danne fushinsa, ya ci gaba da zama kamar dutse amma idanunsa suna sauƙa a hannun Zayd da yake kan kunkumin Amal... Amal: Gabanta ya mungun faɗuwa, hannunta ya saki files suka kusa faɗuwa ƙasa. Idonta na kan Maleekh, zuciyarta ta yi sanyi gaba ɗaya. Bata iya magana ba, jikinta yana rawa. Jama’a: Wasu suna dariya suna ganin kamar abin soyayya ne, wasu kuwa suna musayar kallon mamaki. 🌙 Bayan Event Ana kammala taro, kowa ya watse. Amal ta yi saurin kwace kanta daga wajen Zayd. Babu wata magana da ta yi, kawai ta tattara kanta cikin damuwa ta nufi motarta. Zayd yana kiranta: “Pretty wait! I can drop you home…” Amal ta girgiza kai, cikin rawar murya ta ce: “No thanks…” Ta shiga motarta, zuciyarta na bugawa da tsoro da kunya, sannan ta bar wurin. Daren nan, bayan sun dawo daga event ɗin. Maleekh ya shige cikin ɗakinsa ba tare da ya yi magana da kowa ba. Ya cire rigarsa ya zauna daga shi sai singlet, ya zauna tare da jingina da kujera, ya ɗauki glass na wine amma bai sha ba kawai yana wasa da shi ne... Idonsa jajur, zuciyarsa na bugawa da sauri. Duk abinda ya faru a wurin yana dawowa masa a rai. Haka yake magana da kansa, cikin ɓacin rai. “Hannu… a kunkumin Amal? … Zayd ya isa ya riƙe ta haka a gaban idona? … Kuma ita ta tsaya kamar dutse tayi shiru? Amal fa!…” Ya miƙe da sauri, ya daki bango da ƙarfi. “Zayd… you bastard. Ka ɗauka zan bar maka ita? Never!” Sai ya ja tsaki, ya shiga tafiya a ɗakin yana juya kansa. Yana ƙoƙarin lulluɓe zuciyarsa da cewa “she’s just my assistant”, amma zuciyarsa na ƙaryata shi. ✨ Meanwhile Zayd A gefe guda, Zayd yana ta waya da wani abokinsa yana dariya tare da faɗin: “My friend, ka ga yadda na tsaya nake riƙe da wuyan ɗuwawun Amal kuwa? Gaba ɗaya jama’a suka tsaya kallon mu! She’s mine, ba wanda zai hanani…” Yana dariya yana waya da abokinsa... 🌹 Amal A gida kuwa, Amal ta zauna a gado tana riƙe da pillow. Idonta cike da hawaye, zuciyarta tana tunawa da yadda Maleekh ya kalleta. Cikin rauni ta furta.. “Ya Allah, me yasa zuciyata bata iya ƙin Maleekh ba? Kuma yanzu Zayd ya fara nuna ni a bainar jama’a… ya zanyi?…” NEXT NEXT NEXT asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 49 to 50 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Washegari da safe, suna cikin parlor suna breakfast. Zayd yana ta faman hira kamar kullum, shi kaɗai yake magana, Maleekh kuwa ba daɗi yake ji ba amma yana danne zuciyarsa. Zayd yana ɗan dariya ya ce: “Bros gaskiya wannan Amal ɗin… wow! Yarinyar na da class wallahi. Na kasa bacci jiya saboda ita. Yanzu kam dole ka tayani jan hankalinta… ko ka mata magana game dani.” Maleekh ya ɗago kai da sauri, idonsa ya ɗan kaɗa. Cikin nutsuwa da murya mai nauyi ya ce “She’s my assistant, Zayd. Ba zan bari ta raina ni ba. Tunda tana ƙarƙashina, don’t cross the line.” Zayd yana dariya, bai fahimci zurfin maganar ba ya ce “Ohh bros… kai fa kullum serious! Ai ba wani abu bane. Assistant ɗinka ce, amma ba ka nuna min akwai wata alaka tsakaninku ba ko? Ni fa kawai ina son ta, kawai ka barni da ita.” Maleekh ya ɗauki cup ɗinsa ya sha coffee a hankali, yana ƙoƙarin danne fushinsa. Amma zuciyarsa na tafarfasa. Cikin siririyar murya, yana kallon ƙasa ya ce “Zayd… don’t try to touch what you can’t handle. Karka shiga inda bai kamata ba…” Sai ya miƙe daga kujerar, ya nufi stairs ya bar Zayd a wurin. Zayd kuwa ya biyo shi da ido, yana murmushi, yana magana da kansa. “Bros fa ya ɗauka wasa nake ko? To wallahi wannan Amal kam dole sai na mallaketa. Zayd baya rasa abu…” A Campany Amal tana office ɗinta tana typing report da aka barta ta kammala. Cikin natsuwa take, tana ƙoƙarin mantawa da abin da ya faru jiya. Sai ga knocking. Ba tare da ta ɗago ba ta ce: “Come in…” Zayd ya shigo cikin shigar suit mai kyau, yana ɗauke da ƙaramar box mai kyau da ribbon a jikinsa. Yana murmushi sosai ya ce: “Pretty, na san kina da aiki sosai… amma na ce yau zan kawo miki little something… just for you.” Ya ajiye gift ɗin a kan desk ɗinta. Amal ta ɗago da mamaki ta ce. “Gift? For me?… But why?” Zayd ya ce: “Because you deserve it. Kullum kina aiki, kina supporting bros, kuma honestly… na kasa samun kwanciyar hankali in ba na nishaɗi da ke.” Amal ta tsaya tana kallonsa, ba ta ce komai ba. Sai ta juyo da box ɗin a hankali ta buɗe… Cikin box ɗin ƙaramar zinariya necklace mai kyau sosai, da wata karamar gold bracelet. Idanun Amal suka canza da mamaki, a hankali ta furta. “Zayd… this is too much. I can’t accept this.” Zayd yana matsawa kusa da ita tare da faɗin “Why not? Ni fa ba na yi miki komai face because you’re special. Ko ki sa yanzu na gani…” Yana kai hannu zai ɗauki necklace ɗin. Amal ta ja baya da sauri, zuciyarta tana bugawa ta ce: “Please, don’t. I appreciate it, but I don’t think I can…” A lokacin ƙarar buɗe ƙofa ta cika office ɗin. Maleekh ya shigo cikin nutsuwa idanunsa suka sauƙa kai tsaye kan Zayd da Amal, da kuma necklace ɗin da ke kan desk. Zuciyarsa ta yi wani irin nauyi. Ya tsaya kallon su seconds kaɗan, sannan ya ce cikin sanyin murya amma mai cike da ƙarfi: “What’s going on here?” Amal ta tsure gaba ɗaya. Zayd kuwa ya kalli Maleekh yana murmushi, kamar bai damu ba, ya ce. “Bros… ai ba komai. Just showing appreciation to your hard-working assistant. Ka ga necklace ɗin nan? Perfect for her ko?” Maleekh bai ce komai ba sai ya juyo ya kalli Amal. Idonsa ya nuna alamun ƙunci da ƙona zuciya, amma sai ya danne ya ce: “Amal… we need to talk. Now.” Ya juya ya fice daga office ɗin. Amal ta tsaya kallon Zayd cikin tashin hankali, zuciyarta na bugawa da sauri.. Zayd yana murmushi yana jingine da kujera ya ce. “Don’t worry pretty… bros ɗinai yana da girman kai kawai. Ni da ke ne fa future…” Amal ta gyara gyalenta da sauri ta bi bayan Maleekh, zuciyarta cike da fargaba. Ta bi bayan Maleekh zuwa part ɗinsa na office. Hannunta har rawa yake yi, zuciyarta na tsalle-tsalle saboda yadda ta ga irin kallon da yake mata a cikin taron... Da ta shiga, ta ganshi tsaye a gaban desk ɗinsa, hannuwansa a riƙe da gefen desk ɗin kamar yana ƙoƙarin danne wani bacin rai da ya kasa sarrafawa. Amal a hankali, tana shigowa ta ce: “Sir… ka ce kana buƙatar magana da ni?” Da sauri ya juyo, idanunsa jawur, numfashinsa yana fita da sauri. Kafin ta iya wani motsi ya ƙarasa wurinta da sauri, ya riƙo damtsenta da ƙarfi, ya mannata da bango. Shi ma ya kwanto kanta da hannunsa guda, suna kallon fuskar juna, numfashinsu na haɗuwa. Maleekh cikin ƙasa-ƙasan murya, mai cike da ƙarfi ya ce: “I hate you, Amal… I hate the way you make me feel. I hate the way you let him touch you, call you names, gift you…!” Yana zazzaro ido cikin tsananin bacin rai da kishi. Amal ta ƙurawa idanunsa ido, jikinta har rawa yake, amma sai ta tattara ƙarfin guiwa ta ce: “Tin da kai ka zaɓi ka bar ni, ka tura ni gefe… ka bari wani ya samu damar kusanto ni. Ka ce baka buƙatar soyayyata. To yanzu… idan akwai wani da yake so na da gaske, me zai hana na ba shi zuciyata?” Maleekh ya matso kusa sosai, hancinsu kusan ya haɗu. Idonsa ya ƙafe cikin nata, zuciyarsa na bugawa da karfi. Cikin rawar murya ya ce: “Don’t you dare… don’t even think of it, Amal. Karki kuskura ki bari wani ya shige wurin da ni kaɗai nake da shi a zuciyarki…” Amal ta runtse idonta, hawaye suka taru a gefen idon ta ce: “Wannan wurin da kake faɗi… kai ne ka yashe shi. Kai ne ka ƙi kallo na lokacin da nake jiran ka. Ka ce bana da daraja a gurinka… yanzu kake nuna kishi?” Maleekh ya ɗan saki hannunta, amma bai bari ta motsa ba. Ya ɗaga hannunta da ya riƙe cikin fushi, ya ce: “I hate myself… saboda na bar ki. I hate myself saboda na bari wani ya ƙira ki ‘pretty’. But Amal… wallahi duk da na faɗi cewa bana sonki, amma ban daina son ki ba. Ban daina buƙatarki ba.” Amal ta girgiza kai da sauri, tana ƙoƙarin janye jikinta amma idonta ya kasa barin nasa.... Cikin rawar murya ta ce: “Stop it, Maleekh… ka riga da ka yanke hukunci. Ka bar ni in rayu da zafin rabuwa. Idan ka ce baka sona, to ka bar ni in nemo farin ciki na a wani wuri.” Ya rufe idanunsa na ɗan lokaci, sannan ya buɗe su da wani irin yanayi cike da kishi, sha’awa, da tsananin soyayya. Hannunsa ya sauƙe daga bangon zuwa kuncinta, yana shafa fuskarta cikin raunin zuciya. A hankali, kamar yana furta wani sirri ya ce: “You’re mine, Amal… whether you like it or not. Ko da zan ƙone da kishin Zayd, ko da na tsani kaina, amma bazan yarda na rasa ki ba…” Amal tana hawaye, tare da lumshe eyes ɗinta.. Numfashinsu na ci gaba da haɗuwa, ɗakin ya cika da wani irin zafi da ba su iya magancewa. Numfashinsu na ci gaba da haɗuwa a hankali, bugun zuciyarsu yana ƙaruwa kamar kiɗa. Maleekh ya sauƙe hannunsa zuwa kuncin ta yana shafawa. Hannunsa na rawa.. Ya yi wani irin tsaki a ƙasin harshensa, ya ce cikin rawar murya: “Amal… kin sani… na daɗe ban yi kewarki irin yanzu ba.…” Idanunta sun cika da hawaye, amma ta kasa magana. Sai dai ta tsaya kallonsa, jikinta har rawa yake. Ya lumshe idonsa, ya ɗan jingina goshinsa da nata. Hancin su ya haɗu, numfashinsu ya haɗu. Wani irin zafi ya ratsa su duka biyun. Amal ta ji hannunsa ya sauƙe a wuyanta yana shafa mata a hankali. Shi kuwa ya kasa danne kansa. A hankali ya ɗaga fuskarta, ya ƙura mata ido, idanunsa suna magana da duk abinda zuciyarsa ta kasa faɗi. Ya ɗan matsar da bakinsa kamar zai ce wani sirri a kunnenta, amma murya ta makale. Amal ta runtse idonta tana girgiza kai..ba tare da ta furta komai ba... A hankali ta ji numfashinsa yana ratsawa a fuskarta. Ya ce cikin wata murya mai rauni: “Na rasa tunanin da zan yi… Na rasa yadda zan ce miki…” Sannan ya matso da fuska sosai, lips ɗinsu suka yi karo da juna a wani irin shiru mai cike da zafi, suka yi lips touch na tsawon lokaci da aka yi missing juna. Amal ta kasa jurewa ta buɗe idonta, lokaci guda ta rufe su ta sakar da wani irin numfashi mai taushi... Sun tsaya haka na ‘yan dakiku suna jin numfashin juna, hannayensa a gefen fuskarta, nata hannayen a kirjinsa. Wani irin kewar juna ya lulluɓe su gaba ɗaya... Sai daga baya Amal ta ja numfashi ta janye jikinta ta koma gefe a hankali, idonta a ƙasa, hawaye suna gangarowa. Maleekh kuwa ya sauƙe hannayensa, ya juyo gefe, zuciyarsa na bugawa kamar zata fashe... A hankali cikin rawar murya ta ce: "Ni zan tafi ..." Ba tare da ya bata amsa ba ya ƙara tako wa yanda ta ke. Yasa hannu yana ɗago da ha6arta..kallon juna suka yi daga bisani ya ƙara mannata a jikin bango... Ya ce: "kina so ki je wancan yaron ya ci gaba da shiga jikinki?.." Ya matseta sosai a bango, idanunsa suna tsiyayar da ƙiyayya da kishi, amma zuciyarsa ta cika da kewar da ya kasa ɓoye wa. “Na tsane ki, Amal…!” ya furta cikin rawar murya, amma idanunsa sun bayyana akasin maganar. Amal ta runtse idonta tana hawaye, zuciyarta tana karyewa. “Ka tsane ni… amma zuciyarka har yanzu tana kirana Maleekh. Idan ba haka ba, me yasa kake tsayawa kusa dani haka?..” Shiru ya ratsa su. Numfashinsu ya haɗu, jikinsu ya haɗu. A hankali hannunsa ya zame daga jikin bango zuwa fuskarta, ya ɗago haɓarta. Amal ta buɗe idonta ta kalle shi, su biyun suka tsaya kallon juna, idonsu na magana da ɗaruruwan kalmomi. Sannan kamar wani abu ya rinjaye shi, Maleekh ya sauƙe ƙaramin bakinsa akan nata a hankali. Wani irin sanyi ya ratsa zuciyar Amal, ta yi ƙoƙarin janye kanta amma ta kasa. Ya fara soft, yana tsotsa a hankali kamar mai roƙon gafara. A hankali ta lumshe ido tana mayar masa da martani, sai sumbatar ta rikid'e zuwa mai zafi, kewar da suka daɗe suna dannewa ta fashe gaba ɗaya. Hannayenta suna kan kirjinsa, jikinta a manne da jikinsa. Hannunsa ya koma bayanta yana rungumeta sosai, tamkar zai haɗiye ta gaba ɗaya. Sun tsaya cikin doguwar sumbata mai ɗauke da soyayya, ciwo, da kewar juna. Duk wani ɓacin rai da zargi ya rikide zuwa zafi mai cike da soyayya. Da ƙyar suka rabu da juna, dukansu sun kasa numfashi yadda ya kamata. Amal ta jingina kanta a kirjinsa tana sauƙe numfashi, shi kuma yana shafa kanta yana rarrashi zuciyarsa na bugu.. Numfashinsu ya ragu ya koma nauyi, kallo ɗaya suke iya yi wa juna. Amal ta ɗago idonta, idanunta sun cika da hawaye. A hankali ta furta da murya mai rawa: “Wannan… bai kamata ya faru ba, Maleekh.” Ta zame jikinta da ƙarfi daga hannunsa, tana girgiza kai kamar wacce aka yi wa asiri. Hawaye suka cika a idanunta... “Ka daina… kar ka ƙara kusantata haka,” ta faɗa cikin tsananin ruɗani, kafin ta juya da gudu ta fice daga office ɗinsa. Maleekh ya tsaya a tsaye, hannunsa yana kan bango, zuciyarsa na tsananta bugawa. Idonsa ya kaɗa ja, ya shaƙi iska kamar zai yi ihu... “Amal…” ya furta da ƙasa-ƙasan murya, kamar yana magana da zuciyarsa. Shi dai ya kasa bin bayanta, kawai ya buga hannunsa da ƙarfi a kan tebur, gilashi ya girgiza. Ya dafe kansa, yana ƙoƙarin murƙushe kewar da ta sake tashi cikin jikinsa. Amal kuwa da gudu kai tsaye ta shige cikin office ɗinta. Ta rufe ƙofa ta jingina tana huci, tana kuka. Ta dafe bakinta da hannunta tana ambaton Allah a zuciya: “Me yasa haka yake faruwa? Me yasa ban iya tsanar Maleekh ba duk da abinda ya min?… Ya Allah ka bani ƙarfin zuciya…” Ta zauna a kan kujerarta, da biro a hannunta, amma jikinta na rawa. Amma abin da zuciyarta ke bugawa shi ne ɗan ɗanɗanon sumbatar da har yanzu ba ta iya mantawa da shi ba. Amal tana zaune a kan kujerarta tana ƙoƙarin danne kukanta, tana share hawayen da ba su daina zuba ba. Ganin wani ƙaramar gift box a kan desk ɗinta yasa ta dakata tana kallonta. A hankali ta miƙa hannu ta ɗauka. A saman akwatin an rubuta da ƙaramin salo: “To my pretty 🌹 From Zayd.” Amal ta tsaya cak tana kallo, zuciyarta na wani irin bugu. A hankali ta buɗe akwatin, duk da tasan meye a ciki... A ranta take faɗin "Wannan mutumin bai tafi da wannan abun nashin ba?.." Ta ciro ƙayataccen necklace mai ɗauke da ƙaramin heart pendant. Ta ɗaga shi sama, hasken office ɗin ya daki pendant ɗin ya ƙara haskawa da kyau. Wani irin nauyi ya sake saukar mata a zuciya. Ta rufe idanunta, ta tuna da kalaman Zayd kullum yana kiranta “my pretty”, sannan ta tuna yadda Maleekh ya kalleta a ɗazun cikin kishin da bai iya ɓoyewa ba. Hawaye suka sake zubo mata, ta jingina da kujerarta tana riƙe da necklace ɗin. A hankali ta furta cikin shessheƙar kuka: “Me yasa rayuwa zata min haka?… Me yasa kowanne yana ƙoƙarin mallake ni, amma zuciyata bata son kowa face shi da ya kore ni?” Ta ajiye necklace ɗin a kan desk tana kallonsa, kamar yana yi mata tambaya. Zuciyarta ta ƙi amsa. ☆☆☆☆☆ Ranar weekend, gidan ya yi shiru bayan sallar la’asar. Amal da Inna zaune a falo suna kallon wani tsohon shirin Hausa a TV. Sai ga maigadi ya shigo da sallama. Maigadi ya ce: “Amatu, anzo ana cewa sallama dake a waje.” Amal ta ɗago daga kan remote tana dubansa da mamaki. Ta ce: “Maleekh ne?…” Inna tayi saurin katse ta da cewa. “To waye in ba shi ba? Kaje ka ce ya shigo mana, ai ya cancanci ya shigo ba tare da tambaya ba, ai nan ma gidansu ne.” Ta ƙarasa tana kallon Amal da ɗan harara.. Amal ta kalleta kawai, bata ce komai ba, ta maida kai ga TV. Maigadi ya tashi ya fita. Bayan ɗan lokaci sai suka ji knocking a ƙofar falo. Inna ta juyo ta dubi Amal. Ta ce: “Je ki buɗe masa falon mana.” Amal ta tashi da ɗan rashin son takura, tana sanye da guntun jeans da t-shirt mai ɗan siriri. Da take bata shirya baƙo ba, sai tafiyar ta ɗan yi nauyi. Ta kai hannu ta buɗe ƙofar… sai ta zaro manyan idanu tana kallon Zayd, wanda yake tsaye da ƙayataccen jan flower irin na masoyan soyayya. Zayd ya tsaya yana murmushi, idonsa yana biye da ita daga sama har ƙasa. Yana murmushi ya ce: “Mu shiga ciki mana, Pretty. Na gaisa da Mama ko?…” Kafin Amal ta samu damar magana, sai ya ratsa gefenta cikin sauƙi ya shiga falon. Inna da ta ɗaga kai tana sa ran ganin Maleekh, sai ta haɗa ido da wani sabon fuska mai ɗauke da annuri.. Ta sake baki tana faɗin: “Amatu! Wannan kuma a wane daji kika samo shi? Ko shima ɗan club ne?!” Amal ta tsaya bakin ƙofa tana mamakin yanda ya shigo gida da sauƙi haka. Zayd ya yi murmushi yana kallon Inna cikin natsuwa. Ya ce: “Wannan da dukkan alamu kakarki ce, ko Pretty? naga kwakwalwarta ta fara juyawa…” Inna ta zabura ta miƙe tsaye, ido a waje tana faɗin “Ni kake ƙira mahaukaciya? Kai ɗan iskan yaro!” Zayd ya ɗaga hannunsa cikin nutsuwa yana faɗin “A’a, Kaka, kwantar da hankalinki. Wallahi ba haka nake nufi ba. Ina nufin kamarki irin na ƴan birni, da surutu irin na masu kuɗi...” Amal ta hanzarta tsoma baki da cewa. “Inna… wannan ɗan uwan Maleekh ne.” Inna ta tsaya cak. Fuskar ta sake kamar wadda aka zare wuta daga jikin lantarki. Inna ta ce: “Uhmm… ai na ga shi ma akwai kyau, kamar irin ƴaƴan Ƙaruna. To shigo, shigo, ya zama dole ai a tar6e ka...” Ta zauna tana hararar Amal, ita kuwa Amal bata san inda zata saka idonta ba. Zayd ya miƙa flower ɗin hannunsa ga Amal yana murmushi, sai ya zauna kamar mai gidan, ya ɗora ƙafafunsa cikin natsuwa. Ya zauna a kujera cikin kwanciyar hankali, ya ɗora flower ɗin a gefen Amal. Yana gyara zaman rigarsa, idonsa na bin Amal a hankali. Ya furta “Kaka, wato wannan irin kallo da kike min yanzu, zai iya sa mutum ya fi ƙarfin soyayya.” Inna ta ce “Soyayya kuma? Kai dai ka bayyana, ɗan wane kai? Ko ma dai ɗan waye, kada ka zo mana da zancen club nan.” Zayd ya yi murmushi, yana jingina da kujera ya ce: “Toh, ni dai ni Zayd ne. Na dawo daga ƙasar waje wato London, yanzu haka dai ban saba da kowa ba sai Amal.” Amal ta yi saurin kakkabe maganar da cewa. “Eh, amma dai Inna, ni ba abinda ya haɗa mu da shi sosai. Ɗan uwansa ne dai Maleekh …” Zayd yana katsar mata magana da lumshe ido ya ce “Ɗan uwana? Ni ma na ji kamar ɗan uwana ne.” Inna ta kalli Amal sannan ta ce “Amatu, wannan saurayin kuma sai kace an yi masa training a club. Yadda yake surutun nan ya fi maza nan garin. Toh, kai ɗan wane ka ce? Kuma kai ne babban ɗan uwan Maleekh ko ƙarami ne?” Zayd ya ce: “Ni dai zan fi son ki ƙira ni Angon amarya tunda na shigo gida.” Inna tayi dariya tare da rashin fahimtar sa ta ce: “Yau na ga wannan yaron, akwai raini da sa dariya sosai. Amma duk da haka, akwai kyau.” Amal ta ɗan kauda kanta gefe, zuciyarta na bugawa. Bata taɓa tunanin Zayd zai shigo har gidan ta ba.. Zayd ya ɗauki flower ɗin ya miƙa mata da murmushi, yana faɗin “Wannan ba domin Kaka bace, don ke ne. Pretty, ke kika jawo ni har gidanku.” Amal tana kallonsa ta ƙi karɓa.. Inna ta harareta tare da faɗin: “Amatu, karɓi kyautar nan mana, ki ajiye. Ai mace ba ta ƙin kyauta, ko daga wane ne.” Sai ta juyo tana kallon Zayd da murmushi. Inna ta ce. “Toh Zayd, ina wannan ɗan uwanka ne? Shi ma ya zo ne?” Zayd ya ɗan gyara murya, ya ce: “Shi?… yana can wajen guda. Amma Kaka, bari na gaya miki gaskiya, ni dai Amal ce nake so, ba wani abu ba.” Amal ta kalli Inna a firgice, idonta cike da faɗuwa. Inna kuwa tayi dariya tana girgiza kai ta ce: “Toh Amatu! Ai yanzu komai ya fito fili. Wannan ɗan uban yaron ya fi ƙarfin ɓoye ɓoye. To Allah ya sa alheri. Tin da wancan ɗin ya ƙi ki sai ki kama wannan kar kiyi sake reshe kama ganye...” Amal ta kaɗa kanta a hankali, zuciyarta cike da rikici tsakanin Maleekh da kishinsa, da kuma Zayd da kulawarsa.. Inna ta kalli Amal da murmushin sannan ta miƙe tana faɗin: “Ni dai zan je ɗaki na kwanta, ku ci gaba da hirarku. Amma Amatu, ki tuna da maganata, mace ba ta ƙin kyauta, ko nawa ya baki ki karɓa …” Ta wuce tana dariya, ta bar su biyu a falon. Amal ta yi shiru, ta kasa kallon Zayd kai tsaye, zuciyarta na buga wa.. Zayd yana jingine a kujera, yana mata kallon soyayya ya ce. “Pretty, gaskiya yau na samu farin ciki. Na yi tunanin zaki kore ni daga ƙofar gida, amma sai ga ni har cikin falonku, na zauna lafiya.” Amal ta ɗan gyara zaman ta, tana wasa da flower ɗin da ya kawo ta ce: “Ni ban taɓa tsammanin zaka iya zuwa gidana haka ba, bare har ka sami damar zama a nan.” Zayd yana matsowa kusa da ita a hankali ya ce: “Kina so in gaya miki gaskiya? Ni dai ina ji kamar kin tsare zuciyata. Duk sanda naga murmushinki, komai a raina yana sauka.” Amal ta ɗan ja numfashi, tana ƙoƙarin boye fargabar da ke cikinta. Ta ce: “Zayd, don Allah ka tsaya… bana son irin wannan maganar.” Zayd yana ƙanƙance ido, yana matsowa kusa sosai ya ce “Wani lokacin magana ba ta isa, sai zuciya ta furta kanta. Ki duba idona Amal, kiga gaskiyar da ke ciki.” Ya ɗan kai hannunsa yana ƙoƙarin taɓa hannunta me flower, ya riƙe tafin hannunta. Amal ta yi saurin janye hannunta, tana jin zuciyarta na bugawa fiye da yadda ta saba. Amal cikin murya mai rawa ta ce: “Don Allah ka daina. Wannan abun bai dace ba.” Zayd yana murmushi cikin natsuwa ya ce: “Shikenan, zan daina faɗa… amma ba zan taɓa daina ji ba. Komai ya faru, Amal, na tabbatar ina ji dake.” Amal ta yi shiru, ta kasa cewa komai. Ta ji kamar idan ta zauna da shi naɗan lokaci, zuciyarta zata rufta gaba ɗaya. Sai kawai ta miƙe tsaye, tana daidaita flower ɗin a hannunta. Ta ce: “Na gode da ziyara, Zayd. Yanzu fa sai ka tashi.” Zayd ya kalleta cikin natsuwa, sannan ya murmusa. “Ba damuwa, pretty. Zan tafi yanzu… amma ki sani, ni ba zan fasa ba.” Ya miƙe, ya nufi ƙofa, sai kuma ya juyo ya sake kallonta. “Ki bar wannan flower a zuciyarki, koda kuwa baki karɓi zuciyata ba.” Ya fita a hankali, ya bar Amal tsaye a falon tana riƙe da flower ɗin, zuciyarta cike da rikici. ☆☆☆☆ Bayan komawar sa gida... Zayd ya shigo gida cikin annashuwa, yana ta tauna chewing gum da murmushi a fuskarsa. Sai ya nufi babban falon da Maleekh yake zaune, yana kallon TV amma hankalinsa ba a wajen shirin yake ba. Da ya hango Zayd, sai kawai ya ce da sanyin murya. “Lafiya yau sai farin ciki kamar wanda ya ci award?” Zayd ya zauna a gefensa yana dariya ya ce: “Bros! Wallahi zan gaya maka gaskiya… na ziyarci pretty ɗina.” Maleekh ya ɗan ɗago kai a hankali kamar wanda aka kai masa duka, yana tambaya da yanayin da bai dace ba: “Wace pretty?” Zayd yana wasa da key ɗinsa ya ce: “Wace kuma idan ba Amal ba? Wato assistant ɗinka nan. Kai bros, gidan nata kuwa cikakke ne, Kakarta ma ta sanni yanzu.” Maleekh ya kasa amsawa. Kallon Zayd yake da wani irin yanayi da ba za a iya fassara shi ba. Zuciyarsa ta cika da kishi, amma fuska ta ɓoye komai. Zayd yana murmushi, bai ma lura da halin Maleekh ba ya ce “Wallahi bros, Amal ba irin sauran girls bane. Tana da nutsuwa, tana da kamala. Ka ga ai da irin wannan mace ce za ta zama wife ɗina, company ɗinka ma zai sami nutsuwa” Maleekh ya tsaya cak, muryarsa ta sauya. “Zayd.” Zayd ya tsaya yana kallonsa, yana mamakin yadda muryarsa ta yi nauyi. Maleekh ya ce: “Ka ce ka je gidanta?” Zayd yana murmushi ya ce “Eh mana! Me yasa?” Maleekh yana jujjuya glass cup a hannunsa, yana ƙoƙarin danne damuwarsa ya ce “Ba komai... kawai na tambaya ne. Ka ce Kakarta ta karɓe ka da fara’a?” Zayd ya ce: “Fara’a kuwa sosai. Gaskiya sun karɓeni sosai. Amal ma... hmm bros, idan ka ga yadda ta yi kyau cikin casual wear ɗinta kai, ba zan iya mantawa da wannan kallo ba.” Maleekh ya kalli gefe, yana maida numfashi da ƙarfi, kamar wanda zuciyarsa ke ƙonewa amma yana ƙoƙarin zama cool. Maleekh da murmushi mai ɗaci ya ce: “To, ai sai ka cigaba... idan kana ganin hakan zai sa ka farin ciki.” Zayd ya yi dariya yana faɗin: “Ni kuwa ina da tabbaci bros! Zaka ga yadda pretty ɗina zata sauko cikin soyayya ba da daɗewa ba.” Ya miƙe yana jefa key ɗinsa sama yana catching. Ya ce: “Goodnight bros, ka huta. Ni zan fara tsara plan na gaba.” Ya fita da murmushi. Da ƙyar Maleekh ya iya ɗaukar numfashi. Ya riƙe glass ɗin da yake riƙe sosai, har sai da ya ji yana girgiza. Sai kawai ya furta cikin ƙasa da murya, zuciyarsa na rawa: “Amal... me kike son yi min?” Ya miƙe a hankali, ya nufi window, yana kallon dare kamar yana neman amsar da zuciyarsa ta kasa faɗa masa... asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 51 to 52 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Ƙarfe 12 na dare, Maleekh ya kasa bacci. Duk jikinsa cike yake da wani irin zafi da naci. Ya kasa jure tunanin Zayd yana kusa da Amal, yana bata kyauta, yana murmushi da ita. Ya miƙe ya ɗauki key ɗin motarsa, ba tare da ya faɗa wa kowa inda zai je ba. Security na bakin gate suka tsaya da mamaki suna tambaya: “Sir, midnight fa... ina zaka je haka?” Amma ya wuce su tamkar ba ya jinsu, fuskarsa ta cika da nufin ɗaya.. A ɗari yake gudu da motar ya nufi gidansu Amal.. Bayan mintuna ya isa. Motarsa ta tsaya a gaban gidan Amal. Ya yi horn sau biyu, maigadi ya fito da sauri. “Haba Oga Maleekh! Wannan lokaci fa?” “Buɗe mun ƙofa.” Ya furta cikin murya mai sanyi mai cike da iko ta sa maigadin bai sake tambaya ba. Ya shiga cikin gidan, falo a kulle an rufe ko ina, duhu ya lulluɓe komai.. Ya ƙira Amal a waya, ringing... amma babu amsa. Yayi shiru yana sauraron numfashinsa, sai daga bisani ya ɗaga kai zuwa sama, inda taga windown ɗakinta yake.. Ya furta a hankali. “In gan ta... ko da sau ɗaya ne.” Window ɗin a ɗan buɗe take. Babu jinkiri ya haura yana taka wuraren da zai iya kai shi sama. A hankali ya tura window ɗin, Da kyar ya shige, ya tsaya yana kallon ɗakin komai tsaf, ya ji ƙamshin turarenta da ya saba ji a ofis. A nan ya tsaya… A katafaren gadon nan, Amal na bacci, tana sanye da soft pink sleepy dress, gashin kanta ya bazu saman pillow, fitilar ɗakin ta haskaka fuskarta cikin nutsuwa. Maleekh ya zauna bakin gadon. Ya jingina hannu da cinyarsa, yana kallonta. Daga bisani ya miƙar da hannu yana shafar fuskarta a hankali kamar wanda yake taɓa mafarki. “Amal…” “My pretty…” “Kina tunanin zan iya jure ganin wani yana miki kyauta?” Muryarsa ƙasa ƙasa, ya furta hakan.. Amal, a cikin baccinta, ta ji kamar ana taɓa fuskarta. Ta motsa, ta buɗe ido a hankali Ganinsa yasa ta zabura ta tashi zaune cikin tsoro. Ta buɗe baki zata yi ihu Da sauri ya toshe mata baki da hannunsa. Maleekh cikin raunin murya ya ce “Shhhhh! Amal... it’s me. Ni ne Maleekh.” Jin muryarsa yasa hawaye taruwa acikin idanunta. Zuciyarta ta tsaya cak. Idanunsu suka haɗu a cikin duhu, hasken wata na sauka saman fuskarsu. Amal cikin muryar kuka ta ce “Me kake yi a nan, Maleekh...? Me yasa zaka shigo min gida cikin dare haka?” Maleekh ya ce “Saboda bazan iya bacci ba... Bazan iya jure ganin wani yana sonki ba, Amal.” Ya miƙe tsaye yana kallonta, numfashinsa na fita a hankali, kamar mutum da yake yaƙi da kansa. “Na rantse ban zo don in takura miki ba... Na zo ne don in faɗa miki gaskiyar zuciyata.” Tana kallonsa da shanyayyun eyes ɗinta. Numfashinta yana saurin fita... A hankali ya furta cewa “Ina so muyi magana, Amal.” Ta kasa cewa komai. Sai kawai ta jinjina kai, tana dubansa cikin rashin fahimta. Ya ƙaraso kusa da ita, idanunsa suka cika da wani irin kishi mai nauyi. “Amal, akwai abu guda biyu da nake so ki faɗa min yau a daren nan. Ni kike so… ko Zayd?” Ta kalli ƙasa, muryarta ta kasa fita. “Maleekh…” Ta furta sunansa a hankali... Ya ce: “Kada ki ƙira sunana idan baki da tabbaci.” Shiru ya biyo. Sai a hankali ta buɗe baki ta tambaya: “Idan na zaɓe ka fa?” Ya ɗan saki numfashi, ya ce da murya mai taushi mai cike da iko: “To ki daina karɓar kyauta daga hannunsa. Ki daina bari ya taɓa ko yatsanki. Kuma kada ki sake barinsa ya kusance ki.” Ta jinjina kai, idanuwanta na ɗauke da hawaye. Sai kuma ta ce da ƙaramin murya: “Idan kuma Zayd na zaɓa fa?” Maleekh ya ɗan janye daga kusa da ita. Ya ɗauki numfashi mai zurfi, sai kuma ya furta cikin sanyi: “Zan kashe ki… sannan na kashe shi.” Kalmar ta tsaya a kunnenta kamar ƙarar guguwa. Ta zaro ido tana kallonsa da tsoro. Shi kuwa ya tashi tsaye, bai sake cewa komai ba. Ya nufi window ɗin da ya shigo ta, ya fita a hankali, ya ɗinka harabar gidan cikin duhu.. Yana fita daga gidan. Motarsa ta tashi da sautin injin mai ƙarfi, ya bar gidan da zuciya mai raɗaɗi da kishi... _Washegari_ Amal ta farka da safe cikin wani irin nauyin tunani da bugun zuciya. Tunanin abin da ya faru da daddare bai bar kanta ba. Ta zauna a gefen gadonta tana kallon window ɗin da Maleekh ya shigo ta jiya, zuciyarta na bugawa kamar ana danna ƙaho a ciki. “Zan kashe ki… sannan na kashe shi…” Kalmar ta koma tana juyawa a kwakwalwarta. Ta dafe kanta da hannaye biyu tana numfashi mai nauyi. “Ya Allah! Ka sauƙaƙa mun halin da nake ciki” Ta miƙe ta shiga toilet ta watsa ruwa, amma har cikin ruwa tana jin kamar hannun Maleekh yana shafar fuskarta, irin taushin hannunsa, amma kuma da dumin barazana a cikinsa.. Ta fito ta shirya tsab..Tana riƙe da handbag da waya, ga wani irin takalmi mai tudu da ta sanya, tana sanye da blue jeans da wani ƙaramin t-shirt sai ta ɗora abaya mai tsaguwa ta gaba daga sama zuwa ƙasa yanda Jeans ɗin da ta sa zafi fito wa... Ta fito elegant look 😍 Da ta fito ta nufi kitchen, ƴar aikin gidan ta tarar da ita da murmushi tana faɗin. “Hajiya Amal, antashi lafiya? Tin jiya ban ganki ba sai yau…” Amal ta yi murmushi sannan ta ce “Lafiya kalau… kawai dai na gaji.” Amma cikin ranta tana cike da ruɗani. Tana zaune a dining tana breakfast sai ga ƙiran Zayd a waya, ta kasa ɗagawa. Ga kuma saƙon da ya turo “Good morning my pretty 🌹” ta duba kawai ta rufe wayar. Kowanne numfashi nata ya cika da tambayoyi: Me yasa ya je har ɗakina da dare? Me yasa yake da irin wannan kishi? Shin Maleekh na sona har haka? Ko kuma yana so ya mallake ni ne kawai?" Bayan ta kammala breakfast. Ta tsaya gaban madubi dake manne a wurin dinning tana kallon kanta, sannan ta furta cikin sanyi: “Zayd baya da laifi... amma idan Maleekh har zai iya haka saboda ni to wannan ba abin da za'a ɗauka da wasa ba.” Ta ɗauki jakar ta fita zuwa office. Amma kafin ta shiga mota, zuciyarta ta sake fasa tambaya: “Ko dai in faɗa wa Zayd gaskiya? In gaya masa cewa Maleekh ni ɗin ta Maleekh ce?” Sai kuma ta girgiza kai. “A’a… idan nayi haka zai iya haddasa fitina da Maleekh… kuma Maleekh zai iya aikata duk abin da yace…” Ta shiga mota cikin ruɗani, idonta ya cika da hawaye, zuciyarta ta kasa zaɓar tsakanin soyayya da tsoro... Kai tsaye campany ta nufa.. Motar Maleekh na tafe cikin nutsuwa, iska tana kaɗawa daga gilashin da aka ɗan buɗe. A gefensa Zayd ke zaune, yana ta lalubar jakar da ke jikinsa da murmushi mai cike da nishadi. Zayd yana murmushi ya ce “Bros, ka ga wannan kuwa?” Ya zaro wata kyakkyawar golden shoe mai sheƙi kamar rana. “An yi order ɗinta ne daga London, limited edition, ba wanda ke da irin ta a Afirka gaba ɗaya. Kyautata ce ga pretty — Amal!” Maleekh bai amsa ba, sai kawai ya kalle shi da ido masu zurfi, ya ɗan gyara steering ɗin motar cikin natsuwa. Maleekh ya ce: “Hmm… expensive taste.” Zayd yana dariya ya ce “Kai bros, kai ba zaka gane ba. Pretty deserves special things. Ba irin sauran mata bane…” Maleekh ya murmusa kaɗan amma idanunsa sun ɗan kaɗa, yana danne wutar kishi da ke tasowa a zuciyarsa... “If you say so…” Suka isa company, suka fito daga mota cikin natsuwa. Ma’aikata suna gaida su cikin girmamawa. Sai dai lokacin da suka shiga reception, abin da suka gani ya sauya yanayi gaba ɗaya. Amal tana zaune a kan kujera mai tsari, da ƙaramar handbag a gefenta. Idonta ya ɗan gaji da tunanin daren jiya, amma ta ƙoƙarta ta ɓoye shi da murmushi. Zayd, idonsa ya sauƙa kanta, sai fuskar sa ta yalwata da farin ciki. Ya zaro golden shoe ɗin daga jakarsa ya yi gudu kamar ɗan wasa, yana faɗin: “Surprise my pretty!!! 🌹💛” Kafin Amal ta ankara, Zayd ya durƙusa a gaban ta gaban jama’a. Ya sa hannu ya cire takalmin ƙafarta, sannan ya ɗaura mata golden shoes ɗin da kansa. Kowa a reception ya tsaya, wasu suna dariya, wasu kuma suna yaba kyan takalmin.. Amal ta kasa motsi, ƙirjinta na bugawa da sauri, idonta na neman Maleekh, wanda ke tsaye a gefe cikin wani irin yanayi na shiru da raɗaɗin zuciya. Maleekh ya kasa ɓoye fushin da ke cike da kishin da bai taɓa ji ba. Ya ɗaure fuska sosai, sai idonsa suka kaɗa suka cika da bacin rai. Sai dai ya danne komai cikin sirri, ya juya kamar ba komai, ya wuce da ƙarfin hali zuwa ofis ɗinsa. Amal ta gane a lokacin yanzu fa Maleekh zai iya yin komai saboda wannan Zayd ɗin. Amal a ranta ta furta: “Ya Allah… wannan ba kyauta bane kawai, wannan zai tayar da bala’i.” Zayd ya ɗago kai yana kallon ta da murmushi: “Na gaya miki pretty, Zayd baya yin nasara a rabin hanya. Look at you, you’re shining like queen of gold!” Amal ta yi murmushi na ɗan lokaci, amma cikin zuciyarta tana jin tsoro da damuwa. Ta san Maleekh ya ga komai kuma yanzu yana cikin zafin kishinsa ... Amal tana zaune a office ɗinta, ta ji ƙira daga intercom. “Miss Amal, CEO is calling you to his office… now.” Muryar secretary ɗin na rawa, alamar ta gane akwai wani abu a ɓoye. Amal ta ɗan gyara, ta fesa turare, ta nufi office ɗin Maleekh. A ƙofar, zuciyarta na ta bugu kamar ana buga ganga. Bayan ta tura ƙofar ta shiga, ta ganshi a tsaye fuskar sa ba annuri, idonsa sun kaɗa, hannunsa yana kan desk yana girgiza yatsunsa kamar mai tsare abun hari.. Maleekh a hankali cikin murya mai zafi ya ce: “So... wannan shine aikin da kike yi a company? Kinyi kyau sosai… da sabon takalmin da masoyinki ya sa miki a gaban mutane.” Amal ta tsare shi da ido sannan ta ce: “You have no right, Sir. Ba kai ne mahaifina ba, ba mijina ba. Sannan kai kace mun rabu — to let me live my life!” Maleekh ya ɗaga murya cikin fushi ya ce: “Your life? A company ɗina? A gaban idona? Kin bari wani yaro ya durƙusa gaban ki, ya sa miki takalmi kamar... kamar me?!” Amal ta daga murya itama ta ce: “Eh! Saboda kai baka ganin darajata ba! Yana gani na kamar Sarauniya, kai kuma kullum faɗa da tsawa! Ka ce ka rabu da ni amma ka kasa barin zuciyarka ta sake!” Idon Maleekh ya ƙanƙance, numfashinsa ya yi nauyi. A hankali ya matso kusa da ita. “Ki faɗa min gaskiya... kina sonsa?” Amal ta kalle shi da hawaye sannan ta ce: “Idan na ce eh fa? Me zaka yi?” Kafin ta gama maganar, Maleekh ya zabga mata mari mai ƙarfi! 😢 A cikin ɗan lokaci ta firgita, ta faɗi jikin kujerar executive tana riƙe da kuncinta, numfashinta na rawa, hawaye na bin fuskarta.. Maleekh ya tsaya yana kallonta da ido masu zafi, yana girgiza kai. Cikin murya mai raɗaɗi ya ce: “I warned you... ki guji wannan abin. Amma kin ɗauki maganata wasa.” Ya juya da sauri, ya fice daga office ɗinsa, yana tafiya cikin takaici. Amal ta miƙe a ruɗe, tana ƙiran sunansa cikin kuka: Amma bai tsaya ba ya nufi office ɗinta kai tsaye. Ya shiga ya buɗe drawer ɗinta, ya ɗauko takalmin gold ɗin da Zayd ya bata, yana kallonsa kamar abu mai ban tsoro. Sai ya ɗauki takalman biyu, ya fice daga building ɗin cikin fushi kamar hadari. Amal da gudu ta biyo bayansa tana ƙwala masa kira: “Maleekh! Don Allah ka tsaya! Ka faɗa min me kake yi haka?!” Ya fita zuwa bayan company, hasken rana na haskawa kan fushinsa, ya tsaya a fili ya zaro ashana (lighter) daga aljihunsa. Ya ajiye takalman a ƙasa, ya zuba petur ya kunna wuta… Amal ta karaso tana kuka tana ƙiran sunansa cikin firgici. “Maleekh! Stop it please! Ka tsaya! Maleekh! Don Allah ka daina! Wannan kyauta ce, ka bar shi!” Maleekh cikin fushi ya ce: “Kyauta ce daga wanda kike so ko? To ku biyu ku huta, bana so ina ganin komai daga gare shi!” Ya sa wuta kan takalman. Suna ƙonewa suna sheƙin zinare.. Amal ta durƙusa a ƙasa tana kuka, tana kallon wutar tana magana cikin murya mai rawa: “Ka yi hakan ne saboda kishi... ko saboda ƙiyayya, Maleekh?” Shi kuwa ya tsaya yana kallonta, idanunsa suka cika da hawaye amma bai nuna ba. Ya juya kawai, ya bar wajen cikin shiru.. Motarsa ya shiga ya bar campany... Ita kuwa Amal tayi saurin tarar ruwan fanfo dake gefe da ita, ta kashe wutar amma sai dai takalman sun fita hayyacinsu.. Tana kuka ta bar wurin itama.. Washegari da safe... Tunda ta fito daga gida har ta shiga mota, idonta kumbure saboda kuka. Tun daga bakin gate ta lura ma’aikata suna ta magana a hankali, suna nuna hannayensu zuwa bayan company. “An samu wuta fa jiya… takalmi masu tsada sun ƙone!” “An ce gift ɗin CEO Assistant ne…” Amal ta tsaya cak, numfashinta ya tsaya. Zuciyarta ta fara dokawa kamar ana danna gangar yaƙi. Ta san ana magana ne akan ƙonewar takalman, amma ba wanda yasan wa ya aikata hakan.. Ta yi shiru kawai, ta shiga ciki tana ɗauke da wani nauyi a zuciya. Amma a fuskarta babu komai sai “professional smile.” Da ta shiga reception, sai ta hango Zayd yana tsaye yana dariya tare da ma’aikata biyu. Yana riƙe da kwali mai kyau, an nannade shi da ribbon. Da ta shigo, Zayd ya juya ya hango ta, nan take ya ciro sabon gift daga cikin kwalin. “My Pretty! I was looking for you... amma fa na zo da gift ɗinki, me yasa kika bar wancan a company jiya? Na ga a waje, wai an ce ya ƙone 😳.” Amal ta tsaya cak, zuciyarta ta buga. Ta ɗan washe baki cikin karfin hali, ta ce: “Eh… ban ma san yadda hakan ta faru ba. Maybe wani ne ya bar wuta kusa da shi…” Zayd ya ce: "Aina kika ajiye? Amma a waje fa aka same su.." Amal ta ce "Maybe wani ne ya kai can.." Zayd ya ce "Bar su hassada ce kawai..." Zayd ya dafa kafaɗarta a hankali, yana murmushi. “Sorry fa, my Pretty. Ni fa bana son a sa ranki a wani abu mara kyau. Kin san ai duk abin da nake miki, daga zuciya yake.” Ta murmusa kaɗan, tare da sauƙe hannunsa daga kafaɗarta cikin raunanniyar murya ta ce “Na sani, Zayd. Na gode sosai… Allah ya saka da alkhairi.” Zayd ya matsa kusa, yana kallon fuskarta da kulawa. “Amma fa… naga kin canza yau. Kin yi kuka ne?” Ta girgiza kai tana ɗan dariya: “Kuka kuma? Ina! Na yi bacci ne kawai sosai.” Sai ya ɗan murmusa, ya riƙe hannunta da ta kasa janye wa.. “To idan kina buƙatar faranta rai, bari na fitar da ke yawo yau. No office stress, no Maleekh calls, just us.” Ta ɗan kalle shi cikin ido, tunawa da kalaman Maleekh jiya: “Ki zaɓi… Ni ko Zayd.” Zuciyarta ta yi nauyi, ta ɗan janye hannunta a hankali, tana murmushi. “Ba yanzu ba Zayd… muna da meeting da company masu saka jari. Maybe later.” Zayd ya gyara rigarsa, yana dariya: “To na yarda my Pretty. Amma ki yi min alkawari za ki bani lokaci na gaba. Ni dai Zayd bana fushi da ke, ko kina so ko baki so…sannan ga sabon gift nan” Amal ta ce "Kai dai baka gajiya, kawai leave it.." Ya ce: "Okay idan kika fito zaki amsa ai.." Ya fara yin gaba. Yana tafiya yana juyowa, yana kallonta da murmushi, Amal kuma ta tsaya tana binsa da ido, hawaye suka taru a idanunta. A zuciyarta ta ce: “Zayd mai kirki ne… amma zuciyata har yanzu tana da rauni da sunan Maleekh.” Bayan Amal sun fito daga meeting room. Kai tsaye kitchen ɗin campany ta wuce domin haɗa tea. Zayd yaga shigarta hakan yasa ya bi bayanta.. Amal ta shigo kitchen ɗin da nutsuwa tana buɗe flask ɗin ruwan zafi. Kamshin coffee da mint ne suka cika wurin. Ta ɗan sauƙe ajiyar zuciya tana haɗa tea. Zayd ya biyo bayanta cikin shiru. Ya tsaya daga nesa yana kallonta na wasu sakanni kafin ya ƙaraso kusa da ita. “Yau kyautar ta zobe ne…” ya furta da murya mai sanyi. “Ban taɓa miki kyautar zobe ba, kuma shine farkon da ya kamata in baki.” Amal ta ɗan yi murmushin rashin jin daɗi. “A’a ka bari kawai, bana buƙata.” Zayd ya ɗan matsa kusa. “Kar ki ƙi. Wannan fa na zuciya ne.” Tana ja da baya tana girgiza kai, “Zayd, don Allah” Amma ya riƙe hannunta yana ƙoƙarin saka zoben. A lokacin ne suka fara jayayya, ta ƙi karɓa ne saboda tana gudun matsala daga Maleekh, shi kuma yana ƙoƙarin nuna soyayyarsa. Daidai lokacin ƙarar buɗar ƙofa ta karade kitchen ɗin. Maleekh ya tsaya a bakin ƙofar, idonsa a rufe da zafin rai. Idonsa ya sauƙa a hannun Amal da Zayd ke riƙe. “Zayd…” ya furta a hankali, murya cike da tsawa. Kafin kowa yayi magana, ya ƙaraso da sauri ya cafke kolar rigar Zayd.. Amal ta firgita ta matsa gefe tana faɗin, “Maleekh, don Allah ka saurara” Amma kafin ta ƙarasa, Maleekh ya zabga wa Zayd mari..cikin zafin rai ya kai masa naushi a baki... Sai da bakin ya fashe.. “Bros! Me nayi maka kake dukana?” Zayd ya furta yana kare kansa. Maleekh ya ɗauke shi da wani marin da yasa rigarsa ta ɓalle... “Amal is mine!” ya furta cikin bacin rai.. Lokaci guda ya fara kai masa naushi yana marinsa. Ya ja shi waje yana dukansa.. Amal tana kuka tana bashi haƙuri amma sam ya ƙi. Har sai da suka fito reception..Yana dukansa. Ma’aikata suka fara fitowa daga ofis, kowa ya tsaya da mamaki. Wani murmushi mai tsoro ya bayyana a fuskokin wasu domin kowa ya san labarin Amal da Maleekh, sai dai sun yi tunanin sun rabu. Amal tana kuka tana ƙoƙarin tsayar da shi amma ya ƙi. Sai da ya ja Zayd har zuwa tsakiyar reception yana dukansa... Sai ya juyo ya kamo Amal, ya mannata a bango, jikinsa na ruri da fushi ya ce: "Baki yadda da abinda na gaya miki ba ko?..." Ya wurgata tsakiyar wurin ya ce: "Yanzu faɗa da ƙarfi kice... Ni Amal matar Maleekh ce.." Tana kallonsa da hawaye ta ce, “Bazan faɗa ba! Dukansa ba zai canza komai ba!” “Faɗa!” ya tsawata. “Faɗa da kanki — ki ce ni Amal, matar Maleekh ce!” Tana girgiza kai, tana kallonsa cikin takaici. Kallon su duka ma’aikata ke yi.. Cikin zafin nama Maleekh ya ɗaga ta, ya ɗauke ta sama kamar jaririya. Kowa ya yi shiru yana kallon su. Ya fita da ita daga reception zuwa harabar waje. “Maleekh! Ina zaka kaini?!” Ta furta tana kuka.. Ya buɗe motarsa ya jefar da ita cikin seat, ya rufe ƙofar da ƙarfi. Tana kuka tana bubbuga glass, “Maleekh, don Allah ka saurare ni!” Shi kuwa ya kunna motar cikin huci, bai ce komai ba sai kallo ɗaya da ke cike da haɗari. Engine ya yi vrrrm! motar ta nufi titi da gudu… Cikin mota shiru ya mamaye su. Amma shiru ne mai nauyi kamar ana iya jin bugun zuciyoyinsu. Ƙarar engine da A.C motar, da hucin iska daga window ne kawai ake ji. Amal tana zaune tana kuka a hankali, hannunta a gefe tana share hawaye. Maleekh kuwa yana tuƙi da hannuwa biyu a steering, idonsa a hanya, amma zuciyarsa na tafarfasa. Cikin murya mai nauyi ta ce, “Maleekh… kai ka faɗa min cewa nayi nesa da Zayd, sannan ina ƙoƙarin yin nesa da shi. Amma me yasa haka? Me yasa zaka dake shi a gaban mutane? Kamar ba ɗan uwanka ba...” Ya ƙara danne ƙafarsa kan accelerator, motar ta ƙara gudu... “Saboda bana son ganin wani na taɓa ki!” Amal ta zaro ido.. “Taɓa ni? Mai kake tunani ne? Wallahi ba abinda ya faru, kuma ba abin da zai faru, Zayd mutumin kirki ne..” “Na ganki!” ya katse ta cikin tsawa. “Na gan ku a kitchen, hannunsa a kan naki, kina dariya kamar babu komai!” Amal ta ɗan matsa baya tana girgiza kai.. “Ka yi tunanin hakan yana nufin soyayya ne? Zayd kawai yana ƙoƙarin saka min zobe. Amma ni na ƙi!” “Zobe?” ya yi dariya mai ciwo. “Toh me yasa kika ƙi ƙaryata shi a wajen jama’a? Me yasa kika tsaya kina kallo lokacin da yake ƙoƙarin saka miki?” “Saboda bana son rikici!” ta faɗa cikin kuka.. “Bana son a sake ganin ka haka, Maleekh! Ka san yadda jama’a ke kallonmu? Ka lalata min mutunci a gaban kowa!” Ya kalle ta da idanu masu kaifi, “Mutuncin ki?” ya maimaita cikin muryar tsawa. “Wato ni ban da mutunci? Amal, kina son ki yi wasa da ni?!” Ta yi shiru tana huci tana kallonsa. Sannan ta ce cikin rawar murya, “Ba wasa nake da kai ba, amma kai ba zaka taɓa fahimta ta ba. Kai kullum fushi, tsawa, da iko. Ka manta ni ma ina da rai!” Motar ta tsaya cak! Ya taka brake da karfi har jikin Amal ya bugi dashboard. Ya juyo ya kalle ta, idonsa jawur, numfashinsa yana fita da ƙarfi.. “Amal… bana wasa da ke. Na gaya miki zaɓi biyu ne kawai.” Ta juyo tana kallonsa cikin hawaye, “Ka ce min fa… idan na zaɓi Zayd?” Ya ɗan rufe ido kamar yana ƙoƙarin hana kansa fushi, sannan ya buɗe su a hankali. “Zan kashe ki… sannan in kashe shi.” Amal ta riƙe cikinta da hannunta, tana girgiza kai da firgici.. “Ka rasa magana me kyau sai wannan? Wato rayuwata ta koma wasan hannunka?” “Rayuwarki tawa ce!” ya furta da ƙarfi. “Bazan iya ra6an ki da wani ba. Ki yi tunani Amal, wallahi indai inada rai ba zan bari wani ya mallake ki ba.” Tana kallonsa cikin hawaye ta ce, “Kana ƙiran wannan da soyayya kuma? Wannan fa tsoro kake dasa mun a zuciya, sannan ka zalunci bai ji ba bai gani ba..!” Ya ɗan yi shiru na ɗan lokaci, sai murya ta sauya, ta koma kamar mai kuka: “Zalunci ne amma saboda ƙauna nake yi. Wallahi bazan iya ganin ki da wani ba. Kullum ina tunanin tafiyar ki da yanda zamu kasance tare...” Amal ta ɗan yi shiru, zuciyarta na bugawa da tausayi da tsoro a lokaci guda. Ta ce a hankali, “Idan haka kake jin ƙauna… to wallahi, ba ka sona. Son mallaka kake yi mun.”.. Maleekh ya ɗan kalli steering, ya dafe kansa da hannu ɗaya, yana maida numfashi da wahala. Sannan ya juyo ya ce a hankali, “Ki sani… ki na abin da na kasa bari, Amal.” Shiru ya biyo. Motar ta ci gaba da tafiya a hankali har duhu ya fara shiga domin tafiyar na da nisa, domin har su ɗan fita daga cikin gari.. Amal ta rufe idonta tana kuka, shi kuma yana tuƙi yana kallon hanyarsa kamar wanda ya manta inda yake nufa… Iska na kaɗawa a gefen villa ɗin, wacce ta daɗe babu mai zama a cikinta. Hasken chandelier ɗin falon yana ta rawa kamar zai mutu. Maleekh ya ja Amal har cikin babban falon, yasa key ya kulle sannan ya jefa key ɗin a aljihunsa... Amal ta tsaya tana kallonsa da kumburarren ido... “Maleekh me yasa muka zo nan?” ta ce cikin rawar murya. Ya juyo da wani murmushi mai sanyi amma cike da ɓacin rai. “Honeymoon muka zo, baby…” ya ce cikin muryar da ke cike da sarƙaƙƙiyar soyayya da iko. “Zamu huta anan, mu biyu… kafin zuciyata ta sauƙo daga wutar da kika kunna.” Amal ta ɗan matsa baya tana girgiza kai, “Honeymoon? Ka ɗauke ni da karfi ka kawo ni cikin daji, ka ce honeymoon?”. “Na gaya miki bana wasa da ke,” ya ce yana ɗaukar laptop daga saman kujera ya kunna, ya jingina da sofa. “Yanzu zan tambaye ki abu ɗaya, kuma bana so kiyi mun wasa.” Amal ta ƙure idonta a kansa tana huci.. “Me kake son sani?” Maleekh ya zaro wani file daga cikin jakarsa, ya jefa mata a gabanta. “Wannan rahoton ne daga likita,” ya ce cikin sanyi, muryarsa na dukan kunne kamar ƙaho. “Yana cewa kin zubar da cikin wata huɗu. Wannan rahoton ne daga club ɗin da aka sameki cikin jini.” Zuciyar Amal ta buga. Ta dago a hankali tana kallonsa, hawaye suka cika idonta. “Maleekh…” ta ce da muryar da ke rawa. “Ka kasa saurara na tun lokacin… ka kasa tambayata me ya faru.” Ya ɗan jinjina kai cikin ɓacin rai.. “To yanzu nake son jin ki. Ina sauraronki yanzu.” Amal ta miƙe da sauri tana faɗin, “To yanzu kake buƙatar ji na? Bayan ka riga ka yanke hukunci? Bayan ka riga ka ɗauke ni a matsayin mai laifi?”.. Amal tana surutai ta nufi ƙofa zata buɗe ta tafi taji ko ina a kulle. Haka ta haƙura tana kuka. Maleekh yana danna computer Ya ce. "Ke, bana wasa dake! Yanzu gaya mun, a kwanakin baya meya faru aka sameki a gidan club hakan ma a cikin jini sannan doctor ya ce, kin zubar da cikin wata huɗu..." Amal tana harararsa ta ce "Tin lokacin Meyasa ka kasa saurara ta?.." Ya ce cikin izzah. "Yanzu..Ina sauraronki.." Amal ta ce. "To nima banida lokaci yanzu.." Wani irin gigitaccen tsawa ya daka mata har sai da ta gigita. Sauran kaɗan ta fece jikinta na 6ari..." "Gaya mun na ce.." Muryarta ta rikice, tana girgiza kai, jikinta na rawa...Ta ce: “Ka yi mun hukunci ba tare da shaidar gaskiya ba, Maleekh! Ba ciki na zubar ba!” Ya ɗan miƙe daga kujerar, ya sauƙe ido daga kanta yana furta a hankali, “To menene ya faru, Amal? Me yasa aka sameki cikin jini a club?” Tana kallo cikin idonsa, murya ta fara karyewa, “Na ji labarin Aurenka da Farha shine nayi ta ƙiran ka, baka ɗaga ba. Na fita saboda ina sonka na je gidanku aka sanar mun cewa kana club, hankalina ya kasa kwanciya hakan yasa naje domin dubo ka. Na samu wasu ƴan mata suka sanar mun cewa kw fita amma zaka dawo yanzu...Na sha juice da suka kawo, sai na ji duniya ta fara juyawa… daga nan ban sake sanin komai ba. Ina farkawa sai a asibiti... Bayan zargina da ake akan batun nan naje wani hospital domin tabbatar da kaina. Likita yace babu wani cikin da aka zubar, amma an zuba wani abu a cikin abin sha na.” Ya ɗan tsaya shiru, idonsa ya ƙanƙance kamar mai son yin kuka amma ya danne cike da iko ya furta. “Me kike nufi? An drug ɗin ki?” Amal ta gyaɗa kai cikin kuka, “Eh… amma baka saurare ni ba. Ka bar ni cikin rauni, ka yi min hukunci kafin ka ji gaskiya.” Da sauri ta fara lalu6o wayarta yanda tayi snap ɗin result ɗin da doctor ɗin ta ya bata cewa babu abinda ya faru illah drugs da ta sha... Ta ce cikin rawar murya. "Ka ga..." Ya karɓa ya duba da kyau sannan ya jinjina kai ya ce: "Wa ya tura ki wurin? Ina nufin wa ya sanar miki cewa ina club?..." Amal ta girgiza kai ta ce "Kawai kayi haƙuri komai ya wuce.." A tsawa ce ya ce "Wa ya sanar miki?..." A ruɗe ta ce: "Fa F Far Farhaaa.." Ya rufe ido da hannu ɗaya, yana maida numfashi cikin wahala. Sannan cikin tsawa mai rauni ya ce, “Me yasa baki faɗa min tun farko ba?” Ta ɗaga kai tana kallonsa cikin hawaye, “Saboda baka tambaye ni ba.” Shiru mai nauyi ya sauƙa tsakanin su. Ƙarar iska daga window kawai ake ji tana shigowa tana motsa labulen bakin gilashi. Amal ta juyo gefe ta share hawayenta, ta ce cikin murya mai sanyi, “Wannan shine dalilin da yasa nake son barinka. Kai ka kasa sauraro na sai lokacin da zuciyarka ta riga ta yanke hukunci.” Maleekh ya kalleta sosai, idonsa ya canza daga fushi zuwa nadama. Ya matso kusa da ita a hankali, amma kafin ya iya cewa komai Amal ta juya ta kama ƙofa, ta fara dukan ƙofa tana faɗin, “Ka buɗe ƙofar, Maleekh. Ka barni in tafi.”.. Ya tsaya a gefe yana kallonta, muryarsa ta yi rauni sosai. “Idan na buɗe, ki gaya min gaskiya bakya sona?” Amal ta tsaya ta juyo tana kallonsa da hawaye, “Na taɓa sonka, amma yanzu tsoranka ne kawai a zuciyata.” Ta juya ta zauna a ƙasa tana kuka. Maleekh ya zauna yana kallonta, zuciyarsa ta rikice gaba ɗaya.... A bangaren Zayd kuwa... Zayd ya shigo gida da jiki gaba ɗaya a raunane. Rigar sa ta tsage, fuska ta kumbura, leɓensa ya fashe. Ya tsaya a bakin ƙofa yana riƙe da ciki da hannunsa, yana fitar da numfashi da ƙyar.. Ammy da yaranta suna zaune a babban falon suna hira da dariya, sai suka juyo da ganin yadda yake jina-jina... Ammy a tsorace ta ce: “Subhanallah! Zayd! Me ya same ka haka? Waye ya maka haka?” Zayd ya zauna a kujera yana jan numfashi. Ya share jinin da ke gefen leɓensa sannan ya ce cikin muryar da ke cike da haushi: “Maleekh ne... Maleekh ya kwace min masoyiya sannan ya dake ni kamar ɗan yaro a gaban mutane...” Falon ya ɗauki shiru, kowa ya kalle shi da mamaki. Ammy ta ɗaga gira ta ce: “Masoyiya kuma? Wace yarinya ce da zata sa Maleekh yayi maka haka?” Zayd ya ce: “Amal... Sunanta Amal. Tana aiki a cikin campany ɗin mu.” Daga nan kowa ya girgiza kai. Arfat ta zabura da sauri tana faɗin: “Tabbas ai dole ne Yaya Maleekh ya maka duka! Kai baka san yanda yake ji da Amal ba? Har sumar dani yayi saboda ita, wallahi a lokacin na ɗauka kashe ni zai yi saboda wata Amal!” Islam ta ƙara da murmushi mai cike da raini: “Ai ba kwace maka masoyiya yayi ba, dan tun farko ita masoyiyarsa ce. Amal ta Maleekh ce, kai dai baka san komai ba.” Zayd ya kalli Islam da Arfat, idanunsa suka kaɗa da fushi. “Shi yasa ke kike magana kamar kina farin ciki da hakan!? Idan masoyiyarsa ce me yasa yake rayuwa kamar wanda ya tsane ta? Me yasa baya nuna cewa yana son ta? Yake toshe mata hanya, yana tsareta kamar bai damu da ita ba?” Arfat ta ɗaga kai tana murmushi mai ɗan raini ta ce: “Eh to... Wannan ai shi ne irin soyayyar Maleekh, mai zafi, mai daɗi, mai ƙarfi. Kai dai baka san komai game da su ba, in taƙarƙare maka to akanta Yaya Maleekh ya kwanta jinya, ya samu matsalar zuciya...” Farha ta harare su duka biyu cikin bacin rai ta ce: “Dallah ku daina wannan sakarcin magana! Naga yanzu Maleekh ba ya son Amal, wallahi ba ya yinta. Dole ne ku gane hakan.” Zayd ya miƙe tsaye a hankali, yana goge jinin da ke gefen fuskarsa. Idonsa ya sauya, ba na zafi kawai ba, har da na ƙuduri... Ya ce da muryar da ke cike da alƙawari: “Ko da Maleekh yana so ko baya so... sai na mallake ta. Amal zata zama tawa ko ta halin ya ya ne.”.. Ya juya da fuskar da ta haɗa zafi, rauni da azama, sannan ya nufi ɗakinsa... NEXT NEXT NEXT.... asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 53 to 54 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Fitowar hasken safiya, rana ta fara bayyana a saman tagogin gidansu Amal. Inna tana zaune a falon ƙasa, tana sanye da hijabi tana lissafin tasbihi, amma idonta duk ya nuna damuwa. Tana tunanin dalilin da yasa Amal bata dawo gida ba tun jiya. Ƴan aiki suna ta motsi a kusa, wata na share falo, wata na haɗa breakfast. Cikin wannan yanayi ne maigadi ya shigo yana ƙiran Inna. Maigadi yana tsaye a ƙofar falon ya ce: “Inna, anyi baƙi.” Inna ta ɗago kai da mamaki ta ce: “Baƙi kuma? Da mota ne suka zo?” Maigadi ya ce “A’a Inna, da ƙafa suka zo. Wani dattijo ne da matarsa, sai wani saurayi da wata ƙaramar yarinya..” Inna ta haɗe gira ta ce “Toh, to. Kace su shigo nan cikin falon.” Maigadin ya juya ya fita. Ba da jimawa ba, sai ga su sun shigo cikin falon, dattijon yana da farin gashi da tsintsiya, matarsa tana sanye da hijabi mai launin toka, sannan wani saurayi da ya cika kamar ɗan gari, kyakkyawa da tsawo, sai karamar yarinya mai kimanin shekara 17 zuwa 18. Inna tana kallonsu har suka ƙaraso. Tana ganin dattijon sai ta zabura ta miƙe tsaye da mamaki. Inna da mamaki da farin ciki ta ce “Yawale!? Kai malam Yawale! Ashe kai ne?” Malam Yawale yana dariya ya ce “Na’am Inna Delu! Kin gane ni ke nan.” Inna tana dariya ta ce “Wallahi na kasa gane ka, Malam Yawale! Ai shekaru sun ja fa. Ina Zainabu? Ga ita nan ko?” Zainabu matar Yawale, tana murmushi ta ce. “Eh ni ce, Inna. Na gode Allah da naga fuskar ki bayan shekaru.” Inna ta ce. “Lallai yau gida yayi albarka. Kun taho daga ina haka?” Malam Yawale cikin farin ciki ya ce “Daga ƙauyen Gajeren Rafi a cikin Kaduna Local Government. Ai kin san shi can bayan Rijana, hanyar zuwa Kachia. Mun daɗe muna shirin zuwa ganin ku, sai yau muka samu dama.” Inna ta gyara zama ta ce “Toh, ai kunzo gida. Ku zauna. Allah ya kawo ku lafiya. Yanzu ga wannan saurayin da karamar yarinyar nan fa?” Malam Yawale yana nuna su ya ce “Wannan ɗana ne, Kabiru. Ga matata Zainabu, kuma wannan karamar yarinyar mu ce wato auta kenan Halima. Dake yaran duk sun mutu sai iya biyun nan, Kabiru da Halima ne suka rage mana, ai Halima tunda aka gaya mata akwai ƴar uwarta Amatu a burni sai ta nace zata zo ta ganta da idonta.” Cikin jin wannan kalma, Inna ta ɗan tsure, sai ta murmusa da ƙyar tana danne tsoro. Inna ta share gumi a goshi ta ce: “Eh, eh... Amatu dai tana wurin aiki yanzu. Tunda safe ta fita ba ta dawo ba. Aikin campany ne, kin san dai irin aikin birni babu sauƙi.” Zainabu ta ce cikin kalar tausayi. “Eh ai haka rayuwar burni take. Amma sai ta dawo fa mu ganta. Mun daɗe muna son muje mu gaisheta, tun bayan rasuwar mahaifiyarta.” Inna tana murmushi amma idonta cike da damuwa ta ce. “Insha Allahu zata dawo. Ku huta da gajiya. A girka muku abin ci. Ke Halimatu! Je ki ce a dafa muku tuwo da miyar taushe.” Halima ta tashi da hanzari kamar wanda aka zabure ta.. Kabiru yana duban falon ya ce “Ai gidan nan ya ginu sosai. Amatu kenan ke zaune a irin wannan gida? Lallai ta samu albarka a burni.” Inna tana dariya cikin ɗan ɗoki ta ce “Eh, ai Amatu yarinyar kirki ce. Ta dage da aiki sosai. Allah ne ya bamu arziki ta hannunta.” Malam Yawale yana kallon Inna ya ce. “Toh Alhamdulillah. Sai dai Inna, muna fatan komai lafiya. Na ji kamar kin damu ne tun muna shigowa.” Inna tana ƙoƙarin boye damuwarta ta ce. “A’a, lafiya lau. Kawai gajiya ce ta kwanan jiya.” Suka zauna suna hira, amma Inna tana ɗan duban ƙofa lokaci-lokaci zuciyarta cike da fargaba, tana addu’ar kada Maleekh ya dawo da Amal cikin wannan yanayi, musamman yanzu da danginta daga ƙauye suka iso. Bayan an ci an sha, an jera kofin shayi a kan teburi. ƙamshin tuwo da miyar taushe ya ratsa ko ina. Kowa ya ɗan yi nishaɗi, ana hira a hankali sai Malam Yawale ya tashi ya gyara zama, fuskar sa cike da murya mai nauyi... Malam Yawale yana kallon Inna ya ce: “Inna Delu, daman ina so mu yi wata magana mai muhimmanci.” Inna ta gyara zama, tana miƙewa a hankali ta ce: “To malam yawale, ina jinka. Me ke ranka? Me kake so mu tattauna?” Malam Yawale ya ɗago kai yana kallon duk wanda ke falon, ya dubi Kabiru da Halima a gefe sannan ya koma kan Inna. Malam ya ce "Kin dai san ni Yayan Mahaifiyar yarinyar nan ne wato Amatu, kuma iyayenta mahaifiyarta da mahaifinta sun juma da rasuwa tin tana ƙarama, yanzu abinda na yanke shine, me zai hana zumuncin mu yayi karko, mu haɗa zumunci sosai, inaso zan haɗa ɗana kabiru da Amatu Aure.." Kabiru yana gefe yana farin ciki... Inna taji batun baiyi mata daɗi ba ta ce "Wai malam yawale taya ma kuka san muna nan Abuja?" Malam ya ce "Ai mun shiga Kaduna can gidan da kuke akace kun daɗe da barin Kaduna kun dawo Abuja. Shine muka zo Abuja munata nema saida muka yi sati guda anan Abuja kafin muka samu gidan ku.." Inna ta ce "Aww saboda kun ji munyi arziki shine zaku wanko ƙafa kuzo wai akan a haɗa aure ko? To sannu masu son zuciya.." Malam ya ce "Me kike faɗa haka Inna Delu?.." Inna ta ce "Lokacin da iyayen Amatu suka rasu tin tana yarinya ba ƙin kula da ita kukayi ba? Saboda babu dukiyar iyayenta duk sun ƙone a gobara shine kuka guji ɗiyarsu, kuma alhalin lokacin da iyayenta suke da rai babu abinda kuke rasawa daga wurinsu, kullum a cikin maula kuke, ni mahaifiyar mahaifin Amatu ce inada iko akansa amma ban hanashi taimaka muku ba, shi kaɗai na haifa a duniya bashi da wa bashi da qani...Na tabbata da inada wasu ƴaƴa bayan shi nasan zasu taimaka mun...amma dake babu kowa, ku da kuke ƴan uwan mahaifiyarta sai kuka kama gabanku, wai bakwa so a ɗaura muku dawainiya, saboda iya Amatu kawai, amma ai kuna riƙe da ƴaƴanku ko? Marasa imani kawai, badan zuciyar musulunci ba ai bazan kalli yanda kuke ba tinda kuka kasa riƙe ɗiyar ƴar uwarku saboda bata da rai, kun ji kunya, yanzu kuma ko kunya babu kunzo wai batun auren zumunci, to baza'ayi baaa...." Malam yawale ya ce "To bamuda halin taimaka muku ya zamuyi? Shiyasa muka daina zuwa yanda kuke...ba gashi yanzu tayi arziki ba, nima dai inada iko akan Amatu, don haka sai anyi auren nan..." Zainabu ta tsoma baki cikin maganar ta ce: “Inna Delu, ba mu zo ne don mu tayar da hayaniya ba. Mun zo ne saboda mu gyara kuskuren da muka aikata a baya, mu tayar da zumunci, mu ba wa Amatu gida na gaskiya. Mun zo ne da niyyar taimako, ba da tada faɗa ba.” Malam Yawale yana jin zafi amma cikin nutsuwa ya ce: “Inna, gaskiya ba mu zo don mu yi ruɗu ba. Na san abin da kuka ji lokacin da iyayen Amal suka rasu, amma ni da matata, duk lokacin da muka yi tunani, zuciyarmu ta cewa mu taimaka. Ina son Amatu tun tana ƙarama. Yanzu da akwai damar a gyara, me ya hana mu haɗa Kabiru da ita? Zan riƙa kula da ita, in ba haka ba za ta ci gaba da zama a burni ita kaɗai a yayin da babu ranki..." Inna ta dafe goshi, idanuwanta sun cika da hawaye. Ta kalli Kabiru, ta ji raɗaɗi a ranta. Sai ta miƙe hannu ta ɗaga ƙofin shayin ta karɓa.. Inna ta yi sanyi sosai, ta tsinke muryarta da cewa. “Kun bar ta lokacin buƙata, kun guje ta saboda rashin dukiya yanzu kawai kun dawo saboda nufin ku ɗaura mata aure da ɗanku? Ai ni mahaifiya ne, na san halin da ƙasa take; Ba da sauri zan yarda ba, Malam Yawale. Zumunci abu ne mai tsarki; amma gina zumunci ya danganta da niyya, tausayin juna da gaskiya ba don abun duniya ba.” Malam Yawale ya kusanci Inna, ya yi magana da murya mai laushi da ƙarfin gwiwa ya ce “Inna, ina roƙon ki da zuciya ɗaya: ki yi la’akari da abin da zai faru da Amatu idan ta ci gaba ita kaɗai, ko da Aure zata yi dole fa sai an nemo ƴan uwanta, shin waye madaurin auren ta?. Ni ba zuzzurfan arziki nake nema ba; ina neman ‘yar uwa, ina neman wurin da za ta samu gida. Kabiru ba ɗan son duniya ba ne; yana da niyyar gaskiya. Inna, ki kalla zuciyarta ki nuna karamci. In ba mu yi ba, me zai faru da ita? Zamu haɗa zumunci ne domin ta samu gida, ba domin mu mallaki dukiya ba.” Inna ta rufe baki, idanuwanta sun yi ja. A gefen, Zainabu ta kalli mijinta ta ɗan matsa masa hannu: suna ƙoƙarin nuna jituwa. Kabiru ya yi ƙasa ya yi murmushi, sai ya tashi ya yi jinjina kai ya ce “Inna, ina roƙonki. Zan riƙa kula da ita saboda gaskiya ce a raina. Ba ni da wata buri sai kula da Amatu, mu gina mata gida mai cike da nutsuwa.” Halima ta ɗago itama ta ce “Inna, don Allah, ki ba mu dama. Mu za mu yi mata biyayya, mu kula da ita kamar matar gida.” Inna ta ɗan yi shiru, ta duba fuskokin su duka, ganin kyakkyawan niyya a idonsu ya sa zuciyarta ta ɗan sassauta, amma tana riƙe da ƙarfin magana ta ce: “Zan yi tunani, Malam Yawale. Ba zan ɗauka a sauƙaƙe ba. Ku ba ni lokaci nayi tunani. Kuma ku sani: idan kuka yi niyya na gaskiya, zan yi marhaba amma idan niyyarku ta sha alamar biyan buri ne kawai, to ku bar ni kawai. Kada ku yi tsammani na yarda da gaggawa.” Malam Yawale ya yi godiya, ya yi jinjina, Zainabu ta yi murmushi, Kabiru ya sunkuyar da kansa cikin godiya. Suka gyara zama, an dawo da yanayin hira amma a hankali, Inna kuwa ta nufi ɗaki ta zauna tana tunani... Anan ne bayan Inna ta zauna a ɗaki tana dogon tunani, tana ta kai komo tsakanin abin da zuciyarta ke so da abin da al’adun rayuwa ke ɗora mata. Bayan ta yi tunani, ta tashi ta fito falo cikin sanyin jiki. Dukkan su Malam Yawale suna zaune suna hira a hankali, Halima na wasa da ƙaramar wayarta, Kabiru kuma yana ta kallon ƙasa yana murmushi lokaci zuwa lokaci. Da suka ga Inna ta fito, duk suka gyara zama. Inna Delu ta zauna a kujera, ta kalli Malam Yawale sannan ta ce “To malam Yawale, bayan tunani mai zurfi da nayi… na yanke shawarar cewa babu laifi idan zumunci ya tabbata. Na amince da auren nan.” Malam Yawale ya ɗaga kai cikin farin ciki, ya saki murmushi mai nuna godiya. Malam Yawale ya ce “Alhamdulillah! Wallahi Inna Delu, kin faranta mana rai sosai. Wannan zumunci ba zai gushe ba in sha Allah.” Zainabu ta dafa kafadar mijinta da murmushi ta ce: “Na faɗa maka ai, Inna Delu mai zuciya ce. Allah ya saka da alheri.” Halima ta tafa hannuwa da murna tana faɗin. “Wai da gaske ne? Amatu za ta zama babbar yayata? Amma naji daɗi sosai.” Kabiru ya murmusa cikin jin daɗi, ya sunkuyar da kai yana jin kamar ya yi nasara mafi girma a rayuwarsa. Kabiru a hankali ya furta. “Alhamdulillah… zan nuna mata ƙauna fiye da yadda ta zata.” Sai kawai Inna ta ɗan gyara zama, ta miƙa hannu tana nuna alamar magana. Ta daidaita murya sannan ta ce “Amma ba ƙauyenku zata koma ba, ko? Ni ban yarda ku kai ta can ba.” Malam Yawale ya yi saurin girgiza kai da murmushi mai kwantar da hankali ya ce “Ke da kanki kin san yau zaman ƙauye ya zama tarihi gare mu. Mun bar can. Muna nan Abuja yanzu, kuma zamu cigaba da zama tare da ku nan kusa. Ba mu zo da zancen kai ta ƙauye ba.” Inna ta ɗan ɗaga gira tare da faɗin. “Too… kenan zaku cigaba da zama anan tare damu kenan?” Zainabu ta amsa kafin ma mijinta ya buɗe baki. “Eh ai duk mun taho da kayayyakin mu gaba ɗaya. Mun sayar da shanayen mu, mun siyar da gonakin masara saboda hidimar auren nan. Mun yi niyya da gaskiya. Wannan aure muhimmi ne a wurinmu.” Inna ta ɗan rintse ido tana murmushi amma zuciyarta ta yi nauyi. Ba ta so zama da mutane masu hayaniya ba, amma a wannan lokaci ta kasa yin musu magana mai zafi. Inna a hankali, tana numfasawa ta ce: “To Allah ya sa alheri. Amma fa ku sani, wannan gida ba wurin zazzafar hayaniya bane. Kowa ya san iyakarsa.” Malam Yawale da girmamawa ya ce. “Insha Allah, komai zai tafi da nutsuwa, Inna Delu. Mun gode sosai da wannan karɓa. Allah ya saka da alheri.” Kabiru cikin farin ciki, yana miƙa hannu ya ce “Inna, na gode sosai. Wallahi zan yi duk abin da zai tabbatar miki cewa na cancanci amincewarki.” Inna da ɗan dariya ta ce “To ka tabbata kana son ta da gaske, ba saboda ‘yar birni ce ba?” Kabiru ya ce: “Da gaske, Inna. Ba saboda burni ba, saboda ita ce wadda zuciyata ke gani har yanzu a mafarki.” Kowa ya yi murmushi. Falo ya cika da sanyin iska, amma a cikin zuciyar Inna akwai shakku, da tambayoyi da ba ta so ta faɗi a baki. Sai ta kalli ƙofa inda Amal ke saba shigowa da murmushi... sai kawai ta furta a zuciyarta: "Ya Allah ka shiryar da komai, ka kare ta daga abinda ba alheri ba..." Kwana uku kenan rabon da Amal ta fito daga cikin tsohuwar villa ɗin da Maleekh ya kulle ta a ciki. Wurin yana da yalwa, amma babu farin ciki, babu annuri sai tsananin shiru da bugun zuciya.... Amal tana zaune a kan kujerar falo, ta lumshe ido tana jin karar sautin agogo da ke bango “tick… tick… tick…” kamar yana ƙara mata damuwa. Idonta ya kumbura saboda kuka da rashin barci. A gefe kuma, Maleekh yana zaune a kan kujera mai launin duhu, gaban sa akwai laptop, yana danna keyboard ba tare da kallonta ba. Duk da haka, idonsa na bibiyarta lokaci zuwa lokaci. Amal a kasalance ta ce “Maleekh… sau uku nake tambayarka, har yanzu baka ce min me kake nufi da wannan tsarewar ba. Wannan ai kamar ɗauri ne.” Maleekh ya tsaya daga typing, ya ɗago ido yana kallon ta daga bisani ya ce “Ba ɗauri bane, Amal. Hutu ne. Hutu daga duniya, daga Zayd, daga duk wanda ke son shiga tsakaninmu.” Amal ta tintsire da dariya cikin takaici ta ce “Hutu? Hutu da kuka? Hutu da tsoro? Hutu da ƙunci? Wallahi kai ba ka sona, kana son mallakata ne kawai.” Maleekh ya miƙe tsaye, yana tafiya a hankali zuwa gareta ya ce. “Na fi kowa sanin abinda ke cikin zuciyata, Amal. Idan mallaka ce kike gani, to saboda bana so wani ya shiga cikin zuciyarki, ko da kuwa hakan yana nufin ki tsaneni.” Ya tsaya a gabanta, idonsa ya cika da zafin so. Hannunsa ya kai ya taɓa fuskarta, da sauri ta ja kanta gefe tana hawaye.. Amal cikin murya mai sanyi da zafi ta ce: “Idan kana son kare ni, to ka bar ni in zaɓi rayuwata da kaina. Wannan… wannan tsarewar ai azaba ce, ba kariya ba.” Maleekh ya janye hannunsa a hankali, ya koma ya zauna yana sauƙe numfashi. Sai shiru ya cika falon na tsawon mintuna. Sautin iska daga taga na ta kaɗawa. Daga nan sai ya ɗauki magana a hankali kamar wanda yake magana da kansa: “Na yi alkawarin bazan bar wani yaci zarafinki ba, bana son wani ya sake taɓa ki. Amma ki faɗa min gaskiya Amal…” Ya ɗaga kai yana kallonta kai tsaye cikin ido sannan ya ce “…me ke tsakaninki da Zayd. Har yanzu zuciyarki na rawa idan aka ambaci sunansa?” Amal ta girgiza kai cikin takaici ta ce “Babu komai tsakanina da shi! Wallahi babu komai. Sai dai ban san me yasa kai kullum kana ɗauka akwai wani abu ba…” Maleekh ya katse ta, cikin ɓacin rai.. “Saboda idan kika dubi idanunki a lokacin da yake kusa da ke, sai suyi kama da yadda suke kallona a da.” Amal ta share hawaye ta ce. “Ka manta ne? A da kaine ka fara juya idanunka daga gare ni.” Suka kalli juna na wasu daƙiƙu masu zafi, zuciyoyi biyu masu rauni, amma kowanne cike da ƙiyayyar soyayya. Maleekh ya lumshe ido, ya furta a hankali. “Na kasa tsoratar da ke kamar yadda nake so. Amma wallahi Amal, idan kika fita daga wannan gidan ba tare da iznina ba, sai duniya ta ga sabon Maleekh.” Amal ta miƙe tsaye tana kallonsa cikin kuka ta furta: “Duniya ta riga ta gani tun ranar da ka fara rufe ƙaunarka da fushi…” Ta juya ta shige ɗaki ta rufe ƙofa da ƙarfi... Daman wurin kwanciyarta cikin ɗakin can bedroom, shi kuma a kujerar falon.. Maleekh ya tsaya a tsaye yana kallon ƙofar da ta rufe, hannunsa na karkarwa. Sai kawai ya sau numfashi a hankali, yana furta “Ko da ke ce azabata, sai na kare ki daga duk wanda ba ni ba.” Washegari da asuba bayan sun yi sallah suka koma bacci, yanzu misalin ƙarfe 9 hasken safe ya fara ratsawa ta ƙofar window mai yalwa. Rana ta fara bayyana a hankali. Amal ta tashi daga kan gadonta, ba ta yi barci ba. Tun asuba zuciyarta ke sarƙaƙiya; tunanin Maleekh, da Inna komai ya rudeta.. A hankali ta miƙe, ta nufi tagar da take kallon harabar gidan. Wani ƙaramin tsuntsu ya tsaya a kan reshen bishiyar mango yana waka, kamar yana kiranta da “taho ki fita daga wannan zullumi.” Amal ta lumshe ido, ta furta cikin muryar da ke rawa: “Ya Allah… ban san me yasa soyayya ta zama kamar ɗaurin kurkuku ba.” Ta ɗauko gyalenta da ke kan kujera ta lullube jikinta da shi. Ta duba gefen falon, inda Maleekh ya kwana bisa kujera yana bacci a gajiye — laptop ɗinsa a gefe, hannunsa ɗaya a jikin kujera. Idonsa a rufe, amma yana numfashi da sauri, kamar wanda yake cikin mafarkin tashin hankali. Ta tsaya tana kallonsa na daƙiƙu da dama. Zuciyarta ta ƙuna tsakanin ƙauna da tsoro. Amal a cikin zuciya ta furta. “Ka ɗaure ni saboda kana son kare ni… amma daga me? Daga kai ne ko daga wasu?” A hankali ta fara matsowa da sauri, ta nufi ƙofar falon. Sai kuma ta tsaya ta dawo tana duba jikin kujerar Maleekh. A kan stool ɗin kusa da shi akwai makullai. Ta ɗan tsaya tana saurarar numfashinsa har yanzu yana bacci. Sai ta matso da sannu ta ɗauki makullin a hankali, ta riƙe a tafin hannunta... Amal a hankali, cikin zuciyarta ta furta. “Ka gafarce ni, Maleekh… amma sai na gudu daga wannan soyayyar da ta fi ƙauna zafi.” Ta nufi ƙofa, ta cire makulli tana ƙoƙarin buɗewa. A lokacin ne ƙaran “click” na makullin ya ɗan motsa. Maleekh ya motsa a hankali, ya buɗe idanu. Idonsu ya haɗu. A wannan lokacin lokaci kamar ya tsaya, iska na kaɗawa, zuciyoyi na bugawa. Maleekh da taushin murya mai cike da umarni ya ce “Amal… ina zaki je?” Ta tsaya a ƙofa tana rawar jiki, hawaye na silalowa a kumatunta. “Zan tafi gida… Zan koma wajen Inna.” Maleekh ya miƙe a hankali daga kujera, yana tafiya zuwa gareta. “Ba zaki tafi ba.” Amal ta ce: “Ka tsaya Maleekh… ka barni. Na gaji da zama cikin fargaba. Ka barni in tafi, wallahi zan dawo idan lokaci ya dace.” Maleekh ya tsaya da nisan matakai biyu daga gareta, idonsa a kanta ya ce: “Idan kika fita a yau, ki manta da ni gaba ɗaya. Kuma kar ki sake dawo da sunana a bakin ki.” Amal ta share hawaye sannan ta ce: “Idan hakan ne… to zan manta da kai, amma bana fatan na manta da ƙaunarka.” Ta buɗe ƙofa ta fita da gudu... Maleekh ya tsaya a tsaye yana kallonta ta bar gidan, jikin sa na rawa, idonsa cike da ƙwalla da zafin ɓacin rai. Ya daka tsawa yana furta: “Kin gudu a yau, Amal… amma soyayya ba ta da hanyar guduwa, zata dawo da ke gare ni.”... ☆☆☆☆☆ Ƙamshin turaren wuta ne ya cika falon lokacin da Amal ta shigo cikin gidan a hankali. Idonta cike da hawaye, amma a yau farin ciki ya fi fitarwa — ganin Inna bayan kwanaki huɗu a tsare. Amal ta murmusa tare da yo wa kan Inna. “Innaaa…” Inna da sauri ta miƙe, tana rungumarta... “Subhanallah! Amal! Ina kika shiga ne har kwanaki huɗu? Na kusa hauka fa!” Malam Yawale da murmushi amma cikin mamaki ya ce “Wani irin aiki ne haka da mace ke kwana huɗu bata dawo gida ba?” Amal ta kalli ƙasa, tana neman magana... “Ina… ni dai…” Inna tayi saurin katsewa cikin ladabi. “Aiki mana ya riƙe ta, Malam. Tunda ta fara wannan aikin dai ta shiga hannu sosai, sai yanzu ta samu hutu.” Malam Yawale yana girgiza kai ya ce “To ai Allah ya kyauta, amma mace ta san iyaka da fita. Kwana huɗu fa ba wasa bane.” Ya koma ya zauna, yana ɗan ɗaga rigarsa cikin nutsuwa. Inna ta kama hannun Amal, tana jan ta ciki: “Zo mu shiga ciki mana, ki sha ruwa ki huta, tukunna.” Suna shiga ɗaki, Inna ta rufe ƙofa, ta kalli Amal da idon tambaya. “Amal, yanzu fa ki faɗa min gaskiya. Ina kika tafi da Maleekh har kwanaki huɗu...?” Amal ta sauke numfashi, muryarta tana rawa ta ce. “Inna… ya tsare ni ne saboda kishi. Ba don komai ba. Bai yarda in fita ba, saboda wata magana da ya ji.” Inna ta ɗan numfasa, tana kallonta da tsantsar tausayi ta ce: “To ai kishi ba hujja bace ta tsare mutum, Amal. Amma yanzu ba wannan ba, saurara.” Amal ta ɗaga kai da fargaba ta ce: “Mene ne kuma, Inna?” Inna ta kalle ta a hankali sannan ta ce. “Sun zo ne Malam Yawale da iyalinsa da batun haɗa ki aure da yaronsu. Sun ce idan kin yarda, zasu cigaba da zama damu a nan har bikin ku ya yi kusa.” Amal ta firgita, idonta ya faɗa sosai ta ce: “Aure? Da yaronsu?” Inna ta gyara zama ta ce. “Eh mana, Malam Yawale ya faɗa da bakinsa. Da ma suna son hakan tun da daɗewa. Ni kuma ban ce komai ba, na ce sai na ji ra’ayinki tukunna.” Amal ta lumshe ido, tana jin zuciyarta ta buga kamar zatayi kuka ta ce: “Inna… ni kuwa Maleekh fa?” Inna ta kalleta kai tsaye ta ce. “Na san kin kamu da shi, amma kin ga irin halayensa. Kin ga irin duniyar da yake ciki. Ki yi tunani sosai, Amal, aure ba soyayya kawai ba ce, idan kika auri Maleekh baza ki taɓa samun kwanciyar hankali ba, domin duk iyalansa basa sonki, ga uwarsa ga kannensa da suka zo har gida suka miki dukan tsiya, sanadiyyarsu kika shiga hannun ƴan sanda, ki nutsu Amal, auren masu kuɗi bala’i ne gashi suna gadara da gidan da muke ciki ɗansu ne ya siya mana, kin ga wulakanci kuwa sai mun ture....” Amal ta durƙusa, idonta cike da hawaye ta ce: “Inna… wallahi ban san yadda zan yi ba. Zuciyata ta fi karfi na.” Inna ta dafa kafadarta ta ce “To ki natsu, ki bar komai a hannun Allah. Amma ki sani, rayuwa tana tafiya da hankali, ba da zuciya kaɗai ba.” Iskar yamma ta busa a hankali, tana ɗauke da ƙamshin hayaki daga kicin inda Zainabu ke dafawa. Rana ta fara faɗuwa, hasken ta ke ta ratsa gilashin windows na gidan da nutsuwa. Amal ta fito daga ɗakin Inna cikin doguwar riga, ta ɗaura veil ɗin kanta da nutsuwa, amma fuskarta cike da ruɗani da tunani. A can gefe, sai ta hangi Kabiru yana zaune a kan chair kusa da bishiyar flower, yana wasa da wayarsa. Fuskarshi mai cike da kamala, yana murmushi kamar wanda bai san komai ba. Zainabu ta fito tana faɗin. “Kabiru, ina ƙanwarka Halima ta kawo muku kunu, ku sha kafin abincin yamma.” Kabiru yana murmushi ya ce: “Na gode Mama, amma dai sai mu ci gaba da zama lafiya a gidan nan, ko?” Zainabu da murmushi ta ce: “Insha Allah, ai yanzu dai mun zama dangi ɗaya. Komai Allah ya haɗa.” Sai Amal ta ƙaraso a hankali, ta tsaya tana kallonsu. Zainabu ta hango ta ta ce: “Ai gata nan fa Amatu. Zo nan yarinya, kin huta koh” Amal ta ɗan yi murmushi mai nauyi sannan ta ce. “Eh, Alhamdulillah.” Kabiru ya tashi tsaye da murmushi mai cike da fara’a ya ce: “Sannu da dawowa, Amatu. Na jima ina son in ganki. Sun faɗa min labarinki sosai.” Amal ta ɗan ɗaga kai cikin ladabi ta ce: “Na gode.” Kabiru yana kallonta ya ce “Mama tana ta cewa mu ne muka dace, saboda zumunci. Amma ba lallai kina ganin hakan ne, ko?” Amal ta yi shiru, tana kallon ƙasa sannan ta ce “Ni ban san me zan ce ba… komai yanzu sai abunda iyaye suka tsara...” Kabiru ya matso da murya a hankali ya ce. “Ni dai bana son a ce an tilasta miki. Amma ina fata ki gane ba wai aure kawai nake nema ba, ina son a riƙa zama da juna lafiya, kamar ‘yan uwa cikin mutunci. Na ga yadda kike da kunya, ina girmama hakan.” Amal ta ɗan yi murmushi mai rauni ta ce “Na gode Kabiru. Allah ya saka da alheri.” Sai shiru ya rufe tsakanin su, iska na kaɗa flowowin wurin... Sai dai a zuciyarta, Amal tana ji kamar ta kulle kanta ta yi kuka. Domin ko da Kabiru yana da halin kirki, har yanzu hoton Maleekh bai bar kwakwalwarta ba. Daga nesa, Inna ta leƙo daga window tana kallonsu, zuciyarta cike da damuwa da shakku tana so ta ga farin cikin ‘yarta, amma tana jin tsoron cewa soyayyar Amal da Maleekh zata kawo bala’i. Washegari da safe.. Rana ta fito. Falo cike yake da mutane Inna Delu, Malam Yawale, Zainabu, Kabiru, Halima, da Amal wacce take zaune a gefe cikin nutsuwa amma fuskarta cike da damuwa. Ammy ce ta shigo gidan cikin sheƙin kaya, da ƙamshin turarenta mai ƙarfi. Tana rike da jaka mai tsada, fuskarta cike da ɗaga kai da girmankai. Maigadi ya biyo bayanta yana gaisuwa, tana amsa kai tsaye da ƙasƙantacciyar murya. Da zarar ta shiga falo, idanunta suka tsaya akan Amal. Ammy cikin ɗaga murya ta ce. “To, ashe nan kika ɓuya? Shine kika janye ɗana daga gida, kika mai da shi ɗan wahala, ashe kina nan kina zaune lafiya!?” Inna ta ce “Subhanallah, Hajiya, lafiya kuwa? Kamar dai baƙuwa ke ba! Me yasa ki shigo gidan mutane haka kina ɗaga murya kamar a kasuwa?” Ammy ta harari Inna tare da faɗin. “Ba magana nake da ke ba, tsohuwa! Ke dai kin iya boye ‘yar marainiya a nan, to indai kinada hankali, ki gaya mata ta bar ɗana, kar na manta asalin ta…” Ta kalli Amal da ɗan murmushin raini. “Kin ji ni ko, yar talakawa, jikar matalauta! Indai kinada zuciya to ki fita daga rayuwar yaro na!” Amal ta miƙe a hankali, tana kallonta kai tsaye cikin ido ta ce “Yaronki ne yake cikin rayuwata, ba ni ba. Don haka idan kin isa dashi ki dakatar da shi daga shiga rayuwata.” Ammy ta yi dariyar raini ta ce. “Hahaha, baki san kanki ba! Ke ce kika jawo rikici a cikin iyalai na. Kin faɗa rayuwar Zayd ma, sai kuma ki haɗa ƴan uwa fada? Maleekh ya daki ɗan uwansa saboda ke, kina so ki haɗa fitila a tsakaninsu ko?” Amal ta haɗe hannuwanta a kirji ta ce “Na bar komai ga Allah. Ni bana neman su. Su suke shiga rayuwata, ai ke uwarsu bai kamata ki yi mun jan kunne akansu ba, sai ki tuntubi yaranki ki ji...” Ammy ta harareta, murya ta ɗan karye saboda ɓacin rai ta ce. “Wato ke baki da kunya koh? Ni kike ɗaga mury? A gaban kowa?” Inna ta tashi tsaye cikin tsawa ta ce. “Ke! Ki kiyaye bakinki. Wannan gidan ba gidan ku bane. Idan baki da girmamawa, mu muna da shi. Ku kuna da arziki, amma baki san kanki ba! Ba komai sai girman kai da raini.” Malam Yawale cikin tausasawa ya ce. “Yar uwa, don Allah ku natsu...” Zainabu ta ce “Allah ya sa ayi zaman lafiya. Aure fa a hankali ake tattaunawa, ba da faɗa ba.” Inna ta ɗaga kai da izza ta ce: “Eh! Amal aure zatayi, zata bar Maleekh da shi Zayd ɗin. Ga wanda zata aura ɗan uwanta Kabiru.” Ammy ta ɗaga hannu cikin farin ciki ta ce. “To Alhamdulillah. Idan aure ne, ai ni na fi kowa farin ciki. Auren ya zama hanya ta rabuwa. Ke Inna, kina cewa za ku aura mata ɗan uwan ta ne?”.. Inna ta ce "Eh gashi nan kuwa..." Ammy ta ce "Ai abinda nake nema kenam, nesa tazo kusa, daman ai Amal bata yi kala da yarana ba, ko da wasa kalar zaren ba kalar yadin bane, sun fi ƙarfin ta....kin ga kuwa talaka sai talaka, mai kuɗi sai mai kuɗi..." Kabiru ya tashi a hankali, yana kallon Amal da murmushi mai nauyi ya ce. “Ni ne Kabiru, Ba da gaggawa ba, amma idan Allah ya yarda, zamu zama dangi ɗaya.” Ammy ta murmusa da mamaki ta ce. “Alhamdulillah! Allah ya sanya alkhairi. Na fi kowa farin ciki, domin Maleekh da Zayd suma sunada wanda zasu aura. Ba matsala, ga ka kaima shushushu kamar ita, duk dai haka za'a ƙare da talauci...” Zainabu ta ce "Ai wannan gidan yafi ace gidan talaka ne, domin a masu rufin asiri ma da wuya su mallaki irin wannan kyawun gidan.." Ammy ta kwashe da dariya tare da faɗin. "Ohhh Ɗan ƙauye yazo birni, wato babu kalar wannan gidan a ƙauyenku ko? Daman taya zaku samu ƙauye duk bukkoki..." Malam Yawale shima ya ce. "Da za ki dubi asalinki kema talaka ce..." Ammy tayi saurin cewa. "Tirrrrr, wallahi ƙarya ne, ku je ku binciki asalina, ban tashi cikin talauci ba, kaff zuriya ta babu talaka..." Kabiru ya ce. "Amma Amatu itama ba talaka bace, du bi gidan da take zaune..." Ammy ta harare su tare da faɗin. "Abar dai kaza cikin gashinta, amma arzikinsu bai isa siya musu gidan anan ba..." Ta juya tana hararar Amal ta fita cikin izza.... Bayan ta fita, Amal ta durƙusa a ƙasa tana hawaye. Inna ta tsaya ta kalleta cikin tausayi, sannan ta ɗan juyo ga Malam Yawale: Ta ce. “To ga yarinyar nan, kuje ku shirya yadda kuke so. Amma wallahi ni har yanzu zuciyata ba ta so wannan auren…” Malam Yawale ya ce: “Allah ya shirya, Inna Delu. Komai da lokacinsa. Amma mu ba da mugunta muka zo ba. Dubi wannan matar da ta zo ta wulakanta ku akan yaronta, shin haka za'a aurar da Amatu a danginsu?...” Ɓangare Maleekh.. Maleekh ya kashe wayarsa gaba ɗaya yanda babu wanda zai same shi... Bayan kwana biyu ansa ranar bikin Amal, sauran sati ɗaya... Abbah ne ya ziyarci Amal, ya zauna a falo shi da Amal su biyu, ta durƙusa ta gaishe shi... Ya gaisa da sauran mutanen gidan har da Inna, daga baya aka basu wuri.. Anan Abbah yayi mata fatan alkhairi akan bikin da zata yi. Yayi mata nasiha akan ta dage da addu’a, ta zauna a gidan mijinta lafiya tayiwa mijinta biyayya. Sannan ya bata hak'uri akan wulakanci da Ammy ta zo tayi musu domin a shigowarsa Inna ta sanar masa.. Daga nan Abbah ya roƙe ta akan ta sanar masa yanda Maleekh yake. Amal ta sanar masa yana old villa... Daga nan sukayi sallama. Abbah kai tsaye ya wuce can yanda Maleekh yake.. Abbah ya sameshi shi kaɗai a daji yana rayuwarsa.. Dare ne, fitilar villa kawai ke haske. Maleekh na zaune a waje, cikin sanyi, yana kallon sararin sama. Fuskar sa cike da tunani da gajiya. Sai ga security ya kawo Abbah... Security yayi sallama sannan ya ce. “Sir, ga babban Alhaji, Abbah…” Maleekh Ya miƙe da mamaki ya ce. “Abbah?” Abbah Ya karasa kusa da shi, yana kallonsa cikin kulawa ya ce “Eh, ni ne, yaro na. Na ji shiru baka koma gida ba, shine na zo in ganka da kaina.” Maleekh ya sauƙe numfashi sannan ya ce: “Abbah... bana so kowa ya damu da ni. Nayi nisa da rayuwar mutane, yanzu ina so in huta kawai, daga komai aiki, soyayya, tashin hankali, komai.” Abbah ya zauna kusa da shi, cikin tausasawa ya ce. “Na gane, amma hutu ba yana nufin gudu daga gaskiya bane. Rayuwa bata tsaya saboda ciwon zuciya, Maleekh.” Maleekh ya juya gefe yana kallon wuta. “Ba ciwon zuciya bane, Abbah… wannan yanke zuciya ne. Na rasa amincewa da kowa. Kowa yana neman wani abu daga gare ni. Amma ni ina neman nutsuwa kawai.” Abbah ya girgiza kai sannan ya ce. “Yaro na, kai namiji ne, kuma jagora. Ka koyi rike kanka. Amma kar ka kulle kanka a cikin daji kamar wanda ya gudu daga duniya. Na zo ne don in tabbatar da kana lafiya, ba don in tilasta maka komai ba.” Maleekh ya ce. “Abbah, ina da bukata ɗaya…” Abbah ya ce “Meye hakan?” Ya ce. “Ka bar ni a nan. Kada ka sanar wa kowa inda nake, hatta Ammy. Inason in huta. In har zuciyata ta dawo daidai, zan dawo da kaina.” Abbah Ya yi shiru na ɗan lokaci sannan ya ce cikin natsuwa. “To, idan hakan zai ba ka kwanciyar hankali, zan yarda. Amma ka ɗauki tsaro. Zan bar maka maza biyu su taimaka maka a nan.” Maleekh Ya ɗan murmusa kaɗan sannan ya ce. “Nagode, Abbah. Ka san kai kaɗai ne mutum ɗaya da zuciyata bata iya ɓoye masa komai.” Abbah Ya dafa kafaɗarsa “Karka manta da addu’a, Maleekh. Idan ka rasa kowa ka nemi Allah, zai baka nutsuwa fiye da duniya baki ɗaya.” Abbah ya miƙe, ya kalli villa sannan ya fita cikin shiru. Maleekh ya zauna yana kallon fitilar villa, idanunsa suka cika da hawaye, yana furta a hankali: “Amal... kin mayar da zuciyata gurɓatacciya… amma har yanzu... ina ji a jikina ba zan iya manta ki ba.” Kwana biyu daga baya, ana gefe ana cigaba da shirye-shiryen bikin Amal da Kabiru, yayin da Maleekh ke zaune cikin dajin, ba tare da sanin komai ba. Wannan ya ƙara sanya bambanci tsakanin natsuwar da yake nema da rikicin da duniya ke shirya masa daga nesa... NEXT NEXT NEXT... asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 55 to 56 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 A wannan rana ne kafin bikin Amal, Zayd da jin Amal zata yi Aure ya tayar da hankalinsa, sai gashi ya danna burki a ƙofar gidan cikin tashin hankali... Knocking ya rinƙa yi maigadi ya buɗe masa, kafin maigadi ya yi wani magana Zayd ya fuu ya wuce ciki, sallamarsa shine "Pretty! Pretty!! Pretty ki fito, please ki fito. Pretty..." Kabiru wanda yake bayi a flowowi ganinsa yasa ya dakata yana kallon Zayd wanda ya rikice.. Amal kuma daman a falo take zaune tana kallo, jin ƙira kuma alamun sun nuna mata Zayd ne, domin shine mai ƙiran ta da sunan..ta fito ta tsaye daga nesa, ta takarƙare cikin kayan gida masu launin shudi. A hankali ta tako zuwa yanda yake kamar zai yi kuka... Zayd cikin rawar murya, fuskarsa ɗauke da fushi ganinta yasa shi faɗin: "Pretty… why? Kin tsani zuciyata haka ne? Kin manta da ni, da duk abinda ke tsakanina dake? Kin manta fa da soyayyar da na gina tun kafin duniya ta fahimceni.." Amal cikin nutsuwa idanuwanta cike da hawaye ta ce: "Zayd… soyayya ba ta isa ta rushe kaddara ba. Idan Allah ya rubuta abin da zai faru, babu mai canzawa. Ban tsane ka ba, amma wannan ba ƙaddarata bace. Kuma ai ba wai soyayya muke ba, ni na ɗauka mutunci ne a tsakanin mu, kuma taya zanyi soyayya da kai har kayi tunanin zan aure ka alhalin kana tare da Maleekh kuma ɗan uwanka ne, bari yau na sanar maka da baki na, ka riƙe a kwakwalwarka cewa 'Maleekh shine zuciyata, kuma wanda na so, wanda nake so har zuwa yanzu, ni ce yarinyar da ya yi break-up da ita..." Zayd yana matsowa kusa, muryarsa na rawa ya ce: "Na sani ai, Maleekh ɗin shi zai hanani soyayya da ke ne? Ba nono ɗaya nasha da shi ba balle kiyi tunanin wani abu, ni yanzu ba wai akan Maleekh nazo magana akai ba, tinda shima bata shi kike ba, aurenki zaki yi, kina cewa ƙaddara. To meye ƙaddararki? Wannan ɗan ƙauyen? (ya nuna Kabiru da yatsa) Wannan ne kika zaɓa akan ni, bayan na mayar da zuciyata gida gareki? Amal, kin fi haka wallahi!..." Kabiru da ɗan zafi yana nuna Zayd da yatsa shima ya ce: "Kai fa… ka kiyaye harshenka! Ni mijinta ne nan gaba, kuma ba ka da ikon tsoma baki a rayuwarta. Ka fita da mutunci kafin ka rasa shi.." Zayd ya doke hannun Kabiru gefe yana faɗin: "Mijin me? Ka san me ake nufi da love kuwa? Ka san menene ruwan da ke gudana a cikin jini idan zuciya ta kamu da kauna? Ba zaka fahimta ba, kai dai ka zo ne daga ƙauye da niyyar mallake abinda baka gina ba!.." Amal ta ɗaga hannu cikin tsawa ta ce: "Zayd! Ya isa haka. Ka girmama kanka. Ban taɓa rainaka ba, amma kar ka zubar da mutuncinka saboda ni. Ka dawo da hankalinka, Zayd — duniya fa ba ƙarama bace. Bayan ni akwai wasu..." Zayd yana murmushi cikin ciwo ya ce: "Duniya ba ƙarama bace, amma ni ma ba ƙaramin so nake miki ba, Amal. Ba zan iya jure ganin wani ya ajiye hannu a kan abinda zuciyata ta amince da shi ba..." Amal tana hawaye, ta sassauta murya, ba komai ta tuno ba illa Maleekh, ta ce: "To ka jure, Zayd. Domin rayuwa haka take tana koya mana haƙuri ta hanyar rashi. Ka bar ni na natsu. Allah zai baka wadda tafi ni a gareka.." Zayd ya kasa daurewa, ya kauda kai yana jan numfashi ya ce: "Wadda tafi ki? Babu wadda zata maye gurbin Pretty a zuciyata. Amma... (ya ɗaga kai yana kallonta da ido) …ki sani, ko da kin auri wannan ɗan ƙauyen, soyayyarki ba zata taɓa mutuwa a cikin zuciyata ba. Har abada..." Kabiru yana tunkararsa cikin zafin rai ya ce: "Ka fita kafin na sa ka fita da ƙarfi, munafukin burni!..." Zayd yana murmushi mai ciwo, yana tafiya zuwa ƙofar fita ya ce: "Ba sai ka tura ni ba Baƙauye... Sai dai ka kula da ita, kar ka karya mata zuciya kamar yadda na bari tawa ta karye..." Ya juya yana kallon Amal a karo na ƙarshe. Ya ce "Goodbye… Pretty...." Zayd ya fice cikin hanzari, ya buɗe ƙofar da ƙarfi ya buga ta da ƙarfi. Amal ta tsaya cak tana kallo, hawaye na zuba a fuskarta. Kabiru ya kalleta da damuwa, amma ta kauda kai cikin shiru.... Kafin Kafin Kabiru yayi magana ta juya da gudu ta koma ciki... 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🩷🩷🩷🩷🩷 🌹🌹🌹🌹 An hallara a wurin event, an ƙawata shi da fitilu masu walƙiya, ƙamshi ya cika wurin, kowa cikin ado da farin ciki, sai kiɗan walima da yake tashi a hankali.. Aisha (ƙawar Amal): ta matso kusa da Amal tana murmushi ta ce. “Amal kin zama kamar sarauniya wallahi, wannan gown ɗin ya karɓeki fiye da kowacce mace da na taɓa gani.” Amal ta ƙara gyara zaman gyalen tana murmushin ƙarfin hali, ta ce: “Aisha… wallahi ban jin daɗi. Babu wanda yasan halin da zuciyata ke ciki. Na rasa Maleekh… wayarsa a kashe, ban san meya faru da shi ba.” Aisha ta ce: “To, amma ki daure. Karki bari kowa ya fahimci kina cikin damuwa, kowa yana kallonki a matsayin amarya mai sa’a.” Amal ta ɗan lumshe ido cikin murya mai rauni ta ce: “Sa’a fa kika ce? Idan wanda zuciyata ke nema baya tare dani, meye amfanin wannan shigar, wannan walimar?” Aisha ta ja numfashi sannan ta ce: “Ki bar komai a hannun Allah. Wataƙila Maleekh zai bayyana kafin auren. Ban yarda zai iya ƙyale ki ba.” Amal ta ce: “Na roƙi Allah haka, Aisha. Amma har yau sati guda… babu labarinsa. Da na san haka zai faru, da ban barshi a can ba.” Aisha ta riƙe hannunta tana rarrashi... Aisha ta ce: “To yanzu dai ki yi haƙuri, karki ɓata mana taro. Ga kowa yana kallonki. Abbah ma yana wurin shima yana alfahari dake kamar ƴarsa ta jini.” A wannan lokacin Zayd ya shigo wurin event ɗin cikin suit mai tsada, idonsa cike da ɓacin rai. Farha ta hango shi ta ce da Islam da Arfat... Farha ta ce: “Ga Ya Zayd can, amma ya rame, kamar wanda bai san abin da yake yi ba.” Islam ta ce itama: “Ai duk saboda Amal, ya kasa manta ta, bai san duk soyayyarsa da Amal bai kai Yayana Maleekh ba...” Arfat ta ce: “To ai yanzu ta zama matar wani, sai su haƙura...” Zayd ya tsaya nesa yana kallon Amal cikin gown ɗinta, zuciyarsa na tafasa. Ya furta a hankali cikin haushi... “Pretty… kina ta haskawa a gaban kowa, amma baki san zuciyata tana ƙone ba.” Abbah ya hau kan stage yana ɗaukar mic, cikin murya mai cike da natsuwa ya furta.. “Assalamu alaikum jama’a. Na ƙira wannan walima ne domin bikin yarinya da na ɗauka kamar ƴa ta. Amal kyakkyawar yarinya mai tarbiyya da ladabi. Allah ya sanya albarka a rayuwar aurenki, ya muku albarka, ya sa zaman lafiya.” (Kowa ya amsa da “Amin!”) Ammy, Farha da Islam da Arfat suna zaune a tsararrun kujeru, Ammy ta ce cikin murya mai kaushi... “Ai na fi kowa farin ciki yau. Wannan itace ranar da Maleekh zai farka daga mafarki. Yanzu yasan babu Amal a gare shi.” Farha ta murmusa sannan ta ce: “Zan je na gaishe ta, in ga yadda take da wannan farin cikin ƙaryar...” Ta tashi ta ƙarasa wajen Amal da murmushi... Cikin izza ta ce da ita. “Amarya, kin yi kyau sosai. Amma kin san duniya juyawa take. Wasu lokutan abin da muka tsaya akai sai ya wuce mana.” Amal ta kalleta kai tsaye cikin idanu sannan ta ce. “Eh, haka ne. Amma kuma akwai wasu abubuwa da idan suka shiga zuciya… ko da duniya ta juya, ba sa fita.”.. Farha ta ɗan yi dariya ta juya ta koma wajensu Ammy... A wannan lokacin kabiru yana gefen Amal yana ƙoƙarin riƙe hannunta amma ta ja hannunta gefe, idonta ya cika da hawaye. Aisha ta lura da hakan... Aisha ta ce: “Amal, ki daure, mutane suna kallo. Kada ki nuna rauni.” Amal ta ce cikin muryar da ke karyewa. “Ba zan iya ɓoye damuwata ba Aisha. Wannan walimar ana yi ne, amma zuciyata tana tafasa. Waye ya san halin da nake ciki?” Aisha ta rungumeta tana faɗin “Shhhh…” tana rarrashinta. Kiɗan ya sake tashi, jama’a suna murna, amma a zuciyar Amal kamar ana binne mata rai a raye… Cikin babban hall ɗin da aka kawata da haske da kyalli, sautunan walima da kiɗa na tashi a hankali. Kowa cikin farin ciki yake. Amal tana zaune gefenta Inna ce, fuskarta ba yabo ba fallasa duk da ta yi kyau fiye da yadda aka taɓa ganinta, zuciyarta na cike da nauyi... Inna da murmushi tana kallon jama’a ta ce. "Yau fa Allah ya tabbatar da burina. Gashi dai Amatu na ta zama Amarya.” Halima ƙanwar Kabiru, itama ta sha kyau sosai.. Cikin wannan shagalin ne aka ji ƙarar ƙofar waje ta buɗe da karfi “BAAANG!” aka tsayar da kiɗan. Mutane suka juya da mamaki... Arfat a tsorace ta furta: “Wayyo Allah, meye haka? Waye ya buɗe ƙofa haka kamar ana faɗan daji?” Farha ta ɗan saki kofin hannunta, ido a buɗe ta ce: “Wait... na gane wannan buɗewar...!” Cikin hayaƙi da ƙamshin turaren da aka saba jin yana biyo shi, Maleekh ya shigo. A sanye yake cikin baki suit, fuskarsa ɗaure, idonsa jajur kamar wanda bai taɓa bacci ba. Mutane suka fara yin kakkauce wa kamar hanya ta buɗe da kanta... Wani daga cikin ma’aikata a hankali ya furta: “Wannan fa Maleekh ɗin ne... oga Maleekh ne...” Abbah ya miƙe da mamaki, yana tsoron yadda zai kasance: “Subhanallah... Maleekh?” Idanun Maleekh suka sauƙa kai tsaye kan Amal, tana zaune gefen Aisha da Inna, a ɗayan gefenta kuma Kabiru ne.... Shi kaɗai yake gani hasken hall ɗin, sautin mutane, komai ya daina motsi a kunnensa... Maleekh a zuciyarsa, cikin murya mai zafi ya furta: “Amal... har kike iya yin aure ba tare da kin ce min komai ba? Bayan soyayyar da na ba ki?” Amal ta miƙe a zabure. Ta kasa tsayawa. Cikin zuciyarta kamar ana ja mata rai da zafi. Ta tattara doguwar rigarta mai sheƙi, ta fara gudu kamar wacce ta tsere daga mafarki... Kai tsaye wurin da Maleekh yake tsaye ta nufa. Tana ƙiran sunansa cikin kuka.. “Maleekh! Maleeeekh!!” Mutane suka ɗaga kai suna kallon ikon Allah. Halima ta riƙe hannun kabiru tana faɗin "Ya salam!"... Zayd kuwa ya tsaya a gefe yana kallo kamar wanda ake caccakar zuciya da wuka... Kabiru ya tashi tsaye da mamaki yana faɗin. “Wannan kuma waye, meye haka?” Zaynabu ta dafe ƙirji ta ce: “Laa ilaha illallah, wannan ai kamar amarya ta san shi sosai…” Kafin a iya hanata, har ta ratsa cikin taron ta isko shi, ma’aikata da mutane suka tsaya suna kallonta. Ta isa wurin ƙofar tana kuka, ta faɗa cikin jikin Maleekh, ta rungume shi da duk ƙarfinta tana kuka sosai.. “Ka barni haka… ka tafi ka ɗaure ni da kewar ka… me yasa baka dawo ba, Maleekh?” Maleekh ya tsaya kamar dutse, hannayensa a buɗe. Sai kuma a hankali ya rungumeta, zuciyarsa na harbawa da ƙarfi, ya ce a hankali cikin murya mai sanyi da raɗaɗi: “Na dawo, Amal… na dawo kafin wani ya karɓe min ke…” Amal tana rungume da shi murya na rawa ta ce: “Maleekh... bazan taɓa manta wa da kai ba... wallahi bana son wannan auren...!” Maleekh ya dafa kanta, cikin murya mai ƙarfi mai cike da ƙauna yana furta: “Na sani... bana buƙatar jin komai daga bakin kowa, Amal. Ke tawa ce — har yanzu, har abada!” [Kowa cikin mamaki yake kallo, wasu suna sharar hawaye, wasu kuma suna ƙaraɗa ido. Abbah ya sauƙe numfashi da ƙarfi. Ammy kuwa ta zuba masa ido cikin tsoro da fushi. Zayd yana matse haƙora, yana faɗin cikin takaici: “Daman... dama duk bata son mu. Ni da wannan da take cewa za ta aura. Dama zuciyarta tana wajen shi!” Farha ta dafe kanta tana hawaye ta ce: “Na faɗa muku! Wallahi wannan Amal ba mace bace... aljana ce kawai ta ɗaure masa kai!” Abbah a hankali ya je kusa da Maleekh ya ce: “Maleekh... ka yi hankali da abinda kake aikatawa. Wannan ba lokaci bane...” Maleekh yana kallo cikin idon Amal ya ce: “Abbah, lokacin da aka ɗauke min ita babu wanda ya tambaye ni. Yanzu kuma, ni ne na dawo domin karɓar abina.” Amal ta dafe kirjinta tana kuka tare da faɗin: “Dan Allah, kar ka sake bari na, Maleekh... kar ka barni...” A hall ɗin kuwa hayaniya ta tashi. Ma’aikata da manyan baki suna ta magana, wasu na cewa a katse bikin, wasu kuma suna cewa “Soyayya kenan.” Kabiru yana kallo cikin ɓacin rai ya ce: “To ni fa, me kuke nufi? Auren fa nawa ne... amma yanzu sai gashi an kwace min amarya a gaban jama’a!” Halima ta ce a hankali, tana kallon Kabiru: “Yaya Kabiru... ni dai ina gani... wannan soyayyar ta fi ƙarfin ka.”.. Zayd ya buɗe baki yana huci, fuska cike da ɓacin rai, sai furta kalma ɗaya yake: “To yanzu gaskiya ta fito fili… Ashe daga ni har shi ango bata sonmu… saboda shi ne a zuciyarta tun farko.” Kabiru ya ɗaga kai cikin ɓacin rai ya kuma cewa: “Wannan wace irin raini ne kuma a bikin aure? Wannan yarinyar ba ta da kunya!” Inna ta taso cikin tashin hankali, tana faɗin: “Amatu! Me kike yi haka a gaban mutane?! Ki sake shi ki dawo nan!” Amal ta girgiza kai cikin hawaye, ta ce cikin murya mai rawa: “Ba zan sake shi ba Inna… saboda shi ne zuciyata, shi ne rayuwata!” Maleekh ya ƙara matse ta a jikinsa, yana kallon kowa a hall ɗin da idanu masu tsanani. “Wanda bai ji ba yaji, Amal tawa ce… kuma zata zauna dani… babu wani aure da za’a ɗaura.” Wurin ya hargitse. Farha ta zaro ido tana faɗin cikin jin haushi: “Ashe har yanzu bai bar ta ba! Wallahi wannan abun ya isa haka!” Ammy ta miƙe a fusace, ta ce cikin tsawa: “Maleekh! Karka raina mana hankali! Kai baka da hankali ne? Wannan talaka ce, baka isa ka tozarta iyayenka saboda ita ba!” Amal ta ɗago kai tana share hawaye ta ce: “Ammy, wallahi ban tozarta kowa ba, ni dai ina son Maleekh, kuma shi ne ya dawo gareni.” Abbah ya tashi tsaye, yana ƙiran sunan Maleekh cikin natsuwa: “Maleekh... ya isa haka. Kowa yana kallo, wannan abin da kuke yi a bainar jama’a ba dai-dai ba ne.” Maleekh ya ce da muryarsa mai zurfi: “Abbah, ni dai na faɗi gaskiya. Bana buƙatar auren Amal da wani. Idan hakan za ta faru, to wallahi sai dai ku ga gawata.” Amal ta kalle shi tana kuka, zuciyarta cike da ruɗani da tsoro, tana faɗin cikin rauni: “Ka rage zafin rai, Maleekh… don Allah ka saurare su…” Maleekh ya riƙe hannunta sosai ya ce: “Zan saurare su, amma ba zan sake ki ba.” Shiru ya sake ratsa hall ɗin. Kowa na kallo. A yau, walimar aure ta koma farkon rikicin soyayya, alfahari, da zafi sun gauraya cikin zuciyoyin jama’a... Da ƙyar Abbah ya ja Maleekh da Amal suka koma gida.. A babban falon gidan Amal suka hallara gaba ɗaya, bayan taron an watse. Iska tana busowa daga window, ɗan ƙamshin turaren flowers da aka kawata da su ya cika ɗakin. Amma babu wanda ke jin daɗin zaman. Abbah ne ya zauna a babban kujerar tsakiyar falo, yana kallon Maleekh da Amal da suka zauna a gefensa. Inna da Malam Yawale suna gefe, Zainabu na lulluɓe da mayafi, Kabiru kuma yana zaune yana murɗa yatsunsa cikin rashin haƙuri. Abbah ya gyara murya, ya ce da nutsuwa: "To yanzu, tunda kowa ya zauna, ina so muyi magana cikin natsuwa. Wannan abin da ya faru yau, abu ne da ya girgiza ni. Amma ina so mu magance shi ba tare da tashin hankali ba. Maleekh, ka nutsu ka saurare ni." Maleekh, da fuskarsa a haɗe, ya ce cikin tsananin murya: "Abbah, me kake so in saurara? Bayan gobe za’a ɗaura wa Amal aure da wani? Amal ɗina? A gabana?" Amal ta sunkuyar da kai, hawaye na gangarowa a fuskarta ta ce: "Ina ruwana da duk wani abu da suka tsara, Abbah wallahi ban amince da wannan auren ba. Wallahi ni bana son Kabiru, kuma bana son in aure shi!" Inna ta kalle ta da mamaki ta ce: "Ke Amatu, baki da kunya? Wannan magana ce zaki furta a gaban manya? Ai ni da bakina na amince da wannan auren, kuma sai da na sanar miki kema, Meyasa tun farko baki ce bakya so ba? Sai da wannan yaron Maliku yazo ya hure miki kunne zaki mana tawaye? To wallahi auren nan ba fashi kin kuma san ikon da nake da shi a kanki." Malam Yawale ya shigo cikin magana yana ɗan ɗaga murya ya ce: "To ai dole ne a yi aure, auren zumunci kenan. Tunda mahaifiyarki da mahaifinki sun rasu, mu ne iyayenki yanzu. Kuma wannan aure dole ne ayi shi." Maleekh ya tashi daga inda yake zaune, ya tsaya a tsakiyar falo, idanunsa sun canza launi kamar wanda ya daɗe da rashin bacci...cikin fusata ya ce: "Ba za a yi ba! Ba za a taɓa ɗaura mata aure da wani ba, tunda ina raye!" Zainabu ta ce cikin tsoro: "Subhanallah! Wannan yaro fa yana da zuciya kamar wuta. Waye kai da zaka hana aure da doka ta tabbatar?" Kabiru ya miƙe shima yana kallon Maleekh da fushi ya ce: "Wato kai ne kake hana auren? To ka sani, ko kai waye, ni dai bazan haƙura da Amal ba. Na ɗauki alkawari, gobe da safe za’a ɗaura auren nan, sai meye?" Maleekh ya yi murmushi mai sanyi, idanunsa sun cika da fushi ya ce: "Za’a ɗaura aure a kan matata? Kai,(yana nuna Kabiru) sannan yace "ka shirya, saboda idan aka yi hakan wallahi a ranar sai dai a zubar da jini!" Amal a zabure ta miƙe ta riƙe hannunsa cikin kuka ta ce: "Dan Allah Maleekh ka tsaya, ka bari muji me Abbah zai ce..." Abbah ya miƙe da kansa, yana duba duka fuskokinsu cikin girmamawa da ƙasaita ya ce: "Na fahimci akwai son juna a tsakaninku. Amma Maleekh, ka saurare ni. Amal yanzu tana ƙarƙashin ikon waɗannan, kuma aure a musulunci yana bin hanya da izinin iyaye. Na roƙeka ka haƙura har sai an samu mafita. Kada ka yi abu da zaka yi nadama." Maleekh ya juyo da idonsa yana kallon Abbah, hawaye suka taru masa a fuska ya ce: "Abbah, meye amfanin doka idan zuciya tafi ƙarfin dokar? Ni bana son wata mace face ita, Amal ce rayuwata!" Abbah ya sauƙe ajiyar zuciya, ya ce a hankali: "Zan nemi hanyar da zata daidaita wannan lamarin, amma ban yarda da tashin hankali ba. Bari mu bar wannan maganar zuwa gobe da safe." Inna ta harare su ta ce: "Ni dai babu wanda zai shawarce ni! Aure za’a yi, gobe sai an ɗaura. Sai dai idan wannan saurayin yazo ya tarwatsa mana gidan!" Maleekh ya juyo yana kallon Amal cikin murya mai rauni: "Idan har gobe suka ɗaura auren nan Amal, wallahi ba zan taɓa ƙyale kowa a nan cikin lafiya ba." Amal ta rufe fuskarta tana kuka sosai, tana faɗin: "Ya Allah, ina zan saka kaina yanzu...?" Abbah ya kalli Amal, ya ce da nutsuwa: "Ki kwantar da hankalinki, komai zai daidaita, amma ki bar komai hannun Allah. Ki yi addu’a kawai." Falonnan ya cika da shiru. Sai ƙarar bugun zuciya da ajiyar rai kawai ke tashi.. Kabiru ya sake magana cikin daga murya ya ce. "Gobe da safe Aure, ba wata tattaunawar da za'ayi..." Maleekh a fusace ya juyo yana kallonsa, fuska a murtuke yake nuna Kabiru da yatsa ya ce... "Kai ƙazamin ƙauye, ka iya harshenka, domin idan ka cigaba da ɗaga mun murya zan daddatse maka harshe, ko nasa ayi kidnapping ɗinka, inada iko akan hakan..." Zainabu ta riƙe Kabiru tana faɗin "A'a Kabiru ka daina jayayya da wannan domin zai iya yin komai aradu.. Ka kiyaye shi ba sa'arka bane.." Malam Yawale shima kallon Kabiru yayi tare da girgiza masa kai akan yayi shiru kada su rasa shi... Maleekh ya ce: "Bana wasa da kai..." Abbah ne ya bubbuga kafaɗar Maleekh yana rarrashinsa... “Yaron kirki ka zauna. Wannan ba wurin hayaniya ba ne. Mu raba hankali, mu tattauna.”... Abbah ganin Maleekh ya kasa kwantar da hankalinsa yasa shi kallonsa ya kuma kalli Amal ya ce. "Auren nan an dakatar da shi, Amal da Maleekh ta dace, saboda haka kowa yayi hak'uri a bar maganar auren nan, idan lokaci yayi za'a ɗaura auren Maleekh da Amal..." Sai yanzu Maleekh ya ɗan yi murmushi yana kallon Amal.. Sannan Abbah ya ce da su. "Amal--Maleekh yanzu ku tashi ku tafi an gama da ku..." Suka tashi suka fita cikin kwarin gwiwa.. Daga bisani Abbah ya kalli su Malam Yawale ya ce da su. "Ku kwantar da hankalinku, kamar yanda kuke so ku haɗa auren zumunci insha Allahu zaku yi, babu abunda zai fasa auren Amal da Kabiru gobe, ku cigaba da shirin ku...ina tare da ku, nayi hakan ne saboda yaran su kwantar da hankalinsu..." Kabiru ya ce "Sai yanzu naji zuciyata tayi sanyi..." ♡♡♡♡♡♡ ▪︎▪︎▪︎▪︎▪︎▪︎ Washegari da safe, Abbah yana sanye da manyan kaya da gariya, ya sanya farin glass akan idonsa yana zaune yana tunanin yanda zaiyi da Maleekh, ga shi yanzu duk sunyi shirin tafiya ɗaurin aure ba tare da sanin Maleekh ba, yana so ya ɓoye masa maganar ɗaurin auren.. Sai ga Ammy ta shigo falon ta zauna kusa da Abbah, ta ce "Lafiya kuwa?.." Abbah ya ce "Tunani nake yanda zan tsare Maleekh daga batun auren Amal da wancan yaron, nayi masa alƙawarin an janye auren, alhalin za'ayi babu fashi..." Ammy ta ja dogon numfashi sannan ta ce "Kar ka damu da wannan zan san yanda zanyi da shi, bazai je wurin ɗaurin auren ba balle ya ta da rigima.." Abbah ya ce "Taya zaki dakatar da shi?..." Ammy ta ce "Kai dai kawai ka zuba ido, za'a je a ɗaura aure lafiya a dawo lafiya, yanzu ya riga da ya kwantar da hankali akan a fasa..." Abbah ya ce "Shikenan, ku ma zaku je ne?.." Ammy ta ce "Eh, zan je naga ɗaurin auren Amal, zanyi farin ciki da hakan domin hankalin kowa ya kwanta..." Abbah yayi shiru ba tare da ya furta komai ba, shima kansa yana son Amal da Maleekh... A part ɗin Maleekh kuwa.. Yana zaune a bakin gadonsa, yana sanye da farar t-shirt, idonsa jawur kamar wanda bai kwanta ba tsawon dare. Har yanzu maganganun jiya suna dawo masa, musamman yadda aka nemi tilasta masa barin Amal. Ya jingina da bangon gado yana sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi, ta wani ɓangare yana jin daɗin dakatar da auren da akayi... Sai ga ƙarar ƙofar falo ta buɗe, sannan aka ƙara turo ƙofar bedroom da sallama.. Ammy ce ta shigo a hankali, hannunta riƙe da tray ɗin da ke ɗauke da lemo da cup. Tayi murmushi, ta zauna kusa da shi. Ammy tana murmushi ta ce: “Maleekh... ka rage tunani, kaji? Abbah ya magance komai. Ba wani aure da za’a ɗaura wa Amal, komai ya ƙare.” Ta miƙa masa lemo. Ya ɗauka, ya shanye a hankali. Ta ƙara da cewa, “Ka kwantar da hankalinka ɗana, komai zai gyaru.” Sai dai cikin lemun da ta zuba, akwai maganin bacci mai ƙarfi — 24 hours. Domin ba za su taɓa iya ɗaura auren Amal ba idan Maleekh yana cikin hayyacinsa. Bayan mintuna kaɗan, idanunsa suka fara lumshewa. Ya jingina da jikin gadon, sannan a hankali ya kwanta, numfashinsa ya daidaita. Ammy ta miƙe, ta ɗan murmusa da ƙarfin hali tana faɗin: “Ka huta ɗana... komai zai kasance yanda nake so.” 🌤️ A gefe guda... A gidansu Amal kuwa, ana ta shiri kamar ana shagalin sarauta. An kafa tent a waje, an kawata da farin balloon da golden ribbon. Muryar tana tashi ƙaramar wakar soyayya, mutane na ta dariya da murna. Malaman ɗaurin aure sun iso, an shimfiɗa manyan tabarmai da kujeru.... Abbah ya shirya cikin babbar riga da hularsa, ya gyara ɗan farin gemunsa, fuskarsa da annuri, sai dai idanunsa sun ɗan nuna gajiya da damuwa. Zayd ma ya fito cikin shadda navy blue, yana takawa cikin nutsuwa, amma zuciyarsa kamar ana hura masa wuta. A yau dai, za’a ɗaura auren Amal da Kabiru.. 👰 A ɗakin amarya Amal... Tana zaune a gaban madubi, idonta a kumbure saboda kuka. Ƴan mata suna shirya ta, amma ita babu walwala. Hannunta na rawa, idonta na zubar da hawaye kamar ruwan sama. Amal cikin kuka ta ce: “Allah ya sani... bana son wannan aure, bana son shi... Maleekh ne kaɗai a raina.” Inna tana tsaye a gefe tana share zufa tana faɗin, “Shiyasa nace kar a bar ki da wancan Maliku, kinji yadda yake ruɗar da ke yanzu...” Amal tayi saurin durƙusa wa ta kama ƙafarta tana faɗin, “Inna ki taimaka ki sanar musu, wallahi bana so...” Inna ta girgiza kai. “Magana ta gama tsaruwa, aure ake yi yau.”.. A wajen ɗaurin aure... Mutane sun taru sosai. Ƙarar “Allahu Akbar!” da “barka da war haka” na tashi daga ko’ina. Malaman aure sun zauna da takardunsu, ana jiran kawai a shafa fatiha. Kabiru na gefen malam yawale cikin farin shadda, yana murmushi da sanyi a zuciya. Abbah yana gefe, yana ƙoƙarin riƙe nutsuwarsa.. Kabiru ya sanar da cewa "Ya amince da auren Amal" Abbah shine mai karɓan auren Amatullah Abdulsamaad bisa sadaki dubu ɗari biyar... Cikin farin ciki ana ƙoƙarin shafa fatiha...kowa ya ɗaga hannu.. Sai kawai aka ji ƙarar mota a wajen. “Vruuuuuum!!!” Wani irin danna burki akayi har sai da mutane suka tsorata, wasu na ƙoƙarin guduwa... Motar tayi brake a fusace har ƙura ta tashi. Kowa ya juya yana kallon motar... A nan ne aka ga Maleekh ya fito daga cikin motar sanye da white t-shirt da 3quater, idonsa jajur kamar wuta, fuskar sa a rikice. Shiru ya mamaye wurin. Kowa ya tsaya, malamai suka tsaya da takardunsu. Kabiru shima ya kasa motsawa.. Maleekh ya ɗago hannunsa da wuƙar da ke hannunsa, yana tafiya a hankali cikin natsuwa mai firgitarwa. Yana zuwa ya tsaya a bayan Kabiru, ya ɗora masa wuƙa a wuya... Maleekh cikin tsawa yake furta: “Ana shafa fatiha da sunansa... wallahi zan yanke masa makogoro! In ya sake sunansa ya fito daga bakinku a matsayin mijin Amal, to zan jira ta yi takaba — sannan na aureta!” Jikin Kabiru ya fara rawa. Yana jijjiga hannunsa yana ihu, tare da faɗin “Don Allah kar ka yanka ni! Na fasa! Ku dakata da ɗaurin auren!”. Jin hayaniya yasa mata daga cikin gida suka firfito gaba ɗaya.. Zainabu ta ɗauki ihu tana neman taimako, “Wayyo Allah, a taimake ni! Maleekh zai kashe ɗana!!” Malam yawale ya durƙusa yana kuka, “Don Allah malamai ku dakata! Kada ku ɗaura aure, don Allah!” Abbah ya nufi gaba yana faɗin, “Maleekh! Ka ajiye wukar nan, please yarona! Ka saurare ni!”.. Amma Maleekh ya rufe ido ya ɗaga masa hannu yana huci, ya ce: “Abbah kada ka matso mun! Idan har aka ɗaura, jini zai zuba ne!” Wasu daga cikin jama’a suka soma gudu, wasu kuma sun ɗauka ya haukace. Hayaniya ta tashi, mata sun fito daga cikin gida da hijab a hannu.. Inna ta durƙusa tana kuka tana cewa, “Wannan wani irin al’amari ne haka? Ya Allah ka kare mu da jarabar nan!” Amal da gudu ta fito daga cikin gida, rigarta tana ja a ƙasa, idonta cike da hawaye. Ta nufi wurin, ta kama hannunsa tana kuka, “Maleekh dan Allah ka ajiye wukar nan! Ka saurare ni, bana son auren nan nima!” Sai lokacin ya saki wuƙar a hankali, ya kama Amal da hannu biyu ya rungumeta kamar zai haɗiyeta, yana huci cikin kuka.. “Bazan taɓa bari su raba mu ba Amal... wallahi bazan bari wani ya aure ki ba.” Kowa ya tsaya yana kallon su, shiru ya mamaye wurin. Kamar film ɗin da aka tsaya a tsakiyar zafi... Wurin ɗaurin aure ya tarwatse. Malaman aure suka tashi suka tafi. Kabiru da iyayensa suka ɓuya don guje wa rigima. Abbah ya rasa kalmar da zai ce. Ammy kuwa ta rikice, hawaye na zubo mata. Zayd ya janye gefe yana faɗin, “Daman wannan mutumin ne a zuciyarta... mu dai wasa ne gareta.” Amal ta kalli Maleekh cikin hawaye, tana murmushi da zafin da zuciyarta ke ji, “Na san zaka zo... ban taɓa yarda zaka bari su ɗaura aure na da wani ba.” Maleekh ya girgiza kai, “Ba rabuwa a tsakanina da ke, har sai rai ya fita daga jikina.”.... Abbah ya rufe fuskarsa da tafin hannu yana sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi. Ammy ta kasa magana, ta kalli ɗanta da kallo mai ɗauke da mamaki, fushi, da ɗan tsoron irin yadda zuciyar Maleekh ta iya rikicewa saboda soyayya. Malam Yawale kuwa ya kamo ɗansa Kabiru da hannunsa yana faɗin: "Kai Kabiru, mu tafi gida kafin wani abu ya sake faruwa. Kaddarar da ba ta zama taka ba, ka bari ta tafi. Allah zai baka rabonka kaima..." Zainabu tana kuka ta biyo bayansu, ita ma tsoron abin da ta gani bai bari ta zauna ba. Halima ƙaramar ’yar su kuwa ta manne jikin mahaifiyarta tana faɗin cikin rawar murya: "Umma wannan mutumin fa mahaukaci ne wallahi..." Amal ta tsaya tana kallonsa, zuciyarta ta cika da farin ciki da tsoro a lokaci guda. Tana jan numfashi a hankali, sannan ta ɗan murmusa cikin hawaye: "Na san baka son rabuwa da ni, Maleekh. Amma da ace baka zo yau ba, da na zama mallakin wani. Na gode Allah da ya kawo ka akan lokaci..." Maleekh ya ɗan murmusa, murmushi mai haɗe da zafi da nutsuwa. Ya ɗora hannunsa a kafaɗarta, yana faɗin: "Kada ki sake bari wani ya kusance ki ko ya sake shirin aure dake. Koda ni ban gani ba, soyayyata zata gani.". Daga nan ya juya ya nufi motarsa zai tafi... Yana tafiya kamar basaraken sarki... Amal ta saki dariya mai sanyi, ta share hawayenta tana kallon yadda yake fita daga cikin taron da mutanen da suka rage ke bin sa da ido. A gefe, Zayd yana tsaye yana kallon su daga nesa, ransa a ɓace, yana faɗin cikin haushi: "To yanzu meye nake jira? Tabbas dole ne na samu Pretty, ko da kuwa dole sai na bi ta hanyar da ba kowa yake so ba..." Sai ya juya ya bar wurin da sauri, yana cike da nufin da ba kowa zai gane ba....... NEXT NEXT NEXT asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 57 to 58 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 A falon babban gidan Abbah da Ammy zaune a kan kujera, Maleekh kuma yana tsaye a gaban su kamar yaro da ya aikata babban laifi. Idanunsa sun kumbura saboda fushi da gajiya, yayin da hannunsa ke ƙasa yana karkarwa. Abbah na daka masa tsawa cikin murya mai nauyi: “Maleekh! Ka san abinda kayi kuwa?! Ka san irin abin kunyar da kayi mana a gaban jama’a? Ka san irin abin da hakan zai iya haifarwa ga sunanmu da matsayina a idon mutane?!” Maleekh ya sunkuyar da kai, idonsa ya kaɗa yayi ja saboda tsananin zafi da baƙin ciki. MALEEKH a raunane ya ce: “Abbah… bazan iya haƙura ba. Bazan iya kallo ana ɗaura auren Amal da wani namiji ba. Na tabbata da ban shiga tsakani ba, da yanzu—” AMMY ta katse shi da tsawa tana faɗin: “Da yanzu me?! Da yanzu ka kashe mutum?! Kai ba ka da hankali ne Maleekh?! Wannan soyayya ta Amal zata kaika ga hallaka ne! Wallahi bazan taɓa yarda ka auri waccan matsiyaciyar yarinyar nan ba!” Ta zabura ta miƙe tsaye, hannunta na rawa, idonta cike da hawaye. AMMY ta cigaba cikin fushi: “Kai ɗan gata ne, ɗan gwamnati, ɗan masu daraja! Amma yanzu ka juya saboda matsiyaciyar yarinyar can? Ƴar talakawa? Yarinyar da babu ko asalinta mai daraja? Kai baka ganin yadda take wulaƙanta mu?” Maleekh ya ɗago kansa a hankali, murya a karye: “Ammy, karki ci gaba da cewa haka. Amal bata da laifi… bata taɓa cutar da kowa ba. Ita ce rayuwata… idan har ba ita ba, to babu wacce zata iya maye gurbin ta a zuciyata.” Abbah ya hura iska cikin takaici, ya juyo da murya mai taushi da ƙarfi yana faɗin: “Maleekh! Ka saurare ni sosai… ba haka rayuwa take ba. Idan ma soyayya kake, akwai iyaka. Kai ɗan manya ne, ka san irin matsayi da nake dashi a ido al’umma. Ba zamu iya bari ka zubar mana da mutunci saboda mace ba.” Maleekh ya matso kusa da su, muryarsa na rawa ya ce: “Abbah, wallahi bana neman abin duniya. Bana neman gadonku. Abinda nake nema kawai shine ita. Ita ce nake so. Kuma idan wani ya sake ƙoƙarin ɗaura mata aure, wallahi sai dai a mayar da wurin, gurin jana’iza!” Ammy ta rintse ido cikin fushi, ta ɗaga hannu tana nuna masa ƙofa: “To sai ka fice daga wannan gida! Idan soyayyar Amal tafi iyayenka, tafi martabarka, to fita ka koma wajenta! Amma wallahi a wannan gidan, baza ka taɓa auren ta ba. Na rantse da Allah!” Shiru ya ratsa ɗakin. Sai numfashin Maleekh da ya tsananta. Abbah ya kalli Ammy ya ce "Kin ga, ɗauko mun ruwan sanyi, makogorona ya bushe..." A fusace Ammy ta bar falon kai tsaye frig ta nufa... Abbah cikin murya mai sanyi ya ce: "Maleekh... kai da nake ganin ka fi kowa nutsuwa, sai ka zama abin mamaki? Shin wannan aikin da ka aikata daidai kake ganin yayi ne? Gidan mutane ka shiga da wuƙa a hannu, ka firgita jama'a, ka tozarta sunan iyayenka?" Maleekh ya kasa ɗaga kai. Idanunsa sun kumbura, a hankali ya furta: "Abbah… ba zan iya kallon Amal tana auren wani ba… wallahi ba zan iya ba." Abbah ya girgiza kai cikin takaici. Ya ce "Amal mace ce, kuma auren nan addini ne, ba hauka ba. Kana so mutane su ce ɗana ya haukace saboda mace?" Kafin ya ƙarasa, Ammy ta shigo cikin falon da sauri. Tana ɗauke da tray da jug ɗin ruwan sanyi da cups kananu, tana harararsa cikin fushi... Ta ajiye glass ɗin ruwan da ƙarfi a tebur.. Ta cigaba da faɗa tana faɗin: "Bazan taɓa yarda ka auri yarinyar nan ba! Wacce bata da asali, bata da daraja. Kai ɗana ne, ɗan mutunci da ƙima — ba zaka lalata rayuwarka saboda ita ba!" Maleekh ya ɗaga kai cikin zafi, hawaye na zubo masa, murya na rawa ya ce: "Ki faɗi duk abinda kike so, Ammy… Amma wallahi bazan iya rayuwa babu Amal ba. Ko dai ta zama matata, ko kuma ni na bar wannan duniyar gaba ɗaya!" Ammy ta ɗaga hannu cikin mamaki da haushi, ta ce: "Inna lillahi! Ka fara hauka kenan Maleekh?! saboda mace?" ABBAH a tausashe ya ce: “Daina faɗin haka ɗana. Ka bar wannan fushin. Idan har kaddara ta ce ita ce taka, babu wanda zai iya hanaka. Amma yanzu, ka kwantar da hankali. Ka barni da wannan maganar.” Maleekh ya girgiza kai, hawaye suka zubo masa a kunci. Ya ce: “Abbah, ko da me zai faru, bazan taɓa bari a raba ni da ita ba. Babu wanda zai iya raba zuciyata da Amal. Koda hakan zai zama ajali na…” Abbah cikin murya mai ƙarfi, yana ɗaga hannu ya ce: "Is enough! Ku daina wannan maganar a gaban na.. Maleekh, wannan abun da kayi ba daidai bane. Amma yanzu… kayi shiru. Idan har kana son kiyayewa da wannan yarinya, to sai ka nutsu. Ka bar min maganar. Amma ka sani —" Ya ɗan ja numfashi. "Duk wanda ya kuskura ya sake jawo irin wannan tashin hankali, sai hukunci ya ziyarce shi. Amma, idan soyayyarka gaskiya ce, zan bincika wannan al’amari." Maleekh ya zube a ƙasi yana share hawaye, yana kallon Abbah kamar ɗan da yake neman gafara. Ya ce "Abbah, wallahi bana neman komai… burina ka bari Amal ta zama tawa. Zan iya fuskantar komai saboda ita." Abbah a hankali, yana kallon shi da tausayi ya ce: "Ka tashi ka je ka huta. Zan yi magana da Inna Delu… amma idan har na sake jin wani tashin hankali, ka sani wannan karon ba zan tsaya ba." Maleekh ya tsaya tsayin daka yana kallon ƙasi. Ammy ta tsaya tana kallonsa da mamaki, ganin hawaye suna zubo masa... Maleekh ya ce: "Ko me zaku yi, ba zan bar Amal ba. Soyayya ce, ba son zuciya ba." Ammy ta yatsina fuska ta ce: "To mu gani… wane ƙarfin soyayya ne zai doke ikon uwa da ɗanta." Yayi shiru yana kallon su, ya juya a hankali, ya fice daga falon cikin nutsuwa amma a zuciyarsa wuta ce take ci. Abbah ya bishi da ido cikin damuwa, ya sauƙe numfashi. Ammy ta zauna ta dafe kai, tana faɗin: “Allah Ya shirya mana wannan yaro… saboda ina tsoron abin da soyayyar nan zata haifar.” Falon ya koma shiru kamar ba kowa... ☆☆☆☆☆ Washegari da safe, zuciyar Abbah cike take da nauyi. Duk daren jiya bai runtsa ba. Kalaman Maleekh, duk suna masa yawo a cikin zuciyarsa. Yasan yanzu lokaci ne da ya kamata ya ɗauki mataki mai kyau domin rikicin ya kai matakin da idan bai shiga tsakani ba, zai iya lalata komai. Ya shirya cikin farin babban riga, ya ɗauki hularsa ya fita da nufin gidansu Amal. Lokacin da ya isa, gidan yana cike da natsuwa. Inna na zaune a falo tana lissafin kuɗin da aka kashe wajen shirye-shiryen auren da aka wargaza. Ganin Abbah yasa ta ɗan firgita ta tashi da girmamawa. Ta ce da murmushi mai nauyi, “Alhaji, sannu da zuwa, ai bamu tsammanin ganinka yau ba.” Abbah ya gyara zama, ya ɗan shafa gemunsa cikin natsuwa, sannan ya ce: “Inna Delu, na zo da magana ta hankali. Akwai abubuwa da suka kai yanzu dole sai an fahimta.” Inna ta girgiza kai, ta ce: “To ai yanzu duk duniya ta ji abin da ɗanka yayi jiya. Wani irin abin kunya wallahi. Idan ba don kai mutum ne mai mutunci ba, da na fadi abinda zuciyata ke ji.” Abbah ya sauƙe ajiyar zuciya. Ya ce “Inna, wallahi abin ya bani haushi fiye da kowa. Amma ki fahimci abu guda — ɗana yana cikin soyayya, kuma soyayyar da ta kai mutum ya yi wauta irin waccan… ba ƙaramin abu bane.” Inna ta saki dariyar takaici, “Soyayya fa kake cewa, Alhaji? Wannan hauka ce, ba soyayya ba. Kasan irin abinda ya aikata a gaban jama’a kuwa? Ya ɓata mun suna, ya ɓata sunanku. Yaronka fa ya ɗora wuƙa a wuyan ɗan mutane!” Abbah ya ɗan lumshe ido, yana magana cikin tausasawa, “Inna, na fahimci damuwarki. Amma ki saurare ni — ni a matsayina na uba, bana son wannan auren Amal da Kabiru, domin hakan ba zai kawo mata farin ciki ba. Maleekh ya fi ƙarfin da kike tunani, kuma soyayyarsa ta kai matakin da idan kika ƙi, zai iya lalacewa gaba ɗaya.” Inna ta jinjina kai da takaici, “To ai wannan ba dalili bane da zai sa a mayar da abin da ya aikata kamar wasa. Ko a ƙauyensu waɗancan ma da mutum yayi haka da wuƙa, ai tuni an ɗaure shi.” Abbah ya ce cikin natsuwa, “Na sani, amma yanzu ina so mu duba gaba. Ki faɗa min gaskiya Inna — Amal, har yanzu tana son Maleekh?” Inna ta ɗan yi shiru, sannan ta ce, “Wallahi ina ganin tana son shi. Duk da kuka da ƙuncin da tayi, tun jiya bata ci abinci ba, bata yi bacci ba. Amma ni ban yarda da shi ba, tunda mahaifiyarsa ta riga da ta nuna bata son ‘yar talakawa kamar mu.” Abbah ya sauƙe numfashi a hankali, ya ce: “Inna, ni zan daidaita komai. Zan je na zauna da Uwar yaron da kaina. Idan Allah ya yarda, zamu warware komai cikin mutunci. Ba a son ta auri wanda bata so. Kuma ni a matsayina na uba, bana son wulakanta ɗiyar da nake ganin kamar ‘yata ce.” Inna ta ɗan share hawaye tana murmushi, “Alhaji, Allah ya saka da alheri. Idan har zaka iya daidaita wannan, to ni na yafe masa. Amma fa, ka gaya wa matarka ta kiyayi yi wa Amal rashin mutunci.” Abbah ya miƙe, ya ce da nutsuwa, “Zan gaya mata. Na yi alkawari. Insha Allah wannan soyayyar bazata zama jaraba ba, sai dai rahama.”. Ya ciro damin kuɗin wanda zai kai 300k ya bata akan ta rage asara.. Inna tana washe baki ta fara godiya, ta durƙusa har ƙasa tana masa albarka... Suka yi sallama da nutsuwa. Abbah ya fita yana tunani “Yanzu lokaci ne da zan fuskanci Maryam. Amma da yaushe zata fahimci cewa zuciyar ɗa ba a mulkinta?” ✨ Inna tana kallon ƙofar da Abbah ya fita tana faɗin cikin zuci: “Allah ka shirya wannan al’amari. Kada a sake jefa Amal cikin wani tashin hankali…” A daren yau.. A cikin babban falon gidan Abbah, ƙarshen daren ranar da ya dawo daga gidansu Amal. Wurin ya cika da nutsuwa, sai ƙamshin turaren oud da aka kunna. Abbah yana zaune a kujerar fata yana sosa gashin kansa cikin gajiya. A gefe kuwa Ammy ta shigo da sauri, tana sanye da rigar babu da ya lulluɓe jikinta, idonta kuwa cike da fushi... Ammy cikin ɗaga murya ta ce: "Alhaji! To ka dawo ko? Ashe gidan su waccan yarinyar Amal ka je? Abbah: cikin natsuwa, yana ɗan sauƙe numfashi ya ce: "Na tafi ne saboda neman lafiya, Maryam.. Na je ne in fahimci gaskiyar abin da ke faruwa tsakanin Amal da ɗanmu Maleekh..." Ammy ta taka zuwa gabansa ta ce: "To meye abunda zaka faɗa yanzu? Wancan matsiyaciyar yarinyar nan da bata da komai face tsiya? Wallahi bazan yadda ta shigo gidanmu a matsayin suruka ba!.." Abbah yana kallonta cikin tausasawa ya ce: "Maryam, ki kwantar da hankalinki. Wannan al’amarin ya rigaya ya fita daga ikonmu. Maleekh yana sonta, kuma na ga soyayyar nan bata wasa bane. Ki barshi ya samu nutsuwa..." Ammy ta dafe ƙirjinta cikin jin haushi ta ce: "Nutsuwa kake faɗa? Wato bayan duk abinda aka riga aka shirya, bayan Farha, yanzu za’a wurgar da ita kamar jaka saboda wata yar talaka? Alhaji, wallahi wannan ba zai taɓa faruwa ba! Ba da ni ba!.." Abbah ya miƙe a hankali yana dubanta da murmushi mai natsuwa ya ce: "Maryam... na fahimci kina son Farha kamar ƴarki. Amma mu bar Allah ya zaɓa wa ɗanmu abinda ya fi alkhairi. Duk mu mun ga yadda yake fama tun da aka fara wannan maganar. Ki duba zuciyarsa, ya fita hayyacinsa saboda soyayya..." Ammy ta juyo da ƙarfi tana nuna shi da yatsa tare da faɗin "Kai dai ka sani, ko Maleekh ya auri Amal, wannan ba zai taɓa zama cikin farin ciki ba idan har ba a daidaita al’amura ba!.." Abbah ya zauna yana tambaya cikin natsuwa. "Me kike nufi da “daidaita al’amura” Maryam?.." Ammy ta tsare shi da ido, muryarta ta ɗan yi sanyi ta ce: "Sharadina guda ɗaya ne, Alhaji. Idan har kana so in yarda Maleekh ya auri waccan Amal ɗin, to sai ya haɗa aure da Farha. Na ce dole sai ya auri mata biyu Amal da Farha a lokaci guda. Idan ba haka ba, wallahi ba zan taɓa yadda da wannan auren ba!.." Abbah ya tsaya kallonta cikin mamaki, yana jin nauyin maganarta ya ce: "Maryam… wannan sharaɗi naki yana da nauyi sosai. Kin tabbata wannan shine abin da ke ranki?.." Ammy ta ɗaga kai da tabbaci ta ce: "Na tabbata. Idan har Amal zata shigo gidan nan, to Farha ma zata shigo a lokaci guda. Babu mace guda da zata mallaki zuciyar ɗana gaba ɗaya..." Abbah ya sauƙe numfashi, yana jinjina kai ya ce: "To... Maryam, na ji. Amma ki sani, wannan al’amari sai dai mu bar Allah ya hukunta shi. Domin soyayya bata da dokar da mutum yake rubutawa da hannunsa... Ammy ta ɗan juya tana kallon ƙasa ta ce "To kai dai ka sani Alhaji, na faɗa maka abinda ke cikin zuciyata. Wannan shine sharaɗi na ƙarshe..." Ta juya ta bar falon, tana daidaita numfashinta. Abbah ya zauna yana kallonta a yayin da take barin falo, ya dafe kansa da hannuwa biyu, yana faɗin a hankali... “Subhanallah… soyayya ta fi ƙarfin iko. Amma wannan gwagwarmaya zata ba da tarihi mai tsawo.” Washegari da sassafe a gidan su Maleekh. Sanyin safiya na shiga cikin babban falon da yake cike da nutsuwa da ƙamshi. Abbah yana zaune a kan kujera mai faɗi, A gefe Ammy tana zaune cikin ɓacin rai. Maleekh yana gefe yana jujjuya zoben hannunsa, Farha na kusa da shi tana ɗaure fuska. Sai ga Amal an kawo ta gidan cikin hijabi, idonta cike da nutsuwa amma a bayyane akwai tsoron abin da ke gabanta... Abbah a hankali, yana kallon Amal ya ce: "Ki zauna nan, ‘yata. Muna so muyi magana cikin natsuwa..." Amal ta durƙusa har ƙasi ta ce: "Na’am Abbah… ina kwana.." Abbah ya amsa da... "Lafiya lau..." Amal ta gaishe da Ammy. Ammy ta kawar da kai tare da jan dogon tsaki ta kawar da kai gefe... Abbah yana fuskantar Amal ya ce. "Kin ga, wannan magana ba ta yara bace, saboda tana da nasaba da rayuwar mutane uku — ke, Maleekh da kuma wannan yarinya (ya nuna Farha). Ni dai ban so wannan rikici da ya faru ba, saboda ni kai na na ji kunya a gaban jama’a..." Maleekh ya ɗago kai da ƙarfi ya ce. "Abbah, ni ba na jin kunya! Na aikata abinda na yi ne saboda bana so a cuce ni. Amal tawa ce, kuma ba zan bari a ɗaura mata aure da wani ba!.." Ammy ta tsawata masa da cewa: "Kai kayi mun shiru, Maleekh! Tun da na haifeka ban taɓa tunanin zaka zubar min da mutunci irin haka ba. Ka shigo cikin manya, kana ɗaga wuƙa da alfaharin zaka kashe mutum! Idan ba hauka ba, menene haka?.." Maleekh yana yatsina fuska ya ce: "Hauka kike cewa? Saboda ina son Amal? Ammy, ina girmamarki, amma ki sani soyayya ba ta kallon arziki.. Kina so ne in auri wadda kike so, ba wadda nake so ba?.." Farha cikin muryar kuka tana kallon Maleekh ta ce: "To me yasa sai ita? Ina sonka Maleekh, ka san hakan. Tun muna yara ake cewa mu biyu mun dace da juna, Amma yanzu, sai wata talaka ta kwaceka? Me take da shi da ni ban dashi?.. " Amal tana kallon Farha cikin nutsuwa ta ce: "Farha… ban so in shiga tsakaninku ba. Farha, wallahi ba ni na nemi wannan soyayya ba. Ƙaddara ce ta haɗa ni da shi. Ba nayi ne da ganganci ba. Ki daina ganina a matsayin mai kwace...." Ammy ta tsuke baki, tana dariya cikin raini ta ce: "Kaddara ko? Kaddarar talauci?. Ki ji ni da kyau Amal, bana son ki cusa kanki a cikin zuciyar ɗana. Idan kika ci gaba da kusantarsa, sai kin ga abin da bai miki daɗi ba!.." Abbah ya ɗaga hannu cikin natsuwa ya ce: "Maryam! Iska ce ta fi zafi yanzu. Ki bari nayi magana..." Ya kalli Amal da ta sunkuyar da kai. "Amal, na san kina cikin tashin hankali. Amma ki sani, ba wanda zai iya raba soyayya ta gaskiya da niyyar Allah. Ni da kaina na ga irin ruɗanin da Maleekh yake ciki, kuma wannan abu ba zai daidaita sai an zauna an fahimta..." Ya kalli Maleekh da idanu masu nauyi sannan ya ce "Kai kuma, Maleekh, daga yau ban so in sake jin tashin hankali daga gareka. Idan wannan soyayyar taka gaskiya ce, za mu bi ta hanya mai kyau. Amma idan wata zuciya ce ta hauka, ka kwantar da kai ka gyara halinka..." Maleekh ya sauƙe numfashi, yana girgiza kai ya ce: "Abbah, wallahi bana hauka. Ni dai ba zan bar Amal ba. Idan za’a hukunta ni saboda haka, to na amince..." Abbah da murya mai tausayi ya ce: "To idan haka ne, za mu fara da sulhu. Na ƙira ki (ya nuna Amal) da ke (ya nuna Farha) domin yau in ji gaskiya daga bakin kowanku. Saboda wannan soyayyar ta zama rigima..." Yana kallon su uku a jere Maleekh, Amal, Farha. Abbah ya sauƙe murya cikin tausayi ya ce: "Wannan gida nawa ne. Ba zan bari soyayya ta zama dalilin rarrabuwar kai ba. Amma duk wanda ya ci gaba da tada hankali to dole sai ya fita daga rayuwarmu..." Amal ta share hawaye, ta yi murmushin ƙarfin hali. Maleekh ya ɗaga kai yana kallon mahaifinsa da girmamawa, sannan ya kama hannun Amal a hankali yana farin cikin haɗuwarsu. Abbah ya yi shiru, ya zuba musu ido cikin tausayi, yayin da Ammy ta ɗauke kai tana jin haushi... Maleekh cikin murya mai taushi ya ce: “Abbah, ni fa ba zan bari a ɗaura auren Amal da wani ba. Tunda rayuwata ta haɗu da tata, ita ce nake so, kuma ba zan iya rabuwa da ita ba.” Ammy tana huci ta ce “Ka daina faɗin hakan, Maleekh! Wallahi bana so inji sunan wannan yarinyar a bakinka. Yarinyar da bata da asali, jikan talakawa, matsiyaciyar da ta lalata gidanmu! Ba zan yarda ka aureta ba!” Maleekh ya ɗaga kai yana kallonta kai tsaye ya ce: “Ammy, ki ce komai, amma ba zaki raba ni da ita ba. Ni Amal zan aura, ko da zan rasa komai.” Ammy ta miƙe tsaye tana daka masa tsawa.. “To shikenan! Idan har ka nace zaka auri wannan yarinyar, to sai ka aura da Farha a lokaci guda. Ita da Amal! Wannan shine sharadina, kuma haka na tsara da mahaifinka, in shi ya kasa sanar maka to ni zan faɗa domin ba tsoronka nake ji ba..!” Abbah ya ce cikin murya mai nutsuwa.. “Ka ji abin da mahaifiyarka tace, yarona. Ka yarda da ita. Ita uwa ce. Ka faranta mata, ka bi umarninta. Ka aure su duka biyun, Allah zai sa albarka.”.. Ya kalli Farha, wacce ke zaune cikin jin daɗi da ƙasa da murya: “Ke kuma Farha, na roƙeki da ki riƙe Amal, ki zauna da ita lafiya. Bana son tashin hankali a cikin gidan.” Sai ya kalli Amal, wacce take gefe, idonta cike da hawaye.. “Amal, kiyi haƙuri. Komai sai da jarumtaka. Wannan rayuwa ce, kuma idan kika dage da addu’a, Allah zai saka miki. Ki yadda a haɗa ku, domin zaman lafiya.” Amal da murya mai rauni ta ce.. “Na ji Abbah… amma…” (ta kasa magana, tana share hawayenta)... Maleekh ya ɗaga kai, yana murmushin dole, cikin dariyar da ke cike da ciwo ya ce: “To, idan haka ne, zan yarda in aure su biyu…” Kowa ya kalle shi da mamaki. Sai ya juyar da kallonsa zuwa ga Farha. Maleekh cikin murya mai ƙarfi, yana kallonta kai tsaye ya ce: “Amma kafin hakan ta faru, akwai sharaɗi guda ɗaya. Idan Farha tana so in aureta, to sai ta zauna a gaban television ta amsa laifinta. A gaban kowa.” Kowa ya juyo, yana kallonsa da tambaya. Ammy ta ce: “Laifi kuma? Wane laifi?” Maleekh yana numfasawa cikin fushi ya ce: “Laifin da ta aikata wa Amal. Farha ce ta haɗa shirin da kawayenta suka tozarta Amal, suka kai ta gidan club, suka mata ƙaryar cewa na ina wurin, sannan suka yi sharri da cewa ta zubar da ciki! Duk ita ce ta tsara komai, saboda kishin da take yi. Sai ta faɗi gaskiya a gaban kowa kafin wannan auren ya tabbata!” Faloo ya ɗauki shiru. Farha ta zaro ido, ta kasa motsi. Ammy ta kalle ta cikin mamaki. Abbah ya ɗan murmusa, yana kallon Maleekh cikin gamsuwa da jarumtar sa. Maleekh ya miƙe ya ƙarasa kusa da Farha yana faɗin “Idan kina so a ce ni mijinki ne, sai kin faɗi gaskiya yau. Idan ba haka ba, auren nan ba zai taɓa faruwa ba.” Amal ta ɗago kai, hawaye suna sauƙa a kumatunta, amma bata ce komai ba. Farha ta fara kuka tana faɗin: "Wallahi Ammy kuyi hakuri, ba haka nake nufi ba… kawai ina son… ina son Maleekh ne shi yasa nayi wannan sharrin. Ban san zai kai haka ba..." Abbah ya juyo da sauri, yana duban ta da fushi ya ce: "Farha! Kin san abinda kika aikata kuwa? Kin yi ƙarya akan yarinya marar laifi, kin wulakanta sunanta a gaban duniya! Wannan abin kunya ne, har ga iyayenki!" Ammy ta share gumin fuska da mayafi tana faɗin: "To ai abunda ya wuce ya wuce, ba sai an je Television ba. Me kake nufi Maleekh? Kanaso ka zubar da mutuncin ‘yar uwarka ne saboda waccan marainiya? Hakan ba za ta iya dawo da darajarta ba." Maleekh ya ɗago kai, idonsa ya rine da ƙwalla, amma muryarsa cike da ƙarfi ya ce: "OK. To a idonku Amal ba ta da daraja, ko? Fine. Amma a idon al’umma tanada matsayi. Kuma zan dawo da martabarta, ta hanyar wanke sunanta daga ƙarya da zargi. Na ɗauki alkawari a gaban kowa sai na goge wannan ƙazantar da aka ɗora mata." Sai ya juyo da fushi ya dubi Farha: "Ki tashi yanzu mu tafi kamfani. A gaban kowa, a gaban ‘yan jarida da kafafen TV, zaki faɗi gaskiya. Zaki faɗi abinda kika aikata da bakin ki!" Farha ta dafe ƙirjinta cikin tsoro, tana kallon Ammy: "Ammy don Allah… ki ce masa ya barni. Na tuba wallahi…" Ammy ta ce cikin gaggawa: "Ba sai an kai hakan ga jama’a ba Maleekh. Ka daina. Wannan magana ta gida ce, mu rufe ta a gida." Abbah ya sau numfashi yana tsaki ya ce: "A’a. Ba a rufe gaskiya da sirri. Farha, tashi ku tafi. Ka ji, Maleekh? Kaje ka tabbatar gaskiya ta fito. Ba mu da wani abin da muke tsoro idan gaskiya ce." Maleekh ya ɗauki makullin motarsa yana cewa cikin daci: "Mu tafi yanzu. Amma Amal ma zata tafi. Domin yau zan tabbatar duniya ta san cewa ita ce wacce aka zalunta, ba wacce ta aikata zunubi ba." Sai suka fita gaba ɗaya, Maleekh, Farha, Amal. Zasu nufi kamfanin CashTalk Media House, da niyyar wanke gaskiya a gaban kowa... Ammy tana zaune a kujera, tana riƙe da kai cikin damuwa, yayin da Arfat da Islam ke kallonta cikin shiru, Farha na kuka a wajen ƙofa, sai dai ba mai dawowa daga wannan hukuncin da Maleekh ya ɗauka... 🎬 GASKIYA ZATA BAYYANA... Location: babban studio na TV station, mutane da yawa sun hallara, cameras suna kunne, haske na ɗaukar fuska, murya tana rawa. A gefe Maleekh da Amal suna tsaye, fuskokinsu a cike da damuwa. A gefe kuma Farha ce tana sanye da farar riga mai sauƙi, ba kwalliya, idonta jawur kamar marar bacci, tana kallon camera a gajiye... 🎙️Presenter a hankali ya furta: “Yanzu muna da bayani mai mahimmanci wanda zai iya canza fahimtar jama’a game da shari’ar Amal da Maleekh... Gaskiya zata fito daga bakin Farha da likita da suka san komai.” Camera ta tsaya kan Farha. Microphone a gabanta. Jikinta yana rawa... Cikin kuka ta fara da cewa: “Ni... ni ce... na jawo komai! 😭 Ni ce na tura Amal gidan club... Na yi mata ƙaryar cewa Maleekh yana can yana jiran ta... Na kuma tura wasu ƙawayena suka ba ta kwayoyi, suka haɗa mata da abin sha da maye... Lokacin da ta suma, suka kwantar da ita a toilet suka zuba mata jini a jikinta... Sannan suka ajiye maganin zubar da ciki a gefe don a nuna kamar ita ta yi ne!” (ta share hawaye, tana karkarwa) “Ni... ni ce silar rabuwar da suka shiga. Saboda kishi, saboda tsanar ganin Maleekh na son wata mace fiye da ni...” (Camera ta ɗan matsa kusa. A gefe Amal ta fashe da kuka, tana riƙe da hannun Maleekh. Abbah yana kallon TV a gida yana girgiza kai. Inna kuwa ta dafe ƙirji tana kuka tana faɗin: “Subhanallah! Ashe hakane? gaskiyar ta fito... Ashe jikata bata aikata komai ba...” Farha: ta cigaba da kuka sosai tana bayani.. “Bayan haka... na je wurin Doctor ɗin da ya karɓi Amal lokacin da Maleekh ya kaita asibiti. Na ba shi kuɗi masu yawa... Na roƙe shi da ya rubuta result ɗin ƙaryar cewa Amal ta zubar da cikin wata huɗu... Ya yarda... ya karɓi kuɗin... ya karya gaskiya saboda ni... saboda son zuciyata!” (Ta durƙusa ƙasa tana kuka sosai. Muryar ta na rawa.) “Na aikata zunubi! Na lalata rayuwar mutane biyu da soyayyarsu ta gaskiya! Na aikata laifi ga Allah, ga Maleekh, ga Amal...” (Camera ta motsa zuwa likita wanda yake zaune a gefe yana sanye da farar rigar doctors. Ga fuska a farfashe duk ya kumbura kamar wanda yayi hatsarin mota, wannan hukuncin Maleekh ne kafin ya bayyanar da a gaban television..) Doctor ya ce: “Eh... abin da Farha ta faɗa gaskiya ne. Ni na karɓi kuɗi daga gareta. Na rubuta result ɗin ƙarya domin na kare mata suna... Na karya alƙawarin da na ɗauka a matsayin likita. Na tuba... Na nemi gafara daga Allah da daga waɗanda na cuta.” (Camera ta dawo kan Farha da Amal. Amal ta kasa tsayuwa, ta durƙusa tana kuka. Maleekh ya rungume ta yana lallashi cikin taushi, ya ce:) “Na yarda dake, Amal... na yarda dake tun farko, sai dai zuciyata ta kasa yarda da gaskiyata. Amma yanzu na san... kina da gaskiya tun farko.” Farha tana kuka sosai, tana faɗin: “Don Allah ku yafe mini... Wallahi ba da gangan nake son kashe muku soyayya ba, kawai zuciyata ce ta rufe ni da kishi!” (Camera ta rufe da slow zoom inda Amal da Maleekh suka rungume juna tana kuka, Inna tana kallon TV tana hawaye, Abbah yana dafe kai da tausayi, yayin da Farha ta durƙusa tana kuka tana karanto istigfari...) 🎬 Fade out background voice: “Gaskiya ba ta ɓuya. Ko da ta jinkirta, sai ta fito...” NEXT NEXT NEXT... asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 59 to 60 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Daga cikin gidansu Maleekh labarai a TV suna nuna yadda Doctor da Farha suka amsa laifinsu. Wani ɗan shiru ne ya rufe falon. Bayan nan duniya ta fara girgiza da labarin… TV na kunne, labarin yana fita: “...an tabbatar da cewa Farha, tare da haɗin gwiwar wani likita, sun yi amfani da miyagun dabaru wajen cutar da Amal... Hukuma ta tabbatar da kama su don bincike...” Ammy ta miƙe a hankali daga kujera, tana kallon TV da rikitattun idanuwa. cikin zafin rai ta ce: “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Maleekh kenan, abun nakan har ya kai ga yaudara mu? har zaka kai ƴar uwarsa hukuma? Ya kai ƴar uwarsa hukuma? Wannan wane irin hauka ne haka?!” Abbah ya kalli Ammy cikin nutsuwa sannan ta ce “Maryam ki kwantar da hankalinki... gaskiya dole ta bayyana, ko ta ɓoye shekaru goma. Amma ni ma ban yarda da matakin da Maleekh ya ɗauka ba. Ya kamata ya bari mu muyi hukunci a gida, ba a kai hukuma kai tsaye ba.” Ammy ta girgiza kai tana hawaye. “A’a Alhaji! Wannan abun zai tarwatsa zumunci! Farha ai ɗiyar ƙanwata ce... yanzu duk duniya sun ganta a TV kamar wata mai babban laifi, hakan ma bai wadatar ba har sai a haɗa da hukuma?..!” Zayd ya shigo cikin fushi, yana ɗauke da wayarsa...Yana faɗin “Abbah, Ammy... yanzu danginmu suna ƙira suna zagin Maleekh a WhatsApp group ɗin family! Wasu suna cewa Maleekh ya fifita wata ƴar talakawa akan jinin jikinsa... kuma nima nace Maleekh bai mun adalci ba, inda kara ai Farha ƙanwata ce jini ɗaya, shin zai iya aikata haka wa ƴar uwarsa uwa ɗaya uba ɗaya?...” Ammy ta kalli Zayd da ido mai cike da hawaye da fushi ta ce: “Ai wannan abin kunya ne Maleekh ya aikata, ni dana haife shi ma zai iya yi mun abunda yayi wa Farha balle, Hmmm! yau ya juya mana baya saboda yarinyar da bamu san asalinta ba!” Abbah ya miƙe, yana kallon su sannan ya ce “Kuyi shiru kawai! Ku manta da jinin dangi idan ana magana akan gaskiya. Farha ta yi abin da ba ta kamata ba. Likita ya ci amanar ƙasa. Kuma Maleekh yayi abin da ya dace, ya tabbatar da gaskiya. Idan mu ne, mu ma da za mu yi haka!”... Ammy a hargitse tana kallon Abbah ta ce "Eh! Ai daman kai da ɗanka bakwa son farin ciki na, duk abinda yayi da mai kyau da marar kyau koda yaushe kana kan goya masa baya, to wallahi zaku ji kunyar duniya ne wata rana..." Daga nan Ammy ta bar falon.. Shima Zayd a fusace ya wuce ɗakin da yake.. Shiru ya rufe falon. Sai wayar Abbah da ke yin ƙara, ƙira daga wurin ɗan uwansa, Malam Salihu, daga Kano.... Sai ji nayi ABBAH na cewa: “Salihu, naji... eh, gaskiya ne. Eh, shi ya kai Farha hukuma... to ai doka ta fi zumunci idan zunubi ya wuce ƙima. Ka daina magana da fushi, mu ma muna cikin zafin lamarin...” Daga nan ya kashe wayar a hankali yana sakin numfashi... Ƴan uwa sun taru suna kallon TV. Muryar TV na fita, hoton Farha tana riƙe da hannun Police... Sam babu wanda yaji daɗin wannan al’amarin.. Daga ƙasar london, saƙo ya iske su... Mahaifin Farha kamar zai yi hauka, ya rasa yanda zai yi, gaba ɗaya yaji ya tsani Maleekh da yarinyar da yayi wa ɗiyarsa wulakanci akan ta... Mahaifiyarta tana kuka tana faɗin. “Ya Allah, wannan wane irin abin kunya ne? Maleekh ya lalata sunanmu! Ashe Maleekh bashi da tausayi, sai ya wulaƙanta ƴar uwarsa haka, me muka masa haka?” Mahaifin yana huci ya ce: “Wallahi wannan Maleekh ɗin ya raina mu. Ba zai ƙara samun goyon bayanmu ba. Ya fifita wata banza akan jininsa, yanzu abun da zamu yi shine zamu koma Nigeria, domin bazan bari ɗiyata ta wulaƙanta ba...!” Hajiya Sa’adatu uwar Farha ta ɗauki waya ta ƙira Zayd, bugu ɗaya ya ɗauka. Yana ɗaga wa ta fara zaginsa da cewa: "Kai wawa ne marar amfani, kana kallon ina har Maleekh zai tozarta ƴar uwarka haka? Meye amfanin zamanka a Nigeria idan bazaka iya kula da Sister ka ba? Mun tura ka can ne fa akan ka sa ido akan Family gidan, sannan ka rasa Maleekh da yarinyar da yake nema amma har yanzu bamu ga wani abun arziki ba, Zayd kana ji ba? Aiki na ƙarshe da zan saka yi mun shine, inaso ka kashe mun Maleekh, bana so na ƙara ganinsa a duniya, daman abu ɗaya ne yasa zan haɗa ƴata da shi shine munaso mu karɓe duniyar da mahaifinsa yake da shi, da shi kansa Maleekh ɗin amma tin da hakan bai yi ba, just ka kawar da shi daga doron duniya...." Daga nan suka katse wayar... A washegari jirgin su zai ɗaga zuwa Nigeria... JAMA’A A SOCIAL MEDIAyy Hotuna na yawo a Instagram, TikTok, da Twitter. Hashtag ɗin #JusticeForAmal da #FarhaTrial sun ɗauki hankalin jama’a... COMMENT 1: “Allah ya saka wa Amal! Yau kowa ya ga irin zaluncin masu kuɗi, Allah ya tabbatar da gaskiyar Amal!” COMMENT 2: “Farha da likita sun jawo wa family ɗin su abun kunya. Amma ai gaskiya ta fi komai!” COMMENT 3: “Maleekh ya yi abin da ɗan gaske zai yi, sai dai ya lalata zumunci, meyasa bai yi hakuri an magance matsalar a cikin gida ba?” A TV, ana nuna Amal tana fita daga ofishin lawyers da hawaye a idonta duniya ta fara rarrabe tsakanin masu goyon bayan Amal da masu kare Farha... GIDANSU AMAL Inna tana kallo, tana jin labarin da murmushi mai sosa zuciya. “To Alhamdulillah... Allah ya fito mana da gaskiya. Amma wannan rikici ne da zai shude, mu dai mu ci gaba da addu’a. Gaskiya da zuciya sun fi dangi da dukiya.” Amal wacce ta dawo gida ta share hawayenta tana kallon Inna.. “Ni banji daɗi da ya kai su kotu ba, Inna... amma ni dai na gode Allah da gaskiya ta fito fili. Duk duniya ta san ba laifi nayi ba.” Inna ta ɗora hannu a kafaɗarta tana faɗin “Toh hakane Amatu. Komai ya wuce, sai ki tashi ki roƙi Allah ya sassauta zuciyoyin jama’a. Duniya da baka zaune da ita lafiya, sai gaskiya ta baka kariya.” Su Malam Yawale sun zuba ido basa cewa komai, tin da Auren nan ya wargaje gaba ɗaya suka cire hannunsu akan lamarin Amal...amma har yanzu suna zaune a gidan.. A wannan ƴan kwanaki. Ba Maleekh ba hatta Abbah ya samu matsin lamba a wurin ƴan uwa... domin duk dangi babu wanda ya goyi bayan Maleekh... Abbah yana zaune a part ɗina bakin gado yana ta tunanin wannan al’amarin.. “Lokacin da gaskiya ta fito, ba kowa ne zai iya jure ta ba. Amma wanda yake da gaskiya, ko duniya ta juya, Allah zai tsaya masa.” Abbah yana maganar zuci... A babban falo. Maleekh ya shigo cikin gidan, fuskar sa cike da gajiya, idanunsa sun ɗan kumbura kamar wanda bai kwanta ba tun jiya. Yana shigowa falon Ammy ta taso a zabure. Kafin ya iya cewa komai, ta ɗaga hannu ta zabga masa mari sau ɗaya, sau biyu, sau uku, sau huɗu, har sau biyar a take... har sai da gefe na bakinsa ya fitar da jini, abunka da mai taushin lips... AMMY cikin ɗaga murya take faɗin: “Wai me kake nufi da wannan haukan, Maleekh?! Aure kai da Amal na janye! Na janye wallahi! Ni ce na yarda akan ka aure ta da Farha amma yanzu na fasa! Na fasa gaba ɗaya!”.... Maleekh yana tsaye cikin shiru, hannayensa a sake alamun babu wani ƙarfi a tattare da shi, ga saƙonni na zagi da ƴan uwa suke ta turo masa, yana ɗan girgiza kai cikin kunar rai. AMMY ta cigaba da cewa “Yanzu ina Farha? Kasa an kaita cell ko? Daga nan sai kotu! Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Maleekh, anya ni ce na haife ka kuwa?! Ka zubar mana da mutunci a idon duniya! Kai ɗa ne da ake alfahari da shi yanzu ka zama abin tausayi da zargi!” Da sauri Abbah ya fito daga upstairs, yana sanye da jallabiya, yana kallon Ammy da Maleekh ya ƙarasa kusa da su. Cikin muryar tsawa yake faɗin. “Me ke faruwa ne haka cikin gida? Maryam, me ya faru?” Tana kuka da huci ta ce: “Ka tambaye shi, kaima kasan abunda ya aikata ai! Wannan ɗan naka yana da hauka! Farha yarinyar nan yanzu tana cikin cell! Ka tambaye shi me yasa ya saka ta a hannun hukuma kamar wacce bata da gata!” Abbah ya juya yana kallon Maleekh kai tsaye. “Maleekh! Wane irin abin kunya ne ka ƙara kawo mana haka? Shin ba ka sanar mana cewa a TV zata sanar ba? Me yasa har da hukuma?!” MALEEKH cikin muryar tausayi, ya ce: “Abbah... ba hukuncin kaina nayi ba. Hukuma ta riga da ta shiga cikin case. Babu komawa baya. An samu gaskiya, kuma duk masu laifi sun amsa laifinsu.” AMMY ta zabura cikin takaici ta ce: “Ka ce gaskiya?! Gaskiyar me? Wannan ita ce ‘yar da na raina da hannuna, da nake kallon ta tamkar ‘yata! Ka kasa daurewa ka tafi da lamarin cikin gida?” MALEEKH ya ɗago kai yana faɗin: “Ammy, babu wanda ya fi ni son a warware komai cikin gida. Amma idan abu ya kai ga cin zarafi, da cutar da wanda bai da laifi to adalci dole ne ya yi aiki!” Abbah ya ja numfashi mai zurfi yana girgiza kai, zuciyarsa na tafasa da ciwon abin da ke faruwa. ABBAH ya ce: “Maleekh, ka sani… rayuwar mutane ba wasa bace. Idan dai kotu ta shiga, to babu wanda zai iya ja da hukuma. Amma, na baka shawara: ka kwantar da hankali, ka bar doka ta yi aikinta kawai...” AMMY ta juya da hawaye tana kallon Abbah: “Au kaima Alhaji yanzu haka zaka tsaya masa? Kana ganin ɗanka ya hallaka zumunci? Ni bazan taɓa yarda da wannan auren Amal ba! Tunda har ya zaɓe ta akan ƴar uwarsa, ku je kotu ta yanke hukunci ɗin...!” Maleekh ya kalli iyayensa da idanu masu cike da tausayi ya furta a hankali. “Ku yi haƙuri, amma hukuma ta riga ta kama hanya. Kotun ce zata yanke hukunci, ba zuciyar mutum ba.”... Ya nufi part ɗinsa cikin natsuwa, ya bar Abbah da Ammy cikin mamaki da tsoro yayinda iska mai sanyi ta lulluɓe Ammy... Ammy ta zube a kujera tana kuka, Abbah na zaune cikin tunani mai nauyi, yana cewa a hankali: “Rayuwa... idan ɗa ya fara tafiya akan hanyar da yake ganin ita ce adalci, babu wanda zai iya ja da shi.”.. Washegari iyayen Farha sun sauƙa a Airport. Zayd da kansa yazo ɗaukan iyayensa a motarsa. Zayd ne yake tambayarsu cewa gidan su Maleekh zasu nufa?..." Mahaifinsa a firgice ya ce "Allah ya kiyaye, ai akwai gidan mu anan, don haka akai mu can, ai mun daɗe da raba zumunci da su. Babu mu babu su don haka mu tafi gidan kanmu..." Zayd ya ce "Saboda haka yasa nasa aka gyara muku gidan domin nasan bazaku taɓa rayuwa anan gidansu ba..." Sun shiga mota suka yi gidan su acan Estate... Bayan sun ci abinci sun huta.. Hajiya Sa’adatu ta kalli Zayd ta ce "Ya muke akan maganar mu?..." Zayd ya ce "Ina sane da haka Mom, mu bari sai an gudanar da zaman kotu tukun, kuma akwai hanyoyi da yawa da za'a kawar da shi ba tare da an san wa ya kashe shi ba, mu kasance masu wayo kafin hakan..." Alhaji Wadata mahaifinsa ya ce. "Tabbas sai anyi tunani tukun..." Suna cikin wannan zama sai suka ji knocking.. Zayd ne ya je ya buɗe sai ga wani babban mutum mai kuɗi wanda yaci sunansa Alhaji Gusau, asalin ɗan Gusau ne yake zaune anan Abuja, shima tsohon ɗan siyasa ne... Ganinsa yasa Alhaji Wadata miƙe wa yana kallonsa da mamaki kafin ya ce. "To pah Alhaji Gusau taya kasan da zuwan mu alhalin ba wanda yasan mun zo ƙasar?..." Alhaji Gusau ya zauna sannan ya ce "Ai daman nasan zaku zo, yau ne fa zaman da za'ayi a kotu, kuma ƴarku ake ƙara da cin zarafi..." Alhaji wadata ya ce "Yanzu ba wannan ba, shin meya kawo ka?..." Alhaji Gusau ya ce "Nazo sanar maka abin da baka sani ba, kuma kasan cewa duk sirrinka a tafin hannuna yake...A shekarun baya nasan bazaka taɓa manta babban abokin mahaifin Maleekh ba wato Alhaji Abdulsamaad...." Alhaji Wadata ya yatsina fuska ya ce. "Yanzu me ya kawo maganar mutumin da ya daɗe da mutuwa nan..." Alhaji Gusau ya tintsire da wani irin dariya, sannan ya ce. Alhaji Abdul-Majeed mahaifin Maleekh babban abokin Alhaji Abdulsamaad mahaifin Amal wacce tayi silar shigar da ƴar ku cikin cell...." Hajiya Sa’adatu zaro ido tayi waje tana kallon Alhaji Gusau..Shima Alhaji Wadata ƙirjinsa ne yayi wani irin bugawa, shi dai Zayd bai san komai game da abunda ake faɗin ba... Alhaji Wadata tsabar ya rikice cikin tashin hankali ya ce. "Kana nufin ɗiyar marigayi Abdulsamaad tana raye?..." "Hhhhhh! Har da uwar marigayin duk suna raye, su biyu suke raye anan garin Abuja, kuma Maleekh ne ya siya musu gida, tana aiki kuma a campanyn sa..." A cewar Alhaji Gusau... "Innalillahi wa inna ilaihi raji’un..." Alhaji Wadata ya kama kai cikin tashin hankali... Hajiya Sa’adatu ta ce "Mun shiga uku, Alhaji kun kashe maciji baku sare kai ba, na tabbata wata rana gaskiya zata fito..." Zayd yana kallonsu a baibai ya ce "Wai akan wa kuke magana ne yanzun?..." Hajiya Sa’adatu ta daka musa tsawa da cewa "Kai dallah kayi wa mutane shiru.." Alhaji Gusau ya ce "A'a ku kwantar da hankalinku"... ya kalli Alhaji Wadata sannan ya ce "Kai ka manta da tsarin ne?..." Ya ciro wani memory ya soka a jikin plasman...A cikin wannan memory flash babu komai a ciki sai video lokacin mutuwar Iyayen Amal... LABARIN MUTUWAR IYAYEN AMAL... A shekarun baya, mahaifin Amal yana daga cikin hamshakan masu kuɗin Nigeria 🇳🇬...garin Kaduna.. Kuma masu gaskiya da riƙo amana, shi da mahaifin Maleekh shiyasa wasu daga cikinsu suke jin haushinsu, a cikin maƙiyansu mahaifinsu Farha yana daga ciki... Wata rana da daddare misalin ƙarfe 2. Wasu motoci suka parker a ƙofar gidan Alhaji Abdulsamaad, suka fara knocking, mai gadin gidan ya tambaya suka sanar masa cewa "Alhaji Wadata ne yazo..." dake shima abokin maigidan ne...jin hakan yasa maigadi ya buɗe tare da mamakin zuwansu cikin dare haka... Already sun zo da ƴan daba, shigowar su suka harbe maigadi take ya mutu... Alhaji Wadata da Alhaji Gusau ne su biyu sai ƴan daba suka kutsa ciki.. Knocking suka fara yi a ƙofar falo, a lokacin Matar gidan ta fito ɗaukan ruwa a frig, jin knocking yasa ta tsorata tana mamakin a wannan daren za'a zo musu. Tayi ƙarfin halin cewa "Waye ne?.." Murya daga waje ne ya ce "Su Alhaji Wadata ne, abokin mai gidan..." Hajiya Khadija cike da mamaki ta ce "abokin takarar mijina mai ya kawo shi cikin daren nan?..." Amma ta kawar da wannan tunanin ta je ta buɗe musu.. Ganin ƴan daba sun shigo da manyan bindigai yasa ta ja baya a tsorace, sai ga Alhaji Wadata da Alhaji Gusau sun shigo suna wani irin shu'umin murmushi.. Wani daga cikin ɗan daba ne ya ɗora mata bindiga suna daka mata tsawa da cewa "ta kaisu can ɗakin da Alhajin yake..." Hajiya Khadija a fusace ta ce "Tsautsayi ne da ƙaddara yasa na buɗe muku domin nasan ku ɗin maƙiyanmu ne, ƴan adawarmu, kuna neman kujerar takarar mu ne yasa zaku nemi rayuwarmu? Macuta azzaluman bayi....in Allah ya yarda ƙarshen ku bazai yi kyau ba..." Alhaji Wadata ne ya zabga mata mari tare da tura ta akan su wuce yanda Alhaji yake... Haka suka yi gaba zuwa upstairs... Alhaji yana bacci ya ji an tura ƙofa da ƙarfi, tashi yayi tana faɗin "Haba Khadija ke kin ƙi bacci kuma kin hanani yi? Kinsan fa gobe inada meeting da zan gudanar da sassafe, don Allah ki barni nayi bacci na .." Ita kuwa ba abunda take sai kuka, kamar a mafarki Alhaji ya ji ance. "Sai dai ka gudanar da meeting a lahira, ba dai a nan duniya ba..." A zabure Alhaji ya tashi zaune.. Khadija tana kuka ta ce "Ku ma ai ba tabbata zakuyi a duniyan ba..." Wani daga ciki ne ya buga mata bindiga a kai har sai da ta faɗi ta suma, shi kuma sun ɗago shi tare da zaunar da shi akan kujera sannan suka ɗaure shi da igiya.. Alhaji yana kallon Alhaji Wadata da Alhaji Gusau ya ce . "Nasan daman wannan lokacin zai zo, burinku shine ku ci amanar ƙasa kuma na kafe na tsare babu wani dama, shine yanzun zaku shigo mun gida?..." Alhaji Gusau ya ce "Ka kalle mu tamkar mala'ika azara'ilu domin mun shigo tafiya da ranka ne..." Abun mamaki maimakon ya ji tsoro sai ji sukayi Alhajin yana dariya, daga bisani ya ce: "Kun ban dariya matuƙa, domin babu wanda rai yake hannunsa face Ubangiji, don haka kar kuyi tsammanin ku ma zaku bar nan a raye, domin rai a ƙididdige yake...amma sai dai komai da silar sa, idan hakane burinku to a shirye nake dana amsa ƙiran ubangijina, kuma zan tafi ina alfahari da al'umma suna yi na, na riƙe gaskiya bisa amana..." Alhaji Wadata ya ce: "Kar kayi tunanin haka zaka mutu ka tafi, dole sai kayi abu ɗaya domin ceton matarka da ƴarka ɗaya tilo a duniya da kuma mahaifiyarka..." Alhaji Abdulsamaad jin an ambaci iyalainsa yasa shi girgiza ya ce. "Inason duk hukuncin da zaku yi mun kuyi akaina kawai, ku kyale su, zan amshi duk abinda kuke so amma ku kyale mun iyalaina..." "Okay! Abin da muke so shine, zamu kunna video recording kayi bayanin cewa babban abokinka Alhaji Abdul-Majeed shine wanda yake neman rayuwarka, kuma ka bayyana cewa yanzu zaka mutu shine yasa a kashe ka sannan ya kwashe duk takardun dukiyarka da duk abinda ka mallaka..." Alhaji Abdulsamaad a fusace ya ce "Akan me zanyi masa wannan sharrin alhalin bai ji ba bai gani ba? Bazai taɓa yuwa ba..." Alhaji Wadata ya kalli ɗaya daga cikin ƴan daba ya ce "Ku fara harbe kwakwalwar matarsa kafin guje ku ɗauko mun ƴarsa da uwarsa mu gama da su kafin shima ya bi bayan su..." Har an kunna kunamar bindigar za'a harbe Hajiya Khadija dake kwance a ƙasi sumammiya da sauri Alhaji Abdulsamaad ya dakatar da su a tsorace yana faɗin. "Ku dakata dan Allah, ku dakata zanyi abun da ku ka ce..." Alhaji Gusau ya ce "Okay, yanzu zamu since igiyar da aka ɗaure ka saboda kar ayi tunanin tirsasa ka akayi, za'ayi tunanin ka fake ne kai ɗaya ka zayyana gaskiya kafin mutuwarka..." Kamar yanda suka tsara hakan akayi, sai da aka since shi, sannan aka haska camera ya fara video, Alhaji Abdulsamaad yana hawaye ya fara zayyana abun da suka umarce shi.... Cewar "Alhaji Abdul-Majeed ne yake neman rayuwarsa, sannan yasa karɓe masa takardun dukiya da gidajen da yake da shi da duk wani abunda ya tara ta hanyar barazanar kashe iyalainsa........" Duk abin da ya faɗa a cikin video su suka tsara masa, bayan ya kammala ne suka sa ya basu duk takardun dukiyarsa, da check na babban bankinsa yayi musu signed yanda zasu ɗebe kuɗaɗen gaba ɗaya, yasa musu hannu a takardun gidajensa da filayensa har da gonayensa dake can ƙauye da saniyoyinsa da duk abunda ya mallaka a duniya, duk sun karɓe....Babu abin da ya saura yanzu.. A ta bakin ƙofa kuwa Inna wacce a lokacin suke ƙiranta da Uma, tana leɓe duk ta saurari tattaunawarsu daga farkon shigarsu....jin an tura wani daga cikin ƴan daba cewa, "ya je ya dubo ƴarsa da uwarsa shin suna nan?.." yasa Inna ta juya da gudu, kai tsaye ɗakin Amal ta nufa duk da ƙarama ce a lokacin bazata wuce shekara uku ba amma ɗakinta da ban.....Inna ce ta shiga ɗakin Amal ta kwanta a gefenta a yayinda Amal take bacci... Sai da ta tabbatar da ɗan daban ya shigo ya same su suna bacci kafin ya juya yabar ɗakin, yana fita Inna ta ɗauki jakar Amal na makaranta ta zuba kuɗin dake jikinta sannan ta goya Amal a baya tana bacci suka fita da gudu, ta ɓoyayyen hanya suka fi a gidan wanda babu wanda yasan da hanyar suka fita domin ta can get ɗin akwai wasu ƴan daba da suke tsare da hanya... Ɗan daba ne ya sanar musu cewa "Duk suna bacci..." Alhaji Wadata ne ya ce: "Bar su suyi baccin su yanda suna farkawa zasu tsinci kansu a lahira..." Alhaji Abdulsamaad hankalinsa ba ƙaramin tashi yayi ba, yanata roƙon su da Allah akan su kyale su... "Kun mun alƙawarin idan kuka samu kpmai zaku ƙyale iyalaina, meyasa zaku ci amana, kun sa nayi wa babban abokina sharrin da bazai taɓa goguwa ba wanda hakan zaiyi silar ruguza shi, sannan na baku duk abin da na mallaka, sannan kun nemi rayuwata kuma duk na baku da sharaɗin ƙyale family na, kuma kuma Shalelena ƙaramar yarinya ce, bata san komai ba, ku ji tausayin yarinya mana..." Haka yake kuka kamar ƙaramin yaro... Amma duk da haka basu saduda ba, Hajiya Khadija tana sume amma haka suka sa bindiga suka harbe kanta...😭😭😭 Sannan suka sanar wa ƴan dabar cewa su zuba wa ko ina petur su ƙona gidan da mutanen dake gidan... Suka nuna Alhaji Abdulsamaad da yatsa cewa "baza mu harbe ka ba domin bama so kayi mutuwar sauƙi wato fatt ɗaya, so muke kaita kururuwa a ciki wuta babu wanda zai jiyo ka har ka mutu, haka mahaifiyarka da Shalelenka wacce kake matuƙar ƙauna itama Allah sarki wuta ne ajalinta..." Alhaji Wadata ya ƙara da cewa "Ina tausayin yara da tsofi hakan yasa baza mu harbe su ba, wuta zata yi aikinta... Su na dariyar mugunta suka bar Alhaji Abdulsamaad a ɗaure a kujera, sun bar gidan bayan sun tattara komai har da su gwalagwalai Hajiya Khadija..... An gama saka petur a ko ina, ganin petur bazai musu yanda suke so ba suka ƙara da kunna gas...sannan suka cilla wuta a gidan.. Su kuma suka shiga motocinsu suka bar yankin kamar basu taɓa zuwa ba.... Sai washegari aka tarar da asarar da aka tabka... Alhaji Abdul-Majeed ba ƙaramin girgiza yayi ba, har sai da ya suma kusan sau biyar, ya ji mutuwar babban abokinsa wanda bazai taɓa samun aboki like him ba... Ganin babu wani shaida ko hujja akan abunda ya faru ne yasa aka baza cewa gobara ce ta kama cikin dare a gidan Alhaji Abdul-Majeed, an sara rayukan mutanen gidan, da shi Alhajin da Matarsa da Ƴarsu da Mahaifiyar Alhaji da maigadi......A haka labarin ya wuce... Inna kuwa da Amal can wani ƙauye suka nufa, wato ƙauyensu Mahaifiyar Amal, ƙauyen su Malam Yawale. Anan suka cigaba da zama, har suka yi shekara guda..... Anan ne Malam Yawale ya basu haƙurin cewa shima dawainiya ya masa yawa bazai iya riƙe su ba.. duk da yana Yayan Mahaifiyar Amal amma ya kasa riƙe su, babu yanda basu zagaya ba amma kaf ƴan uwa sun kasa riƙe su.. Sai da Inna da Amal suka ɗau shekara biyu zuwa uku suna zagaya ƴan uwa kafin suka koma cikin Kaduna ganin babu mai taimakonsu, a ƙauye Uma ta samo sunanta Inna... Suka samu wani yanki na talakawa a garin Kaduna suka zauna, Inna ta cigaba da neman kuɗi tana biyan kuɗin haya duk shekara dubu 20 dake ƙaramin gida ne, babu fasali ga kuɗin makarantar Amal da ta sakata, ita kuma Amal taƙi ko wani school sai na ƴan gayu, wato irin makarantar da ta fara yi tin farko, ba yanda Inna ta iya haka ta sakata a private school, tana amsa ƙira Amal Abdulsamaad saɓanin asalin sunan Amatullah Abdulsamaad Cash maker.. Inkiyar sunan mahaifinta kenam " _CASH MAKER"_ A school ɗin Amal ya haɗu da babbar ƙawarta A'isha, ƙanwar Maleekh... Har Amal ta girma ta samu aiki a gidan rediyo Rayuwa FM. Ta fara biyan kuɗin hayan gidan da suke... Anan Inna ta sanar mata cewa "Mahaifinta ɗan siyasa ne, kuma maƙiyansa ƴan siyasa ne sukayi silar mutuwarsa ta hanyar dasa gobara saboda riƙon amana da gaskiyar da yake da shi, baya karɓan cin hanci sannan baya karɓar kuɗin ruwa, ya tara dukiya ta halal kuma an karɓe su, bamu tsira da komai ba sai da jakar makarantarki da wasu photunanki da kikayi da abokinki Maleekh, na zuba wasu kuɗi a ciki wanda zamu yi amfani da su..." Inna ta ƙara da cewa "Wannan sirrinki ne Amal, ki zamo mai gaskiya kamar mahaifinki,..." Amal ta sha tambayar inna "su waye suka kashe mun iyaye?..." Inna sai dai ta sanar mata cewa: "Wasu ƴan siyasa ne amma bata sanar mata su waye ba balle ta ambaci sunan su..." A haka aka cigaba da tafiya hakan yasa Amal ta tsani duk wani ɗan siyasa marar gaskiya a lokacin da take aiki a rayuwa FM, ba yanzu da ta zama ƴar love ba.... An dawo daga labarin... Alhaji Wadata da Alhaji Gusau da Hajiya Sa’adatu da Zayd suka tsaya suna kallon video da Alhaji Abdulsamaad yake magana cewa "Alhaji Abdul-Majeed ne yake neman rayuwarsa, video ya daɗe yana showing kafin suka kashe, Alhaji Wadata ya karɓi memory ya ce "shi zai ci gaba da ajiyarsa a wurinsa tinda Allah bai yi zasu basa labarin ba a wannan shekara..." Alhaji Gusau ya ce "Hanya ɗaya mafi dacewa a baza labarin nan shine, mu jira kotu ta gama aikinta, bayan haka sai mu sa a kashe ita yarinyar wato ƴar macijin da muka kashe, bayan mutuwar ta zamu sa a sanar cewa Alhaji Abdul-Majeed ne yasa a kashe ta, mutane zasu yanda ta hanyar ganin wannan video mahaifinta..." Hajiya Sa’adatu ta ce "Yanzu duniya bata riga tasan wacece Amal ba, amma zamu fitar da hakan bayan mutuwarta ta hanyar baza wannan video..." Alhaji Wadata ta kalli Alhaji Gusau cike da mamaki ya ce "Amma taya ka gane cewa yarinyar nan ɗiyar Marigayi ce?..." Alhaji Gusau yayi dariya sannan ya ce. "A Kaduna tana yawan fitowa a gidan rediyo da television dake aikinta ne, tana yawan ƙalubalantar ƴan siyasa, kullum maganarta akan ƴan siyasa ne, ta yanda na gane hakan shine a bikin A'isha ƴar Amaryar Alhaji Abdul-Majeed ta bada tarihinta duk da ba cikakke bane amma ta sanar cewa "iyayenta sun mutu ta hanyar gobara, a wani kafar sadarwa ta sanar cewa iyayenta sun mutu ta silar siyasa...Hakan yasa na ƙarfafa bincike akanta, acan bayan iyayenta na da rai tana amfani da suna Amatullah Abdulsamaad Cash maker, yanzu kuma Amal Abdulsamaad, naga ba abin da ya bambanta, da haka har na samo asalinta....." Alhaji Wadata ya ce "Kanada wayo sosai ..." Duk suka kwashe da dariya... Zayd ya kalli mahaifiyarsa ya ce: "Mom. Ya batun kashe Maleekh?..." Hajiya Sa’adatu ta ce "Ka dakata mun sai an gama da wannan yarinyar kafin a dawo kansa, domin zata iya bamu matsala nan gaba..." Zayd kamar zai yi kuka ya ce "Mom, na fara sonta fa..." "Son ɗin banzaaaa, dallah ja baya..." A cewa Hajiya Sa’adatu tana daka masa tsawa... Alhaji Gusau ya duba agogo ya ce "Kun ga yanzu lokaci yayi, kotu tayi ƙira..." Hajiya Sa’adatu ta zabura kamar zata yi kuka ta ce: "Dan Allah mu tafi wayyo daughter na, inason ganinta, ban san wani hali take ciki baaa...abun kunya ƴarta ta kwana biyu a cikin cell..." Duk suka fita.. Kai tsaye kotu suka nufa.. ••••••••••••••••••••••••••••••••• Kotun ta cika da jama’a. An jera wasu manyan kujeru, alkalin yana zaune a tsakiyar kujerarsa cikin baƙar riga da hular court, yana duba takardu a gabansa... A gefe guda, Amal tana zaune cikin hijab ɗinta, fuskarta a nutsuwa amma idonta na nuna zafin zuciya da ciwon tozarcin da aka yi mata...ba kuma son zaman kotun nan take ba gaba ɗaya a tsorace take.. A gefenta Lawyer ɗinta ke tsaye — babban lauyan da Maleekh ya ɗauka domin kare ta... A gefe guda kuwa, Farha tana tsaye a rikice, tana hawaye. A gefenta kuma Doctor Khalid, wanda ya taimaka wajen ƙirƙirar ƙazafin da suka yi kan Amal, yana ta zufa da motsa labbensa cikin rashin natsuwa... Su ne “defendants” a gaban kotu... A kujerun masu sauraron kallo Maleekh na zaune a baki baki— cikin farin suit, yana kallon Amal da idanu masu cike da tausayawa... Bai ce komai ba, amma duk wanda ya kalle shi yasan yana cikin baƙin ciki... Ya yi tsayin daka ya shigar da ƙarar da kansa domin kare sunan Amal, bayan tozarci da ya bazu a kafafen labarai... Ammy tsabar takaici bata ma zo kotun ba, sai Abbah da Islam da Arfat... A gefe guda kuma Inna ce zaune da wasu mutane.. Acan baya Hajiya Sa’adatu ce take ta hararar Amal da Maleekh.. ga su Alhaji Wadata da Alhaji Gusau da Zayd.. Farha ce ta fashe da kuka tana faɗin "Wallahi ƙarya ake mun ban aikata komai ba, Maleekh ya tilasta ni ne akan na faɗi haka a TV saboda manufarsa..." Maleekh sake baki yayi yana kallonta cike da mamaki jin yanzu tana ƙaryata ƙarar da ake tuhumar ta... Maleekh ne ya miƙe cikin fushi yana faɗin. "Ƙarya kuma? Da bakin ki kika amsa laifinki fa a gaban duniya kowa ya ji kuma ya saurara, please Farha kar ki wahalar da kotu..." Lawyer da yake Hajiya Sa’adatu ta ajiye domin kare Farha ne ya miƙe ya ce wa Maleekh "Please ka saurara, nan kotu ne ba kasuwa ba, dole sai anyi bincike domin bazamu yadda da barazanar da kayi mata saboda wata manufarka ba, mu kotu ba shashashu bane..." Maleekh ya ce "To ayi bincike mana, nima ai ba shashasha bane, sai da na tabbatar da hujjoji kafin na kawo kotu..." Alkali ne ya buga guduma yana faɗin "Nan kotu ne ku nutsu.." Maleekh ya zauna yana huci.. Alkali: ya dube su gaba ɗaya cikin nutsuwa "Wannan shari'a ce tsakanin Miss Amal da waɗanda ake tuhuma Miss Farha da Dr. Khalid. An shigar da ƙara bisa ƙarya, ƙazafi, da yaɗa labaran ƙarya a kan mutunci da suna na wannan baiwar Allah. Kotun nan zata tabbatar da adalci, ba tare da son rai ba." Lawyer Amal ya miƙe cikin izza: "My Lord, mu muna gabatar da hujjoji masu ƙarfi. Wannan yarinya ta tozarta, ta rasa mutunci saboda ƙarya da makirci. Akwai sauti da hotunan da suka nuna cewa waɗanda ake tuhuma sun tsara wannan komar da nufin lalata sunanta da kuma tarwatsa aikinta a kamfani..." Ya nuna takardu. Aka kunna recording wayar da aka saurari muryar Farha tana cewa: “Na gaya miki hanyar da zaki samu Maleekh? To ki tafi gidan club. Ki je can zaki same shi, kuyi bankwana na ƙarshe.…” Wannan Islam ce tayi recording a yayinda Farha take sanar wa Amal... Recording na biyu. "Kasan nan ɗin nawa ne?....Kimanin 2 billion dollers ne. Kuma duk naka ne idan ka yi mun abu ɗaya kawai." "Yarinyar da aka kawo jiya da daddare Amal. Nasan result ya nuna ba ciki a jikinta, kuma bata sha maganin zubar da ciki ba....." "Ina so ka canza result ɗin. Ka rubuta cewa Amal ta zubar da cikin wata huɗu, ka tabbatar labarin ya zama ya shiryu, yanda babu wanda zai iya ƙaryatawa..." Duk wannan recording an same shi a wurin wata nursing da ta laɓe ta saurari tattaunawar su.. Jama’a suka cika da mamaki. Farha ta sunkuyar da kai... Doctor Khalid ya fara zufa sosai... Alkali ya ce: “Ina ganin akwai hujja mai karfi a nan.” Lawyer ɗin Farha ya miƙe yana ƙoƙarin kare su: “My Lord, abinda aka faɗa ba nufin ɓata suna bane, kawai tsokaci ne…” Amal ta fashe da kuka tare da faɗin: “Na rasa mutunci, na rasa suna mai kyau, saboda su suka ƙirƙiri ƙarya a kaina. Na kunyata saboda wannan al'amarin… amma yau na dawo neman adalci.” Kowa yayi shiru. Lokacin da Maleekh ya kalli Amal, hawaye ne ya cika idonsa saboda tuna irin wulakanci da yayi mata, amma ya daure... Alkali ya ce “Kotun ta saurari ƙarar da hujjoji, kuma daga ganin gaskiyar al’amari, akwai tabbataccen shaida akan waɗanda ake tuhuma. Saboda haka kotu zata yanke hukunci a zama na gaba. Amma kafin nan, ana buƙatar su rubuta bayani na gaskiya (written confession) kafin kotu ta ɗauki mataki na gaba.” Ya buga guduma. “Case adjourned till next week.” Kotun ta watse da hayaniya. Farha ta yi ƙasa da kai tana hawaye, a lokacin iyayenta suka nufe ta cikin tausayawa... Amal ta durƙusa ta gode wa Allah, ko ba komai yanzu ta wanke kanta a kallon da mutane ke mata, amma har cikin zuciyarta bata son a yanke musu wani hukunci... Maleekh ya tsaya a bakin ƙofa yana kallonta da murmushi mai taushi, idonsa cike da nutsuwa.. “Kin yi nasara, My Beb… gaskiya ta fito fili.”... NEXT NEXT NEXT.... asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 61 to 62 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Monday morning.. Zaman kotu na biyu rana mai cike da alhini (public trial) Babban kotun tarayya. A babban ɗakin shari’a, kujeru sun cika, ‘yan jarida, jama’a, manyan mutane, da kuma masoyan ɓangarori biyu. Ana shirye-shiryen zaman sauraren shari’a: an zaɓi majalisa, alkalai uku, da lauyoyi a shirye. Farha da Doctor an kawo su cikin tsaron ‘yan sanda, suna zaune a gaban masu tuhuma. Fuskokin mutane sun cika bege da kuma kallo da sauraron hukunci; ƴan jaridu suna ta ɗaukan videos da photuna.. An Fara shari’a lauyoyi masu ƙara sun gabatar da hujjoji. Chief Prosecutor (wani lauyan gwamnati): ya tsaya, ya juya ya dubi kotu tare da faɗin. “Mai girma Alkalinmu, al’ummar nan sun shaida yadda ake shirin halaka sunan wannan yarinya; akwai bidiyoyi, sakonni, rubuce-rubuce, takardun labo na asibiti da aka canza; akwai shaida daga admissions na club; kuma akwai shaida daga bakin wanda ya yi wannan manufa. Mun gabatar da manyan hujjoji guda uku: (1) shaidun bidiyo da aka tura wanda Farha ta sa. (2) canza result na doctor wanda ke nuna akwai zubar ciki (wanda asali ba haka ba ne), (3) confession na wasu masu laifi da aka kama a hannu akwai rubutu da hotunan da suka nuna Farha ta shirya wannan aikin tare da mata kawayenta..” Alkali yana gyara takardun ya ce: “Mu fara sauraren shaida daga witnesses. Kawo shaidu.” Shaidu na farko Security na club, mai gidan club da witness na farko Wanda yake kula da tsaro a club ya hau tambari; ya bada labari yadda Amal ta shigo, yadda wasu ‘yan mata suka bata drink ta sha, yadda suka kulle ta a male’s toilet, yadda suka yi injection da kuma yadda aka samu jini da kayan zubar da ciki a wurin. Ya bada hotuna da videos, domin akwai CCTV... Kwamitin Mutane a kotu suka cika da mamaki; Farha ta lumshe idanu, ta zamo kalar tausayi.. Shaida na biyu wanda ya gano bidiyon (friend/informer) Wanda ya samu video mai ɗauke da kisan sunan Amal ya bada labarin yadda Farha ta umarci asa a social media... Shaida na uku Doctor yayi confession A nan an kawo doctor. Lauyan karewa ya yi ƙoƙari ya kare shi; amma bayan gagarumin hujja (jakar kudi, record maganganun da suka yi da Farha a office daga wata nurse da ta saurara, saƙonnin waya daga Farha), doctor ya soma faɗa cikin ƙarar sa. Bayan an yi masa tambayoyi mai ƙarfi, an sami confession, doctor ya tabbatar da canza sakamakon (falsifying medical report) saboda kuɗin da Farha ta kawo... Doctor cikin rawar murya ya ce: “Na karɓi kuɗin. Na canza sakamakon. Na yi laifi. Ina roƙon Allah gafara; na yi kuskure babba.” A wannan lokaci, ofishin kotu yayi shiru sosai, mutane suna girgiza kai cike da mamaki da baƙin ciki.. Shaida na hudu Amal ta yi bayanin abin da ta fahimta Amal ta hau, tana ƙanƙancewa cikin sanyin jiki, ta gaishe kotu, ta yi shaida: labarin tafiyarta zuwa club (shin ta tuna wani abu?), yadda ta tarar da kanta a male’s toilet, yadda jinin ya ratsa jikinta, yadda take samun hotuna a social media, yadda abin ya lalata mata suna. Kuma ta bayyana yadda ta kasance ba ciki, yadda doctor ya canza sakamakon... Amal cikin kuka da ƙarfin hali ta ce. “Ina neman adalci. Don Allah a hukunta wadanda suka shirya wannan sharri.” Lauyoyin kare Farha da doctor sun yi ƙoƙarin kare su: sun nuna dalilai, gargaɗi, zancen ko an tilasta doctor ko kuwa an yaudare shi. Amma lauyoyin gwamnati sun tada hujjoji masu nauyi: hotunan, bidiyon, confession, shaidu, saƙonnin waya. Kotun ta ci gaba da watsi da rawar karewa. Jawabin Alkali Bayan an rufe shari’a da hujjoji, alkali ya ɗauki lokaci kaɗan, ya tsaya ya dubi duk wanda ke gaban kotu. Alkali cikin murya mai nauyi ya ce. “Mun ji hujjoji. Mun ga bidiyo, takardu, shaidu. Wannan ba ƙaramin laifi ba ne kisan suna, kokarin halaka mutum, da conspiring to defraud, da tampering with medical records. Wannan al’amari ba kawai laifi ba ne, har ma cin amanar rayuwa ce. A bisa hujjojin da aka gabatar, kotu tana ganin akwai isasshen hujja da ke nuna laifin Farha da Dr Khalid.” Ya dubi fuskar Farha da doctor sannan ya ce: “A yanzu ina yanke hukunci na masu laifi: Farha an same ki da laifin conspiring, defamation, conspiracy to harm, attempt to cause grievous bodily harm. Doctor an same ka da laifin forging medical records, accepting bribe, and conspiracy. Kotun na hukunta Farha da shekara 5 a gidan yari, tara tarar kuɗi, kuma an umarci a yi mata restitution. Doctor kuma an hukunta shi da shekara 2 a gidan yari, ya rasa lasisin aiki na dindindin (revocation), da kuma toshe sunansa daga aiki a asibiti... ” Sauran masu hannu a ciki (kawayen Farha) an gudanar da ƙarin bincike. Kotun ta umurci social media da jaridu su share duk wani abu game da rashawa da zargi da suka tura (injunction), kuma an bayar da umarnin a dawo da mutuncin Amal, tare da neman a biya ta diyya don asarar sunanta. Sannan gargaɗi ya zo daga Alkali: “Wannan hukunci ne na riga. Duk wanda ya taimaka a wannan sharrin zai fuskanci hukuncin da ya dace.” Farha ta zunduma ihu, iyayenta suna faman rarrashi tare da ƙarfafa mata gwiwa cewa zata fito nan da wata ɗaya.... Jama’a sun yi yabon adalci, wasu na jin takaici, wasu na tausayawa Amal. Amal ta faɗi ƙasa tana kuka domin bata yi farin cikin wannan hukunci ba saboda tasan yanzu ba ita ba auran Maleekh, Inna ta rungume ta tana bata hak'uri, Maleekh ya tsaya a gefe yana kallonta ya kasa furta komai... Bayan an watse, Abbah, Maleekh, Amal da Inna sun zauna a wajen kotu. Abbah yana rarrashin Amal: Abbah yana riƙe da hannunta ya ce: “An yi adalci yau. Ban ce duniya ta koma kyakkyawa ba amma wannan hukunci zai yi mana amfani. Ki yi haƙuri...” Maleekh ya matsa kusa da Amal yana murmushi mai rauni ya ce. “Beb, ni nayi ƙoƙarina Inma baki ga hakan ba. Na yi alƙawarin zan share miki hawaye. Wannan hukunci zai zama misali ga duk masu son yin sharri a rayukan mutane.” Amal ta kallesa, idanuwanta sun yi sanyi ta ce “Na gode. Amma akwai abin da ke damu na a raina...” Inna ta yi murmushi kaɗan, ta dubi Maleekh da kallon godiya, ta ce: “Allah ya kawo mana wannan rana. Na yi nadama da abubuwan da na ce a baya amma yanzu zan gyara komai. Mabud'in shine hakuri da addu’a.” A wannan ranar Farha da Doctor sun tafi gidan yari, duk da yiwuwar daukaka ƙara, amma shaidun sun yi masu yawa. Amal ta samu diyya da umarni na shari’a: a farfaɗo da kundin da aka wallafa a social media, a share hotuna, a biya mata diyya... Al’umma sun koyi darasi, shari’a ta nuna cewa ba za a bari zalunci ya yi galaba ba. Bayan Amal da Inna sun tafi a motarta.. Abbah shima ya shiga motarsa ya tafi. Maleekh yana shirin shiga motarsa cikin nutsuwa, fuskarsa cike da gajiya da tunani. Sai ji yayi an furta sunansa da ƙarfi, Zayd ne ya nufo wurinsa fuska a ɓace, zuciyarsa cike da fushi... Zayd yana huci, ya kai hannu ya shaƙo kwalar rigar Maleekh, tare da haɗin. "Ka bani mamaki, Maleekh! Baka da imani! Sannan baka da kunya! Ka kai ƴar uwata gidan yari saboda mace?! Saboda wancan yarinyar nan Amal?!" Maleekh yana ƙoƙarin kwace kansa daga riƙon, yana magana cikin natsuwa amma idonsa na nuna haushi tunzura ya ce: "Ka sake ni, Zayd... ka sake ni kafin in manta kai ɗan uwana ne...! Ka sauƙe hannunka da kyau kafin kayi nadama." Zayd yana dariya mai zafi ya ce: "Nadama? Kai zaka sa ni nadama?! Kai wanda ka lalata sunan mu gaba ɗaya saboda soyayya? Kai wanda ka tozarta iyayenmu saboda mace marar asali? Wallahi baka cancanci ƙiran ɗan family ba!" Maleekh ya fisge hannunsa daga kwalar da yayi masa, yana fuskantarsa, murya ta dushe cikin ƙarfin zuciya ya ce: "Yau pretty ɗinka ce marar asali Zayd? Yau ita kake ƙira da wannan kalmar?… to kada ka sake! Idan baka san darajarta a gurina ba, ka fara koya daga yau! Amal bata da laifi, ku ne masu zuciyar duhu, kuna ganin ƙimar mutum tamkar bola..." Zayd yana jijjiga hannunsa cikin ɓacin rai ya ce: "Kai ɗan wulakanci ne Maleekh! Ƴar uwarka ta wulakanta saboda kai! Ko ka manta Farha ƴar uwarka ce? Kayi mata wannan tozarci saboda ƙalilan ɗin mace da ta iyayenka basa na'am da ita...! Kana da tabbaci zaka aure ta ne? Impossible.." Maleekh ya bugi ƙirjinsa da ƙarfi, yana nuna masa yatsa ya ce: "Banaso yanzu a ga laifina da yawa saboda na dake ka akan wacce nake so, saboda haka ka ƙyale ni da wani batun Farha! Farha ita ta jawo akanta, ba ni ba! Kai kuma, kar ka sake ce min na tozarta ƴar uwata saboda ban taɓa wulakanta ta ba, kawai na kare wanda ba kowa ke iya kareta ba!" Zayd yana ɗaga hannu kamar zai mare shi ya ce: "Wallahi idan baka daina wannan haukar soyayyar ba sai na nuna maka ni ɗan family ne, ba kai ba!" Maleekh yana girgiza kai ya ce: Bana sa'in sa da mutum saboda nafi ƙarfin haka, don haka ka tafi ka bani wuri, ni ba sa'anka bane.." Zayd ya saki numfashi da ƙarfi, yana nuna shi da yatsa cikin fushi. "Wallahi wannan soyayyar zata hallaka ka, Maleekh. Kai kaɗai kake tunanin kana da iko, amma ba zaka iya cin karo da dangi ba!" Maleekh ya ƙare shi da kallo mai tsanani, ya ce cikin zafin rai. "Dangin banza da wofi, akan su nake rayuwa ne? Ko zan mutu in ba su? To ka je kace wa Dangi basa gaban Maleekh, ni ba ta su nake ba, da su da babu su duk ɗaya ne a guna, Iyayena waɗanda suka haife ni sune rayuwata... That's all...." Zayd ya tsaya kallonsa cikin mamaki da takaici, zuciyarsa na tafasa, kafin ya juya ya tafi yana bugan ƙasa da ƙarfi... Maleekh ya tsaya da numfashi mai nauyi, ya rufe idonsa yana furta cikin sirri: "Ku tsane ni gaba ɗaya... amma soyayyata da Amal... ba wanda zai iya raba ta."... Da yamma gidan Abbah ya cika da hayaniya... Hajiya Sa’adatu mahaifiyar Farha tana zaune a kujerar falo, tana jijjiga ƙafafunta cike da ɓacin rai. Gidan ya cika da manyan ‘yan uwa, wasu daga ciki daga Kaduna suke wasu daga Kano wasu daga Borno, duk an hallara, saboda jin labarin abin da Maleekh ya aikata... Hajiya Sa’adatu tana ɗaga murya cikin ɓacin rai, tana faɗin: "Wallahi wannan abin kunya Maleekh ya jawo mana! Yaro kwata-kwata bai san darajar kowa ba, duk irin ƙaunar da ake nuna masa, yanzu saboda wata matsiyaciyar yarinya ƴar talakawa sai ya tozarta ƴar uwarsa?!" Uban Farha, Alhaji Wadata ya ce: "Duk duniya babu wanda ya tozarta ni kamar Maleekh, kuma bazan taɓa yarda da wannan abu ba. Maleekh bai san darajar asalin iyayensa ba. Ko da jini ɗaya ne tsakaninsa da Farha, wannan wulakanci da ya nuna ya isa a raba zumunci!" Zayd kuwa yana gefe yana share hawaye, yana kallon mahaifiyarsa da mahaifinsa, ya ce: "Wallahi Mom, ban taɓa tsammanin Maleekh zai zubar mana da mutunci haka ba. Ina alfahari da shi a matsayin ɗan uwa, amma yanzu na tsani jin sunansa ma." A gefe kuma Ammy mahaifiyar Maleekh ta shigo cikin falon cikin tsantsar fushi. Ta gama jin duk complain da ƴan uwa suke yi. Ta zauna tare da faɗin: "Ni ma dai na gaji! Na yarda da ku gaba ɗaya. Wannan yaron yanzu ya fita daga kulawata. Tinda ya iya hukunta ƴar uwarsa saboda mace, to ni bana da ɗa mai irin wannan hali! Wallahi ba zai taɓa auren waccan ƴar talakawar yarinya ba." Duk falon suka ɗauki hayaniya suna maimaita kalma ɗaya, wasu suna girgiza kai saboda baƙin ciki.. Daga can gefe, Islam da Arfat suna tsaye suna sauraron maganar cikin mamaki. Islam ta ce a hankali: "Wai duk saboda Yaya Maleekh ake so a lalata dangantaka? Kowa da abinda zai ce akansa, haba dallah, daman can basa sonsa, kuma wai har da Ammy wacce ta haife shi ake kushe shi..maimakon ta tausayawa ɗanta.." Arfat ta ce cikin tausayi: "Ai Yaya Maleekh yana cikin rikici... amma yanzu fa komai ya lalace..." Ana cikin wannan hayaniyar sai ga Abbah ya sauƙo daga upstairs, yana sanye da farar jallabiya, ya tsaya a tsakiyar falo yana kallon kowa... Kafin ya zauna, ya ce cikin natsuwa: "Ku saurare ni! Duk kun manta ne?, Maleekh ɗin nan fa ɗana ne, jinin jikina kuma ɗa namiji a guna ɗaya tilo. Kuma in har inada rai babu wanda zai kore shi daga wannan family, idan kuma kun ce a raba zumunci saboda shi to na amince nima a cire ni daga dangi, zan kula da shi da kaina. Tin da ni na haife shi to bazan taɓa gudun sa ba, bazan taɓa kushe shi ba a ko ina, saboda haka idan zaku ƙi ɗana to ku ƙi mu gaba ɗaya da sauran ƙannensa su biyu waɗanda suke jini ɗaya, domin mahaifiyarsa ma ba ƙaunarsa take ba, gata nan shiyasa za'a haɗu da ita a zage shi tasss..." Hajiya Sa’adatu ta ce tana turo baki: "To Alhaji, idan haka ne, mu dai bazamu ƙara zuwa yanda kuke ba. Tinda kana son ƙiyayya ta cigaba tsakanin yara." Sai ta ɗauki jakarta ta fice da mijinta. Ammy ta tsaya tana huci, tana faɗin: "To da kyau! Ku tafi. Ni ma daga yau ba zan sake kula Maleekh ba!" Abbah ya ce "Oh bazaki ƙara kula shi ba? To ai ba amfanin zamanki a gidan nan tinda gidan mahaifinsa ne, kuma ina sonsa sosai, don haka kema kama hanya kiyi tafiyarki bana buƙatar ganin maƙiyan ɗana, zan nema masa wata uwa mai ƙaunarsa ba ke ba..." Haka kowa ke fita waɗanda suka zo daga wani gari, duk Abbah ya kore su. Islam da Arfat ne suke roƙon Abbah akan ya bar Ammy ta zauna, da ƙyar ya barta.. Ammy tana kuka ta nufi ɗakin ta.. Abbah ya zauna a kujerarsa cikin nutsuwa, yana murɗa agogo, sannan ya ce a hankali: "Soyayya ta zama jaraba....." A ɓangaren Amal kuwa, Hajiya Sa’adatu mahaifiyar Farha ce ta ziyarce ta bayan barinta gidansu Maleekh da sauran ƴan uwanta... Inna tana zaune a falo tana lissafin abubuwa sai ga ƙarar horn ɗin mota ta dawo da ita daga cikin tunani. Kafin a ankara, motoci uku suka tsaya a harabar gidan bayan maigadi ya buɗe musu. An buɗe ƙofar mota, sai ga Hajiya Sa’adatu, mahaifiyar Farha, ta fito cikin hargowa da matsananciyar fushi. Tare da ita akwai wasu ‘yan uwa mata guda su biyar, duk sanye da kayan alfarma, amma fuskokinsu cike da ƙyama da hargowa. Maigadi ya yi gaggawar ƙarasowa yana tambaya, “Hajiya lafiya kuwa?” Ta ce da ƙarfi, “Ina Amal take? Muna son ganinta yanzu haka! Idan ba ta fito ba sai na sa an fito da ita da ƙarfi.!” Inna ta fito da sauri tana murmushi cikin tsoro, “Hajiya sannu da zuwa… lafiya kuwa?” Hajiya Sa’adatu ta ce cikin tsawa, “Lafiya? Lafiya ce bayan yarinyar nan ta jefa ‘yata cikin tashin hankali?! Ke kike zaune lafiya ita kuma Farha tana kwana a cikin kurkuku saboda irin ɗabi’un wannan yarinyar..!” Inna ta tsaya cak, ta kasa cewa komai. Sai Amal ta fito daga ɗaki cikin sanyin jiki, ta tsaya a bakin ƙofa tana kallonsu. Hajiya Sa’adatu ta kalle ta sama da ƙasa sannan ta matsa kusa da ita tana nuna ta da yatsa tana faɗin, “Ke ce Amal ko? Ke ce dalilin da yasa Farha take cikin wahala yanzu ko? Wallahi idan har ba ki sa Maleekh ya je yasa an yafewa ‘yata ba, rayuwarki zata zama ɗaya daga cikin ƙalubalen da ba za ki iya jurewa ba!” Amal ta ɗaga kanta a hankali, ta ce cikin murya mai rauni, “Wallahi Hajiya ba ni na saka Farha ta shiga gidan yari ba… komai da ya faru…” Hajiya Sa’adatu ta katse ta da cewa, “Karya kike yi! Ba sai kin faɗa min komai ba! Amma zan faɗa miki abu guda indai ba ki tsugunna kika nemi yafiyar farha ba, ki sa yaron nan Maleekh ya je ya sa Farha ta fito daga kurkuku ba, to zan tabbatar da kin fuskanci bacin rai da wahala da ba ta da misali!” Daya daga cikin matan da suka zo tare da ita ta ce, “Ai irin wannan yarinya ya kamata a koya mata darasi, saboda ta manta da asalinta! Tana ganin ta sami soyayyar ɗan masu kudi sai ta fara raina mutane.” Inna ta tsala kuka tana roƙon su da su yi hakuri, “Don Allah kuyi hakuri, wannan ba hanyar warware matsala bace..." Hajiya Sa’adatu ta ce "Daman ce miki akayi munzo warware matsala ne? Ai mu duk yanda matsala take nan muke tunkara, mu da kika ganmu nan bama son zaman lafiya ko kaɗan, idan har Amal bata sa an ciro mun ƴata ba to wallahi sai mun ƙona gidan nan da ku kan ku...." Daga nan tayi shiru domin ta san abun da ya faru da iyayen Amal kenam... Inna ta ji kanta ya fara juyawa tana tunanin ɗanta da yanda aka ƙona su da azabar wuta... haka jikinta ya fara rawa, gaba ɗaya ta gama tsurewa... Hajiya Hauwa’u wacce aka taho da ita ta ƙara da cewa: “Idan ba ki gaggauta ganin Farha ta fito ba, wallahi za ki ga tashin hankali a rayuwarki, aure? Ki manta da shi! Rayuwa? Zamu tabbatar kin shiga wahala fiye da ta Farha!” Inna ta shige tsakani cikin fushi ta ce: “Ku ji tsoron Allah! Wannan wane irin hari ne haka a gidan mu? Me yarinya tayi muku da kuka zo da cin mutunci haka? Saboda Kuna da ikon raina kowa? To wallahi Amal tafi ƙarfinku, idan baku ƙona mu ba, baku cika mutane ba...!” Hajiya Sa’adatu ta kalli Inna sama da ƙasa cikin raini, ta ce: “Ke ma tsohuwa, ki kula da bakinki! Idan ba ki koyar da ita hankali ba, zamu koya mata da hannunmu!” Sai ta juya tana nuna Amal da yatsa, muryarta tana rawar fushi: “Idan har kika wuce sati biyu ba’a saki Farha daga kurkuku ba, ki shirya da Inna taki! Rayuwarku za ta zama darasi ga masu taɓa mu!” Suka juya suka shiga motarsu suna ta harara da cizon baki, suka bar Amal da Inna cikin firgici da hawaye. Amal ta durƙusa ta dafe ƙirji tana faɗin cikin kuka: “Ya Allah… me yasa rayuwata ta zama irin haka?.. Ina zan saka kaina yanzu?” Inna ta zauna kusa da ita tana share mata hawaye tana faɗin: “Ki kwantar da hankalinki yarinyata… Allah ne kawai zai kareki daga mugayen mutane, ki dage da addu’a…” ☆☆☆☆☆☆☆ Maleekh bai dawo gida ba sai dare misalin ƙarfe 12. A falo ya tarar da Abbah yana zaman jiransa. Abbah yayi saurin miƙe wa tare da faɗin. "Maleekh aina ka tsaya haka sai yanzu? Baka saba kaiwa wannan lokaci a waje ba meyasa yanzu?..." Maleekh yana lumshe idanu alamun bacci yake ji sosai, ya ce "Abbah saboda gudun matsala ne yasa ban dawo da wuri ba, kowa jira yake yayi magana dani ni kuwa duk girman mutum bai isa ya shiga gonata na gyale ba in ba iyayena ba, ni nasan kaina ba hak'uri ne dani ba hakan yasa na dawo yanzu..." Abbah ya ce "okay to wuce ka je ka kwanta. .." Kowa ya kama part ɗinsa.... _WASHEGARI DA SAFE_ Maleekh ya fita office da wuri... An kunna AC, fitilun ofis suna haskawa cikin sanyin yanayi. Maleekh yana sanye da farin suit, yana kallon cikin laptop ɗinsa, idonsa na cike da gajiya da tunani. Sai kawai ƙofar ta buɗe da ƙarfi, Amal ta shigo cikin hanzari, idanunta sun kumbura saboda kuka. Hannunta na riƙe da jakarta da waya alamun yanzu isowarta, ko office ɗinta bata samu shiga ba, tana murɗa zoben hannunta cikin damuwa... Ta ce da sauti mai rauni, tana rawar murya: "Please... Maleekh... in har kana sona da gaske, to ka taimaka, ka sa a fito da Farha... don Allah..." Maleekh ya ɗago da mamaki, yana kallonta kai tsaye: "Amal, me kika ce? Na fito da Farha? Wannan magana ba a hannuna take ba, kin ji ko?." Amal ta matso kusa da tebur ɗin, tana kuka ta ce: "Na sani... amma kai mai faɗa a ji ne, kai ɗan babban mutum ne, kai ɗan hamshaki mai faɗa a ji ne. Kai zaka iya faɗa su janye ƙarar, ko su jawo maganar kotu a sake ta! Farha tana can a kurkuku saboda ni, saboda soyayyata da kai!" Maleekh ya miƙe tsaye, yana jujjuya alkalami a hannunsa ya ce: "Kin manta me Farha ta aikata? Kotun ce ta yanke hukunci, ba ni ba. Ba zan iya tsoma baki a cikin hukuncin doka ba, Amal." Amal tana girgiza kai, cikin kuka ta ce: "Zaka iya komai idan kana so... za ka iya sa duniya ta motsa idan ka buƙata, to me yasa baza ka iya ceto Farha ba? Ka ji yadda nake jin wannan a raina? Taya zanyi farin ciki idan na san yar’uwarka tana can cikin wahala saboda ni?" Maleekh ya ɗan dafa tebur, yana kallonta cikin ƙunci ya ce: "Kin san ba Farha ba ce kawai ta shiga matsala saboda ke, har ni ma... duk gidan mu ya rikice saboda soyayyar nan, Amal. Amma inaso ki ji kalmomi na, ba ni da iko akan kotu, ba ni da iko akan dokar ƙasa." Amal ta share hawaye, ta ce da muryar raɗa: "To me kake da iko akai, Maleekh? In baka iya kare Farha ba, in baka iya kare soyayyarmu daga iyayenka ba, to me yasa kake cewa kana sona?.." Maleekh ya ɗauke kai, yana riƙe kansa da hannu ya ce: "Amal... kada ki faɗi haka... bana son ki rikita ni da wannan zancen." Amal ta ce cikin ɓacin rai. "To sai ka tabbatar da kalmarka... idan kai kaine Maleekh ɗin da nake so, ka je ka fitar da Farha saboda ita yar’uwarka ce, kuma saboda kai ne dalilin da yasa take cikin wannan hali..." Ta juya a hankali, ta kama ƙofar zata fita, tana kuka sosai. Sai kawai Maleekh ya ƙira sunanta cikin raunannen murya. "Amal..." Ta tsaya, bata juyo ba. Ya ce: "Zan yi iya ƙoƙarina... amma ki sani, ba komai a hannuna yake ba. Ki yarda dani..." Amal ta amsa ba tare da juyo ba: "Na daina yarda da ƙoƙarinka idan bata ceto waɗanda suka shafe rayuwata ba..." Ta fita, ƙofar ta rufe da ƙarfi... Maleekh ya tsaya cikin shiru, yana kallon ƙofar, zuciyarsa cike da tashin hankali da soyayya mai zafi. Ya jingina da bango, yana maimaita a hankali: "Farha... Amal......" _BAYAN SATI GUDA_ Amal da Maleekh sun daina mu'amala kamar yanda suka saba, Amal yanzu tunaninta da damuwarta shine Maleekh yasa a fito da Farha...amma samm ya ƙi, hakan yasa kullum suke cikin samun matsala... Falon Amal yana ɗauke da hasken wuta mai launin zinariya, wanda ke ba da sanyi da natsuwa... Amal tana kwance akan kujerar falo, ta lullube kanta da blanket. Idonta a rufe, amma zuciyarta tana tafasa da tunanin Farha da kuma barazanar mahaifiyarta.... “Farha tana gidan yari saboda ni… Ko da kuwa ta tozarta ni, bai kamata hakan ya kai ta wurin hukuma ba. Kuma Maleekh… meyasa yake jin haushin ta haka?” Sai ta lumshe ido, hawaye ya zubo. Cikin zuciyarta tana fadin: “Allah ka sa duk abinda ke tsakaninmu ya warware lafiya… bana son ganin ɓacin ran kowa saboda ni.” Cikin wannan tunanin sai ta ji ƙarar bugun ƙofa, ƙarar da ta firgita mata zuciya. Ta miƙe a firgice, ta nufi ƙofar. Kafin ta kai hannu ta buɗe, sai aka ƙara buga ƙofar da ƙarfi.... “Subhanallah! Waye ne haka?” ta furta cikin tsoro. Kafin ta ankara, Zayd ya shigo cikin huci da fushi, idonsa a rufe da ɓacin rai. Hannunsa na motsawa kamar wanda yake neman abinda zai bugawa mutum. Amal a tsorace ta ce: “Zayd! Lafiya kuwa? Meyasa zaka shigo mun haka ba sallama?” Kafin ta ƙara cewa komai Zayd ya zabga mata mari. “PATTT!” Muryar mari ta cika falon, blanket ɗin da ke jikinta ya faɗi ƙasa, daga ita sai kananan kaya short jeans da best... Amal ta riƙe fuskarta, idonta suka cika da hawaye da mamaki... “Zayd… yau ni ka mara? Ni?!” Zayd a fusace ya ce: “Abinda yafi mari ma zan miki idan baki gyara kuskurenki ba, Amal! Kin wulakanta ‘yar uwata, kin sa an kai Farha gidan yari! Duk son da nake miki, yanzu ya zama ƙiyayya! Indai baki sa Maleekh ya ciro mun ƙanwata ba, ki manta da zaman lafiya!” Amal ta matso kusa da shi cikin kuka, tana girgiza kai: “Zayd… nice fa Pretty ɗinka… wannan maganar shin ba'a cikin mafarki kake yin sa ba kuwa?” Zayd ya murtuke fuska tare da faɗin “Pretty ɗin banza! Idan kina son ki huta, je ki samu Maleekh ya fitar da Farha daga gidan yari. Idan ya ƙi, to ki rabu da shi. Idan ya ga kun rabu, zai yi abinda kike so!” Amal cikin kuka ta ce "na rabu da shi kuma?..." Ya ce "Kwarai kuwa, in ba haka ba zai cigaba da buga wasan sa akan soyayyarki, Maleekh ba sonki yake ba, domin inda yana sonki da gaske to da zaiyi abin da zai sa kiyi farin jini a wurin ƴan uwansa ba wai kiyi baƙin jini ba, yanzu kowa ya tsane ki a kaff dangi. Babu mai goyon bayan akan Maleekh ya aure ki, ki auna ki gani, Maleekh yau yayi wa ƴar uwarsa wannan tozarci to gobe kuma a ke zaiyi wa, kiyi hankali da shi domin yana can yana cikin farin ciki ke kuma ya barki da tashin hankali, abun nan da yayi ba laifinsa ake gani ba duk ya ɗora miki laifin ne saboda haka Maleekh ba masoyinki bane na kwarai..." Daga nan ya juya ya fice daga falon yana fizgar ƙofar da ƙarfi... Amal ta tsaya da hawayenta, zuciyarta kamar za ta faso ƙirjinta. “Zayd… kai ma…? Duk duniya babu wanda ya fahimce ni…” Ta share hawayenta da bayan hannu, ta ɗauki hijabinta, ta fita da sauri, ta shiga motarta.... In the Evening Gidan na cike da natsuwa, an saka turaren wuta, ƙarar kiɗa mai natsuwa na tashi a hankali daga parlour. Amal ta shigo da sauri, tana jin bugun zuciyarta. Ta tsaya a tsakiyar falon ayayinda ta tarar da Ammy a zaune, tana kallon wani fashion show a TV. Ammy ta ɗaga kai a hankali, idanunta suka haɗu da Amal. Ta miƙe, tana ɗaure fuska, ta ɗauke kai tana cewa. “Lafiya? Me ya kawo ki nan, bayan haukar da kika sashi yayi akan ‘yar uwarsa? Kinsa ya kai Farha gidan yari! To yanzu me kika zo yi? Kin zo neman afuwa ko neman cigaba da cusa masa hauka?” Amal ta share hawayenta, tana murmushi cikin nutsuwa da nauyin zuciya: “Ban zo faɗa ba, Ammy. Nazo ganin Maleekh ne kawai.” Ammy ta kwaɓe baki ta ce: “Wai ganin Maleekh? Bayan kin jefa shi cikin bala’i da sunan soyayya? Ashe baki da kunya ban sani ba? Ƴar matsiyata..!” Amal ta kasa magana, hawaye suka fara zuba. Ta juyo da niyyar fita sai ta ji muryarsa. Maleekh daga sama ya furta: “Beb? Me ke faruwa ne nan?” Ya sauƙo daga upstairs sanye da farin shirt da wando mai duhu, yana kallon Amal da mamaki da damuwa. Sai dai kafin ya ƙaraso, Amal ta juya gare shi da fuska cike da zafi da rauni. "Ina so ka gaya mun, me kake nufi da wannan hukuncin? Ka kai ‘yar uwarka kotu saboda ni, hakane ko? Kuma haka danginka ke cewa, Duk da cewa ban so haka ba? Kasa danginka sun tsane ni, suna zagina, cin mutunci ba kalar wanda ba'a mun..! Shin hakane soyayya?..” Maleekh cikin nutsuwa da ɓacin rai ya ce: “Na yi hakan ne don kare mutuncinki, Amal. Ba zan bari a ci zarafinki ba!” Amal tana kuka ta ce: “To ni ban so! Ni ban ce ka kai Farha kotu ba! Ni na yafe mata tuni… Me yasa baza ka saurare ni ba, Maleekh?” Ammy ta tsaya gefe tana kallon su da ɓoyayyen murmushi tana jin daɗin rabuwar da take gani ta fara tasowa... Maleekh cikin ɗaga murya shima ya ce: “Ke Amal, kina bani umarni ne? For what? Ki tsaya ki ji, ba zaki faɗa mun abinda zan yi ba! Na yanke hukunci ne saboda gaskiya, ba don son rai ba!” Amal itama cikin ɗaga murya ta ce: “Gaskiya? Gaskiyar me? Wacce ta sa ni cikin baƙin ciki? Idan ka fi kowa sanin adalci, me yasa kake cutar da zuciyata? Idan har kana sona da gaske inaso ka aure ni a yau, aure ni nace Maleekh...” Cikin fusata sosai ya ce: “Stop it Amal! Don’t talk to me like that!” Tana hawaye ta ce: “Na gaji da wannan soyayyar, Maleekh. Soyayyar da ba aure, hauka ne, soyayyar da sam ba'a ganin mutuncin ta, kuma bata da kariya daga danginka. Idan haka kake so, ka riƙe soyayyarka da su, ni na yafe komai!” Maleekh ya tsaya kallonta, idonsa ya canza launi saboda ɓacin rai. Cikin fusata ya ɗaga hannu ya zabga mata mari. “PAATTT!” Shiru ya cika falon na wani ɗan lokaci... Amal ta tsaya cikin rawar jiki, tana kallonsa cikin girgiza kai, hannunta na kan kumatunta. “Ni ka mara, Maleekh? Bayan duk wannan soyayyar?” Maleekh cikin nauyayyen murya ya ce: “Na mare ki. So what? Zaki rama ne?” Hawaye na zubo mata sosai, zuciyarta na tafarfasa. Tana riƙe da key ɗin mota, ta furta cikin rawar murya: “Shikenan. Tunda haka kake so, daga yau ba kai, ba ni. Ba zan tsaya ɓata lokaci na akan soyayyar da nake wulakanta ba.!” Maleekh ya yi dariyar takaici tare da faɗin: “So what idan kin tafi? Oya Go. Go get out!” Ta ɗago tana nuna shi da yatsa “Stay away from me!” Maleekh a fusace, ya riƙo hannunta: “Zo na taimaka miki ki fita! Daga yau bazaki sake ganin fuskar Maleekh ba! Zan koma England inda babu irin ki!” Ya ja ta da ƙarfi zuwa ƙofar harabar gidan. Amal tana kuka tana ƙoƙarin kwacewa, amma zuciyar Maleekh ta rufe da fushi. Yana fitar da ita ya wurga ta gefe. “Out! OUT!” Amal ta zauna ƙasa tana kuka mai ƙarfi, a lokacin ruwan sama ya fara zuba a hankali kamar sama na tausaya mata... Wani irin harara ya wurga mata tare da juya wa cikin gidan.. Ammy tana tsaye bakin ƙofa da murmushin mugunta.. A hankali ta furta: “Da kyau, ɗana. Wannan karon, ka faranta mun sosai.” Maleekh ya hau sama da sauri, ko tsaya kula Ammy da ƙannensa bai yi ba. Ya shiga ɗakinsa, ya buɗe akwati yana haɗa kaya cikin fushi da tashin hankali. “Ba za ta sake raina ni ba… Ba wata Amal a rayuwata daga yau.”.. Amal a waje tana cikin ruwan sama, tana kuka, tana faɗin cikin sanyi: “Ya Allah… idan wannan soyayyar ta zama hukunci, ka bani ƙarfin yin haƙuri…” A hankali ta miƙe da ƙyar ta shiga motarta, ta ja a hankali cikin ruwan, idonta cike da hawaye.. Gidansu Amal yayi shiru kamar ba kowa. Kukan ta ya cika falon amma babu wanda yake nan. Zuciyarta na bugawa da nauyin kalmomin Maleekh da suka tsaya a kunnenta kamar ƙaho. "Daga yau bazaki sake ganin fuskar Maleekh ba! Zan koma England inda babu irin ki!”.. Tayi murmushi cikin hawaye tana faɗin, “Ni kuma babu kai babu rayuwata…” Sai ta share hawayenta ta hau sama zuwa ɗakinta, tana ji kamar gabanta na faɗuwa. Ta sa hannu ta buɗe ƙofar ɗakin, wani sanyi da tsoro suka ratsa ta... Ganin Zayd a tsaye, ga duhu ya fara shiga, yana kallonta da idanu masu cike da nufin da ba a iya fassara shi... Amal ta ja baya tana faɗin cikin firgici: “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un… Zayd? Me kake yi a ɗakina haka?” Zayd ya saki murmushi marar daɗi, yana matsowa kusa da ita, “Na zo karɓar abinda zaisa in mallake ki, tunda kin rabu da masoyin ki… yanzu ni zan zama sabon masoyin.” Amal ta dafe ƙirji, murya na rawa, “Zayd, me kake faɗi haka? Wane irin hauka ne wannan?” A take ya cafke hannunta ya ja ta kusa da shi, yana shakar ƙamshin jikinta kamar wanda ya haukace. “Wani irin kamshi kike da shi, Amal… kin manta ni ne nake son ki tun farko?” “Ka sake ni! Zayd don Allah ka sake ni!” ta faɗa tana ƙoƙarin kwacewa, amma ƙarfin sa ya rinjaye ta... Ya jefa ta kan gado, tare da binta da sauri yana shashshafa jikinta cikin tsananin sha’awa da mugunta. Amal tana ƙoƙarin tura shi, ta buɗe baki zata yi ihu yayi saurin toshe mata baki da nasa, yana sumbatar ta da ƙarfi. Hawaye da gumi suka gama gauraye jikinta gaba ɗaya. Cikin wannan lokacin, zuciyarta ta cika da addu’a, “Ya Allah, ka ceci ni daga wannan azaba…” Yayinda Zayd ke ƙoƙarin cire mata rigarta, sai suka ji ƙarar ƙofa ta turo da ƙarfi...! Zayd a zabure ya tashi daga kanta yana kallon bakin ƙofar! Amal ta ja blanket da sauri ta rufe jikinta tana kuka. Idanunta suka haɗu da na Maleekh, wanda ke tsaye bakin ƙofa, hannunsa riƙe da takardar da ya zo bata. Idanunsa sun kumbura, zuciyarsa na harbawa da jin zafi fiye da rauni. Ya kalli Amal, ya kalli Zayd, sannan ya yi dariya mai ciwo. “Toh... dalilin rabuwar kenan?.. har gida kike kawo ‘visitor’? Har cikin ɗaki? Har kan gado?” Amal ta ɗaga murya tana kuka, tana son yin bayani amma muryarta ta kasa fita... “Maleekh... ba haka bane wallahi...” Zayd yana riƙe da rigarsa da yake kokarin sa, yana faɗi cikin ƙarfin murya, “Amma kai ɗan iska ne Maleekh! Ka turo mana ƙofa ba sallama, shin kai maigidanta ne...?” Maleekh ya yi wani murmushi mai haɗe da zafi da raini... “Ba sai na zama maigida ba don in gane ƙazanta. Na gani da idona kuma hakan ya wadatar...” Amal ta yi sauri katse wa da cewa, “Wallahi Zayd bai—” Kafin ta ƙarasa, Maleekh ya juya. Idanunsa sun cika da hawaye, zuciyarsa ta cika da ɓacin rai da rauni. Ya matse envelope ɗin da yake riƙe da shi, sannan ya jefa shi ƙasa...Yana furta “Kin gama da ni, Amal. Daga yau bana buƙatar ganin fuskarki. Kina da wanda yafi ni... ai kin same shi.” Yana faɗin haka ya fice daga ɗakin. Ƙarar rufewar ƙofa ta ƙara girgiza jikinta, ta durƙusa ƙasa tana kuka, tana faɗin: “Ya Allah! Ina zan saka kaina? Me yasa rayuwa take min haka? Na rasa soyayya, na rasa mutunci a idon wanda nake so…” Zayd ya tsaya bakin ƙofa yana kallonta, sai da ya gama sa rigarsa kafin ya fita yana wani irin murmushi.... Jiragen sama suna tashi da ƙarar da ke shiga kunne, amma a zuciyar Maleekh, ba ƙarar jirgi yake ji ba, ƙarar bugun zuciyarsa kawai yake ji. Ya tsaya bakin glass window yana kallon hasken titin jirgin, fuskarsa ta kumbura da damuwa, idanunsa sun yi ja kamar wanda bai kwanta ba kwana biyu. A hannunsa akwai boarding pass, amma a zuciyarsa akwai rashin natsuwa. Ya furta a hankali kamar yana magana da kansa: “Yanzu duk abinda nayi mata da abin da zata sakamun kenan? Duk da kaunar da nake mata, ta iya wannan abin? Amal?...” Ya jinjina kai, hawayen da yake ƙoƙarin boyewa suka zubo da kansu. Ya share da hannu, yana ƙoƙarin daurewa ya zama namiji, amma zafin ya fi ƙarfinsa... Wani mutum ya wuce kusa da shi yana riƙe da hannun matarsa, suna dariya cikin farin ciki. Maleekh ya bi su da kallo, sannan ya murmusa cikin ciwo. “A lokacin da nake ganin soyayya aljannar duniya ce... ban san cewa ta fi jahannama zafi ba.” Ya juya, ya nufi chair ya zauna. A gefe, wayarsa ta yi ƙara, Ammy ce ke ƙira. Ya ɗaga cikin kasala. “Hello Son, ka tafi ne? Ina gida ina yi maka addu’a Allah ya tsare ka. Kada ka damu da waccan yarinyar nan, Allah zai baka wadda tafi ta komai.” Maleekh da kasalalliyar murya ya ce: “Na riga na manta da ita, Mom. Na riga na manta da ita...” Ammy ta ce: “Hakan nake so. Kar ka juya baya, idan jirgin ya tashi ka bar komai a nan.” Ya kashe wayar, ya jingina da kujera, amma zuciyarsa ta ƙi yin shiru. Duk yadda yake ƙoƙarin tuna ƙiyayya, sai tunanin so ke dawowa. Yana tuno ranar farko da suka haɗu a office acan Kaduna, yadda Amal ta tsaya a gaban ofishinsa tana faɗin: “Ni ba’a raina ni saboda talaucina.” Da yadda yake kallonta yana ganin wata irin nutsuwa da bai taɓa gani a wata mace ba. Sai zuciyarsa ta soma bugawa da sauri. Ya matse hannunsa cikin fushi, “Amal... me yasa kika bani dalilin tsanarki bayan na fi so in mutu saboda ke?” Sai wani announcement ya cika hall ɗin: “All passengers traveling to London Heathrow, please proceed to gate 6…” Maleekh ya miƙe a hankali, ya ɗauki hand luggage ɗinsa, amma kafin ya taka ƙasa zuwa gate ɗin sai ya tsaya. Idanunsa suna masa raɗaɗi, jikinsa ya ɗan yi sanyi. Wata murya a zuciyarsa ta furta masa: “Ka tafi, amma soyayyar nan zata dawo maka. Ka tafi, amma ba za ka taɓa mantawa da ita ba.” Ya ɗan murmusa cikin raɗaɗi, “Toh, insha Allahu zan manta da ita kafin ta manta da ni.” Ya nufi hanyar gate, yana tafiya a hankali, kamar mai gudu daga wani abu da yake binsa a zuciya. Jirgin ya tashi amma a ƙasan duniya, akwai Amal da ke neman rai cikin hawaye da nadama..... NEXT NEXT NEXT... asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 63 to 64 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Bayan Amal ta gama shan kukan ta idonta ya sauƙa akan envelope dake ya she a ƙasi... Da sauri ta sauƙa daga kan gado ta ɗauka. Ta buɗe letter hannu na rawa.. "Ban san yadda zan fara ba… sai dai kawai zan faɗa miki gaskiyar cewa zan tafi, kuma bana son ki ƙara gani na a gajeren zango. Rayuwa ta rikice, zuciyata ta gaji da yaƙi da soyayyar da take ban wahala. Na tafi ba don na gaji da ganinki ba, ba kuma dan na tsaneki ba, zan tafi ne don kawai na bar zuciyata ta huta daga tunaninki. Kullum idan na rufe ido, ke nake gani amma kin kasa fahimtar halin zuciyata, baza mu taɓa kasancewa tare ba indai baki koyi zama dani ba.... Please Idan kika tuna da ni, kar ki yi kuka. Ki yi addu’a kawai, domin duk inda nake, sunanki yana rayuwa cikin zuciyata. Maleekh 💔..." Tana kammala wa ta fashe da kuka, tana furta cikin rawar murya: “Wayyo Allah, meyasa zaka tafi ka barni inda gaske kake kana sona? Meyasa na bashi dalilin tsanata?… Amma ban fa yi komai ba! Me yasa rayuwa bata bani dama in bayyana gaskiyar zuciyata ba?” Ta share hawayen, ta miƙe a zabure. Ta zura rigar jikinta da hanzari, ta ɗauki key ɗin motarta, tana hawaye tana furta: “Zan same shi! Ko da kuwa a bakin jirgi ne, zan gaya masa gaskiya kafin ya bar ni.” Tana fita daga gida sai ta ja motar cikin gudu, tayoyi na rawa tsabar gudu... Fitilar gari ta zama hazo a idanunta saboda hawayen da suka hana ta gani sosai. “Ya Allah ka tsare ni… kar in isa jirgin ya tashi kafin in gan shi…” Tana isa gate na tashar jirgi, ta tsaya cak ganin motoci da mutane da yawa suna barin wurin. Da gudu ta shige cikin tashar, tana share hawaye, tana tambayar ma’aikacin tsaro: “Don Allah, jirgin London… jirgin London Heathrow, ya tashi ne?” Ma’aikacin ya duba agogonsa, sannan ya ce: “Madam, jirgin ya tashi mintuna goma da suka wuce.” Amal ta tsaya kamar an zuba mata ruwan sanyi. Hannunta ya saki key ɗin motar da take riƙe, ya faɗi ƙasa. Tana kallon taga mai nuni da jiragen da ke tashi a sararin sama, sai hawayen da sake gangarowa cikin zafi.. Ta durƙusa ƙasa ta fara ihu kamar zuciyarta zata tsage: “MALEEKH! Don Allah ka tsaya ka saurare ni! Wallahi ba haka bane, ban ci amanarka ba!!” Wata mata dake wucewa ta tsaya tana kallonta cike da tausayi, amma Amal bata ma lura da ita ba. Tana kuka tana faɗin: “Na rasa shi... Na rasa shi... Allah Ya sani ban yi masa laifi ba, amma bai tsaya ya saurare ni ba…” Ta durƙusa sosai, ta tallafi kanta da hannu guda tana kuka kamar ranta zai fita. Jikin ta na rawa, murya na dusashe wa. A hankali ta ɗaga idanunta ta kalli sama, tana faɗin a fili: “Allah, idan akwai adalci a duniya, ka tabbatar gaskiyata ta bayyana... kar Maleekh ya rayu cikin ƙarya... kar ya rayu yana tsanata da abin da ban aikata ba…” Hawayenta suna zuba gaba ɗaya ta jiƙe gaban rigar abayar ta, ta rufe fuska da tafukan hannayenta tana kuka. Wani sanyi ya ratsa jikinta, kamar an busa iska mai ƙarfi. Tayi shiru na ɗan lokaci, sai ta ɗaga kanta cikin tashin hankali: “Idan soyayyata ta ƙare da Maleekh, to ni ma zan kare daga rayuwar nan…” Sai ta tashi a hankali, ta fice daga tashar, tana tafiya kamar mai neman hanya cikin duhu, zuciyarta na bugawa... Haka ta shiga mota ta tafi jiki ba ƙwari.. Kwana Biyar Bayan Tafiyar Maleekh... Tunaninsa bai taɓa barin Amal ba. Tun ranar da ta dawo daga airport da kuka, babu rana da ta tashi ba tare da ta ƙira lambar sa ba. Kowane lokaci da ta danna “call”, sai ta tsaya tana sauraron sautin “number you are calling is switched off…” sautin da ya zama kamar wuƙa a zuciyarta. Tana zaune a gaban window, ta jingina kai a jikin gilashi, tana kallon ruwan sama da yake sauƙa cikin nutsuwa. Wayarta a hannu, idonta a kumbure, jiki duk ya rame. Tana faɗa cikin disasshen muryar : “Maleekh… har yanzu baka dawo ba? Ko baka ji ƙiran zuciyata ba?... Kai nake nema, Allah yasa kana lafiya.” Sau da yawa tana duba WhatsApp, babu last seen. Instagram shiru. Email babu amsa. Kamar ya ɓace daga doron ƙasa... Amal ta kasa cin abinci. Idan ta ɗauki cokali, sai hawaye su gangaro. Inna tayi iya ƙoƙarin lallashinta, amma ita kanta ta gane cewa ciwon soyayya ya fi kowanne ciwo ciwo. Da daddare Amal takan tashi tsakar dare, tana tunanin ko ya ci abinci, ko yana lafiya. Ta ɗauki wayarta ta kunna voice recorder, tana magana kamar yana gabanta: “Maleekh… ni ce Amal. Ka tuna mun yi alƙawarin cewa babu rabuwa a tsakaninmu, ko?” “Zan jira ka, har sai lokacin da ka dawo min da murmushi ɗaya daga cikin naka.” Ta dinga faɗin haka cikin kuka, tana maida numfashi a hankali. Da asuba, ta tashi ta shiga bathroom, tayi brush sannan tayi wanka tare da ɗauro alwala, ta saka hijab ɗinta ta tsaida sallah... Bayan tayi sallah tare da addu’o'i, ta tashi cikin ƙarfin hali tana faɗin. “Uhmmm, ban isa in mutu saboda ciwon soyayya ba. Zanyi aiki, zanyi rayuwa har sai lokacin da Allah Ya dawo min da shi.”... Da wannan niyyar, ta shirya ranar ta biyar, ta saka suit skirt da rigar office, ta ɗaure tie ɗinta a wuya, ta ɗauki handbag ta nufi falo, a wannan ranar ta dage tayi breakfast, daga nan ta shiga ɗakin Inna suka gaisa sannan ta wuce company. Lokacin da ta shiga reception, murmushi marar zurfi ne ya bayyana a fuskarta, murmushin wacce ta sha kuka amma ta nuna ƙarfin hali... Sai nan ne ma’aikatan suka yi mata sannu da dawowa, tare da gaisheta... Sai kuma Zayd ya bayyana da kalmar nan “My pretty…” Amma wannan karon, mari ya riga da ya sauƙa kan fuskarsa kafin kalmar ta gama fita daga bakinsa... Zayd ya tsaya dafe da kuncinsa, kowa a reception ya tsaya shiru. Sai sautukan takalman Amal da take taku cikin ƙasaita.. Idonta cike da zafi da hawaye, amma ta tsaya a gabansa kamar shugabar da ya kama wani da laifi... “Kayi farin ciki, ko? Ka rabani da mutumin da zuciyata ke numfashi dashi! Ka ɓata min suna a gabansa, kayi amfani dani wurin cimma burinka…Ba tare da nayi wani tunani ba na biye maka, wallahi ban yafe maka ba Zayd..." Zayd ya yi ƙoƙarin murmushi, amma muryarsa ta nuna gurbatacciyar niyya. “Eh, gaskiya ne. Ni nake sonki shiyasa nayi haka, na daɗe ina jiran wannan damar. Maleekh ya tafi, yanzu ba wanda zai tsaya tsakanina da ke. Wannan itace gaskiya, Amal.” Ta matso kusa da shi, tana kallon sa da idanunta masu cike da hawaye da tsantsar tsana ta ce. “Burinka bai cika ba, Zayd. Ba zaka iya maye gurbin Maleekh ba. Jininmu ya riga da ya haɗu, ba a cikin jikina kawai ba, har cikin ruhi da numfashina. Ka ji da kyau: ko ka kawar da ni, ko ka kawar da shi, ƙauna bata da kabari.” Tana kaiwa ta juya da ɗan huci. Ma’aikatan suka ba ta hanya, babu wanda ya iya magana. Ta shiga elevator, ƙamshin turarenta ya ci gaba da yawo cikin reception... Bayan ta hau saman bene na takwas, ta fito tare da shige office ɗinta ta rufe ƙofa. Ta jingina da ƙofar, hawaye suka fara sauƙa kamar ruwan sama. Ta zame a ƙasa ta durƙusa, tana riƙe da kanta tana faɗin “Ya Allah... har yaushe zai waiwaito ni? Ko da gaske ya tafi ne har abada? Maleekh, don Allah ka amsa ƙiran da nake yi maka…” Ta lalubo wayarta daga jaka, ta sake ƙira. number you are calling is switched off. Ta saki wayar ta faɗi gefe, ta lumshe ido tana kuka kamar ranta zai fita. A cikin office ɗin akwai hotonsu su biyu da Maleekh a kan tebur, lokacin da suka yi launching na sabon project ɗin CashTalk FM. Ta miƙa hannu ta ɗauka, ta kalli hoton, ta shafi fuskar sa a hankali tana faɗin. “Ka faɗa min cewa ba zaka taɓa yin nesa dani ba… ka faɗa min cewa zaka kasance dani har abada…” Sai ta ji kanta na sarawa. Tana numfashi da sauri, zuciyarta na bugawa da kyar. Ta tashi ta nufi window, tana kallon sararin sama, tana jin kamar ta ƙira sunan sa cikin iska... “Maleekh…” Sautin sunan ya fito da ƙarfi, yana haɗuwa da hawayen da suka zubo kamar ruwan sama daga idonta. Tana nan tsaye har sai da hasken rana ya fāɗi, sannan ta zauna a kujera, ta riƙe kai tana murmushi cikin hawaye: “Ba zan daina jiranka ba. Ko ka bar ni, zan ci gaba da yi maka addu’a.”.. A wannan ranar Amal bata samu ƙarfin gudanar da aiki ba.... Tafiyar da aka yi shi cikin fushi, bata taɓa sa ran zama makamin hallaka kamar haka ba... Maleekh ya bar Najeriya da zuciya mai raɗaɗi, fushi da ƙaunar Amal suka haɗu suka zama wuta a ƙirjinsa. A hannunsa akwai jakar da ya ɗauko kai tsaye daga cikin motarsa wanda yana tunanin nashi ne domin sak irin jakarsa ce, tunani ya dabaibaye kwakwalwarsa, yana tunanin komai lafiya. Bai san cikin jakar akwai abinda zai iya ruguza rayuwarsa gaba ɗaya ba.... Yana shiga jirgin. Ko wayar Amal da ke ta ƙira, bai amsa ba. Ya kashe komai, yana son mantawa da komai amma ba zai taɓa iya mantawa da yadda ya ga Amal cikin ɗakin nan tare da Zayd ba. Lokacin da jirgi ya sauƙa a Heathrow, tsaftataccen iska mai sanyi ya daki fuskarsa... Ya sauƙo cikin natsuwa, hannunsa na riƙe da pasport ɗinsa, sai kawai ya ji murya daga gefe ta ce: “Sir, can we have your luggage, please?” Ya miƙa musu cikin nutsuwa. Amma kafin ya ankara, sai ya ga wasu ma’aikatan tsaro biyu sun tsaya a bayansa, suka ɗauki jakar nan da suka saka a scanner. Cikin mintuna biyu, komai ya canja, hasken da ke kan fuskar screen ya yi ja, wani ɗaya daga cikin su ya ɗago da murya mai tsanani. “We have an issue here…” Maleekh ya kalli fuskar su cikin mamaki. “What? Is there any problem?” Suka nuna masa allon: cikin jakarsa akwai ƙwayoyi masu hatsari waɗanda a ƙasar nan hukuncinsu ɗaya ne da kisa... Cikin rawar murya, ya ce: “That’s… impossible. That’s not mine! Wallahi I don’t know about that!” Amma ba wanda ya saurare shi. Nan take suka kwace wayoyinsa, suka sa masa handcuff, suka tura shi cikin wani ƙaramin ɗaki mai duhu, inda ake tsare waɗanda ake zargi da laifin safarar miyagun abubuwa... A nan ya zauna, ba tare da kalmar da zata fito daga bakinsa ba. Abinda ke masa yawo a zuciya shi ne “Amal… idan ta ji wannan fa?” A can gida kuwa, kwana uku suka wuce ba labari. Ammy tana ganin kamar ya kashe wayarsa ne don ya huce. Abbah kuma ya ce, “Ku barshi, zai dawo da kansa.” Sai rana ta bakwai sati guda kenam, lokacin da Amal ta isa kamfani da safe, cikin kaya masu kyau amma idonta kumbure saboda rashin kwanciyar hankali. Ta shiga reception da sallama, ta amsa gaisuwar ma’aikata da natsuwa, tana ƙoƙarin ɓoye ɓacin ranta... phone ɗin receptionist yana yawan ring.. Receptionist ta ga wani number da yake meta da rubutu: “International Airport Authority. URGENT CALL”. Kafin Amal ta wuce sai ta ce cikin girmamawa: “Miss Amal. Wani ke ƙira daga Airport London. Sun ce akwai buƙatar a yi magana da dangin Maleekh.” Amal cike da mamaki take kallon receptionist ɗin da take ƙoƙarin bata wayar: Amal ta karɓa da faɗuwar gaba, zuciyarta na dukan kamar ana buga ganguna a ƙirjinta. Da ƙyar ta furta, “Hello....“Hello? …Waye ke magana?” Sai wata murya mai sanyi ta amsa daga can ƙetaren teku: “We’re calling from Heathrow Airport. A man named Mr. Maleekh Abdul-Majeed has been detained in our custody for drug trafficking. We need his family or representative.” Wayar ce take ƙoƙarin faɗuwa daga hannunta, da ƙyar ta riƙo wayar da sauri ta ƙara karawa a kunne. Cikin tsoro ta matsa kusa da receiver tana faɗin. “A, Mr… wai… me kuke cewa? Maleekh? Amma… ya tafi ne, ya riga ya sauƙa? Ya… ya faɗa muku da abin da ya faru?” Ma’aikata suka tsaya kallonta yanda ta firgita. Idonta ya cika da hawaye... Officer ya kuma cewa: “Muna neman mu tabbatar da gaskiya. An tsare shi ne lokacin da aka samu kayan miyagun kwayoyi a jakarsa. Yana nan a interrogation room yanzu. Muna buƙatar wanda zai zo a matsayin danginsa ko wakili. A halin yanzu wayoyinsa an kwace, kuma ana nazarin jakarsa. Muna bukatar lambobin danginsa: akwai yiwuwar mu yi contact da su don sanarwa….” Amal a ruɗe ta ce “What…? Maleekh…?” Ƴar amsa kawai ta fito daga bakinta kafin ta durƙusa, ta dafa tebur tana huci, hawaye na zuba kamar an kunna famfo.... A wannan lokacin, wurin ya yi shiru kamar anyi mutuwa. Wasu ma’aikata suka juya suna kallo Amal. Zayd ya tsaya a gefe, fuskarsa ta canja launi. Idanunsa sun yi kama da wanda ya yi farin cikin labarin amma matsayinsa ya kasance, ya yi saurin ciro muryar nuna damuwa... Zayd ya matso da sauri yana faɗin “Me!? Maleekh?! Amma… wannan ba zai yiwu ba! Ashe abun da ya faru da shi kenam...?! Pretty … Amal! Me ye abun yi yanzu?” Amal ta daka masa tsawa cikin kuka ta ce: “Ka daina ƙirana da sunan nan! Ka rabani da shi, yanzu kuma wannan! Ka ji daɗin hakan ko Zayd?” Zayd ya ja da baya, amma ya ɓoye murmushi a ƙarƙashin haƙoransa. Amal ta riƙe kanta da hannuwa biyu tana kuka tana faɗin: “Allah na tuba… Maleekh, Allah ka kare ka… duk wannan saboda ni... saboda son da na kasa karewa...” Amal ta yi ƙoƙarin ƙara yin magana amma jikinta ya mutu. Don haka ta miƙawa receptionist waya da rawar hannu, murya na kakkarwa ta ce: “Ku ba su lambar ofishin Mahaifinsa ko Mahaifiyarsa… da wani ofishin lauyanmu. Ku gaya musu su yi contact da su nan take!”.. Receptionist ta tura musu lambar Abbah... A can London kuwa suna ganin lambar suka danna ƙiran number Abbah. Ganin international call ne yasa Abbah ɗaga wayar tare da faɗin. “Sannu…wa ke ƙira?” Officer ya fara bayani: “Alhaji Abdul-Majeed, muna neman mu sanar da ku cewa an tsare ɗanka, Mr. Maleekh Abdul-Majeed, a Heathrow Airport. An samu abubuwan da ake zargi a cikin jakarsa. Muna buƙatarku da ku zo ko ku tuntubi ofishin jakadancin nan da nan. An kwace wayoyinsa kuma yana nan a tsare. Muna bukatar wanda zai zo ya tabbatar da shi.” Innalillahiwa’inna ilaihirraji’un, Abun da Abbah yake ta maimaitawa kenem, Abbah ya kasa magana na ɗan lokaci. Sai ya tambayi: “In…in yaushe hakan ya faru? Yaya lamarin yake?” Officer ya ce: “Ya sauƙa ne tin last week Mr. Abdul-Majeed, kuma an kama shi a lokacin da ake bin diddigin tafiyarsa ko a lokacin da ya sauƙa. Muna tuntubar masu gabatar da shari'a, kuma ana ci gaba da bincike. Muna bukatar ku hanzarta zuwa nan, ko ku tuntuɓi ofishin jakadanci.”... Abbah ya ajiye waya, zuciyarsa ta tsaya. Ya kashe wayar da rawar murya, ya miƙe da sauri gaba ɗaya ya rasa me zai yi tsabar ruɗewa. A gefe, Abbah ya ƙira Ammy da kyar, suna mamakin abin da ya faru... Abbah ya samu yin waya daga hukumar jirgin a wannan lokacin, ko wani ne ya masa canji... a firgice yake tambayarsu... Ammy ta zauna tana kuka cike da nadama, tana zargin Amal ce ta jawo wa ɗanta wannan bala’in... A wannan ranar suka fara shirye-shiryen tafiya London don ceton Maleekh... ☆☆☆☆☆☆☆☆☆ A cikin office, Amal ta ji kamar ƙasa ta tsage ta shige. Gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi, idonta na zubar da hawaye da ba zata iya ɓoyewa ba... Tana cikin wannan halin sai ga lawyer (wanda yake senior counsel na kampani) ya shigo da sauri lokacin da aka sanar da shi... Yana waya da ofishin jakadanci, ya soma neman hanyoyin tuntuɓa. Bayan ya gama, sai ya koma ya tsaya a gaban Amal.. Yana faɗin “Miss Amal, ke da family ɗin Mr. Maleekh dole ku tashi ku tafi London ko ku tuntuɓi ofishin jakadanci nan take. Wannan lamari ne na ƙasa da ƙasa. Zan shirya duk takardun da ake buƙata; amma ku sani, a irin wannan hali gwamnati na iya ɗaukar matakan doka masu tsauri. Dole mu yi gaggawa.” Amal ta nufi taga, ta kalli sararin sama kamar mai neman mafita, zuciyarta cike da laifi da fargaba... “Amal zata zauna a Nigeria, domin bani da wani ƙarfin zuwa tuntubar hukumar ƙasar waje, iyayensa ne suke da alhakin hakan kuma an sanar musu, ina tunanin a yau zasu tafi.... Ya Allah… wannan duk saboda ni ne? Ko saboda wani ne yake son wargaza rayuwarsa? Maleekh… ina nan… ina addu’ar kar su cutar da kai….” A gefe Zayd yana la6e a bakin ƙofa ta waje yaba sauraron komai, lokaci guda ya sauƙe numfashi tare da sakin murmushi kamar wanda yayi wata gagarumar nasara... ●●● Amal kuwa, bayan ta koma gida da dare, ta kasa kwanciya. Wayarta a hannunta, tana ta ƙiran lambar Maleekh kamar wata mahaukaciya, amma komai shiru. Cikin ƙarfin kuka ta durƙusa ta ce: “Ya Allah, idan akwai wanda ya shirya masa, ka bayyana gaskiya… ka kare min shi, domin ni ba zan iya rayuwa ba tare da shi ba…” Wannan shi ne farkon azabar da ƙaddara ta shimfiɗa musu. Tun daga ranar da aka ɗauke Maleekh, gidan su ya shiga tashin hankali. Abbah ya kasa bacci, Ammy kuma kuka da addu’a ke damunta. Cikin kwanaki biyu da zuwa London domin ganin yaron nasu. Amma ba'a basu damar ganinsa ba tukun... Sai yau kwana uku da zuwansu.. Sai yau aka fitar da Maleekh daga ɗakin duhu domin ganawa da iyayensa. Maleekh zaune ne a ƙaramin kujerar ƙarfe. Idonsa ya kumbura, gashin kansa ya fita daga tsari, gaba ɗaya haskensa ya dusashe.. Ƙofar ɗakin ta buɗe... Ammy ce ta fara shigowa, tana sanye da farin hijab, sai Abbah dake biye a bayanta.. Da zarar Maleekh ya gan su, hawaye suka cika idonsa, ya miƙe tsaye kamar wanda aka zare masa numfashi.. “Abbah… Ammy…” ya ƙira da muryar da ta karye, yana kuka kamar yaro... Ammy ta nufi gare shi da sauri, ta rungume shi, tana girgiza kai, tana kuka... “Maleekh ɗana, me suka yi maka haka? Waye ya maka wannan sharrin?” Maleekh ya runtse idanu, hawaye na zubo kamar ruwan sama... “Ammy, wallahi ban san da komai ba!” Ya fashe da kuka, muryarsa ta cika da rawar zuci. “Na bar Nigeria da jakata a hannuna, amma lokacin da na sauƙa suka ce sun ga wani abu a ciki. Na rantse ba jakar da na ɗauka bace! Jakar iri ɗaya ce da tawa, amma kayan ciki sun bambanta. Na gane daga baya cewa an sauya ta, amma kafin in yi magana, sai suka rufe ni..." Abbah, wanda yake tsaye a gefe, yana ɗaure da fuska ganin halin da ɗansa yake ciki, idonsa ya cika da hawaye. Ya matso kusa, ya zauna kusa da ɗansa, ya dafa kafaɗarsa tare da faɗin... “Na yarda da kai, ɗana. Ban taɓa ganin ka da makamancin irin wannan abu ba. Amma su ba su san Maleekh ɗina ba, sun manta da irin tarbiyyar da muka baka.” (A'a Abbah yana shan Shisha faa 🤣🤣🤣🤣) Abbah ya share hawayensa da yatsansa, ya ci gaba da magana cikin sauti mai nauyi: “Za mu bincika gaskiya. Ba zan bar wannan lamarin ya wuce haka ba. Na riga na fara tuntuɓar lauya da ofishin jakadancin Najeriya. Amma ka yi haƙuri, ɗana. Kar ka bari wannan ƙaddara ta karya maka zuciya.” Maleekh ya girgiza kai yana kuka, “Abbah, ina ji kamar mafarki ne. Na rasa komai, mutunci na, sunana, rayuwata. Wallahi Abbah, ni ba mai laifi bane!” Ammy ta riƙe hannunsa da ƙarfin zuciya, ta ce cikin kuka: “Allah yana tare da kai, ɗana. Ba mai gaskiyar da yake jimawa dole sai ka tsira. Zan roƙi Allah a kowace raka’a ya tabbatar da gaskiyarka.” Ƙarar ƙofar ta buɗe, jami’an tsaro sun dawo don su fitar da su daga ɗakin ganawa. Ɗaya daga cikinsu ya ce da nauyayyen murya: “Time’s up, please.” Ammy ta ƙara riƙe hannun ɗanta, tana kuka, tana faɗin: “Ka tsaya da addu’a, Maleekh. Kada ka bari shaidar ƙarya ta ci nasara akan ka.” Abbah ya miƙe, ya kalli ɗansa da idon da ke cike da ƙarfin hali irin na uba: “Ka san me ya fi ƙarfi akan duk wata shaidar ƙarya? Gaskiya. Kuma gaskiyar ka zata fito. Na rantse da Allah, zan tabbatar da hakan.” Jami’an suka buɗe ƙofar, suka ja Maleekh zuwa yanda aka fito da shi... A lokacin yana waiwayen iyayensa, yana hawaye, yana faɗin cikin murya mai rauni: “Abbah… Ammy… ku yarda da ni…ku sanar musu... wallahi ban taɓa aikata irin wannan kazantar rayuwa ba…” Ƙofar ta rufe da ƙarfi, ɗakin ya sake yin shiru da duhu... tin daga ciki yake jin kukan Ammy.... ●●●●● Amal kuwa, tun bayan wannan tashin hankali, ta fara ganin abubuwa masu ban tsoro. Da farko tana cikin mota akan hanyar gida sai ta lura da wata motar black jeep tana binta a baya. Tana ƙoƙarin wucewa, motar na binta kamar ana bibiyanta... Tana isowa mai gadi ya buɗe mata gate, kafin ta shige, sai ta hango wani mutum a bayan gilashin motar sanye da black hoodie, yana kallonta da ido razana, tamkar ba mutum ba... Ta shiga cikin gida da gudu jikinta na rawa, zuciyarta na bugawa kamar za ta faso ƙirji... A razane ta fito daga motar ta nufi ciki da gudu, Inna tana zaune a falo bata tsaya kulata ba tsabar tsoro... Tana kaiwa ɗaki ta rufo ƙofa, ta jingina da bango tana huci. Hannunta na rawar jiki, ta ɗauki wayarta da gaggawa ta ƙara ƙiran Maleekh... “The number you’re trying to reach is not available at the moment…” Kamar daga sama ta fasa ihu tare da faɗin “Ya Allah! Me yake faruwa dani ne?” Knocking aka fara yi, Inna tana faɗi "Lafiya dai ko Amatu? Me yake faruwa ne?..." Amal cikin kuka take faɗin. "Inna ki tafi kawai ba komai, kai nane ke ciwo, ina buƙatar hutawa, bacci zanyi ...." Inna ta ce: "Yanzu saboda ragon taka Amatu a ciwon kai ne zaki shigo a razane sannan kina ihu haka? To Allah ya kiyaye ..." Ta juya.... *NEXT NEXT NEXT* asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 65 to 66 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Cikin dare misalin ƙarfe 2, Amal tana zaune a ƙasan gado tana kuka, sai faman tura message take zuwa ga Maleekh amma no reply... Ta kasa bacci kwata-kwata.. Tana cikin wannan halin sai ta ji sautin ƙwanƙwasa ƙofa. Da farko ta zaci mai aiki ce, amma sautin ƙwanƙwasawar ya sake maimaituwa, wani irin ƙara ne mai ƙarfi, da ban tsoro... “Waye ne!?” ta tambaya cikin murya mai rawa. Babu wanda ya amsa.. Ta tattara ƙarfin hali ta ƙarasa kusa da ƙofar, ta ɗan buɗe, amma babu kowa. Sai dai takardar white envelope a ƙasa. Ta ɗauka, jikinta yana rawa, ta buɗe cikin takardar ta ga an rubuta: “You can’t hide from us.” A lokacin ta saki takardar, ta soma karkarwa gaba ɗaya. Hawaye suka fara sauƙa a fuskarta. Ta yi ƙoƙarin ƙiran Zayd, amma sai ta tuna da abin da ya aikata mata. Ta ɗan yi jinkiri, ta ɗaga kai ta dubi hoton Maleekh da yake jikin mirrow. Tana hawaye ta furta “Ka dawo gare ni, dan Allah… karka barni haka. Ina fama da tashin hankali da rashin nutsuwa..duk saboda rashin ka..” Tana faɗin haka ta fashe da kuka. Tun daga ranar da ta samu takardar “You can’t hide from us,” Amal ta rasa natsuwa gaba ɗaya. Cikin kwanaki biyu ta lura da abubuwa da ba su da ma’ana: Wayarta tana kunna kanta da kanta. A ofishinta, tana jin kamar ana kallonta daga cikin gilashin taga. Kuma kowace rana, idan ta fito daga gida, sai ta ga wata motar black tinted a can nesa, ba ta san ta wa bace... Amal ta fara samun matsanancin damuwa. Bata taɓa jin irin wannan fargaba ba. Ranar Litinin, bayan ta idar da sallah da asuba, ta ɗauki shawarar zuwa wajen aikinta da wuri fiye da kowane lokaci... Bayan ta fito harabar gidan tana shirin shiga motarta sai kwatsam ta tsinci wani farin envelope a saman motarta, kamar irin wanda ta gani a baya... Da gaggawa ta buɗe. A ciki aka rubuta da jan biro: “Stop asking questions about Maleekh, or you’ll be next.” Jiki a sanyaye ta shiga motar ta ja a hankali, zuciyarta cike da tunani daban-daban.. Kafin ta isa wurin get mai gadi ya buɗe mata, kafin ta fita kuwa sai da ta dubi mai gadi sannan ta tambaye shi, "Da daddare akwai wanda yake shigo wa gidan nan?..." Maigadi ya bata amsa da cewa: "Wallahi Hajiya babu wanda yake shigo wa, tin lokacin da kika tsawatar mun da cewa, 'kada na kuskura na ƙara barin wancan yaron wato zaydu ya sake shigo wa, tin daga ranar ban ƙara ba, shekaran jiya ma yazo nayi masa koran kare...." Amal ta jinjina kai sannan ta ce: "Ba Zayd kaɗai ba, ko ma waye kada a bar mun kowa ya shigo mun gida indai ba wanda yake da alaƙa da gidan ba..." Maigadi ya ce "har da oga Maleekh?..." Ba tare da ta bashi amsa ba tayi ficewarta... Tana fita sai motar black jeep ɗin da ta saba gani ta tsaya a can nesa, fitilunta na kunne kamar dai tana jiran ta motsa... Cikin ƙarfin hali ta ja motar ta bar wurin, ɗayar motar ma ta bi bayanta, duk bayan mintuna saita dubi motar ta glass da haka ta isa campany... Tana shiga ofishinta, tayi ido huɗu da wani envelope again... A zabure ta nufi tebur ta buɗe.. "Your welcome fine girl, ina miki albishir da cewa daga yau ki fara ƙirga kwana kin mutuwarki, kamar yanda iyayenki suka tafi, ki tabbatar zaki bi su, ka da kiji tsoron fito wa domin ko akan gadonki zaki mutu. HAHAHAHA...." Da gudu ta je ta rufe office tare da sa key.. Tsaya ƙare wa ofishin tayi da kallo ƙirjinta ta bugawa da ƙarfi, jiki a sanyaye ta je ta zauna.. Ɗaukar telephone tayi ta ƙira secretary ɗinta, “Karki bari kowa ya shigo min yau. In wani ya tambaye ni, ki ce ban zo ba.” Ta kifar da kanta akan tebur cikin tashin hankali... _____________________________________ Kunna system ɗinta tayi, ta fara binciken bayanan cikin company musamman files na security footage, tana son ganin ko za ta gano wanda ya ajiye takardar. Bayan mintuna goma sha biyu, ta hango wani abu mai tayar da hankali. A cikin video ɗin CCTV, wanda ya saka takardar a saman tebur ba kowa bane bace Zayd... Ta zaro ido, tana kallon allon screen kamar wacce ta hango fatalwa. Hannu ta kai ta rufe bakinta... “Zayd…? Shi ne bayan komai…?” Tana nan cikin tsoro sai ƙofar office ɗinta ta buɗe da ƙarfi! Zayd ya shigo cikin sanyi, da murmushi a fuskarsa. “Ke dai kina da curiosity sosai, pretty.” Amal ta ja baya, tana faɗin, “Me kake nufi da hakan Zayd? Me yasa kake bibiyata? Me kake son gani daga gareni?” Ya yi dariya mai ɗan ban tsoro. “Kin san me yasa na fi son ki, Amal? Domin kina da jarumtar tambaya amma akwai tambayoyin da a duniya ba’a amsa su sai da mutuwa.” Yana matsowa kusa da ita, Amal tana ja da baya cikin tsoro tare da faɗin, “Karka kuskura ka matso kusa dani, wallahi zan ƙira ‘yan sanda!” Zayd ya tsaya, ya ɗora hannunsa akan teburin cikin sanyi, ya ce: “Ki ƙira su mana. Amma kafin su zo, zan tabbatar baki sake ganin Maleekh ba har abada.” Ya ciro wata ƙaramar bindiga a aljihu ya saita goshinta da shi, kafin ka ce mai ya harba akan goshinta..." A zabure ta ɗago kanta daga kan tebur tare da faɗin, Innalillahi wainnailaihiraji’unu, cikin tana rawar jiki take zanga addu’o'i, hannunta na kan kirji, tana jin kamar numfashinta ya tsaya. Ga gumin da yake yanko mata, a ɗan kifar da kanta da tayi har tayi wannan mummunan mafarki... “Ya Allah… menene yake faruwa dani?” A wannan ranar sam bata yi wani aikin azo a gani ba, haka ta tattari jakarta ta bar company.. Har dare ya tsala haka take wannan mummunan tunanin mafarkin da tayi.. Cikin wannan halin bacci ya ɗauke ta, amma ba baccin da ke kawo natsuwa ba, Sai mafarki mai tayar da hankali. A mafarkin, ta ga kanta tsaye a cikin wata tsohuwar falo mai cike da hayaƙin wuta. A gabanta ta ga wata mata da take kama da ita sosai tana kuka, wani mutum kuma yana roƙon wasu maza masu bindiga su kyale ta. Sai ga wani ya harbi matar, sannan aka fara ƙona gidan. Amal ta yi ihu, ta ce “Mooommm! Dadddd!!!” Tana neman nufansu sai wata murya mai rauni ta ce: “Amal... gudu ki gudu... kar ki yarda su same ki...” A zabure ta farka da kuka, jikinta duk ya jiƙe da gumi, zuciyarta na bugawa. Ta dafa kirjinta tana ambaton “Inna... Innaaa...Innalillahi wa inna ilaihi raji’un....” Ta tashi cikin daren, ta fito falo, ta ga fitillu a kunne sai plasman da yake kunne alamar akwai wanda ya kunna bayan an kashe kafin a kwanta...Domin yanzu ƙarfe 3 ne na dare... Idonta ta kai kan ƙofar falo ta ga a buɗe yake. Da sauri ta nufi ƙofa, sai ta hango wata ƙaramar takarda a ƙasa bakin ƙofar. Ta ɗauka, ta buɗe tana karantawa.. “Truth always returns, just like fire. 🔥” Nan take ta saki takardar tana girgiza kai. “Wannan me yake nufi? Wane gaskiya ake nufi?” A lokacin ta kukunna fitullun gidan gaba ɗaya, har na waje dana can ƙofar gida.. Ta fito a tsorace tana kalle-kalle, daga ita sai sleeping dress mai gajeren wando iya cinya sai riga ƙarama mai hannun breziyya... Da sauri ta nufi get da ta gani a wangale. Tana isa ta fice waje tana dudduba ko zata ga wanda ya fita.. Tana tsaye kwatsam taji an rungumota ta baya, tana shirin yin ihu taji an juyo da kanta tare da toshe mata baki da bakin wanda ya rungume ta.. Kissing ɗin bakinta aka rinƙa yi sosai tare da mammatsa mata nonuwa...haka hannunsa yake ta shafa duk ilahirin jikinta har su ƙasin mararta, still ba'a sake mata baki ba.. Alamun akwai wani shirin da ake son haɗa wa... A lokacin kuwa, wani ne daga cikin masu bibiyanta ya ke ɗaukar hotonta daga mota mai tinted da ke tsaye a nesa. Sai da ya ɗauki hotuna sannan ya kunna wayarsa ya tura su cikin group ɗin sirri da ke da suna Operation Cash Maker.. Duk kissing da hugs da sock and lick duk an ɗauki hotunan like da saninta akayi, irin ba tilastata akayi ba... A cikin group ɗin kuma mutanen da suke ciki basu fi mutum biyar ba... Alhaji Wadata da Zayd da kuma Alhaji Gusau da kuma Maleekh da akayi joining ɗinsa a ciki...But sun cancanza numbobi yanda Maleekh bazai gani ko mutum ɗaya a ciki ba, da zaran an fito da shi daga international cell...domin sun san cewa tin da mahaifinsa ya je to bazai dawo ba sai da Maleekh... Wanda yake kissing Amal kuwa baza'a taɓa gane ko waye ba domin yana sanye da bakaken kaya ne sai kuma black fenti da yayi a fuskarsa... ga kuma haske dadau dadau... Amal tana ta ƙoƙarin kwace kanta, bayan ya gama ya hankad’a ta, ta faɗi ƙasi har sai da ta buga gwiwar ta sosai... Kafin ta ɗago kuwa mutumin ya ruga da gudun gaske ya nufi motar, yana zuwa ya shige suka ja suka tafi... Bayan ta gama koke-kokenta da shan kuka ta tashi da ƙyar tana ɗingishi ta shige gida.. Tana shiga ta fara buga wa mai gadi ƙofa, can ya fito da torch ɗinsa mai uban haske duk da hasken fitullun gidan.. ga ƴar sandarsa a hannu.. Yana fito wa ya ci karo da Amal, cike da mamaki yake binta da kallo sannan ya ce. "Hajiya lafiya kuwa?..." A fusace ta ce. "Meye aikinka a gidan nan? Shin an kawo ka saboda ka bar get a buɗe kayi ta bacci?..." Maigadi cike da mamaki ya ce. "A buɗe kuma Hajiya? ..." Idonsa ya kar wurin get ya ga a wangale, ya sake baki tare da faɗin. "Ah!Ah!Ahhh, to wallahi sai da na kulle get ɗin nan har da bida, ya akayi a buɗe haka?..." Amal tana kuka ta ce "To wa ya buɗe get ta waje kuma?..." Maigadi ya haska ƙasi yanda aka fasa kwad'on a yayin da za'a fita amma ba'a san ta yanda aka shigo ba, abun ya bada mamaki sosai... A zabure Maigadi ya yi waje da gudu yana faɗin "Yau sai na kamo ɓarawon da ya shigo mana wallahi..." Ita dai ta tsaya tana kallon waje gaba ɗaya jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba... Haka kawai take jin tsinkar jikinta yana zuba wa, gabanta yana faɗuwa, da gudu ta zabura tayi ciki tana dingishi... Tana shiga falo ta kulle tare da sa key, sannan ta haura saman upstairs nan ma ta kulle bedroom, ta zauna a tsakiyar saman gado tana kuka.... 《》《》《》《》《》《》《》《》《》 A gefe guda kuwa, a London, Abbah da Ammy suna cikin tashin hankali... Suna ta tunanin sanar musu cewa an kama ɗansu Maleekh Abdul-Majeed a filin jirgi saboda samun kwayoyi masu haɗari a jakarsa... Tin lokacin da suka baro wurin Maleekh da kuma halin da yake ciki gaba ɗaya sun rasa sukuninsu.. Suna zaune a wani gidansu dake nan London.. Abbah yana zaune ya riƙe kansa, ya ce da murya mai rauni: “Na san ɗana ba zai taɓa yin hakan ba… akwai makirci a nan.” Ammy tana zaune a gefensa tana kuka, ta ce: “Alhaji, wannan makirci ne! Amma waye zai iya yin haka? Me ya ja wannan makircin?” Abbah ya dube ta cike da damuwa. “Sai na gano asalin komai. Kuma zan rantse da Allah, duk wanda ya sa hannu a cikin wannan sharrin, sai gaskiya ta fallasa shi, akwai lauyoyina da suke nam zasu tsaya masa gobe, domin daga yau insha Allahu bazai ƙara kwana cell ba.”... _Washegari_ A ɓangaren Maleekh kuwa.. Wani sanyi na fluorescent ne yake dukan saman ɗakin ƙaramin cell ɗin, ƙaramin taga da ke da reja a kai ya nuna ƙaramin layin haske mai ƙarfi kamar sanda. Maleekh ya farka da sabon rikicin zuciya, ba bacci mai annashuwa, sai gajiyar damuwa da rashin sanin makoma. Hannayensa na rawar sanyi, ya leƙa gefensa ya ga babu komai a tattare da shi. Ba wayoyinsa, babu passport, babu komai... Jakarsa na ƙarƙashin kulawar hukumomi... Ya dafa kansa da hannu, yana ƙoƙarin tunawa... Barinsa gidansu, zuwa gidansu Amal, ganin Amal da Zayd a gado ɗaya... Zuwansa filin jirgi, da sauƙarsa anan ƙasar london, jin muryar wani jami'in da ya ce “we have an issue here.” Sai kuma lokacin da aka ɗaure masa hannu, an ɗauke masa komai. Cikin zuciyarsa akwai tambaya ɗaya mai ƙwazo: “Ta yaya abubuwa suka kai ga haka? Wanene zai yi mun haka? Amal? Ko Zayd?..” Sai murmushi marar daɗi ya bayyana a leɓensa. Tunanin Amal ya dawo masa kamar an ƙwanƙwasa masa ƙirji... A lokacin aka buɗe ƙofar cell ɗin, wani jami’in interrogations ne ya shigo da fuska mai tsanani, yana riƙe da wani babban fayil. Ya zauna a gaban Maleekh tare da ajiye takardun a teburin gefensa.. ya kallesa kamar wanda yake auna abu.. kafin daga bisani ya ce: “Mr. Maleekh,” sannan ya fara da harshen Ingilishi mai sautin hukunci, “you are being charged with possession and intent to distribute controlled substances under UK law. We discovered illegal substances in your luggage upon arrival. Do you understand the charges?” Maleekh ya tashi a hankali, idonsa sun yi ja, zuciyarsa na duka kamar za ta fashe. A hankali ya furta. “No... no, I don’t understand. This is not mine. I swear wallahi ba na da hannu a ciki. Someone planted it. Ask my family. Ask my lawyers!” Jami'in yana girgiza kai ya ce “We will try to engage a local counsel, Mr. Maleekh. The Embassy can assist with consular visits, but legal representation is a matter you must fund or your family must arrange. The process here is strict possession with intent can lead to very severe penalties if convicted.” (Zamu yi ƙoƙarin neman lauya daga cikin mutanen garin nan, Mr Maleekh. Ofishin jakadanci zai iya taimakawa wajen ziyarar diflomasiyya, amma batun lauya wanda zai kare ka dole ne kai ko iyalinka ku biya kuɗin sa ko ku shirya hakan da kanku. Tsarin shari’a a nan yana da tsauri, kama mutum da kayan da ake zargi yana da niyyar amfani da su na iya haifar da hukunci mai tsanani idan aka same shi da laifi...) Cikin ƙaryewar murya Maleekh ya furta: “Ina Abbah?... ina Ammy... Ina fatan sun yi wani abu. Don Allah ka taimaka.” Lauyan ya dinga rubutu. Cikin akwai rashin tabbaci. Wannan hukuma ce mai tsauri, ba kamar wajen zaman gida can Nigeria ba inda magana za ta warware cikin husuma. A nan, takarda, hujjoji, signatures, da scanning ne suke magana. Washegari da safe an shigar da Maleekh kotu.. Ga lauyoyin da Abbah ya kawo domin kare Maleekh, Abbah da Ammy su ma duk suna zaune cike da tausayawa yaronsu... Maleekh yana tsaye a gaban kotu, a can ne ya ga idanuwan mutane daban-daban: wasu suna kallonsa da tausayawa, wasu suna ganin shi kamar wanda ya yi kuskure mai muni. an umurce shi ya zauna a gefen matsayi. Alkali ya duba takardu, ganin babu wasu hujjoji ne yasa shi faɗin: “The court hereby remands Mr. Maleekh in custody pending further investigation and trial. He is to remain in custody.” (Kotun nan ta bayar da umarni cewa a tsare Mr Maleekh a gidan yari har sai an kammala bincike da shari’a. Za a ci gaba da tsare shi a halin yanzu...) Wannan hukunci ya sauƙa a cikin zuciyarsa kamar dutse. Duk mafarkinsu da tsarinsu na rayuwa a cikin kunnuwa abbah da yake zuba fata ga shi yanzu ya koma ruwa... Bayan zaman kotu, an mayar da shi cell, inda ya zauna. A wannan dare Maleekh yana zaune sai tunani yake. Tare da maganar zuci. “Idan suna so in faɗi, to kuwa za su faɗi tare da ni. Zan yi yaƙi da wannan, zan nemi wakilcin lauya. I will not die as someone’s pawn.” 《》《》《》《》《》《》《》《》 A can Abuja A yau Amal tayi dare a wurin aikinta ga ana ruwan sama. Ta fita zatayi gida. Sai taga wasu black cars guda biyu na binta A baya.. Haka ta ƙara gudun mota suma suka ƙara gudu. Tana gudu da mota su ma suna binta da gudu.. Har tayi kusan accident sauran kaɗan motarta ta faɗa cikin wani rami. Sai ga wani mota ya sha gaban motarta sai motarta ya daki motar da yasha gabanta... Da karfi ta buga kanta da sitiyarin motar... A gigice ta buɗe ta fito, a lokacin motar da yasha gabanta Zayd ya fito a ciki yana ƙiran sunanta pretty... Amal tayi gudu ta nufi wurinsa tana faɗin "Zayd dan Allah ka taimaka mun wasu ne suke bina da gudu.." Bata san Zayd fuska biyu yake nuna mata ba, da sa hannunsa a cikin waɗanda ake bibiyanta, amma a gaban idonta sai ya nuna tausayawa, ya riƙe ta tare da rarrashinta yana faɗin "Kar ki damu ina tare da ke, ba abunda zai same ki..ina sonki sosai har yanzu..." Sauran motocin kuwa juyawa sukayi suka tafi... Zayd ya rakata har gida kafin ya tafi yana murmushin mugunta. A ransa yake faɗin "Haka zaki cigaba da zaman tsoro da firgita yarinya, wanda zai kare ki bayanan ya tafi...kuma ba dawowa..." Bayan tafiyarsa ta shiga gida tana tunanin mafarkin da tayi a office ɗinta akan Zayd.. Sai ta ƙara tsorata da shi, amma wani zuciyan ya sanar mata cewa "Ai mafarki ba gaskiya bane..." Rana ya ta yau ne za'ayi zama na ƙarshe a kotu.. an kawo shi gaban kotu a tsare, hannayensa a jikin sarkar da ke ɗaure. Idanuwansa sun yi ja. A katu mutane sun hallara: lauya, ‘yan jarida, ma’aikatan jakadanci, 'yan uwa, da sauran masu sha’ani. Kowa ya mayar da hankali ga taron zama na uku, za a gabatar da sababbin shaidu... Alkali ya yi shiru, ya duba takardun da ke gabansa, ya ce cikin murya mai nauyi: “An kawo shaidar da zata buƙaci sauraro. Prosecution, ku gabatar.” Wani jami’in ofishin tsaron filin jirgi daga Najeriya ya hau gaban kotu. A nutsuwa ya na ɗauke da wani fayil na hotuna da video. An kunna allon domin a nuna wasu frames na CCTV. A cikin video ɗin da aka kunna, an ga hoton tashar jirgin Najeriya, hoton check-in counter. Jakar guda biyu sun bayyana, ɗaya tana da tambarin kamfanin jirgin, ɗayan kuma jakar Maleekh wanda ya kasance iri ɗaya ne. Sai kuma an ga mutanen biyu daga cikin su wani ya ɗauko jakar, ya maida ta a kan trolley, tare da musayar sa da wani mutum da ya yi kama da ma’aikacin tashar. A frame ɗaya kuma an nuna wani mutumi ya ɗago jakar da sauri, ya tura ta cikin wani trolley daban. Lauyan Maleekh ya tashi tsaye, fuskarsa ta cika da bege. Ya miƙa hannu ya ce: “My Lord, wannan hoton ne zai nuna muhimmin abu: an maye jakar ƙasa a filin jirgi kafin tafiyar zuwa London. Wannan bayanin yana tabbatar da cewa jakar da aka tsare a Heathrow ba ta da alaƙa da abun da Mr. Maleekh ya shigo da shi.” Prosecution ya yi ƙoƙarin tada tambayoyi, amma mai gabatar da bincike daga Nigeria ya ci gaba da bayanin: “Mun gano ta hanyar passport da address an yi scanning a tasha. Jakar da aka samu a London ta fito ce sakamakon bayanan da muka samu a check-in. An duba signatures, an kwatanta lambar tag da passport kuma mun gano cewa jakar an sauya ta a Abuja, kafin jirgin ya tashi.” An kawo shaidun da suka nuna ticket number, boarding pass da hoton wanda ya aika da jakar, an gano sunan wani mai aiki a kamfanin tafiye-tafiye da ya shiga da wani ɓangare na aikin amintacce. An kuma gabatar da labarin forensic, analysis ya nuna cewa abubuwan da aka samu cikin jakar sun bambanta da abubuwan da ke cikin irinsa a Nigeria, hakan ya nuna maye gurbi ne... An yi tir da shaidu na prosecution waɗanda suka riƙe cewa an samu abubuwa masu haɗari a cikin jakar Maleekh. Amma bayan ganin hoton musayar jakar a Nigeria, da bayanan check-in, da kuma sakamakon forensic da ya nuna ana samun bambanci a cikin jaka ɗaya da ɗayan, alkali ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya yi magana. A wannan lokaci, lauyan Maleekh ya tashi ya gabatar da jawabi: “My Lord, abun da Allah ya nuna a bidiyon nan ya bayyana gaskiyar cewa an maye jakar. Abun da aka samu a London ba shi ne abin da Mr. Maleekh ya ɗauka daga Nigeria ba. A cikin wannan hali, akwai shakku mai zurfi. Babu cikakken hujja da za ta tabbatar da laifin wanda aka zarga. Mun roƙa a saki Mr. Maleekh domin babu hujjar da ta gamsar.” Prosecution ya yi ƙoƙarin ɗaga murya, ya nunawa kotu wasu bayanai amma dukan bayanan sun rushe ta hanyar hoton musayar jaka. Alkali ya ɗago idonsa, ya kalli lauyan da ke tsaye, sannan ya yi jawabi cikin murya mai tsanani: “Bisa ga abin da muka gani a gaban kotu, an samu cikakkiyar shaidar musayar jaka a tashar jirgin Nigeria. Hakan ya kawo shakku mai zurfi a kan sahihancin hujjojin da ake amfani da su a wannan shari’a. A saboda haka, kotu tana yanke hukunci cewa babu isasshen hujja da za ta tabbatar da laifin Mr. Maleekh Abdul-Majeed.” A nan ne ɗakin shari’a ya yi wani irin murna da farin ciki. Wadansu suka yi shiru. Maleekh ya ji kamar wani nauyi ya faɗi daga kansa, hawaye na zubo daga idonsa. Abbah ya miƙe tsaye cikin zaune, ya kalli ɗansa, idanunsa cike da hawayen murna. Ammy kuwa ta faɗi ƙasa cikin kuka ta rungumi Abbah. Jami’in ofishin jakadanci ya tashi ya tafi kusa da Maleekh ya ce cikin rarrashi: “Mr. Maleekh, your release is granted. We will assist with your travel documentation and liaise with authorities in Nigeria to investigate further the persons responsible.” Maleekh ya juya ya kalli alkali, ya yi godiya da karyayyen muryarsa: “Allah ya saka da alkhairi. Na gode. Na gode sosai.” Lauyoyi kusan huɗu ne waɗanda sukayi fice da shige wurin kwato Maleekh domin duk mutanen Abbah, wasu daga Nigeria wasu kuma daga nan ƙasar... A waje kuma ‘yan jarida da ke jiran fitar da sakamako sun yi ta dropawa da tambayoyi, Ammy da Abbah sun ɗauki lokaci suna rungumar ɗan su.. hawayensu na haɗuwa da godiya da jin daɗi. Amal dake can Niger ta ji labarin a wayarta ta hanyar wani abokin aiki ya ƙira ta: “Wallahi an wanke shi.” Ta ji kamar zuciyarta ta yi tsalle da daɗi sai kuma fargaba ta dawo: “Amma me zai faru gaba?” Ta rungumi kanta, tana addu’a a hankali... Ammy ta yi ta godiya, tana ta furta: “Allah mun gode maka! Waɗanda suka yi wannan sharrin ba zasu yi nasara ba.” Acan ɓangaren Alhaji Wadata da Alhaji Gusau da shi kanshi Zayd da mahaifiyarsa sun yi baƙin cikin fitowar Maleekh... Bisa tsaron jami'ai aka shigar da Maleekh mota tare da iyayensa suka nufi gida dake nan London.. Sai dai kuma, a ƙarshen wannan rana, akwai wani abu da ya rage: tambayar wanene ya maye jakar? Kuma wa zai amsa saboda irin wannan sharrin? Wannan tambaya ce da zata jefa labarin cikin sabon babi, bincike mai zurfi, haɗin gwiwar lauyoyi, da faɗakarwa ga wanda ya yi shirin. A babban falo duk suka hallaru.. Komai ya lafa sai nutsuwa, amma zuciyoyin su na ɗauke da abubuwan da suka sha wahala akan sa.. Maleekh ya zauna ya jingina da kujera, yana riƙe da wayarsa. Idanunsa sun yi ja saboda rashin bacci da damuwa. A hankali ya kunna wayar, sai ga jerin saƙonni daga Amal guda sama da ɗari! “Maleekh please ka yarda da ni…” “Wallahi ban san da komai ba…” “Don Allah ka amsa wayata…” “Ina cikin fargaba…” "Naji labarin kana cell sakamakon abin da aka samu a jakar ka, shin gaskiya ne?..." "Allah ya fitar mun da kai Maleekh..." Saƙonni suna ta shigo wa a jere, kamar ruwa da aka buɗe masa hanya. Ya runtse idonsa da ƙarfi. Zuciyarsa na bugawa. Duk da ciwon da yake ji a cikin ransa, har yanzu yana sonta amma hoton da ya gani ita da Zayd a ɗaki yana bin kwakwalwarsa kamar wuta. Wayar ta sake yin ƙara, “Amal Calling…” Sai dai ya tsaya kawai yana kallo, bai ɗaga ba. Ya rufe idonsa, yana sauƙe numfashi mai nauyi. A gefe kuwa, Abbah da Ammy suna zaune suna kallonsa cikin tausayi da godiyar Allah. Haka abokansa suka rinƙa ƙira suna masa fatan alkhairi, duk ƙiran da ya shigo sai ya ɗauka amma banda ta Amal, tana kiransa akai akai amma sam ya ƙi ɗaukan kiranta... Abbah ya murmusa kaɗan, yana cewa cikin murya mai nutsuwa, “Alhamdulillah, Allah ya tabbatar mana da gaskiya. Na gode da irin juriyar da kayi, ɗana. Wannan komai ya zama tarihi yanzu.” Ammy ta ɗan share hawaye, ta ce, “Ni har yanzu jikina yana rawa idan na tuna da wancan ranar… amma Alhamdulillah ka fito lafiya.” Maleekh ya ɗan sunkuyar da kai, yana cewa cikin murya mai sanyi, “Ni ma haka nake ji, Ammy. Amma har yanzu kamar mafarki nake kallon abun, ban taɓa zato cewa zan shiga irin wannan masifa ba.” Sai Abbah ya gyara zama, yana ɗan murmushi da girmamawa: “Maleekh, yanzu dai lokaci ne na farin ciki. Da zarar mun koma gida, zan so mu fara shirye-shiryen auranka da Amal.” Ammy ta zabura da sauri, tana kallon mijinta da fuskarta cike da mamaki: “Haba Alhaji! Daga fitowarsa a cell sai aure? Ai yaron nan har yanzu yana cikin tashin hankali, bai da cikakkiyar nutsuwa.” Abbah ya jinjina kai, yana dariya kadan. “Maryam, aure ma wani hutu ne. Kuma ya dace mu gyara kuskuren da ya faru. Maleekh da Amal sun jima da haɗuwa da soyayya, babu dalilin da zai sa mu jinkirta.” Maleekh ya ɗan motsa, yana kallon iyayen nasa. Zuciyarsa na bugawa da sauri. Sai dai ya ƙudura a ransa ya gama da soyayya. Ya ce da murya mai natsuwa da kuma cike da rauni, “Abbah... ta mun laifi sosai. Don haka a barni in huce tukun kafin a kai batun aure.” Abbah ya kalle shi da ƙarfi, yana murza agogon hannunsa. “Wannan ba mai yuyuwa bane, domin bazaka lalata wa yarinya Aure ita da ɗan uwanta ba kuma kai ka ƙi aurenta, wannan kuskure ne da kuma yaudara, don haka dole ne aure..." Shiru ya cika falon. Sai Maleekh ya sauƙe numfashi, ya ɗan murmusa cikin gajiyar rai. “Shikenan Abbah... ba damuwa. Na amince.” Abbah ya saki murmushi, yana duban Ammy da fuska mai natsuwa. “Alhamdulillah. Da wannan magana, zuciyata ta huta.” Ammy kuwa ta yi shiru kawai, tana kallon Maleekh, zuciyarta na ɓoye da damuwa, saboda ta san ba soyayya bace ta sa ya amince ba, kawai biyayya ce ga mahaifi. Kuma sannan ba wani ƙaunar Amal take ba..." Ammy ta buɗi baki ta ce. "Amma da sharaɗin idan mun koma za'a je a fito da Farha..." Abbah ya ce "wannan ba abun damuwa bane.." Sai falon ya sake komawa cikin nutsuwa, sai muryar TV da take showing a gefe. Zuciyarsa ta mutu, amma fushin da yake da Amal bai mutu ba…domin har yanzu yana kallon ta da Zayd ne a kan idonsa. Kuma ya ci alwashi duk san da ya ƙara ganin su a haka sai yayi musu hukunci marar misaltuwa... Yana cikin duba wayarsa, ga kuma saƙon WhatsApp da suke ta shigo masa, bai yi niyyar duba wa yanzu ba har sai ya gama huta gajiyarsa kwatsam sai yayi ido huɗu da wani group da bai san shi ba samm... Saboda wannan group ne yasa shi shiga WhatsApp, kai tsaye kafin ya duba meye a cikin group ɗin sai da ya duba su waye a ciki, ganin duk babu wanda ya sani sakamakon rashin sanin numbobin, yana shiga group ɗin abinda ya gani kawai a cikin group ɗin shine photuna.. Da farko yayi tunanin group ɗin BF ne har zai fita kafin photunan su buɗe, sai kawai ya hango fuskar Amal da wani a rungume da ita ta bayanta.. ga videos.. Zaro ido yayi yana duba wa. Nan ƙirjinsa ya tsananta bugawa.. Abbah da Ammy ganin canjin da ya shigo lokaci guda yasa su tambayarsa "lafiya kuwa?.." A zabure ya ɗago kamar zai fashe da kuka ya ce. "Ba komai, komai na ga campany na ya ja baya, babu wani ribar da ake samu yanzu..." Abbah ya ce "kuma shine abun damuwa? Kana komawa komai zai yi normal...itama Amal bata cikin nutsuwa shiyasa..." Ammy dai kawar da kai gefe tayi, ta bar su da halin halinsu domin yanzu ta cire hannunta. A cewar ta... Abbah ya kuma cewa. "Amma babu wani damuwa akan batun auren koh?..." Maleekh ya jinjina kai cikin sassanyar murya ya ce "Sosai ma.." Daga nan ya bar falon, kai tsaye bedroom ya nufa. A wannan ranar gaba ɗaya ya kasa bacci sai kallon hotunan da video.... _NEXT NEXT NEXT_ asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 67 to 68 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Yamma liss misalin ƙarfe 6:30. Rana ta faɗi sai launin duhu dake sauƙa daga sararin sama.. Amal ta fito daga Office ɗin “The Awaken Project” dake cikin Campany CashTalk, da gajiya a fuskarta domin tun safe take aiki ba kakkautawa, tana bin bayanin wasu bayanai da ta samu daga manema labarai game da batun shari’ar Maleekh da kuma waɗanda suka kitsa sharri a kansa... A cikin zuciyarta akwai farin ciki, saboda labarin cewa Maleekh ya fito daga kurkuku ya bazu, amma ba ƙaramin tsoro ke ratsa jikinta ba tun mako guda take jin ana bibiyarta.. Ganin duk ma'aikata sun tashi babu kowa yasa itama ɗaukan jakarta ta nufi harabar campany domin shiga motarta... Sai security ne kawai dake ta zirga-zirga.... Ta kunna motarta cikin nutsuwa, ta ɗan lumshe ido sannan ta ce a hankali: “Ya Allah, ka tsare ni daga sharrin makiya...” Motar ta tafi a hankali ta bar harabar kamfani. Titunan Abuja suna cike da hasken fitilu, yanzu kusa magariba, cunkoso yayi yawa. Amal ta zaɓi hanya mai sarari domin gujewa cinkoso, hanyar da bata da yawan jama’a, Airport link road extension.. Sai dai yau, ƙaddara ta rubuta wani abu dabam... Da ta shiga tsakiyar hanya, kwatsam sai ta hangi wata baƙar mota daga nesa, black Prado tana tahowa da sauri kamar mai tuƙi cikin fushi. Tana tunanin kamar motar da yake bibiyanta ne, cikin kankanin lokaci motar ta iso gabanta, ta shige mata gaban hanya da ƙarfi! Amal a firgita ta ce, “Subhanallah!” Ta juyar da sitiyarin cikin hanzari, tana ƙoƙarin kaucewa. Amma kafin ta daidaita kansa sai ga ƙaton trailer daga bayan ta, yana tahowa da gudu! Wani irin ƙara trailer ya yi, “Tuuuunnn!!!” Sai a nan lokaci ya tsaya! Komai ya haɗu cikin daƙiƙa: Motar Amal ta yi wani irin juyin juyi, ta yi tsalle kamar ƙwallon roba, sannan ta faɗa cikin rami mai zurfi a gefen hanya. Wurin babu jama’a, hanya ce da ba a yawan bi. Taya ta ƙone, gilashin motar suka watse. Cikin hayaki da ƙura, motar ta tsaya cak. Sai ɗaya daga cikin mutanen cikin baƙar motar ya fito, sanye da farin riga da hula baki, ya duba cikin ramin da wayar torchlight. Yadda Amal ta kwanta, jini na malala daga goshinta, jikinta ba motsi. Ya ce da muryar ƙarfi, “Boss, ta gama! Babu numfashi!” Wani daga cikin motar ya amsa daga ciki cikin murya mai sanyi: “Ka tabbatar. Ba zan so a bar wata shaida ba.” Sai ɗayan ya ɗaga torchlight ɗin ya sake duba jikin Amal, ya taɓa ƙirjinta da yatsansa. “Laf! Ta mutu... Babu motsi ko numfashi.” “Good.” “Mu tafi.” Motarsu ta bar wurin da sauri, tana shirin bacewa cikin duhun dare. A bayan su, motar Amal tana nan cikin rami, tana ta hayaƙi kamar wanda akayi gobara... Dare ya gama shigowa, iska tana busa ganyaye a hankali. Cikin duhun da bai da haske, ƙarar wata ƙaramar tsuntsuwa ce kaɗai ke ji kamar tana kuka... Sai dai a can nesa, wani mai babur dake wucewa ya tsaya yana kallon hayaƙi da ke tashi daga ƙasa. Ya ce da mamaki: “Innalillahi… wace irin hatsaniya ce kuma haka?” Ya fara saukowa daga babur ɗinsa zuwa ƙasan ramin, yana ƙira da murya mai sauti: “Hello! Hello! Wani yana ciki?!” A lokacin da ya haska torchlight ɗinsa, fuskar Amal ce ta bayyana jini a goshinta, numfashinta a hankali kamar wacce duniya ta fara barinta... Ganin irin halin da take ciki ne yasa ya lalumo wayarsa zai ƙira ƴan sanda, cikin tashin hankali ganin ba credit a wayar ne yasa ya dubi Amal da rabin kunkuminta ke cikin mota, zuwa samanta kuma na wajen motar.. "Baiwar ALLAH! Baiwar ALLAH kina ji na?..." Haka yake ta tatta6a fuskarta babu wani motsi... anan ya cigaba da gadinta ko akwai wanda zai zo. Shiru babu kowa ga dare yayi sosai, gashi har 11 ta wuce. Anan wani dabara yazo masa, ya fara bincika motar ko zai samu wayarta yayi amfani da ita, cikin sa'a ya samu amma sai dai ta farfashe.. Amma bata mutu ba, sai dai kuma wani tashin hankali akwai security. Ganin Amal ta tafi dogon suma yasa yayi amfani da fingerprint ɗinta, cikin sa'a ya buɗe anan ya samu damar ƙiran lambar gaggawa ta police (199)... Asuba, gari ya ɗan fara waye wa. A kan titin da hatsarin Amal ya faru, an riga an zagaye wurin da igiya, motar FRSC da ta ‘yan sanda na wurin tun cikin dare duk ana bincike kuma har yanzu ba'a samu wani shaidar da zai sa da ganga akayi hatsarin... A lokacin da suka ciro Amal daga cikin motarta, jikinta a jike yake da jini, rigarta kalar fari duk ya rine kamar ba farin riga ba, idanunta a rufe kamar wacce take barcin mutuwa. “Gaggawa! Ku ƙira ambulance!” “Ba zata iya rayuwa ba idan ba a kai ta yanzu ba!” Motar ‘yan sanda ce ta ɗauke ta, aka nufi babban National Hospital Abuja da ita. Likita ne yake bada umarni cikin tashin hankali: “Blood level ɗinta ƙasa da kashi 10%. A nemo masu jini nan take! Waye ‘yar uwarta? Waye nata?” Amal na kwance babu numfash..Da farko duk wanda ya ganta bazaiyi tunanin akwai rai a jikinta ba.. 🇬🇧 A London A gidan da Abbah da Ammy ke zama, labarin hatsarin ya iso da safiyar nan. Wani daga cikin ma'aikata campany ne ya ƙira: “Sir, Madam Amal had an accident last night... she’s in a critical condition.” Da wannan kalma guda, wayar Maleekh ta sulale daga hannunsa.. Hankalinsa ya tashi kamar wanda aka cire masa rai. “What? Amal? Accident?!” Ya ɗauki wayarsa ya nufi part ɗin da Abbah yake da sauri. “Abbah! Amal ta samu hatsari! Ba zan iya zama ba, dole mu tafi yanzu!” Ammy ta riƙe ƙirji, ta ce cikin tsoro: “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Meya haddasa hatsarin?... Allah Ya bata lafiya, idan kuma ta mutu Allah ya jikanta. Amma meye namu da zamu tafi haka da gaggawa sai kace Islam ce ko Arfat tayi hatsari..” Abbah ya ce "Insha Allahu tana nan da ranta, kuma itama Amatu ƴa ce a wurina, dole mu tafi ko bakya so..." Nan Maleekh ya ji do musu akwatuna... Ba a ɓata lokaci ba, aka nufi filin jirgi. Duk tafiyar ta Maleekh ta cika da hawaye da addu’a. Yana cikin jirgi, hannunsa na riƙe da hotonta a wayarsa, hoton da take dariya da idanu masu cike da kyalli... “Amal, ki tsaya ki jirani... don Allah kar ki barni.” ✈️ A Abuja Da suka sauƙa, Abbah ya sanar cewa su fara zuwa hospital. Ammy ta ce "Ni kam zan wuce na gaji.." Abbah ya ce "Sai mun je kinga halin da sirikar ki take.." Ba yanda ta iya haka ta haƙura. Kai tsaye hospital suka nufa cikin gudu da motar da aka kawo musu airport.. Jikin Maleekh sai rawa yake, zuciyarsa kamar zata faso ƙirji.. A bakin ƙofar asibiti, likitoci da nurses ne suka cika wurin, haka suka kutsa ciki, Maleekh yana shiga kowa ya tsaya kallonsa saboda hotunansa sun bazu a kafafen labarai, kama shi da akayi a london sakamakon miyagun kwayoyi da aka gani a jakarsa... Abbah ne yayi magana da cewa: “Excuse me! Where is Amal Abdulsamaad? The accident victim from last night!” Wata nurse ta ce: “Room 204… but sir, her condition is very critical.” Suka nufi ɗakin kamar zasu fira.. Ita kuwa Ammy a nutse take takun ta.. Abbah shima dakatawa yayi sakamakon wata Nurse da ta sanar musu cewa "Ku ɗan dakata ana duba majinyaciyar, ga can wurin zama..." Kafin ta ƙarasa Maleekh har ya buɗe ya shige ciki. Abbah girgiza kai yayi yana mamakin ɗan nasan da taurin kai. Haka suka nufi wurin zama kafin ayi musu iso.. Bayan ya shiga, Maleekh ya tsaya cak.. Amal na kwance cikin farin zanin asibiti, fuskarta duk raunika ga an zagaye kanta da bandeji, jinin da aka ɗaura mata ya kusan ƙarewa.. Hankalinsa a tashe ya ƙarasa kusa da ita ya riƙe hannunta, muryarsa na rawa: “Amal… kina ji na? It’s me… Maleekh. Don Allah ki buɗe idonki… kar ki barni.” Nurse dake kusa ta ce: “Bamu da isasshen jini, kuma jinin nata AB positive ne mai wuyan samu, wannan ma da ƙyar muka samu, yanzu muna neman ledar jini uku.”.. Maleekh ya miƙe, yana faɗi cikin murya mai ƙarfi: “Ni O- ne. Ku ɗauki nawa! Ku ja jini daga jikina yanzu! Don Allah ku ceto ta!” Nurse ta kalle shi da mamaki: “Kai ne za ka bayar?” “Eh! Ba tare da tunani ba. Ku fara yanzu!” Maleekh ya ce yana jan ye hannun rigarsa... Ɗakin ya cika da sanyin AC, duk da haka gumi ke keto a goshin Maleekh saboda tashin hankali. Amal tana kwance, oxygen a hancinta, jini na gudana daga bututun da aka haɗa a hannunta.. Likita ya fito daga wani ƙaramin ɗakin dake cikin room ɗin da sauri yana faɗin "Meke faruwa anan?..." Nurse ce ta sanar masa cewa. "Sir wannan ɗan uwanta ne yazo..." Maleekh ya ce "Me kuke kike jira ne? Ki ja ki farfaɗo mun da ita..." Doctor ya kalli Nurse sannan ya ce "Kun yi ne akan zaki ja jininsa? Sannan kin sanar masa adadin jinin da ake buƙata ne?.." Nurse ta sunkuyar da kai cikin kikkina ta ce "Sir. Shi ya ce a ja ukun..." "Mtssww you are not serious..." Doctor ya ce tare da kallon Maleekh ya ce... “Mun jira babu wanda yazo a cikin ƴan uwanta, meyasa sai yanzu? Shin baku damu da ita bane?...." Maleekh ya goya hannayensa akan ƙirji ya ce "Look Doctor! Kar ka nemi ka gaya mun magana, yanzu haka daga London nake, a yau nake jin labarin, kuma ni mijinta ne..." Doctor ya ce "Okay! Bamu da isasshen jini, kuma jinin nata AB positive ne, wanda yake da wahalar samu a halin yanzu. Wannan ma da ƙyar muka samo leda ɗaya, yanzu muna neman ledar jini uku kafin ta iya farfaɗowa gaba ɗaya.” Maleekh wanda ke tsaye yana fuskantar Doctor ya ce cikin murya mai ɗaure kai, “Nurse ta mun bayani. Amma taya AB zai yi wahalar samu? Jini na O-negative ne, ku janye daga jikina yanda zai iya mata..!” Likitan ya kalle shi da mamaki, “Amma Sir Maleekh, jinin O- yana da tsada sosai ga jikin mutum, kuma jini leda uku bazai jitu da lafiyarka ba. Zai iya raunata zuciyarka.” Maleekh ya ɗan ɗaga murya cikin ƙarfi, idonsa ya cika da hawaye, “Na ce ku janye! Tunda rayuwarta tana cikin haɗari, babu wani abu da ya fi muhimmanci fiye da ta rayu. Ku janye ku bata tunda jinin nan da kuke gani yana gudana ne saboda ita!” Likita ya tsaya na ɗan lokaci kafin ya ce, “To shikenan, amma dole mu lura da lafiyarka. Wannan haɗari ne, sai mu shiga can bangaren ka kwanta bayan an gama don a saka drip ɗin ƙarfi a jikinka.” Dake room ɗin babba ne, ya kwanta a ɗan nesa da ita wanda glass ne ya tare tsakaninsu..amma yana iya hangota ta cikin glass ɗin... Maleekh ya ɗan murmusa cikin damuwa, yana duban Amal daga nesa ta cikin gilashin ƙofar d'akin jinya, “Ina roƙon Allah ya karɓi wannan jinin ya mayar da shi da albarka a jikinta. Ko da zan rasa rayuwata, ta rayu kawai.” Likitan ya girgiza kai da tausayi, “Wannan soyayya ce mai haɗari, amma Allah ya sa ta tashi lafiya.” Sai aka ɗauki bututun jini aka haɗa da hannun Maleekh, zuwan jinin a cikin bututun yana fitowa a hankali. Maleekh ya lumshe ido, jikinsa yana rauni amma zuciyarsa cike take da natsuwa. A gefe, Ammy da Abbah suka shigo cikin gaggawa. Bayan nurse ta sanar dasu halin da ake ciki... Suka shiga Ammy ta nufi Maleekh da gudu. Ammy ta ce cikin rawar murya, “Me ya faru da shi? Me yasa aka haɗa shi da na’urar jini?” Likitan ya kalle su cikin ladabi, “Yana ba wa Amal jini ne, saboda babu wanda yake da jinin da ya dace da nata.” Abbah ya tsaya ya goya hannayensa akan ƙirji, yana kallonsa da idanu masu cike da ƙauna da damuwa, “Maleekh… ka cika jarumta. Amma me yasa baka faɗa min ba kafin ka yanke wannan hukuncin?” Maleekh ya buɗe ido a wahalai, ya ce cikin rauni: “Abbah… idan na rasa jini saboda ita, to hakan ma bai kai na rasa Amal ba.” Ɗakin ya ɗauki shiru na mintuna biyu, sai ƙarar na’urar jinin da ke motsi, tana nuna ana cigaba da tsotsar jinin. Likitan ya kalli ma’aikata ya ce da sauri, “Ku kula, kada ku wuce pints biyu kawai. Wannan jarumin zai iya faɗuwa a nan idan kuka wuce.”.. Bayan mintuna talatin, aka sake ɗaura wa Amal jinin da aka ja daga Maleekh... Doctor yana kallon Maleekh ya ce "ka jira zuwa nan da awa 5 za'a sake jan na biyu.. Maleekh ya ce "Ni kam ku cire gaba ɗaya bana son jinkiri, 2 pints ku ka ce, sannan 3 ake buƙata kuma kun cire 1..." Doctor ya ce, "Sorry..." Kafin ya ƙarasa Maleekh ya katse shi da "Sorry for what?..." Doctor ya cigaba da jan jinin kamar yanda ya buƙata... Jinin Maleekh yana shiga cikin Amal a hankali, likita yana kallon monitor ɗin zuciyarta. Sai suka ga bugun zuciya ya fara motsawa a hankali. “Doctor! Heartbeat is rising!” “Keep it steady. Don’t stop the transfusion!” A cewar wata Nurse... Maleekh juyar da kansa yayi cikin damuwa yana tuna abubuwan da suka faru a tsakaninsa da Amal.. Haka al'amura suka cigaba da tafiya... Bayan doguwar suma na kwanaki uku, Amal ta fara motsi. Idanunta sun fara buɗewa a hankali, Inna da Abbah dake ɗakin, ba ƙaramin farin ciki suka yi ba, suna hamdala cikin nutsuwa... Likita ya shigo, ya dubi lafiyarta da bugun zuciyarta. “Lafiyarki tana nan, amma za ki buƙaci hutu da kulawa sosai,” in ji likitan. Amal kuwa ba abunda take faɗi illa ƙiran Maleekh: “Ina ya Maleekh? Ina yake? Ina son ganinsa...” Ganin ta damu da ganin shi, Abbah ya ɗauki waya da gaggawa, ya ƙira Maleekh. Bayan wasu mintuna kaɗan, sai ga Maleekh ya shigo cikin haɗa rai. Fuskar sa cike da damuwa, idonsa na nuna nauyi da ƙiyayya, tunanin hoton da ya gani na Amal da kuma ganinta akan gado da Zayd a ɗaki ya cika ransa da rikici. Amma zuciyarsa ta ɗan tsaya: zai amince ya aure ta bisa umarnin Abbah, duk da cewa yana son Amal sosai. Maleekh ya zauna a gefen gadon asibiti, bai kalli Amal ba. Kamar yana ɓoye wani abu a zuciyarsa, ya nisanci kallonta da duk wani murmushi da zai iya bayyana. Amal ta ɗan yi motsi, ta gane cewa shi ne ya shigo, sai hawaye suka gangaro mata tare da murmushi mai rauni a bayyane akan fuskar ta. Ta riƙe hannunsa tana jin ɗumin jikinsa, tana jin ƙaunar sa da kewar sa... Maleekh ya yi ƙoƙarin daidaita numfashinsa, bai jan ye hannunta ba haka ya daure yana danne fushinsa. Daga baya, Inna da Abbah suka tashi suka bar ɗakin, suka basu wuri su biyu kaɗai.. Amal ta ɗan motsa, idanunta suka haɗu da na Maleekh. Hawaye suna gangarowa amma fuskar ta na cike da farin ciki. Ta miƙa hannu ta shafa fuskarsa tana wasa da gemun... “Maleekh… kai ne?..." Ya ce "Uhm! Uhm bani bane...ke ce.." "Wallahi na daɗe ina kewarka…” Ta ce tana murmushi... Maleekh ya ɗan kalleta ta wutsiryar ido, bai amsa da tsawo ba. “Hmm…” Amal ta ɗan yi murmushi, tana jin ɗumin jikinsa. “Na yi kewarka sosai… watanni da babu kai…” Maleekh ya kawar da kai gefe, yana ɗan lumshe idonsa. “Ba komai…” Amal ta ɗan yi dariya, ƙaramar muryarta na rawa ta ce: “Na yi tsammani zan rasa ka, har na firgita…” Maleekh ya ɗan girgiza kai, amma bai yi magana mai tsawo ba, sai ya ce: “Ki tsaya… lafiya nake yanzu.” Amal ta ɗan yi murmushi mai rauni, ta rungume hannunsa da ƙarfi, tana jin kamar komai zai daidaita yanzu. A cikin shiru, Maleekh ya ɗaga murya da cewa “Meye dalilin hatsarinki?” Amal ta ɗan ɗago, muryarta na rawa saboda raunin jinyar: “Ban san dalili ba… me yasa ina yawan ƙiran ka, amma ba ka ɗauka?” Maleekh ya kawar da kai gefe, yana murmushi cikin natsuwa ya ce “Uhm… nothing.” Amal ta ɗan kalli fuskar sa, da bai nuna wani abu ba. Haka suka zauna, yana amsa mata magana sama-sama, cikin shiru mai cike da nauyin zuciya. Maleekh yana ƙoƙarin ɗaukar damuwarsa, yana tunani akan abin da ya gani a hoton da aka ɗauka. Amma a zuciyarsa, akwai ƙauna mai ƙarfi ga Amal sai dai bai bayyana hakan a halin yanzu, saboda damuwa da haushin abin da ya gani. A gefe guda, Amal kuwa tana jin ƙarfin zuciya saboda ganin sa a gefenta, duk da raunin jikinta, tana jin kamar komai zai daidaita... Hannu yasa ya ɗaga ta daga kansa dake yana zaune ne a bakin gadon da take. Ya kwantar da ita akan gadon. Cike da mamaki take binsa da kallo ganin ya ɗaga ta daga kansa. Amma haka ta sharar.. “Inaso na aure ka… please, yaushe ne auren mu?” Maleekh ya ɗan danne zuciyarsa, haushin ganin ta cikin wannan yanayi da kuma tunanin abinda ya gani, yana lumshe ido ya ce: “Kina kwance a hospital za’ayi auren?” Amal ta ɗan girgiza kai, tana jin sautin kamar ba Maleekh ɗinta ba: “Ko baka sona yanzu?” Maleekh cikin fusata ya ce: “Please ki kyale ni da wannan shirmen nakin…” Amal ta ɗan ƙira sunansa cikin raunannen murya: “Ya Maleekh…” A wannan lokacin, Abbah, Inna, da Islam suka shigo cikin ɗakin. Abbah yana murmushi, idonsa kan Amal ya ce: “Ƴata, kwantar da hankalinki. Mun dawo ne da shirin auren ki da Maleekh.” Lokaci guda Amal ta ruɗe, tana ƙoƙarin sauƙa daga kan gado: “Da gaske Abbah? Muje a ɗaura yanzu, dan Allah… banaso Ya Maleekh ya sake kubuce mun.” Abbah ya ɗan saki murmushi, yana mai sassauta yanayi: “Ki yi haƙuri. Maleekh yana nan tare da ke. Ki bari sai kin ƙara samun sauƙi tukun ko…” Amal gaba ɗaya ta ruɗe, zuciyarta cike da gaggawa ta ce: “A’a Abbah, na samu sauƙi yanzu ma… muje kawai!” Tana miƙe wa sai hajijiya ya ɗauke ta ga ƙafarta a ɗaure da bandeji. Maleekh da sauri ya rungume ta, idanunsu suka haɗu. Sun tsaya a haka na ɗan lokaci, suna kallon juna cikin shiru, daga bisani suka dawo cikin nutsuwa. Maleekh ya kwantar da ita a gadon tare da faɗin: “Ki shiga taitayinki fa…” Ya juya ya fita daga ɗakin, idanunsa suna ɗauke da haɗin damuwa da kulawa. Amal ta tsaya kallon bayansa har ya ɓace. Inna ta ɗan murmusa, tana kallon Amal: “Ai nasan yaran suna ƙaunar junansu, shiyasa suka tsaya kallon juna…” Amal a hankali ta furta: “Abbah… me yake faruwa da Ya Maleekh ne?” Abbah ya ɗan saukar da murya, yana mai sassauta murya: “Ki bar shi, ai kinsan ya fito ne daga cell, shiyasa. Amma in ya nutsu, hankalinsa zai dawo…” Amal ta ɗan yi shiru, idonta a shanye kamar mai jin bacci, amma zuciyarta na jin ɗumin soyayya da ƙarin aminci ga Maleekh.. 《》《》《》《》 Babban falon gidan su Zayd.. Zayd yana cikin tashin hankali, zuciyarsa cike da damuwa da fushi akan hatsarin da Amal tayi. Ya tsaya, idonsa akan mahaifinsa ya ce: “Dad, meyasa zakuyi haka? Kun yanke hukunci ba tare da sanina ba, meyasa bazaku iya barin Amal da rayuwarta ba? Meye laifinta? Ka tura mutanenka su je su buge ta da mota, to Allah ya cece ta, bata mutu ba…” Alhaji Wadata ya kalle shi cikin fuska mai nuna rashin fahimta: “Meye damuwarka da ita?” Zayd ya ɗan girgiza kai, zuciyarsa cike da ƙarfin hali da soyayya ya ce: “Ni ma sonta nake. Inaso nayi takara da Maleekh akan soyayyar Amal. Dan Allah kada ku sake yunkurin kashe ta. Bata cancanci haka ba…” Alhaji Wadata ya ɗan ɗauke kansa, yana mai nuna tsauri: “Mutuwar Amatullah ya zama dole. Idan bazaka iya ganin mutuwarta ba, ka koma London…” Zayd ya kalli mahaifinsa cike da kwarin gwiwa ya ce: “Idan har ina raye, bazan taɓa barin haka ba… Duk abubuwan da nake mata inayi ne saboda na rabata da Maleekh, sannan a tsorata ta, amma banda mutuwa…” Alhaji Wadata ya ɗan nuna fushi a fuskarsa sannan ya ce: “Kana jayayya dani ne?!” Zayd ba tare da ya tsaya ba ya juya ya bar falon. A wannan lokacin, mahaifiyarsa, Hajiya Sa’adatu, ta sako baki cikin shiri da tsauri: “Alhaji, nayi wani tunani. Tinda Zayd yana sonta, a barta da rayuwarta, yayi duk abinda zai yi ya rabata da Maleekh. Kai kuma, Alhaji, sai ka raba mahaifin Maleekh da kujerar siyasar da yake nema. Ita kuma, yarinyar Amal, da zaran Zayd ya aureta, anan ne zamu musguna mata, sai muyi mata duk abinda muke so…” Alhaji Wadata ya ɗan hango fuskar Hajiya Sa’adatu, yana mai nazarin shawarar: “Wannan shawarar taki tayi. Alhaji Abdul-Majeed daga wannan kujerar zai nemi kujerar governor, kuma ni zan nema. Don haka, zanyi takara dashi, shi kuma Zayd yayi takara da ɗansa ta wurin soyayya. Inaso na gansu kullum a ƙasa…” A wannan lokaci, Farha, wacce yanzu ta dawo daga prison, Maleekh ya ciro ta, ya kawo ta har gidan iyayenta anan Abuja. Tana tsaye a bakin ƙofa, duk taji tattaunawar da sukayi tin daga farkon da Zayd yayi har ya bar falon da shawarar da iyayen natan suka yanke.. daga baya kuma Maleekh wanda ya kawo ta ya tsaya fitar mata da jakakkunanta da siyayyar da yayi mata. Ya iso wurin da take a tsaye. Ya tsaya a gabanta, ya ce: “Ki buɗe mu shiga ciki mana…” Farha ta ɗan tsaya, duk ta rarrame tayi baƙi, ta buɗe ƙofar, suka shiga cikin gidan. A falo ta tarar da iyayenta. Hajiya Sa’adatu ba ta iya ɓoye farin cikinta ba, ta tafi da gudu ta rungumi Farha tare da faɗin: “Wayyo, Daughter na, ta dawo! Allah na gode maka, nayi farin ciki sosai da ganinki...” Alhaji Wadata shima, idonsa cike da farin ciki, ya dubi ‘yar sa sannan ya ce: "Your welcome my daughter.." Maleekh ya dube su dakyau sannan ya ce, “Ga ƴar ku nan. Na ciro ta daga prison, daga nan muke yanzu. Ku cigaba da riƙe ƴar ku sannan ku ja mata kunne akan shiga shirgin da bai shafe ta ba…” Maleekh ya juya, idonsa cike da kulawa da tsaro, ya fice daga falon. Alhaji Wadata ya tsaya a wurin, yana kallon Maleekh cikin wani irin kallo mai cike da nazari, tsauri, da kuma ƙiyayya na abin da zai yiwa Maleekh... Zayd ya shiga dakinsa, zuciyarsa cike da tunanin Amal. Ya zauna a bakin gadon, ya ɗaura hannunsa kan fuskarsa, yana mai ƙoƙarin kwantar da hankalinsa, amma duk da haka, zuciyarsa ta kasa kwanciya.. Zayd cikin zuciyarsa yake faɗin: “Ban taɓa jin mace mai zaƙin yawu kamar Amal ba… tun ranar da ta fito daga gidan ta har zuwa yau, gaba ɗaya ta mamaye tunanina. Sumbata ɗaya ya gamsar da ni, zuciyata ta tsumu… Muradina yanzu shi ne, sumbatarta ko da sau ɗaya… domin idan hankalina ya kwanta, zan iya mallakar ta gaba ɗaya...” Rufe idonsa yayi, lokaci guda tunaninsa ya koma wurin lokacin da suka kasance a baya, lokacin da Amal ta tsinci kanta a hannunsa a cikin dare, sumbatarta ɗaya kawai ya ratsa zuciyarsa kamar wutar lantarki. Ya ji kamar komai ya tsaya cak, zuciyarsa tana taƙaicewa, a hankali yake furta. “Yanzu kullum sai nayi mafarkin Amal… Kullum… Duk lokacin da na kwanta, dole sai na yi mafarki cewa mun zama ma’aurata. Ba zan iya barin tunaninta ya tafi ba, duk lokacin da nayi mafarkin ta dole sai na yi wankan tsarki... please Amal kada ki lalata mun zuciya da tunaninki da mafarkin ki.…” Ya saki dogon numfashi, idanunsa sun yi jawur, yana kallon bango kamar wanda ya tafi dogon tunani mai zurfi. Duk cikin dare, zuciyarsa tana tashi da wani irin salo na ƙaunarta, tana nuna masa irin son da yake yi wa Amal, son da bai taɓa ji a rayuwarsa ba. Ya jingina kansa a bango, idonsa a rufe, yana mai ƙoƙarin kwantar da hankalinsa, amma zuciyarsa ta ƙara tsunduma cikin mafarki da tunanin Amal... Duk dare ɗaya, Zayd yana cikin wannan hali: kewarta, son ta, da kuma tsoro kada wani ya aure ta... 《》《》《》《》 Maleekh ne ya shigo falon gidansu, ya tarar da Ammy ita kaɗai zaune a kujera tana kallon TV. Ya yi murmushi a hankali, ya zauna kusa da ita, idonsa cike da nutsuwa. "Ammy, bazaki ce wani abu akan batun aurena da Amal ba?" Ammy ta ɗan juyar da kai, tana mai shafa hannayenta cikin natsuwa, sannan ta ce: "Maleekh… to mezance? Har cikin zuciyata bana ƙaunar Amal, kuma bazan taɓa kaunarta ba. Amma ba yanda na iya… dole na haƙura ku auri juna. Duk faɗan da yafi ƙarfinka, sai ka mayar shi wasa. A dalilin haka Farha take prison, zumunci ya yanke a tsakanina da ƴan uwana gaba ɗaya. A dalilin Amal kaima ka faɗa hannu har kayi zaman cell a ƙasar da ba naka ba, kullum tashin hankali, kullum damuwa, duk akan wannan yarinya. To tinda haka ne, gwara kawai kuyi auren. Allah ya bada sa'a, ya baku zaman lafiya… Ni bazance komai ba." Maleekh ya sauƙe dogon numfashi, idonsa ya yi ja, ya ɗan jingina kansa a jikin kujera. "Abbah yana son haɗin nan… amma ina bakya jin haushina? Domin banaso ki rinƙa kwana da damuwata." Ammy ta kallesa cikin murmushi mai taushi, ta ce: "Ko kaɗan bana jin haushinka, Maleekh… akan meye to? Nayi maka addu’ar fatan alkhairi." Maleekh ya ɗan murmusa, ya ce: "Shikenan, Ammy… sannan zan gaya miki cewa na sa an fitar da Farha daga prison. Yanzu haka na kaita gidan da iyayenta suke." Ammy ta ɗan yi tsalle cikin farin ciki, idonta na walwali ta ce: "Da gaske Maleekh? Ai kuwa nagode! Zumunci zai dawo. Amma meyasa baka fara kawota nan ba?" Maleekh ya yi shiru, sannan ya ce cikin nutsuwa: "Gwara ta je can kawai… bana son damuwa." Ammy ta ɗan saki murmushi, idonta cike da nishaɗi: "Shikenan, ni zan je gidan nasun na gano ta. Duk da nasan da wuya zumuncin ya dawo kamar da… amma zan je." Maleekh ya kalli Ammy, idonsa na nuna damuwa da kulawa, amma bai faɗa komai ba. Kansa a jingine da kujera, zuciyarsa cike da tunani akan yadda zasu magance halin da Amal take ciki da kuma zaman lafiya a tsakanin su gaba ɗaya..... _NEXT NEXT NEXT_ asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 69 to 70 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Bayan Sati Biyu Hasken rana yana sauƙa a hankali daga taga. Amal tana zaune a kan kujera cikin doguwar riga street gown mai launin pink, jikinta ya nuna alamun samun sauƙi, amma idanuwanta cike yake da damuwa.. Inna itama na zaune a one seater suna kallo. Suna zaune suka ji ƙarar motar da ta tsaya a waje. A zabure Amal ta miƙe tare da leƙa wa ko Maleekh ne. Ganin Abbah ne yasa ta zo ta zauna. Ba'a juma ba sai ga mai gadi ya shigo yana cewa: “Inna, ga Alhaji minister ya iso…” Da sauri Inna ta miƙe tana murmushi, ta fito harabar gidan tana marabtar shi. “A’a Alhaji! Maraba da zuwa..” Abbah yana murmushi ya ce: “Ai inaso nazo amma sai dai aiki ne yake hanani zuwa. Yaya jikin Amal?” Inna ta amsa suka shige babban falo. Amal ta ɗan tashi daga zaune cikin ladabi, ta durƙusa, ta gaishe shi. “Sannu da zuwa Abbah… Allah ya saka da alheri.” Abbah ya ce: “Yauwa ƴata, kin ɗan ƙara kyau. Allah ya ƙara lafiya.” Amal ta ɗan lumshe ido, ta ce cikin muryar da ke nuna damuwa: “Abbah… tun ranar da na farfaɗo daga asibiti ban ƙara ganin Ya Maleekh ba. Sati uku yanzu, bai dawo wurina ba. Lafiyarsa kuwa?” Abbah ya ɗan yi murmushi, yana kallon Inna kafin ya kalli Amal: “Kar ki damu, ƴata. Maleekh ma baya jin daɗin jikinsa ne, shiyasa yake hutu. Amma yana ta kiranki a zuciyarsa.” Amal ta sauƙe numfashi, ta ɗan saki murmushi mai taushi. “Na gode Abbah. Ina roƙon Allah ya bashi lafiya.” Sai aka yi shiru na ƴan daƙiƙu, daga nan Abbah ya gyara zama, ya dubi Inna da nutsuwa: “Inna, abinda ya kawo ni yau kenan. Na zo neman auren Amal ga ɗana Maleekh.” Inna ta ɗan ɗago kai da mamaki, murmushi ya bayyana a fuskarta. “Mashaa Allah, wannan dai albishir ne Alhaji. Ai daman muna jiran wannan ranar. Insha Allahu zan sanar wa ƴan uwan mahaifinta dake Borno, su zo su karɓi auren ta.” Abbah ya yi dariya a hankali, yana girgiza kai: “A’a Inna, ba sai sun zo ba. Mu zamu je da kanmu. Mu ma muna son mu nuna girmamawa da ɗa’a.” Inna ta ce cikin farin ciki: “Wallahi Alhaji wannan magana ta yi kyau. Allah ya daɗa haɗa zumunci, ya tabbatar mana da alkhairi.” Amal tana sauraron su tana wasa da hannunta, hawaye na taruwa a idonta saboda farin ciki. Ta ce cikin muryar da ta cika da godiya: “Abbah… nagode sosai. Allah ya saka da alheri, Allah ya bawa Ya Maleekh lafiya da natsuwa.” Inna ta ce "Ke do Allah yi mana shiru, ke ko kunya bakya ji? Har da wani godiya? Kaiii yaran zamanin nan sun lalace. To a zamanin mu lokacin da za'a zo neman auren ka ma guduwa kake, kuma har ayi aure yarinya bazata yadda ta haɗa ido da miji ba balle uban miji..." Abbah ya yi murmushi mai ɗan taushi, yana kallon Amal da Inna cikin kulawa. “Amin ƴata. Insha Allahu komai zai tafi lafiya. Ki cigaba da hutawa, komai zai tabbata a lokaci mafi kyau.” Bayan tattaunawa da Abbah akan aure Inna ta lumshe ido tana kallon Abbah, muryarta ta ɗan canza cikin nutsuwa da tausayawa ta ce “Dan Allah Alhaji … ga amanar Amatu. Domin kai mahaifi ne a wurinta, kuma bazaka so wani abu ya cutar da ita ba. Kaima me karɓa mata aure ne a wani wuri… hakika kai aminin mahaifinta ne, kuma ɗan hannun damansa. Ban manta da kai ba tun daga lokacin da muka fara ganawa.” Ta ɗan yi shiru, hawaye suna taruwa a idonta ta cigaba da cewa. “Nasan kai ma ka shaida ni, ko da yake shekaru sun ja kafin mu sake haɗuwa.” Abbah ya tsaya yana kallonta, numfashinsa ya ɗan yi nauyi. Guntun hawaye ya zubo masa, ya share cikin natsuwa. “Tabbas Mama… ni ma ban manta ba. Amma bansan me yasa kika ɓoye kanki ba. Ganinki a haka, baki bayyana cewa kin sanni ba, yasa nima ban nuna hakan ba saboda ban san dalilinki ba. A tunani na gobarar da ta cinye abokina, wato mahaifin Amal da matarsa… har da ke a ciki, shi ne ya sa na shiga ruɗani. Ganinku a raye yasa na shiga tunani… Ikon Allah kenan.” Inna ta juyo da murmushi mai raɗaɗi, ta ce cikin sautin da ya haɗa baƙin ciki da natsuwa: “Yanzu kai ka yadda cewa ɗana abokinka da matarsa Khadija gobara ce haka kawai ta cinye su?” Abbah ya girgiza kai a hankali, yana duban Amal da ke gefe tana sauraro cike da mamaki sannan ya furta. “A’a Mama, ban yadda ba gaba ɗaya… amma babu hujja da zata tabbatar min da an sa musu gobara da gangan. Amma ki gaya min, meye silar mutuwar su? Har aka sa musu gobara?” Inna ta ɗan lumshe ido, ta saki guntun murmushi mai nuni da sirri. “Zamuyi maganar daga baya Alhaji … ba yanzu ba.” Sai aka yi shiru na daƙiƙu. Abbah ya ɗan kalli Amal, ya ce cikin muryar tausayi: “Amal, my daughter… ke baki gane ni ba ko?” Amal ta ɗago kai, idonta cike da hawaye ta ce, cikin rawar murya: “Abbah… na daɗe da ganeka. Tun lokacin da na gane Ya Maleekh shine Leekh ɗina na yarinta… amma shi har yanzu bai gane ni ba.” Abbah ya ɗan yi murmushi, yana kallonta cikin ƙauna. “Allah sarki daughter… wato baki manta Maleekh ɗinki ba kenan. Gashi, ikon Allah, kun sake haɗuwa da shi. Gaskiya, ya kamata shima Maleekh ya gane ki, yasan cewa ke ce yarinyar da yake tare da ita tun ƙuruciya, fiancé ɗinsa tun yarinta.” Amal ta share hawayen da suka sauƙo a kumatunta, ta ce cikin dariya: “A’a Abbah, dan Allah, kar ka gaya masa yanzu. So nake sai ya aure ni kafin nayi masa wannan albishir. Na tabbata idan ya sani kafin aure… to ba irin farin cikin da nake zato zai yi ba.” Abbah ya saki murmushi mai taushi, yana girgiza kai: “Wannan babban albishir ne a wajensa. Akoda yaushe, burin Maleekh kenan ya sake haɗuwa da masoyiyarsa ta yarinta. Allah ya tabbatar da hakan da alkhairi, ƴata.” Amal ta yi dariya, tare da faɗin “Amin Abbah, Allah ya saka da alheri.” Inna ta tashi tana fatan alkhairi, ta kalli Abbah: “Allah ya daɗa haɗa zumunci, Alhaji. Mun gode sosai da kulawa.” Abbah ya miƙe, sannan ya kalli Amal da murmushi mai cike da natsuwa. “Sai mun sake ganawa, ƴata. Ki kula da kanki sosai.” Yana fita, Amal ta zauna ta jingina da kujera, tana lumshe ido cikin tunani mai daɗi da fargaba a lokaci guda, ta tabbata lokaci ne da sirrinta zai bayyana nan ba da jimawa ba.. Da daddare misalin ƙarfe 11 Ƙamshin turaren “oud” ya cika ɗakin, sai ƙarar agogo da ke danna lokaci a hankali kamar yana bin bugun zuciyarta. Amal ta zauna a gaban taga, hannunta ɗauke da ƙaramin photo. Tana kallon shi, hoton da suka ɗauka da Maleekh tun suna yara, ita sanye da uniform ɗin primary, shi kuma yana sanye da uniform ɗin junior. Ta riƙe hoton sosai a kirjinta, hawaye na taruwa a idanunta, ta furta cikin sanyi: “Ya Allah… wannan shi ne Leekh ɗina…” Numfashinta ya ɗan ɗaure, ta jingina da bango tana kallon sama. Sai tunanin baya ya fara dawowa cikin kwakwalwarta kamar fim. Flashback, shekaru goma sha takwas da suka shuɗe Da yamma a cikin gidan su Maleekh, yara suna wasa a tsakar gida. Amal ƙarama ce, ƙarama sosai tana sanye da doguwar riga na kanty, ta ɗaure gashin kanta da rivon. Shi kuma Maleekh, ɗan shekara goma sha uku, murmushi da wasa ba su gushe daga fuskarsa ba. Yana dariya tare da faɗin: “Ke Amatu, ki tsaya ki gani zan iya rubuta sunanki da ƙasa!” Amal ta ce: “Ai ban yarda ba! Yanda baka iya rubutu sosai ba, zaka ɓata min suna.” Maleekh ya ce: “Ki kalli nan!” Ya ɗauki sanda ya rubuta a ƙasa “A + M = ❤️”, sai ya kalleta yana murmushi. “Gashi nan, A Amal, M Maleekh. Idan mun girma, za mu zama A + M na gaskiya, babu wanda zai raba mu.” Amal ta riƙe hannunsa tana dariya, ta ce: “Ka yi alkawari? Wallahi idan ka manta, zan faɗa wa Ammy da Mommy.” Ya ɗan yi dariya yana riƙe da hannunta sosai: “Na yi alkawari, Amatu. In na girma, sai na aure ki.” A gefe kuwa, iyayensu suna kallonsu da murmushi. Abbah da mahaifin Amal suna ta dariya suna cewa: “Wannan yarinyar taka ta zama tamkar gold a wurin Maleekh. In Allah ya yarda, idan sun girma, sai na haɗa su aure.” A cewa Mahaifin Amal... Haka nan aka ɗaura soyayya a kalma ɗaya amma ƙaddara bata bari ba... Ranar gobarar bata manta ba. Wuta ta tashi a gidan su Amal, Inna ta rungume ta tana gudu cikin duhu, ita kuwa tana kuka tana ƙiran sunan mahaifinta da mahaifiyarta. > “Mommyyy! Daddy!!!” Amma babu wanda ya amsa. Daga wannan rana, komai ya ɓace rayuwa ta canza, ƙauna ta rabu hanya biyu. Ta tashi a cikin wani sabon gari, sabon suna, sabon rayuwa. Babu Maleekh, babu Mommy, babu Daddy....... Koma wa ga yanzu Amal ta share hawayenta da hannunta, tana kallon hoton da ke hannunta. “Kai ne ka ce zaka dawo, ka aure ni… amma yanzu kana gabana, baka ma gane ni ba.” Ta ɗauki biro ta buɗe littafinta na rubutu, ta fara zana haruffan sunansa da nata a jere: A + M = ❤️ Sai ta lumshe ido, ta murmusa cikin zafin kewar soyayya: “Ko da bai gane ni ba, zuciyarsa zata tuna… zuciyarsa dole ta tuna da Amatu ɗinsa.” A hankali ta jingina kanta a bango, tana jin hawaye suna zuba amma wannan hawaye ba na baƙin ciki bane gaba ɗaya, akwai ɗan farin cikin tunawa da soyayyar da ƙaddara zata sake haɗa ta da ita a sabon zamani... Kamar yadda ta kasa bacci a wannan daren tana tunanin Maleekh. Shima a ɓangarensa. Maleekh yana zaune cikin ɗakinsa. Ɗakin da yake cike da hutu da tsari, amma a yau wani irin shiru ne ya lulluɓe shi. Ya jingina da kujera, yana kallon wani ƙaramin agogon yara da ya jima yana boyewa cikin drawer, agogon da ya rasa dalilin da yasa bai iya jefar da shi ba, duk da shekaru da suka wuce. Yanzu haka yana riƙe da shi a tafin hannunsa, yana juya shi cikin nutsuwa. Wani sanyi yana ratsar masa jiki, kamar ana busa masa iska daga wani wuri mai nisa. Ya tuna lokacin da yake zuwa junior Amal ta sanya masa agogon, duk san da yaje school da shi sai an masa dariya da cewa “Agogon yara ka sa!” Amma har zuwa yanzu ya kasa rabuwa da shi, saboda ƙaramar yarinya ce ta bashi shi. Yarinya mai fara’a, mai murmushi irin wanda yake gyara dukkanin ranarsa, amma kamanninta ya ɓace daga zuciyarsa… Sai dai hoto da ƙamshi ne kawai suka rage masa a tunani... Ya furta cikin natsuwa, muryarsa yana raɗa tamkar yana magana da iska: “Wani lokaci ina jin kamar zuciyata na sanar mun cewa zata dawo gare ni... Domin a zuciya na, na san akwai wadda na taɓa yiwa alƙawarin aure, amma wata zuciyar na sanar mun cewa ta mutu...” Ya lumshe idanu, yana jin wani irin nauyi a ƙirjinsa irin ƙiran da zuciya ke yiwa ɗayan zuciyar ba tare da kalma ba. A daidai wannan lokacin, a can nesa Amal ma ta lumshe idanu tana tunani. Zuciyarta na bugawa da irin sautin da yake kama da wanda yake buga a kirjin Maleekh. Ba su san suna magana da juna ba, amma ruhohinsu sun haɗu. Kamar iska da ruwa, kamar haske da inuwa kowanne yana jin ɗayan.. Iska ta ɗan motsa labulen tagar ɗakin Maleekh, agogon ya yi ƙara “tik… tik… tik…” kamar yana tuna masa da wani alƙawari da bai cika ba. Ya ɗaga agogon zuwa fuska, yana kallonsa da murmushi mai raɗaɗi. “Kina so na manta ki ne?” ya furta a hankali. “Meyasa bazaki dawo gareni ba? Duk da kina zuciyata amma zan sanar miki cewa zanyi aure, zan aure macen da take mun kama da ke....” Cikin wannan tunanin bacci ya ɗauke shi.. 《》《》《》 Washegari da safe, hasken rana yana ratsa gilashin window ɗin babban office ɗin CashTalk. Maleekh yana zaune a kujerarsa mai juyawa, ya jingina da baya, yana kallon taga amma zuciyarsa tana nesa, cikin duniyar da ba ta da suna.. Sai kawai ƙofar office ɗin ta buɗe da ƙarar “click”, sectaria ta shigo cikin ladabi. Tana riƙe da wata envelope, ta ce da muryar kasaita: “Sir, wannan wata ce mai nikab ta kawo, tace in baka yanzu yanzu. Ta tafi kafin in tambaye ta komai.” Maleekh ya ɗan ɗaga kansa cikin mamaki, ya karɓi letter ɗin. Ya ɗauki biro, ya tsinke envelope ɗin a hankali amma bayan ya fara karantawa, zuciyarsa ta buga! A cikin letter ɗin aka rubuta: *Assalamu alaikum masoyina na yarinta, fiance ɗinka ce me magana bayan tsawon lokaci. Naji ance zakayi aure, to kar ka manta da alkawarinmu tun yarinta. Iyayenmu sun yi mana alƙawarin aure, kuma akwai soyayya mai zurfi a tsakaninmu. Idan kayi aure ka auri wata ba ni ba, ka sani ka ci amana, kuma Allah ba zai barka ba. Ina bibiyarka akoda yaushe. Kada ka damu da ganina yanzu, akwai lokaci zan bayyana maka kaina, kuma zamu cika burinmu na aure. Nidai kamun alkawarin, bazaka auri wata ba, in ba ni ba... Daga masoyiyarka, your fiancee… 💌* Bayan ya kai ƙarshe, letter ta sulale daga hannunsa, idonsa a zazzare. Numfashinsa ya ɗan tsaya na ɗan lokaci, kamar wanda aka tsayar da lokaci a jikinsa. Ya miƙe cikin razana, ya fita da gudu daga office, har zuwa harabar campany... Ya fara magana cikin ruɗani: “Ina take?! Ina fiancee ɗina?! Ina take?! Meyasa baku riƙe ta ba lokacin da ta kawo saƙon?!” Ma’aikata suka tsaya suna kallonsa da mamaki. domin ba su taɓa ganin CEO dinsu cikin wannan yanayi ba. Daidai wannan lokacin, Amal ta iso, ta sauƙa daga napep, Ta dawo wurin aikinta tunda jikinta ya fara sauƙi bayan hatsarin motarta. Ganin Maleekh cikin wannan halin yasa ta ƙarasa da sauri cikin damuwa ta ce: “Ya Maleekh, lafiya kuwa? Meyake faruwa ne haka?” Maleekh ya juyo cikin hargitsi, idonsa ya cika da hawaye. Ya ce cikin rawar murya: “Rayuwata ce tazo har nan campany, ta aiko mun da letter amma na rasa ta! Na rasa fiancée ɗina!” Ya dafe goshinsa yana girgiza kai kamar wanda ya rasa fahimta. Amal cikin mamaki ta ce: “Rayuwarka kuma?...” Cikin ƙarfi da tashin hankali ya juyo yana fadin: “Eh rayuwata! Fiancee ɗina ce tazo! Wacce na daɗe ina jiran dawowarta! Wanda aka ɗaura alkawari tsakanina da ita tun muna yara!” Maganar ta fito daga bakinsa kamar ƙara, Ma’aikata suka yi shiru kowa kallon kowa. Wasu suka riƙe baki, wasu suka ɗauke kai. Amal ta tsaya cak! Idonta ya cika da hawaye. Zuciyarta na bugawa da sauri, kamar ana murza mata wuta a cikin ƙirjinta. Tayi tunani cikin zuciyarta: “To wacece wannan ‘fiancée’ ɗinsa bayan ni?.. Ni ce fa fiancée ɗinsa tun yarinta! Amma ban gaya masa ba har yanzu... Wacece zata rubuta masa letter ta yi amfani da sunana domin ta rikita shi?...” Amal ta ce da rawar murya: “Ya Maleekh… ni ce… ni ce” Amma kafin ta gama, Maleekh ya ɗaga mata hannu cikin takaici, idonsa a ƙasa, bai bari ta ƙara magana ba. “Ki bar ni Amal, bana cikin hayyacina yanzu… don Allah ki barni.” Ya juya, ya nufi mota, yana share gumin goshinsa cikin tashin hankali. Amal ta tsaya cak a wajen, tana kallon bayansa da hawaye masu zafi. Sai ta juyo da hankali cikin natsuwa, ta shige reception kai tsaye elevator ta shige ta kaita sama, tana fita ta nufi office ɗinta, ta kulle ƙofa, ta kifa kanta akan table tana kuka... “Har yau, har yanzu baya iya kallona da soyayya… me na masa ne haka?, ya canza mun, baya ganina a matsayin masoyiyarsa…” Cikin shiru Amal ke zaune a office ɗinta, tana kuka kamar yarinya da ta rasa uwa. Hawayenta na sauƙa a kan takardun da ke kan tebur, zuciyarta na murɗawa da zafin kalaman Maleekh. Sai kawai taji ƙofar ta buɗe a hankali. Tayi zaton wata ma’aikaciya ce, saboda haka bata ɗago ba. Sai kawai ta jiyo wata muryar da ta dasa mata tsoro da farin ciki lokaci guda. “Meye dalilin kukan?...” Tayi saurin ɗago kai. Idonta ya haɗu da na Maleekh, yana tsaye a bakin ƙofa, hannuwansa a aljihun wandonsa, yana kallonta da ido masu cike da raunin zuciya. Zuciyarta na bugawa.. Ware mata hannu yayi, ya furta a hankali: “Zo nan…” Kamar wacce aka ja da ƙarfi, Amal ta miƙe da sauri, ta ƙarasa da gudu ta faɗa ƙirjinsa. Ta kwantar da kanta a kirjinsa tana kuka sosai. Maleekh yana shafa bayanta a hankali. “Na ce meye dalilin kukan haka?” Amal cikin rawar murya ta ce: “Saboda kai… saboda kalamanka, saboda ina jin kamar kana ƙaunar wata fiye da ni…” Ya ɗan yi murmushi cikin gajiyar zuciya, ya ɗago fuskarta da hannunsa biyu, ya kalle ta kai-tsaye cikin ido. “Amal… kar ki sake kuka saboda haka. Zan aure ki. Amma ki sani idan fiancé ɗina ta bayyana… dole sai na aure ta itama. Domin ni ɗaya aka halicce ta, haka ma ita ɗaya aka halicce ni. Amma saboda ke, saboda ba zan iya rayuwa ba tare da ke ba… zan aure ki kafin ta bayyana.” Amal ta tsaya tana kallonsa, zuciyarta tana bugawa da zafi da farin ciki a lokaci guda. Tana so ta ce masa ni ce fiancé ɗinka, amma ta kasa. Zuciyarta ta ce “a bari lokaci ya nuna masa gaskiya.” Da murmushi mai zafi ta ce cikin ƙaramar murya: “Na amince… tunda kai ne, ko mai zaka faɗa zan yarda.” Maleekh ya ɗan murmusa, yana jin yadda kalamanta suka rage masa nauyin zuciya. Ya ce: “Na gode Amal. Kiyi haƙuri da komai, rayuwa ce ta jirkita mana abubuwa. Amma na tabbata alkawarin da na miki zan cika shi.” “Wani alkawari?” ta tambaya tana kallonsa da murmushi. “Alkawarin cewa bazan taɓa watsar da ke ba… ko mai zai faru, komai zaki zama.” Kalaman sun sosa mata zuciya. Ta yi dariya cikin hawaye. “Na yarda, Ya Maleekh…” Suka ɗanyi shiru. Sai hancin ta da yake shakar ƙamshin turarensa, da bugun zuciyarsa da ke dukan kunnenta. Ya zaro envelope daga aljihunsa, ya miƙa mata cikin nutsuwa. “Ga invitation card ɗin bikin… next week. Ke ce amaryata, ki shirya, ki zamo matar CEO...” Amal ta karɓa da hannuwa biyu, tana kallon rubutun da ke jikin card ɗin. “Wedding Ceremony of Maleekh Abdul-Majeed & Amal Abdulsamaad ” Ta fashe da dariyar farin ciki mai haɗe da hawaye. “Bayan wahala… sai farin ciki.” Maleekh ya ce yana kallonta da murmushi mai taushi: “Ko me zai faru, karki sake barin wani ya share miki wannan murmushi.” Ta ɗaga kai ta ce: “Sai kai ne kawai zaka share mun hawayena.” Ya ɗan ɗago habarta da yatsansa, ya ce: “Da izinin Allah…” Suka yi shiru. Sai A.C da ke busa cikin Office... 《》《》《》《》 Farha ta shigo falon da idanu jajawur, tana busar da numfashi. “Yaya… dan Allah… kada ka sake sakani a cikin wannan masifar. Indai akan Maleekh da Amal ce, ni babu ruwana a ciki. Ka barsu suyi auren su, ka bar komai ya tafi cikin tsari.” Zayd ya ɗago kai a hankali, muryarsa ta yi sanyi ya ce “Yanzu kenan Farha… kin haƙura da Maleekh? Bayan duk abinda kika ce min, kin daina son shi haka kawai?” Farha ta kalli gefe tana share hawaye. “Na haƙura, Yaya. Wallahi na haƙura da shi. Wannan soyayyar bata da amfani gare ni. Ban ga dalilin da zai sa mu ƙara cin mutuncin mutane saboda kishin da babu amfanin shi ba.” Zayd ya ajiye da gilashin ruwan, ya jingina da kujera. “To, shi kenan ke kin haƙura… amma ni Farha, bazan haƙura ba. Bazan haƙura da Amal ba. Ta rusa mun duk masarautar zuciyata, ta mayar da ni kamar wani ba shi da daraja… kuma bazan bar komai haka kawai ba.” Farha ta juya da sauri tana kallonsa da fargaba. “Yaya! Me kake nufi? Har yanzu baka gane cewa Allah ne ya haɗa wannan auren ba? Ka bar komai zuwa ga Allah, kada ka ƙara lalata rayuwarka saboda ta Amal! Ga mata kala-kala sai ka zaɓa” Zayd: ya yi dariya mai taurin gaske sannan ya ce. “Kin manta da kalmar da ki ka faɗa Farha? ‘Auren Amal da Maleekh bazai taɓa yiwuwa ba’. Kin manta ke kika fara taimaka wajen rushe komai? To yanzu kin dawo kina nuna tausayi kenan?” Farha: ta durƙusa kusa da ƙafarsa, tana magana cikin tausayawa. “Yaya, don Allah ka saurare ni. Na yi kuskure, na shiga abin da bai kamata ba. Amma yanzu na gane kuskurena. Yau zan je gidansu Amal na nemi yafiyarta. Indai har ni ce sanadin rikicin da ya lalata rayuwarsu, zan roƙi Allah ya gyara tsakanin mu.” Zayd ya zuba mata idanu, yana tauna lebensa, bai ce komai ba. Farha ta ci gaba da magana cikin murya mai rauni. “Yaya, Ammy tana son ka auri Islam, ‘yarta. Ka bar Amal ta zauna da wacce zuciyarta ke so. Kada ka ƙara ninka zunubi da makirci akan rayuwarta…” Zayd ya dafa hannuwansa a goshi, yana furta cikin muryar da ke ƙunshe da ɓacin rai “Farha… kin yi rauni sosai. Kina ganin zaki iya zuwa wurinta yau, ki nemi yafiya, kamar babu abin da ya faru? Kina ganin haka zai goge komai?” Farha ta kalle shi cikin nutsuwa. “Eh Yaya. Domin babu wanda yake girma akan kuskure. Amma kai zaka ci gaba da rayuwa cikin ƙiyayya ne? Zaka dinga jin zafi a duk lokacin da ka ji sunanta ne? Ka bar komai da Allah, don ni wallahi na gaji da wannan makirci.” Zayd ya kalli ƙasa, yayi shiru na ɗan lokaci. Sai ya ce a hankali “Farha… idan kin je wurinta… kada ki faɗi komai game da ni.” Farha ta ɗan murmusa cikin tausayi sannan ta ce “Na sani. Ba zan faɗa ba. Amma ina roƙonka da ka sake zuciyarka, Yaya. Kada wannan soyayyar ta lalata maka rayuwarka gaba ɗaya.” Zayd ya kalleta sannan ya ce. “Ki tafi Farha. Amma ki sani… wannan labarin bai ƙare ba.” Farha ta miƙe, ta fita daga falon cikin nutsuwa, tana addu’a a zuciyarta: “Ya Allah, Ka kawo ƙarshen wannan fitina cikin salama.” Zayd ya rage hasken fitila, ya jingina da kujera yana kallon duhu, alamar zuciyarsa bata cikin natsuwa... Dab da mangariba sai ga Farha ta iso gidansu Amal, bayan Mai gadi ya tabbatar da bada tashin hankali tazo ba, ya buɗe mata ta shige.. Inna tana zaune ita kaɗai a falo, ganin Farha yasa ta zabura tana kallonta, lokaci guda ta ɗaure fuska cike da fushi, ta ce. “Daga fitowarki a prison har kin dawo neman bala’i? Saboda kinji wannan satin bikin masoyan ko?!” Farha ta durƙusa cikin ladabi, tana sanye da dogon hijabi, fuskarta cike da tawali’u.. “Inna ina wuni… dan Allah kiyi haƙuri, ban zo da wata fitina ba.” Inna bata ce komai ba, ta juya gefe da ɗan tsaki. Kafin su ƙarasa magana, sai ga Amal ta sauƙo daga bene tana riƙe da glass cup na juice. Idonta ya sauƙa akan Farha, cike da mamaki ta tsaya cak, muryarta cike da mamaki. “Laa Farha kece?!” Farha ta miƙe daga tsugunonta cikin sauri, zuciyarta kamar zata burtso. Ta ƙarasa wurin Amal ta rungumeta da hawaye a fuskarta.. “Amal… na yi kuskure. Na zo ne da zuciya ɗaya. Dan Allah ki yafe mun…” Amal ta tsaya cak, hannunta a bayanta, tana kallon Farha cikin mamaki. Inna kuwa tana zaune a hankali tana kallonsu, har yanzu bata ce komai ba. Amal a hankali ta furta. “Ki zauna Farha…” Suka zauna a kan kujera guda, Inna na kallonsu. Amal ta ɗan murmusa cikin natsuwa.. “Ki kwantar da hankalinki, komai ya wuce Farha…. " Farha ta share hawayenta sannan ta ce. “Na gode Amal. Wallahi na zo da niyyar samun yafiyarki. Abinda nayi miki bai dace ba. Na ɓata miki suna, na jefa ki cikin tozarci. Amma yanzu na tuba, na daina, na kuma haƙura da Yaya Maleekh. Ina muku fatan alkhairi da zaman lafiya.” Amal ta ɗan murmusa. “Ki daina kuka. Komai ya wuce, ki cire ranki akan abin da ya faru. Allah ya saka da alheri.” Farha ta ɗan duƙa kai, tana kallon ƙasi ta ce. “Amal… jiya ina so in faɗa miki gaskiya. Bazan ɓoye ba, nice na aikawa Yaya Maleekh da letter cewa fiancée ɗinsa ce…” Amal ta ɗan buɗe baki da mamaki ta ce. “Amma… ina kika san fiancée ɗinsa?” Farha ta girgiza kai sannan ta ce. “Ban santa ba. Yayana ne Zayd ya bani labarin wata first love ɗin Yaya Maleekh tun suna yara. Ya ce sun rabu lokaci guda, kuma tun daga lokacin bai ƙara ganin ta ba. Shine ya bani shawara na rubuta cewa ni ce fiancée ɗinsa, in ce kada ya auri kowa saboda har yanzu tana raye tana jira…” Ta yi shiru, ta share hawayenta sannan ta ƙara magana da cewa. “Yaya Zayd ya ce, a duniya babu macen da Yaya Maleekh yake so kamar fiancée ɗinsa, har ya ce ko Amal ba zata kai fiancée a wurinsa ba…” Inna wacce ta saurare su ta girgiza kai, muryarta ta sauya cikin nutsuwa mai haɗe da tausayawa..Ta ce “Farha… fiash (fiancée)ɗin da kike magana akanta... ita ce Amatu.” Farha ta kalli Amal da mamaki ta ce. “Ban gane ba…” Inna ta soma magana cikin zafin rai da ƙarfi, “Ai Amatu ce fiash ɗinsa tun yarinta! Maleekh da Amal sun daɗe da alkawarin soyayya, sannan sun sha bambanci na ƙaddara amma soyayyarsu ta ci gaba da numfashi har yau!.. A lokacin tana ƙarama ce sosai, shekara biyar kacal a duniya, amma ta riga ta saba da Maleekh. Shi kuwa yana da shekara goma sha uku, ɗan saurayi mai wayo da murmushi wanda yake burge kowa. Sun taso tare tamkar ‘yan uwa, saboda iyayensu abokai ne na ƙud da ƙud, musamman mahaifiyar Maleekh da mahaifiyar Amal kawaye ne, aminan juna da ke yin komai tare. Ko da yake Maleekh ya girme ta da shekaru takwas, shi ne mai bata dariya, mai kora mata karnuka idan ta tsokano su, mai bata lemo da sweet idan ta yi kuka. A gidansu Amal ake yawanci samun su suna wasa, wani lokaci kuma sukan koma gidansu Maleekh. Har ma iyayensu suka saba da cewa, “Ku dai idan kun girma, aure zamu muku, ku zama daya har abada.” Wannan magana tana nan cikin zuciyar Amal kamar alƙawari mai tsarki. Ta yi imani cewa da zarar ta girma, shi ne mijinta, shi ne abokin rayuwarta. Sai dai rayuwa ta juyo da wata fuska. Wata rana da dare, gidan su Amal ya kama da wuta. Gobara ta cinye komai mahaifiyarta, mahaifinta… komai ya ƙone. Sai ni ce nazo da gudu na ɗauke ta muka tsere cikin duhu, muna kuka, muna neman mafaka. Tun daga wannan rana Amal bata sake ganin Maleekh ba, bata sake jin labarinsa ba... Amma a zuciyarta, tana rayuwa da hotonsa, ƙaramin yaro mai murmushi, wanda yake saka zuciyarta jin daɗi. Hotonsa ta riƙe har zuwa yanzu, wanda ta gani cikin wani tsohon jakar makarantarta... Irin wannan hoton ta gani cikin ɗakinsa a manne ita da shi, shi ne ya tabbatar mata wannan ne Maleekh nata… A yau kuma, shi ne mutum ɗaya da zuciyarta ke bugawa saboda shi..." Farha ta sake baki tana kallonsu cike da mamaki, ta ce "Amma me yasa bai gane ta ba? Me yasa har yanzu yake kallonta kamar ba su taɓa sanin juna ba?..." Amal ta lumshe idanu tana sauƙe ajiyar zuciya mai raɗaɗi. Ta ɗan murmusa cikin ɓacin rai. “Rayuwa… tana da ban mamaki,” ta furta a hankali. “Mutumin da aka rubuta a zuciyata tun ina ƙarama, yau yana gabana amma bai san ni ba.” Farha ta riƙe hannunta, idanu a cike da hawaye ta ce. “Subhanallah… amma ai da kun sanar da shi da wuri!…” Amal ta ɗago kai cikin mamaki da shiru mai cike da tsoro da farin ciki lokaci guda. Zuciyarta ta yi wani irin nauyi. “Maleekh…” ta maimaita a cikin zuciya, “ko da bai gane ni ba, ƙaddara ta dawo da mu.” Ta ɗan kalli Inna sannan ta ce cikin nutsuwa.. “Inna, mu bar komai haka. Farha, ki min alkawarin kar kowa ya ji wannan magana. Iya ke kaɗai ce yanzu kika san cewa ni ce fiancée ɗin Maleekh.” Farha ta ɗago hannayenta sama ta ɗora akan Amal sannan ta ce. “Nayi miki alkawari Amal. Wallahi ba zan faɗa wa kowa ba. Wannan sirri ne a tsakaninmu.” Yanayin ya sauya daga damuwa zuwa fara’a. Inna ta ɗan sake fuska, Amal ta yi murmushi... Farha ta share hawayenta cikin dariya ta ce. “To, yanzu bari mu koma magana ta bikin. Ya labarin anko ne? Don naga ana ta shiri sosai.” Amal ta yi dariya cikin salo. “Ku ai a ɓangaren maza kuke, ni kuma ban da wasu kawaye balle nayi maganar anko…” Farha ta kwaɗaita idanu sannan ta ce. “Da ke kawai za’a iya yin anko fa! Ni zan miki odar ankon daga Dubai, ko ya kika gani?” Amal ta yi murmushi, ta dafa kafaɗarta ta ce. “Ki bar wannan sai gobe, zan gaya miki irin launin da nake so. Yau dai naji daɗin ganinki.” Farha ta ɗan miƙe da murmushi itama ta ce. “Ni ma Amal. Na gode da yafiya, Allah ya albarkaci bikin ku.” Ta rungumi Amal a karo na ƙarshe. Inna ta ɗan amsa mata da murmushi mai nauyi, sannan ta rakata har ƙofar get. Lokacin da Farha ta tafi, Inna ta juya ta kalli Amal da nutsuwa, tace: “Kin ga yadda komai yake dawowa daidai. Allah yana da tafarkin sa.” Amal ta yi shiru tana kallon ƙofar da Farha ta fita. “Eh Inna… amma har yanzu zuciyata tana jin tsoron abinda ke tafe.”... Farha tana cikin motarta zuwa gida.. Sai tunani take tayi akan maganar da taji iyayenta suke akai, cewar "za'a kashe Amal. Sannan su sukayi silar hatsarin Amal, to meyasa suke neman rayuwarta?..." Wannan tambayoyin sun tsaya mata a rai.. _NEXT NEXT NEXT_ asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 71 to 72 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Ranar Alhamis da safe a gidansu Maleekh. Ranar ta fara da motsin ma’aikata, sautin “sweep! sweep!” na tsabtace gidan yana tashi a ko’ina. Gaba ɗaya gidan ya canza kalar sa, ga sabon fenti ya ratsa bango. A jikin bango an rataye hoton Maleekh da Amal, wanda aka tsara cikin kwali mai tsada, an rubuta a ƙasa: “Forever Begins Here A&M.” Sabbin kayan alatu daga Dubai sun cika falon. Kujeru masu launin royal blue, tagogi sun ɗauki labulen silk masu sheƙi, ƙamshin turaren oud yana yawo har ƙofar shiga. A waje, ana gyaran lambu. Ƙamshin furanni na tashi, ga murya ta masu gyara suna dariya da raha..kowa da farin ciki akan fuskarsa. A gefe, ana ɗora manyan fitilu masu walƙiya crystal chandeliers waɗanda zasu haskaka gidan.. A cikin babban falo, Maleekh yana tsaye a bakin window yana kallon aikin. Ya zura hannuwansa cikin aljihun wando, idanunsa a kan yanayin gidan yana tunanin Amal. A hankali, murmushi ya suɓuce masa. “Ko gidan ma ya fahimci farin cikin da zuciyata take ciki…” Ya faɗa a hankali, yana shakar ƙamshin sabon fenti. Gidansu Amal kuwa, ya koma aljanna ta mutane. Daga ƙofar shiga har cikin tsakar gida, an yi ado da furen gwangwani, fitilun string lights suna walƙiya kamar taurari. Ƴan uwan mahaifinta daga Borno sun iso, suna ta dariya da raha cikin ƙayatattun kaya. Ƴan uwan mahaifiyarta daga ƙauyen Kaduna suma sun iso, wasu suna kitchen suna dafa girki, wasu suna gyara falo, wasu kuma suna saka kayan ado. An saka sabon carpet, an canza labule zuwa pink and silver launin da Amal tafi so. Daga sama har ƙasa gidan yana sheƙi. Ana ta shirya turaren wuta, ga ƙamshi ta ko ina, an haɗa wa Amarya wasu arnar turaruka na jiki dana wanka dana ɗaki dana kaya dana gaban mace, su almisk da sauran su dake ƴan uwan mahaifinta daga Borno duk ƴan shuwa ne.... Ga kayan lefen da aka kawo daga gidansu Maleekh da kayan ɗaki... A ɗaya sashen, Amal tana tsaye a gaban mirror tana kallo, tana murmushi cike da nauyin zuciya. Ta taɓa fuskar ta a hankali. “Wannan ce ni?... fiancée ɗinsa tun yarinta...” Ta faɗa a hankali, muryarta kamar sirri.. Sai kawai ta ji Inna daga ƙasa tana faɗin: “Amatu! Ki sauƙo ki gani, ƴan uwan mijinki sun kawo kayan lefe ɗin Dubai!” Da gudu Amal ta sauƙo. Kayan lefen sun cika babban falo, akwatuna masu launi, wasu gold-plated, wasu rose pink, wasu silver diamond design. Daga cikin akwatunan akwai turaren jiki, kayan kwalliya, riguna, takalma, jewelries, hijabai, kayan sallah, kayan kwanciya. komai sabo daga Dubai. Ni kaina bazan iya misalta yawan kayan ba.. Ƴan uwa suna tafa hannu suna yaba wa kyawun kayan.. “Wallahi Maleekh yayi ƙoƙari sosai!” wata daga cikin dangin tace da dariya. “Ai Amal ta same shi a sa’a,” wata kuma ta ƙara. Inna ta yi murmushi kawai tana kallon jikarta, hawaye na farin ciki suna shirin zubo mata.. Abin da ba kowa ya sani ba shine gaba ɗaya Maleekh ya saka CCTV a gidansu Amal, daga ciki har waje. Yana kallon ta a gida, yana lura da komai cikin sirri. Yana ganin yadda take murmushi, yadda take tafiya, har yadda take gaishe da mutane. Wani lokaci yakan tsayar da bidiyon ya ƙara kallon fuskar ta yana murmushi. “Ni da ke mun wuce nisan duniya, Amal…” Ya faɗa cikin lumshe ido, yana jin wani irin nutsuwa ta ratsa shi. A wannan ranar da daddare za'a gudanar da waliman aure.. Rana ta fara faɗuwa, hasken rana ya dushe. Gidansu Amal yana cike da hayaniya, dariya da nishadi. Ƴan uwa suna ta ɗora shirin walima, masu kwalliya suna yi, masu saka kayan walima, Inna tana tsara jeren kayan lefe.. Amal tana tsaye a jikin tagar ɗakinta, tana kallon sararin sama, zuciyarta na bugawa da jin daɗi da shakku lokaci guda. Ta ɗago hannunta ta murza zoben da Maleekh ya sanya mata lokacin da suka samu matsala a kaduna.. “Gobe fa za a ɗaura auren…” Ta faɗa a hankali. Sai murmushi ya suɓuce mata amma a cikin murmushin akwai ƙanƙanin hawaye.. Gidan da Maleekh ya kera domin Amal, ya zama abin da ake kallo kamar aljannar duniya. Yana cikin unguwa ta manyan mutane, inda kowane gida yake da bango mai tsayi, fitilu masu sheƙi, da ƙofar wuta mai sarrafa kanta. Gidan Amal ya fi yawancin sauran tsari da kyau sabuwar ƙira ce ta zamani, storey building mai parts uku: Part ɗin Amarya da Ango Part ɗin baƙi masu ziyara Sai Garden Area da aka tanadar don walima.. Wurin da za'a gudanar da walima. Hasken fitilu masu launin warm gold sun lulluɓe wajen, suna kyalli a cikin iska mai sanyi. A ƙofar shiga, banner ɗin da aka tsara na rataye da rubutu: “Welcome to the Union of Hearts Amal ❤️ Maleekh 2025” Ƙamshin turaren oud da vanilla rose yana gauraya da ƙamshin furen da aka shuka a jikin hanyar shiga. A gefe kuma, ana busa saxophone mai daɗi, yana haifar da nutsuwa da nishaɗi. An kafa big white tent mai gilashin bango da fitilu masu walƙiya a ciki. Kujeru sun jeru cikin tsari, kowace kujera da flower centerpiece a tsakiyarta. Jerin kujerun mazan gefe ɗaya, na mata gefe ɗaya kowa cikin kwalliya da annuri. Ƴan uwa da abokai, Kaduna, Abuja, Lagos, Borno, England, American, Dubai, da sauran manyan ’yan siyasa da ’yan kasuwa duk sun hallara. Wani lokaci zaka ji wani daga cikin jama’a yana faɗin: “Wallahi wannan shi ake ƙira bikin manya." A bakin shigowa, ma’aikatan walima suna ta yin ushering cikin ladabi. Ƙamshin abinci yana yawo fried rice, jollof, salad, grilled chicken, pepper soup, da non-alcoholic champagne da aka shigo da su daga Italy. Fitowar Amarya Kowa ya ɗaga kai lokaci guda! Sai Amal ta shigo cikin long gown mai kyalli, launin champagne gold ɗauke da silver stones. Rigar ta zagaye jikinta cikin salo da nutsuwa, ta ɗora veil ɗin light gold net da aka shafe shi da diamonds. Ƙamshin turarenta ya cika wajen, haɗin Ajmal Amber da Mukhallat Shams... Da kallo guda zaka fahimci ba kawai kyanta ake gani ba, ana ganin natsuwa, kunya, da hasken zuciya. Ƴan uwa mata suka tashi suka fara shewa: “Amarya ta fito! Amarya ta fito!!” Sai hayaniya ta barke, ana ta tafi da waka da ihu cikin nishadi. Wata daga cikin danginta tana dariya ta ce: “Allah ya sa albarka cikin wannan aure.” Amal tana murmushi, tana tafiya a hankali, hannunta a cikin hannun kawarta Aisha da ke rakiyarta zuwa kujerar amarya.. Fitowar Ango Maleekh.. Sai kuma Maleekh ya fito daga sashen sa, cikin white suit mai sheƙi, da black tie, gold wristwatch, da shoes masu glass shine. A gefe ɗaya Abbah ne yana murmushi da alfahari, yana zaune. Duk inda ya taka sai jama’a sun juya suna kallonsa.. Ga wasu manyan abokansa a gefe da gefensa. Ga ƙannensa Islam da Arfat suma sun fito, sun sha kyau sosai.. Hankalinsa duk yana kan Amal. Idanunsa sun haɗu da nata. A lokacin, duniya ta tsaya cik a gare su. Babu kowa a cikin ido sai su biyu... A gefe, Ammy ba ta hallara ba. Tana zaune a gida cikin living room ɗinta, tana kallon walimar ta hanyar TV live broadcast.. A gefe ta ajiye cup ɗin tea amma ba ta sha ba. Tana kallon Amal a fusace. “Yaron nan... wannan ce mace da zai ɗauka? Wannan ce har zai ce ta fi masa kowa?” Ta lumshe ido, ta ɗaga hannu a hankali tana faɗin: “Allah Ka kare ɗana daga halin da bai sani ba...” A zuciyarta akwai ƙunci da kuma wani ɓangare na soyayyar ɗanta da ta kasa fitarwa... An kunna lights show, DJ ya saka waka mai nutsuwa. Amal da Maleekh suka zauna kusa da juna a kujerar aure, fuskokinsu cike da annuri. Ƴan uwa suna ta ɗaukar hotuna, ana ta murna, ana dariya. Maleekh ya juyo a hankali yana kallon Amal. “Yau kowa yana gani… amma ba kowa yake fahimtar yadda zuciyata ke bugawa saboda ke ba.” Amal ta yi murmushi, ta ɗaga kai ta ce: “Daga yau ni ce matar da zaka ƙira naka… har abada.” Sai suka kalli juna lokaci ɗaya fitilun wajen suka sauya launi zuwa gold and white. Jama’a suka tashi da tafi da shewa: “Auren shekaraaa!!! 🎉🎉🎉” Daren Walimar Aure An rufe taron da murna da nishaɗi. Wurin ya cika da farin ciki, kiɗa, da ƙamshin turaren da ke fita daga ko’ina. Kowa na faɗin, “Allah ya kaimu gobe lafiya, Allah ya tabbatar da ɗaurin auren lafiya.” Yamma ta wuce, dare ya sauƙa da sanyin iska mai ɗauke da ƙamshin furanni. Gidaje suna walƙiya da hasken fitullun gilashi da aka rataya a ko’ina. Misalin ƙarfe 9 na dare Kowa ya koma gida, Amal ta cire veil ɗinta, ta zauna gaban madubi tana duban kanta da murmushi. Cikin ranta tana jin kamar ta shiga mafarki auren da ta jima tana mafarki da shi, yanzu gobe ne. A gefe kuma Farha, Aisha da wasu ‘yan uwanta mata suna zaune a akan gado suna ta dariya, suna tsokanar Amal: Farha wacce yau ta kasance a wurin hidima kuma ta shiga sahun ƙawayen Amarya, yau a gidansu Amarya zata kwana cikin ƙawaye... Farha ta ce “Ke fa Amal, kin san idan aka ɗaura auren nan gobe, gobe da dare ba zaki huta ba!” Duk suka yi dariya. Aisha ta ce “Ke Farha ki bari mana amarya ta huta, kin manta da walimar yau? Duk jikinta a gajiya yake, kika sanar mata wannan al'amarin ai sai ta tsorata kuma...” Suka kwashe da dariya gaba ɗaya. Amal ta ɗago kai daga madubi, tana murmushi cikin kunya. “Ku dai ku bar ni in sha iska, na gaji sosai.” Wata daga ciki ta ce "Ji sai kace wacce kika yi wani rawar azo a gani..." Amal ta ɗan harareta tana shirin tashi kenan, sai wayarta ta yi ƙarar message. Ta ɗauka, zuciyarta na bugawa. Number ɗin “Amaleekh ❤️” ce, ta bayyana... “Please Beb, ki fito waje yanzu... inason ganin kyakkyawar fuskarki kafin na wuce gida.” Amal ta ji zuciyarta ta yi wani irin sanyi. Ta tashi, ta saka veil, ta ɗauki jakarta da wayarta ta ce da murmushi: “Ina zuwa yanzu…” Farha ta ce da dariya: “Ango yayi ƙira kenan, to Ya Maleekh amarya zata fito!” Aisha ta miƙe da sauri tana faɗin. "Tsaya a kwaskware miki fuskar mana.." Nan aka sake tsara mata sabon makeup.. Ta matsu ta fita saboda kar ta ɓata masa lokaci.. Farha ta ce "Dan Allah ku barta haka kar Ango ya gudu.." Suka kwashe da dariya gaba ɗaya, Amal ta fita tana murmushi. A Harabar Gidan Daren ya yi shiru. Iska mai sanyi na busowa, Haske na haskaka filin gidan... Amal ta iso bakin get, ta ce wa mai gadi cikin ladabi: “Please ka buɗe mun ƙofa, ina dawowa yanzu.” Mai gadi ya buɗe, yana murmushi. “To Amarya, ki kula fa, dare yayi.” Tana tafiya a hankali cikin doguwar gown mai ruwan milk, tana ɗauke da ƙamshi mai sanyaya zuciya. Ga takalminta mai tsini sosai, ta ɗan ɗaga rigarta kaɗan saboda kar ta taka takalmin.. A gaban get ta hango wata babbar mota baki mai taya ta baya, fitilunta a kashe. Ta ɗan yi murmushi a zuciya ta ce, “Laa, har yanzu yana nan a mota yana jirana.” Tana kusantowa ta buɗe motar ta shiga da murmushi. Bayan ta shiga ta rufe ƙofar, ta tsaya cak ganin wasu mutane daban a ciki.. Kafin ta yi magana, wani mutum daga bayan kujerar ya damƙeta da ƙarfi, ya sanya handkerchief mai ɗauke da turare a hancinta. Amal ta fara ƙoƙarin yin ihu, amma muryarta ta sare. Idanunta suka fara lumshewa, numfashinta ya yi rauni. “Ssshhh… shiru, komai zai dai-daita,” wani murya mai sanyi ya faɗa, kafin komai ya rufe mata duhu. A lokacin ta sume domin turaren irin mai saurin sumar da mutum ne... Motar ta tashi da sauri cikin dare, ba kowa ya lura ba. Sai ƙarar motar ta ɓace cikin shiru... 🕛 A cikin gidan kuwa. Lokaci yana tafiya. 11 na dare. 12. Har 1 na dare. Farha ta miƙe daga inda suke zaune, tana kallon agogo cikin tashin hankali. “Ni fa har yanzu hirar bata ƙare bane? Ko kuwa ta koma wajen Maleekh ne da kwana?” Aisha ta ce: “Ai ta ce ‘ina zuwa yanzu’. Ta tafi ne kamar za ta dawo nan da minti goma…” Farha ta ɗauki wayarta ta ƙira Amal ringing... amma ba’a ɗauka ba. Ta sake ƙira still not picking. “Ba’a ɗauka ba. To bari na ƙira Yaya Maleekh.” Ta ƙira. Switch off. Farha ta kalli Aisha cikin tashin hankali. “Wayarsa a kashe... wannan ba daidai bane.” Aisha ta ce: “Ku tashi mu fita mu duba waje.” Suka fita zuwa harabar gidan, suka tambayi mai gadi. Mai gadi ya ce musu: “Ai ta fita ta ce za ta dawo yanzu. Ban gani ta dawo ba.” Farha ta ce da mamaki: “Ba yanda za'ayi Ya Maleekh ya tsaya a waje ba tare da shigo wa gidan ba… wannan abin akwai matsala.” Mai gadi ya buɗe musu gate. Suka fita, waje wayam. Shiru. Hasken fitullun titi kawai ke haskawa. Suka dawo cikin gidan, zuciyoyinsu na bugawa. Amal ba ta dawo ba. Haka suka yi ta ƙira, har wayarta ta daina shiga gaba ɗaya. A cikin daren kafin Asuba misalin ƙarfe 3, Inna ta fito daga ɗaki da tsoro a idonta jin hayaniya.. “Wai menene ke faruwa?” Farha ta ce cikin kuka: “Tun jiya da daddare Amal ta fita, bata dawo ba har yanzu.” Anan aka ƙira Abbah, aka sanar masa. Abbah ya ƙira Maleekh, ya tambaye shi cikin tashin hankali: “Maleekh, ina Amal take? Ya zaka ɗauke ta ba tare da ka sanar ba?.” Maleekh ya amsa da muryar bacci: “Amal kuma? Wallahi bayan mun rabu a walima ban sake ganin ta ba. Na shiga ɗakina kai tsaye bayan na dawo. Me ke faruwa ne?” Kowa ya rikice. Cikin mintuna kaɗan gida ya cika da hayaniya, kukan mata da ruɗanin dangi. “Amarya ta ɓace! Amarya ta ɓace fa a daren daurin auren ta!” A daren Abbah da Maleekh suka zo gidansu Amal.. Mai gadi yana ta rantsewa: “Ni wallahi ta fita da kanta, motar baki ce kawai na gani.” Abbah ya riƙe kai yana cewa: “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un… Amal fa yarinya ce mai kamun kai… wa zai yi haka?” Maleekh kuma yana tsaye, a filin gidansu Amal da Abbah da kowa da kowa. Zuciyarsa na bugawa cikin tashin hankali, bai san ko mafarki yake ba ko gaskiya. Daren farin ciki ya koma daren kuka. Amarya ta ɓace a daren kafin ɗaurin aurenta. Gobe da safe, duniya za ta firgita. Da safe gari ya waye cikin tashin hankali da hayaniya. Labarin bacewar Amal, amaryar da za a ɗaura aurenta yau, ya baza ko’ina. Daga unguwa zuwa social media, daga bakunan dangi har zuwa gidajen makwabta kowa na magana: “Amarya ta ɓace kafin ɗaurin auren ta!” “Wai me ya faru ne?!” Gidansu Amal ya cika da jama’a, wasu suna kuka, wasu suna addu’a. Abbah ya ƙira Maleekh, yana faɗin cikin tashin hankali: “Ka ƙira ‘yan sanda yanzu, ba za mu zauna mu jira ba. Dole a bincika ko ina!” A Ofishin Tsaro Maleekh yana zaune cikin tashin hankali da damuwa, idonsa ya kumbura saboda rashin bacci. Jami’an tsaro suna zagaye da shi a ofishin CCTV, ana kallon footage ɗin gidansu Amal. A screen ɗin aka ga Amal ta fito daga gidan da kanta, cikin doguwar riga, ta tsaya a bakin get. Ta yi magana da mai gadi, sannan ta nufi wata baƙar mota mai gilashin tint. Ta buɗe motar da kanta ta shiga, ba wanda ya ja ta ko ya tilasta mata. Jami’an tsaro suka kalli juna. Ɗaya daga cikinsu ya ce, “Gaskiya, daga yadda ta fito da kanta, wannan ba sacewa bace. Wannan alama ce ta wanda aka ƙira a waya.” Wani jami’i ya ƙara cewa, “Yuwuwar saurayinta ne ya ƙira ta. Yana waje, sai ta fito.” Maleekh ya cije leɓensa yana duban screen ɗin da idanu jawur. Ya ce da mai sarrafa CCTV: “Please, ɗan dawo baya. Inason duba wani abu kafin ta shiga motar.” Aka dawo kaɗan, sun ga lokacin da Amal ta ɗaga kanta sama, ta dubi CCTV camera kafin ta shiga motar. Kowa ya yi shiru. Sai Maleekh ya furta cikin ƙasa-ƙasa: “Ta san ana kallonta... ta kuma san za a ga wannan... Amma duk da haka ta tafi.” Wani jami’i ya ce cikin sanyi: “Yallabai, wannan ai kamar ta tafi da niyyarta ne. Ba alamar karfi ko tsoro a jikinta.” Maleekh ya dafa kansa, sannan cikin ƙarfi ya ce: “Enough! Ku bar komai. A janye ƙarar. Idan da gaske sace ta akayi, da wata alama za ta nuna. Wannan dai ita ce ta shirya tafiyar.” Ya tashi tsaye, ya dube su da idon da ke cike da ɓacin rai. “Munafurcinta ne kawai. Idan ta gama sharholiyarta, zata dawo kamar yadda ta tafi.” Jami’an suka kalli juna cikin mamaki. Amma babu wanda ya ce komai. A gida kuwa, Abbah, Inna, Farha, Ammy da dukkan dangi sun hallara. Kowa na jiran zuwan Maleekh da wani labari. Inna tana kuka sosai, ta miƙe tsaye cikin tashin hankali, ta damƙi rigar Farha tana faɗin: “Da haɗin bakinki kika sa aka sace mun Amatu na ko? Ki gaya min gaskiya a gaban kowa! Daman tubarki ba gaskiya bace! Na san halinki!” Farha ta ruɗe, tana kuka tana cewa: “Wallahi Inna, bana da hannu! Tallahi bana da hannu akan bacewar Amal! Na tuba, amma wannan ba laifina bane!” Abbah ya matsa kusa da Inna ya ce cikin tausasawa: “Kinga Mama, ki bari ta sake jikinta. Babu tabbacin haka. Mu saurare ta.” Ya juyo ya kalli Farha cikin nutsuwa: “Ki gaya mana gaskiya, Farha. Shin da haɗin bakinki aka ɗauke Amal?” Farha ta share hawayenta, ta ce da rawar murya: “Wallahi Abbah, ban san komai ba. Ni yanzu nayi hankali, wallahi zuciyata tsaf, bana da hannu a bacewar Amal.” Ammy, ta ce cikin murya mai ƙarfi: “Haba Alhaji! Ta ce ba ita bace, me yasa za ku tozarta yarinya haka a gaban jama’a? Ba zaku iya ɗora mata laifi ba akan abin da babu tabbaci!” Inna ta ce cikin kuka mai ƙarfi: “Na rantse da Allah idan ba ta da hannu, to waye zaiyi haka! Wayyo Amatu na... wayyo yarinya ta!” Ta rushe da kuka, tana faɗin, “Ai wannan bikin ya zama bakin ciki! Waye zai iya jurewa?” Kowa ya kame yana ta sauraron ruɗani a cikin falon. Sai ga Maleekh ya shigo cikin hanzari, fuska cike da ɓacin rai. Kowa ya juya yana kallonsa. Sai shiru ya mamaye falon gaba ɗaya. Maleekh ya tsaya a tsakiyar falon, ya ce da murya mai sanyi. “Farha bata da hannu a bacewar Amal.” Duk suka juya suna kallonsa, suna jiran abin da zai ce. Ya ɗauko laptop daga hannun ɗaya jami’i, ya kunna bidiyon CCTV. A screen ɗin aka ga Amal ta fito da kanta, ta dubi sama, ta nufi mota, ta shiga da kanta. Kowa ya kalli juna, wasu da hawaye, wasu da mamaki. Maleekh ya ce cikin muryar da ta karye: “Ga shaida. Ita da niyyarta ta fita daga gidan, ba wanda ya sace ta. Ta ƙi auren saboda ta tozarta ni. Ta bi wani saurayi daban.” Wani ƙara ya fito daga bakin Inna: “Karya ne! Ƙarya kake Maliku! Amal ba zata yi haka ba!” Abbah ya ce cikin ɗaga murya: “Kai Maleekh, kana hauka ne? Taya yarinya a daren aurenta zata bar gida da kanta? Tana so fa, ba wai tilasta ta akayi ba! Taya zaka ce ta tozarta ka?” Maleekh ya ce cikin tsanani: “Haka ta tsara makircinta! Da gaske bata so na. Ta yi wannan don ta ɓata min suna.” Aisha, ƙawar Amal, ta ce cikin tsoro: “Amma fa, kafin ta fita, mun ga text ɗinka a wayarta! Ka turo mata message cewa ta same ka a waje!” Maleekh ya juyo da idanu masu cike da zafi: “Ta nuna muku message ɗin ne? Ta nuna muku number da ya turo mata ne?” Aisha ta girgiza kai, hawaye na gangarowa. “A’a... bata nuna mana ba...” Farha tana kuka, ta ce: “Ni dai na tabbata akwai lauje cikin naɗi. Amal ba zata aikata haka ba. Tana ƙaunarka fiye da komai. Wallahi akwai wanda ya shirya wannan.” Maleekh ya ja dogon numfashi, sannan ya ce cikin sanyi da raɗaɗin zargi: “Ku bar komai. Kada kowa ya saka kansa a cikin damuwa. Idan ta gama shan sharholiyarta, zata dawo. Ba zan ƙara bata minti ɗaya daga zuciyata ba.” Ya juyo cikin fuska mai cike da ciwo, ya fita daga falon, ya buga ƙofar da ƙarfi. Shiru ya rufe wurin. Kowa ya kame, zuciya cike da tambayoyi. “Amal ta tafi da kanta?” “Ko dai wani ya yi amfani da sunan Maleekh ne ya jawo ta?” Duk suka kalli juna cikin shiru, duniya ta canja musu launi a ranar da ya kamata ta zama farin ciki... 《》《》《》《》 Haske kaɗan ne ya shigo ta ramin taga. A cikin ɗakin, Amal tana zaune a kujera; an ɗaure mata ƙafa da hannu, an toshe mata baki gam. Jikinta gabaɗaya na rawa, idanuwanta sun kumbura, hawaye suna zuba amma ba za ta iya ihu ba. A gefenta wasu gafza-gafza matasa ne, fuskokinsu a rufe da baƙar hula, hannayensu na riƙe da bindigogi. Tana ta kuka a sirrance.. Farha ta koma gidansu. Mahaifiyarta ta sata a gaba sai masifa take ta mata. "Wallahi yanzu ban san wani irin rashin zuciya Allah ya ɗora miki ba Farha, saboda rashin zuciya har kije bikin Maleekh? Mutumin da ya gujeki ya nuna baya ƙaunarki har ki saura da shiga jikinsa, wani abun baƙin ciki har ki kwana a gidan su Amal? Mutanen da suka tozarta ki suka durkufa ki a gaban kotu suka sa kika zauna a prison amma har ki shiga jikinsu.... Gashi abinda ya faru ai, Ƴar su ta gudu sun makala miki sharrin ke kika sa aka sace ta, madalla gobe kya ƙara zuwa yanda suke ai.." Farha tana kallon mahaifiyar ta, idanu cike da hawaye ta ce, “Mom... anjuma ma zan koma gidansu Amal na ji ko an samu labarinta… wallahi ban san yanda matsalar take ba ..” Hajiya Sa’adatu tana ɗaga murya ta ce, “Kin yita marar zuciya! A haka zaki ƙare! Banza shashasha! Sai sun ƙara makala miki wani sharrin ai…” A wannan lokacin Zayd ya shigo cikin falon, ya tsaya a tsakiyar falon yana kallon mahaifiyarsa da Farha ya ce, “Ya! Meke faruwa anan?” Farha ta miƙe cikin hanzari, ta juya zuwa ga Zayd: “Yawwa Yaya! Dan Allah idan kasan kana da hannu a ɓatan Amal ka gaya mana! Ka fita daga rayuwarta! Nasan ba mai haka sai kai, daman ka ci alwashin raba soyayyarsu!” Hajiya Sa’adatu ta juya zuwa ga Farha ta ce. “Au ke! An ɗora miki sharrin sace ta, ke kuma kin zo ki ɗora wa ɗan uwanki sharrin sace ta? Me kike nufi kenan!?” Zayd ya kalli mahaifiyarsa yana sarrafa fushinsa, ya juya zuwa ga Farha cikin tsananin iko: “Na rantse idan ban kwaɗa miki mari ba, ki sanja mun suna! Kin raina mun wayo, ni da nake shirin kwamushe ta, kwatsam naji labarin bacewar ta, kuma yanzu kin zo kina mun wani irin question? ‘Yarinyar da akace tabi saurayinta. Kuma shima Maleekh ya tabbatar da hakan…” Hajiya Sa’adatu ta ƙara murya da cewa: “Ka rabu da ita! So take azo a kamaka! Ai idan zaka ji tawa, kawai ka nemi wata! Amma wannan kam ta gama amfani...” Farha tana kuka, ta ja numfashi mai ƙarfi tare da faɗin: “To dole na yi zargin haka… saboda ku kuka yi silar hatsarinta sannan kuke shirya kashe ta! Duk naji komai ai.. ” Hajiya Sa’adatu ta tsaya, kirjinta na bugawa da ƙarfi, ta kalli Farha da mamaki da fushi lokaci guda ta ce: “Ke! In ƙara jin wannan maganar ta fito daga bakin ki wallahi sai nayi mungun sa6a miki, wawuya kawai...!” Farha ta ru ga da gudu saman upstairs yanda ɗakinta yake... Hajiya Sa’adatu ta riƙe ƙirji tana kallon Zayd ta ce "Ka duba yarinya zata jawo mana bala'i?..." Bayan Sati guda... Yanda Amal take a wannan karon an rufe mata fuska gaba ɗaya. Wani hamshakin mutun ne mai tafiya akan iska ya fito daga cikin tsararren motarsa. Yanayin tafiyarsa kasan handsome guy ne, yana tafiya yana zukar shisha. Bodyguards suka yi escort ɗinsa har ciki yanda Amal take. Yana shiga ya tsaya a gabanta ba tare da yayi magana ba yayi alama da hannu cewa 'a miƙo masa wayarta..' Hakan akayi ya karɓa ya buɗe wayar sannan ya shiga wurin message ya goge saƙon da aka turo mata, ya shiga wurin Gmail ya goge domin yasan kan wayar duk abinda ya shigo cikin wayar sai yayi saving a email... Sannan ya kashe wayar ya bayar akan a cigaba da riƙe wa... Ƙerarren mutu yana tsaye, komai nashi a tsare, yatsun hannayensa a jere da zobina kala-kala, ga hannun farin tas irin na ƴan hutu. Ɗayan hannun yana riƙe da shisha. Ya durƙusa a gaban Amal da fuskarta yake a rufe ga baki a toshe, hannaye da kafafuwa a daddaure.... Haka yake zuƙo da hayaƙin shisha yana busa mata akan fuskar da yake rufe... Ya gama yin sa ba tare da ya furta komai ba, daga bisani ya manna mata kiss akan goshi sannan ya miƙe ya fita. Bodyguards suna biye dashi a baya, wasu kuma sun cigaba da tsaya wa a gun da Amal take ɗaure... Shiga tsararren motarsa ya yi, ya zauna a backseat sannan security yayi driving ɗinsa. Sauran Bodyguards kuwa suka tsattsaya suna gadin dajin... (Ni iya ƙafafunsa da hannayensa zuwa wuya na gani 😄 ban ga fuskar ba balle nayi muku gulma 🤭😝😝....) AMMA ZAN BADA CHANKI-CHANKI!... DUK WANDA YA CHANKI DAIDAI ZAN MASA KYAUTA MAI TSOKA 🤣🤣🤣🤣 SHIN WAYE????..... *_NEXT NEXT NEXT_* ... asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 73 to 74 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Sati Biyu Bayan Bacewar Amal Gidansu Amal ya koma gidan shiru. Sai ƙarar agogo da ke bango shi kaɗai ke yi, tik...tik...tik... Gidan da yake cike da dariya, kiɗa da annashuwa, yau ya koma gidan jimami. Inna ba ta da wani natsuwa. Ba ranar da zata faɗi, ba ta ambaci sunan Amal ba. “Ya Rabbi... ina jikata? Me ya same ta? Me Amal ta yi har ta cancanci haka?…” Hankalinta ya tashi sosai, har ta ɗan rame. Idanunta sun kumbura da kuka, jikinta ya yi sanyi kamar mara rai. Duk lokacin da zata yi sallah, sai ta roƙi Allah cikin kuka: “Ya Allah ka dawo min da Amatu ta, ko da matacciya ce kawai in ganta in saka ta a idanuwa na...” Abbah ya dage sosai. Ya kasa kwantar da hankalinsa, kullum sai ya nufi ofishin ƴan sanda. Kusan kullum sai an nemi wayar Amal ko za'a samu damar yin tracking ɗin wurin da take amma lambar kullum “The number you have dialed is not reachable at the moment…” Ƴan sanda sun bazama suna bincike daga CCTV har zuwa makwabta, daga motar da ta ɗauke ta, har zuwa duk inda ake zargi. Sun saka hotonta a gidan rediyo da talabijin. “Wannan yarinya mai suna Amal Abdulsamaad, shekaru 22, ta ɓace tun ranar walimar bikinta. Duk wanda ya ganta ko ya san inda take, a tuntubi ofishin ƴan sanda mafi kusa.” Kowa ya ji labarin. Mutane suna ta fassara lamarin da zato.. “Wata kila saurayinta ta bi...” “Ko an sace ta ne saboda kishi...” “Ko dai akwai makirci a tsakanin danginsu…” Amma Inna ta san jikarta ba irin waɗannan mata bace. Ita dai kuka kawai ta iya sai addu'a. A ɓangaren Maleekh kuwa, babu alamar damuwa. Yana kwance a ɗakinsa, ya jingina da gadonsa, yana kunne da headphones. Gaba ɗaya ya cire kansa daga lamarin.. Ƴan sanda sun zo har gida, amma bai damu da su ba. Idan Abbah ya ƙira shi, sai ya ce, “Amal dai ta bi hanyar da ta zaɓa. Ina fatan tana jin daɗinta.” Kowa ya daina gane Maleekh.. Duk san da akayi masa maganar Amal sai ya ce “Inda ta je, ta sani. Zan jira ranar da gaskiya zata fito..” 🕯️ Mutanen da suka zo daga Borno da Kaduna sun koma gida. Gidansu Amal ya watse. Sai Inna da ƴan aiki, kowa ya koma yanda ya fito. Inna kullum tana zaman jiran saƙo. Duk lokacin da taga motar da ta tsaya a bakin titi sai ta miƙe da sauri, tana cewa: “Ko Amal ce? Ko labari ne daga gareta?” Sai dai kullum amsar duniya ɗaya ce, shiru. Abbah yana zuwa kullum da safe, yana bata haƙuri da cewa: “Ki daure, Mama. Allah yana gani. Insha Allahu, Amal zata dawo lafiya.” Inna ta share hawaye, ta ce da murya mai rauni: “Alhaji, ni dai bazan daina addu’a ba. Allah ya dawo min da jikata, ko da a mafarki ne.” ☆☆☆☆☆ Haske ɗaya kacal ne ke fitowa daga ƙaramin rami a bango, yana zana layin fuskokin mutane da inuwa. A cikin ɗakin, Amal tana zaune a kujera; an ɗaure hannaye da ƙafafu da igiya mai ƙarfi. An toshe mata baki, sai ƙanƙanin numfashin da take fitar wa. Gashin kanta ya zubo gaba ya rufe mata fuska... A kusa da ita, wasu matasa uku ne, fuskokinsu a rufe da baƙar hula, hannunsu riƙe da bindigogi, wasu kuma suna riƙe da wayoyi. Sun zauna kamar suna tattauna aiki, amma a kowane lokaci suna duba Amal kamar dabbobi cikin yunwa... Jagoransu ya zauna a kan kujerar kusa da ita, ya buɗe kwalin abinci, ya ɗan ciro lemo a leda. Ya dubi Amal a hankali, murya tamkar goge tabo, Jagoran ya ce, “Kar kina jin kunya, yarinya. Wannan ba kuɗin banza ba ne. Aiki ne kawai. Ki yi shiru, ki zauna da haƙuri, za mu juya miki labari.” Amal ta lumshe ido, ta gwada motsa leɓe, ta ƙara yin ƙoƙarin faɗi wani abu amma gam ɗin baki ya hana ta.. Ya yi dariya mai ƙarfi sannan ya ce “A, kina ƙoƙarin magana ne? To dai ki tuna, komai zaki faɗa zai koma gefen mutumin da ya aika mu. Don haka shiru kawai.” Ya ji wayarsa tayi ƙarar shigowar message ya duba sannan ya ce, “Boss, client ya aiko saƙo yanzu: ‘Ku an kare guys domin kar ku bari bincike ya yo ta wurin ku, ƴan sanda suna kan bincike kar ku bari a same ta, ku shirya yadda za ku ɓoye ta gaba ɗaya but please kar ku barta da yunwa kuma kada wanda yayi ƙoƙarin cutar da ita..’.” Other one: “Dole mu mishi yanda yake so domin Boss ba wasa fa, ya turo da kuɗin da yace zai bamu mu raba?” Jagoran ya ce: “Eh. An riga an tura da yawa ma. Amma ya ce mu jira umarni na biyu, kar mu yi wani abu har sai an ƙira mu.” Jagoran ya miƙe ya matso kusa da Amal, ya share gashin fuskarta da hannu, “Mun dafa miki abinci da ruwa. Duk da haka, kar ki yi ƙoƙarin gudu. Kowane ƙoƙarin gudu zai cutar da ke.” Ya kun ce mata hannu sannan ya bata... A hankali ta ɗauki spoon tana caccakar abincin kamar bazata ci ba... Daga bisani ta ɗan taɓa, bayan ta kammala ta sha ruwa aka sake ɗaure mata hannayen.. Cikin zuciyarta tana mamaki "Me yasa? Wane irin zunubi na yi da ya sa ake mini haka? Ta tuna saƙon da Maleekh ya turo mata, tana murmushi haɗe da hawaye ta ce "Allah sarki bawan Allah, maybe ya gaji da jirana ne yasa ya tafi, bayan tafiyar kuma hakan ya faru da ni..." Tana ƙoƙarin motsa ƙafafunta domin sunyi matuƙar gajiya da tsami, igiyoyin suna da ƙarfi. Ta jujjuya kai, ta kalli wani rami a bango, waje ne da ba za ta iya gani sosai ba amma da duk kan alamu nan daji ne... *1 MONTH LATER* Waya ce take ringing. Jagoran ya amsa ƙira a wayarsa. Ya ɗaga wayar a hankali, ya sa a kunne, yana magana: “Yes, boss... mun tsare ta da kyau. Ba mu cutar ba... bata gane komai ba, mun rufe wayarta. Muna jiran umarnin ka.” Muryar a waya: “Kada ku sanar mata komai, ku jira gobe da safe. Zan sanar muku abin da zakuyi. Kada ku dameta sosai tukuna. Idan ta yi hayaniya, ku mayar da ita cikin shiru.” Jagoran ya katse ƙira, ya dawo wajen sauran yana faɗin. “To, mu shiryawa safe. Mu yi bincike kafin mu fito dan Da safe za mu kai ta wani wuri. Kada kowa ya kusanci jejin gidan nan.” 🕯️ Washegari da safe suna jiran saƙon da za'a aiko musu.. A gefe, wani ya ɗaga hannu ya ce cikin natsuwa: “Mu jira umarnin client. Da safen nan, za mu zamo masu aiki, amma a hankali. Kada kowa ya san inda muka kai ta. Wannan aikin ya fi kuɗi.” Jagoran ya kalle su sannan ya ce: “In ba haka ba, idan wani ya sanar, za su fara bincike, su neme mu. Da mun riga mun kai ta wuri mai kyau, babu wanda zai taɓa gane komai.” A wannan lokacin misalin 9 na safe. Tana ɗaure da sauran security masu gadinta. Ita dai ta kasa fahimta duk lokacin da Boss ɗinsu zai zo sai sun rufe mata fuska yanda bazata iya ganinsa ba. Kuma idan yazo baya magana har ya tafi, kuma duk sanda zai tafi sai ya sumbace ta akan goshi. Kuma abinda yake ƙara ɗaga mata hankali shine ƙamshin turaren Boss ɗin irin na Masoyinta Maleekh ne amma ta kasa yadda da hakan... Bayan ya gama ganinta yayi abin da ya saba wato ya sumbace ta akan goshi. Sai bayan ya fita can outside ne ya tara su sannan ya ce. “Ku shirya. Ku fita da ita yau da daddare. Ku rufe mata fuska yanda bazata gane ko'ina ba. Ku a jiye ta a bakin gidansu, ku wuce ba tare da kun tsaya ba.” Security biyu suka kalli juna, ɗaya daga cikinsu yace: “Boss, muna nufin mu sake ta? Kai tsaye?” Boss ya ce, “Eh. Ku tabbata ba wanda ya ganku. A yi abin cikin tsari. Bayan kun aje ta, ku ɓace kafin ta shaida ku.”... Daga bisani ya shige motarsa ya tafi kamar walƙiya... Da daddare misalin ƙarfe 12. Amal tana zaune kamar yadda suka saba ajiyeta, Wasu daga cikinsu su biyu suka ƙaraso da rigar fuska, ɗaya ya kwance igiyar hannunta da ƙafarta.. Security na 2 a hankali ya furta, “Ki yi shiru, Madam. Kada ki yi magana.” Suka riƙe ta suka fitar da ita zuwa mota, suka zaunar da ita a baya. Mota ta kama hanya cikin nisan gari, babu wanda ke magana. Sai numfashinta kawai ke ji. Awa guda da wuce wa, mota ta tsaya. Aka buɗe ƙofa da sauri. Security na 1 ya ce, “Ki zauna seconni biyu, sannan sai ki fita.” Bayan sun tabbatar da ba kowa a layin suka fitar da ita, suka aje ta a bakin titi kusa da gidansu. Sannan ɗaya daga cikinsu ya zare fuskar da aka ɗaure mata fuska da ita. Amal ta ɗan rintse ido, haske ya bugi idonta kamar wuta! Ta lumshe, tana jin dishi-dishi. Idanuwanta sun yi duhu sakamakon ɗaure su da akayi ba.. Hasken fitillun ne suke ta haskawa amma wurin shiru ba motsin kowa.. Ta buɗe ido a hankali, tana ganin haske, titin da ta sani… sannan ta ɗago kai cikin rawar murya: A hankali ta furta “Wannan… wannan gidanmu ne…? Wannan unguwarmu ce?” Tana ƙoƙarin juyawa ta ga motar da ta kawo ta, amma wayam, motar ta ɓace! Ta ɗan kalli kewayenta, tana jin kamar mafarki take.... Zuciyarta ne ya fara bugawa. Da gudu ta nufi cikin unguwar, ƙafafunta na rawar sanyi da farin ciki a lokaci guda.. A bakin ƙofar gidansu ta tsaya tana buga ƙofar da ƙarfi. Tana kuka tana furta, “Mai gadi! Mai gadi don Allah buɗe ƙofa! Ni ce! Ni ce Amal!” Mai gadi wanda ke zaune a cikin bukkarsa, ya fito da fitilar hannu. Idanunsa a zazzare ya ce, “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Amal?! Ke ce haka? Subhanallah! Ke dai gaske ke ce kuwa?!” Amal ta kalle shi cikin hawaye, ta ce da rawar murya: “Ni ce Mallam Musa… ni ce wallahi… don Allah ka buɗe ƙofar… ka bari in shiga gida!” Da sauri ya buɗe ƙofar. Tana shiga ciki, ta fara ƙiran: “Innaaa!! Inna taaa!! Ina kike Innaaa!!” A cikin falo, Inna tana zaune tana duba hoton Amal da hawaye a idonta. Da ta ji muryar Amal, ta tsaya cak, hoton ya zame daga hannunta. Ta tashi da gudu ta fito daga falon, tana faɗin: “Subhanallah! Wannan murya… Amal… Amal ce!” Inna tana fito wa Amal ta faɗa mata a jiki, suka rungumi juna. Amal tana kuka sosai ta ce: “Innaaa! Na dawo! Na dawo Innaaa! Na gaji! Na sha wahala Innaaa!” Inna ta fashe da kuka tare dafaɗin: “Ya Allah na gode! Ya Rahman! Na rasa muryarki, na rasa dariyarki! Amal ɗina kin dawo… kin dawo min lafiya!” Suna kuka suna rungume da juna. Inna ta zare daga jikinta ta ɗaga fuskarta tana duba Amal da hawaye, tana shafa kumatunta ta ce: “Amal... kina raye? Meya faru dake? Su waye suka yi miki haka? Ina suka kai ki?” Amal tana girgiza kai cikin kuka ta ce, “Inna… ban sani ba… ban san inda nake ba, ban san me yasa ba, amma na dawo Inna…” Inna ta rungume ta da ƙarfi kamar tana tsoron kar ta sake ɓacewa. Inna tana kuka ta ce, “Shikenan Amal… shikenan. Allah ya isa. Ki shiru, ki huta. Ki gode wa Allah. Ya dawo da ke gare ni.” Mai gadi ya tsaya bakin ƙofa yana share hawaye, yana kallon ikon Allah. Mai gadi a hankali ya furta, “Wallahi ikon Allah babu iyaka… wata guda, duk muna tunanin ta mutu…” Amal ta sunkuyar da kai cikin jikin Inna, zuciyarta na bugawa cikin tsoro da farin ciki. A cikin ƙasan ranta, ta rantse, duk wanda ya aikata min wannan, sai na san wanene... Suka shige ciki, a wannan daren Inna ta ƙira Abbah ta sanar masa dawowar Amal... Ana salar Asuba duk suka nufo gidan. An sanar wa ƴan sanda su ma sun zo. Ƴan sanda, Abbah, Ammy, Islam, Arfat, har da Maleekh kansa, da Farha wacce ta tsinci labarin daga bakin Islam duk sun hallara a falon gidansu Amal. Amal tana zaune a kujera, jiki a sanyaye, idonta yayi jawur tsabar kuka. Farha na gefenta, tana rarrashinta, yayin da Islam ke miƙe a gefe tana kareta da kallo..duk ta rarrame tayi baƙi. Ƴan sandan suna ta mata tambayoyi, amma duk abin ya yi musu duhu. Ɗaya daga cikin ƴan sanda ya ce, “Kinyi hakuri, Amma kin ce ba ki san inda aka kai ki ba? Kin tuna fuskar wanda ya yi miki haka?” Amal tana hawaye ta ce, “Wallahi ban sani ba... kullum suna sanye da hular fuska. Ban taɓa ganinsu ba, ban san inda nake ba. Duk lokacin da wani yazo, sai a rufe idona, ba magana ake ba...” Ƴan sandan suka kalli juna da mamaki, ɗaya daga cikinsu ya ja biro yana rubutu. A gefe kuwa, Maleekh yana tsaye, hannuwansa cikin aljihu, fuskarsa cike da ɓacin rai. Ya ɗaga murya cikin ƙasaita: “Ai baza ku samu wani bayani daga gareta ba. Tasan inda ta tafi, ba wai an sace ta bane. Ta tafi gantalinta da saurayinta.” Wuri ya ɗauki shiru. Kowa ya kalle shi. Amal da ke zaune ta ɗago kai a ruɗe, idonta ya haɗu da nasa. Kuka ya ƙara taso mata. Tana girgiza kai ta ce, “Ya Maleekh... wai me kake faɗa haka?...” Farha ta kamo hannunta tana faɗin, “Amal ki nutsu, don Allah ki zauna.” Islam ma ta kalle shi cike da mamaki ta ce, “Yaya, wannan magana ba daidai bane. Amal bata da ƙarfin halin nan.” Inna da ke zaune can gefe, ta share hawaye, tana girgiza kai da damuwa, ta kasa cewa komai. Abbah ya kalli Maleekh cikin ɗaga murya ya ce, “Kai Maleekh, bana son hauka fa! Yanzu wannan yarinyar da take a rame tayi baƙi saboda wahala, shine zaka ce gantali ta tafi? Kana muzanta ta da irin waɗannan maganganu.” Ammy ta ɗan juyo daga inda take zaune ta ce cikin gadara. “Ai gaskiya ya faɗa. Kowa yasan wannan yarinyar ta iya wasa da hankali. Kar a wahalar da ƴan sanda akan irin wannan shashanci.” Amal ta ɗago kai, tana girgiza kanta cikin hawaye, “Wallahi banyi haka ba! Ban san meya faru dani ba! Na farka a wani wuri, an ɗaure ni, kullum duhu, ba rana, ba magana... don Allah ku yarda da ni!” Maleekh ya ɗaga hannu yana nuna ƴan sandan, “Please, ku tafi. Wannan lamari na gida ne. Ku bar mu da ita domin babu wani abin da zaku samu..” Ƴan sandan suka kalli Abbah, suka ce: “Toh Alhaji, idan haka ne, zamu bar ku da ita. Amma idan wani abu ya taso sai a sanar da mu.” Suka tafi. Cikin tsananin damuwa, Amal ta tashi tsaye ta ce da rawar murya: “Wai meyasa baza ka fahimce ni ba, Ya Maleekh?... Me yasa baka yarda dani ba, shin zaka bada shaidar haka nake?....” Maleekh ya matsa kusa da ita, idonsa cike da ɓacin rai. Kafin kowa ya yi magana, cikin zafin nama ya ɗaga hannu ya zabga mata lafiyayyen mari! “Ahhh!” Tayi ƙara tare da dafe kuncinta, hawaye suna sulalowa da sauri... Kowa a falon ya tsaya cak! Inna ta dafe ƙirji, Wani irin shiru ya mamaye falon gaba ɗaya. Maleekh ya tsaya, yana kallonta da fuska a murtuke.. A tsawa ce yake faɗin “Ta ya zan fahimce ki bayan kin karya mun zuciya? Kin tozarta ni, kin wulakanta ni. Kin wuce gona da iri. Ki sani da ke gwara mutuwa.” Wani irin huci da kuka ya taso mata Ta cire hannunta daga fuska, ga fuska ta kumbura, ta yi ja, tana nuna shatar hannunsa... Amal cikin kukan takaici ta ce, “Ya Maleekh… me yasa? Har zuwa wannan matakin?...” Farha ta miƙe kusa da Amal tana rarrashinta, yayin da Abbah ya zauna cikin kaɗuwa, yana kallon Maleekh kamar ya miƙe ya fara dukansa a wurin... Inna a gefe, tana ta share hawaye da mayafi, yayin da Amal ta durƙushe a ƙasa, tana kuka kamar ranta zai fita. Sai a lokacin Abbah ya daka masa tsawa cikin murya mai nauyi, wacce ta girgiza falon: “Maleekh! Meye dalilinka na yin haka? Wace irin zuciya ce kake da ita har ka ɗaga hannu ka mari matar da kake ikirarin so? Me yasa kake zarginta da abunda ka san bazata taɓa aikatawa ba? Idan baka son aurenta sai ka faɗa a fili, amma kar ka zalunce ta da shaidar ƙarya!” Ɗakin ya ɗauki shiru. Maleekh ya ɗan gyara tsayuwa, ya janye hannunsa daga aljihu. Ya kalli Abbah kai tsaye cikin murya mai sanyi sannan ya ce. “Abbah, akwai dalilai da yawa. Ba kuma zarginta nake ba, ina magana ne da hujja. Akan daidai nake tafiya.” Ya jawo wayarsa daga aljihu, yana cewa cikin kasaita: “Zan nuna muku wasu hotuna da zasu tabbatar da cewa wannan yarinyar bata da kamun kai... tana wasa da hankalin kowa.” Ya kunna projector ɗin da ke cikin falon, wato na'urar haska bidiyo a bango Duk idanu suka koma can. Sai hotuna suka fara bayyana ɗaya bayan ɗaya... Na farko: Hoton da Zayd ke cikin ɗakin Amal, yana kwance a kanta, rigarsa a cire, ita kuma tana kare kanta tana ƙoƙarin turesa. Amal ta kalle su a ruɗe, tare da riƙe ƙirjinta... Inna cikin rawar murya ta ce, “Subhanallah!... a gidan nan?... Amal wannan ɗakinki ne kuwa?” Amal ta buɗe baki cikin kuka tana girgiza kai: “Wallahi ba haka bane! A lokacin muna kokuwa ne, yana ƙoƙarin ya ci zarafina, ban yarda ba... Allah ya sani!” Farha itama bata san lokacin da hawaye ya sulalo mata ba, ganin ɗan uwanta ne... Maleekh ya murmusa yana kallonta, ya ce: “Kokuwa? Haka ake kokuwa a kan gado har da cire kaya?” Inna ta lumshe ido, ta kasa cewa komai. Abbah kuwa ya haɗe gira, yana kallon Maleekh cikin tuhuma. Sai Maleekh ya ƙara danna wayar, ya nuna hoton na gaba. Photonta tana bakin get ɗin gida, daga ita sai sleeping dress, wani mutum yana rungume da ita ta baya, fuskarsa a rufe. Hankalin kowa ya ƙara tashi. Ammy ta ɗan ja numfashi tana cewa: “To yanzu kun gani da idanunku... Ni da bakina nace, wannan yarinya bata da tarbiya. Kyan ɗan maciji ne.” Amal ta fashe da kuka sosai, tana faɗin: “Wallahi ban taɓa yin haka ba! Wannan hoton an yi min sharrin photoshop ne! Ba ni bace wallahi! Wannan ma barawo ne!” Sai Maleekh ya sake matsa kusa da projector, ya nuna hoton na ƙarshe: Photonta tana bacci a ɗaki, wani mutum yana gefenta cikin blanket ɗaya. Maleekh yana duban kowa ya ce, “Kuma wannan fa? Hoton bacci ɗaya da saurayi. Yana wani rufe fuska don kar a gane shi. Amma ku gane abinda nake gaya muku...” Ɗakin ya yi shiru. Amal ta riƙe kanta tana faɗin: “Ya Allah!... waye yake yi min haka?... waye yake son halakar da rayuwata?...” Maleekh ya juya ya kalli kowa a cikin falon, yana murza hannunsa tare da faɗin: “To kun gani da idanunku. Wannan ce wacce nake son aura? Allah ya kiyaye! Na gode wa Ubangiji da baka sa na auri wannan karuwar yarinya ba. Mazinaciya dabbiya, wacce ta gama lalacewa! Ki sani, daga yau babu ni, babu ke! Ko da mata sun ƙare a duniya, bazan taɓa aurenki ba.” Hasken projector ya daina aiki, falon ya koma shiru. Sai Ammy ta ce cikin jin daɗi: “Dakyau ɗana, haka nake son ji. Sai yanzu ka nuna jarumtaka. Ka tuna, duk wanda ya tsarkake kansa daga irin wannan muguwar baiwa, Allah yana ƙara masa daraja.” A lokacin ne Abbah da ke zaune ya ɗago kai a fusace, ya miƙe tsaye yana huci. Cikin lokaci guda ya taka gaban Maleekh ya ɗaga hannu cikin zafin rai ya zabga masa lafiyayyen mari, sai da Maleekh ya juya... Abbah cikin fushi ya ce, “Wawa! Mahaukaci! Ka ɗauki hoton da baka san asalin sa ba, kana wulakanta mutuncin ɗan Adam haka?, Kai da bakinka kake zargi yarinya da karuwanci? Waye ya tabbatar maka da gaskiya?” Kafin Maleekh ya maido da numfashi Abbah ya sake zabga masa wani mari na biyu. Falon ya yi tsit! Maleekh ya tsaya cak, yana dafe da gefen fuska. Inna ta rufe fuska da mayafi tana kuka, Amal tana ƙara volume kuka ta ce: “Abbah, dan Allah ka barshi... Allah zai nuna gaskiya.” Abbah ya kalli Amal cikin tausayawa, sannan ya kalli Maleekh cikin fushi ya ce, “Idan akwai Allah a cikin zuciya, wallahi gaskiya zata fito. Kuma idan karya kake, wallahi wannan muryar da kake da ita zata zama la’ana a gareka har ƙarshen rayuwa!” Abbah ya juya ya fice daga falon cikin ɓacin rai, yana huci. Kowa ya tsaya yana kallon Amal da ta durƙusa, tana kuka da rawar jiki. Wani irin shiru mai nauyi ya mamaye gidan, shiru da ke cike da zafi, kunci, da rashin gaskiya. Bayan fitar Abbah, ɗakin yayi shiru kamar ba a taɓa yin magana ba. Maleekh ya tsaya yana kallon Amal cike da jin nasara, yana ɗan murmushi irin wanda yake cike da mugunta da wulaƙanci. Sannan cikin sanyi da murya mai nauyi ya furta: “Ban kwana…” Ya juyo ya fita daga falon ba tare da ya waiwayo ba. Ammy ta bi bayansa tana jan Islam da Arfat. Sai Farha da Amal kawai suka rage a wurin. Amal ta juyo ta kalli Inna, idonta cike da hawaye da tambaya, tana shirin magana. Inna ta ɗaga hannu a hankali tana girgiza kai da cewa: “Ki tsaya, ki je ki huta, Amatu. A yanzu ba lokacin magana bane. Komai ya zama ruɗani… in gaskiya ce, to gaskiya zata fito. In ƙarya ce, itama zata bayyana. Don Allah kar ki takura ni, kar ki takura kanki.”** Ta ƙarashe cikin kuka... Farha ta kama Amal da ta riga ta zama kamar gawa, jikinta yana rawa saboda zazzabi, zuciyarta kuma kamar an ta da ta daga kabari. Ta rakata zuwa ɗakinta sama. Bayan sun shiga, Amal ta faɗa kan gadonta tana lulluɓe jikinta da bargo, tana rawar sanyi. Farha ta fara zagayawa ɗakin tana neman magani a drawers. Tana cikin dube-dube ne idonta ya sauƙa kan wani ƙaramin akwatin da yake haske, mai sheƙin azurfa. A hankali ta ɗauka, ta dubi Amal da take rufe da ido kamar marar numfashi. Farha ta buɗe akwatin... Sai ga hotuna kusan guda goma na Amal da Maleekh tun suna yara. Hotunan cike da annuri, murmushi, da ƙaunar juna. A gefe kuma akwai ƙaramin sarƙa da aka ɗaure da ribbon, sannan wata takarda da aka rubuta da turanci cikin salo: “A + M = Forever. Amal and Maleekh.” Farha ta tsaya, idonta ya cika da hawaye. Tana magana a cikin zuciyarta: “Amal, ki yafe ni… Na ɗauki alkawari cewa bazan bayyana sirrinku ba amma yanzu dole. Wannan cin mutuncin da yayi miki… da yasan kece fiancée ɗinsa, da yasan kece asalin wacce yake jira shekaru da yawa… da yasan kece, da bazai wulaƙanta ki ba.” Ta ja numfashi, ta rufe akwatin a hankali, sannan ta ɗauke shi ta saka cikin jaka. Ta fita daga ɗakin da niyyar tafiya kai tsaye wurin Maleekh... Amal kuwa ta cigaba da kwanciya cikin zazzabi, tana rawar sanyi, idonta lumshe, zuciyarta na tafasa da ƙunci da kukan da ya ƙi tsayuwa. Hawayenta suna bin kan kuncinta a hankali, tana faɗin cikin zuciya: “Ya Allah… kai ka san gaskiyar zuciyata. Ka bayyana ni daga ƙaryar da duniya ta min...” 🕯️ A lokacin da Abbah ya dawo gida, ya zauna cikin fushi da tunani. Bayan wasu mintuna, sai ga su Maleekh da Ammy suka shigo. Bayan sun shigo Abbah ya miƙe cikin ɓacin rai yana nuna Maleekh da yatsa: “Wallahi, wallahi, ka zubda damarka, Maleekh! Damar da ba zata dawo gareka ba har abada. Ka sani Amatu itace damar ka! Amma ka bari ta kuɓuce maka saboda jahilci da ƙiyayya. Nine yanzu madaurin aurenta, kuma na rantse da Allah, bazan taɓa aura maka ita ba!” Ya sauƙar da numfashi mai zafi sannan ya ci gaba: “Ka yi asarar abunda kake farauta. Ka daina tunanin zaka iya dawo da ita. Kayi asara mai girma, domin lokacin ka ya wuce time done go!” Ya kalli Ammy yana daga murya: “Ke kuma! Uwar asara. Ke kike zuga shi, ke kike juyar da zuciyarsa! To ki jira ranar da zaki dawo kina kuka kina cewa: ‘Da na sani…’” Ammy ta zazzaro ido da cewa, “Akan wannan matsiyaciyar? Wallahi babu ranar da zamu yi dana sani!” Abbah ya yi mata kallon da ya cika da tsana da fushi, ya juya ya haura saman part ɗinsa yana girgiza kai. Maleekh kuwa ya tsaya, zuciyarsa cike da ruɗani, bai fahimci cikakken ma’anar kalaman Abbah ba. Ya juyo yana kallon Ammy kamar wanda ya rasa hanya. Ammy ta dafa kafaɗarsa a hankali tana murmushi mai cike da mugunta: “Ka je, yarona. Ka tafi part ɗinka ka huta. Kada ka damu da maganganun tsoho. Gaba ɗaya duniya zata fahimci cewa kai baka da laifi.” Maleekh ya ɗan ɗaga kansa ya yi shiru, ya juya cikin sanyi ya tafi part ɗinsa, amma zuciyarsa tana bugu da tambayoyi masu nauyi, "me yasa Abbah yace na rasa damar rayuwata? Wace ce Amatu to? Bayan awanni da suka wuce, Farha ta iso harabar gidansu Maleekh. Tana shiga babban falon, ta tarar da Ammy a zaune cikin shigar alfarma tana kallo. Ammy ta ɗago idonta da murmushi mai ɗauke da ƙasaita ta ce: “Ha’a, Farha kece? Lallai yau ƙamshin soyayya ya cika gidan nan.” Farha ta tsaya cikin nutsuwa, tana riƙe da jakarta wanda ƙaramin akwatin da ta ɗauko daga ɗakin Amal ke ciki. Cikin murya mai daidaito ta ce: “Ammy… Ya Maleekh yana ciki ne?” Ammy ta ɗan kwaɓe fuska, tana murmushi ta ce, “Kinzo raya soyayyarki ne? Tunda kin san ina son ki, da zan fi kowa farin ciki idan kika same shi.” Farha ta ɗaga kai a hankali ta ce: “Ba wannan ne ya kawo ni ba, Ammy.” Kafin Ammy ta sake cewa komai, ta wuce kai tsaye zuwa saman part ɗin Maleekh. Tana isa ƙofar ɗakinsa, ta fara knocking da ƙarfi. Babu amsa. Sai ta sake bugu, ta danna kararrawar ƙofa, ding… ding… ding… A cikin ɗaki kuwa, Maleekh yana can kwance cikin baccin gajiya. Ƙarar kararrawar ta shiga kunnensa a hankali, yana jan numfashi cikin jin daɗin baccin da aka tarwatsa masa.. A gigin bacci, ya miƙe da ɗan fushi, yana tafiya da ƙyar har bakin ƙofa. Yana buɗewa sai ga Farha a tsaye tana kallonsa.. Ya ɗaga girarsa cikin gajiya, ya ce da ita. “Me ya kawo ki ke kuma?” Farha ta ce cikin kwanciyar hankali: “Nazo wurinka ne.” Ya juya yana komawa ciki tare da faɗin: “Ban da lokacin ki, Farha.” Ta bishi da kallo, sannan ta ce cikin izza, “Ai nasan baka da lokaci na amma ni ma ba wai nazo ganin kyan fuskarka bane ko surar jikinka.” Ya tsaya cak, ya juyo yana kallonta da ɗan murmushi mai ɗauke da raini: “Farha, na daɗe da gaya miki cewa tsakani na dake ba soyayya. Ni ba aurenki zanyi ba.” Farha ta ƙure shi da ido, sannan ta ce cikin ɗaga murya: “Ka ci amanar wacce kake so ma balle ni! Ni asu wa? Ido ba kwalli? Wacce kake yi akanta ma baka kyale ta ba balle wata Farha a gefe! Ni yanzu ba wannan ne ya kawo ni ba don bazan tsaya ɓata lokaci na akanka ba..." Maleekh ya ɗan motsa baki kamar yana son yin dariya, amma daga ƙarshe ya ce cikin taushin murya, “Ni kike gaya wa haka?” Ta ɗaga kai, ta ce: “Eh, kai nake gaya wa. Kar ka manta tsakani na da kai babu soyayya. Don haka kada ka ɗauki komai da zafi don na gaya maka haka..” Ta kai hannu cikin jaka, ta ɗauko ƙaramin akwatin azurfa, ta jefa masa a kirji cikin ƙarfi tana faɗin: “Ga saƙon Amal.” Maleekh ya kama akwatin da sauri, ya kalle shi, sannan ya ja dogon tsaki mai cike da raini: “Mtsssww… banda lokacin ta. Kuma ba abinda zanyi da wannan abun banza.” Farha ta ɗan jinjina kai, ta ce cikin nutsuwa: “Ai dama bata buƙatar lokacinka. Tunda yanzu haka tana kwance tana fama da zazzabi, tana raye ne kawai saboda Allah. Wannan box kuma baya buƙatar lokaci, Duk san da kayi niyyar kan ka zaka iya buɗe wa..." Bayan ta gama maganar, ta juya ta nufi ƙofa cikin nutsuwa ba tare da ta waiwaya ba. Maleekh ya tsaya yana kallonta har sai da ta ɓace daga gani, sannan ya rufe ƙofar yana mamakin ta... Ya koma cikin ɗaki yana faɗi da ƙaramin murya: “"bazan tsaya ganin wani shirme anan ba... nonsense.” Ya tura akwatin can karkashin gadonsa, ya koma ya kwanta, amma wannan karon baccin ya ƙaurace masa.. Yana tunanin meye a cikin box ɗin? Sai dai girman kai ya hana shi buɗewa. Ya rufe ido, amma hoton Amal ne yake yawo a cikin tunaninsa kamar fatalwar da ba za ta bar shi ba.... *_NEXT NEXT NEXT_* asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 75 to 76 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Washegari Amal ta tashi da ƙyar, kanta na mata wani irin mungun sarawa. Kamar wanda aka jefar da ita cikin duhu, haka take ji.. Da kyar ta nufi ƙofar ɗakin tana shirin saukowa daga beni, a yayin da take shirin sauƙo wa ne wani irin hajijiya ya ɗauke ta. Kafafuwanta suka zame daga kan benin. Ta kife akan stairs tana fara gangarowa, sai da ta zo ƙasi goshinta ya bugu da ƙasa, take goshinta ya ɗan fashe... A daidai lokacin Inna ta fito daga ɗakinta, ganin Amal a ƙasa ya sa ta nufar ta da gudu, tana salati. Ta durƙusa tana girgiza ta da rawar murya, “Amal! Amal! Subhanallah! Ina ƴan aiki suke?!” Ƴan aiki suka fito da gaggawa, suka ɗago Amal suka kwantar da ita a kujerar falo. Inna ta haɗiye kuka tana ƙoƙarin ƙiran Abbah da sauri ta sanar masa.. Yana ɗaga wa ta ce. “Don Allah ka turo likita gida. Ba za mu iya kaita asibiti ba, mutane sun ji labarin dawowarta, an riga an baza maganar cewa ta gudu ne a ranar bikinta...” Cikin mintuna ƙalilan Abbah ya turo likita. Shi ma daga baya ya iso. Suka tarar da ita a sume.. Likita ya duba jikinta, ya taɓa goshinta, ya girgiza kai. “Jikinta yayi zafi sosai, da damuwa. Zuciyarta da kanta suna buƙatar hutu.” Suka ɗaga ta zuwa saman ɗakinta, aka kwantar da ita akan gadonta. Aka ɗaura mata drip, likita ya mata allurai sannan ya fice. Abbah ya zauna a bakin gadon, yana kallonta cike da tausayi... Bayan lokaci kaɗan ta motsa, ta fara buɗe ido da ƙyar. Muryar Abbah mai taushi ta fara ji a kunnuwanta, “Alhamdulillah... daughter, kin farfaɗo. Ki daina saka damuwa a ranki..." Ya ɗago ta a hankali sannan ya ɗauki abincin da aka kawo mata. "Ki ci abinci, ko kaɗan ne. Damuwa bata gyara komai.” Da ƙyar ta iya buɗe baki tana ɗan ci, Abbah da kansa yake bata a hankali. Bayan ta ɗan huta, Abbah ya ce da ita cikin tausayi, “Ki kwantar da hankalinki Amal. Ki daina saka Maleekh a zuciyarki. Ki bar komai a hannun Allah.” Amal ta kalle shi cikin hawaye, ta ce da murya mai rauni, “Abbah... shine fa fiancé ɗina...” Abbah ya dan yi shiru, yana kallon idonta cikin tausayawa sannan ya ce, “And so what? Bayan shi akwai waɗanda suka fishi komai, halayya, mutunci, da soyayya. Kina da masoya da dama, har wasu sun zo wurina suna roƙon su aurenki, nace musu ai ni mahaifinki ne zan iya aurar dake ga duk wanda ya cancanta, sai dai ki yarda da wanda kika zaɓa. Ki kwantar da hankalinki. Allah zai baki wanda yafi shi sau dubu.” Amal ta share hawayenta, ta sauƙe numfashi cikin rauni. “Abbah... duk yadda ka yanke...” Abbah ya sa hannunsa ya shafi kanta yana murmushi, “Shikenan, daughter. Kar ki damu. Allah zai ba ki farin ciki dawwamammiya.” Bayan ya gama bata kulawa yasa ta ci abinci sosai, ya miƙe cikin nutsuwa, yana kallonta da idanu masu cike da ƙauna da tsoron kada ta shiga cikin halin da zai tarwatsa rayuwarta gaba ɗaya. Bayan Amal ta kwanta... Abbah ya tsaya cak a bakin ƙofar ɗakin yana kallonta, idonta a rufe tana shakar iska cikin rauni. Ya ɗan numfasa, ya fita a hankali. A falo ya tarar da Inna tana zaune da hijabi a jikinta, hannunta riƙe da tasbihi tana kan sallaya.. Abbah ya zauna kusa da ita, ta juyo tana kallonsa ta ce “Alhaji... ni kam zuciyata ta kasa kwanciya. Wannan yarinyar ta rame kamar wanda ake tsotse jininta. Idan ka kalle ta, ba kamar Amal ɗin da muka sani ba.” Abbah ya dafa kansa, ya girgiza kai. “Ni ma haka nake gani, Mama. Wannan abun da ya faru ya girgiza ta sosai. Amma tunda ta dawo gida, in sha Allah zan kula da ita da kaina. Zuciyarta tana buƙatar natsuwa, ba tambayoyi ko zargi ba.” Inna ta share hawayen idonta ta ce: “Allah Ya kyauta, amma ka dai lura. Wannan kukan zuciya da take boyewa yana da hatsari. Ko da yake ban san me ya faru da ita a lokacin da ta ɓace ba, amma akwai wani abu da ta ɗauko a ranta daga can.” Abbah ya ja numfashi mai nauyi, sannan ya ce, “Kin faɗi gaskiya. Har yanzu ban gane yadda ta ɓace ba, balle yadda ta dawo. Amma ko meye sirrin nan, lokaci ne kaɗai zai bayyana mana. Abin da nake so yanzu shi ne ta rayu lafiya...Shi kuma Maleekh zanyi maganinsa domin duk saboda shi ta kasa kwantar da hankalinta..” Ya ɗan yi shiru, yana kallon gefen sama kamar yana neman karfin gwiwa daga sama. “Mama, ki kula da ita sosai. Kada ta bar gida ko da minti ɗaya. Zan saka masu tsaro biyu su kula da ƙofar gida..” Inna ta gyada kai, ta ce. “Toh, Allah Ya taimake ka. Zan kula da ita kamar jaririya...” Suka yi shiru na ƴan dakikoki. Inna ta ɗan ce da muryar kuka. “Allah Ya dawo mana da jikata yadda take da…” Abbah ya amsa da “Amin” cikin murya mai sanyi da ƙasaita kamar wanda yake ƙoƙarin ɓoye wani abu a ransa. Sai ya miƙe, yana kallon beni inda ɗakinta yake. Wani irin shiru ya mamaye falon.. Cikin dare. Iskar sanyi tana kaɗawa daga taga, labulen ɗakin yana motsawa a hankali. Wutar ɗakin ta yi lumm, lamp mai green light dake gefen gado ce kaɗai ke bada haske, tana haskaka fuskar Amal da ta kwanta cikin shiru. Inna ta fito daga ɗakinta bayan ta idar da sallar tahajjud. Zuciyarta ta kasa samun natsuwa, saboda tunanin yarinyar nan da take can ɗakin ta.. Da taka-tsantsan ta ɗauki fitilar hannu sannan ta nufi sama. Ta tura ƙofar ɗakin Amal a hankali, ƙamshin turaren ɗakin ne ya buge ta. Ta tsaya a bakin ƙofa tana sauraron numfashinta. Sai kuma taji kamar Amal tana sambatu a hankali, tana magana cikin bacci. Da sauri Inna ta ƙaraso kusa da gadon, ta durƙusa, ta ji Amal tana faɗin cikin rawar murya: “Maleekh... dan Allah ka daina gudu na... kada ka cutar dani... na rantse... ka yarda dani, dan Allah ka yarda dani, wallahi inasonka...” Sai hawayenta suka fara gangarowa a kan pillow, tana juyi a gadon kamar wacce ke gudun mafarki mai ciwo. Inna ta dafa kafaɗarta a hankali tana lallashinta: “Shh... shh... ya isa Amatu...ki kwana lafiya, ki huta. Komai zai yi dai-daita in sha Allah.” Amal ta ɗan buɗe idonta, kamar wacce ta farfaɗo daga mafarki, amma sai ta sake runtse su, tana fitar da numfashi mai nauyi. Inna ta zauna gefen gadon, ta dafa kanta. Hawayen tausayi suka cika idonta. A hankali ta fara karanta mata surar Yasin, tana shafa kanta bayan kowace aya. Lokacin da ta gama, ta jingina da jikin gadon tana kallon Amal da ta koma bacci cikin shiru. A ranta ta ce, “Ya Allah, idan akwai gaskiya a cikin soyayyarsu, ka mayar musu da zaman lafiya. Ka tabbatar da adalci, ka kare jikata daga zafin ƙaddara.” Ta sake share hawayenta, ta miƙe cikin nutsuwa, ta rufe mata ƙofa, sannan ta fita a hankali tana ƙiran sunan Allah har ta sauƙo ƙasa. A cikin ɗakin, fitilar ɗaki ta cigaba da haskaka fuskar Amal, fuskar da hawaye suka shafe, amma a gefen leɓenta akwai ƙaramin murmushi kamar tana jin wani a zuciyarta… ☆☆☆☆☆ Cikin babban office ɗin Abbah, mai cike da kayan alfarma, framed certificates, tambarin ƙasa a bango, da ƙamshin turaren oud mai sanya nutsuwa. Abbah yana zaune a kan babban kujerarsa mai juyi, yana kallon wasu takardu.. A gefe guda, jami’in sa na tsaro ya kawo masa saƙon cewa Zayd ya iso. Abbah ya ɗaga kai kaɗan, ya ce da shi: “Ka shigo da shi ciki.” Bayan mintuna ƙofar ta buɗe, Zayd ya shiga cikin ladabi, yana sanye da suit mai kyau. Ya tsaya yana gaishe shi: “Assalamu alaikum, barka da aiki Abbah.” Abbah ya ɗaga kai kaɗan, ya amsa da murya mai ƙarfi: “Wa’alaikumus salam, Zayd. Zauna.” Zayd ya zauna da ɗan ɗoki, yana dafe ƙafarsa da hannunsa, kamar wanda ba ya jin daɗin zama a wuri ɗaya.. Abbah ya jingina da kujerarsa, ya ɗan dubi Zayd sama da ƙasa, sannan ya ce cikin nutsuwa da nauyin murya: “Ya Daddyn naku? Har yanzu yana kasar nan?” Zayd ya amsa cikin girmamawa: “A’a Abbah, ya koma London. Yanzu haka yana duba harkokin business ɗinsa can.” Abbah ya jinjina kai sannan ya ajiye takardun hannunsa gefe. Sai kuma ya ɗan yi shiru kafin ya ɗaga ido ya dubi Zayd kai tsaye: “To, bari muje kai tsaye. Ina tambayarka, meye tsakaninka da Amatu?” Zayd da yake zaune ya ji kirjin sa ya buga da karfi. Ya ɗan dafe ƙirjinsa, ya kasa kallon Abbah a ido. Sai kuma ya ce da sanyin murya, “Abbah, gaskiya tsakaninmu... wallahi ina sonta ne. Kuma wannan son ba na wasa ba ne, son gaskiya ne. Ba na neman cutar da ita.” Abbah ya kalle shi cikin tuhuma, sai kuma murya ta canza: “Kana sonta ne, sannan kake neman ta da lalata? Kake neman cin zarafinta?” Zayd ya sunkuyar da kansa, ya kasa cewa komai. Abbah ya ɗan tafa hannuwansa biyu cikin takaici. “Zayd! A duk lokacin da kake neman kusantar ta sai kayi hoto ka turawa Maleekh? Me yasa? Me kake nema?” Zayd ya girgiza kai: “Wallahi Abbah, banyi haka da niyyar cuta ba. Sau ɗaya ne, lokacin da muka haɗu a waje na rungumeta ta baya, sai wani daga nesa ya mana hoto... amma ban sake ba!” Abbah ya ce cikin ɓacin rai: “To wa ya je ya kwana da Amal a gadonta ba tare da ta sani ba? Waye?!” Zayd ya yi shiru, jikinsa ya soma rawa. Abbah ya daka masa tsawa da ƙarfi: “Ina tambayarka Zayd! Waye ya kwana da ita?!” Zayd ya ɗan girgiza kai cikin firgici: “Abbah... ni ne... amma wallahi bana nufin cutar da ita. Na tura wa Maleekh ne saboda ina son shiga tsakaninsu. Ina sonta ne Abbah, hakan yasa...” Abbah ya datse maganarsa da murya mai nauyi: “Kana sonta ne amma ka zubar mata da mutunci? Kasan hoton nan idan ya fita waje ya labarin zai kasance?. Ka san irin abin da kayi kuwa?” Zayd ya fara hawaye yana cewa: “Abbah dan Allah kayi haƙuri, kayi haƙuri...” Abbah ya ɗan jingina da kujera, ya runtse ido cikin takaici. “Saboda baka son aurenta da Maleekh ne ka sace ta, ko?” Zayd ya zabura da sauri yana girgiza kai: “Wallahi tallahi, Abbah, ban sace ta ba! Ban san inda ta je ba. Na rantse da Allah ban da hannu a ɓatanta ba!” Abbah ya ɗaga masa hannu sama da murya mai cike da iko: “To idan na gano kana da hannu fa, Zayd? Idan na tabbatar da kai ne fa?” Zayd ya share hawayensa yana cewa da rawar murya: “To Abbah kayi mun duk abinda ka ga dama. Kasa a harbe mun kwakwalwa, bana buƙatar jinƙai idan hakan gaskiya ce...” Abbah ya jinjina kai, sannan ya ce cikin sanyin murya. “To ka sani, daga yau na shiga tsakanin ka da Amal. Ba ka da izinin kusantar ta, ko ta hanyoyi, ko ta magana, ko ta waya. Ni zan kareta daga sharrinku.” Zayd ya sauƙe kansa, yana magana a ƙasa ƙasa: “Na fahimta Abbah... shikenan.” Ya miƙe, ya juya ya fita da sauri cikin wani yanayi na kunya da damuwa. Abbah ya bishi da ido har ya fice, sannan ya jingina da kujerarsa yana hura numfashi mai nauyi, ya ce a hankali: “Allah ya kare yarinyar nan daga sharri.. Son zuciya sai ya lalata ku saboda rashin hankalinku....” 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 Bayan sati biyu, Amal ta samu sauƙi daga ciwon jikinta, amma ba ta samu sauƙin zuciya ba. Da safen nan tana zaune a dinning area tare da Inna suna breakfast cikin natsuwa. Sai ga wayarta ta fara ringing. Ƙiran da ya bayyana a fuskar wayar ya sa jinin jikinta ya tsaya cak. “Maleekh…” ta furta a hankali da idanu a zazzare. Inna ta kalleta, ta ɗan ɗaga gira tace: “Meya faru ne, Amal? Waye ke kiranki haka duk hankalinki ya tashi?” Amal ta kalli Inna da fargaba, muryarta na rawa: “Maleekh ne Inna… wayarsa ce!” Inna ta ɗan ɗaure fuska: “To uban me zai miki? Kina jin tsoro saboda yau ya ƙira ki?” Amal ta ɗan girgiza kai, muryarta a sarke: “Ban sani ba Inna… amma kamar zuciyata na sanar min akwai wani abu…” Ta kasa ɗauka har wayar ta katse. Bai jima ba sai ta sake ringing karo na biyu. Ta ɗan matsa kusa da Inna, ta ce a tsorace: “Wallahi bana son ɗauka, Inna. Yanzu da yake ƙirana, ji nake kamar yana ƙirana zuwa mutuwata ne…” Inna ta miƙe ta ɗauki jug ɗin shayi tana zubawa a ƙaramin cup domin ƙarawa, ta furta, “To ki ɗaga ki ji mai zai ce. Ba kowa ke ƙiran mutum sai da dalili.” Amal ta lumshe idanu, ta ja numfashi mai nauyi sannan ta ɗaga wayar. Muryarsa ta fito daga can ƙasa, mai cike da iko: “Ina nemanki a office ɗina… yanzu.” Sai wayar ta yanke. Amal ta kalli Inna cike da mamaki: “Inna wai yana so naje campanynsa.” Inna ta ɗan ɗaga kai: “To ki je. Ki natsu, kar ki ji komai. Ki je ki fuskance shi kamar yadda kika saba.” Bayan breakfast, Amal ta shirya cikin kayan office masu sauƙi. Tana fita daga gida ta tare napep, saboda yanzu ba ta da mota a hannunta. Tafiyar ta ɗauki awa biyu kafin ta isa CashTalk. Bayan ta shiga, ma’aikata suka fara tarar ta da murmushi da girmamawa: “Good morning ma’am!” “Welcome back ma’am!” Ta mayar musu da sallama cikin ladabi, tana murmushin dole... Ta shiga reception, sannan ta shige elevator ya kai ta bene na takwas. A hankali ta nufi ƙofar office ɗin CEO Maleekh.. Tayi knocking sau biyu, daga ciki aka ce: “Come in.” Ta buɗe ta shiga. Ta gan shi zaune a kujerarsa, fuskarsa a ɗaure yana aikin danna computer, ba tare da ya kalleta ba. Ta tsaya a bakin ƙofa, ta ce cikin ladabi: “Gani…” Shiru. Ya cigaba da duba system ɗin kamar ba wanda ya shigo. Mintuna goma cif tana tsaye, jikinta har ya fara rawa domin har yanzu jinyar bai gama sakinta ba. Sai daga bisani ya furta cikin izza: “Baki iya gaisuwa bane?” Amal ta ɗan lumshe ido, ta ce a hankali: “Ina kwana…” Ya ɗan ɗaga kai, yana murmushin gefen baki: “A wannan company kin taɓa jin ana gaisuwa da Hausa?…” Ta ɗan ja numfashi: “Good morning, sir.” Ya amsa da gajeriyar kalma: “Fine.” Sai ya ɗaga kai daga system ɗin, yana kallonta kai tsaye: “A matsayinki na assistant CEO, me ya hanaki zuwa wurin aiki tsawon sati biyu bayan dawowarki daga yawon shalholiyarki?” Amal ta haɗiye yawu cikin rawar murya: “Banda lafiya ne, sir…” Ya ɗan lanƙwasa wuya: “Awa kika sanar?…” Ta ɗan sunkuyar da kai: “Sorry, sir…” Ya yi dariyar raini, yana murmushin mugunta: “Ba haka kawai ba, Amal. Akwai abubuwan da nake son sanar miki. Ba sirri bane, kuma ba ɓoye miki nake ba, domin ba tsoronki nake ji ba.” Ta ɗan ɗago kai cikin ƙarfin hali: “Ina sauraronka.” Ya miƙe daga kujerarsa, yana tafe a hankali har ya tsaya kusa da taga, yana kallon waje. “Oh, sorry ban baki izinin zama ba ko? Amma ba buƙatar haka.” Sai ya juyo da idanu masu kaifi yana mata wani irin kallo sannan ya ce: “Kin ma san waye Maleekh Cash Bank kuwa?” Amal ta ɗan motsa baki: “Na san shi tun kafin na kawo wannan matsayin. Hasali ma saboda shi na zo Abuja.” Ya gyara murya: “Good! Fatan baki manta irin ɗabi’unsa tun farkon haɗuwarki da shi a Kaduna?” Amal ta ce cikin mamaki: “Me ya kawo wannan maganar?” Ya ɗan murmusa, yana matsowa kusa da ita kadan: “Ina so ki tariyo baya. Lokacin da kike ƙazamar yar jarida a ƙaramar gidan rediyo Rayuwa FM Kaduna… kina sanye da kodadden kaya, kina ta surutai, kina cika mutane da maganganun banza.” Sai ya juyo da ƙarfi yana kallonta kai tsaye: “Kin manta irin kalaman ki a rediyo? Ke ce kike cewa Maleekh Cash Bank mai girman kai ne, mai lalata zuciya, mai sayar da zuciyar talakawa and so so so so!” Amal ta tsaya cak. Hankalinta ya soma rikicewa. “Me ya kawo wannan yanzu?” Ya cigaba da magana kamar wanda yake karanta rubutu daga zuciya: “A lokacin kin zubar mun da mutunci. A gaban mutane kika raina ni, kika ba ni suna mai tozarci. Amma na shiga zuciyarki domin baki soyayyata… na nuna miki, amma kika mayarni mahaukaci, kika sa mutane suna mun dariya. Har kina da bakin cewa ‘idan da gaske yake sona, ya fito ya furta soyayya a gaban duniya' shin ba haka kika sanar wa ƙanwata Aisha ba?.." Ya ɗan murmusa sannan ya cigaba da faɗin. “Na fito, Amal. Na furta soyayyata a gaban duniya. Amma me kika rama mun? Mari! A gaban dubban mutane, cin mutunci da tozarci kala-kala… Na yi siyayya na aika gidanku amma haka kika rabar da kayan wa mutanen unguwa sannan kika riƙe kwalar rigata kika fitar dani daga gidanku, kika yi mun korar kare a gaban ƙazaman mutanen unguwar, da girma na da mutunci na da daraja ta..." Ya juya ya kunna computer ɗinsa, ya janyo fayil, sai ga video clip ɗin lokacin da Amal ta mare shi a Kaduna. A cikin video ɗin, muryarta tana faɗin: “Join yourself, Maleekh! Bana sonka kuma ba zan taɓa sonka ba!” Ya juyo ya nuna mata screen ɗin. “Kin san irin zuciyar da Maleekh yake da ita kuwa?” Amal ta kasa magana, ta jingina da bango, numfashinta na sarkewa... “Ni ba na barin mutum har sai na ɗau fansa. Rana dubu ta ɓarawo, rana ɗaya ta mai kaya. Na ce sai na rama abinda kika mun… sai na sa zuciyarki ta ƙone kamar toka...” Ya ɗan yi shiru, sannan ya furta da murya mai zurfi: “Na rantse sai na yi wasan ball da rayuwarki, Amal. Sai kinyi kukan da baki taɓa yi a rayuwarki ba…” Amal ta kalle shi cikin tsoro, tana rawar murya: “Me kake nufi da haka, Maleekh? Me kake shiryawa?” Ya yi wani irin dariya mai cike da ciwo, yana tafiya kusa da ita: “Kin tuna kalmar da kike ta faɗa a baya? Tafiya ɗaya ake da yaro mai ji da kansa…” Amal ta ɗan ja da baya. Ya ɗan ƙarasa yana furta cikin nutsuwa: “Broken heart shine maganinki, Amal.” Ta ce cikin zabura: “Me kake nufi?” Sai ya rufe computer sa, yana murmushin mugunta: “Hotunan ki da Zayd… duk ni na ƙirƙire su.” Amal ta tsaya cak, idonta ya faɗa, jikinta ya yi sanyi kamar an jefa ta cikin ruwan sanyi. Maleekh ya ɗan tafa hannayensa a hankali yana murmushin mugunta kafin ya ce, “Duk hotunan da kika gani… waɗanda suka zubar miki da mutunci, suka karya girmanki a idon iyalai, ni ne na tsara su. Dan ma nayi miki da sauƙi da ban bayyana a duniya gaba ɗaya ba, but nasan darajar mace bazan yi haka ba..” Amal ta kalle shi da idanu masu cike da ƙuna, kamar mai son tabbatar da abin da kunnuwanta suka ji. Ya matsa kusa da ita, ya furta da ƙasaita, “Ni na sa Zayd ya tura min hotonku lokacin da nayi masa bayani kan irin wulakancin da kika yi min. Lokacin da kika tarar da shi a ɗakinki, har ya kwantar da ke a gado, ni ne na shirya komai. A lokacin kuma, na shigo na tarar da ku… domin na gani da idona da abinda zuciyata ke nema.” Numfashinsa ya ƙara nauyi, idonsa ya yi duhu kamar wanda yake daɗa jin daɗin azabtar da ita. “Hoton da kika gani kina bacci? Ni na aika Zayd ya shiga ɗakinki ya kwanta kusa da ke. Aka ɗauka.... Sannan lokacin da kika fito da sleepy dress ɗinki, kina duba wanda ya shigo muku gida, ni na sa shi ya zagaye ki daga baya, ya rungume ki. Aka ɗauki hoto. Komai tsarona ne, Amal. Fansata ce...” Amal ta ɗago a ruɗe, jiki na rawa. Idonta na neman fita daga socket... Duk yana cikin ɗaukar fansa ta... Sannan na nuna miki soyayya ne saboda ki shiga jikina har na yi broken dinki. Na amince da aurenki sannan a ranar walimar bikin kafin washegarin aurenki dani nasa aka sace ki..." A wannan lokacin Amal ta dago a zabure tana kallonsa a ruɗe.. Ya ce "Yess! Aikin gama ya gama tinda na gama aikin dana tsara kuma ya tafi yanda nake buƙata... A lokacin da na sa a sace ki na kasance a wurin... kuma duk lokacin da zanje ana rufe miki fuska sannan idan zan tafi na sumbace ki yanda zan bar miki signing amma kin kasa fahimta, hakan yasa na ƙira ki yau domin na fitar ki daga duhun da kike ciki..." Hawaye suka fara gangaro mata. Muryarta na rawa ta tambaye shi cikin rauni: “Kenan duk soyayyar da kake nuna min… duk na ƙarya ne?…” Ya yi murmushin gefen baki. “Of course…” Kalmar ta bugi kunnenta kamar wuƙa. Ta girgiza kai a hankali, hawayenta na zuba kamar ruwan sama. “Amma ka cuce ni, Maleekh… ka cuce ni sosai.” Ya ɗan yi shiru, sannan ya furta cikin sanyin murya kamar kankara: “Haka nake son ji.” Cikin zafin rai ta ɗago hannu zata mare shi, cikin sauri ya cafke hannunta da ƙarfi. “Kin taɓa yin wannan a baya amma yanzu, hannunki ba zai ƙara taɓa fuskata ba. Idan kika yi kuskuren haka, a take zan yanke miki hannu...” Ya tura ta baya. Amal ta yi saurin bugan kirjinsa tana kuka, tana furta cikin ƙunci da hawaye: “I love you, Maleekh! I love you! I love you!…” Tana dukan kirjinsa tana kuka tare da furta "I love you , I love you, I love you.." Kamar mahaukaciya take dukan kirjinsa da hannaye biyu, muryarta ta karye wa, zuciyarta na ƙuna. Cikin fushi ya riƙe hannuwanta, yana kallonta cikin tsantsar tsana. “I hate you, Amal.” Ya hankad’a ta da ƙarfi ta faɗi ƙasa. Shiru ya biyo baya, a lokacin kukan da ke fita daga bakinta ya koma dariya.. A hankali ta fara dariya… dariyar da ke cike da zafi da hauka. “Hahahaha! Hahahaha!! Hahahaha!!! Hahaha!!!!” Tana nuna shi da yatsa tana dariya, ta miƙe tare da juyawa ta fita daga office ɗin tana dariyar hauka. Maleekh ya tsaya yana kallonta, zuciyarsa na bugawa, amma fuskarsa na nuna babu ɗan tausayin da ya rage... Har ta sauƙa ƙasa, tana wannan dariyar, ta wuce reception. Ma’aikata suka tsaya kallonta da mamaki. Duk da ganin yanayinta, ta wuce tana dariya.. Haka ta fita daga campany tana wannan dariyar, mutanen titin suka tsaya kallonta kowa yana nuna ta yana faɗin, “Wayyo Allah, me ya samu Amal?…” Haka ta riƙa tafiya tana dariya cikin hawaye, kamar mace da ta rasa komai a duniya. Amal tana tafiya a titi tana dariya kamar wacce ta tsinci kanta a tsakanin dariya da kuka. Tayi tafiya mai nisa daga campanyn, kafafunta sun gaji, sun rasa inda zasu nufa. Haka take tafiya tana ta dariya, tana ta waige-waige cikin duhun rana. Cikin gari ta hangi wani ƙaramin restaurant a gefen titi, tsohon wurin cin abinci ne, cike da wasu samari masu shaye-shaye, wasu suna dariya, wasu suna ta tafka magana da ba kowa ke fahimta ba. A hankali ta ƙarasa wurin, ta zauna a kan wani kujerar roba mai datti, ta kifa kanta a kan table. Dariya ta tsaya ta koma kuka. Kuka take sosai, da ƙarfi, kamar ranta zai fita... Wani daga cikin masu shaye-shaye, wanda idonsa ya cika da ja saboda maye, ya matsa kusa da ita yana buga bayanta a hankali. “Yar uwa, ya kika tsinci kanki a cikin damuwa haka? Ki sha wannan kwayar, duk damuwarki zata tafi,” ya furta yana mika mata wasu ƙwayoyi guda uku da ruwa a kwalba. Amal ta ɗago kai, tana kallonsa da idanu marasa hangen komai. Bata yi tunani ba ta karɓi ƙwayoyin, ta zuba su gaba ɗaya a baki, ta kora su da ruwa. Sai ta ja numfashi, ta jingina, idanunta suka fara lumshewa a hankali. Wanda ya bata ƙwayar ya tafi yana dariyar maye, yana surutan da babu wanda ke fahimta. Can bayan ƴan mintuna, Amal ta tashi da ƙyar. Ta fara tafiya a hankali, tana rikicewa, tana tangal-tangal. A lokacin maganin ya fara aiki. Jikinta ya fara rawa, idanunta suka ɗauki duhu, zuciyarta tana bugu da gudu kamar ana rera mata waƙa a ciki. Ta shiga tsakiyar titi tana tafiya ba tare da sani ba. Motoci suna yin horn ɗin tsoro, napep suna tsayawa cikin firgici. Ta fara bugu da jikin mota, wani lokaci ta ƙetare titi, wani lokaci ta dawowa da baya... Wurin ya zama hayaniya, kowa na kallonta, wasu suna maganar cewa "yaushe ta fara shaye-shaye kuma?..", wasu na cewa, “Wayyo Allah, mace ce fa! Ku taimaka mata mana!” A dai-dai lokacin motar Maleekh ta iso daga nesa. Shi kansa sai da ya taka burki da sauri saboda tana gab da shiga gaban motarsa. Ya hango ta da kyau, amma zuciyarsa ta ƙi yarda ya taimake ta... A hankali ya furta “Ba zan iya kasancewa da ita ba…” Sannan ya ja motarsa ya wuce cikin sauri, bai tsaya ba.. Amal kuwa ta ci gaba da tafiya a tsakiyar kwalta, tana murmushi tana faɗin, “I love you, Maleekh… I love you…” idanunta na cike da hawayen maye da ciwon rai. A wannan lokacin ne wata mota ta tsaya a gefe. Farha, wacce ta fito daga supermarket tana ɗauke da leda, ta tsaya cak da ganin Amal. Da gudu ta ƙarasa, tana ɗaga hannu tana tsayar da motocin da ke kusa da Amal. “Please! Please ku tsaya! Ku tsaya mana!!” tana magana cikin tsoro. Ta shiga tsakiyar titi da gudu, ta kama Amal tare da jan yo ta gefe da ƙarfi. Ta rungume ta tana faɗin, “Subhanallah! Amal! Me ya same ki haka? Subhanallah! Ki dubeki mana! Me kike yi a tsakiyar titi haka?!” Amal ta ɗago kai a hankali, idanunta a rufe, numfashinta ya rikice. “I love you Maleekh … yana sona… yana ƙi na…” Ta furta cikin rikicewa kafin jikinta ya sake a hannun Farha... Farha ta girgiza kai cikin tashin hankali. Ta riƙe Amal sosai sannan ta buɗe murfin motarta, ta saka Amal a ciki. Ta zagaya cikin hanzari ta shiga, ta tada motar. Kai tsaye gidansu Amal ta nufa, zuciyarta na bugawa, hannayenta na rawa a kan sitiyari. “Allah ka kiyaye… Amal, ki buɗe idonki dan Allah… ban ga dalilin da zai sa ki fara shaye-shaye ba, muma da muke sha addu’a nake Allah ya yaye mun…” Ta faɗi cikin murya mai rauni, tana hawaye har zuwa ƙofar gidan Amal... A ƙofar gidan suka tarar da Abbah ya fito zai shiga motarsa, tare da Inna da wani mutumi, Mutumin ya kawo musu gulmar cewa 'Ga can Amal tayi shaye-shaye tana ta tangad'i a tsakiyar titi... Motar Farha ta parker. Ta fito da sauri sannan ta buɗe back seat ta ciro Amal da har yanzu tana ta surutai.. Abbah da Inna ganin an fito da Amal ne yasa suka nufi wurin da sauri. Abbah ya riƙe ta yana faɗin "Me ya faru da ita haka?.." Farha ta ce, "Wallahi Abbah nima na fito a supermarket na zanyi gida na hango ta a tsakiyar titi tana maye..." Amal kuwa ba abin da take faɗi sai "I love u Maleekh. I love u Maleekh..." Inna ta ce, "Yanzu wancan mutumin yazo yana sanar mana.." Abbah ya ɗaga ta suka shige gida. Kafin Farha ta shiga sai da ta tsaya yiwa mutumin da ya zo magana. "Ka iya kawo tsegumi amma baka iya taimaka mata ba a lokacin, na naushe ka munafiki..." Mutumin ya wuce yana faɗin. "Na fi ki dabanci alkur'an.." Ya kama hanya ya tafi, itama ta shige tana zaginsa. Ga security a tsaye wanda Abbah ya ajiye su domin tsare gidan, duk suna riƙe da bindigu da bakaken suit... *NEXT NEXT NEXT* asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 77 to 78 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Abbah ne ya shigo ɗakin Amal ya kwantar da ita, sai ga Inna da Farha sun biyo bayansa, hankalin kowa yana kan Amal wacce take ta sambatu... Kallon Amal kawai yake, yana jin kalmar “Maleekh” na fitowa daga bakinta... Bacci ne ya ɗauke ta na ɗan mintuna daga bisani cikin bacci, ta fara faɗin “Maleekh… meyasa ka min haka?... ka sani ina sonka... dan Allah ka janye fansar nan… muyi aure, muyi zaman lafiya…” Tayi shiru na ɗan lokaci, sai kuma ta ja numfashi da ƙarfi tana ci gaba da sambatu. “Maleekh ya ɗauki fansar abubuwan da na masa a Kaduna… ya sa Zayd ya yi hoto dani ta hanyar da bata dace ba… shine yasa aka sace ni… ya rushe aurenmu… rayuwata bata da amfani, kuma ina son sa fa…” Ta juya gefe, ta ɗaura hannunta a kan ƙirji kamar mai jin ciwon da ya daɗe yana taruwa a zuciya. Abbah ya tsaya cak, idonsa na kan Amal, zuciyarsa na bugawa da karfi kamar ana danna ganguna. Ya ja numfashi mai nauyi, ya furta da kyar: “Fansa kuma?... Wannan yaron ya haukace ne?...” Inna ta share hawayenta, Farha kuwa ta zame gefe tana jin tsoron abin da zai biyo baya. Amal ta lumshe idanu ta yi shiru, bacci ya lullube ta gaba ɗaya. Abbah ya jinjina kai, ya furta cikin takaici: “Dole Maleekh ya mata wani abu… amma me ya mata?... Wani irin fansa zai ɗauka akan macen da ta baka ƙauna?” Ya miƙe tsaye da hanzari, ya fita ba tare da ya kalli kowa ba... Kai tsaye Abbah gida ya nufa.. A lokacin da Abbah ya shiga falonsa, ya tarar da Islam, "Ke je ki ƙira mun Maleekh. .." Islam ta ga yanayinsa gaba ɗaya ya sanja, ta zaro ido. Ba tare da wata tambaya ba, ta hau sama domin ƙiransa.. Knocking ɗaya biyu ya buɗe... “Yaya Maleekh… Abbah yana ƙiran ka, amma… da fushi!” Maleekh wanda yake tsaye a bakin ƙofa yana zukar shisha, ya yi murmushin rainin hankali. “Abbah da fushi? To wannan ai ba sabon abu bane.” Ba tare da ya koma ciki ba, ya sauƙo sanye da gajeren wando da singlet, yana ɗauke da shisha a hannu. Yana shiga falon, ya zauna kan kujera yana shan shishar sa cikin nutsuwa. Abbah na zaune a gefe yana kallonsa da wani irin yanayi mai nauyi. Cikin tsawa ya ce: “Zaka ajiye wannan banzar abin ko sai na ci maka mutunci yanzu?! Shashashan yaro marar tunani!” Maleekh ya tsaya, yana kallon gefe, shishar na fitar da ƙamshi mai daɗi...Ya ajiye a gefen ƙaramin table. Ammy ta fito da gaggawa tana tambayar, “Subhanallah! Me ke faruwa haka?!” Abbah ya miƙe tsaye da hanzari, yana nuna Maleekh da yatsa: “Me ka aikata wa Amal? Me ka mata? Ka bani amsa kafin na ɗauki mataki!” Maleekh ya ɗan yi shiru, yana mai duba gefe kamar wanda ya gama komai a zuciya. Sai ya ce da murya ƙasa-ƙasa “Na gaya mata gaskiya ne.” Abbah cikin fushi ya ce, “Gaskiyar me, Maleekh?!” Maleekh yana kallonsa kai tsaye: “Gaskiyar ɗaukan fansa da nayi akanta.” Da sauri Abbah ya miƙe ya zo yanda yake zaune yasa hannu ya ɗauki sumar kansa da ƙarfi, yana ɗaga murya cikin fushi kamar zai fashe. “Fansa! Fansa! Fansa!! Wani irin fansa ne haka, kai wani irin mutum ne? Marar mutunci kawai! Da kanka kake lalata rayuwar macen da kace kana so? Kuma marainiyar Allah? Ka sani sai Allah ya saka mata..” Ya ƙare maganar tare da fincikar gashin kansa da ƙarfi, Maleekh ya ɗan yi ƙara yana riƙe da kansa. Ammy ta ruga ta riƙe Abbah, tana faɗin: “Don Allah ka sassauta murya! Me yasa zaka ɗauki irin wannan zafi akan soyayyar su?!” Abbah ya nuna su da yatsa, idonsa na cike da hawayen takaici: “Idan wani abu ya faru da yarinyar nan, wallahi tallahi, saina saka a ɗaure ka! Kayi shekaru a prison kafin ka sake ganin rana!” Ya juyo ya ficewa daga falon, ƙafafunsa na dukan tiles cikin ƙarfi. Ammy ta zauna kusa da Maleekh tana rarrashinsa, tana share hawayen da suka zubo masa... Ba komai ne ya sa shi yin hawaye ba sai don Amal tasa mahaifinsa yana ɗaga masa murya kuma har da hawaye, ya rasa meyasa haka.. Ammy ta ce, “Kai ne ka jawo wannan, Maleekh … kasan sun riga da sun asirce mahaifinka. Bazai taɓa ganin laifin Amal ba. Kuma me ka mata ne?..” Maleekh ya dauƙi shishar a gefe, idonsa ya cika da hawaye, amma bakin ya ƙi furta komai. Sai kawai ya ce cikin sanyi: “Ba zaku taɓa gane menene fansa ba… sai na gama...” Shima ya miƙe ya bar falon, kai tsaye part ɗinsa ya nufa.. 🌹🌹🌹🌹 Kwana biyu kenan da dawowar Amal cikin hayyacinta, amma dai ta kasa furta komai tinda ta farka, kamar wacce tayi mutuwar zaune... Idonta kawai ke buɗewa, amma kalmarta ta ɓace tamkar zuciyarta. Inna ta zauna a gefenta tana magana, tana kuka, tana dariya don ta motsa ta amma Amal kamar mutum-mutumi. Inna tana hawaye ta ce: “Amatu, ki ce kalma ɗaya kawai… ki ce ‘Inna’, ko ‘ruwa’ ma! Me yasa haka! Me yasa kike yi min haka, Amatu?” Shiru. Hawaye kawai ke sauƙa daga gefen idon Amal, amma baki ko motsawa bai yi. Abbah ma ya zo ya zauna gefenta, ya yi mata maganar duniya, amma bata ko ɗago kanta ba. Har sai da ya lumshe ido, ya ce cikin tausayawa: “Duk irin laifin da kika aikata, ki yafe wa kanki. Rayuwa ba haka take ƙarewa ba, daughter…” Shiru. Kamar da gwinki ake magana... Farha ta zo ta zauna, ta riƙe hannunta tana mata magana amma Amal bata ma kallonta ba. 🕯️ Sati Guda tana cikin Shiru, ko sau ɗaya Amal ta kasa furta kalma ɗaya.. Kowa yana cikin tsoro da fargana har sati guda. Amal bata yi magana ba, bata cin abinci, bata shan ruwa. Kowa cikin gidan hankalinsa ya tashi. Likita ya zo, ya duba ta sannan ya ce: “Babu wata matsalar jiki. Amma zuciyarta ta ƙone. Wannan shiru ba rashin lafiya bane, kin magana ne saboda raunin zuciya. Idan har ba a samu wanda take ji ya motsa ta ba… zata iya faɗa cikin haɗari.” Wannan maganar ya bugi zuciyar Abbah sosai. Da hanzari ya miƙe daga kujerar, yana faɗin cikin tsawa: “To tunda kai likita baka da mafita, ni zan nema da kaina! Wanda ya jefa ta cikin wannan halin, shi zai fito ya gyara!” A wannan ranar Abbah ya ƙira Maleekh akan yazo cikin ƴan mintuna... Maleekh kwata-kwata baya ƙaunar zuwa gidansu Amal amma ba yanda ya iya.. Da daren, gidan yayi shiru. Sai hayaniyar zuciyar kowa ke yawo. Sai ga Maleekh ya shigo cikin gidan yana shan shishar sa kamar ba komai ya faru ba. Kallon raini da ɗan murmushin mugunta na yawo a fuskarsa. Abbah da Inna suna zaune a falo, Abbah ya nuna masa hanya da murya mai nauyi: “Je ka shiga ɗakin Amal. Sai ta yi magana yau. Tunda kai ka jefa ta cikin wannan mummunan halin, sai ka fitar da ita!” Maleekh ya ɗan kalli gefe, yana yatsina fuska cikin ƙasƙantacciyar murya ya ce: “To ni meye haɗina da rashin maganarta? In ta ga dama kar tayi mana, ban ce ta yi ba har duniya ta nad'e.” Abbah ya tashi da sauri, cikin fusata ya ce. “Kar ka raina min hankali, Maleekh! Idan baka shiga ka yi abin kirki ba, wallahi saina rufe ka da duka!” Maleekh ya ɗan ja hayaƙi daga shisha yana murmushi cikin nutsuwa, sannan ya haura sama. 💔 Ya tura ƙofar ɗakin a hankali. Ƙamshin turaren lavender ya cika ɗakin domin koda yaushe ɗakin a cikin ƙamshi yake, dake akwai masu gyaran gidan... Amal tana zaune a tsakiyar gado, kai a jingine da bango, idonta jawur, hawaye na sauƙa a hankali. Bata ko motsa ba lokacin da ƙofar ta buɗe. Maleekh ya shigo a hankali, ya zauna a bakin gado kusa da ita. Ya zu'ko hayaƙin shisha ya busa akan fuskarta kamar yana gwada ta da gangan. Amal ko motsi babu. “Oh, a wancan lokacin ke baki ga abinda kika min ba? Kin tuna ranar da kika mare ni a bainar jama’a a Kaduna?... Hm, da nine a matsayinki na mace marar juriya da nima haka zan shiga halin da yafi wanda kike ciki yanzu, da yau ni ne a halin da kike yanzu…Amal voice...” Ya ɗan matsa kusa, ya kalli idonta kai tsaye, amma bata ko lumshe ido ba. Sai kawai ya ƙara da murya mai kaifi: “Ki sani, fansa ta a gareki itace maslaha. Da kin san ciwon raini kamar yadda na sani, da kin san dalilin da yasa na shiga soyayya dake. Da ba'a zo wannan ga6ar ba..... Amal yanzu da kika zauna haka shiru, kin fi kyau fiye da lokacin da kike ta ihu da surutan banzaa...” Ya saki ƙaramar dariya mai cike da ɗacin zuciya. “Kin san me Amal? Fansa tana da daɗi. Amma a lokacin da na ɗanɗana naki... sai na gane ba farin ciki bane, azaba ce mai baƙar wuya...” Ya ɗan ja numfashi, ya ɗaga kansa sama yana kallon fan da take juyawa, sannan ya ce a hankali: “Ina son ganin yadda zaki sake tashi daga wannan karyewar, saboda sai kin sake ɗanɗanar fansa ta mai sanya maye a titi....” Ya miƙe, ya juya yana shirin tafiya, amma kafin ya kai ƙofa, Amal ta motsa hannu ɗaya ba tare da ta furta komai ba.. Maleekh ya tsaya a bakin ƙofa, ya juyo kaɗan, yana kallon ta. Idonsa ya ɗan sauya launi, Ya juyawa zai fita daga ɗakin sai kawai wata ƙaramar murya, mai rauni mai cike da iko ta fito daga bayan sa: “Dakata…” Kamar iska ta tsaya a cikin ɗakin. Murya ce mai sanyi amma mai tsinke zuciya. Maleekh ya tsaya cak, ya juyo a hankali, yana kallonta da mamaki. Idonsa ya faɗa cikin nata, wanda ke cike da hawaye amma kuma akwai wani sabon haske a ciki kamar wacce ta dawo daga duhu.. Murmushi yayi sannan ya ce, “Oh, ashe ba haukacewa kika yi ba? Iskanci ne kawai...?” Amal bata amsa ba. Kawai ta tashi a hankali daga kan gadon, ƙafafunta suna danna ƙasan tiles a hankali, tana takowa gare shi kamar mai zuwa wajen ƙaddara. Hawaye na bin kuncinta, amma fuskarta ta nuna nutsuwa da ɗan murmushi mai sa tsoro. Ta tsaya gabansa, sun tsaya fuskantar juna. Hannuwanta suka tafi kai tsaye ga wuyansa... kafin ya yi wani tunani, ta haɗe bakinta da nasa... Da farko Maleekh ya tsaya kamar an dasa shi. Idonsa ya zaro, zuciyarsa ta tsaya. Sai dai sannu a hankali jikin sa ya fara yin sanyi, ya fara narkewa a hannunta... Amal ta riƙe kansa sosai, ta zurfafa sumbatar. Ba sumbatar ƙauna bace kawai, sumbatar azaba ce, sumbatar ramuwar rai, sumbatar mace da zuciyarta ta kone. Hawayenta na gauraye da numfashinsa, tana sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi, kamar wacce ke sakin wani zafi da ta ɗauka shekaru. Mintuna suka shuɗe suna a haka. Kamar wanda aka tsayar da lokacin domin ya tsaya ne cakk. Numfashin Maleekh ya canza, hannunsa ya zame a hankali daga jikinta, jikin sa ya ɗau rauni, kamar wanda aka tsaga masa zuciya da yatsa. Amal ta dakata. Ta ja numfashi mai zurfi, ta ɗan matsa baya kaɗan tana kallonsa cikin ido. Sai ta saki wani murmushi mai taushi da ke ɓoye ciwo. “Na baka raunanniyar zuciyata…” ta ɗan numfasa “Na karɓi taka lafiyayya.” Ta ɗan jinjina kai, ta ƙara da murya mai ƙarfi kaɗan: “Je ka. Ka jira… abin da zai faru.” Kamar an soka masa wuƙa a cikin zuciya, Maleekh ya tsaya yana kallonta. Zare baƙin glass ɗinsa daga idonsa yayi, ya jingina kai, yana kallonta da idon da ke bayyana abu biyu lokaci guda, mamaki da ƙiyayya... Ya ɗan ja numfashi, ya juya ba tare da ya furta komai ba. Ƙarar takalminsa ta ɓace daga ɗakin a hankali... A lokacin, Amal ta faɗa kan gado, ta rufe fuska da hannaye tana numfashi cikin zafi, hawaye na sauƙa kamar ana wanke zuciya da jini. Bayan Maleekh ya fita daga gidan, sai Abbah da Inna suka shigo ɗakin da sauri, zuciyarsu cike da fargaba. Amal tana zaune a gefen gado, idonta na kallon ƙasa kamar wacce ke jiyo muryar zuciyarta. Abbah ya matsa kusa, ya furta cikin tausayi: “Daughter…” Amal ta ɗago a hankali, ta kalli Abbah da Inna, murya a sanyaye kamar wacce ta fito daga ƙasa ta ce: “Ina son ganin Zayd…” Kallon juna suka yi da mamaki, Inna ta dafa kafaɗarta cikin farin ciki da jin sauƙin zuciya ganin yanzu Amal tayi magana. Abbah ya murmusa, yana faɗin: “Alhamdulillah…! Yanzu kin yi magana kenan. To shikenan, kar ki damu, zan ƙira shi.” Ya miƙe ya fita da sauri, zuciyarsa cike da godiya ga Allah... ☀️ Washegari da safe. Zayd yana zaune a falo, cikin nutsuwa da ɗan damuwa. Ƙiran Abbah ne ya kawo shi, bai san me Amal zata gaya masa ba. A zuciyarsa, yana jin ƙaunar Amal kamar da gaske amma har yanzu yana jin kunyar abinda suka aikata tare da Maleekh. Sai ga Amal ta sauƙo daga beni. Takalminta na yin ƙaramar ƙara, kowane mataki yana jawo hankalin Zayd ya kasa motsawa. Ta tsaya a gaban kujera, ta zauna cikin kwanciyar hankali amma idonta na cike da nutsuwar da ke ɓoye wuta. “Duk nasan komai, Zayd. Duk shirye-shiryen da aka yi mun, daga photona har zuwa zubar da mutuncina duk shirin Maleekh ne.” Zayd ya yi shiru, ya kasa ɗago kai. ta ci gaba. “Kaima nasan baka da bambanci da shi, tinda duk ɗaya kuke wurin ɗaukar fansa. Amma ban tsaneka ba…” Zayd ya ɗago, ya ce cikin raunannen murya “Amal… kiyi haƙuri. Wallahi ba da niyyar cutarki nayi ba. Na biye masa ne saboda ina son ganin farin cikinsa amma daga baya, na gane… Na gane ke ce matar da nake so da gaske.” Amal ta ɗan saki murmushi sannan ta furta “Da gaske kake?” Zayd ya jinjina kai da sauri, idonsa cike da tabbaci: “Na rantse da Allah, ina sonki da gaske, kuma zan so ki har karshen raina.” Ta ɗan juyo gefe tana murmushi, ta ce cikin sanyin murya: “To in har da gaske kana sona to sai an tabbatar.” Ya kalleta cikin tambaya. “Ta yaya?” Amal ta ɗago idonta kai tsaye cikin nasa, ta ce da murya mai daɗin sauraro: “Ina so nan da sati ɗaya a ɗaura mana aure.” Zayd ya yi firgigit, amma murmushin farin ciki ya bayyana a fuskarsa. “Aure? Amal... kina nufin... muyi aure?” A taƙaice ta ce: “Eh. Auren gaskiya. Na riga na sanar da Abbah cewa kai nake so, kuma na tabbata ba zaka ƙi ni ba.” Zayd ya kasa boye farin cikinsa, zuciyarsa ta ɗau haske kamar ɗan ƙaramin yaro. “Insha Allahu! In har kin amince, ko gobe kika ce, zan ɗauka da hannu bibbiyu.” Amal ta ɗan kalli gefe, “To, next week ɗaurin aure, kai dai ka sanar da iyayenka, su zo su samu Abbah. Ni kuma zan fara shiri tun yau.” Zayd ya miƙe da murmushi yana faɗin: “Nagode Amal. Na rantse bazan taɓa cutar da ke ba.” Amal ta ɗan saki murmushi, “Na sani. Ka tafi lafiya.” Da farin ciki Zayd ya fita daga falon, yana jin kamar mafarki. Amal kuwa ta jingina kanta da kujera, ta lumshe ido, numfashinta ya yi nauyi. Sai ta ce a ranta, cikin zafi da ƙuduri: “Zaka sha mamaki Maleekh… Zan ga yadda zuciyarka zata yi lokacin da ka ji cewa zan auri Zayd.” Ta saki murmushi mai cike da zafi, murmushin mace da aka karya wa zuciya, amma yanzu ta zama wuta. 🔥 Washegari Mahaifin Zayd ya samu Abbah, suka yi magana akan auren Amal. An fara shirye-shiryen aure cikin gaggawa, ana ta walwala da cike da murna a gida, amma Amal dai kamar inuwar kanta bata runtsa ba, bata fara gyaran amare ba. Lokaci kawai take jira, ba saboda son aure ba, sai don burin zuciyarta... A gidansu Zayd. Farha ta riƙe hannun Zayd da murmushi ta ce, “Dan Allah Yaya, ka riƙe Amal da amana. Ta sha wahala sosai, kar ka ƙara mata ciwo.” Zayd ya jinjina kai cike da niyyar gaskiya. “Farha, wallahi zan kare ta. Zan ba ta farin cikin da ta rasa. Zan zama murya a lokacin da wani ya kasa jin nata.” Sai dai cikin zuciyarsa yasan, ƙaryewar zuciya ce kawai ta sa Amal ta amince da shi... A can wajen Maleekh, lokacin da labarin auren Amal da Zayd ya riske shi, sai kawai yayi murmushi, murmushin ƙarfin zuciya.. Sai kawai ya buge da cewa. “To tunda ta ce tana so, ai sai tayi. Ni kuma ban damu ba...” Ya faɗa yana shan shisharsa, amma a ransa akwai rikici da tambayoyi marasa amsa. 🌹🌹🌹 Ana saura kwana uku a ɗaura auren Amal da Zayd, Abbah ya ƙira iyalansa gaba ɗaya a babban falo. Yana zaune a kujerar tsakiyar falo, kowa yana kallonsa. Ammy, Maleekh, Islam, Arfat, da Zayd wanda zai auri Amal. A cikin nutsuwa Abbah ya gyara murya, yana murmushi. “Na tara ku saboda wani abu mai muhimmanci. Kuma maganar akan Maleekh ne.” Maleekh ya ɗago kai yana kallon mahaifinsa cikin rashin fahimta. “Ni kuma? Me ya faru, Abbah?” Abbah ya ɗan murmusa, sannan ya ce da ƙarfi mai nauyin gaskiya: “Saboda ina tausaya maka, Maleekh. Na san baka tausayin kanka, Ka ji auren Amal, ko? Toh, yanzu zaka ji sirrin da muka ɓoye a cikin wannan shekarar...” Ammy ta ɗan matsa kusa da shi ta ce, “Wani sirri ne haka Alhaji?” Abbah ya ɗaga mata hannu alamar ta dakata. “Zan gaya muku duka. Maleekh... waccan Amatu da ka bari a shekarun baya, wadda ka ɗauka ta mutu a gobarar gidan su... to itace Amal!” Falonsu ya ɗauki shiru na ɗan lokaci. Maleekh ya ɗago da sauri, yana kallon Abbah, zuciyarsa ta tsaya. “Me... me kake faɗa Abbah?” Abbah ya daure ya cigaba. “Ita ce fiancée ɗinka tun yarinta. Na faɗa maka labarin, ko? Gobarar gidan iyayenta? To, iyayenta ne suka mutu, ba ita ba. Kakarta Inna ce ta gudu da ita kafin gobarar ta ci gaba. Wannan dalilin yasa bata da wani a duniya face Inna.” Maleekh a rikice yake kallon Abbah yana girgiza kai tare da faɗin, “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un... na wulakanta ta... ni na ci amanar wadda ta kasance fiancée ɗina tun yarinta...!?” Ammy ta riƙe kirjinta tana kallon Abbah da mamaki. “Kace Amal ɗiyar Hajiya Khadija ce? Ƴar gidan Babban Governor Alhaji Abdulsamaad Cash Maker?!” Abbah ya ce da karfi, “Itace! Itace ‘yar Alhaji Abdulsamaad babban abokina, wanda aka kashe da gobara a lokacin siyasarsa! Amma ga ɗiyarsa ka zalunce ta!” Maleekh yana riƙe da kansa yana faɗin, “Me yasa... me yasa ban gane ba? Me yasa ban bincika wacece ba? Sunanta ma Amal Abdulsamaad... ya kamata nayi tunani... amma na makance da ƙiyayyar fansa!” Zayd ya yi shiru yana kallon ƙasa, zuciyarsa na bugawa jin wannan al'amarin... Maleekh ya ɗago idonsa cikin hawaye ya kalli Abbah. “Abbah, me yasa baku gaya mun da wuri ba? Meyasa Amal ta ɓoye min alhalin tasan nine Leekh ɗinta?” Abbah ya ce da murya mai nauyi, “Saboda kai ka lalata komai. Daman burinta shi ne a daren farkonku ta sanar maka da gaskiya. Amma ka wulakanta ta, ka karya mata zuciya. Ka mayar da soyayyarta zafi da ciwo. To yanzu babu abin da zai iya dawo da wancan lokacin, aurenta da Zayd ba zai fasa ya ba.” Ammy ta ce cikin kuka, “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Ashe wannan yarinyar ce Amatu? Ashe mu ne muka gaza?” Abbah ya kalleta, ya ce, “Kuma yanzu da ya sani, me zai canza? Rashin jin tausayin ɗan Adam shi ne ya jefa shi wannan halin...” Maleekh ya miƙe cikin ruɗani, hawaye na sauƙa daga idonsa, ya juya zuwa ɗakinsa. Yana zuwa, ya buga ƙofar da ƙarfi, ya shiga tare da durƙusa ƙasi yana ihu kamar ransa zai fita. “Na lalata komai! Na lalata komai Amal!!!” Sautin ihunsa ya fita zuwa falo. Ammy ta rufe fuska tana kuka. Abbah ya jingina yana kallon sama da murmushi mai ciwo, ya ce a hankali: “Ko mutuwa zakayi, yanzu Amal ba taka bace.” Sai ya juya ya dubi Zayd ya ce cikin kwanciyar hankali: “Je ka, ka cigaba da shirye-shiryenka. Jibi ɗaurin auren.” Ammy ta ɗago tana kallon Abbah da mamaki da ɗan tsoro a fuskarta. “Alhaji... kana nufin kace... Hajiya Umma itace Inna?” Abbah ya ɗan juya kansa a hankali yana kallonta da murmushi. “Da kika kasa ganeta ai shikenan.” Ammy ta ɗaga murya cike da rashin yarda. “Wallahi Alhaji, ban san ita bace! Gaba ɗaya ta canza mun! Hajiya Umma da na sani farar mata ce sosai, ga haƙoran Makkah, sannan tana da dirin jiki. Wayayyar tsohuwa ce, mai ƙamshi, mai kalar hutu. Amma wannan Inna da nake gani yau, ta tsufa sosai, ta yi baƙi, wasu haƙoranta ma sun cire, bata da dirin jiki kuma sai masifa! Wancan kuwa mai sanyi da nutsuwa ce, amma wannan kamar ba ita ba ce... gaba ɗaya ta sauya, Alhaji.” Abbah ya ɗan yi dariya mai zafi, yana jinjina kai. “Au ke da haka kike? Haka na auro ki? To ai lokaci tafiya yake, rayuwa bata tsaya a kalar jiki ko kamanni. Ita Inna ta sha wahala, ta rayu a cikin talauci. Shi yasa duk siffofinta suka canza. Amma ni kallo ɗaya na ganeta. Kuma ita ma ta gane ni. Ta sanadiyyarta ne ma yasa na gane Amatu.” Ammy ta ce cikin mamaki, “To ya akayi ni na kasa gane ta, Alhaji? Ni dai a ganina ba ita bace.” Abbah ya juyo yana dubanta da idanu masu cike da raini. “Ai daman ke da ɗan naki, duk kwakwalwarku a toshe take. Idan aka ce ku yi gabas, sai ku yi yamma.” Daga nan, Abbah ya ɗauki hularsa, ya tashi ya bar falon cikin ɓacin rai. Ammy ta tsaya kallon ƙofar da ya fita tana guntun murmushi mai cike da zafi. “Amatu... Amatu da na ɗauke ta tamkar ‘yar cikina, yau ita nake gava da ita? Amatu da a baya take yawan wasa a gidan nan har ta kwana, amma yau ita nake ƙi? Tir da rashin sani. Ashe ba talaka bace, ba matsiyaciya bace. Ashe ita ce ƴar gidan Babban Governor! Wayyo ni... kullum nake zaginta da talauci, nake cin zarafinta... ashe ni ce mai kaskanci!” Ta riƙe kanta tana kuka a hankali, hawaye na bin fuskarta. A can sama, Maleekh ya shiga tashin hankali. Gaba ɗaya ya hargitsa ɗakin. Duk ɗakin ya birkice, gilashe duk sun faffashe, takardu a yage, hotunan Amal da ya ɓoye a jaka ya baza su a carpet, hoto na yanzun ta. Yana cikin tashin hankali, ya janyo wani akwatin azurfa da Farha ta kawo masa a baya, akwatin Amal.. Ya buɗe shi hannu na rawa... Sai ga hotunansu tun suna yara shi da Amatu a lokacin suna sanye da kayan makaranta, suna dariya, hannunsa riƙe da nata a bakin wata bishiya. A ƙasan hoton akwai rubutu da ƙaramin salo da Amal ta rubuta: “My Leekh… my promise will never die.” Maleekh ya firgita, hoton ya faɗo daga hannunsa, idonsa suka rufe da hawaye. Yana riƙe da kansa yana faɗin: “Amatu... ashe kece? Ashe kece? Na lalata rayuwarki, na wulakanta ki...Dan Allah! Me yasa ba ki faɗa min ba? Me yasa kika bari har na zama abokin gavarki?” Ga hotunan akwatin duk ya baza su.. Ya zube ƙasa, yana dariya cikin hawaye, dariya mai ciwo, kamar wanda ya rasa hankali... “Na yi fansa a kan soyayyata... na kashe farin cikina da hannuna... yanzu menene ya saura gare ni?”... A ƙasa kuwa, Ammy ta zauna shiru, tana tunanin rayuwar da ta wuce, tana faɗin a zuciya: “Inna da Amatu sun dawo ne don su zama hasken da muka ƙi gani... amma yanzu babu haske, duhu kawai muka bari ya lulluɓe mu.” A wannan ranar Da daddare, misalin ƙarfe 8:00, Maleekh ya isa gidansu Amal. Shigarsa cikin falon ta zo da mamaki, ya tarar da ita zaune akan kujera tana hira cikin natsuwa da Zayd. Da ƙafe su da rinannun idanuwansa. Wani irin zafin takaici da haushi ya ratsa zuciyarsa. Ya ƙarasa cikin ruɗani, murya na rawa ya ƙira sunanta: “Amal…” Ta ɗago kai tana murmushi, kamar wadda babu komai a zuciya, ta ce cikin nutsuwa: “Sannu da zuwa…” Maleekh ya ɗan matsa, muryarsa cike da raɗaɗi da rashin fahimta, ya ce: “Meyasa zaki mun haka, Amal? Ashe ke ce fiancée ɗina kika wahalar dani wurin jinkirin jiranta? Ashe ke ce ita? Why Amal? You are part of everything in my life…” Amal ta tashi a hankali, tana murmushi, ta ce cikin kwanciyar hankali: “Maleekh, wannan shi ne Zayd, wanda zan aura.” Ta ƙarasa maganar tana nuna Zayd da hannunta cikin sanyi, amma kalmarta ya zame masa kamar kibiya. Maleekh ya yi gabanta yana faɗin cikin rawar murya. “Ki fahimce ni Amal…” Sai ta katse shi da murmushi, ta ce: “Maleekh, jibi ɗaurin aurenmu da Zayd. Amma gobe za’ayi shagalin walima fatan zaka halarta.” Maleekh ya dafe ƙirji kamar wanda aka soka masa wuƙa. Ya yi wani irin ihu da murya mai raɗaɗi: “Please, Amal! Ke ɗin rayuwata ce. Kar ki manta akwai alƙawarin aure a tsakaninmu. Ni ne Leekh ɗinki wanda zai iya bada rayuwarsa saboda ke!” Amal ta cigaba da murmushin da yake haɗe da zafin tausayi, ta matsa kusa da Zayd. Ta riƙo hannunsa cikin nata, ta ɗago shi tsaye sannan ta dafa kafaɗarsa, tana cewa: “Ga Zayd mijina na gobe kuma abin alfaharina.” Maleekh ya zaro idanu yana kallonta, muryarsa ta dushe cikin rawar murya: “Oh my God! Ina ruwana da wani Zayd? Ina miki magana ne akan rayuwarmu, Amal…” Ta ɗan ja numfashi, ta yi murmushi mai sanyi amma idonta ya nuna ƙarfin hali da yanke hukunci: “Rayuwata ai gashi nan…” Ta nuna Zayd da hannunta. Maleekh ya girgiza kai, hawaye na sauƙa daga idonsa kamar ruwa. Ba tare da ya sake cewa komai ba, ya juya da sauri, ya fice daga falon cikin fusata.. Kofar ta rufe da ƙarfi bayan fitarsa... Amal ta kalli Zayd sannan ta ce "Please Zayd kaje sai gobe zamu sake haɗuwa..." "A wurin shagali ko kuwa?..." Ya tambaya yana kallonta. Ta ce "A wurin shagali..." Daga nan ta zauna tare da ɗaukar cup tana shan lemon cikin. Shi kuwa Zayd sallama yayi mata ya fita... Wannan rana ta kasance daren da ya fi kowanne tsayi. Maleekh bai runtsa ba, sai zirga-zirga yake a cikin ɗakinsa kamar wanda yake gujewa tunaninsa. Zuciyarsa na bugawa da sauri, numfashinsa na fita cikin nauyi. Ya tsaya gaban madubi yana kallon kansa, yana tambayar kansa da murya mai raɗaɗi: “My fiancée zata auri wani ina ji ina gani? Me yasa ta iya furta mun haka kamar ban taɓa zama komai gareta ba?” Ya janye ido daga madubin, ya koma gefe da gadonsa duk hotunan Amal da su tun lokacin yarinta, suna nan a baje a kan gado. Wasu hoto tana dariya, wasu tana kuka, wasu kuma tana tare da shi lokacin da soyayyar su ta fara. Ya ɗauki ɗaya daga cikin hotunan da hannu mai rawa, ya ce cikin murya mai raɗaɗin ƙauna: “Amal… kina tuna wannan hoto? Ran da kika ce ni ne masoyin da ba zai iya rabuwa dake ba. To yau me ya faru, Amal?” Hawayen da yake ƙoƙarin ɓoye suka zubo. Ya ajiye hoton yana kama kansa da hannu biyu, yana tafiya gaba da baya kamar mai ciwon zuciya... Ya doku a gado yana kallon ceiling a hankali ya furta. “I thought I was enough for you… But maybe I was just a memory you wanted to forget.” Zuciyarsa ta matuƙar nauyi, jikinsa duk yayi sanyi. “Amal… zaki yi aure, ni kuma zan zauna da tunanin ki har abada?” _NEXT NEXT NEXT_ asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 79 to 80 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Da sassafe, kafin shagalin walima, Ammy ta nufi gidansu Amal cikin nauyin zuciya. Da ta shiga, ta tarar Inna zaune kan kujera, Amal na gefenta tana nuna mata akwatunan auren da za'a kawo a wayarta... Inna ta ce "Yanzu to ya zamu yi da lefen wurin Maliku? Ga su Abbanku yace 'abar miki su' ai zasu yi yawa kuma.." Amal ta murmusa sannan ta ce "Inna, ai kogi bai ƙi yayyafi ba.." Suna cikin tattaunawa sai suka ji buɗewar ƙofa. Tsaya kallon Ammy suka yi wacce ta shigo jiki a sanyaye. Ammy ta tsaya cak, hawaye suka taru a idonta. A hankali ta durƙusa a gaban Inna, kafin ta sa hannu biyu ta rungumeta tana kuka kamar ƙaramar yarinya. Ammy cikin kuka, ta ce. “Uma… ki yafe mun. Ki yafe wannan zuciya ta da ta kasa ganeki… Ki yafe ni Uma. Na wulakanta ku, na ƙyamace ku… wallahi ban san ke bace Hajiya Umma… Ki yafe ni, wallahi ban san ke bace ba!” Inna ta share hawayen fuskarta, ta dafa bayanta. Tare da faɗin, “Allah ya yafe ki, Maryama. Rayuwa tana canzawa, jiki yana canzawa. Ba laifinki bane, sai dai ki riƙe min jikata kuma ƴarki da amana.” Ammy ta juyo da sauri, ta rungumi Amal sosai kamar zata maido da shekarun da suka ɓace. Ammy ta ce, “Amatu… wayyo ‘yata… tun rasuwar mahaifiyarki na shiga kewar da ban taɓa fuskantaba. Wallahi ni ban san ke bace ‘yar Khadija ba… Ban san ke bace ‘yarta ba… Don Allah ki yafe min, ki yafe wannan zuciya ta da ta rufe saboda rashin sani…” Amal cikin kuka ta ce, “Na yafe miki, Ammy. Ni ban taɓa ɗaukar ki abokiyar gaba ba. Kullum ina roƙon Allah ya shirya zuciyarki saboda ni.” Suka rungume juna, kuka ya cika ɗakin. Farha da wasu mata suka shigo, suka tarar da su cikin kuka, kowa sai tausayin wannan rana ta mamaye zuciyarsa... A wannan ranar Ammy wuni tayi a gidan, domin ita ta shirya Amal domin tafiya wurin shagalin Walima.. An kawata wurin cikin natsuwa... wannan karon ba kiɗe-kiɗe, ba rawa. Malamai ne zaune a gaba suna wa’azi kan hikimar aure, zaman lafiya, hakuri da biyayya.. Domin Abbah ya sanar cewa yawan kiɗe-kiɗe ne yake kawo fitina da rashin zaman lafiya, domin shaidan yana fitsari a wurin... Wurin Amarya da Ango an gyara shi cikin kayatarwa, an jera furanni, an haxa fitilu masu launi. Amal na zaune cikin rigar walima, Zayd a gefenta cikin nutsuwa. Wurin cike yake da mutane sosai, ƴan uwa, abokan arziki, dattijoji, duk sun hallarta... Hajiya Sa’adatu wannan ranar, ranar baƙin cikinta ne domin ta sa ran za'ayi hidima sosai a bikin ɗanta na fari... amma sai aka fake da wa'azi da karatu.. Ana cikin wa'azi sai ga hayaniya a bakin ƙofar shiga.. Kafin a ce meye, Maleekh ya shigo… Cikin black jeans da white t-shirt, idonsa jawur kamar wanda bai runtsa ba. Hannunsa na riƙe da bindiga. Mutane suka miƙe cak! Amarya ta miƙe da sauri, zuciyarta na bugawa. Zayd ya miƙe da fargaba. Abbah ma ya taso.. Maleekh bai tsaya ba, ya haura kai-tsaye zuwa wurin Amal da Zayd. Kamar mahaukaci, ya ɗaga bindigar ya saita Amal. Muryarsa ta karye wa, hawaye na kwance kan fuskarsa.. Abbah cikin firgici ya ce, “Maleekh!! Kana hauka ne? Za ka kasheta ne?!” Maleekh cikin rawar murya, yana rikitar da bindiga ya ce, “Naje gidansu… nayi mata magana… akan dalilin da yasa ta ɓoye min cewa itace fiancée ɗina! Amma ta maida ni kamar mahaukaci! To yau zan nuna muku haukata! Bazan bari ta auri kowa ba… In ba ni ba, sai dai mutuwa! Ni da hannuna zan kashe ta… sannan na kashe kaina! Fiancée ɗina ba mallakin kowa bace sai ni!” Amal tana kuka, ta kasa motsi. Zayd ya yi baya yana jijjiga kai cikin tsoro. Maleekh ya kunna kunamar bindigar… Ya ɗora yatsa… Ya ɗaga hannun… Bindigar na gab da tashi… Kowa ya rufe ido cikin tsoro… Sai kawai ya kawar da bindigar. Ya jinjina kai, ya miƙa bindigar ga Amal, yana rawar jiki. “Bazan iya kashe ki ba… fiancée ɗina… rayuwata… Amma ga bindiga… don Allah ki harbe ni! Ki huce wannan baƙin cikin da na saka miki. Na jawo miki raɗaɗin da ba zan iya gyara ba… Ki kashe ni Amal… ki yi min adalci…” Amal ta karɓi bindigar da kuka mai ƙarfi. Ta ɗaga ta kai saman kanta, tana kallonsa. Murya na kakkarwa ta ce, “Na gode da bindigar da ka kawo min… Ka ce in huce, ko? To ga shi… mutuwa ta fi zaman da zanyi da wani ba kai ba… Ka bar ni lokacin da nake buƙatarka, ka wargaza min zuciya… Iyaye na sun mutu, nima mutuwa zanyi… Domin babu wani farin ciki a tattare da ni…” Ta rufe ido… Ta matse bindigar… Ta ɗan matsa kunamar Wani ƙara bindigar yayi na fitar bullet!!! Bullet ɗin ya yi karo da mirror da aka kafa don kwalliya ya tarwatse! Kowa ya fara ihu! A lokacin da ta matsa Maleekh yayi saurin karɓar bindigar lokacin kuma ya matsa... Ganin babu abinda ya same ta ne yasa hankali kowa kwanciya.. Inna da Ammy rufe idonsu sukayi zuciyoyinsu na bugawa da ƙarfi... Abbah ne ya je ya tsaya a tsakiyarsu cikin fushi yake kallon Maleekh tare da faɗin “Ka zo domin ka hallaka ta kenan?! Maleekh, shin ka rasa hankalinka ne!?.. Ko me zaka yi, ba zan taɓa aurar maka da Amatu ba! Ka rusa damarka da hannunka! Da ma na gaya maka duk wanda ya iya wargaza zuciyar mace bai cancanci soyayya ba! Ka tafi, ka je ka ƙare haukarka!” Maleekh ya yi ƙasa da bindigar, ya durƙusa ƙasa da gwiwowinsa, hawaye na gangarowa cikin mugun raɗaɗi. Ya fashe da kuka kamar yaro… Kowa a wurin ya tsaya yana kallonsu.. Maleekh yana durƙushe ƙasa, hannayensa a haɗe, idanu suna ciccike da hawaye kamar ruwan sama. Cikin kuka mai karyar da zuciya, ya ce. “Abbah… dan Allah… kar ayi auren nan. Amal da ni ta dace… ita ɗin rayuwata ce. Na gina burina da ita tun farko… har ƙarshen numfashina… Dan Allah ka taimake ni… ina ƙaunarta… wallahi ina ƙaunarta Abbah…” Abbah ya tsaya yana kallon ɗansa wanda ya rikice gaba ɗaya, fuskar sa cike da takaici... Abbah ya ce, “Ka ce kana ƙaunarta? Shi yasa ka wargaza mata rayuwa? Shi ne ka kawo mata bindiga don ta hallaka kanta? Hakan ce soyayyar taka?” Ammy da ta tsaya gefe tun farko, zuciyarta ta taɓu sosai da ganin ɗanta cikin kaskanci da kuka. Ta matso tana share hawayen ta ce, “Alhaji… dan Allah kuyi haƙuri. Ku aura masa Amal. Mahainfinta ya yi alkawarinta ga shi tun tuni, ka sani. Kuma hakan ya zama wasiyya” Abbah ya yi shiru… yana tunani. Maganar Ammy ta kama shi sosai, domin alkawari ne. Amma kuma ba zai yi wa Amal dole ba. Ya juyo a hankali yana kallon Amal. “Amatu… ga shi nan. Maleekh yayi miki rashin adalci, amma kin ga matsayin alƙawari, kin ga matsayin zuciyarsa. Kin ga yadda yake nan a gaban jama’a saboda ke… To yanzu ki faɗa da bakinki: Kin yafe masa za ki aure shi?” Duk wurin ya yi shiru. Ko kukan jariri babu. Kowa ya zuba ido yana jiran amsar Amal. Ta ɗago kai a hankali, hawaye na kwance kan fuskarta. Ta ce da muryar da ke rawar zuciya: “To Zayd fa?..” Abbah ya shafa gemunsa, ya juyo da natsuwa: “Zayd zai yi haƙuri. Shi ma ya san aure kaddara ce. Tunda dama bai yi tsammanin zai same ki ba.” Amal ta riƙe zuciyarta tana huci cikin tausayi da baƙin cikin abin da Maleekh yayi mata.. Amal ta ce, “Shi Maleekh ɗin zai yi haƙuri… domin ya rasa ‘Amal’ har abada. Na yafe masa… amma bazai taɓa samun aurena ba.” Wannan kalaman sun yi masa tasiri fiye da harbi. Maleekh ya yi saurin matsowa ya rikice, ya kama ƙafarta yana kuka kamar wanda aka yanke masa hukuncin kisa: “Amal dan Allah! Dan Allah ki karɓeni… dan Allah ki bani dama… Ki aure ni… ki taimakeni… ki ceci rayuwata…” Amal ta janye ƙafar, hawaye na gangarowa, bata ko dube shi ba. Abbah ya kama kafaɗar Maleekh ya ɗaga shi tsaye da ƙarfi. Yana cewa. “Kayi haƙuri ka je ka nemo wata. Ba zan yi mata dole ba. Ka fita… ka bar mutane nu nutsu. Malamai na yin wa’azi.” Maleekh ya so magana, amma Abbah ya dakatar da shi da hannu. Ya ƙira securities biyu da ke bakin ƙofa.. "Ku fita dashi. Ana karatun kur'ani..." Ya furta tare da juyawa.. Securities suka tasa shi a gaba, suna jansa suna tura shi. Shi kuwa sai kuka yake, muryarsa na karyewa: “Amal! Amal please! Kar ki min haka! I love you Amal! I love you wallahi! You are my life… my everything… Amal please!!!” Suka fice da shi har waje, muryarsa na ƙara nisa da su… har ya ɓace... Amal kuwa zuciyarta ta rikice. Kaman numfashinta ya tsaya.. Soyayyar da take ɓoyewa ta taso da ƙarfi, amma dama ta riga ta yanke hukunci. Ta zauna tana kuka, Inna ta rungume ta. Kowa ya zazzauna zuciya cike da girgiza. An cigaba da wa’azi a hankali, malamai suka soma karanta ayoyi da hadisan aure. An fara raba kayan ci da sha. Sautin ƙira'a ya cika wurin, yana sanyaya zukata. Bayan haka aka fara ɗaukan hotuna. Amal na tsaye amma ba ta cikin duniyar nan, tunaninta gaba ɗaya yana wurin. Maleekh. Ana hotuna ciki walwala. Ita kuwa zuciyarta na can a rikice.. Islam da Arfat sam basu ji daɗin wannan al'amarin ba. Farha duk da Zayd ɗan uwanta ne amma tafi son Amal da Maleekh... Ammy ma bata cikin walwala. Iyayen Zayd kuwa suna farin ciki ne saboda zasu samu dama akan Amal.. Abbah, Ammy, da Amal suka ɗauki hotuna masu kyau a tare.. Sai kuma suka ji ƙarar engine mai ƙarfi daga waje: FWMMMMMM!!! Kowa ya dakata da hoton da yake yi. Engine ɗin ya ƙara kusantowa da gudu! Gabanin kowa ya gama juyawa.. TAAASHHH!!! Gilashin ƙofar da aka kawata ya FASHE ya tarwatse! Superbike mai sheƙi ya bankaɗo ta ciki cikin gudun wuta! “Wayyo Allah!!” Mutane suka firfita suna ja da baya. Wanda yazo kan Superbike ɗin yana rufe da helmet, babu wanda ya gane ko wanene ko mai ya zo yi.. Ya shigo tamkar tauraron fim! Ya yi sufa ɗaya zuwa tsakiyar taron. Kafin a ce .U. ya yi wani irin juyi da kwarewa, ya miƙa hannu ɗaya ya cafke Amal! Kamar iska ya ɗaga ta sama tamkar ba ta da nauyi ko kaɗan! Kafin kowa ya ankara, ya ɗora ta a gaban Superbike ɗin, ya danne throttle… FWMMMMMMMM!!! Hayaƙi ya turnuke wurin! Mutane suka watse! Kafin a iya rufe baki SUN ƁACE! Kamar wuta a cikin iska. Wanda ya ɗauke Amal cikin mintuna kaɗan ya ratsa titin Abuja ta baya. Amal na ta bugun ƙirjinsa, zuciyarta na huci cikin tsoro da fargaba. Cikin kuka da rawar murya take faɗin.. “Waye ne kai…kai ɗin waye? Kodai Maleekh ne ya ƙara turowa a sace ni?…” Bayan sun bar cikin garin gaba ɗaya, mutumin ya buɗe fuskarsa.. Ya cire hular helmet, sai ga fuskar Maleekh tana sheƙi da annashuwa... Amal, ganin Maleekh, sai ta buɗe baki tana kallonsa. Idanunta cike da hawayen farin ciki da tsoro. Amal cikin kuka, ta daki ƙirjinsa da ƙarfi. “Maleekh… kai ne…!” Ta zagayo da hannayenta ta rungume shi sosai, ta kifar da kanta akan ƙirjinsa. Maleekh kuwa sai dariya yake, cike da nasarar karɓe fiancée ɗinsa a ƙarƙashin ikon wani... Suna tafiya cikin daji mai tsanani. A wani tsauni, Maleekh ya tsayar da machine ɗin, domin wurin babu kowa. Kukan tsuntsaye kawai ke yawo, dajin babu mai shiga... Ya sauƙe Amal a ƙasa. Amal ta tsaya kallon wurin cike da tsoro, zuciyarta na huci. Cikin rawar murya da tsoro ta ce. “Maleekh… ina ne nam? Ina ka kawo ni? Nan fa kamar ba Nigeria ba ne… wannan… wannan daji ne kawai…” Maleekh ya murmusa, ya ɗaga kai, idonsa na sheƙi da annashuwa. Cikin muryar natsuwa, cike da ƙarfin zuciya ya ce, “Idan muka ƙara tafiya kaɗan, zamu iske ruwan Maliya…” Amal ta buɗe baki sosai, tsoro ya cika zuciyarta. Hawayen mamaki da fargaba suka zubo a fuskarta. Cikin rawar murya ta ce: “Akan iska kake tafe ne? Na ga akan machine muke… har mu bar Abuja… mu isa kusa da Maliyaaa???” Maleekh ya yi murmushi mai sanyi, ya riƙe hannunta cikin nasa. Ya matso kusa da ita, ya rungume ta sosai, yana jin fiancée ɗinsa a ransa gaba ɗaya. Cikin ƙarfi zuciya ya ce. “This machine is not like any other… it can take us anywhere we want safely.” Amal ta tsaya kallonsa, hawaye na kwance a idanunta, zuciyarta na bugawa da sauri. Maleekh ya matsa kusa da ita, yana riƙe kunkuminta tare da manna ta a jikinsa, yana jin farin ciki na mamaye shi... Yana murmushi ya ce "Wasa nake miki bamu zo red sea ba, Maliya ai ba'a Nigeria take ba..." Cikin shagwaɓa ta ce "To inane nam?.." Ya ce "har yanzu bamu fita daga Abuja ba, kawai na ratso ta daji ne..." Ya rungume ta sosai, hannayensa na zagaye da kunkuminta, yana jin zuciyarta na bugawa da sauri a ƙarƙashin ƙirjinsa. Dajin da ke kewaye da su, kukan tsuntsaye da numfashin iska mai sanyi yana ƙara musu nutsuwa. Amal cikin muryar tsoro ta ce, “Maleekh… wannan wurin… yana lafiya kuwa? Please Ina ka kawo ni?” Maleekh cikin murmushi, idonsa na sheƙi ya ce, “Ki kwantar da hankali, fiancée ɗina… wannan wuri na musamman ne. da iska mai sanyi, babu kowa da zai cutar da ke. Wannan machine ɗin na musamman ne, ba kamar sauran ba… zai kai mu ko ina lafiya.” Amal ta ɗora hannunta akan ƙirjinsa, zuciyarta cike da haɗuwa da tsoro da farin ciki. Hawayen farin ciki suna zubo a fuskarta. Cikin rawar murya, tana kallon Maleekh ta ce. “Maleekh… idan har kana tare da ni, zan iya amincewa da komai… amma ina son sanin komai a bayyane.” Maleekh ya ɗago kai, yana kallonta da ɗumin zuciya. Ya ɗan sumbace ta akan goshi, yana riƙe da ita sosai. Ya hau machine ɗin sannan ya ce "hau..." Ta ce "Ina muka nufa daga nan?.." Ya ce "Zamu ƙara gaba, nan ba tsaro, koda yaushe za'a iya afko mana..." Ta hau bayan machine tare da zagayo hannayenta ta gabansa ta riƙe shi sosai, kanta a kwance kan bayansa.. Suka ci gaba da tafiya da machine ɗin zuwa wani ɓangare na daji, bakin ruwa ya bayyana a gabansu, ruwan yana da haske sosai.. Anan suka sauƙa domin hutawa.. Amal ta tsaya, ta ɗaga hannunta, ta taɓa ruwan, tana jin sanyinsa mai daɗi. Amal cikin murmushi ta ce. “Maleekh… wannan wurin… yana da kyau sosai… kamar wani aljanna duniya...” Maleekh cikin dariya ya ce. “Duk wannan wuri na musamman ne, saboda ke. Na kawo ki nan domin ki ga cewa babu wani da zai iya ɗaukar ki daga gare ni. Wannan wuri shine tsaro da zaman lafiya, musamman ga fiancée ɗina.” Amal ta rungume shi sosai, ta sauƙe kanta cikin ƙirjinsa. Hawayenta sun haɗu da dariyar farin ciki, zuciyarta na cikewa da jin daɗi. Amal cikin annashuwa ta ce, “Maleekh… yanzu na fahimci cewa, komai da ya faru a baya… kuskure nane. Kuma kaine kafi cancanta da na kasance dakai...” Maleekh ya ɗaga kansa yana kallonta, ya ƙara matsa kusa da ita, yana jin fiancée ɗinsa na ɗaukaka a ransa... Suka zauna a bakin ruwa ga duhu ya shiga sosai domin dare yayi... Yana zaune ita kuwa tana kwance ta ɗora kansa saman cinyarsa.. Maleekh cikin tsantsar so yana shafa sumar kanta ya ce, “Amal, ki sani, ba zan bar ki ga kowa ba. Ko da menene ya faru a baya, yanzu ni da ke ne… rayuwa ɗaya, soyayya ɗaya. Zan yi komai don kiyaye fiancée ɗina.” Suna zaune a bakin ruwa, suna kallon hasken wata a sararin sama... Kowane numfashi, kowane motsi, ya kasance mai haɗa su da juna. Daji da iska da ruwa sun kasance kamar shaidar soyayya da tsaro.. Ƙafafunsu na cikin ruwan suna wasa da ruwan.. Dare ne sosai domin yanzu misalin ƙarfe 11 ne. Da wayan Maleekh suke ganin haske amma sai dai ba network kwata-kwata balle a dame su da ƙira...Sai power bank ɗinsa da yake chargy. Ita kuwa Amal bata tafo da waya ba.. Cikin lokaci ƙanƙani bacci ya ɗauke Amal.. Shi kuwa yana zaune yana shafa gashinta a hankali, Haka suka zauna a bakin ruwa, suna jin daɗin zaman lafiya da soyayya.. A wannan dare, dajin da ruwan sun zama alamar soyayya, tsaro, da alkawari tsakanin Maleekh da Amal... Maleekh haka ya kwana a zaune, Amal a kwance kan cinyarsa har lokacin asuba yayi.. Duba wayarsa yayi yaga ƙarfe biyar, dake ba masallaci balle su ji ƙiran sallah... Tasar da Amal yayi ta hanyar sumbatar bakinta. Jin ana tsotsar lips ɗinta ne yasa ta farka.. Tana lumshe ido a hankali. A hankali ya furta "Beb! Time to pray, daga nan sai mu hau kan hanya..." Ta furta tana lumshe ido "Sai ina?.." Ya ce "Sai gaba..." Haka suka tafi sukayi alwala da ruwan kogin. Sannan suka tsayar da sallah.. Bayan nan suka hau kan machine. A tsawon hanyar, babu motsi face ƙarar tayar mota. Sun shigo cikin jihar Taraba ta gefe, hanyar ta fara canzawa, bishiyoyi sun rufe hasken rana.. Tafiya sosai suka yi har suka shiga gindin dajin Mayogwo, sai suka tsaya anan... Babu wani alamar mutum ko ƙauye. Babban daji ne sosai.. A gefen su kuma, kogi ne a kwarare kamar yana bacci. Ruwa mai duhu, mai sanyi, mai zurfin da ba za ka iya ganin ƙasa ba. A saman ruwan ana iya ganin yadda ganyen bishiya ke sauƙa su narke a hankali. Masoyan suka tsaya suna sauraron dajin. Wani irin shiru ne ba irin na wancan ba wanda suka bari, shiru ne da yake cike da sirri, da fargaba, da kuma wani abu mai ban tsoro... Suna tsaye a bakin kogin inda ƙasan kasa yake da launin toka... Ga wani irin sanyi mai ratsa jiki.. Wani iska ne ta ratsa ta, gashin kanta na kaɗawa, ta lumshe ido tana sauƙe numfashi mai nauyi... Maleekh ganin yanda take ta kakkarwar sanyi ne yasa ya cire rigar sweter ɗinsa, ya ɗora mata, shi kuwa ya tsaya da farar singlet ɗinsa.. Ya ce mata, “Ba wanda zai same mu a nan… mu kaɗai ne.” Ta kalle shi, idonta cike da hawaye da fargaba ta ce, “Ka tabbata za mu iya kwana a nan?” Ya kama hannunta, ya ɗan matsa yana jin yatsunta sun yi sanyi. “Inasonki… kuma zan kare ki. Wannan dajin… yau tamu ne.” Da suke magana, kogin ya yi wani ƙaramar ƙara kamar yana magana da su. Dajin ya yi wani irin motsin iska wanda ya sa jikin su ya yi sanyi, amma a lokaci guda ya ƙara haɗa su wuri guda. Suka zaɓi wani ƙaramin fili a kusa da babban dutse, gefe da kogin. Suka kunna ƙaramin wuta, hayaƙin yana tashi sama yana ɓacewa cikin duhun bishiyoyi.. Dare bai wani yi sosai ba domin ƙarfe 6 na yamma ne, amma tsabar bishiyoyin da suka rufe sararin sama yasa dajin yayi duhu ƙirin.. A wannan wurin. Babu wanda zai san inda suke. Duhu mai zurfi ya lulluɓe komai. Wutar da masoya suka kunna ta fara ƙara tash,tash,tash… tsatsatsa… Iska ta yi sanyi... Dajin ya ƙara yin shiru. Sai kukan kogin da suke ta ji.. Suka zauna gefe da juna, begensu ya haɗu, hannunsu riƙe da na juna kamar kar su sake... 🌬️ Ta lumshe ido zata yi magana sai ta tsaya cak. Tana jin wani sautin iska. Fiiuuuuuuuuuuuu… Fiiuuuuuu… fiiuuuu… Kamar iska ce ke kiran wani abu a ciki. Ta matsar jikinta kusa da shi. “Ka ji motsi kuwa?” ta tambaya da wata murya mai kunshe da tsoro. Ya kalleta. Ya ɗan murmusa, duk da shi ma jikinsa ya ɗauki sanyi. “Ki kwantar da hankalinki. Dajin ne yake motsi da dare. Nan babu mutane… babu mai cutar da mu.” Amma kafin ya gama, guuuuuummmm wani irin sauti ya ƙara a cikin dajin. Kamar wata bushashshiyar bishiya ce ta faɗi, ko kukan wata dabba. Ya tsuke baki. Ita kuwa ta riƙe wuyansa kamar zata shige cikin zuciyarsa. Wani tsuntsu ya yi tsalle daga reshe, yana yi masu kuka: Krrr… krrr… krrr… Sai kuma ya tashi da sauri kamar yana gudun wani abu. Daga can cikin inuwa, ana jin ruffa-ruffa na ganyayyaki kamar mutum yana tafiya cikin hankali, yana takowa a sannu, yana ƙoƙarin kada su gane shi. Cikin tsoro ta ce, “Wani yana nan?” “Ba mutum bane… dabba ce.” A cewar Maleekh.. “Wacce dabba ce zata yi tafiya kamar mutum?” Ta ƙarasa tana zazzaro ido waje.. Shiru yayi.. Ita ma ta gane shiru ɗin nasa akwai alamun wani abu. Kogin ya yi bugun ruwa mai ƙarfi, kamar wani abu ya faɗa ciki ko ya taso daga ciki. Sai jikin su ya tsaya. Tana girgiza kafa cikin tsoro ya ce. “Ina tsoron wannan wurin… wallahi ina ji kamar wani na kallo na.” Ya janyo ta jikinsa sosai, ya jinginar da kansa da nata. “Ki saurara… komai lafiya. Wannan dare anan zai zama sirrin mu. Da safe zamu fita mu nemo wani wuri mafi kyau.” 🔥 Wutar na haskaka su, tana bayyana farin idonta da motsin hawaye. Suka zauna suna jin ɗumin wutan.. Tana rufe da rigarsa ta jingina kanta a kirjinsa. Numfashin su biyu na gauraye cikin iska mai sanyi. A cikin wannan duhu mai tsoro, soyayya ta ƙaru. Ta kama hannunsa, tana ɗan matsawa a hankali. “Ka tabbata ba za ka bar ni ba?” Ya ce mata da murya mai taushi. “Ba a barin mace a daji… musamman wacce nake so.” Sannan… wani abu ya tunkaro su. Daga cikin duhun dajin, daga can inda kogin yake, an fara jin wata ƙara mai sanyi: Hooooooo… hooooooo… Kamar dai mutum ne... Wani lokaci kamar dabba ce, wani lokaci kamar iska ce, amma da ƙarfi… tana matsowa a hankali. Ta ɗago da sauri, idonta ya cika da tsoro. “Kai… wannan kamar tsuntsu. Kamar dabba. Kuma wannan… kamar—” Ya miƙe tsaye a hankali, ya kamo hannunta. “Ki tsaya a baya na… kada ki yi magana.” Wutar ta yi ƙara, kogin ya yi bul-bul-bul kamar yana jan wani abu. Daga nesa, an fara ganin inuwa tana motsawa tana kusantowa… _NEXT NEXT NEXT_ asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 81 to 82 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Inuwar nan tana tafe a hankali, amma tabbas ba irin tafiyar dabba ba ce. Ba ta da sautin ƙafa. Ba ta da nauyi. Kawai tana shawagi… tana matsowa kamar iska mai rai. Wutar gabansu ta fara ja da baya kamar tana tsoron ta. Kogin kuwa ya yi wani irin bulk-bulk-bulk kamar wani abu ya taso daga ƙasan sa. Ta riƙe hannunsa sosai yatsunta suna rawa.. “Wannan… wannan aljani ne?” Muryarta ta kaɗe kamar na yarinya Ya ɗaga mata hannu ya ce ƙasa-ƙasa “Ki yi shiru…” Daga cikin duhu, shafan iska ya fito, ya buɗe hanya ga inuwar da take matsowa… har ta bayyana. Fuskarta ta fara bayyana… ba mutum ba ce, ba kuma dabba ba… Da fari abin ya yi kama da mace. Doguwar mace. Siril, ba ta taka kasa ba. Gashinta yana shawagi kamar yana cikin ruwa. Idanuwanta kuwa… farare tsaf, babu ƙwayar ido. Jikinta smokin haske ne, ba ta da nauyi, tsayin ta daidai yake da reshen bishiya. Ta tsaya ƙarshen wutar su, tana kallon su ba tare da motsi ba. Kamar ba ta numfashi... Lokaci guda ta yi magana… ta cikin iska ba ta baki ba. Fiiuuuuuuuuuu… har kun zo…??? A zuciyarsu suka ji muryar, ba a kunne ba... Ta durƙusa a hankali, ba tare da ta taɓa ƙasa ba, ta ƙarasa zuwa bakin wutar… Amal idonta cike da hawaye, ta ce a hankali: “Kai… wacece wannan?” Abin ya juya kai yana kallon su duka biyun, kamar yana nazarin su. Sai ta ɗaga hannunta mai tsawo, siriri kamar kara, ta nuna su: “Ba ku kamata ku kasance a nan ba… ku biyu kun karya doka… kun shiga hannu…” Ta ja iska. Tana yawo a cikin iska. “…kun shiga dajin da ba’a bijirewa… dajin Tsakar-Malmai.” Maleekh ya matso gaban ta, yana kare masoyiyarsa Amal ya ce, “Me kike nufi? Ba mu zo domin cuta ba. Muna neman mafaka ne kawai.” Sai ta yi murmushi, murmushi marar rai. “Mafaka?” ta ce. “A dajin Malmai… mafaka ba ya zuwa da mutane. Sai dai tsoro. Shan wahala… ko kuma… fatan fansa.” Ta matsa kusan su. Tana shirin kai hannunta kusa da fuskar Amal. Amal ta ja baya da sauri. Inuwar ta tsaya cak. Ta sauya launin ido daga fari zuwa duhu. “Na daɗe ina jira… Kujerar ku biyu… tun kafin a haife ku… an rubuta cewa zaku zo wannan dajin a daren yau.” Suka kalli juna cikin tsoro. Wani irin bugu zuciyar Maleekh yayi.. “Me ake nufi? Wane ne ya rubuta haka?” Sai iska ta buga cikin dajin, ganyayyaki suka fara kaɗawa kamar ana tsawa. Inuwar ta juyo da sauri ta kalle shi. Idanuwanta sun yi ja kaɗan. “Wanda yake sane da komai. Mahafinku ya taɓa kawo sunanku nan… shekaru dubu da suka wuce.” Amal ta zaro ido waje ta ce, "Kaii shekaru dubu ai ba'a halicci Nigeria ba ko?.." Aljanar ta ɗaga hannun ta. Wutar ta mutu.. Daji ya zama baƙi ƙirin... Kogin ya yi ihu kamar mutum ya faɗa ciki... Sai fitacciyar inuwar ta ƙarasa da wani zafi ta ce: “Ku biyoni. Ko ku mutu.” Da zarar halittar nan ta ce “Ku biyoni ko ku mutu,” idanuwan Maleekh suka kaɗa.... Zuciyarsa ta fashe da tsoro. Jininsa ya hau sama... Ya kamo hannun Amal da ƙarfi kamar kada ta zame. “Mu gudu! Kada ki kalli baya!” Ba ta ko yi tambaya ba, tsoron da yake fuskarta ya isa ya gaya mata cewa wannan ba lokacin maganganu ba ne. Suka yi tsalle suka fice daga wajen ruwan kogin, suka kutsa cikin kauraye ganyayyakin da suka rufe hanya. Suka isa wajen da suka ajiye machine ɗinsu, Superbike. Ya hau da sauri Ya ɗaga mata hannunta ya ɗora ta a bayan sa Ta rungume shi tana rawar jiki Kanta a bayan wuyansa Hawaye suna zubowa saboda tsananin tsoro. “Ka kunna! Ka kunna! Ka kunna da hanzari!” ta furta, muryarta na rawa. Ya buɗe choke Ya danna Machine ɗin ya yi fummmm–wummmm–wummmmmm! Dajin ya yi duhu sosai. Bishiyoyi suna bugun gefen su, wasu rassan suna shafan jikinsu kamar hannun mutum. Sauti ɗaya rak ya biyo bayan su: “Hooooooooooooo…” Bai yi kama da ihu na dabba ba. Bai yi kama da iska ba. Kamar an haɗa muryar aljanar da kukan tsuntsaye tare zuwa sautin da ya fi ƙarfin kunne... Amal ta matse shi sosai, hawaye suna fita ba tare da numfashi ba. “Maleekh! Wannan sautin ya na biye da mu! Ya na tahowa!” Ya ce da ita cikin tsananin murya. “Ki rufe kunne! Kada ki saurari komai! Ina nan… ba zan bari mu hallaka ba!” Machine ya na tsalle-tsalle akan ƙasa mai cike da duwatsu, wani lokaci yana ɗaguwa sama, kamar zai faɗi, amma bai tsaya ba. A bayan su, wani farin haske yana shawagi a sama, yana bin su cikin sauri kamar hazo.. Ba ya tangalewa. Ba ya tsayawa. Sannan ba ya gajiyawa. Dajin ya yi sanyi sosai. Amal tana ihu, tare da faɗin “Wayyo! Innalillahi! Tana kusa! Wallahi ta kusan iso mu!!” Ya jawo handle ya yi wani irin mugun zaro da machine ɗin: “Hold me tight!” Suka ƙara gudu ta hanyar mutuwa ko rayuwa.. Ya ce: “Mun kusan fita daga ɓangaren dajin! Ki daure!” A gefe kuwa, muryar halittar ta sake cika sama: “Kuuuuuuuuuuu… ba ku tsere ba…” Amal ta fashe da kuka... 🏍️💨 Machine ya shige cikin wasu manyan duwatsun, hayaƙi tana fitowa cikin duhu, duwatsun suna gogan jikinsu saboda matsin wurin.. Suka fita kai tsaye daga cikin duhun. Sai iska ta buso su. Dajin ya yi haske wato sun wuce ɓangaren da halitta ke iya fakewa.. Machine ya tsaya da ƙyar saboda zafin gudun. Maleekh ya yi numfashi mai nauyi. Amal ta faɗa jikinsa tana kuka, tana rawar tsoro. “Ka… ka ceci ni…” ta furta cikin kuka. Ya rungume ta sosai, yana jin hucin numfashinta a kan kirjinsa. “Ba komai… kin ji? Ba zan taba barin ki ba.” Amma… kafin su samu nutsuwa… Sai suka ji ƙara daga cikin dajin da suka baro, wanda iyakarsu sai an ratsa ta cikin manyan duwatsu.. “Babu inda za ku je… zamu sake haɗuwa.” Daga dajin da suka tsere, suka koma wani daji daban, ba duhu sai nau’in tsoro daban... A nan, akwai ƙaramin gari a cikin daji, ba a gani daga nesa saboda bishiyoyi sun rufe shi. Mutanen garin kuwa… mafarauta ne masu ƙarfi, masu jini a jikinsu, masu kamannin daji. Suna amfani da wuƙaƙe, kibiyoyi, gatura, da makaman gargajiya. Jikinsu ba kaya sai ganyayyaki da ƙugiya ɗin da sahon farautarsu ke rataye a wuyansu. Da suka shigo cikin dajin, kafin su fahimci komai sai suka ji “Ffff! Ffff! Ffff!” Wuƙaƙe suna miko musu hari daga kowane ƙarshen bishiya.. Maleekh yana riƙe da hannunta haka suke sunsunkuya. Kafin su yi magana, mutane goma sha biyu suka fito suka kewaye su. Dukkansu babu kaya, sai ganyayyaki da ke rufe da ƙugunansu.. Ganin mutane kewaye dasu yasa suka durƙusa cikin tsoro, domin fuskokin mutanen sun sha baƙin fenti.. Suka karɓe su da wuƙaƙe a hannu, sannan suka ɗauke machine ɗin.. Shugaban su, Babban Mafarauci, ya yi gaba.. Idonsa jajir, kan sa yana rufe da fatar bauna.. Ya kalle su sama da ƙasa ya ce da muryar da ta cika daji: “Me ke tafe da ku? Wa ya ce ku shigo dajinmu?” Maleekh ya yi saurin ɗago wa yana kallonsa, saboda jin tsananin muryarsa. Amal ta riƙe hannunsa tana kuka.. Ya ce cikin tsananin tsoro: “Hanya ce ta kawo mu nan… mun tsere… wallahi ba mu zo cutar da kowa ba.” Mafarautan ne suka fara magana ta tsawa: “Ƙarya ne! Duk wanda ya shigo dajinmu sai an yanka shi! An ci naman sa! Wannan dokar kakanninmu ce!” Amal ta fashe da kuka, tana rawar jiki. Ta durƙusa gaba ɗaya, ta ɗago kai, tana roƙonsu. “Dan Allah… kada ku kashe mu… ba mu da laifi… Ni da shi masoya ne… aure za a ɗaura min da wani wanda bana so… Shine muka gudu… don mu tsira…” Dajin ya yi shiru. Mafarautan suka kalli juna. Wasu suka yi shewa: “Ahhh! Masoya!!” “Aure! Aure!!” “A yayanka su! A ci naman su tun kafin su yi aure!”... Matar shugaban mafarautan ce ta fito. Babbar mace ce, mai taushi fiye da mijinta. Ta duba Amal sosai ta hango tsoron gaske a idanunta. Ta ce da muryar mace mai hangen zuciya. “Kada a yanka su. Masoya da suka gudu don juna ba a kashe su. Wannan al'ada ce ta tsohuwar mahaifiyata… A bar su… a kula da su.” Mafarautan suka yi shewar daji.. Shugaban mafarautan ya ɗaga hannu, ya ce: “To! Idan wannan ne hukuncin mata…” Ya juya ya kalle su, idonsa na haske. “Za mu ɗaura muku aure a nan… yanzun nan… domin wannan shi ne tsawon zaman dajinmu.”.. Duk mutanen suka fara tsalle! Suna shewa! Suna rawa! Suka fara busa ƙaho da ƙarfi domin shugaba ya yi magana.. A nan cikin dajin, a tsakanin ganyayyaki da wutar da aka kunna da rassan itatuwa, aka kafa da'ira. Mutanen gari sun yi tsaf, suna tsatstsaye. An sa Amal a tsakiyar da'irar. Maleekh kuma a gefe. An ɗaure su da igiyar reshe. Shugaban ya yi rantsuwa cikin harshen daji, ya ɗaga wuƙa sama, ya ce: “An ɗaura aurenku da dokar daji, da dokar ruwa, da dokar mafarauta. Daga yau… ku biyu miji da mata ne.” Mafarautan duk suka yi ihu: “Auuuuuuuuuuuuuuuuuuu!!!!” Amal tana kuka. Ba kukan farin ciki ba sai na tsantsar razana... Maleekh ya riƙe hannunta, ya ji hannayenta sunyi sanyi kamar kankara.. Ya ce cikin ƙasa da murya: “Ki da kiji tsoro… ki sani… ina nan tare da ke.” Mafarautan suka fara rawa. Suna ɗaga wuta sama. Ganyayyaki suna kaɗawa... Auren da ba su taɓa mafarki ba yau an ɗaura musu... A cikin daji. A tsakanin mutane marasa kaya. A ƙarƙashin hukuncin daji. Akwai wata tsattsauran al'ada da dole su bi. Shine zasu zauna anan. An kafa wa Maleekh doka cewa dole ta samu ciki a cikin kwana uku. Idan ba haka ba zasu jefa shi cikin babban tekun su. Ita kuma Amal su aura mata maza biyu daga cikin mazan su. Kuma a dokar su, maza biyu ne suke auran mace ɗaya domin mazansu sun ninka mata yawa... Amal ta tsorata sosai. An basu wani ɗaki wanda aka gina da itace.. wanda aka rufe da ganyayyaki.. Yana ta tunanin to kenam taya zai mata ciki a cikin kwana uku al'halin ba shine mai bada ciki ba.. Haka aka ajiye wannan dokar. Idan kwana uku yayi akwai abinda suke gwadawa ya nuna musu mace ta samu ciki... Da daddare, aka tura su cikin ƙaramin ɗakin da aka yi da itatuwa. Wurin yana ɗauke da ƙamshin ƙasa da ɗaci na hayaƙin wuta... Amal ta zauna a kusurwar ɗakin tana rawar sanyi da tsoro, idanuwanta sun kumbura saboda kuka. “Me zamu yi?” ta ce cikin murya mai rauni, tana kallon Maleekh da ya kasa zaune saboda damuwa. Shima ya nufe ta ya durƙusa a gabanta. “Ki saurare ni… ba zan bari su cutar dake ba. Wallahi ba zan bari ki shiga wannan muguwar al’ada ba.” Sai kawai ta fashe da wani sabon kuka mai ƙarfi, tana tunanin yadda aka kakaba musu aure na dole, kuma yanzu ga wannan tsattsauran hukunci da ba zata iya tsallakewa ba. A waje kuwa, ana ta busa wutar al’ada. Mazan mafarautan suna ta shirya manyan takubansu, kamar suna jiran ranar uku ta cika su aikata hukuncinsu. Matan kuma suna ta yi wa Amal siyayya ba don tausayi ba, sai don ta zama amarya ga mazansu idan saurayin ya gaza... Maleekh yana ta tafiya a cikin ɗakin kamar zai haukace. “Ya za mu yi ciki cikin kwanaki uku? Ni abun ya ɗaure mun kai… ba ni da damar…” ya tsaya, saboda ba zai iya faɗi gaba ɗaya ba... Amal ta share hawaye ta ce, “Suna cewa idan ban samu ciki ba… za su aurar da ni ga wani har biyu.. Kai kuma za su jefa ka cikin tekunansu. Kasan me hakan yake nufi?” Shiru ya cika ɗakin. A waje kuwa an kunna wuta suna rawar al’adarsu ta dare. Sautin ganguna ya ɗauki dajin da ihu na murna.. Duk suna ɗaki sun rasa abun yi, ya riƙe ta tare da zaunar da ita. “Ni dai abu ɗaya nake so ki sani…” ya ce cikin muryar da ke rawa. “Ko me ya faru, sai dai su kashe ni, amma ba zan bari su aurar ki ga wani ba.” Ta kalle shi wannan maganar ta ƙara mata tsoro, amma kuma tanajin wani nau’in kwanciyar hankali a zuciya. A wannan lokacin, matar shugaban mafarautan ta shigo ta ɗaga bargon ganyen. “Ku shirya. Gobe da safe zamu fara bibiyar al’amuranku.” Suka fita. Amal ta kwanta a jikin Maleekh ta rungume shi saboda tsoro... Da daren sun kwanta amma barci ya ƙi zuwa. Gaskiya kawai ɗaya ce: A cikin kwanaki uku ko dai su tsira… ko kuma su rasa rayuwarsu. Amal tana zaune tana murza yatsunta saboda tsoro da rashin tabbas. Maleekh kuwa ya tsaya a tsaye yana kallon ta, zuciyarsa na bugawa da ƙarfi saboda nauyin abin da ake expects daga gare su. “A yau ne daren farko…” ta faɗa cikin murya mai sanyi, tana kau da kai. “Idan muka yi addu’a, ko Allah zai ba mu sa’a? Mu samu ciki kafin kwanaki uku?” Ya zauna a gabanta a hankali, “Ni ma haka nake fatan,” ya ce. “Ba wai saboda dokarsu ba, don kawai saboda mu tsira. Kuma… saboda ina matuƙar jin ki a raina.” Ta yi murmushi mai raɗaɗin tsoro. “Ni ma ina sonka. Idan Allah ya rubuta a yau ne… toh shi kenan.” Ya kamo hannunta, hannun yana rawa, nashi ma yana rawa. Babu wani wasa a al'amarin, sai zallar tsoro da soyayya, da fatan nasara a wurin Allah.. Suka durƙusa su biyun, suka ɗaga hannaye sama, “Ya Allah, ka ba mu mafita. Ka sanya mu samu abin da zai ceci rayuwarmu. Ka kare mu daga wannan sharrin al’ada. Ka sanya mu samu albarka a wannan daren.” Hawaye ya zubo daga idon Amal saboda tashin hankali da addu’a a lokaci ɗaya. Maleekh ya matsa kusa da ita. “Ko da muna cikin tsoro… ni zan yi iya ƙoƙarina. Allah ya gani.” Ta ɗaga kai, idonta cike da hawaye ta ce, “Ni ma zan yi iya nawa. Ka tuna… muna da aure yanzu shine babban farin ciki, ba wai zina zamu aikata ba.” Suka lumshe ido sannan suka rungumi juna, cikin nutsuwa da jin kunya da kulawa... Babu hayaniya, babu rawar kai kawai nutsuwa, addu’a, da fatan cewa Allah zai basu ikon da zai ceci rayuwarsu.. Haka numfashinsu yake haɗuwa suna shakar ƙamshin jikinsu.. Cikin lokaci ƙanƙani suka haɗe bakinsu.... A hankali suke sumbatar juna, cike da ƙaunar juna da sha'awa lokaci guda.. Sun daɗe suna foreplay kafin a hau aiki 😅. Haka take razana saboda tsananin zafi da raɗaɗi, a hankali ya furta mata a kunne. "Sorry! Kar ki ji tsoro zafin na lokaci kaɗan ne......Zai shiga yanzu.....Zai shiga....Ki nutsu please..." Haka take daure wa saboda kar mutanen waje su ji... A waje ana ta busa ƙaho, alamar cewa mafarautan suna jiran sakamakon kwanaki uku.... ☆☆☆☆☆ Bayan sun gama, suka rungume juna cikin shiru. Ba wanda ya ce wani abu. Kawai jin numfashin juna da fatan cewa Allah ya amsa addu’arsu. Maleekh ya ce a hankali: “Ina fatan wannan dare ya yi mana albarka.” Ta jingina kanta a kirjinsa. “Ni ma haka… gobe safe saura kwana biyu.” Haka suka cigaba da zama, suna zaune rungume da juna cikin tsantsar gajiya da fargaba, sun sanya kayan jikinsu. Wurin ɗakin ya yi duhu, hasken fitilar wuta ta waje kawai ke shiga ta gefen ganyen da aka rufe.. Sai kawai suka ji ƙarar takun ƙafa, kafin ma su yi wani motsi, ɗan mafarauci ya bankaɗo kofar ɗakin da ƙarfi. Ya shigo ba sallama, ba neman izini. Da wuƙa a hannunsa... “Oh! Har yanzu kuna nan zaune? Baku yi komai ba kenan!” ya faɗi cikin tsawa yana huci... Maleekh yana kallonsa cike da mamakin jahilci irin na wannan al'ada, ya ce. “Yanzu muka gama...” Mafaraucin ya zaro ido, yana matsowa kusa.. “Munafukai! Sai kun cire kayanku! Na rantse da dokar mu, sai na ga da idona.” Maleekh ya girgiza kai ya ce, “Yanzu muka gama fa. Kazo ka taɓa tabarmar nan zaka ji a jiƙe yake…” Mafaraucin ya durƙusa ya taɓa tsakiyar tabarmar. Sai kuma ya ɗaga kai ya yi ihu yana cewa. “Ƙarya ne, ruwa kuka zuba! Kuna wasa dani ne? Sai kun cire kayan ku!” Maleekh ya ce, “Ta wahala sosai… ta gaji… ka bari—” Kafin ya rufe baki, mafaraucin ya ɗago wuƙa sama, idonsa ya kaɗa da ja. “Ƙarya kuke! Zaku yi yanzu! Ko sai nayi masa yankan damo..?” Amal ta fashe da kuka, ta tashi a rikice tana marairaicewa: “Dan Allah ka saurare mu! Zamu yi! Zamu yi! Amma ka fita. Bazai yu mu cire kayan mu a gabanka ba…” Ta durƙusa tana roƙonsa, muryarta na rawa. Amma mutumin ya girgiza kai: “A'a! Sai an fara kafin na fita. Sai na tabbatar da gaskiya, domin turo ni akayi domin na duba.” Haka ya tilasta su yin abin da yake so, sun tilasta kansu cire rigunansu bisa kunya, zuciya na rawa. Sai da suka fara kusantar juna ba don sha’awa ba, sai don su tsiratar da kansu. Sannan mafaraucin ya tintsire da dariya, ya juya ya fita. Amma kafin ya tafi ya ce: “Ku tabbatar na ji ihunta. Ko ba haka ba, gobe akwai hukunci.” Ƙofar ta rufe da ƙarfi, ya bar su cikin yanayi, zafi, tsoro, da bugun zuciya. Lokacin da su ka rage su kaɗai… Amal ta fashe da kuka, hannunta na rawa kamar wacce aka jefa cikin wuta. “Wallahi bana jin ƙarfin jikina… amma idan muka ƙi… za su kashe ka.” Maleekh ya matso ya rungumeta a hankali: “Ki yi haƙuri. Ba zan taɓa cutar da ke ba. Amma dole mu tsira. Ki bari mu yi abin da ya kamata, sannan mu yi abinda Allah ya sa a bisa aure.” Suka yi addu’a cikin hawaye, sannan suka kusanci juna a hankali, cikin kwarin gwiwar auren da suke da shi... Maleekh ya mara mata baya cikin sassauci, yana kwantar mata da hankali. Ya zamar da rigarsa, tana jin bugun zuciyarsa kamar nata. Sannan… suka shiga second round.. Na bar wannan bangaren cikin mutunci 🤭🙈 Amma a wannan karon Amal ta yi ihu... Ihun tsoro raɗaɗi nutsuwa da kuma dalilin da za su tsira... Ihun nata ya fita har wajen dajin. Mafarautan suka ji. Har an fara busa ƙaho, alamar sun gamsu da cewa “aikin daren” ya tabbata. Wani dattijo a waje ya yi ihu yana faɗin. “Sun yi! Sun yi! A gobe mu haɗa musu kayan ciye-ciye!” Dajin ya cika da kiɗe-kiɗe da buge-buge.. A ciki kuma… Amal na kwance a jikinsa tana kuka, shi kuwa yana shafa kanta: “Ki yi haƙuri… ki yi haƙuri… duk da tsananin tsoro, Allah ya ga abinda ya faru. Allah ya sani ba da son ranmu ba.” Ta ce cikin rawar murya: “Gobe sauran kwana biyu… idan ba ciki ba… zasu kashe ka…” Shiru ya ratsa ɗakin. Su biyun kawai, cikin duhu, cike da addu’a da fatan gobe zata kawo sabon numfashi ko kuma sabon bala’i… 💥 Asubar fari ya fara haskowa ta cikin ganyen da ke rufe rufin ɗakin itacen da aka basu. Amal ta farka cikin firgici, tana rungume da jikinta kamar mai jin sanyi. Idonta ya kumbura saboda kuka.. Babu kaya a jikinta, haka ta lalumi kayan ta saka..Tana rawar sanyi.. Maleekh yana kwance sai baccin yake ta sha. Baccin gajiya.. A hankali ta tatta6a shi. Ya farga yana addu'a tare da lumshe ido.. Wani ƙaramin yaro ne ya leƙo cikin ɗakin, yana cewa: “Shugaba ya ce ku fito. Akwai abubuwan da za a gwada yau.” Dukkansu suka kalli juna da tsoro. “Wane irin gwaji kuma?” Maleekh ya tambaya. “Ba ni da ikon faɗi,” in ji yaron, ya gudu. A Wajen Gari Sun fito. Mafarauta suna tsaye a layi, tsirara daga sama zuwa ƙasa, sai ganyayyaki a jikin su. Da makamansu wuƙa, baka, kibau, sanda mai karan ƙarfe.. Mutanen gari sun yi shiru. Shugabansu, dattijo mai dogon gemu da tabo a fuskarsa, ya ce: “Yau kwana na biyu kenan. Dole mu tabbatar idan akwai ‘alamar ciki’ ko babu.” Maleekh ya ji jikinsa ya sake, tsoro ya daki zuciyarsa. “Wace alama kuke nema?” ya tambaya a hankali. Shugaban ya ɗauko wani ƙaramin kwandon itace da ganye kore da farar laka a ciki. “Zamu yi gwajin ganyen Takur-shi. Idan matar nan ta zauna a kai, ganyen ya yi fari to ciki na nan. Idan ya koma baƙi, to babu komai. Idan babu komai kafin kwana uku, sai dai hukuncinmu.” Amal ta jijjiga kai tana kuka: “Don Allah, na gaji! Wannan abu ya yi min yawa…” Sun ba ta ganyen. Sai suka tafi su biyun zuwa wani yanki na dajin da babu mutane. Sai wasu mata masu rakiya.. Suka isa wani wuri mai sanyi da bishiyoyi. Suka zauna a ƙasa... Amal na kuka kamar ranta zai fita. Maleekh ya riƙe hannunta, yana jin zafin duniya a kansa. “Ki yi haƙuri. Ki zauna a kai. Allah zai yi mana mafita…” Ta zauna a hankali kan ganyen da ke cikin kwandon. Suka jira. Shiru. Sai kukan tsuntsaye. Mintuna suka wuce. Maleekh ya ɗaga ta sannan ya duba ganyen a sannu… Ya yi fari. Amal ta yi ajiyar zuciya. Amma shi ya gane wani abu… Ba fari sosai ba ne, daidai tsakanin fari da launin baƙi yake.. “Wannan ba alamar fari bane.” ya faɗa a ransa. Amma bai faɗa mata ba saboda tsoron ya ƙara rikita ta. Ta yi murmushi kaɗan, cikin hawaye: “Alhamdulillah… ka gani?” Ya yi mata murmushin ƙarya: “Na gani.” Amma hankalinsa ya cika da tambaya: “Idan suka ga ba fari sosai ba fa?” Sai suka miƙe suka koma gari.. A GABAN MAFARAUTA Shugaban ya karɓi ganyen ya kalla da kyau. Mafarautan suka kange su a kewayen wuri gaba ɗaya. Dattijon ya ce cikin murya mai nauyi: “Ganyen ya nuna… ba cikakkiyar alama ba ce. Wato… wataƙila ta fara, ko kuma babu komai.” Wani matashi daga cikin mafarauta ya yi ihu: “To mu jefa shi cikin tekun! Dokarmu ba wasa bane!” Amal ta fashe da kuka tana riƙe da Maleekh sosai: “Dan Allah ku ba mu zuwa gobe! Don Allah! Gobe ne kwana na uku! Don Allah!” Matar shugaban wacce ta cece su jiya ta shiga tsakani: “Ku bar su. Ba ku ga fari ba? A ajiye hukunci zuwa gobe. Gobe ne rana na uku..." Mafarautan suka yi gurnani da jin haushi, amma babu wanda ya ƙi umarnin matar shugaba. Shugaban ya yi magana a tsawa ce: “Kwana na uku zai yanke hukunci. Ko ciki ko teku...!” Maleekh ya lumshe ido, zuciyarsa na bugawa. Amal ta riƙe hannunsa tana kuka... “Ba za su kashe ka ba… ba zan bari ba…” Amsar da ta fito daga bakinsa cikin muryar da ya yi ƙoƙarin ɓoye rawar kuka ita ce: “Idan Allah bai kawo mu’ujiza ba… gobe zan ga ƙarshena.” Daren ya gangaro da sauri a dajin. Ga wutar da mafarautan suka kunna a tsakiyar ƙauyen... An mayar da su cikin ɗakin su na ganye da itace. Kamar jiya, babu kofar rufe wa... Sai da suka shiga suka zauna sannan suka ji zuciyoyinsu biyu suna bugawa da sauri. Amal ta jingina da bango, hannunta na riƙe da ƙirji. Maleekh ya zauna a gabanta cikin nutsuwa. “Gobe shine ƙarshe… idan ba a samu cikakkiyar alama ba…” Ya kasa finishing kalmar. Ta ɗago kai cikin hawaye: “Dan Allah kada ka faɗi hakan. Ka tuna da addu’a.” Sai ta matso kusa da shi, ta jingina kanta a kafaɗarsa. Zuciyarsa ta lafa kaɗan. Saɓanin Jiya, A Yau Dajin Ya Yi Shiru Babu sautin komai. Kamar an dakatar da dukkan halittu saboda wani abu da zai faru. Sai dai daga can nesa, suna iya jin: Takk! Takk! Kamar ana yanka itace. Maleekh ya ɗaga kai da sauri. “Ina jin kamar suna shirya wani abu…” Amal ta matso kusa da shi sosai, muryarta na rawa: “Ka riƙe ni… ban jin daɗi.” Ya riƙe hannunta, yana shafa bayanta a hankali... Daga can suka ji shigowar mutum yana matsowa cikin ganyen da ke rufe su. Amal ta sa hannu ta rufe bakinta saboda tsoro kar ya ji motsi. Maleekh ya riƙe ta sosai yana whispering: “Shhh… ki zauna a baya… bari in wuce gaba.” Ganin dajin babu wani abu da zai kare su sai Allah, ya matsa kusa da ƙofar itacen da aka ɗaure. Wani irin bakanen mutum ne ya leƙo gashinsa a ɗaure da igiya, kuma ganyen da ya rufe jikinsa ya fi na sauran nauyi... Ya yi magana a hankali kamar ba ya son wani ya ji: “Ku kwana lafiya… amma ku sani akwai wasu da ba su yarda da ku ba.” Maleekh ya tsaya daram: “Wa ye kai? Ka zo ka cutar da mu ne? Mutumin ya ce: “Ba don cuta ba. Don gargaɗi. Wasu maza sun ce gobe ba za su jira gwaji ko alama ba suna so su ɗauki matar nan.” Amal ta fashe da kuka. “Sun ce idan ba ka ba ta ciki ba, to zasu yi mata ‘tubani’ wato su raba ta gida biyu su bayar ga wasu...” Maleekh ya ji jikinsa ya yi sanyi gaba ɗaya. “Wannan ba adalci bane!” Mutumin ya yi shiru na daƙiƙu kuma ya ce: “Ni ɗin ba ni da iko. Na zo ne in sanar da ku. Ku kwana a farke… ku yi addu’a. Gobe ba zai yi sauƙi ba.” Ya ɓace kafin su ce wani abu. Bayan ya tafi Suka zauna su biyun kamar kurame. Maleekh ya zura ta cikin jikinsa ya rungume ta sosai, zuciyarsa tana bugawa kamar tambari. Amal ta ce cikin kuka mai sanyi: “In ba mu tsira ba fa? In gobe ta yi fa?” Ya goge mata hawaye, “To ki saurare ni. Idan suka zo gobe, ko me zai faru, ba zan bar ki ba. Idan ni za su kashe to ki tabbatar kin gudu. Ki gudu ki kuɓuce...” Ta girgiza kai da sauri: “A’a! Ba zan bar ka ba!” Ya kalli idonta cikin duhun ɗaki, ya shafi kumatunta: “Kin riga kin zama matata. Kuma zan kare ki da rayuwata...” Ta matsa jikin sa sosai, tana jin numfashinsa yana tafiya da sauri. Daren ya yi tsawo, suna jin bugun zuciyar juna kawai. Yau babu wani wanda ya kusanci su cikin ɗaki, amma tsoron gobe ya fi duk wani abu tsanani.. Amal ta yi magana cikin rauni: “Ka yi addu’a ka sake rungumata… zuciyata na tsalle.” Ya sake matseta a hankali, suna kallon fitilar daji ta waje tana ɗaukar ido. Cikin sanyi da matsanancin tsoro, suka kwana suna rungume da juna har gari ya fara haske... Gobe… gobe… ita ce ranar hukunci.... _NEXT NEXT NEXT_ asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 83 to 84 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Da asuba, hasken farko ya shiga cikin dajin. Amal da Maleekh sun buƙaci a kaisu bakin ruwa domin wankan tsarki na janaba, kamar yadda addinin Musulunci ya tsara, duk da cewa mutanen dajin ba sa bin wannan dokar.. ​Maza biyu ne suka rakosu, masu gadinsu. ​Bayan sun yi wankan tsarki, kusa da wurin ruwan, suka yi sallah. Domin wurin shine wurin da suke ganin yafi tsarki. ​A lokacin da masu gadin suka juya bayansu don gudun ganin tsaraicinsu yayin da suke wanka, Maleekh ya fahimci cewa wannan ce damarsu ta ƙarshe. Ya riƙe hannun Amal da ƙarfi. ​A hankali, ya furta ciki-ciki, “Mu gudu… ki riƙe hannuna, mu gudu…” ​Amal ta dube shi cikin tsoro ta ce, “Machine ɗin yana hannunsu. Ba zamu iya tafiya ba!” ​Ya ce, “In sha Allah zamu tsira, ba tare da machine ba. Allah yana tare da mu, zo mu tafi!” ​Basu jira wani tunani ba. Suka ratsa wani wuri da masu gadin ba sa nan. Suka yi amfani da juyawar bayansu a matsayin kariya kuma suka fara gudu cikin dajin. ​Can aka ji shiru. Masu gadin suka leƙa, sai suka ga ba su nan. Nan da nan aka hura ƙaho, kuma dukkan mutanen dajin suka bazama, suna neman su. ​Suna gudu cikin dajin ba ji ba gani. Ba takalmi a ƙafafunsu, suna taka kwalabai da itace masu kaifi, amma basu tsayar da gudun ba. ​Daga nesa, aka fara harbo kibiyoyi. ​Cikin sa’a marar kyau, wata kibiya ta samu nasarar harba ƙafar Maleekh. Wata kuma ta shige shi a baya. Amma bai saki hannun Amal ba. Ya ci gaba da gudu, yana jan ƙafarsa da ƙyar. ​Sun kai bakin wani babban ruwa wanda shi ne iyakar dajin da kuma mafarautar suke. Idan suka tsallaka, sun tsira. ​Cikin sa’a, suka tarar da wani ƙaton taya a wurin. Maleekh ya ɗauko shi da sauri, domin mutanen sun kusan iso wa. ​Ruwan yana da matuƙar zurfi. ​Ya ɗora tayar a wuyan Amal, sannan ya jefa ta cikin ruwan, yana faɗin, “Ki riƙe tayar sosai. Kiyi ƙoƙarin tsallakewa. Ba zan bari a cutar da ke ba!” ​Amal tana kuka tana faɗin, “Babu yanda zanje na barka! Kazo mu tafi tare!” ​Tayar ce ke ta tafiya da ita, kamar jirgin ruwa. ​Shi kuwa Maleekh, jini sai zuba yake a jikinsa. Kibiyar da ya ji a baya ta yi masa rauni, amma da saninsa ya yi ƙoƙarin tare kibiyoyin don kada su same ta. Dafin kibiyar ya fara ratsa shi. ​Yana tsaye, sai da ya tabbatar da ta yi nisa, sannan shima ya juya, ya bi wata hanya daban, yana jan ƙafa da gudu da ƙyar... ​Bayan Maleekh ya bar wurin, sai ga mafarautan dajin sun iso, suna ihu. ​Suka tsaya a bakin ruwan, suna hango Amal ita kaɗai a tsakiyar ruwan, cikin tayar. Har ta kai tsakiya, ta bar yankinsu, ta shiga wani yanki daban. ​Mutanen dajin suka firgita, da cewa “Wannan yarinyar ce ita kaɗai ta tsere mana! Shin ina yaron? Duk yanda akayi yana cikin yankin nan!” ​Suka ga yadda jinin Maleekh ya zuzzuba, ya zama kamar wani rubutu a ƙasa. “Ba zai yi nisa ba. Yana kusa…” ​Suka durƙusa, suna laluben ƙasa. Suna biye da tabon jinin, wanda ya yi layi kamar zane. Suna binsa, kamar karnukan farauta. ​Maleekh yana ci gaba da gudu, numfashinsa na fita. Kibiyar bayansa ta yi masa nauyi, dafin kibiyar yana ci gaba da cin jikinsa kamar wuta marar hayaƙi. Ya ji jikinsa yana sanyi, hannayensa suna rawa. ​Ya ji ƙasa ta juya masa. Yayi tuntuɓe ya faɗi amma da haka ya miƙe da ƙyar, yana jan ƙafa ɗaya kamar gurgu. ​Kamar daga sama ya ji muryar su daga bayan daji, “Ga shi nan! Ga jinin nan yana tafe!” “Kada ku bari ya tsere! Ku kama shi kafin ya tsallake yankin mu!” ​Hankalin Maleekh ya ƙara tashi. Gumi ne ke ta kwaranya a jikinsa, zuciyarsa tana bugawa kamar ƙaho “Kar na mutu kafin in tabbatar ta tsira… kar su kama ni domin bana so na hallaka a hannunsu.” Da ƙyar ya rarrafa. Ya kama jikin wata bishiya mai kaifi, yana jan kansa gaba. ​Har sai da ya ji ƙafarsa ta zame, ya faɗi ƙasa da ƙarfi. Kibiyar da ke bayansa ta makale sosai, ba ƙaramin shigarsa tayi ba.. Ya yi ihu kaɗan yana cije haƙoransa.. ​A lokacin ya ji ƙafafunsu sun kusanto. ​“Ga shi nan!” ɗaya ya yi ihu. “Kada ku bari ya mutu nan! Ya kamata mu jefa shi cikin babban tekun nan, yadda doka ta ce!” ​Ya kalli gaba, sai ya ga ƙaramin kwazazzabo a cikin ƙasa, ramin da ruwa ya tone... ​“Wannan ce damar da ya rage…” ​Maleekh ya tattara ƙarfin da bai san yana da shi ba. Ya nannarke jikinsa cikin ramin, yana ɓoye kansa da ƙasa.. ​A dai dai lokacin da suka iso, sai jinin da ya zuba ya tsaya a bakin ramin, amma babu alamun sa. ​“Sai dai idan ƙasa ta haɗiye shi!” "Amma babu yadda za'ayi ya shige ƙasa, dole yayi wani hanya daban..." Suka ƙareshi maganarsu daga bisani suka ci gaba da bi, suna bazama cikin daji, suna ta ihu. ​Maleekh kuwa yana ɓoye a ciki, kamar gawa. Numfashinsa na fita a hankali. Jikin sa yana rawa. ​A hankali, ya furta cikin zafi. “Allah… ka kare ta… ka kare ni…” ​Ruwan rami ya fara cika wurin da yake kwance, saboda ruwan yana zuba daga sama. Yana jin jikinsa yana nutsewa. ​Sai duhu ya mamaye shi. ​Daga nesa, muryar mafarautan ta sake tashi da ƙarfi, “Mun rasa shi! Amma dole sai an same shi kafin dare! Mai cin dokar mu ba ya rayuwa!” ​Maleekh ya shiga cikin duhu mai sanyi. Ruwan ramin yana ci gaba da cika, yana shigar masa hanci da baki. Dafin kibiyar yana aiki tukuru, yana kashe masa jijiyoyi, kuma zafin kibiyar da ta shige shi ya sanya jikinsa ya yi nauyi kamar guba. Ya ji kamar ruwan ya rufe shi gabaki ɗaya. ​Amma a cikin wannan nutsuwar, wani ƙaramin abu ya haskaka a cikin zuciyarsa wato Amal. ​“Kada in mutu kafin in tabbatar ta tsira…” ​Wannan tunani ya zama ikon numfashinsa. Ko da yake numfashinsa yana raguwa, tunanin cewa idan ya mutu mutanen dajin za su dawo su nemo ta ya ba shi ƙarfin da ya tilasta masa buɗe idanunsa da suka rufe da ƙasa. ​A hankali, Maleekh ya fito da yatsunsa daga cikin laka. Ya ɗaga kansa daƙyar, ruwan ramin ya kusan cikowa, ya zama kamar wani ƙaramin kogi mai ruwan laka. Ya ji motsi sama da shi, sautin tattaunawar mafarautan sun fara raguwa, alamun suna ta nisa. Suna ci gaba da bin sawun da basu samu ba. ​Ya jira har sai da shiru ya sake mamaye daji. Dajin ya koma wurin tsoro. ​Daƙyar ya fito daga cikin ramin. Jikinsa ya yi sanyi, ga zafi, ga zufa. Kibiyar ta shige shi sosai, kuma ya san cewa dole ne ya cire ta ko ya mutu.. Jikinsa duk taɓon ƙasa, haka ya rarrafa ya je ya wanke fuskarsa sannan ya jingina da wata bishiya mai kauri, ya tattara duk wani ƙarfi na ƙarshe. Cire kibiya mai dafi na iya zama haɗari, amma Maleekh ya san cewa barin ta ma zai kashe shi. ​Haka ya riƙe jikin kibiyar da ƙarfi, ya yi ihu marar sauti saboda zafin da bai taɓa ji irinsa ba, kuma ya ja ta da sauri. Jini ya sake ɓarkewa daga jikinsa, amma tare da shi wani nauyi da zafi ya ɗan ragu. Ya faɗi ƙasa yana huci, amma ya yi nasara. ​Ya tattara wasu ganye waɗanda ya san suna da magani ya ɗaura su a kan rauninsa da rigansa da ya yage. ​Maleekh ya fito da kansa gabaɗaya daga dajin, ya fara tafiya zuwa bakin ruwa da ya bari, yana jan ƙafarsa da take ciwo. Burinsa shine ya tarar da wata hanyar da zai iya ƙetare ruwan. Ya san cewa idan har Amal ta tsira, dole ne ya yi haka... A wannan ranar a bakin ruwa ya kwana.. Yana shan iska da sanyin wurin.. Asubar fari duk da bai san lokacin sallah ba a wurin haka ya yi alwala da ruwan sannan ya tsaida sallah. Yana cikin sallah sai ga wasu daga cikin mutanen sun afko masa. Yana jin yanda suke ta ihu suna ɗaga makamansu sama amma haka ya ci gaba da sallah. Wasu ne suka fara kwaɗa masa sanda a baya ga raunin kibiya. Haka yake daure wa sai da ya kammala sallarsa yayi sallama sannan ya ɗaga hannu sama yana addu'a.. Wani ne ya kwaɗa masa a tsakiyar kai sai a lokacin ne ya riƙe kansa tare da sakin ihu... Wani irin ƙarfi ne ya ziyarce shi a take ya riƙe ya riƙe hannun wani daga ciki wanda ya kawo masa sara da adda. Wani irin zulluya yayi ya miƙe ya murɗe addar, cikin fusata yake kai musu sara da addar.. ​Maleekh, duk da raunukan da ya ke fama da su amma jarumtarsa ta ƙaru. Kuma haka ya ci gaba da sararsu, har sai da ya kashe su duk yawansu. ​Bayan ya gama da su, ya fara jin ihun wasu mutane da suke tahowa da gudu, kuma suna da yawa. Maleekh ya jefar da addar, jini na zuba daga raunukan da ya ji. Yana jin ihun sababbin mafarauta suna tahowa. Ya san cewa duk da nasarar da ya samu a kan waɗannan mutanen, ba zai iya sake fuskantar taron mutane ba tare da ya mutu ba. Dafin kibiyar da kuma raunin faɗa sun yi masa nauyi.. ​Ya tattara ragowar ƙarfin da ya rage, ya juya, ya fara gudu cikin zurfin daji inda duhu ya mamaye ko'ina, duk da yanzu ba dare bane. ​ Maleekh yana gudu ne da ƙafa ɗaya mai rauni, raunukan da ya ji a faɗan suna ci gaba da buɗewa, yana zubar da jini a kowane mataki. ​Ya yi ta tuntuɓe a kan kwalabai da sassanyan bishiyoyi, duk yana roƙon Allah ya ba shi ƙarfin da zai ci gaba. Amma ganinsa ya fara rufe wa. ​ Ya tsallake wani rami mai zurfi da duhu. Bai gane ba, saboda duhun ya yi masa katanga. ​Ya faɗa cikin ramin da ƙarfi mai ban tsoro. amma sa'ar ta juya lokacin da kansa ya bugu da wani ƙaton dutse mai kaifi. A take, ya sume a cikin ramin... Mutanen dajin sun isa wurin faɗan. Sun ga gawarwakin 'yan'uwansu a warwatse. Fushin su ya ƙaru. ​“Ya kashe su! Wannan yaron ba mutum ba ne! Ruhu ne na daji!” wani ya yi ihu cikin mamaki da tsoro. ​Suka bi sawun jinin Maleekh. Suna ta ihu, suna ta nemansa, amma duhun ya ba shi kariya. ​Sun zo bakin ramin, amma rami ne mai zurfi da duhu ya rufe shi. Jininsa ya tsaya a bakin ramin, amma ba su ga faɗuwar tasa ba. ​“Babu shi! Ya gudu! Ko kuma duniya ta haɗiye shi! Ku cigaba da nema! Ba za mu koma ba tare da shi ba!” Sun ci gaba da nemansa har tsawon dare, ganin basu same shi ba yasa suka koma yanda suke da safe ba tare da nasara ba. Doka ta ce dole ne a rama mutuwar 'yan'uwansu, kuma sun sanya farashin duk wanda ya nemo Maleekh.... ​Ita kuwa Amal bayan ta tsallake ruwa, tana tafiya a can gefen ruwa, ta fara jin wani irin hajijiya saboda ƙaton ruwan tekun da ta shiga. Anan ta faɗi itama ta suma. ​Sai da ta kwana a wurin. Da sassafe, wasu matasa Fulani suka tsince ta. Mutanen Fulani ne, da matansu da yara. Suka kaita wata ruga. Anan aka fara mata jinya. Amal ta farka daga sumewar wahala da hargitsin jiki da ta samu sakamakon tafiya mai tsawo a ruwa. Ta fara jin ƙamshin madara da hayaƙi. ​Tana buɗe idanunta, ta ga wata mata Fulani tana sanye da kayan fillo farare, tana gauraya wani abu a cikin ƙaramin tukunya.. ​“Sannu da zuwa, 'yar gida,” matar ta furta “Mun same ki a bakin ruwa. Jikinki duk ya yi sanyi.” ​Amal ta yi ƙoƙarin tashi, amma rauninta da hajijiyar da ta shiga sun hana ta. Ta ji kamar ta shiga wata sabuwar duniya. ​Matan Fulani sun yi mata jinya ta gargajiya. Sun yi amfani da ganyen magani da man shanu don shafa mata a jiki. Sun ba ta madara mai zafi da nono don dawo da ƙarfinta. ​A rugarsu akwai zaman lafiya da tsafi. ​Amal ta kwashe kwanaki tana murmurewa. Ta ƙudurce cewa ba za ta faɗa musu cikakken labarinta ba tukuna, don tsoron kada su gane ta kuma su mayar da ita. Ta dai faɗi musu cewa ta rasa iyayenta ne a cikin ruwa. Amal ta koyi zaman gida da kuma yadda Fulani suke mu’amala. ​A cikin zuciyarta, Maleekh shine burinta.. Tunaninta kullum akan Maleekh. 《》《》《》《》《》《》 Tashin hankalin a ya mamaye Abuja. Mutane ba su san inda Amal da Maleekh suka shiga ba tun bayan sace Amal da Maleekh ya yi ta hanyar Superbike a wurin walimar aure.. ​Inna ta shiga cikin tsananin tashin hankali da baƙin ciki. Tana zaune a cikin falonta mai tsada, amma babu wani abu da yake da daraja a idonta face Amal. ​Inna tana kuka tana faɗin “Na rasa Ɗana (mahaifin Amal), yanzu kuma ga Amal ta shiga cikin haɗari! Ina Maleekh ya kaita? Me yasa zai raba ta da mutuncinta har haka?” ​Abbah shima ya shiga gigicewa. Yana jin laifin rashin kulawa, da kuma laifin ɗansa da ya kawo masa ci da baƙin ciki a idon abokinsa (mahaifin Amal) da ya mutu. Abbah ya yi amfani da dukkan hanyoyin jami'an tsaro da kuɗi da yake da su don neman yaran. Ya san cewa idan ba a gansu ba, za a iya zargin Maleekh da sace mutum (kidnapping), duk da cewa an san suna soyayya. ​‘Yan sanda sun fara bincike a duk manyan hanyoyin fita daga Abuja, suna neman motosar Superbike ɗin Maleekh.. ​Hotunansu sun bazama a shafukan sada zumunta da kuma gidajen rediyo, amma babu wani shaida mai ƙarfi da aka samu. Zayd kuwa daman yasan aurensa da Amal ba mai yu wa bane kawai ya amince ne... Domin yasan Maleekh bazai taɓa bari ba.. ​Babban Sufeto mai kula da case ɗin neman yaran, wanda ke da hankali da gogewa, ya gano wasu bayanai masu mahimmanci: ​ Binciken Sufeto ya sanar cewa “Wannan ba sace mutum ba ne na tashin hankali. Wannan guduwa ce ta masoya. Amma gudunsu ya yi nisa sosai har muka rasa sawun su. Ga alama, sun shiga wani wuri ne da ba shi da hanyoyin sadarwa.” ​Ya gano cewa Abbah ya riga ya ajiye wasu tsare-tsare na gano su, ta hanyar satellites da kuma wasu ƙwararrun masu binciken sirri. Ana zargin cewa sun shiga yankin daji ne saboda Motosar Superbike ba za ta iya tafiya nesa a kan hanya ba tare da shan mai ba. ​Bayan kwanaki da yawa na bincike mai tsanani, wata ƙwararriya a fannin fasahar sadarwa ta gano wata yar ƙaramar siginar waya da ta fito daga wani wurin da ba a sani ba a wani wuri mai nisa da Abuja, kusa da wani babban dajin da aka sani da haɗari. ​Sifeto ya fahimci cewa wannan siginar na iya zama wayar Amal ko ta Maleekh, ko kuma wani tsarin sadarwa da suka yi amfani da shi kafin a gano su. ​Ya ƙira Abbah ya sanar da shi cewa, “Muna da wani wuri. Ga alama sun shiga cikin wani babban daji mai haɗari. Dole mu tura ƙwararrun mutane su shiga nan da nan.” Duk da irin bincike mai tsanani da jami’an tsaro da masu neman sirri na Abbah suka yi, binciken ya kasance a banza. An shiga dukkan kwa-kwa da rassa na dajin, amma babu wanda ya ga ko wani alamar Amal ko Maleekh. ​Hakan ya faru ne saboda basu da wata wayar hannu da za a iya bin sawunta (tracking), Maleekh kuma yana kwance sumamme a cikin rami mai duhu, ita kuma Amal tana cikin ruga mai nisa inda hatta mutanen rugar gaba ɗaya basu da wayoyin sadarwa.. 《》《》《》《》《》《》《》《》 ​Bayan tsawon watanni shida na neman da aka yi ba dare ba rana, an haƙura da neman. An ba da sanarwar cewa watakila yaran sun shiga tekun haɗari ko kuma sun rasa rayukansu a cikin daji. Inna ta fita daga hayyacinta, shima Abbah ya shiga cikin baƙin ciki da nadama mai tsanani. Ga an rufe shari’ar... ​Amal ta samu kulawa ta musamman a cikin Rugar Fulani. Ta yi amfani da nutsuwar wurin da magungunan gargajiya don warkewa daga wahalar da ta sha a dajin. ​Bayan tsawon watanni, Amal ta fahimci cewa ikon Allah ya ɗaura mata juna biyu a cikin ɗan kankanin lokacin da suka yi tare da Maleekh a wurin mafarauta. Sun sadu da juna har kwana biyu, a rana ta uku ne suka gudu. A yanzu, tana ɗauke da ciki na tsawon watanni shida. ​Wannan ciki ya zama shaidar soyayyarsu da kuma sadaukarwarsu a ƙarƙashin barazanar rayuwa. ​Amal ta tattara ƙarfin hali ta gaya wa Fulani gaskiyar labarinta daga soyayyarta da Maleekh, zuwa ga sace ta, zuwa ga auren da aka ɗaura musu a daji, har zuwa ga gudun tsira. ​Mutanen Fulani, da yake mutane ne masu tausayi da mutunta rayuwa, sun karɓe ta da hannu biyu. Sun ɗauke ta a matsayin ɗiyarsu ta gaskiya kuma suka yi alkawarin kare ta har sai ta haihu. Cikinta ya zama alamar bege a cikin wannan ruga mai nisa... Duk da a yanzu mutanen rugar basu zauna ba, suna nema mata hanyar da zata bi don ta koma gida.. ​Shi kuwa Maleekh, bayan tsawon wata ɗaya a kwance a cikin ramin da ya faɗa, wasu Sojoji sun tsince shi. Sojojin sun shigo yankin ne domin gudanar da aiki na yaƙi (military operation), kuma sun same shi cikin jini, sumamme a cikin rami mai zurfi. ​Sojojin sun ɗauke shi, sun fara bashi kulawa ta musamman (medical treatment) a sansanin su na ɗan lokaci. ​Bayan wata ɗaya da ya yi a hannun su, ya farfaɗo. Sai dai mamaki da firgici suka lulluɓe Sojojin. ​Maleekh bai san inda yake ba. Ba ya gane fuskarsa ko hannuwansa. Saboda tsananin buguwar da ya yi a kansa lokacin da ya faɗi a cikin rami ya bugu da dutse, kwakwalwarsa ta juye. Ya shiga cikin cikakken mantuwa (Amnesia). ​ Bai san sunansa ba. Ya manta da wata Amal. Sannan a yanzu ya manta da Mahaifinsa. Bai san yadda ya fito daga cikin wayewar gari ba. ​Sojoji sun riƙe shi, suna bashi kulawa sosai har tsawon watanni shida suna jiran farfaɗowar ƙwaƙwalwarsa. Amma shiru. Babu wanda ya sanshi a wurin, kuma Maleekh bai iya bayar da ko wani bayani game da kansa ba. Sun sanya masa wani suna na wucin gadi a cikin sansanin.... _NEXT NEXT NEXT_ asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 85 to 86 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 ​A cikin ruga, kwatsam, wani matashi ɗan Fulani wanda ya shiga birnin Suleja don kasuwanci ya dawo da wani labari mai zafi. Ya samo wata jarida wadda ke nuna hotunan Amal da Maleekh, kuma ana neman su. ​Labarin ya nuna cewa: Ana neman Amal da Maleekh waɗanda suka ɓata. Akwai kyauta mai tsoka wadda za ta wadata mai ba da labari har karshen rayuwarsa. Haka kuma, an saka lambar waya don tuntuɓa. ​Nan da nan, matashin ya koma rugar da wata ƙaramar waya (torchlight phone). Ya sanar da mutanen rugarsu abin da ke wakana. Duk da cewa watanni shida sun shige, wannan wata dama ce ta zinare don bayyana Amal ga iyayenta. ​Amal ta ji labarin, sai farin ciki da tashin hankali suka shige ta lokaci guda. Ta matsu da ta je ta ga Innanta. Amma sai mutumin ya sanar mata da cewa tsakaninsu da Suleja da kuma Abuja nesa ce sosai. ​Sai dai, basu yi ƙasa a gwiwa ba. Suka ƙira lambar wayar da ke jikin jaridar. Lambar jami'in tsaro ce mai kula da binciken tun farko. Mutumin Fulani ya gaya masa duk abin da ya faru. ​Jami'in ya ƙira Abbah a waya, yana sanar masa cewa: "An samu Amal, a wani yankin ƙauye mai nisa." ​Abbah ya kasance tare da Inna a lokacin. Inna ta yi farin ciki sosai har ta miƙe, tana godiya ga Allah tana kuka. ​A wannan ranar, an tayar da jirgi mai saukar ungulu (Helicopter). Abbah da wasu jami’ai suka shiga cikin jirgin. Sun riga sun yi amfani da fasaha (tracking) don gano wurin da aka ƙira su, saboda haka basu buƙaci wani ƙarin bayani ba. ​Nan da nan, sai ga su a sararin rugar Fulani. Mutanen ruga sun yi mamaki sosai sai ganin Elekwabta sukayi yana shirin saukowa a tsakiyar daji! ​Abbah da Jami'an suka sauƙo. ​Jami'i Yana magana da ƙaramar waya "Mun iso. Muna kan bakin rugarku." ​Matashin Fulani Yana duban jirgin sama da mamaki ya je yanda suke yana faɗin, "Na ganku! Ga ni nan! Ku biyo ni!" ​Anan matashin Fulani ya sanar musu wurinda Amal take. Suka fara tafiya da sauri, sai ga su a gidan Fulani inda Amal take zaune. ​Amal tana zaune a ƙasa, da tsohon ciki, wata mata Fulani tana bata nono don ta sha. ​Abbah muryarsa cike da tausayi, ya kusan fashewa da kuka ganin Amal. “Daughter?… My daughter?” ​Amal ta ɗago da sauri a zabure. Ta kalli mutumin da ya zama uba a gareta. ​Amal cikin kuka, muryarta a raunane ta ce “Abbah!…” ​Ta miƙe da gudu duk da nauyin cikinta, ta nufe shi, ta rungume shi da ƙarfi. Shima Abbah ya kasa riƙe hawayensa, ya fara kuka. Abbah ya rungume ta, yana shafa bayan ta, “Alhamdu Lillah! Ƴata, na gode wa Allah! Na gode wa Allah da ya nuna min ke. Na yi zaton na rasa ki har abada!...” Amal tana kuka ta ce, “Abbah, na shiga wahala! Na yi kewar ku! Na yi kewar Inna! Allah ya ceci rayuwata, Abbah!” Jami'i yana motsa Abbah a hankali ya ce “Ranka ya daɗe, ya kamata mu rage kukan nan. Muna buƙatar mu tafi nan da nan. Tana buƙatar kulawa ta musamman.” Abbah ya saki Amal, yana riƙe da hannunta, ya kalli cikin nata ya ce “Wannan… me ya faru? Wannan… Maleekh ne?” Amal ta sunkuyar da kai cike da kunya ta ce, “Eh, Abbah. Auren da suka ɗaura mana ne a dajin… Amma Abbah, Maleekh ya ceci rayuwata. Bai bar ni ba. Muna son juna.” Abbah ya numfasa da wani dogon numfashi, ya shafa cikinta ya ce, “Allah ya muku albarka, rayuwarku tafi komai muhimmanci … Ba komai, ƴata. Wannan tsari ne na Allah. Yanzu dai mu tafi.” Bayan haɗuwar, Abbah bai manta da kyautatawa da mutuntawa ba. Ya yi wa dukkan mutanen ruga babban alkhairi. An raba musu makudan kuɗaɗe, amma gidan da Amal ta zauna da kuma matashin da ya sanar musu sun fi samun alheri da arziki sosai. An cika musu alkawarin kyauta. ​Ba a jira wani abu ba. Suka ɗauki Amal. ​Amal tana kuka tana yi wa matan Fulani da suka riƙe ta bankwana. Sun shaku sosai, kuma sun yi mata alkawarin addu'a da kuma fatan samun lafiya. ​A lokacin da suka shiga cikin Helicopter, Abbah ya tambayi Amal: “Ina Maleekh? Ba ku tare ne?” ​Amal cikin hawaye ta ce, “Na barshi ne a bakin ruwa… An harbe shi, Abbah, ya yi ta jini. Ya bani tayar na gudu… Ban san yanzu yana ina ba.” ​Ganin cewa babu wanda ya san inda Maleekh yake kuma yana cikin matsanancin haɗari, suka yanke shawarar wucewa gida tare da Amal don a ba ta kulawa ta musamman.. Bayan Jirgin Helikwafta ya sauƙa a Abuja, gidauniyarsu ta cika da mutane. Kowa yana cikin mamaki da tsananin alhini. ​Abu na farko da kowa ya lura da shi shine cikin Amal. Sai dai, abin da ya fi muhimmanci a idon kowa shine tambaya ɗaya: “Ina Maleekh? Yana ina shi?” ​Ammy ta rungumi Amal cike da kewa da tausayi. Amma hankalinta ya tashi, ganin cewa ba a samu Maleekh ba, kuma Amal ta tabbatar da cewa an harbe shi a gaban idonta. ​Nan take, Ammy ta durƙusa, ta fara kuka sosai. Muryarta na fita da ƙarfi, tana nuna tsantsar ciwon zuciya da rashin bege na rasa ɗanta. ​Abbah ya numfasa, cike da damuwa, amma yana ƙoƙarin nuna ƙarfin hali: “Ban ga amfanin ihun ba, Maryam. Tunda har aka samu Amatu shima Maleekh za a same shi. Ku kwantar da hankalinku, ina da yakini.” ​Ƙannen Maleekh, Islam da Arfat, suma haka suke kuka na rashin ɗan uwansu. Gidan ya kasance ba annuri tun watanni shida. ​Inna da Amal suka rungumi juna sosai, suna kuka.. ​Inna cikin kuka take cewa, “Duk laifinki ne, Amatu! Da a lokacin kin amince da Maliku, da hakan bata faru ba! Ya baki haƙuri a lokacin! Da kin amince da an fasa aurenki da wancan, an ɗaura da Maliku, da yanzu kuna zaman farin ciki!” ​Amal tana kuka tana shafa cikinta ta ce, “Inna, kaddararmu ce haka. Allah ya nufa hakan zai faru. Ga wannan cikin na Maleekh ne, amma ba ta hanyar alfasha ba. An ɗaura mana aure ne bisa dokar Musulunci… a cikin dajin.” ​Amal ta basu labarin abin da Mafarauta suka yanke musu: Cewa idan Maleekh bai yi mata ciki ba a cikin kwana uku, za su kashe shi su jefa shi cikin tekunsu mai zurfi, sannan kuma ita za su aura mata maza biyu a cikin mafarautan. ​Wannan labari ya sanya tausayi ya lulluɓe kowa. Sun fahimci cewa gudunsu ba wai don sha’awa ba ne, gudun tsira ne. An yi alhini sosai a cikin gidan. ​Nan take, aka ƙira likita aka duba lafiyar Amal da kuma ɗan da ke cikinta. ​Likita yana murmushi ya ce, “Dukkan su suna lafiya, amma dole ne ki rage yawan damuwa. Ki ci abinci mai gina jiki. Ki manta da abin da ya faru. Yanzu kin dawo gida lafiya.” ​Daga nan, aka fara ba Amal kulawa ta musamman, tare da abincin ƙara jini da na lafiya. ​Tana zaune a gidan Abbah don ta fi samun kulawa sosai daga Ammy da Inna. An ma buƙaci Inna ta ci gaba da zama a gidan, yayin da aka kulle gidansu na can. ​Yanzu Amal ta zama cibiyar tausayi ga kowa. ’Yan uwa da abokan arziki sun dinga zuwa duba ta. ​Farha, wacce yanzu ta ɗauki Amal a matsayin ƙawa, kullum sai tazo duba ta. ​Hatta Zayd shima ya zo ya ganta. Ya shigo cikin falo da fuska cike da fushi saboda kunya.. ​Zayd ya goya hannayensa, yana dubanta sama da ƙasa a yayin da babu kowa a falon sai su kaɗai. “Daman kun shirya guduwa ne? In ba haka ba, me zai kawo ciki? Ko ba komai, kun zubar da mutuncinku. Da farko kowa yana tunanin Maleekh sace ki yayi, amma yanzu ganin ciki ya sa kowa ya yarda guduwa kuka yi.” ​Amal, ta dube shi da kyau, ta yi wani murmushi na izgilanci fiye da nasa. ​muryarta a sanyaye ta ce, **“Daman na taɓa cewa ina sonka ne, Zayd? Dalilin da yasa zan aureka, saboda na musguna wa Maleekh ne. Amma kowa ya san cewa Amal da Maleekh su suka fi dacewa da juna. Kuma ga babyn Maleekh a jikina. Kaga kuwa soyayya tayi rana!” ​Zayd yana huci. Ya harare ta da wani mugun kallo sannan ya fita da sauri. Domin ba shi da ta cewa. ​Ammy tana ci gaba da ba Amal kulawa ta musamman har ta shiga watan haihuwarta. ​Kowa yana cikin farin ciki da jiran haihuwar, amma kuma cikin alhini na rashin Maleekh. ​Har zuwa yanzu, babu wani labarin Maleekh. Cikin dare, duk da cewa an rage mata damuwa, cikin Amal ya fara murɗa wa. Ta riƙe cikinta sosai, tana juyawa a kan gado. Ita kaɗai ce a cikin babban ɗakin kwananta da aka tanadar mata don kada a takura mata. ​Ta fara jin zafin nakuda mai tsanani. Ga kuma jini da ruwa suna bin ƙafarta. Ta fahimci cewa lokacin zuwan jaririn Maleekh ya yi. ​Ganin cewa ba za ta iya jurewa ba, kuma tana tsananin wahala, sai ta yi wani ihu mai rauni wanda ya ratsa cikin gidan. ​Ammy da Abbah suna ɗakinsu a upstairs suka ji ihun. Nan da nan suka sauƙo cikin tsananin firgici da gaggawa. A falon ƙasa, suka tarar da Inna da Islam da Arfat duk sun tashi daga barci. ​Dukansu suka nufi ɗakin Amal. Suka sameta a ƙasa, tana kuka riƙe da ciki. Nan da nan aka ɗauke ta da gaggawa zuwa Asibiti domin ba ta taimako. ​An garzaya da Amal zuwa asibitin masu kuɗi kuma mai daraja a Abuja. Asibiti ne da aka gina shi da kayatattun kayan gini, inda nutsuwa da tsafta suka mamaye kowane lungu da sako. ​An shigar da Amal cikin ɗakin aji Biyu (VIP Room) wanda ya yi kama da ƙaramin gida mai cin kansa, maimakon ɗakin asibiti. Bango ne da aka yi da launin zinare da creamy white, tare da fitilu masu laushi da ke ƙara annuri ga wurin. Gadon Amal tsararren gado ne, mai girma, tare da farin zannuwan gado masu taushi. Babban talabijin ne rataye a jikin bango, kuma akwai sofa masu taushi don waɗanda suka zo duba ta. Akwai ƙaramin falo a cikin ɗakin inda Abbah da Ammy suke zaune, yana nuna tsararren rayuwa da kuɗi suke bayarwa.. ​A cikin wannan ɗaki ne Amal ta sha wahalar nakuda har na tsawon dare. An mata allurai don rage mata zafi, amma ta ƙi, tana son ta ji tsananin zafi na haihuwar ɗan Maleekh... ​Da asubar farko, bayan tsananin wahala da jajircewa, Amal ta haifi ɗan namiji. Kafin a gama shirya jaririn, ta sake nakuɗa ta biyu cikin sauri, kuma ta haifi kyakkyawar yarinya mace. ​Amal ta samu Tagwaye (Twins) kyawawa! ​Jariran sun ɗauko kyawun gaskiya daga iyayensu, Maleekh da Amal, waɗanda tun asali kyawawa ne. Jariran manyan-manya ne, kuma fatar jikinsu fari tas mai haske, kamar farar fata ta Indian. ​Dukansu suna da suma mai kauri da dogon gashi a kansu, wanda ya yi kama da gashin al’adun Indiya. Ga ​idanuwansu farare, kuma suna da wani tsantsar annuri a fuskarsu wanda yake nuna cewa sun zo duniya da sa’a. ​Duk ma’aikatan asibitin sun yi mamakin kyawun jariran. ​Bayan an gama shirya jariran, ma’aikaciyar asibitin ta fito cikin farin ciki ta sanar da su Abbah da Ammy da suke jira a Compound (babban falon jira na asibiti). ​Ma’aikaciyar Asibiti tana murmushi ta ce da su, “Alhamdu Lillah! Muna taya ku murna! Allah ya sauƙe ta lafiya! Ba ɗaya ba, ba biyu ba… An samu Tagwaye! Namiji da Mace!” ​Dukansu sun cika da farin ciki sosai har suka yi sallama mai ƙarfi, suka gode wa Allah. ​An basu damar shiga ɗakin Amal domin ganin jariran. ​Suka shiga cikin tsananin farin ciki da kuma tausayi.. Uwar kuwa ta tafi dogon bacci sakamakon wahalar da ta sha da kuma alluran da aka mata don ta huta. ​Suna tsaye kowa ya kasa zama, suna kallon tagwayen da suka zama alama ta Maleekh a duniya.. ​Ammy tana kuka da murna, tana shafa kan jikokinta ta ce, “Maleekh… Maleekh na. Ga ‘ya’yanka sun zo duniya. Ina muku addu’a, Allah ya dawo da Abbansu!” 《》《》《》《》《》《》《》《》《》 Maleekh ya manta da komai a rayuwarsa, amma hakan bai hana shi saba da sabuwar rayuwarsa ba. Ya saba da Sojoji masu kula da shi, kuma kullum suna cikin wasa da dariya. ​Sojojin sun ba shi suna na musamman 'Lion'. Wannan sunan ya biyo bayan wata rana da suka shiga daji don motsa jiki, suka ci karo da wani zaki mai tsananin haɗari. Sojojin sun gudu, domin babu wanda ya taho da bindiga. Sai Maleekh da ya yi nasarar tinkarar zaki da tsananin ƙarfi har ya raunana masa ƙafa, wanda hakan ya sa zaki ya kasa ci gaba da binsu. Anan ne suka fara ƙiran shi 'Lion Man'. ​Sojojin sun fahimci cewa Maleekh yana da zafin rai (intensity), kuma babban mutum ne mai tsananin jarumta da basira. ​Maleekh ya zama cikakken Soja a cikin sansanin, domin aikin training ya ƙara masa jiki da ƙarfi. Ya zama masanin dabarun yaƙi duk da mantuwar da ya yi. ​ Daman yana da tsayi, kuma karfafan jikinsa ya cika da tsoka (muscle-bound), wanda yake nuna cewa mutum ne da yake aiki tuƙuru a harkar motsa jiki. ​ Hasken fatarsa mai laushi ya ƙaru, kuma kwantaccen sumar kansa mai baƙin gaske ya ƙara masa kyau. ​Ya ƙara kyau mai tsanani, wanda ya yi kama da tsararren Balarabe mai ƙarfi da kwarjini.... ​Yana zaune da Sojojin, yana basu training. ​Kwatsam, a yayin da suke tsaka da wani wasan dariya, Maleekh ya ji jikinsa ya yi sanyi sosai. Wani abu ne ya cije shi a zuciyarsa, wani jin daɗi da kuma firgici sun shige shi a lokaci guda. Ya riƙe ƙirjinsa, yana mamakin me ke faruwa da shi. Ya ji kamar yana buƙatar wani abu da yake da nutsuwa.. ​“Akwai buƙatar a ba ni madara in sha, nan take. Wani abu ne nake ji a jikina, amma ban san menene ba.” ​Wani soja ya dube shi da mamaki: “What? Lion! Ko ka fara tuna wani abu ne?” ​Maleekh ya girgiza kai cike da tausasawa ya ce, “Har yanzu dai, ban tuna ba. Amma jikina ya yi sanyi, da alamun akwai abinda ya faru. Kar ku damu, ina kan yin addu’a domin shine kaɗai ban manta ba. Wata rana, haske zai zo mun kuma zan gano kaina.” ​Sojojin sun fahimci cewa Lion yana da haɗin gwiwa na ruhi da wani abu mai mahimmanci a waje. Sun san cewa wannan jin sanyin na iya zama alamar farfaɗowa. Sun tafi da gaggawa domin su samo masa madarar da ya buƙata. 《》《》《》《》《》《》《》《》《》 ​A ɗakin asibiti mai tsada, Amal ta farka daga bacci mai zurfi. Ta ji ƙarfi da nutsuwa sun maye gurbin wahala. ​Ta fara buɗe idanunta a hankali, taci karo da kyawawan jariranta guda biyu. Wata nurse ce ke kula da su a gefen gadonta. ​Amal ta shiga farin ciki sosai. Ta yi kukan murna da godiya ga Allah. Nan da nan ta miƙa hannu, ta ɗauki ɗanta namiji wanda ya yi mata kama da ƙaramin Maleekh. ​Sai dai, duk da murnar, Maleekh yana cikin ranta da kuma zuciyarta. Ta sha alwashin cewa ba za ta taɓa dena kewarsa ba. ​🌟 ​Duk abokan arziki da ’yan uwa sun cika asibitin, domin sai ta samu hutu na musamman kafin su koma gida. Suna ta jiran ganin jariran. ​Amal tana kallon jariran ta yi tunani na musamman game da sadaukarwar Maleekh... ​Amal ta rungume ‘yan biyun, tana furta sunayensu a hankali: ​“Ke sunanki LIHAAM.. kai kuma AR'HAAN.. Ya’yan Maleekh, insha Allah Abbanku zai dawo ya ganku!” ​Ta rungume Ar’haan da Lihaam, tana musu addu’a da tunanin Maleekh a lokaci guda.... Duk mutanen da suka taru a asibiti sun yi mamakin sunayen da Amal ta sa wa jariran, waɗanda ba a taɓa jin su ba. Amma duk da haka, sun yi shiru don mutunta zaɓin uwar... ​Inna wacce ke zaune a gefe, ta kasa jurewa ta ce, “Ai na ɗauka sunan iyayenki da suka rasu za ki sanya musu! Me yasa kika manta da su?” ​Amal cikin ladabi ta ce, “A’a Inna, na tuna da su sosai.” ​Inna ta ce, “To kuwa sai ki sa Abdulsamaad da Khadija… ko kuma ki sa sunan Abbah Maleekh Abdul-Majeed da sunan mahaifiyarsa Maryama…” ​Abbah, yana murmushi, ya shiga tsakani da cewa, “A’a Umah, ki bari kawai. Sunan da tasa ya yi. Ai yanzu an daina yin masu suna domin zamani ya canza. Ki bar yaran su ci gaba da zamani.” ​Inna ta ɗaure fuska ta ce, “To ni ya za a yi da ni? Ni da ban iya faɗin sunayensu ba! Yanzu yaya zan ƙira su?” Islam tana dariya, ta ce: “Inna, zaki iya! Faɗi sunan yaron mu ji!” ​Inna ta motsa baki da ƙyar, ta dage kamar za ta iya furta shi yadda ya dace. Sai ta ce da tsananin murya: “A-ra-ha…” ​Duk suka kwashe da dariya! ​Suka ce, “To Inna, faɗi sunan yarinyar!” ​Nan ma Inna ta daure, ta ce “Haam-ma-ta!” ​Amal ta zaro ido, ta rufe baki, tana dariya: “Inna! Hammata kuma? Ni wallahi kar ki ɓata mun sunan yara!” ​Inna ta ce, “Dan kaniyarki! Haka na iya faɗi, kuma zan rinƙa faɗi! Daga yau haka sunayen suke!” ​Amal ta ce, “To tsaya! Ga inkiyar sunayen masu sauƙi ne. AR'HAAN inkiyarsa shine: ‘Ar’y’. Ita kuma LIHAAM inkiyarta shine: ‘Lii’y’.” ​Inna cikin murna ta ce, “Tooo! Gwanda inkiyar! Zan iya faɗi: Ari da Lili!” ​Amal ta dafe goshi, domin Inna tana shirin sa mata ciwon kai da waɗannan ƙagaggun sunayen nata... ​Abbah yana dariya cikin farin ciki ya ce, “To Daughter, ko za ki gaya mata ma’anar sunayen, da kuma dalilin da kika sanya musu? Wataƙila hakan zai sa ta gane su.” ​Amal ta yi murmushi, wanda ya nuna zurfin tunani da soyayya ta ce, “Shikenan Abbah, ni nasani.” ​Ta fara fayyace musu ma’anar sunayen da kuma dalilin da ya sa ta zaɓe su, tana kallo jariran nata ta ce, ​“Na sanya wa ɗana namiji sunan AR’HAAN saboda yana nufin ‘Jagora’ (The Ruler). Maleekh ya mutu ne domin ya ceci rayuwata, ya sadaukar da kansa don in rayu. Ya zama ‘Jagora’ a cikin wannan faɗan. Na sanya masa wannan sunan don ya tuna min cewa ɗansa dole ne ya zama jarumi kuma mai Gaba-gaba a rayuwarsa, kamar mahaifinsa. Zai zama Mai Jagorantar Rayuwarmu.” ​Ta ɗauki Lihaam, tana ci gaba da furta, ​“Ita kuma Lihaam, sunan yana nufin ‘Girmamawa’ da kuma ‘Tausayi’ (Respect and Compassion). Rayuwarmu ta kasance cikin wulakanci da ƙasƙanci a wajen mutanen dajin. Wannan yarinya za ta kawo mana ‘Girmamawa’ da ‘Tausayi’ a cikin iyalinmu. Kuma zan koyar da ita ta mutunta maza kamar yadda Maleekh ya mutunta rayuwata har ya ceci ni.” ​Kowa ya saurari bayanin Amal da tsananin tausayi da girmamawa. Sun fahimci cewa wannan ba wai zaɓin zamani ba ne kawai, wasiyyar Maleekh ce ta hanyar sunayen jariran.... NEXT NEXT NEXT Allah ya raya mana jikoki wato Ar'haan da Lihaam. 'Ar'y' and 'Lii’y' 🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 87 to 88 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Bayan sun shafe kwanaki a asibiti, Amal da jariranta masu kyau, Ar’haan da Lihaam, sun samu damar komawa gida. An yi musu cikakkiyar kulawa a asibitin. ​Komawarsu gida ya cika da faranta rai da mamaki. An yi wa gidan Abbah ado da balloons da kyaun launi don tarbarsu. ​Ammy da Inna ne suka jagoranci tarbar jariran. ​Inna har rige-rige take don ta ɗauki 'Ari' da 'Lili' (kamar yadda ta ke kiran su).. ​Islam da Arfat sun cika da murna, suna ta daukar hoto da kuma bidiyo na jariran. ​An zaunar da Amal a wani wuri na musamman a cikin babban falon gidan, inda take samun isasshen hutu da kulawa. Bayan mako guda. ​Nan take, aka fara shirye-shiryen hidimar suna. Abbah ya yanke shawarar cewa wannan hidimar za ta kasance babbar hidima don nuna godiya ga Allah. ​“Dole ne mu nuna wa duniya cewa ko da Maleekh ya ɓace, mutuncinsa da abin da ya bari suna da daraja. Wannan suna zai zama bikin Maleekh ne!” ​An ƙira manyan masu shirya biki anan Abuja. ​An tanadi abinci mai yawa na zamani da na gargajiya. An nemi shahararrun masu dafa abinci don su dafa. ​An gina tantuna a babban filin gidan, an yi musu ado da kayatattun kayan alatu da fitilu masu haske. ​ An aika da gayyata ga dukkan manyan abokan arziki, ’yan uwa, da kuma manyan jami’ai a Abuja. Wannan ya zama taron da kowa yake magana a kai. ​Amma a duk cikin farin cikin shirin suna, tambaya ɗaya ce ke ta yawo a zuciyar kowa: “Ina Maleekh?” ​Amal ta yi amfani da lokacinta wajen ba wa jariranta madara da kuma yi musu addu’a. Tana da yakinin cewa Maleekh yana raye, kuma ceton da ta samu ya zama tsanaki cewa Maleekh zai dawo.. ​Amal A Zuciyarta take faɗin, “Zan fara shirin nemanka Maleekh. Ba zan bari ɗana da ‘yata su taso ba tare da sanin Abbansu ba. Wannan bikin suna shine farkon neman dawo da kai.” An yi bikin sunan tagwaye Ar’haan da Lihaam a cikin tsari mai kayatarwa wanda ya dace da darajar iyalan gida. ​An shirya wajen taron da kyakkyawan ado, an kawo manyan makada don nishadantarwa, kuma manyan jama'a sun hallara don taya Abbah murna da kuma nuna girmamawa.. ​A cikin taron, Zayd ya hallara duk da cewa yana cikin fushi.. Hakan nan iyayensa sun hallara su ma. ​A wurin bikin, bayan an gama gabatar da jawabai da kuma kyaututtuka ga Amal da jarirai, an buɗe fili don kowa ya gabatar da murnarsa a gaban taro. ​Zayd ya miƙe. Kowa ya yi shiru, yana tsammanin ko zai faɗi wani abu na cin zarafi ko ɓata rai, kamar yadda ya saba yi wa Amal. ​Zayd ya nufo microphone cikin natsuwa da kwarjini. Ya fara magana da murya mai taushi da girmamawa: ​“Assalamu Alaikum. Ni ne Zayd, Ɗa ga wannan families mai albarka, kuma wanda ya kamata in auri Amal. Na zo nan ne don in nuna girmamawa ta ga Maleekh da kuma iyalai. Na yi farin ciki sosai da Allah Ya ceci Amal kuma Ya ba ta waɗannan kyawawan tagwaye, Ar’haan da Lihaam. A matsayina na dan uwa kuma aboki, ina taya ku murna.” ​Duk mutanen taron sun yi mamaki da wannan juyin magana da ya yi.. ​ Zayd ya juya kansa, ya kalli inda Islam take zaune kusa da Ammy. Ganin Islam ya ƙara masa ƙarfin hali. ​Ya cigaba da maganarsa kamar haka “A ƙarshe, ina so in yi amfani da wannan wuri mai albarka, a gaban duk ‘yan uwa da abokan arziki, don in furta wani abu da yake cikin zuciyata tun lokaci mai tsawo.” ​Ya ɗauki numfashi mai zurfi, ya kalli Abbah da Ammy cikin ladabi, sannan ya koma kan Islam. ​“Yanzu da na fahimci cewa soyayya ta gaskiya tana da wurinta a kaddara, kuma ba a takurawa zuciya... Ni, Zayd, ina son in nemi auren Islam, ‘yar ku mai biyayya. Islam, idan kin karbe ni, ina son ki zama abokiyar rayuwata.” ​Islam ta yi mamaki sosai har ta zaro ido. Ba ta taɓa tunanin cewa Zayd zai yi irin wannan abu ba, musamman a cikin bikin suna! Jikinta ya yi sanyi da zafi lokaci guda. Fuskar ta ta sauya launi saboda tsananin kunya da firgici. ​Abbah da Ammy suka kalli juna cike da mamaki, amma kuma farin ciki ya shige su. Wannan wata alama ce ta rufe shafin baƙin ciki da kuma buɗe sabon shafi na farin ciki a cikin ahali. ​Bayan Zayd ya furta soyayyarsa da kuma neman auren Islam a gaban taro, Islam ta kasa motsi saboda mamaki da tsananin kunya. Dukkannin mutane suna kallonta, suna jiran martaninta. ​Ammy da Abbah sun kalli juna. Abbah ya yi murmushi, wanda ke nuna yarda da kuma begen farin ciki. ​Abbah ya yi magana cikin fara'a ya ce, “Islam, ki duba cikin zuciyarki. Wannan shine kaddarar rayuwa. Ga Zayd ya zo neman ki. Shin kin amince da auren Zayd?” ​Islam ta miƙe a hankali, tana sunkuyar da kai, idanunta na cike da hawayen murna ta ce, “Abbah, na amince. Na karɓe shi.” ​Taro ya cika da ihun murna da godiya. An yi jinjina ga Zayd da Islam. Hakan ya rufe mummunan shafin da ya faru a baya, kuma ya kawo sabuwar yarjejeniya tsakanin iyalai... ​Yayin da taron ya kusa ƙarewa, kuma mutane suna cikin farin ciki da annashuwa, sai ga wani ɗan aike ya shigo da sauri. Ya riƙe wani ƙaramin abu (cassette/memory card), yana mai faɗin: “Ga saƙo da aka ce in isar. Saƙo ne na musamman ga dangin Alhaji Abdul-Majeed. An ce a saka shi a nan take.” ​Kowa ya yi mamaki. Sai wani ma'aikaci ya karɓi memory ɗin, ba tare da sanin bidiyon meye ba, ya soka shi a babban plasman da aka tanada a wurin taron. ​Zayd ne ya zaro ido a ruɗe domin yasan ba alkhairi bane, da sauri ya kalli yanda iyayensa suke. Ganin Alhaji Wadata yanda yake wani irin shu'umin murmushi yasa ya ƙara tabbatar da zarginsa.. Kafin ya ankara. ​Nan take, bidiyon ya fara nunawa: Falo ne mai duhu da aka ɗaure Alhaji Abdulsamaad (Mahaifin Amal) a kan kujera! ​Kowa a wurin taron ya yi shiru. Suka fara ganin wani tsohon bidiyo wanda ya nuna: ​Fuskar Alhaji Abdulsamaad cike da hawaye da firgici. ​Ya fara zayyana maganganu da aka tilasta masa faɗa, cewa: “Alhaji Abdul-Majeed (Abbah Maleekh) shine yake neman rayuwarsa. Kuma ya sa a kashe ni sannan ya kwashe dukiyar da na mallaka….” ​An nuna takardun kuɗi da dukiya da aka karɓe daga hannunsa. ​Bidiyon ya nuna an kashe Hajiya Khadija (Mahaifiyar Amal) wacce ke kwance sumammiya.. ​Bidiyon ya yi showing na ɗan lokaci, sannan ya tsaya. ​Girgiza da tsananin firgici sun mamaye wurin taron. ​Abbah ya miƙe daga kan kujera! Idanunsa sun firfito. Ya kasa magana. ​Ammy da Islam da Arfat sun fashe da kuka mai tsanani. Sun kasa yarda da abin da suka gani. ​Amal ta kalli bidiyon cike da tashin hankali da kuma mamaki! Ta gane mahaifinta! Yanzu ta gane waye sanadin iyayenta! Ta kalli Abbah cikin tsananin mamaki da tunanin cin amana! ​A zuciyarta ta ce, “Shi ne! Abbah ne ya kashe Abbana! Shi ne ya karɓe mana dukiyar mu! Mahaifin Maleekh shine makiyinmu?! Kenam shima Maleekh yasan haka?..” ​Farin cikin bikin suna ya koma gidan alhini da gidan ruɗani a take.. Inna hawaye take tana girgiza kai gaba ɗaya bakinta ya rufe, ta kasa furta komai. Bayan da bidiyon ya tsaya, kuma sirrin mutuwar iyayen Amal ya bayyana a gaban kowa, wurin taron ya zama gidan alhini da rushewa. Mutane sun fara guduwa cikin firgici da mamaki.. ​Amal, wacce ta ga Abbah Maleekh a matsayin makiyi kuma mai cin amanar iyayenta a cikin wannan gajeriyar bidiyo da aka gani, ta kasa jurewa. Damuwar haihuwa, rashin Maleekh, da kuma mummunan cin amana da ta ji daga Abbah, duk sun haɗu. A nan take, ta suma a wurin. Ta faɗi ƙasa tare da kyawawan tagwayenta da ba su san komai ba. Cikin hanzari aka karɓe yaran. ​Abbah, wanda ya kasance mai tsananin gaskiya kuma abokin rayuwar marigayi Abdulsamaad, ya kasa jurewa wannan ƙarya da sharrin da aka jingina masa. Ya fahimci cewa akwai makirci a cikin wannan lamarin. ​Nan take, ya fara tari mai zafi da tsanani, yana riƙe da ƙirjinsa. Yana aman jini a wurin taron. Heart Attack ne yake shirin kama shi, sakamakon tsananin firgici da rashin adalci da aka nuna masa a gaban dukkan mutanen da suke girmama shi. ​Ammy da Islam da Arfat sun shiga gigicewa, gawarwaki biyu a lokaci guda! Sun fara kuka suna ƙoƙarin kula da Abbah wanda yake cikin tsanani. ​Nan take, bidiyon ya fara karade ko ina a kafafen sada zumunta na zamani. Domin an yi live ɗin taron a lokacin, mutane da yawa sun yi recording ɗin bidiyon. ​Labarin ya yadu kamar wutar daji. Mutane sun fara zargin Abbah da cin amanar abokinsa, kisan kai, da kuma kwaɗayin dukiya. ​ An yarda cewa bidiyon gaskiya ne, amma abinda Alhaji Abdulsamaad ya faɗa ya yi wa Alhaji Abdul-Majeed sharrin da bai cancanta ba... Wasu kuma suna cewa yayi video ne a lokacin da ake shirin kai masa farmaki, yasan cewa za'a kashe shi shiyasa ya yi video don abi masa hakki bayan video ya fito. Kuma wanda ya kashe shi shine babban amininsa.. ​Jami'an tsaro sun shiga cikin ruɗani. Sun fara neman bayani kan sirrin mutuwar iyayen Amal wanda aka rufe tun shekaru da yawa. ​An garzaya da Amal da Abbah zuwa Asibitin da aka haifi tagwaye a ciki. ​Amal an shigar da ita ɗakin kulawa ta musamman don ta farfaɗo daga sumewarta. ​Abbah an shigar da shi Sashen Kula da Ciwon Zuciya (Cardiac Care Unit). ​A lokacin da labarin cin amanar da aka jingina wa Abbah ke girgiza Abuja, a sansanin Sojoji kuwa, Maleekh ('Lion') ya sake shiga cikin wani hali mai ban mamaki. ​Sanyin da ya ji a jikinsa lokacin da aka haifi yaran ya canza ya zama tashin hankali da zafin rai mara misaltuwa. ​A lokacin da labarin ya fara yaduwa a gidajen rediyo har ya kai sansanin Sojoji, wani Soja ya ji labarin. ​wani soja a cikinsu ya ce, “Kun ji labari kuwa? Wani babban mai kuɗi a Abuja, Alhaji Abdul-Majeed, wai shi ne ya kashe abokinsa don ya kwace dukiyarsa! Yau an yi masa bidiyo a wurin hidima! Labarin nan ya yi zafi!” ​Maleekh ya ji sunan 'Abdul-Majeed'. Wata igiyar wuta ta shige shi a kwakwalwa. Numfashinsa ya fara sarƙewa. Wani tsanannen zafi ya kama kansa, kamar an ciro wani dutse daga cikin ƙwaƙwalwarsa... ​Maleekh A Zuciyarsa yake faɗin “Maleekh… Abdul-Majeed… Maleekh… na taɓa jin wannan sunan. Amma na manta a yanda naji!…” Da haka suka gama shan hirarsu.. Acan bangaren kuwa.. Amal tana kwance abu na farko da ta tuna shine bidiyon tsohon kisan gilla da kuma karyar cin amanar da aka jingina wa Abbah.. Ta fara kuka mai tsanani a kan gadon asibiti.. “Mahaifin Maleekh! Ka cuce ni! Ka kashe Abbana! Ka kashe Mamana! Me yasa! Ni kuma da na zauna a gidanka, na girmama ka! Ashe dukkan ku makiyanmu ne! Ya Maleekh! Ashe ka san komai!, kasan muguntar Abbanka?!…” ​Zuciyarta ta cika da ƙiyayya da baƙin ciki a kan Abbah, wanda a idonta ya zama ainihin azzalumi da ya yi wa iyayenta kisan gilla. ​Inna ce ke zaune kusa da gadonta, tana kuka a hankali, tana riƙe da hannunta. Tagwaye kuwa suna cikin wani ɗakin kulawa na asibitin. ​Inna cikin kuka ta ce, “Sannu Amatu. Allah ya kawo sauƙi. Ki kwantar da hankalinki. Ki yi ƙarfin hali saboda ‘ya’yanki.” ​Amal ta fizge hannunta da ƙarfi tare da faɗin “Inna! Kin ga bidiyon nan? Kin gani da idanunmu! Sune suka kashe Abbana! Mahaifin Maleekh shine! Ba wai gobara ba ce! Abbah! Macuci ne! Inna, mu gudu! Mu bar nan garin da asibitin nan! Dukkan su makiyanmu ne!” ​Inna ta dafe ƙirjinta ta ce “Subhanal Lahi! Amatu! Kaddara ce! Amma ba haka bane! Ba Abbanku bane, Wannan shiri ne na Alhaji Wadata! Tunda har Zayd ya zo neman auren Islam, ya kasa cin nasara a rayuwarki, yanzu yana son ya lalata mana rayuwa!” ​Amal tana girgiza kai ta ce, “Inna, ki yi shiru! Ba Wadata bane! Amma Abbana ya faɗi da bakinsa cewa Abbah Maleekh ne! Dukkan su macuta ne! Mu gudu, Inna! Kafin su kashe mu kamar yadda suka kashe Iyayena!” ​Amal ta kasa yarda da kowa... ​An sanya tsauraran matakai a wajen ɗakin Abbah, saboda jami'an tsaro suna so su kare shi daga jama'a masu fushi da kuma sababbin matakai na neman kamawa daga wasu jami'ai. ​Amal ta tattara ƙarfin hali ta fito daga ɗakinta, ta nufo ɗakin Abbah duk da tsauraran matakan tsaro. Tana son ta fuskance shi kafin jami’an su cika buri na makiyansa su kama shi. ​A bakin ɗakin, ta tarar da Ammy tana kuka mai zafi tana magana da likita.. ​Amal ta matsa kusa da Ammy, tana kallonta da tsaurin fuska ta ce, “Ina Abban Maleekh? Ina mijinki? Ina macuci?” ​Ammy ta ɗago kai, ta kalli Amal, cike da damuwa da tausayi ta ce, “Amal… ba haka bane! Mijina mutumin kirki ne! Wannan sharri ne! Ya shiga cikin haɗari … ba zai iya magana ba! Ciwon zuciya ya kama shi!” ​Amal ta ce, “Shi ne! Allah ya saka masa! Ya kashe Abbana, yanzu shine yake so ya mutu kenam?! Amma ba zai mutu ba har sai ya gaya mun dalilin da yasa ya ci amanar babban abokinsa!...” ​Amal, ta yi ƙoƙarin kutsa kai don ta ga Abbah wanda yake kwance a kayan aiki na numfashi. Jami'an tsaro suka hanata shiga. ​Amal ta fahimci cewa zama a wannan garin haɗari ne. ​Ta koma ɗakinta da zuciya mai cike da kishi da kuma azama.. ​Amal ta kalli Inna cikin kuka ta ce, “Inna! Mu gudu! Mu ɗauki jariran nan! Zan koma rugan Fulani! A can kawai na san ina da kariya! Bayan haka, zan fara neman Maleekh da kaina! Shi kaɗai ne zai gane min wa ye ainihin azzalumi a cikin wannan labarin tsakaninsa da mahaifinsa!”.. ​Ta fara shiri na gaggawa don guduwa da tagwayenta: Ar'haan da Lihaam, ba tare da sanin halin da zata shiga ba. Yayin da Amal ke shirin guduwa ta bar asibiti tare da jariranta, Inna tana kuwa tana kokarin hanata tafiya. ​Inna ta riƙe hannun Amal da ƙarfi tana faɗin “Amatu! Na san me nake yi! Ni na gudu da ke daga Kaduna saboda na san su waye ainihin masu kisan gilla! Ba mahaifin Maleekh bane! Wallahi Alhaji Wadata ne! Shi da Alhaji Gusau!” ​Amal ta fizge hannunta, fuskarta cike da fushi ta ce, “Inna! Ki daina faɗin haka! Abbana ya faɗa da bakinsa! Ba zan saurari karya ba! Shi ne ainihin azzalumi da ya ci amanar abokinsa! Sai da ya kashe su sannan ya fake da fuskar tausayi! Shi ma Maleekh saboda ɗan ahalinsu ne, shiyasa bai gaya mun gaskiya ba!”. ​Amal ta ƙi yarda da Inna, saboda karyar bidiyo ta yi mata gagarumar tasiri a zuciyarta. ​A can wani gefen kuma, Zayd yasan kullin makirci ne na mahaifinsa da Alhaji Gusau. Ya yanke shawarar tunkarar mahaifinsa duk da tsananin tsoro.. ​Zayd yana magana da ƙarfi, cike da hawaye ya ce, “Daddy! Me yasa! Me yasa kuka yi irin wannan muguntar? Ya isa haka! Zan fita fili in faɗi gaskiya, cewa ku kuka kashe iyayen Amal, ba Abbah Maleekh ba!” ​Alhaji Wadata ya ɗauke Zayd da mari, yana huci ya ce, “Rufe mana baki! Wannan sirri ne na rayuwarka! Idan ka kuskura ka fita da wannan gaskiya, zan sa a kashe ka, kuma za a kashe wanda ka sanya a cikin zuciyarka! Ka manta da hakan!” ​Hajiya Sa’adatu itama ta daka masa tsawa da cewa, “Indai ka fitar da gaskiya, to wallahi tallahi saina tsine maka duniya da lahira! Ka zaɓi farin ciki na gidan nan, ko kuma faɗawa cikin wuta!” ​Zayd ya kasa magana, ya kasa jurewa barazanar iyayensa da kuma tsinewa. Ya yi shiru da batun, amma fushin adalci ya cika zuciyarsa... Hospital. ​Amal ta samu nasarar kutsa kai cikin ɗakin da Abbah yake kwance. An cire wasu na'urorin lura don kula da shi sosai. ​Abbah yana kwance, sanye da Oxygen, idanunsa a rufe. Doctor ya sanar da ya yi paralysis, bai iya motsi ko magana ba. ​Amal ta tsaya kusa da gadonsa, hawaye na zuba a fuskarta, cike da fushi da ƙiyayya. Muryarta na rawa take faɗin “Ka ji daɗi! Ka ji daɗi da abin da ka aikata a rayuwa! Ka kashe Abbana! Ka ci amanar abokinka! Yanzu kuma kunama ta cije ka!…” “Ka kashe su da wuta, yanzu kuma Allah ya ɗaure ka! Ka ga yadda ake yi wa mutum mummunan azaba? Ina Mallam Maleekh yake? Ko da yake, shima yana sane da cin amanar nan!…” “Zan yi amfani da wannan jini da ka bari a jikina (tagwaye) in nuna wa duniya cewa kai azalumi ne kuma macuci! Ba zan taɓa yarda cewa Maleekh mutumin kirki bane, tunda kai ne Abbansa!” Islam da Arfat sun shigo ɗakin a lokacin. Suka ji tsatsar maganganun Amal a kan mahaifinsu wanda ke kwance a kayan aiki na numfashi. ​Islam cike da fushi ta ce, “Ke! Ki daina! Ki rufe mana baki! Ba za ki zo ki ciwa mahaifinmu mutunci ba, alhali yana kwance! Wannan sharri ne!…” ​Arfat ta matso gaban Amal, fuskarta cike da hawaye da fushi ta ce, “Ki fita daga nan! kuma ki fice daga rayuwarmu! Ƙarya kike yi! Ba zaki zarge mu da kisan kai ba!…” Amal ta ce, "meye a cikin rayuwar takun banda sharri..." Islam ta ce, "Duk da sharrin da muke da shi bai hanaki haɗa jini damu ba ai.." Arfat ta ce, "ha haka kika nace mana, muna korarki kamar wata kariya amma kina ƙara tuso kanki kamar wata mayya, sai dai kika samu gurbi a cikin ahalin da kike raina wa.." Amal ta daka tsawa tana faɗin "Ku dallah ku rufe mun baki, a wata rayuwar takun masu amfani da jinin al'umma..." Islam ta ce, "a haka kuma mun rufa miki asiri, ƴar bola kawai..." Amal cikin fusata ta zabga mata mari tare da faɗin "ni ƴar bola ce amma ai da dukiyar mahaifina kuke amfanu wa..." Nan ​suka fara dambe, suna shirin faɗa a cikin ɗakin. Sai Ammy ta shigo da gudu, ta raba su cikin kuka. ​tana raba su, muryarta a raunane, “Ku dakata! Ku dakata! Ya isa! Ku bar ta ta tafi!…” ​Amal ta fita daga ɗakin tana faɗin maganganu, da cewa “Babu ni, ba kuma iyalan ku! Kuma jarirai na, Ar’haan da Lihaam, ba za su taɓa shiga cikin ahalinku ba! Na rantse da Allah! Ban ƙaunar Maleekh tunda shima ɗan ahalinku ne! Zan bar garin nan!” ​A wannan ranar, an sallami Amal da tagwayenta. Sai da Inna ta mari Amal a gaban mota jin abin da ta aikata, maganganun rashin da'a da ta riƙa faɗa. Haka suka koma can gidansu rai a ɓace... ​Abban Maleekh kuwa har yanzu jikinsa ba sauƙi. ​Wannan bidiyon da aka baza ya yi mummunan tasiri a Kotu. Kotun ta fara neman Abbah (wanda yake paralysis) domin za a kama shi don amsa tambayoyi kan kisan abokinsa. Amma sakamakon halin da yake ciki yanzu za'a bar shi ya ɗan samu sauƙi tukun. ☆☆☆☆☆☆ Cikin daren wata rana, ƙungiyar Boko Haram sun afka musu sansanin cikin bazata. Nan da nan, yaƙi mai zafi ya kaure. Sojojin, tare da jarumta da tsari, sun yi martani mai tsauri. ​Maleekh ('Lion') ya kasance a sahun gaba na yaƙin. Yana jagorantar Sojojin, yana amfani da dabaru na musamman (tactics) da ya koya. Duk da mantuwarsa, basirarsa ta yaƙi ta bayyana. ​An yi ruwan harsasai da kukan bindigogi a ko'ina. An kashe Sojoji da yawa a cikin wannan yaƙin na tsawon lokaci. ​Yayin da Maleekh ke tsaka da faɗa da wasu 'yan Boko Haram, wani ɗan Boko Haram wanda ke ɓoye a baya ya samu damar buga masa ƙarfe mai tsauri (metal bar) a kan sa cikin ƙarfin tsiya. ​Maleekh ya ji wani mugun zafi wanda ya fi zafin yaƙin da yake yi. ​Ya fara jin 'Zuuuuuuu' a kunnensa, kuma duniya ta fara juyawa masa. Yana ganin dishi-dishi a idanunsa. Wani abu kamar haske ya shige shi.. ​Cikin ƙiftawar ido, ya faɗi sumamme a tsakiyar filin yaƙin. Wannan buguwar ƙarfe ta biyu a kan kansa (bayan faɗuwar rami) ita ce makullin tunawa da kwakwalwarsa ke buƙata. ​Bayan an yi yaƙi mai tsawo kuma an yi wa ƴan Boko Haram galaba, abu ya lafa. Sojojin sun ragu sosai, wasu sun mutu, amma sun kashe ƴan Boko Haram da yawa. ​Sojojin da suka rage suka fara neman waɗanda suka ji rauni. Sun samu Maleekh a kwance sumamme, wanda ya yi kama da ya mutu. Sun ɗauke shi, suka kai shi wurin jinya na sansanin. ​Washegari da asuba, kafin hasken rana ya fito sosai, Maleekh ya farfaɗo. ​Ya buɗe idanunsa, a lokacin ya yi tsammanin ganin Amal a gefensa. Ya tuna tafiyarsu ta daji, guduwarsu, da kuma wurin da ya faɗi. ​Maleekh cikin raunannen murya, ya ce “Amal!… Ina Amal!?” ​Ya farka da sunan Amal a bakinsa! ​Ya tuna sunansa (Maleekh), ya tuna Abbah, ya tuna Ammy, ya tuna dukkan rayuwarsa kafin ya shiga rami. Buguwar ƙarfen ta dawo masa da kwakwalwarsa! ​Maleekh ya miƙe da sauri duk da raunin da ke kan sa. Ya duba hannayensa da jikinsa yana faɗin “Ni ne Maleekh!… Maleekh Abdul-Majeed! Ina sansanin Sojoji ne? Me nake yi a nan? Na tuna! Na tuna komai!” ​Sojojin da suka ga Lion ya dawo, kuma yana ƙiran wani suna Amal, sun yi mamaki sosai. Sun san cewa Lion ya sake samun kwakwalwarsa. ​Maleekh ya fara tambayoyi nan take game da Abuja, iyayensa, da kuma Amal. Wannan tunawar ta Maleekh ta faru ne a daidai lokacin da ake zargin mahaifinsa da kisan kai, kuma Amal ta yi tsammanin cin amana daga dukkan su... _NEXT NEXT NEXT_ asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 89 to 90 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Bayan kwana biyu da farfaɗowar Maleekh, an kammala shirye-shiryen dawowarsa hayyacinsa. Sojoji biyu sun rakoshi har zuwa bakin babbar hanya, suka tabbatar da ya shiga motar haya lafiya zuwa Abuja. Suka biya masa kuɗin mota kuma suka yi masa bankwana cike da kewa saboda 'Lion' ya bar su. ​A cikin Abuja kuwa, Amal ta ƙuduri aniyar barin garin. Tana ganin Abban Maleekh a matsayin maƙiyi, kuma Inna ta ƙi yarda da bin ta saboda tana da yakinin gaskiya.. ​Inna tana hawaye ta ce, “Amatu! Ba zan iya bin ki ba! Ba za ki gudu daga gaskiya ba! Ki yi wa rayuwarki adalci!” ​Amal sam taƙi yarda da abin da Inna take faɗi, ta bar Inna cike da fushi, ta ɗauki tagwayenta da kayansu. Ta shiga Napep don zuwa bakin babbar hanya inda za ta samu motar haya zuwa Kaduna.. ​A bakin babbar hanyar Abuja, aka sauƙe Amal. Ta fitar da keken jariran (Baby Stroller) mai ƙarfi, wanda ke da wurin kwanciya na jarirai biyu (tagwaye). Ta kwantar da Ar’haan da Li’y a ciki, ta sa musu bulun botul (Pacifiers) a bakinsu, suna tsotsa cikin nutsuwa. ​Ta juya baya don ba wa mai Napep kuɗinsa. ​Ikon Allah! Wani iska mai ƙarfi ne ya zo, tyres na keken jariran suka goce ba tare da an lura da hakan ba. Keken ya fara tafiya da kansa a kan gangaren hanya, yana gudu a hankali. ​Amal tana riga-runguma da mai Napep a kan canjin kuɗi (change), ba ta san haɗarin da ke zuwa ba.. ​Juyowar da Amal za ta yi, sai ta ga babu yara! Babu kekensu! A ruɗe ta fara waiwayawa. ​Can ta hango keken jariran yana gudu, yana tunkarar babban titi mai cike da motoci masu gudu! ​Amal ta jefar da jakarta da ke hannunta, ta fara gudu da tsananin ihu don taro su. ​Cikin ihu take faɗin, “Yarana! Ku taimake ni! Motoci! Ku tsaya!…” ​Gudu take, amma mutane a gefen titi babu wanda ya yi tunanin taimako. Sai dai tsayawa suna ɗaukar bidiyo da kallo saboda sun ga abin mamaki. ​Keken jariran ya hau babban titi na Abuja, inda motoci ke gudu da tsananin gaske! ​Dai-dai lokacin da keken jariran ke shirin shiga tsakiyar motoci, sai ga wani zabgegen mutumi ya sha gabansu da tsananin gudu da ƙarfi. ​ Wanda ya sauƙo daga motar haya 'yan mintoci kaɗan da suka wuce, ya tsallake hanya zuwa bakin titi! Ya ga haɗarin da ke zuwa, kuma ya yi amfani da karfinsa don ceton tagwayen.. ​Ya riƙe keken da ƙarfi, ya hana shi shiga cikin motoci! ​Amal ta iso wurin tana haki da kuka. Ta rufu kan jariranta, tana rungume su cike da godiya ga Allah. ​A fusace cikin tsananin zafin nama da fushi a kan rashin kulawarta da ya jefa yaran cikin haɗari: ​Ya ce, “Me kike yi! Me yasa zaki bar yara haka! Baki da hankali!….” ​Ya riƙe damtsenta da ƙarfi, ya ɗagota sama, ya kai hannunsa zai mare ta saboda tsananin fushi… ​Sai kawai idonsa ya sauƙa akan fuskarta! ​Maleekh ya daskarar da hannunsa a sama! Ya kasa motsi.! ​ “Amal!… Amal!…” ​Ita kuwa Amal ta rufe ido sosai tana ƙoƙarin kare fuskarta daga marin. Can da ta ji shiru, sai ta buɗe idonta a hankali… ​Itama idonta ya sauƙa a kan fuskar Maleekh! ​Ta ruɗe, ta zazzaro ido, baki a sake, tana kallonsa da mamaki! Maleekh ne! Cikin tsari da tsananin kyau! Amal da Maleekh sun tsaya, ido cikin ido, a kan titin Abuja. Firgici da mamaki sun cika fuskokinsu. Maleekh a matsayin Jarumi mai Rauni da Tunani ya dawo masa. ​Amal muryarta na rawa, kamar ta ga fatalwa ta ce, “Maleekh! Maleekh ne!…” ​Maleekh ya jefa hannunsa da ya daskare a sama, ya shafa kansa. Cikin murya mai rauni ya ce, “Amal! Ni ne Maleekh! Ta ya kika tsira?! Nasan daman dole zaki tsira domin fatana kenam! Me kike yi anan? Kuma me kike yi da waɗannan yaran?!” ​Amal ta fara kuka da tsananin zafi saboda ta tuna zargin bidiyon “Abin da nake so na sanar da kai shine, na ƙi ka yanzu! Ka rabu da ni! Ban san yaya ka tsira ba! Amma me ya kawo ka nan! Ka zo ka kashe ni ne? Saboda kaji labarin asirinku ya tonu shine zaka bayyana? Ka ga cewa ka yi nasarar cin amana!”.. ​Maleekh ya ƙara fusata. Bai fahimci ma’anar cin amana da take faɗa ba. Sam bai fahimci abin da take nufi ba. “Cin amana kuma! Waɗannan yaran fa? Me ya haɗa ki da su! Me yasa zaki jefa su cikin haɗari! Wane ne ubansu!?” ​Amal ta rungume jariranta da ƙarfi, tana kare su da jikinta. “Maza bar nan! Ba ruwanka! Su ba naka bane! Su ba ‘yan ahalinku bane! Abun takaici ne kawai kuka zo ku cece su daga haɗari! Ka rabu da ni!” ​Maleekh ya dube ta da mamaki na ƙiyayya da take nuna masa, sannan ya kalli jariran da ke cikin stroller. Sai ya fara jin wani bugu a zuciyarsa wanda ya fi zafin yaƙin da aka yi masa. “Shin kin haukace ne? Kodai baki yi farin cikin ganina bane?..yanzun ina kike shirin zuwa? Waima yaran waye waɗannan?..." ​Wani mai wucewa wanda ya lura da rikicin su, ya gane Maleekh wanda labarinsa ya yadu. Ya matso kusa da su. ​Mai Wucewa ya kalli Maleekh sannan ya ce, “Kai ne Maleekh? Kai ne ɗan Alhaji Abdul-Majeed? Labarinku ne ya cika garin nan! Ana zargin Mahaifinka da kisan abokinsa! Yanzu Kotu tana nemansa a yayinda yake kwance a gadon asibiti..!” ​Maleekh ya daskare a wurin! Kisan kai? Abbana? Wani zafi ya ƙara kama kansa.. ​Cikin rashin fahimta ya ce, “Zargin me? Wane Abbana? Kotu kuma? Wace irin magana ce wannan!” ​Mai Wucewa ya ce. “Bidiyo ya nuna hakan! An nuna mahaifin yarinyar nan (Amal) yana jawabin cewa Abbanku yana ƙoƙarin kashe shi don ya ci dukiyarsa! Shi yasa yarinyar nan take shirin guduwa! Tana tsoron kar a kashe ta!” ​Maleekh ya juya, ya kalli Amal, cike da tashin hankali da kuma zargin cewa ta yarda da wannan ƙaryar har tana nuna masa ƙiyayya.. ​Maleekh ya riƙe kansa, wanda yana ɗan jin zafin raunin da ya ji. “Wannan ƙarya ne! Zargin sharrin Abbana! Amma ke… Amal! Ke ma kin yarda da wannan sharri har kike cewa kin ƙi ni! Kin yarda Abbana makiyin ku ne!…” ​Amal ta gane cewa Maleekh gaskiya yake faɗa saboda tsananin raɗaɗin da yake ciki. Tunanin da ta yi na cewa Maleekh ya san komai ya zama ƙarya.. ​Maleekh ya kalli jariran da ke cikin keken, cike da tsananin tausayin kansa, ya durƙusa a gaban keken, ya kalli Ar’haan da Li’y. Wani abu ne ya cake shi a saitin zuciya. “Waɗannan … su wanene… sun yi kama da ni… suna da… wani annuri da na sani…” A lokacin ​Maleekh ya tuna da sadaukarwarsu a ruga. Ya tuna da kwana uku da aka ba su. Ya duba jariran da kyau. ​Ya jefa kansa sama, ya kalli Amal da idanu waɗanda suke rufe da hawaye. “A-mal! Waɗannan… ba yaranmu bane! Su ne tagwayenmu! Sun zo ne! Sun zo?!…” Ya ɗauki Ar’haan da Lihaam a hannunsa, yana kuka da murna da azaba lokaci guda. ​ “Ba zaki gudu ba! Ba zan bari a kama Abbana ba! Ba zan bari a cutar da shi ba! Kin yi shari’a a kaina, kin yi a kan Abbana! Yanzu lokaci ne na wanke shi!…” Maleekh bai bai wa Amal damar musawa ba. Ya riƙe hannunta da ƙarfi, ya saka ta a Napep (Keke Napep), shima ya shiga tare da jariransa a hannunsa. Sun nufi gida.. ​Amal muryarta na rawa ta ce, “Ni ba zan je gidanku ba! Bazan sake shiga gidan maciya amana ba!…” ​Maleekh ya dube ta sannan ya ce, “Rufe mun baki! Ba mu da lokacin faɗa! Kaddara ta haɗa mu a nan! Zaki bi ni! Ba zan bari a cutar da Abbana ba!” ​Bayan an sauƙe su a gidan, kai tsaye ciki suka nufa.. Maleekh ne ya tura ƙofar falon, ya shiga da tagwayensa a hannunsa, da Amal a bayansa. ​A falon, Ammy tana asibiti jinyar Abbah. Sai Islam da Arfat ne ke zaune cikin tsananin baƙin ciki da kuma ruɗanin bidiyon. ​Kannen sun ɗaga kai, suka ga Maleekh! Sun ganshi tsaye kuma yana riƙe da tagwaye! ​Suka zama kamar sun ga fatalwa! ​Islam ce ta fara yin ihu ta miƙe tana faɗin. “Yaya Maleekh!…” ​Arfat ta miƙe itama, da muryar kuka “Yayana!…” ​Nan da nan, suka ru ga da gudu, suka rungume shi, suna kuka mai tsanani da godiya da murna. ​Maleekh yana riƙe da su, yana hawaye ya ce, “Na dawo! Kuna lafiya! Ina Ammy? Me ke faruwa?” ​Bayan sun saki Maleekh, sai suka ga Amal a bayansa. Farin cikin su ya koma kallo na fushi da baƙin ciki. ​Islam ta harari Amal, cikin tsanaki ta ce. “Me kike yi a nan! Bayan kin zagi Abbanmu! Ba kya jin kunya!…” ​Arfat itama ta ce, “Ki fita daga nan! Yaya Maleekh, me ya kawo ta nan! Wannan macuciya ce! Ta yarda da ƙaryar bidiyon nan!…” ​Maleekh ya ɗaga musu hannu yana faɗin, “Shiru! Ku dakata! Ba mu da lokacin faɗa! An gama zargin sa! Yanzu za mu gano gaskiya! Ina bidiyon!?” ​Maleekh ya ajiye tagwayensa a hannun Islam da Arfat (wanda hakan ya rage musu fushi). Ya buƙaci su bashi memory ɗin da bidiyon ke ciki. ​Islam ta ba shi memory ɗin. Ya saka shi a babban Plasman falonsu. Sun kunna bidiyon, Maleekh ya zura ido sosai yana nazari (analysis) na bidiyon. ​Amal ma ta matso, tana kallo saboda tsananin sha’awa na yadda Daddynta ke jawabi, tayi kewar fuskarsa sosai. Ya zauna a gaban Plasman sosai don nazarin bidiyon da ake zargin mahaifinsa da kisan kai. Amal ta tsaya a gefe, tana kuka da hararar Maleekh, ​Maleekh ya kalli video tas. Ya kalli Abbah Abdulsamaad (Mahaifin Amal) yadda yake magana da murya mai rauni. Duk da cewa bidiyon yana zargin mahaifinsa, Maleekh ya lura da wasu abubuwan mamaki waɗanda ba kowa ya lura da su ba. ​Abubuwan da Maleekh Ya Lura da su: A lokacin da mahaifin Amal ke jawabi, Maleekh ya lura da yadda hannun Abbanta yake kaɗa yatsunsa a ɓoye. ​Yana ɗan girgiza kai, yana ƙibkibta idanu a wani yanayi na musamman. ​Maleekh ya fahimci cewa wannan alamar sirri ce, wanda ke nuna cewa akwai lauje cikin naɗi kuma an tilasta wa Abban Amal jawabin. ​Bayan ya gama kallo, ya zare memory ɗin, ya miƙe jiki a sanyaye.. ​Amal ta kasa jurewa, tayi masa tambaya mai zafi, tana harararsa. “To! Shin wata shaida ka samu? Kana so ka kare mahaifinka ne? To mahaifinka shine mutumin da ya kashe mun mahaifi!…” ​Maleekh ya tsaya cak! Wani mugun zafi ya kama shi a zuciyarsa saboda rashin yarda da zargin da take yi masa. Fushin da ya ji ya sa shi manta da rauninsa gaba ɗaya. ​A fusace ya darara mata tsawa mai ƙarfi, ya ɗaga mata hannu da cewa, “Enough, you stupid girl!” ​Zuciyarsa ce take raɗaɗi kamar wuta. Nan da nan idanunsa sukayi jawur, yana kallon cikin kwayar idanunta kai tsaye! ​ “Ke, abun farin ciki ne a kama mahaifina da zargin kisa? Me yasa zai kashe babban abokinsa wanda yake alhinin rashinsa har yanzu? Shin meyasa zai ɗauke ki tamkar ɗiyarsa alhalin shi ya kashe mahaifinki? Kin taɓa samun farmaki ko hantara a wurinsa? Kin taɓa ganin wani sauyin fuska a tattare da shi?…” ​Amal ta yi shiru, ta kasa bashi amsa. Ta tuna da tausayi da girmamawar da Abbah Maleekh ya nuna mata. ​Maleekh ya harzuka da rashin amsarta da kuma zarginta na ƙarya. Ya daka mata tsawa da murya mai ƙarfi: “Answer me!” ​Amal ta tsorata da tsawar, ta fara hawaye ba zato ba tsammani. ​Maleekh ya fahimci cewa magana ba zai kai su ko'ina ba. Abbansa yana buƙatar ceto nan take. ​A fusace, ya yi wa su Islam hannu, ya tattara jariransa. ​ “Islam, Arfat! Ku biyo ni! Za mu nufi asibiti! Za mu ga Abbah! Kuma za mu gano gaskiya!…” ​Islam ta rungume Ar’y (Ar’haan), Arfat kuma ta riƙe Lihaam. Haka suka fita da gaggawa, suka bar Amal ita kaɗai a tsaye a cikin falon, zuciyarta cike da ruɗani da kuma nadamar zargin da ta yi. Yayin da Maleekh da ƙannensa ke kan hanyarsu ta zuwa asibiti, Amal ta tsaya a falo, hankalinta a ruɗe. Ta kasa yarda cewa Maleekh ya dawo, kuma ta yi masa mugun zargi. ​Amal ta ɗauki memory ɗin da suka manta akan TV stand, ta saka a Plasman nan take. Ta fara kallon bidiyon cike da damuwa da kuma ruɗani. Tana maimaita kallon akai-akai, tana neman alamar makirci da Maleekh ya faɗa, amma ta kasa samun hujja daban mai ƙarfi. ​Maleekh da ƙannensa suka isa asibiti. ​Ammy tana zaune a bakin ɗakin Abbah cikin tsananin damuwa da kuka. Ganin Maleekh a tsaye, cikakke kuma ba tare da rauni ba, ya zama kamar abin al'ajabi a gare ta. ​Ammy ta taso da gudu ta rufo shi, ta rungume shi tana kuka mai tsanani. ​Muryarta na rawa, cike da murna da zafi ta ce. “Maleekh! Kaine ka dawo gare ni?! Na gode Allah! Na gode Allah da Ya dawo da kai! Na yi tunanin na rasa kowa!…” ​Maleekh ya rungumeta da ƙarfi yana faɗin, “Mom! It’s okay! Na dawo! Kuma Abbah zai tashi da yardar Allah! Ba za mu bar shi ba!…” ​Ammy ta ɗago, ta ga Islam da Arfat riƙe da tagwaye! Cikin tsananin mamaki da rawar murya ta ce, “Yara na! Waɗannan kuma…? Ina uwar tasu?” ​Islam cikin jin haushin Amal ta ce, “Mun barta a gida. Ba za ta yarda ta zo ba.” ​Ammy ta yi shiru, ta fahimci cewa rikicin bidiyon ya raba kan Maleekh da Amal. ​Maleekh ya shiga ɗakin Abbah. Abbah yana kwance, ya ƙazantu da na'urorin jinya. An tabbatar da cewa zuciyarsa ta ɗan tsaya ne, kuma na'ura ce ke riƙe da numfashinsa. Likita ya sanar da su cewa zai ɗauki lokaci mai tsawo kafin ya farfaɗo. ​Maleekh ya zauna a gefen gadon, ya riƙe hannun Abbansa mai sanyi. Hawaye na zubo a idanunsa saboda rashin adalci da azabar da Abbansa ke fuskanta. ​Maleekh yana magana cikin raunanniyar zuciya. “Abbah! Ba zan taɓa yarda cewa kai ne ka aikata wannan ba! An yi maka sharri a ƙasar nan, kuma an yi maka sharri a cikin zuciyar masoyiyata! Amma na rantse da Allah, za mu wanke ka! Zan yi amfani da kowane irin ƙarfi da Allah ya ba ni don in fito da gaskiya! Ka sani cewa yaran nan suna nan! Ba zan bari kaddarar cin amana ta raba mu ba!” ​Maleekh ya sumbaci hannun Abbansa, ya ƙuduri aniyar fara yaƙi da makircin duk wanda ya aikata haka.. ​Bayan wasu awanni, Amal ta gaji da kallon bidiyo mara ƙarin bayani. Ta ƙuduri aniyar samo gaskiyar al’amarin da kanta. Haka ta koma gidanta tare da Inna. Bayan ta isa, ​Inna ko kallonta bata yi ba saboda fushin yadda Amal ta zargi Alhaji Abdul-Majeed da iyalansa.. ​Inna cikin sanyin murya ta ce, "Kin fasa tafiyar ne? Meyasa kika dawo? Ina jariran?” ​Amal cikin gajiyar zuciya ta ce, “Suna wurin Maleekh. Ya dawo...” ​Inna ta zabura! Farin ciki ya shige ta! Ta san cewa yanzu Allah ya ba ta damar yin amfani da shaidarta ta gaskiya ga mutumin da ya dace.. ​Inna ta zabura, ta yafa mayafinta ba tare da ko kallon Amal ba ta ce, “Maleekh ya dawo? Yana ina?!” ​Amal ta bata amsa a takaice “Yana asibiti wurin Abbansa.” ​Inna ta fita a guje! Ta ɗaura niyyar sanar da Maleekh gaskiyar al'amarin. Ta san cewa Amal tana da ƙaramar ƙwaƙwalwa kuma ba za ta fahimce ta ba. Yanzu Maleekh ne shugaban gida, kuma shi ne wanda zai iya fahimtar komai... _NEXT NEXT NEXT_ asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 91 to 92 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 A cikin Abuja, zanga-zangar ta yi ƙarfi saboda zargin Alhaji Abdul-Majeed da kisan kai. Hakan ya sa go-slow ya tsananta, kuma Inna ta makale a hanya. ​Amal kuwa ta damu matuƙa da jariranta da Maleekh ya riƙe, sannan ga Inna bata dawo ba. Tana ganin Maleekh ya ɗauke su don fansa saboda zargin da ta yi masa. ​Misalin ƙarfe 8 na dare, Amal ta nufi asibiti ganin bazata iya jure kwana ba tare da jariranta ba.. ​A daidai lokacin da ta isa, sai ga hargowa! Wuta ta kama a wani ɓangare na asibitin. Makiyan Abbah ne suka turo 'yan daba don su ƙona shi gaba ɗaya. ​Mutane suna ta fitowa da gudu daga cikin asibitin. Ammy tana tura gadon da Abbah yake kwance kai, tana fitowa da gudu. ​Wani ɗan daba ne ya fito da gudu da jarkar petur (gallon of petrol) a hannunsa. Ya wurgar da ita a gaban Amal da ke tsaye. ​Amal ta ɗauki jarkar tana dubawa! Zuciyarta tana bugawa da mamakin dalilin da yasa za a ƙona asibitin! ​Dai-dai lokacin da Amal ke tsaye riƙe da jarkar petur, Maleekh ya iso da gudun gaske a motarsa. ​Inna ma ta iso a lokaci guda da mai Napep bayan sun samu wurin wucewa. ​Amal kamar wacce aka daskarar da ita, tana tsaye riƙe da jarkar petur a hannunta, tana kallon wutar da ke ci. ​Nan take, kowa ya zagaye ta! ​Inna cike da mamaki da zargi ta furta “Amatu! Yanzu ƙiyayyar taki har takai ki ƙona asibitin kowa-da-kowa ya mutu? Har zaki zo ki kashe Alhaji Abdul-Majeed?…” ​Amal ta zaro ido tana kallonsu! Ta kasa cewa komai. Makirci ya karya ta lokaci guda.. ​Ammy tana kuka da mamaki ta ce, “Amal! Kin zo ki ƙona Abbanku? Saboda kina tunanin shi ya ƙona iyayenki? Wani irin zuciya ne da ke haka?…” ​Maleekh ya kasa magana! Zuciyarsa sai harbawa take da ƙarfi! Wani irin tsanar Amal ya shige shi! Ya tuna duk faɗan da suka yi, da yadda ta zargi Abbansa! Ya ɗauka ta shirya wannan ne don ramuwar gayya! ​Nan motar agaji na ruwa ta iso, aka fara kashe wutar. ​Maleekh ya tunkari Amal a fusace. Ya yi mata wani irin shaka mai ƙarfi, ya shake mata wuya sosai yana zaro manya idanunsa. ​“Macuciya! Kin zo ki kashe Abbana! Kin so ki hallaka iyalaina!…” ​Amal ta ɗage numfashinta! Da ƙyar take jan numfashi, tana riƙe da hannun Maleekh da yake sha'ke da wuyanta. ​Idanun Maleekh sukayi jawur saboda fushi da raɗaɗi. Motar ‘yan sanda (Police) ta iso nan take.. Daƙyar aka janye hannun Maleekh daga sha'kar da yayi mata, cikin fusata ya sake ta. Ya kalli ’yan sanda, ya yi umarni da ƙarfi cikin zafin rai. ​“Ita ta sa wutar! Tayi babban laifi! Don haka ina umartar ku da ku tafi da ita can Station! Zaman prison ya wajaba a kanta! Ku ɗauke ta!” ​Ammy cikin kuka ta ce, “Maleekh! Me kake shirin aikatawa!?” ​Maleekh ya ɗaga mata hannu, ya hana ta magana: “Mom! Abinda ya dace nayi! A tafi da ita!” ​Amal tana kuka, bakinta ya rufe, ta kasa cewa komai. Jami’an ‘yan sanda suka kama ta! ​Maleekh ya juya, ya kalli gadon da Abbah yake kwance ido a rufe. ​ “Ba shiri! Za mu canza masa asibiti! Ko ma ƙasar waje za a fita dashi! Gobe zan kai shi Hospital Ethiopia!” a cewar Maleekh. ​Ya yanke hukuncin kamawa da fitar da Abbansa daga ƙasar a cikin tsananin fushi da baƙin ciki, yana mai cewa Amal ce ta yi hakan. Ba tare da yayi bincike ba kawai hukunci ya yanke. ​Washegari da asuba, shirin Maleekh na fitar da Abbah zuwa Ethiopia ya fara. Ammy ta kasa yarda da yadda Maleekh ya yi wa Amal rashin adalci, har ya yanke mata hukunci ba tare da sauraro ba. ​Ammy cikin kuka da damuwa ta ce, “Maleekh! Zaka bar ƙasar kuma Amal tana can a tsare! Kuma ga jariranta ko wata basu yi ba da haihuwa! Ya zakayi kayi haka? Wannan ba dabi’a mai kyau bace!…” ​Maleekh ya dubi Ammy. Zuciyarsa ta cika da tunanin cin amana da kisan kai wanda ya danganta wa Amal. Cikin tsaurin fuska da yanke hukunci ya ce, “Ba daɗe wa zanyi ba a can. Idan na kaishi, akwai manyan kwararrun likitoci a can da zasu kula dashi. Kwana biyu kawai zanyi na dawo. Kafin na tafi zan aiko wa yaran da madara mai kyau na jarirai. Ita kuma zata cigaba da zama a can cell!” ​Ammy ta sake faɗin damuwarta game da tagwayen da suke buƙatar nono na uwa. ​“Amma ai uwarsu tana raye, kuma suna da nono! Sai a rinƙa basu madara? Sun yi ƙanƙanta sosai!…” ​Maleekh ya girgiza kai, ya ƙuduri aniyar yin abin da ya yi “Kawai ki bar komai a hannu na! Kar ki damu! Amal daga Cell sai Prison na mata! Yara kuma ba yau ake haifan jarirai kuma mahaifiyarsu ta mutu ba! Zan siya musu madara mai inganci wanda zasu cigaba da sha! Innarta kuma zata dawo nan gidan saboda ta samu masu kula da ita! Ni yanzu zamu nufi Airport!” ​Ba tare da ɓata lokaci ba, Maleekh ya ɗauki Abbah cikin tsari mai kyau zuwa Filin Jirgi. An fita da Abbah a na'urar tallafin numfashi (life support), aka shiga jirgi mai zaman kansa (private jet) zuwa Hospital Ethiopia don kulawa ta musamman. ​Maleekh ya aika musu da madarar yara (Infant Formula) masu inganci da yawa don ci gaba da ciyar da tagwayen. ​Bayan Maleekh ya tafi, Inna ta dawo gidansu Maleekh kamar yadda ya umarta. ​Ammy ta tarbe ta da hannu bibbiyu.. An bata ɗaki na musamman.. ​Inna (A Zuciyarta) tana maganar cewa “Alhaji Wadata! Na san ka! Na san sirrinka! Yanzu Maleekh ya dawo, zan bashi dukkan abin da na gani a daren nan! Ba zan bari ka kuma hallaka wannan yaro marar laifi (Maleekh) ba!” ​Inna yanzu tana zaune tare da tagwayen da kannen Maleekh, tana jiran dawowar Maleekh don ta bayyana gaskiya... 🪸🪸🪸 Amal tana Station, inda aka sanya ta a cikin Cell (kurkuku na ɗan lokaci). Washegari antashi da hukunta Amal. ​ƴar Sanda cikin tsaurin fuska da baƙin ciki take faɗin “Ke! Har kina da ƙarfin hali zuwa asibiti! Ki nemi kashe mutumin kirki wanda ya ɗauke ki tamkar ɗiya! Ba zaki ga daɗi ba a hannun mu!” ​An yi wa Amal dukan tsiya! An horar da ita sosai saboda zargin kisan kai da kuma ƙona asibiti. ​Amal tana cikin azaba.. ​Alhaji Wadata ya ji labarin ƙonewar asibiti da kuma kamawar Amal a matsayin wacce ta kawo wuta. Yayi farin ciki sosai. ​Yana faɗin cewa, “Wannan shine tsari mafi sauƙi! Yanzu za a zarge ta da kisan kai da ƙonawa! Makarinta ma ya gujeta! Sun sauƙake mun aiki!” ​Ya kuma ji labarin cewa Maleekh ya tafi Ethiopia da Abbah.. Alhaji Wadata ya lura da tausayin Zayd da kuma yunkurinsa na son tona gaskiya. Ba tare da bata lokaci ba, ya sanya aka ɗaure Zayd a wani ɗaki na sirri a gidansa. A ɗakin sirri yake kallo Zayd tare da faɗin. “Ba za ka taɓa tona min asiri ba! Kai ma za ka shiga azaba har sai na gama da Maleekh da iyalansa!” Shiri na gaba Alhaji Wadata ya nemi Malaminsa (bokaye) ya bashi Laya (sihiri) don rufe bakin dukkan shaidu waɗanda za su iya tona sirrinsa. ​Malami ya bashi laya mai tsanani.... A gidansu Maleekh kuwa, Inna tana zaune ita kaɗai a ɗaki tana tunanin yanda zata gaya wa Maleekh gaskiyar lamarin.. A Zuciyarta take faɗin, “Za ni gaya wa Maleekh… Wadata ne!…” Ta yi ƙoƙarin buɗe baki “Mmm… mmm…” Bakinta ya kasa motsi!.. Bayan kwana biyu da dawowar Maleekh daga Ethiopia, ya yi amfani da ƙarfin ikonsa da kuma tasirinsa a cikin siyasa don shure ƙarar da ake tuhumar Abbansa da kisan kai. An rufe komai. ​Bayan ya huta a gida ya rungumi jariransa (waɗanda ke sanya shi cikin nishaɗi), ya nufi Station don ganin Amal... Bayan ya isa. ​Maleekh ya tsaya a bakin Cell, tare da ƴan sanda biyu a gefensa. Yana ganin Amal a ɗaure, ga tabon dukan da aka mata a fuska da jiki.. ​Maleekh cikin sanyin murya a tsanake ya ce, “Kun yi mata rauni sosai, hakan kuskure ne saboda macece! Amma abinda ta shuka, shi take girbewa! Ku ɗaga mata ƙafa saboda uwar ƴaƴana ce!” ​ƴan Sanda suka ce “Okay Sir, za a kiyaye.” ​Maleekh ya tambayi ko ta ci abinci, kuma aka ce A’a. Ya umarce su da su bata abinci nan take. ​Islam da Arfat sun zo tare da shi, riƙe da tagwaye. Sun tsaya a nesa don Amal ta ga jariranta daga nesa ba tare da an bata su ba. ​Ƴar sanda ta shiga ta ajiye mata kular abinci a ƙasa. Abincin shine farar shinkafa da mai da dakakken yaji, sai tattasai da attaruhu a roba daban mai zafi sosai. ​Amal tana zaune, ta dubi abincin sosai. Ta ɗago tana kallon Maleekh da rinannun idanuwanta (cike da azaba da jarumta). ​Cikin rashin kula da abincin, Amal ta miƙa hannu, ta ɗauki dogon tattasai mai tsananin zafi, ta kai bakinta tana taunawa a hankali! Sannan ta ɗauki attaruhu (hot chili pepper) tana ci. ​Islam da Arfat sun zaro ido suna kallonta! Ƴan sanda sun shiga mamaki! Duk abincin da aka bata tun kwana bakwai bata ci, amma yanzu tana cin kayan miya masu tsananin zafi! ​Ko zafi bata ji! Haka take cinye su, idonta akan Maleekh! ​Maleekh ya fahimci cewa Amal tana aiko masa da saƙon cewa tana da ƙarfin hali da jarumta, ba za ta rushe ba! ​Maleekh Ya yi murmushi a hankali sannan ya furta, “Dakyau! Jaruma! Irin wannan jarumtar ai ko nima zan iya!…” ​Ya kalli ɗaya daga cikin ƴan sanda: ​“Ku miƙo mun tattasan da attaruhun nan! Nima na kwada jarumtar!” ​Aka miƙo masa tattasai da attaruhu a hannu. Yana kallon ƙwayar idanun Amal da sukayi jawur, ya sa attaruhu a bakinsa yana taunawa! ​Da hanzari ya tofar da na bakinsa! Ya fara shishshitu! ​Cikin ruɗewa da gigicewa yake faɗin “Ku ban ruwa! Ku ban ruwa! Kuyi sauri!…” ​Aka bashi bottle na ruwan sanyi. Ya kafa kansa ya fara gwangwada! Sai da ya ga bayan bottle ɗin, duk da haka bai daina shishshutun ba! Sai zaro harshe yake kamar tsohon maye! ​Arfat tana riƙe da Lihaam, sai kunshe dariya take tana kallon Maleekh! Islam kuwa ta ƙafe idonta akan Amal saboda mamaki da ƙarfin hali irin nata! ​Amal ko kibta ido bata yi. Ta cinye tattasai da attaruhun nan tasss! ​A hankali, cikin tsokana ta furta, “Akwai ƙari ne?…” ​Duk zaro ido suka yi suna kallonta! Ko irin shishshitun da Maleekh ya yi bata yi ba! ​Maleekh ya jijina kai cikin mamaki da girmamawa ga jarumtar Amal (amma ya ci gaba da nuna hukunci a zahiri). ​Ya miƙa wa ƴan sanda takardar Kotu na tura Amal zuwa Prison (gidan yari) na mata, inda zata cigaba da zama acan. ​Daga nan, suka juya suka tafi, suka bar Amal a Cell... Bayan Maleekh ya dawo, ya yi amfani da ƙarfin ikonsa don sanyaya al’amarin zargin kisan kai a kan Abbah. A hukumance, an rufe ƙarar kuma Abbah ba ya cikin haɗari na kamawa a Kotu. ​A gida, Inna tana ƙoƙari sosai don gaya wa Maleekh gaskiya. Sau biyar kenan tana tare shi, amma sihirin Alhaji Wadata ya hana ta. ​Yau ma, kamar kullum, ta tsayar da shi zai wuce part ɗinsa. ​“Daman akwai maganar da nake so gaya maka dangane da wannan al’amarin…” ​Maleekh cike da mamaki ya ce, “Al’amarin ai biyu ne Inna. Akwai na Abbana, sannan akwai na Amal.” ​Inna ta ce, “Akan na Abbanka…” ​Ya ce, “To, ina jinki.” ​Inna ta tsaya, ta yi shiru. Ta kasa furta komai! ​Bayan dogon shiru ta ce. “Shikenam ma, ni na manta abinda zan ce ma…” ​Maleekh ya girgiza kai. Ya lura cewa sau biyar kenan tana masa haka. Ya rasa gane dalilin wannan mantuwar kwatsam.. ​Ya kalli Islam sannan ya ce, “Ku kawo mun yarana, ina son ganinsu.” ​Daga nan ya haura sama, inda ya kwanta a kan gadonsa. Islam da Arfat suka shigo da tagwaye, suka ɗora masa su a faffadan kirjinsa. Ya rungume su, yana lumshe ido cikin farin ciki. ​Bayan mintuna kaɗan, Farha ta shigo gidan da sallama. Bayan ta gaisa da Inna da Ammy, ta nufi ɗakin Maleekh. Ta danna ƙararrawa, jin shiru yasa ta murɗa handle ta shiga.. Tana shiga ta sake masa knocking a bedroom part ɗinsa, a hankali ya furta "come in.." Ta same shi kwance da jarirai a saman kirjinsa. ​Farha ta zauna a kujerar gefen gado. ​Idonsa a lumshe ya furta “Ya akayi?” ​Farha ta fara magana, tana bayyana nadamarta akan hukuncinsa.. ​“A lokacin da ka shigar da ni ƙara… nayi zaton ni kawai ka tsana… amma yanzu na tabbatar da cewa kai ɗin na Musamman ne, zaka iya ɗaukan hukunci akan kowa. Ban tabbatar ba sai da ka aiwatar akan masoyiyarka… amma abinda nake gani yanzu shine sam bai dace kayi mata wannan hukunci ba ko don saboda yaranta…” ​Maleekh ya dube ta sannan ya ce, “Shin ke bakya tunanin zakiyi aure ne? Idan kika haihu yaranki suka girma bazasu san cewa kin taɓa zaman prison ba? Ki fara duban kanki kafin ki dubeta!..." Farha ta ce, "Amma mutane sai magana suke..." "Bana duban mutane idan zan aiwatar da abinda ya dace, domin ba tsoron kowa nake ba a cikin mutane!” ​Sannan ya ƙara furta “Shin me ya kawo ki?” ​Farha ta ce akwai wata magana da ta kawo ta. “Kwana kusan uku kina ƙirana a kan zaki gaya mun wata magana amma kin kasa. Kina son raina mun wayo ne?” ​Farha ta girgiza kai ta ce, “Hakan yasa na tako nazo da kaina.” ​Ya ce, “Ina jinki.” ​Ta fara bayyana cewa, “Zargin kisa da ake yi wa Abbah ba gaskiya bane… akwai wata rana da na fara fitowa a prison har ka kawo ni gida… to, to, to, to, to, tooo, tooooo, toooo, toooo…” ​Maleekh ya katse ta saboda tsananin shirme da take yi. ​“To, to, to, ya isa haka! Bana son shirme fa!” ​Farha ta fara hawaye. Ta faɗi cewa ta manta abin da zata furta. ​Maleekh ya kalle ta, sai kuma Inna ta faɗo masa a rai! Itana tana son gaya masa magana amma sai mantuwa ya biyo baya, yana tunanin duk maganar ɗaya ce indai hakane...! ​A hankali ya furta “Kina nufin kice kinsan waɗanda suka shirya makircin nan? Kuma daga gidanku? To waye?…” ​Farha ta tsaya tana kallonsa, ta kasa cewa komai! ​ “It’s okay! Zan binciko komai da kaina! Tashi ki tafi!” ​Farha ta miƙe, jiki a sanyaye. Tana shirin barin ɗakin, sai ga wata kalma ta bugi dodôn kunnenta: ​ “Za ki aure ni?…” ​Kirjinta ya fara bugawa da ƙarfi! Ta juyo baya ido a zare tana kallonsa! ​Ya ƙara maimaitawa “Ki shirya! Next week ɗaurin aure! That’s it!” ​Farha ta sake baki tana kallonsa. Bata yi tsammanin haka ba! ​Maleekh ya kwantar da yaran a hankali. Ya miƙe, ya iso wurinta, ya rungume ta sosai. ​“Idan kinje, ki sanar wa iyayenki cewa zan kawo sadakin ki!” Ya ƙarasa yana shafa mata sumar gashi ta cikin gyalenta... ​Daga nan ya sake ta. Farha ta fice daga ɗakin tana mamakinsa! Bayan kwana biyu. ​A safiyar yau da za a wuce da Amal zuwa Prison, Maleekh ya shirya tsaf domin dashi za’a kaita. Kafin ya fita, ya shiga ɗakin Inna don yi mata bankwana da kuma bayyana ra’ayinsa. ​Maleekh ya zauna a gefen Inna bayan ya gaishe ta.. “Inna, kiyi haƙuri akan abin da nayi na hukunta Amal. Na san ranki bazai yi daɗi ba, amma nima ba yanda zan yi, ba’a son raina nayi hakan ba. Nayi hakan ne domin na samu salama. Zanyi bincike na yanda ya dace a tsare. Zaman ta zai iya bani cikass (clues opportunity to find the truth).” ​Inna ta girgiza kai, tana hawaye ta ce, “Baka yi laifi ba Maliku, abinda kayi daidai ne. Ta cancanci hakan! Wanda yake shirin aiwatar da kisan kai ai hukuncinsa shine gidan yari. Ko kaɗan Amatu ta rasa imaninta! Bata cancanci ta zama uwar ƴaƴanka ba!” ​Maleekh ya jinjina kai, sannan ya tashi ya fice... ​Maleekh ya nufi Station. Ya yi parking motarsa a bakin station, ya fito ya jingina bayansa a jikin motar, yana facing Station. Ya rufe idonsa da baƙin glasses ɗinsa. ​Bayan wasu mintuna, ƴan sanda suka fito da Amal, tana tafiyar wahala saboda dawa da dukan da aka yi mata. Aka kaita gaban Maleekh. ƴan sanda suka juya.. ​Maleekh ya ƙare ta da kallo ta cikin glass. Ya fara furta mata maganganu. "I can do anything for my father, no matter who he is. My father is very important in my life. If anything had happened to him at that time, I would have shot your brains out because you don't know the value of elders. You don't know the value of old age, you don't know the value of the person who loves you." Ya cigaba da faɗin "Rashin hankalinki da taurin kanki da nauyin bakinki yasa sauran kaɗan na kasheki har lahira... inda ace kece asalin wacce kika kai farmaki da kin ƙare rayuwarki a gidan Prison. Sa'arki ɗaya da na gano gaskiyar lamarin...".. ​A cikin rashin sanin kowa, Maleekh ya riga ya gano gaskiyar lamarin. ​An rufe case ɗin Amal saboda an gano gaskiya ta hanyar CCTV (na'urar tsaro) da ke wajen asibitin. An ga ainihin mutumin da ya wurga jarkar petur a gabanta. An kama shi! Yana tsare yanzu haka, amma ya kasa bayyanar da wanda ya turo shi. ​ ​Maleekh ya riƙo hannunta da ƙarfi, ya buɗe murfin motar shi ya wurgata ciki sannan ya rufe. ​Shima ya zagaya ya shiga. Ya ja motar a ɗari ya bar wurin. Maleekh ya sanya mic ɗin sirri a gashin Farha lokacin da ya rungume ta a ɗakinsa. Ta hanyar Bluetooth, ya saurari dukan maganganun da suka faru tsakanin Farha da iyayenta (Alhaji Wadata da Matarsa). ​Abubuwan da Maleekh Ya Ji. Ya tabbatar da cewa Alhaji Wadata ne ya tura ƴan daban don sa wuta a asibiti. ​Ya ji maganganu da ke nuna cewa Alhaji Wadata ne ainihin wanda ya kashe iyayen Amal tare da Alhaji Gusau, kuma sun yi wa Abbansa sharri ta hanyar bidiyo. Ya tabbatar da cewa Alhaji Wadata ya kulle ɗansa Zayd domin kada ya tona asiri.. ​Ya ji batun layar da Alhaji Wadata ya yi amfani da ita don rufe bakin shaidu.. ​A cikin kwana biyu, Maleekh ya san ainihin gaskiya da kuma makiyansa!... ​A cikin mota, Maleekh ya sanar da Amal hukuncinsa mai zafi. “Zanyi aure.” ​Amal ta razana, ta juyo tana kallonsa. Cikin kuka da azaba ta furta: ​“Amma kafin kayi ka tabbatar ka sake ni! Domin ba zan iya zama dakai da wata ba!…” ​Maleekh ya furta. “Whatever you said… Farha zan aura. Next week!” ​Amal ta ja wani irin numfashi mai zafi. Zuciyarta ta buga! Lokaci guda ta sume a kujerar motar. ​Maleekh kallo ɗaya yayi mata, ya cigaba da jan motarsa ba tare da ya damu ba. Ya sani cewa zai farfaɗo da ita a lokacin da ya dace... Kai tsaye gidansu Farha ya nufa. Amal ta farfaɗo a hanya, tana kuka mai zafi ba tare da ta san inda za su ba. Suna isa ƙofar gidan Alhaji Wadata, suka tsaya. ​Ya kalleta, cikin tsanaki ya ce, “Ki share hawayenki! Domin zamu shiga gidan sirikaina! Kar su fahimci kishi ne yasa ki kuka!” ​Amal ta wurga masa wani irin harara mai zafi. ​Ya sauƙa, sannan ya ce “Ta sauƙo!” ​Amal ta nuna ba za ta sauko ba. ​Ya ce, “Kinga irin taurin kan naki ko? Oya come out. Fito!” ​Ta fito jiki a sanyaye. Maigadin gidan ya buɗe musu. Suna shiga babban falo, suka tarar da Alhaji Wadata, Matarsa, da Farha suna breakfast (ƙarfe 12 na rana). ​Farha ta miƙe da tsananin mamaki da firgici ganin Amal a tare da Maleekh! ​Maleekh ya riƙo hannun Amal, ya zaunar da ita a kusa dashi. Amal tana harararsa ciki fushi... ​Ya ɗaga musu hannu da cewa. “Yaa ku zo mana! Ko bakuyi farin cikin ganina bane?” ​Suka nufo falon da mamaki da damuwa lokaci guda. Maleekh yana daga zaune ya furta. “Ina wuni Uncle, duk da naga yanzu kuke breakfast! Kuma nasan kunyi mamakin ganina duk da na sanar da yarinyarku cewa zan zo.” Ya kalli Farha ya ce “Ko ba haka bane?” ​Farha ta jinjina kai tare da fad'in “Hakane.” ​Amal ta wurga mata wani irin harara, tare da jan dogon tsaki! ​Maleekh ya kalle ta ya ce, “Ya haka? Baki san gidan sirikai na bane? Ke ba daga cell kika fito ba?!” ​Ya maida kallonsa kan Alhaji Wadata. ​ “Daman na wakilci Mahaifina zuwa neman aure na, don haka nazo nemawa kaina auren ƴarku Farha! Ko dan Uncle ai kaima mai nema mun aure ne, kaga tinda ƴar gida za’ayi, shikenam faɗuwa yazo dai-dai da zama!” ​Alhaji Wadata ya ce, “Ita matar takan ta amince ka auri Farha ne?” ​Maleekh ya ce. “Matata ai ni nake auranta ba ita take aure na ba! Don haka yasa ta rakoni zuwa neman aure yafi nazo ni kaɗai. Ma’ana itace wakiliya ta!” Ya kalle ta tare da rungumarta “Ko ba haka ba jarumata?”... "Aww! Ashe dai ke zaki nema mun aure nake ta ɓaɓatu, yanzu abin da zaki ce shine kice 'Ni Amatu, na zo nema wa mijina Maleekh auren ƴarku Farha..." Wani irin wurga masa kallo tayi, idonta har yayi jawur tana kallonsa.. Shima itan yake kallo ya ce "zaki faɗa ko a'a? ..." Haɗe gira tayi kai a sunkuye ta ce. "Ni Amatu, nazo nema wa mijina auren ɗiyarku Farha..." Maleekh ya dube ta ya ce. "Ahhhh! Haka ake neman aure daman? Fuska a murtuke? Ai za ki sa su kore mu kuma..." Yasa hannu ya ɗago da habarta ya ce "ki kalle su ki nema mun aure malama..." Wani irin yawu ta haɗiya sannan ta ɗan sake fuska ta ce, "Ni Amatu, na zo nema wa mijina Maleekh auren ɗiyarku Farha..." Maleekh yayi murmushi yana duban Alhaji Wadata sannan ya ce "To Alhaji gare ka fa, ana nema mun aure a wurinka, ka amince kawai..." Alhaji Wadata ya jinjina kai cikin ɓacin rai sannan ya ce "Shikenan na baku..." Maleekh yana dariya ya kalli Amal ya ce, "kiyi godiya mana an bamu mace..." Amal kai a sunkuye hawaye ya gama cika idon ta ce, "Mun gode..." ​Maleekh ya sa hannu ya ciro ɗamin kuɗi da zasu yi kimanin Dala miliyan 5 ($5,000,000). Ya ba Amal yana faɗin. ​“Wannan sadakin Farha ce! Ki karɓa, kije ki bawa mahaifinta! Yafi ni na bashi da hannuna, kinga ba mutunci ai. Don haka kiyi mun kara kije ki basu!” ​Amal tana turo baki kamar zata fashe da kuka, ta karɓa. Tana takawa a hankali, ta je gaban Alhaji Wadata ta tsaya tana ɗaga kai sama ta miƙa masa kuɗin... ​Alhaji Wadata ya karɓa yana kallon Maleekh. Amal kuwa ta je ta tsaya, ta kasa zama.. ​Shima Maleekh miƙewa yayi yana faɗin: ​“To mu zamu wuce.” Ya kalli Amal ya ce, “Jarumata, ni ya auren zai kasance ne? Wani rana ya kamata asa?” ​Amal ta yi wani irin jan tsaki, ta bar falon a fusace. Ta buɗe ƙofa ta fice. ​Maleekh kuwa ɗaga kafaɗa yayi ya dubi su Alhaji Wadata. ​ “Kuyi haƙuri fa kunsan halin mata, dole sai sun ɗan taɓa kishin nan. Yanzu dai bikin zai kasance ranar Asabat, sauran kwana biyar yanzu!” ​Daga nan ya fice shima. ​A mota, ya tarar da Amal zaune tana kuka. Shiga yayi yana shirin tada mota. ​Amal ta fara ɗaga murya tana kuka. “Ka cuceni Maleekh, kaci amanata wallahi, sannan ka wulakanta ni da kuma alakar dake tsakaninmu na ma’aurata... shin na cancanci kamun wannan wulakanci da cin fuska? Ai gwara ka barni na hallaka a prison akan wannan tozarcin daka mun!” ​Maleekh ya zaro ido tare da faɗin “Me kuma na miki?” ​Amal ta cigaba da faɗin “A tarihi a ina ka taɓa jin mace ta nema wa mijinta auren wata daban? Har ka ban kuɗin sadaki kace na basu? Wannan ai cin fuska ne bayan kasan inada kishi!” ​Maleekh cike da zolaya ya ce, “Au haba! Yanzu kina kishina? Ai ban san haka kike sona ba sai yanzu! Yanzu ana kishina! Ba kuma hakan zai hana a fasa auren ba!” ​Ya ja motar suka tafi, kai tsaye gida suka nufa dake unguwar Maitama... _NEXT NEXT NEXT_ asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 93 to 94 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Bayan sun bar gidan Alhaji Wadata, inda Maleekh ya yi amfani da Amal don wulakanta su tare da bayyana dabararsa ba tare da sun sani ba, kai tsaye suka nufi gidansu Maleekh a Maitama. ​Da suka isa gida, Amal ta fito daga motar tana kuka mai tsanani da tsananin fushi. Bayan ta shiga falo, Ammy da Inna suka tarbe su da mamaki ganin Amal a gida, ba a Prison ba. ​Amal ba ta ko kula da kowa ba. Ta tunkari Maleekh da tsawa a tsakiyar falon. ​Cikin kuka take faɗin “Maleekh! Ka yi zaton dabarunka sun yi nasara! Ka cuceni har sau biyu! Na farko da ka bar ni a cikin ƙazamar cell! Na biyu da ka yi mini wulakanci a gaban danginka! Ka ci amanar ƙaunata! Ka manta da yaranka! Me yasa za ka so ka azabtar da ni haka! Meyasa ka sa ni na je na nema maka auren wata! Ka sani cewa kai ba namijin kirki ba ne! Ni na cancanci mutuwa a Prison a kan na ga wannan cin amanar!” ​Maleekh ya tsaya cak, ya dube ta cikin tsaurin fuska. Ammy da Inna sun yi shiru cike da damuwa da rashin sanin abin da ke faruwa. ​Maleekh ya ɗauki Amal a hannunsa, ya haura da ita can saman Bedroom ɗinsa, ya rufe ƙofar da ƙarfi. ​Ya kwantar da ita a kan gado, sannan shima ya haura saman kanta yayi mata doki yana fuskantar ta. ​Ta buɗe baki zata yi magana, ya yi saurin toshe mata baki da nasa. Tana ƙoƙarin ture shi, ya haɗe hannayenta biyu ta sama ya riƙe da hannu ɗaya. Haka yake ta sumbatar ta ba kakkautawa. ​Jin yanayin ya fara ratsa jikinta ya sa ta fara lumshe ido. A hankali kamar ba zata iya ba take ɗan mayar masa da martani... A lokacin ta fara tuna zamansu a dajin mafarauta da yadda suka kasance.. ​Maleekh ya zamar da bakinsa a cikin nata, yana kallonta da shanyayyun idanuwa. ​A hankali ya furta “Yaa! Akwai daɗi ne?…” ​Ta buɗe ido tana kallonsa. Kallon ya ci gaba.. ​A hankali ya kifar da kansa cikin wuyanta yana kissing. ​“Ya Maleekh! Uhm! Uhmm!! Ina tsoro, please don’t fuck me!…” Ta furta tana ɗago masa breast. ​ “Why! Bakya son ki karɓi tsarabar da na kawo miki ne? Uhmmm Sakaliya ta…” ​Ta ce, “Uhmm! Uhmm!! Ina aure zaka yi…” ​“Kina mun rowa ne shiyasa zanyi…” a cewarsa. “Too! Zan na baka amma ka fasa auren please …” ​Ya ce, “Kinyi alƙawarin zaki na bani sau biyar a rana?” Ta zaro ido a ruɗe.... “Heeeeee! Ka tausaya mun mana…” “Nima ki tausaya mun domin ni ɗin hariji ne…” ​ “Harijiiiiii?… 😳😳😳” ​ “Cikakke ma! In kuma bazaki iya ba sai na kawo miki mai taya ki…” Ya furta yana kanne mata ido ɗaya. ​ “Uhmm Uhmmm Ummmmm…” Ya kuma cewa. “Ok za ki iya ɗauka ta 5 hours ba tare da na sauƙa ba?” “Na shiga uku, na lalace wallahi kai azzalumi neeee!” ​“To! Kuwa sai nayi auren…” ​Kuka ta farayi irin na sakalan nan, a shagwaɓe. ​A hankali ya ƙara toshe musu baki wuri ɗaya, sai kukan ya ɗauke... ​Amal ta ja bakinta daga nasa, ta kalle shi da kakkausar murya: ​“Na rantse da Allah, idan har baka daina ba—” ​Maleekh ya yi murmushin mugunta: ​ “Faɗi na gaba. Rantse da Allah, menene?” “Zan ƙona dukkanin kayan sawa naka.” ​Ya yi shiru na ɗan lokaci sannan ya furta: ​ “Dramatics.” “To gwada ni.” ta furta tana huci.. ​Maleekh ya yi murmushin gefe: ​“Wannan shine barazanar soyayya (romantic threat) mafi daɗi da na taɓa ji.” ​Amal ta tattaro ƙarfinta (ba wai don ta fishi ƙarfi ba ne) ta tura shi gefen gadon tana faɗin: ​“Zauna. Ka nutsu. Ba za a yi faɗa ba a yau.” ​Maleekh ya ɗaga gira: “Yanzu kina ba ni umarni ne?” ​ Tana nuna yatsa a kansa: ​“Ina nufin babu zubar jini. Babu karya ƙashi. Babu kisa.” ​Ya juya idanu yana dariya ya ce, “Funny girl, wato duk halina ne.” ​Ta sauƙa a kan gado tare da miƙewa ta haɗe hannayenta a gaban kirjinta ta ce: ​. “Kana so na?” ​Ya numfasa cike da wasan kwaikwayo: “Abin takaici, eh, ina so ki.” ​Amal ta ja numfashi. Hannayenta suna kan kwankwasonta, tana zura masa idanu: ​“Kai mai ƙazamin hali ne, na rantse...” ​Maleekh ya katse ta cikin nutsuwa: ​“Ina son ki ma (I love you too).” ​Jikinta yayi sanyi: ​“I—mene?” ​ Ya yi murmushi, yana jingina bayansa da jikin marfin gadon: ​ “Oh, na yi haƙuri. Wani abu kika faɗa ne?” ​Amal ta matso jikin gadon tana nuna yatsa a saitin zuciyarsa: ​ “Wannan ba shine lokacin da ya dace ba da za a faɗi hakan.” ​Ya yi murmushin gefe: ​ “Oh? Kina so na jira har ki sake kira na abin damuwa.... A menace ma?” ​Amal ta yi nishi mai zafi: “Ba zan iya jure maka ba.” ​Ya sa hannu ya janyo ta kan gadon tare da zaunar da ita ya jingina jikinsa da nata, sannan ya ɗora haɓarsa a kan kafaɗarta: ​ “Wannan abin dariya ne.” ​ “Me?” ta ce tana zaro ido. ​Ya yi murmushi, “Har yanzu kina nan.” ​Ta juya masa baya, muryarta a kasalce ta ce, ​“Yaushe za a yi auren?” ​Maleekh ya numfasa, sautin numfashin nasa mai nauyi ya cika da shiru: ​. “Kada ki yi wannan tambayar yanzu...” ​A fuskance, idanunta suna wuta ba tare da hawaye sun fito ba, ​ “Ka yi min alƙawarin har abada. Yanzu kuma, kana son kayi rayuwar da ya kamata ta zama tawa da wata.” “Abu ne mai sarkakiya, kin sani.” Ya furta. ​Amal ta matso kusa, tana nuna masa zuciya da yatsa mai rawa: “A’a. Abu ne mai sauƙi ka zaɓi kwanciyar hankali akanmu. Kuma ba zan zauna in kalle kana aure ba.” ​Maleekh ya riƙe hannunta, muryarsa cike da raɗa. ​ “Ke ce kwanciyar hankali na. Ke ce gidana, ko da kuwa dole ne in gina wani gidan daban. Ba zan taɓa daina buƙatar ki ba.” ​Amal ta zare hannunta. ​ “To kada kayi auren indai hakane.” ​Maleekh ya rufe idanunsa, gudun kada ya haɗa ido da ita a yayin da zai furta ​“Dole ne nayi...” ​Muryar ta ya zamo raɗaɗi, idanunta na kallon zoben da yake sanye a yatsanta, wanda ya sanya mata na alƙawarin da bai cika ba. ​ “Ba na buƙatar tausayinka, kuma lallai ba na buƙatar ‘gida’ wanda aka gina don mata biyu daban-daban.” ​Maleekh ya riƙo haɓarta tare da juyo da fuskarta zuwa gare shi, yana miƙa hannunsa, ​“Saurare ni. Wannan zaɓin da na yi—” ​Amal ta katse shi, tayi saurin miƙewa daga kan gadon tana faɗin: ​ “Zaɓin da ka yi shine ka karya ni?. Kada ka ɗauko wani zance daban domin baka da dalili. Idan har ni ce gidanka, da ba za ka yi shirin barin gida don shiga rayuwar wata ba.” ​Idanun Maleekh cike da damuwa ya ce: ​“Ita ce tsayuwa wato (stability). Ita ce hanyar da ake sa ran zan bi. Amma ke ce hanyar da koyaushe zan yi marmarin bi. Zan kiyaye ki. Na yi alƙawari.”.. ​Ta yi dariya, wani irin dariya mai tsanani da karyewar zuciya. ​ “Kiyayewa? Ka jefar da ni a cikin wuta, kuma kana ƙiran hakan kiyayewa. Fita. Ka je ka gina gidajenka. Amma kada ka kuskura ka waiwayo, domin ba za ka same ni a nan ba.” ​Maleekh ya juya idanunsa yana wasa da su yace: “Baza ki iya tsorata ni ba.” ​“Ya kamata ka ji tsorona.” Ta furta tana zaro masa idanu.. ​Ya yi murmushin raini sannan ya furta ​“Tsawon ki ƙafa biyar ne kacal (five foot nothing), kuma kin sato wani abu mai laushi daga gare ni, wato samartaka na, kin riga kin kalle mun kan kaciyata.. Don haka ba ki da wani abu mai tsoratarwa.” ​She narrow her eyes sannan ta ce, ​ “Wannan abin wasan yaran, nawa ne ai yanzu, ba na wata ba...” ​Maleekh ya yi murmushi, yana harararta: ​“Abin wasan yara? Shiyasa naga har da ihun ki a daren farkon ki da kuma majiya...” ​Amal ta yi nishi, sannan ta jefa masa matashi (pillow), tare da faɗin. “you are a worst.” ​ Ya kamo ta, yana murmushi: ​ “Ba haka kika yi ba a daren farkon.” ​Amal ta ƙara jefa masa wani matashin: ​“Ai tilasta mu akayi ba da gaske ba, ba dan haka ba me zai sa na kwana ɗaki ɗaya da kai.....” ​Ya lumshe ido ɗaya: ​“Haka ne. Kuma duk da haka kika juya tare da manne jikinki da ni kamar wata koala.” ​Ta buɗe baki zata yi magana. ​Ya yi saurin jawo ta kusa da shi a saman gado, zafin jikinsa ya lulluɓe ta. Ya ci gaba da yi mata lafiyayyun sumbata masu daɗi daga kafaɗarta har zuwa wuyanta, taɓawarsa mai nuna mallaka da tausayi. ​Amal ta yi ƙoƙarin juyar da kanta, wata iska mai laushi ta fita daga bakinta: “Ina buƙatar—” ​Maleekh bai bari ta ƙarasa ba. Labbensa suka kama nata nan take, wani sumbata mai zurfi, mai sanya shiru wanda bai bar wani wuri don magana ba, sai dai yaren sha'awa.. Hannunsa yasa ya tallabi bayan kanta, yana zurfafa wannan haɗuwar. ​Hannayen Amal sun shiga cikin gashin kansa, wanda hakan ya narkar da ƙin yardar da take yi zuwa yarda mai zafi. Iskar ɗakin ta cika da alƙawurra marasa yawa da buƙatar gaggawa, inda suka gane cewa wani lokacin, kalmomin soyayya mafi daɗi sune waɗanda aka bari ba a faɗar su.. ​Maleekh ya dakata da sumbatar, goshinsa a manne da nata, numfashinsa yana fitowa da sauri. Ya raɗa, muryarsa a kasalance. ​“Manta da duniya a daren yau. Kawai ki kasance tare da ni. A nan. A yanzu.”.. ​Amal ta raɗa sunansa a hankali, muryarta da kyar ake jinta saboda saurin numfashinsu. Yatsunta sun zame a ƙarƙashin rigarsa, suna bin tsatsaran bayan jikinsa mai zubin jarumta, tana ƙara jawo shi kusa da ita, suna tabbatar da alƙawarin da ya yi mata a baya, ita ce gidansa... ​Sumbatun Maleekh sun rikide zuwa na gaggawa, suna motsi da zazzafar sha'awa a jikin wuyanta, yana jin daɗin sautin numfashinta da ke tsayawa a maƙogwaronta... ​Duniyar da ke wajen ƙofar ɗakin kwanciya ta daina wanzuwa. Su biyun ne kawai, suna cikin rami na buƙata da so. Inuwa tana rawa a bangon ɗakin suna shaida soyayyarsu mai tsarki, mai cin dukkanin jiki, kuma mai sa maye.. “Ke ce jarabata,” ya raɗa, wata furci mai zafi da ta rufe makomarsu na daren... “Kuma a daren yau, babu iyaka.” ​Suna motsawa tare a cikin wani irin salo mai kyau, wanda ba a buƙatar magana. Sautin da ke fitowa daga ɗakin shine kawai nishi mai laushi wanda ke fitowa daga labbobinsu, kalmomi sun rasa dukkanin ma'ana, sun zama tsantsar furci na nisantar hayyaci. Suna magana da wani yare wanda jikinsu kawai ke iya fahimta.. ​Hankalin Amal ya karkata gaba ɗaya akan taɓawarsa, kasancewarsa, da yadda sunansa yake ji kamar addu’a a bakinta... Bayan da suka shanye soyayya mai zafi da kuma warware rikicin da ke tsakaninsu a cikin ɗakin, Amal gaba ɗaya jikinta ya sake. Ta kasance cikin kasala ba tare da wani ƙarfi a tattare da ita ba. Tana lumshe ido alamun bacci mai nauyi. ​Maleekh ya yi ƙarfin halin tashi yana sakin ajiyar zuciya kamar wanda yayi wani aikin wahala. Idonsa ya kai da duban Amal. Ya sau murmushi tare da jin ƙaunarta a cikin zuciyarsa.. ​Har ta fara bacci, ya sa hannu yayi mata ɗaukar jaririya sannan ya nufi Bathroom da ita. ​Yana shiga ya nufi Bathtub (wurin wanka), ya zaunar da ita a ciki. Still idonta a rufe, ta kwantar da kanta akan tsararren kirjinsa. ​Hannu ya sa ya kunna tap na bathtub. Ruwa mai ɗumi ne yake zubo mata. ​Hannu ya sa ya debo flowers ya zuba a cikin ruwan bathtub ɗin. Sannan ya zuba turaruka wurin kala biyar a cikin ruwan. ​Ya ɗauki soap mai kamshin bala'i ya fara mata wanka a hankali yana motsa jikinta mai laushin gaske... ​A hankali ta buɗe eyes ɗinta jin ruwa mai ɗumi yana ratsa jikinta. Ruwan kuwa ya canza kala saboda kalolin turaruka, ga kuma flowers. ​Sai da ya tabbatar ya gama mata wankan, sannan ya ɗago ta, ya ce da ita: ​ “Sauran wankan janaba (wankan tsarki), ke zaki yi da kanki.” ​Ya juya zai ɗauko mata towel. A lokacin Amal ta sake haɗa ruwa da ƙyar jiki ba ƙwari, ba tare da haɗin a cikin ruwan ba tayi wankan dashi. ​Maleekh yana zuwa ya ɗaura mata towel sannan ya ɗaga ta ya fita da ita... ​Nan ma zaunar da ita yayi akan kujerar mirror. Sannan ya haɗa mata mayukan turaruka masu kamshi ya mulmulka mata. Ya shafa mata na gashi (hair oil/cream) sannan ya ɗauko mata sleepy dress riga da wando a cikin nasa (wanda ba maza ba mata, wato unisex style), ya sanya mata. ​Yana gama wa da ita ya kwantar da ita akan katafaren gadonsa tare da rufe jikinta da blanket... ​Maleekh shima ya shiga bathroom yayi wankansa haɗi da wankan tsarki ya fito. Shima ya kimtsa cikin jallabiya ya tsaida Sallah. Sai da ya gama lafulolinsa da addu’o’i sannan ya kwanta cikin blanket shi da babynsa.. Ita kuwa ta juma da bacci.. 🪸🪸🪸 Washegari da safe, misalin ƙarfe 8, kowa na falon ƙasa, amma banda su Amal da Maleekh. ​Anata jiran fitowarsu shiru ga breakfast an kammala. Ganin ba zasu iya jira ba yasa suka fara ci. Ammy, Inna, Islam, da Arfat duk sun fara karyawa.. ​Har ƙarfe 9: ​Ammy ta ce “Ni waɗannan kam lafiyarsu ƙalau? Kodai sun mutu ne…” ​Islam tana dariya cikin tsokana ta ce, “Haba Ammy ki barsu su shakata mana, amarcin da basu sha ba shine yanzu suke…” ​Ammy ta wurga mata harara da faɗin “Za ki shige su da iyeyi ai…” ​Arfat tana harara da fushi ta ce, “Ni ai Aunty Amal ta fita mun a rai tinda tayi ƙoƙarin kashe mana mahaifi da wuta…” ​Ammy ta daka mata tsawa da cewa “Kar na sake jin haka daga bakin ki!” ​Inna dake zaune ta ce, “Ai gaskiyarta.” ​Islam ta ce “Ai ni tinda ku ka ga na dawo normal to gaskiya ta fito, domin shekaran jiya na je kaiwa Ya Maleekh abinci naji yana waya da DPO cewa ‘ya tura masa CCTV da ya nuna wanda ya kai farmaki… kuma an kama shi, Aunty Amal sawun ɓarawo ta taka…” ​Ammy ta ce, “Rashin bincike ne kawai a lokacin amma nasan ba yanda za’ayi Amal ta iya kashe Abbanku.” ​Ta kai dubanta kan Food Flask ta ɗauka zata kai musu abin karyawa. ​Islam ta ce, “Ammy kawo a kai mana…” Ta ce, “A’a inaso zanyi magana da su ne…” ​Daga nan ta haura sama. ​Har zuwa yanzu Maleekh da Amal basu farka ba. Tsabar bacci yayi daɗi! Amal na kan Maleekh, shi kuwa ya nannade ta da ƙafarsa. ​Knocking aka fara yi. Sai da aka buga ƙararrawa kusan sau biyar kafin Maleekh ya ɗan buɗe idonsa. ​Shafa sumar kan Amal yayi kafin ya ɗan saukar da ita kan gadon daga saman jikinsa. Jallabiyar duk ya koma ciki, sai ƙaramin pant na maza. ​A hankali ya miƙe yana addu’a. Ɗaga kansa yayi ya kalli agogo: 9:15! ​Ya zaro ido a wahalce tare da furta: ​ “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Subhanallah, a uzubillahi mina shaidani rajin… i missed asuba prayer..." ​Jin an ƙara buga ƙararrawar falon ne yasa ya nufi falo da sauri. Yana zuwa ya buɗe. Ganin Ammy yayi da Flask na abinci. ​ “Wai baccin mutuwa kukayi ne Maleekh?…” ​Sai zazzaro ido yake, kirjinsa na bugawa da ƙarfi. ​Ammy ta dube shi kamar ba'a cikin hayyacinsa yake ba ta ce, “Lafiya kuwa?” ​A hankali ya furta “Shigo, na makara yau banyi asuba ba…” ​“Innalillahi!” Abin da Ammy ta furta, kafin ta buɗe baki har ya bar falon ya koma cikin Bedroom tare da shige Bathroom zai ɗauro alwala. ​Ammy shigowa tayi ta zauna a kujerar falo tana kallon plasman dake kunne, kafin su gama abinda zasu yi. ​Maleekh ne ya ɗauro alwala ya fito yana gyara jallabiyarsa da yayi sukwizin. Hannu yasa yana tattaba Amal akan ta tashi. ​Amal sai mutsil-mutsil take ta kasa buɗe ido. ​“Tashi mana baccin bai isa haka ba?” ​Ta furta a shagwaɓe “Uhm uhmm ni kam ka barni, na gaji da yawa…” “Ƙarfe 9 ta wuce yanzu kuma baki yi sallar asuba ba…” ​Amal ta zaro ido lokaci guda! A zabure ta tashi zaune tana duban agogo! ​“Innalillahi!” Ta furta tare da tashi da gudu ta nufi Bathroom... 🪸🪸🪸 ​A ɓangaren gidansu Farha, Alhaji Wadata ya shiga ɗakin da ya kulle Zayd. Zayd yana kwance a gado, sai dai a kawo masa abinci, amma hatta wayarsa an karɓe. ​Alhaji Wadata ya zauna a bakin gado tare da faɗin: ​“Ka tashi ka zauna.” ​Zayd ya tashi yana kallon Daddynsa. ​ “Yau za ka yi free, domin yau sauran kwana uku bikin kanwarka Farha da Maleekh…” ​Cike da mamaki Zayd yake kallon Mahaifinsa. ​Alhaji Wadata ya kuma cewa, “Ko da ka fitan ba zaka iya faɗin gaskiyar al’amarin ba… Kuma kamar yanda Maleekh yazo neman Auren Farha, to nima na tsara hakan akan kanwarsa (Islam). Don haka dole zaka auri Islam ba tare da wata matsala ba… Na fara gayyato manya mutane na waɗanda zasu halarci bikin yarana biyu… Taro za’ayi na musamman amma sai dai ba a kan idon mahaifinsu ba…” ​Daga nan ya miƙa masa wayarsa sannan ya fice... (Wadata ya san cewa layar rufe baki na kan Zayd shima, don haka bai damu ba). 🪸🪸🪸 ​A ɓangaren su Maleekh kuwa, Maleekh yana zaune a falonsa da Amal, sai Ammy wacce ta tara su take son magana da su.. Bayan Maleekh ya gaisheta, itama Amal ta durƙusa ta gaishe ta.. ​Ammy ta dube su sannan ta ce, “Gobe idan Allah ya yarda zan je Ethiopia domin zama da Abbanku… Sannan meke faruwa ne a tsakaninku?…” ​Maleekh ya ɗago ya kalleta ya ce, “Mom ki bar tafiyan nan sai bayan biki…” “To Maleekh bikin Zayd da Islam ai ba a tsayar da maganar ba sakamakon wannan tashin hankalin…” a cewar Ammy. ​“Aure na da Farha…” ​Amal ta wurga masa harara tare da kawar da kanta gefe. ​Ammy ta yi maganar tana kallon Amal “Kai da Farha kuma?…” ​Maleekh ya ce, “Zan cika miki alkawarin da na ɗaukar miki ne, wanda akayi yarjejeniya a gaban kowa da ita Amal kanta… Duk da ta kasance ta musamman a wurina tun kafin na mallaki hankalin kaina…” ​Ammy ta ce, “Gaskiya ban yarda da kai ba Maleekh, nasan ba batun cika alkawari bane…” ​Maleekh ya yi murmushi shi kaɗai ya san abin da ke ransa. Ya ce: ​ “Da gaske nake, bayan haka babu komai, sannan za a haɗa bikin da na Islam da Zayd… Bayan nan sai ki tafi kije kiyi jinyar mijinki…” ​Ammy cike da mamaki ta ce, “Amma Abbanku fa? Kasan yana kwance jinya shine za a tada hidima?..” ​Ya jinjina kai sannan ya ce, “Nasan inda Abbah yana magana zai goyi bayan haka, sannan kar ki manta ya bar wakilinsa ɗan amana wato ni, zan wakilci komai.” ​Maleekh ya bayyana wa Ammy wani ɓangare na gaskiya da ya sani, domin ya rufe dabararsa. “Domin a duniyar nan wanda kake tsammani ba shi bane… wanda baka tsammani kuma sai ya zamo shi, don haka sauran kwana uku yau. A fara shirye-shirye…” ​Ammy ta ƙara jinjinawa cike da damuwa. “Anya kuwa Maleekh? Ni fa wannan auren nakan zai ban mamaki, ka gaya mun gaskiya…” ​Ya yi dariya yana girgiza kai ya ce, “Haba Mom! Kema fa mace ce, mata kuwa a duk yanda suke abu ɗaya ne… Don haka ki barni a yanda kika ganni…” Ta ce. “To shikenan Allah yasa haka shi yafi alkhairi…” ​Fashewa da kuka Amal tayi tare da miƙewa ta bar ɗakin. ​Ammy ta ce. “Ni fa idan Auren nan zai zamo tashin hankali to gwara a bar shi…” ​Maleekh ya kalleta sannan ya ce: ​“Lokacin da Abbah zai ƙara aure wani irin tashin hankali ne ba a shiga ba akan ki? Har shirin kashe kanki kikayi amma sai da akayi auren nan, don haka itama ko bori zata tayar sai anyi ba fashi…” ​Ammy ta tsaya kallonsa ta ce: ​“Tooo ikon Allah abun har da gayan magana Maleekh? To kayi auren…” A lokacin da Amal ta sauƙo falo daga ɗakin Maleekh, ta tarar da Farha ta shigo da sallama. ​Amal ta wurga mata wani irin harara mai zafi tare da shan gabanta ta tsaya tana kallon ta.. ​Amal cike da kishi ta ce, “Daman shiga jikina da kikayi ashe cin amanata zakiyi?…” ​Farha ta sau murmushi tare da tambayarta: ​ “Ina mijinki?…” ​ “Shi ba kawai mijina ba ne, shi ɗin rayuwata ne, shi ne nutsuwa ta a cikin rikici, kuma soyayyar da ke sa na ji tsaro.” ​Farha ta furta “Dakyau! Hakan zai ƙara bani sha’awar kasancewa tare da ku…” ​Amal ta ce. “Hakan yasa yanzun kika biyo shi gida? Saboda son aure irin naki…” ​Farha ta yi murmushi sannan ta ce: ​“Mutane suna tunanin son su yi aure, amma a wurina, aure ba shine buri ba. Auran mai nasara shine buri. Ni ba kawai ina son ganin zobe a yatsana ba ne. Ina so in yi aure mai farin ciki. Aure mai ɗorewa inda farin ciki, jin daɗi, girmamawa, biyayya, sha’awa, da kuma soyayya ta gaskiya suke kasancewa a koyaushe. Kuma na samu…” ​Amal ta ce, “Uhmm! Har yanzu baki samu ba Farha. Ki auri mutumin da ke da tausayi a gare ki. Kusanci game da tsaro, zaman lafiya da kike ji a wurinsa. Mutumin da zai kula da ke ta hanyoyin da kuɗi ba zai iya yi ba…” ​A lokacin Maleekh yayi magana, jin tattaunawarsu bayan ya sauƙo daga stairs. ​“Meyasa kike tunanin bazata samu hakan daga wurina ba Amal? Meye amfanin auren ta inhar bazan iya yin adalci a tsakaninku ba? Shin kina so saboda ita na shiga Jahannama?…” ​Amal ta fara hawaye ta ce: ​“Kai ne mutumin da na fi so a yau, Gobe da har abada, kowace rana. Zan kula da kai, ya kamata ka san wannan. Kai na musamman ne ga zuciyata. Ina so mu kasance tare har abada. Har abada, za ka zama mai mahimmanci a gare ni. Tare da farin ciki, koyaushe za mu kasance. Ba tareda wata ba a gefe ba…” ​A lokacin Ammy itama ta sauƙo tana sauraronsu. Ga Inna itama acan kujera tana jinsu. Islam na kan dining da Arfat a gefe ta zuba musu ido ganin basu san meke faruwa ba.. ​Maleekh yayi murmushi yana kallonta.. ​Amal ta kalli Farha ta kuma cewa: ​“Yana mu’amala da ni kamar yaro wanda ke kula da kayan wasansa sosai.” ​Farha ta kalli mutanen falon tana dariya tare da faɗin: ​ “...‘Yana mu’amala da ni kamar yaro wanda ke kula da kayan wasansa sosai’…” in ji ta. “Amma ta manta cewa soyayyar da ake yi wa kayan wasan yara tana raguwa yayin da yaron ya fara girma.... Babu wani abu da ke dawwama har abada Amatullah Abdulsamaad. Oh ashe dai ke Auntyna ne yanzu ‘Aunty Amal’…” ​Amal ta buɗi baki zata yi magana, Maleekh ya katse ta da cewa: ​“Amal don't waste your energy and brain to this issue, na riga da na gaya miki ainihin ni…” ​A fusace cikin ɗaga murya ta furta. ​ “Nima Harijar ce Maleekh, kwarai harija ce wacce zata iya gwabzawa da kai…” ​Maleekh zaro ido yayi yana kallonta. Itama Farha sake baki tayi tana kallonta.. ​Ammy da sauri ta sa hannu ta toshe bakinta. ​Inna ta sake baki itama tana faɗin: ​“Ahhhhh Harija dai? To gwara da kika faɗa tun wuri kar ki hallaka yaron mutane.” ​Amal ta zaro ido tare da buɗe baki. Domin ta manta akwai mutane a falon. ​Islam tana kan dining sai kunshe dariya take, ganin bazata iya jure wa ba yasa ta furzo da dariyar da ƙarfi. ​Arfat ta nufi Ammy tana faɗin: ​ “Ammy meye Harija?…” ​Ammy ta kalleta da sauri tare da faɗin “In kika zo mun nan da wannan question saina kwand'a miki mari…” ​Da sauri Amal ta waiwayo tana kallon su Ammy dake ta juya musu baya, kuma lokacin da ta sauƙo falo babu kowa. ​Da gudun gaske ta nufi Kitchen... _NEXT NEXT NEXT_ asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 95 to 96 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 ​Maleekh yana tsaye idonsa akan Farha ya ce: ​ “Lafiya kuwa?” ​Farha tana sunkuyar da kai ta ce, “Uhmm! Daman nazo ne akan batun auren…” ​ “Ya akayi ne?…” a cewar sa. ​Farha tayi shiru domin maganar gaskiya tazo ganinsa ne kawai. Juyawa tayi da gudu ta tafi. ​Maleekh ya tsaya kallon bayanta daga bisani ya fara girgiza kai. Kai tsaye Kitchen ya nufa. ​Yana shiga ya tarar da Amal tana kuka a jikin sink. ​Ya rungumeta ta bayanta yana shakar kamshin wuyanta. ​Amal ta ture shi ta matsa can wurin electric cookto. Nan ma ya bita, yana faman rirrike ta. Ta ƙara ture shi ta nufi wurin refrigerator. ​Yana zuwa wurin ya janyo ta jikinsa da ƙarfi tare da buɗe refrigerator ya ɗauki ƙaton robar zuma. Ya buɗe da bakinsa yana riƙe da shi, ɗayan hannun kuma yana riƙe da ita sosai a jikinsa. ​Nan ya fara zuba mata zuma tun daga fuskarta har zuwa wuyanta, su cikin tsakiyar breast ɗinta. ​Ya ajiye robar, ya fara lacking zumar da ya zuba mata. Haka yake lashe fuskarta duk wurin da zumar ya zuba. ​Ya zuge zip ɗin rigarta ya fara lasar ta yana haɗa wa da kissing. Ita kuwa haka take lankwashewa, tsikar jikinta yana tashi. Wani irin feeling ne yake ziyartar ta. ​Bayan ya daɗe yana mata wasa na musamman, ya juyo da ita ya haɗe musu baki wuri ɗaya. ​Haka suke ta romance 😍. ​Maleekh ya ɗago ta daga ƙasa, ya ɗora ta a saman countertop (wurin aiki na kitchen), yana rungume da ita sosai, kafafuwanta sun haɗe a bayansa. Ya ci gaba da sumbatar wuyanta da kunnuwanta, yana raɗa mata kalmomin soyayya masu daɗi cikin kunne. "Ke ce dukkan wani abu na Amal, wannan wasan ƙarya ne kawai... ke ce gaskiyata." ​Ta fara nishi a hankali, hannayenta sun shiga cikin gashin kansa, suna jawo shi kusa da ita don neman ƙarin kusanci. ​Maleekh ya matso da jikinsa sosai zuwa nata, yana tuna mata kowace daki-daki ta sha'awar da suke da ita. Ya fara wasan sarka (tracing with his fingers) a bayan wuyanta har zuwa fajarta (collarbone), yana shafar ƙirjinta a hankali a ƙarƙashin rigar. ​Ya zauna a gaban ta, yana kallon idanunta waɗanda suka riga sun rufe saboda kasala. Ya fara lasar yatsunta a hankali, yana wasa da su da harshensa kamar mai shan zuma. ​Daga nan ya miƙe tsaye yana murmushi mai zafi. Ya ɗauke ta a kafaɗarsa (fireman's carry) cikin nishi da dariya, ya fara tafiya da ita daga Kitchen zuwa falo, ya zaunar da ita akan kujera.. ​Cikin raɗaɗi da fargaban kar wani ya gansu ta fara faɗin “Maleekh! Ka barni kaga yanzu ba dare bane! Don Allah!…” ​Maleekh ya yi dariya sannan ya ce: ​ “A’a! Dole sai kin biya ni bukatuna na ƙarshe kafin na barki! Ba zan bar ki ki gudu ba! Ki biya ni fansar zumar da na zuba!” Ta ce, "to! to!! Mu koma ɗaki, nan wurin baiyi ba..." Nan ya ƙara ɗaga ta ya nufi Bedroom ɗinta da ita, dake yana ƙasin stairs.. ​Da ya isa ɗakin kwana, ya jefa ta a hankali saman gadon. Ya hau kanta yana murmushi, ya ciro robar zuma daga aljihunsa (wanda ya ɗauko daga kitchen). ​Ya fara zuba zuma a gefen jikinta irinsu cinyoyinta, hannuwanta, da kuma wurin da yake da laushi.. ​A hankali ya furta “Kina son zuma ko ni? Yanzu za ki zaɓa!” ​Amal ta kawar da kai saboda sha’awa da kunyar wasan. Ya fara lasar wuraren zumar a hankali, yana ɗan ciza ta (nibbling) don ƙara mata zafi da sha'awa har sai ta fara bukaɗa... Nan suka fara jin knocking.. Kwan..Kwann...Kwannn... "Mtsswww! Waye wannan kuma? Zai takura mana..." A cewar Maleekh. Muryar Inna suka fara ji tana faɗin "Amatu, ke Amatu fito yaranki suna kuka, tin da ke bakida hankali baki san ki neme su ba....ki fito ki ciyar dasu..." Maleekh ya ɗan haɗe rai ya ce, "shiyasa bazan iya zama anan gidan ba, gwara mu tattara mu koma can gidana, yanda ba mai takura mun..." Nan ya miƙe ya nufi waje, yana zuwa ya buɗe.. Inna ganinsa yasa ta buɗe baki tana kallonsa tare da faɗin... "Ahhhh! Ku bakwa gajiya ne? Kun kwana tare har kuka makara, yanzun ma da rana tsaka ba za ku huta ba, yooo naji tsagerun yara....ohhh Allah ya kawo mu wani zamani, mu a lokacin mu muji ma gudunsa muke, bama taɓa haɗa ido dasu balle rana tsaka a fakaice da juna..." Maleekh kuwa tinin yayi tafiyarsa ko tsaya wa ya saurara bai yi ba.. Amal ta fito ta ce, "Inna ina yarana suke?..." "Oh sai yanzu kika tuna dasu?..." A cewar Inna.. Amal ta wuce domin tasan Inna sai ta iya tara mata mutane.... Washegari Ammy ganin lokaci yana ta gabatowa yasa ta ƙira Islam.. ​Ammy ta zauna a falon ƙasa, Islam na gefenta ta fara bayyana mata tsarin aikin cikin damuwa.. ​ “Islam! Tunda Maleekh ya ce ba fashi kuma kwana biyu kacal ya rage, yanzu za mu fara shirye-shiryen nan take! Gida biyu za mu yi wa shiri... Gidan Wadata na Farha da Zayd da kuma namu gida ke da Maleekh. Muna buƙatar ƙwararrun masu aiki!” ​Islam ta firgita da yadda aka ɗauki zance kamar wasa ta ce, ​“Ammy, kwana biyu kawai? Ba zai yiwu ba! Har ma da kayan ɗaki (furnitures) da lefe! Ba za mu samu kayan da suka dace ba! Sai dai kawai ayi wa kowa guda ɗaya na gaggawa!” ​Ammy ta ja numfashi sannan ta ce, ​"Dole ne ya yiwu! Ba zai yiwu mu yarda da ƙasƙanci a gidan nan ba! Ki ƙira Aunty Fatima nan take, ita ce za ta kula da Kayan Lefe na Amarya Farha da kuma Amal domin itama a fitar da ita kunya...! Ke kuma gidansu Ango zasu shirya miki”... Ba tare da ɓata lokaci ba ​Islam ta ƙira Aunty Fatima wato ƙanwar Abbah ta fara aiki na gaggawa.. ​ Ta fara tuntuɓar manyan shaguna a Abuja don nemo kayan lefe na gaggawa waɗanda za a iya shiryawa cikin awanni 24. ​An raba kasafin kuɗi gida biyu: Lefe na Amal wanda dole ne ya zama na alfarma don rufa asiri da Lefe na Farha... ​Sun zaɓi kayan ɗaki na musamman (exclusive sets) waɗanda aka riga aka yi musu ado (pre-packaged), wanda hakan ya rage musu lokaci... ​Katin Gayyata (Invitations). Tunda babu lokaci, sun zaɓi e-invites (gayyata ta waya) na alfarma, waɗanda za a aika wa manyan mutane da kuma abokan Maleekh da Alhaji Wadata kai tsaye cikin sa'o'i. ​ An zaɓi launuka biyu na musamman, kuma an sanar da kowa cewa Maleekh da Zayd ne za su raba kayan alatu na musamman ga waɗanda za su halarci babban taron (dinner) a ranar Asabar. ​Ammy ta ɗauki nauyin manyan abubuwan da suka shafi aiki da tsaro. ​ Tunda auren zai kasance a ranar Asabar, Ammy ta zaɓi wani katafaren Hall na alfarma a Transcorp Hilton don karɓar taron dinner da ake sa ran za su zama masu yawa saboda yawan manyan mutane. ​ Ammy ta ƙira manyan masu dafa abinci guda uku (catering services) don su fara aiki dare da rana, domin shirya abinci mai tarin yawa wanda zai dace da darajar Ahali.. An tuntuɓi DPO don ƙara tsaro a harabar gidan da kuma wurin biki, domin gudun rigima.. ​Har yanzu Ammy tana cikin tsananin damuwa game da rashin zuwa Ethiopia don duba Abbah.. ​Ammy ta bayyana wa Inna da Arfat cewa: “A yanzu, kowa ya sani cewa Maleekh ya yanke shawara! Kuma dole mu nuna goyon bayanmu a fili don a rage gulma da tsegumi! Mu ne iyalai kuma dole mu rufe wa juna asiri..!” 🪸🪸🪸 A yau washegari, remain one day ɗaurin aure, Maleekh ya haɗu da Zayd akan maganar bikin, a gidansu Maleekh a yayin da suke su kaɗai a falon. ​Zayd ya bada goyon baya ɗari bisa ɗari domin yana son Islam sosai. Amma Zayd bai nuna akwai wani matsala ba. Shima Maleekh bai nuna masa wata matsala ba. Haka suka gama tattaunawa akan yanda tsarin bikin zai kasance. ​Bayan sun gama, Zayd ya tafi. ​Islam da Arfat da wasu ƙawayen Islam ne suka zo zasu fita.. ​Maleekh yana zaune shi kaɗai ya ce dasu: ​ “Ina Ammy?” ​Arfat ta ce, “Ina tunanin ta fita fa.” ​Maleekh ya jinjina kai. Suka tafi. ​Can yana daddanna wayarsa sai ga Amal ta fito daga part ɗinta. ​Ta fito falon tana riƙe da yaranta su biyu, tana zuwa ta zauna a gefen Maleekh. Ta kwantar da Ar’haan akan kujera. Tana shirin bawa Lihaam nono. ​A zabure Maleekh ya dakatar da ita: ​ “Tsaya! tsaya!! Kwananki nawa baki basu nono ba? Sai yanzu da yayi tsami zaki ciro ki d'ura musu tsamamman nono…” “To ina ruwanka?…” Ta furta tana harararsa. Ya ce, “Ni kuwa nake da ruwa, idan kika lahanta su waye da asara bayan irin wahalar da nasha kafin a same su…” Ta ce, “Iyeee! Sannu saboda kai kasha wahalar nakudar haifansu koh? To saina basu…” ​Maleekh ya taso ya zauna a kusa da ita yana faɗin: ​“Maganar gaskiya nononki yayi tsami, idan baki yadda ba bani na fara sha naji idan yayi tsami zan gaya miki idan kuma baiyi ba saiki basu… saboda kar ki sa su yi jinya…” ​Ya kai hannunsa yana ƙoƙarin jawo nonon. Ya durƙusa a gabanta ya kafa kansa akan nono yana zu'ka.. ​Sai ga Inna ta fito daga ɗakinta, idonta ya sauƙa akansu nan ta fara daka salati! ​ “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, innahu min sulaimanu wa innahu bismillahi, mai zan gani haka! Maliku, ruwan nonuwanta kake zu'kewa don mugunta? Idan ka shanye me yaran zasu sha? Nonon uwarsu ai riga kafi ne…” ​Maleekh a zabure ya miƙe yana sosa 'keya. Ya ce: ​“Ammm Inna tsaya kiji…” ​Inna ta ce, “Ba abun da zanji bayan da idona naga kana zu'ke ruwan nonuwanta…” ​Sai ga Ammy ta fito zata fita unguwa ta tarar da matsalar. ​ “Meke faruwa?” ​Inna ta furta da sauri, “Zuqe ruwan nonuwanta yake…” ​Ammy ta ce, “Waye?” “Ruwan Nonuwan Amatu…” Ta furta tana kallon Maleekh... ​Ammy ta ce, “Ina jarirai ne suke sha?” ​Inna ta kuma cewa, “Maliku ne yake zuqe mata, gungumeme dashi…” ​Ammy ta sake baki tana kallonsu cikin mamaki da kunya. ​Maleekh ya ce, “Inna to menene dan na sha, naga matata ce?” ​Inna ta ce: ​ “Kai lokacin da kake shan nonon jatumarka wa ya zuqe mata? Don mugunta irin taka idan ka zuqe mata wato nonuwanta sun kwanta kamar lagwaje, kai kuma kana shirin auran ƴar budurwa mai tsayayyun nonuwa… To bazai yu ba, don ka samu Amatu bata da wayo shine zaka mata wayo ka zuqe mata abun da take gadara da su?…” ​Ammy dai sallama tayi musu tana faɗin: “Ni na tafi saina dawo…” Tsananin kunya ne ya isheta. ​Maleekh shima da sauri ya fice. ​Inna ta kalli Amal ta ce: ​I“Ke kuma shegiya kin zauna kamar Ayu ke mai muji ko? Harijar banza in ya ɗirka miki ciki kyayi jego da dalili, ki rurruɓe, ki kyankwashe, ki zama teba. Shi kuwa yana can da amaryarsa ƴar shela…” ​Amal ta ce, “Kaii Inna kefa kina da zuzuta abu wallahi…” ​ “Dole kice ina zuzuta abu kin ban'kare masa nonuwa sai faman zuqewa yake ga jariranki a gefe kin manta dasu…” ​ “Kaiii Inna please ki daina sa ido a tsakanin mata da miji…” A cewar Amal da take shirin bawa Lihaam nono. ​Inna ta sake baki cike da mamaki ta ce, “Tooo Ayu, sarkin shiƙawa, Ayu mai muji…” ​Amal tana zaune bata ƙara tanka wa Inna ba. Inna ta gama yi ta koma ɗakinta. 🪸🪸🪸 ​Ranar Asabar, da misalin ƙarfe 9 na safe, an shirya ɗaurin aure a wannan lokacin. ​Wannan ranar ne Amal ta fi shiga tashin hankalin da bata taɓa shiga ba. Sai yau ta tabbatar da gaske Maleekh zaiyi aure. ​Tun jiya ta rufe kanta a ɗaki, sai kuka take. Daga ita sai jariranta, idan suka motsa ta basu nono, idan ta gaji ta basu madara har yau. Ba irin bugun da ba a yi a ɗakin ba, amma ta ƙi buɗewa. ​Ammy tazo tayi mata magiya akan ta buɗe, za a haɗa shagalin da ita ne kuma itama an haɗa mata lefenta na musamman da kayan furniture domin ba a nan gidan zasu cigaba da zama ba. Maleekh ya haɗa gidansa na Musamman wanda ko gidan president ma albarka... ​Misalin ƙarfe 9 an ɗaura auren Zayd da Islam, da kuma Maleekh da Farha. Amma za a haɗa shagali da na Amal kasancewar ba ƴan uwa ne suka ɗaura aurensu ba, sannan ba a yi shagalin aurensu ba. ​Misalin ƙarfe 2 bayan ɗaurin aure, Maleekh ya shigo gida. Sai da ya gaggaisa da abokai da ƴan uwa domin ya gama tsara shagalin mata biyu ne. ​Yazo har ɗakin Amal shima yaita bugawa amma ta ƙi buɗewa. Sai da ya fusata ya fara tsawar mata akan ta buɗe. ​Yayi mata barazanar idan bata buɗe ba zai ɗauki mataki akanta. ​ “Amal! Ki Buɗe Ƙofar Nan! Idan ba haka ba, zan faɗa wa kowa a nan falon cewa ke Harija ce..! Kuma zan ɗauki ƴaƴana mu tafi gidan amaryata Farha a can zan zauna, kuma ba za ki ƙara ganin wani abu na mazanta daga gare ni ba har abada..." ​Amal ta zo ta buɗe masa jin tsawar da yake daka mata, da kuma barazanar da ya shafi kayanta da yaranta da kuma mutuncinta... ​Maleekh shigowa yayi yana kallonta sannan ya kalli yaranta dake ta shan bacci a gado. Har sun yi wayo sosai. ​Ya ciro wayarsa yayi ƙira ya sanar da "come in…" ​Bayan mintuna sai ga wasu mata sun shigo su uku suna riƙe da farar rigar wedding gown da takalminsa da farin net wanda zata yafa a kanta. ​Yana kallonta yace: ​ “Ku shirya ta, bamu da isasshen lokaci… Sannan yarana suma inaso su zama abun burgewa a shagalin bikin mahaifinsu…” ​Daga nan ya fice ba tare da ya kulata ba... ​Gida an cika tamm ƴan uwa da abokan arziki. Su Aisha da ƙannenta biyu suma duk sun zo (wato ƴaƴan kishiyar Ammy), a yayin da mahaifiyarsu ta tafi can Ethiopia kula da Abbah duk da Ammy taso zuwa, bata ji daɗin zuwan Kishiyarta ba... ​Bayan sallar la'asar za a gudanar da event a babban hall ɗin da aka tanadar. ​A can ɓangaren gidan Alhaji Wadata suma sun tada babban shagali sosai. An shirya Farha cikin wedding gown itama. Ta shiga farin ciki sosai domin har ta fidda rai akan auran Maleekh saboda irin wulakancin da yayi mata a baya. Bata taɓa tunanin burinta zai cika ba. ​Shima Zayd ya cika da farin ciki sosai.. ​✨ ​Wuri ya tsaru sosai a babban hall ɗin Transcorp Hilton. Ƴan uwa da abokan arziki ne. An jera kujeru tsararru. ​Iyayen Farha duk sun haɗu. An kawo Farha an zaunar da ita a wuri na musamman da amarya da ango suke zama. Sai Islam da Zayd duk a wurin zama ɗaya. ​Maleekh bai iso ba tukun. Kowa ya hallaru. Iyakacin Maleekh da Amal ne basu iso ba, kuma su ake jira. ​Ammy da Inna duk suna nan. Itama Inna ba ƙaramin kyau tayi ba, ta sha less ɗinta mai tsada har da powderta da ɗan kwalliya akai mata. ​Ammy tana ɗauke da Lihaam a yayinda Arfat take ɗauke da Ar'haan. ​Lokaci yana ta wucewa amma ango Maleekh bai iso ba. ​Sai can wani ɗan lokaci Maleekh ya shigo yana riƙe da hannun Amal, domin da ƙyar ya shawo kanta tazo. ​Kowa ya tsaya kallonsu saboda yadda suka haɗu sosai. ​Maleekh yana sanye da manyan kaya farare da babban riga akai da hula tsararre kalar kayan da takalminsa. Sai ya fito kamar Alhaji a cikin manyan kaya. ​Ita kuma Amal tana sanye da farar wedding gown har jan ƙasa yake (kamar auren farko), an ɗora mata farin net akai ya rufe mata fuska. Da wasu mata a ta bayansu cikin ankon kaya... ​Farha tana zaune, ganin yanda Maleekh yake riƙe da hannun Amal suna taku cikin kulawa ya sa suka burgeta. Tayi tunanin inama itace a matsayin Amal, sai ta fara jin kishi kuma. ​Haka aka bisu ta tafi. ​Bayan sun haura saman hall suna facing mutanen da suke zaune a kujeru. An raba abincin da aka tsara da lemuka kala-kala, hidima ce ta musamman... ​🎶 Tsarin Shagali Mai Ɗaukar Tunani.. ​Hall ɗin ya kasu kashi biyu a wurin zama: Wadata’s Side da kuma Maleekh’s Side, wanda ya nuna haɗakar dangin biyu a yau. ​Sanda Maleekh da Amal suka taka zuwa wurin zama, an kunna wakokin soyayya na ƙasashen waje masu sanyaya zuciya, inda Maleekh ya nuna wa Amal cikakkiyar girmamawa a gaban Farha da sauran jama'a. ​Wannan shigar ta Amal cikin Wedding Gown kamar amarya ta ruɗe kowa a wurin; mutane sun kasa gane wa ce ce asalin amaryar... ​Bayan an zauna, sai aka miƙa wa Maleekh microphone don yayi jawabi. ​Maleekh ya fara da godiya, sannan ya ce: “Kamar yadda ku ka sani, yau na cika alƙawari biyu.. Na farko, na auri Farha Wadata don cika alƙawarin mahaifiyata. Na biyu, na sake ɗaura sabon aure da matata ta farko kuma Uwar ƴaƴana, Amatullah Abdulsamaad, wanda shine na farko da na ƙarshe a gare ni. Don haka, ku yi min fatan alkhairi a kan matana biyu, amma ku san cewa Amal ce ta musamman.” ​Jawabin ya firgita Farha wacce ta ji kishi, amma ya sanya Amal ta ji ƙwarin gwiwa sosai a karon farko. ​An fara rawa ta musamman inda Maleekh ya fara da Amal har tsawon minti uku, yana yi mata wasanni masu nuna ƙauna ta gaskiya a fili. ​Sannan ya je wurin Farha don rawa na minti ɗaya kacal, yana nuna mata girmamawa amma ba sha’awar soyayya ba. ​Zayd da Islam suma sun fito sun yi rawa, wanda hakan ya nuna farin cikinsu na gaskiya.. ​An raba motoci biyu a wurin shagalin a matsayin kyaututtuka. ​Maleekh ya miƙa wa Farha mabuɗin motar alfarma (Luxury Car) a matsayin kyautar aure... ​Sannan ya miƙa wa Amal wani zoben hannu mai matuƙar tsada, da kuma takardun mallakar gida (Deed of Ownership) na sabon gidan nasu na alfarma wanda ya ce shine Gidansu na Har Abada wato The Eternal Home... ​Wannan shagalin ya nuna wa kowa cewa Maleekh ya cika dukan alƙawuransa, amma kuma ya bayyana wace ce mafi daraja a wurinsa.... _NEXT NEXT NEXT_ asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 97 to 98 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 Bayan an kammala shagalin, aka fara ɗaukan hotuna. ​Maleekh da Amal aka yi musu hoto na musamman. ​Sannan aka kawo yaran suka ɗauki hoto tare, da ƴan uwa. ​Farha ma ta shiga aka ɗauka da ita. ​Nan ma aka ɗauka da Amal da Farha, ko wacce tana riƙe da yaro ɗaya sai Mijin a tsakiyarsu. ​Zayd ma da Islam an tsattsara musu hotuna na Musamman. ​Daga bisani Maleekh ya riƙe hannun Farha a yayinda take ja baya. Ya matso da ita jikinsa yana kallonta ya ce: ​ “Sauran hoto mu biyu kawai…” ​Farha ta saki murmushi. Aka ɗauki hotonsu. Haka akaita musu ​kalolin Hotuna na musamman. Kala na farko ​The Romantic Embrace, Maleekh yana rungume da Farha daga baya, hannayensa suna kewaye da ƙugunta, yayin da Farha ta jingina kanta a kafaɗarsa tana murmushi. Na biyun ​The Gazing Stare, suna fuskantar juna, Maleekh yana riƙe da haɓar Farha (chin) yana kallon idanunta da tsananin kulawa, yayin da Farha ke lumshe idanunta cike da jin daɗi. N ukun ​The Hand Kiss, Maleekh ya durƙusa ɗan kaɗan, yana sumbatar hannun Farha a hankali, yana nuna girmamawa da mallaka. Na huɗu ​The Forehead Touch, Goshinsu a haɗe, suna numfashi tare a hankali, hannayensu suna riƙe da juna. ​Amal tana daga gefe tana riƙe da Arhaan sai kallonsu take tana jin takaicin cewa, “Wai Maleekh ne yayi aure bayan ita?…” ​Maleekh yana riƙe da hannun Farha, ɗayan hannunsa a bayan ƙugunta (hips), yana mata raɗa cewa, ​ “Kar ki damu da abinda kika gani dangane da kyautar da nayi, ganin ke mota ce ita kuma gida da zobe…” ​Farha tayi saurin katse shi da cewa. ​ “A’a Ya Maleekh, ban damu ba domin ta cancanci haka, tana da matsayi a zuciyarka kuma itama haka, ta juri duk wani kalubale na soyayyarku… Sannan duba ita batada iyaye ni kuma inada su, batada kuɗi ni kuma inada kuɗaɗen da bansan adadinsu ba, kyautarka bazai ƙara mun komai daga cikin dukiyata ba to akan me zan damu? Gidaje nima inada su fa…” ​Ta matsa kusa da shi tana rage murya, ​ “Kuma a halin da Amal take ciki yanzu tana buƙatar kulawa na musamman duba da yanda bata juma sosai da haihuwa ba… tana buƙatar kulawa ita da jariranta a wurinka, wallahi tausayinta ma nake ji… kasan meye? Inda nice a matsayin Amal ba, wallahi da bazan zo shagalin bikin nan ba saboda zafin kishi na… saboda bata samu wadataccen kulawa ita da jariranta ba a wurinka kuma kazo mata da batun aure…” ​Maleekh ya ja numfashi sannan ya ce ​ “It's okay, na fahimci ban ɓata miki rai ba kuma nagode da hakan da kuma fahimtata…” ​Amal daga gefe ta rasa tattaunawar da suke domin a iya tsakaninsu suke yi. Tana cikin nazarin nan sai taji ana ƙiran wayan hannunta wanda ya kasance wayar Maleekh ne. Taga unknown number ne. Cike da mamaki ta katse kiran. ​Sai da aka kira sau uku (3), ana ukun ne ta nufi wurinsa can saman hall da yake tare da Farha. ​Tana zuwa ta ɗora hannunta akan kafaɗarsa ganin ya shagaltu sosai da hira da Farha kuma suna rungume. Ya ɗan juyo yana kallonta cike da fara'a. ​Wani irin harara ta wurga masa sannan ta ce: ​ “Idan kun gama ana ƙiranka a waya…” ​Ya karɓa. Tana shirin juyawa ta bar wurin yayi saurin riƙo hannunta. Da sauri ta juyo tana masa wani irin kallo har idonta ya rine ya koma ja. ​Cikin ƙarfin hali ta fisge hannunta daga riƙon da yayi mata. ​A lokacin MC ya miƙa mata mic akan tayi jawabi yanda take ji akan shagalin nan. Sun bayyana akan zasu fara jin daga bakin uwar gida kafin su koma kan Amarya. ​Amal bataso ba, sai da aka tilasta mata kafin ta tsaya tana fuskantar jama’a dake zazzaune. Maleekh na gefenta a yayinda Farha take ta bayan Amal tana murmushi (kamar mai jiran gado), idan Amal ta kammala ita zata maye gurbinta. ​A can gefe kuma Zayd da Islam ke tsaye su ma. Alhaji Wadata yana cikin Hall ɗin, wurin shagalin. Ya ga yadda Maleekh ya yi amfani da auren Farha don girmama Amal a fili. ​ Murmushi ne ya faɗaɗa a fuskarsa, amma murmushin mugunta.. ​Ya ji Maleekh ya yi rashin adalci a gare shi, amma kuma ya san cewa Maleekh ya ba shi dama a fili. ​Wadata ya danna call sannan ya kara a kunne, ba tare da kowa a wurin zamansa ba, domin sai da ya ja gefe tukun yayi waya. ​ “Ta fara jawabi a mic, zaku iya aiwatar da shirin, wannan ne damar da muke da shi…” ​Daga nan ya katsar da ƙiran. Wanda zasu aiwatar kuwa already sun shigo cikin hall sun saje da mutanen cikin. ​Ɗaya ne ya nufi cikin wani wuri mai sirri yanda baza a ganshi ba. Ya saita bindigarsa yana facing Amal tana nesa-nesa. ​Amal cikin hawaye ta ɗan fara jawabi. Ta karɓi makirufo tana duban Maleekh. ​Muryarta na rawa, hawaye na zuba a fuskarta ta fara faɗin. “Yau rana ce mai zafi a gare ni, kuma rana ce mai daɗi a gare ni. Zafi saboda na raba mijina da zuciyarsa da wata… Daɗi saboda na tabbatar cewa duk inda ya je, ni ce gidansa na farko da na ƙarshe… Wannan aure ya zama juna-biyu a gare ni. Sai dai Maleekh ya san cewa kowace mace tana buƙatar ƙaunataccen mijinta a gefenta. Ina roƙonku da addu’a don Allah ya sanya adalci a tsakaninmu. Kuma a matsayina na uwar gida, zan kula da dukkan matsalolin gidansa, kuma insha Allahu zamu zauna lafiya da Amaryar mu tin da har Allah ya kaddarar da anyi, Allah ya sanya alkhairi. …” ​Maleekh yana kallonta yana murmushi don nuna wa jama’a cewa yana goyon bayanta, still ya kai idonsa kan jama'a.. ​💥 ​Ƙara ƙiran wayarsa akayi da unknown number. Ya ɗaga tare da karawa a kunne. ​Ji yayi an furta: “Kana lura akwai ƴan ƙunar baƙin wake a cikin hall ɗin nan…” ​Daga nan aka katsar. ​Daga nan ya kalli Zayd dake bayansa domin yaji kamar muryarsa ne. Haɗa ido sukayi, Zayd ya masa voting da babban yatsarsa (thumb’s up) alamun dashi yayi waya . ​Maleekh ya jinjina kai daga nan ya fara baza idanu a cikin taron. ​Ya ciro black glass ɗinsa mai matuƙar tsada wanda kimaninsa zai kai 50M wanda yake ɗauke da sirrin da ba kowa ya sani ba. Nan take yake hango abu da glass ɗin (Thermal/X-ray Vision). Kuma duk saurin abu zai iya ganin tafiyarsa. ​Baiyi minti biyar da sanya glass ɗin ba kwatsam ya hango wani harsashi ya saito wurin da Amal take tsaye. ​Da sauri ya kai hannunsa ya janyota gefensa cikin hanzari kamar Spider-Man. Bullet kuwa dake da gudunsa wanda ba wanda zai iya ganinsa Maleekh yana janyo Amal, bullet ya wuce ya sauƙa a saitin ƙirjin Farha dake tana ta bayan Amal ne. ​Nan Farha ta faɗi tare da dafe ƙirjinta. ​Duk mutanen wurin ne suka mimmike suna zaro ido a rikice. ​Maleekh yayi saurin cire glass yana kallon Amal wacce take a tsorace tana kallonsa. A tunaninsa ya tsiratar da ita da harsashi. ​Jin an ambaci "Farhaaaaa…" Daga wajen jama'a ​Nan ya juya baya ya ganta a zube a ƙasa. A ruɗe yayi kanta da gudu ya durkusa tare da ɗagota ya ɗora ta akan cinyarsa. ​Amal itama zaro ido tayi ta toshe bakinta cikin ruɗani.. ​Zayd a hargitse yayo kan Kanwarsa yana furta sunanta. ​Aure ya koma tashin hankali! Maleekh ya ceci Amal, amma ya rasa Farha.. Maleekh yana riƙe da Farha a kan cinyarsa, jinin Farha na zubowa a jikinsa. Ya kasa yarda da abin da ya gani. Aiki ya kasance kan Amal, amma Farha ce ta biya sadaukarwa. ​Zayd ya durƙusa gefensa cikin ruɗani, amma Maleekh ya riga ya shiga cikin yanayin aiki na gaggawa (professional mode). ​Maleekh ya ɗago Farha da gaggawar gaske a hannayensa. ​Da ƙarfi yake faɗin “Maza ku kira motar asibiti! Kuma ku kulle hall ɗin nan! Kada wanda ya fita!!” ​Ammy da Inna suka yi tsalle cikin firgici.. ​Amal tana tsaye, jikin ta na rawa tana kallon Maleekh yana tafiya da Farha wacce yanzu ta zama jini gaba ɗaya. Cikin kuka mai zafi take faɗin "Maleekh! Maleekh!..." ​Amma Maleekh bai ko juyo ba. Ya fara gudu da ita daga saman hall zuwa ƙasa. ​Duk mutanen da ke hall ɗin sun fara ihu da gudu don tsira. ​Ammy ta rungume Amal don kwantar mata da hankali, yayin da kuma Inna ta fara addu’o’i da furuci na al’ajabi game da muguntar mutane. ​Maleekh ya fita da Farha daga hall ɗin. A halin da ake ciki, motocin Maleekh na alfarma suna nan a waje. Ya sanya Farha a cikin motar sa kai tsaye, sannan ya shiga gefen direba ya fara tuki da gudun gaske zuwa Asibiti mai zaman kansa wanda ya sani. ​Zayd da Islam da kuma wasu ƴan sanda na sirri waɗanda ke tsaron Maleekh sun bi bayansu nan take. ​Suna isa Asibiti, an kai Farha ɗakin tiyata (Emergency Surgery) nan take. ​Maleekh ya tsaya a wajen ɗakin tiyata yana duban jinin Farha da ke jikinsa, yana kallon hannunsa wanda har yanzu yana riƙe da tabon jinin Farha. Ya dafe kai cikin damuwa da haushi kan makircin da aka tsara... ​Ya san cewa harbin ba don a kashe Farha bane.. ​A zuciyarsa ya fara furta. "Alhaji Wadata! Ka nuna min cewa ba kawai kai ɗan siyasa bane, kai ne kasurgumin mai kisa... Yanzu zan nuna maka cewa ka yi kuskure!".. ​Bayan da aka harbi Farha, Alhaji Wadata ya fita daga Hall ɗin cikin ɓacin rai, yana fafatawa da mutanen da ke gudu don tsira. Ya yi hasashe cewa Amal za a harba, ba Farha ba. ​Yana isa wajen Parking Lot, ya kira mai aikin sa wanda ya harba. ​Cikin tsawa da murya mai rawa ya ke cewa “Waye ya gaya maka ka harbi ƴata? Waye?!” ​Mai Harbin ya ce, “Muna neman gafara ranka ya daɗe! Mun saita bindigar ne a kan Amal, amma Maleekh ya ɗauke ta da gaggawa… Bullet ɗin ya wuce ya kama matar da ke bayanta…” ​Wadata ya katse wayar ya jefar da ita a ƙasa. Ya shiga motarsa cikin tsananin takaici da haushin gazawa. ​Ya nufi Asibitin da aka kai Farha. ​Wadata ya isa Asibitin cikin shiga ta tashin hankali. Ya tarar da Maleekh a wajen ɗakin tiyata, har yanzu yana cikin kayan ango amma da jinin ƴarsa a jikinsa. ​Wadata ya nufo Maleekh da gaggawar gaske, ya ɗaga hannu zai mare shi. ​Maleekh ya riƙe hannun Wadata a sama da ƙarfi. Ya kalli Wadata da idanun da suka yi ja saboda haushi. ​Alhaji Wadata ya ce, “Maleekh! Ka kashe min ƴata! Ka taɓa furta cewa 'za mu yi amfani da auren don cin nasara' Sannan ka nuna rashin adalci a shagalin, yanzu kai ka jagoranci kisan kai! Me kake son aiwatar wa da Farha?” ​ Maleekh ya furta "kai ne wanda zai kashe ƴarsa domin kawai ya ga Maleekh ya mutu!” ​Zayd ya fito da sauri daga wani gefe, ya tsaya a tsakanin su, yana hana su rigima.. ​ “Daddy! Don Allah a kwantar da hankali! Yanzu ba lokacin wannan bane! Mu yi wa Farha addu'a! Maleekh, don Allah a kwantar da hankali!” ​Maleekh ya saki hannun Wadata ya ja baya. ​Alhaji Wadata Yana huci da fushi ya ce, “Maleekh! Nayi nadamar baka auren ƴata! Zan tsige ka daga dukiyarka! Zan nuna maka ainihin ni! Ba za ka yi amfani da Farha don girmama karuwar da kake aure ba!”.. ​Maleekh ya kalli Zayd, sannan ya kalli Wadata da murmushi mai zafi. ​ “A yanzu Farha matata ce! Kuma zan kasance mijinta har sai ta warke! Amma zan gano wanda ya yi wannan harbin! Kuma zan nuna maka ba kai bane ka kawo ni duniya ba, kuma ba kai bane zaka fitar da ni! ”.. 🪸🪸🪸 ​A wurin Hall, sumar Hajiya Sa’adatu biyar ana farfaɗo da ita ganin Ƴar ta aka harba. Da ƙyar ta yunkuro. Gaba ɗaya iyalai suka nufi Hospital. ​A wannan ranar a Asibiti suka kwana har da Amal. Kowa hankalinsa a tashe. Amal ma ta shiga tashin hankali sosai ganin halin da Farha take ciki, duk da har yanzu ba a basu damar ganinta ba. ​Har aka wayi gari, aka sake wuni. Sauran duk sun koma gida banda Maleekh, Zayd, Amal, da mahaifiyar Farha (Hajiya Sa’adatu). Alhaji Wadata bai zo asibitin ba domin ya shiga tashin hankali sosai kuma ta silar sa hakan ya faru. ​An tsawaita bincike sosai akan wanda ya kawo farmaki domin ba a tantance waye ba, amma Zayd ya san shirin mahaifinsa ne amma ya kasa faɗi sai kuka. ​Maleekh ya tambaye shi akan ya sanar masa waye, domin ai shi ya kira ya sanar cewa akwai ƴan ƙunar baƙin wake. Amma Zayd ya kasa faɗi... ​Maleekh ya dafa kafaɗarsa yana faɗin “Zayd! Ka daina ɓoye min! Ka kira ni a waya! Waye ya aikata wannan? Muryarka ce na ji! Don Allah ka gaya min kafin na ɗauki mataki marar kyau!”.. ​Zayd yana jujjuyawa cikin kuka, yana ta ƙoƙarin magana amma bakinsa ya ƙi buɗewa, “Ni-ni… wallahi ni… ban sani ba… ba zan iya…” Ya kama kansa cikin zafi...Yana jijjigawa. ​Maleekh ya furta yana kallonsa. “Ka tuna! Na san layar rufe baki ne a kan ka! Ka yi ƙoƙari ka kashe shi! Waye ya harbi Farha?!” ​Zayd Ya dafe kirjinsa, idanunsa na nuna tsananin zafi na rashin iya magana. “Aure… Aure ya ci nasara… Farha… ita ta sani… ” Ya faɗi ƙasi yana tari... ​Maleekh ya haƙura da tambayarsa duk da yana zargin mahaifinsu ne ɗari bisa ɗari. Maleekh ya kudirta cewa: “Koma waye asirinsa zai tonu…” ​A daren yau an bada izinin ganin Farha, an fito da ita daga ɗakin tiyata. An kaita wani ɗaki na musamman. ​Bayan sun shiga: Maleekh, Zayd, Amal, Hajiya Sa’adatu, da Alhaji Wadata da Alhaji Gusau sun zo a wannan lokacin. Ammy da Inna dasu Islam da sauran ƴan uwa da suka zo biki duk an hallara a ɗakin Farha. ​Farha ta farfaɗo ba abunda take sai kuka. Ta kasa yin magana da kowa. ​Mahaifiyarta (Hajiya Sa’adatu) ce ta zauna a bakin gadon tana rarrashinta, amma Farha sai ta fizge hannunta daga na uwar. ​Cikin sanyin murya take faɗin “Ku tafi! Bana buƙatar kowa, ku tafi!” ​Hajiya Sa’adatu ta ce, “Farha kinga…” ​Farha ta katse ta da cewa, “Bana son ganinki! Ki fita!” ​Ba yanda ta iya haka ta fita. Alhaji Wadata yazo zaiyi mata magana, ta ce: ​“Kar ka mun magana! Bana son jin muryarka! Daga yanzu har zuwa ƙarshen numfashina bana buƙatar ka!” ​Alhaji Gusau ya ja Alhaji Wadata suka fita. Haka kowa ya fita domin tana buƙatar hutawa. ​A daren nan iya su uku kawai suka kasance a ɗakin Farha: Maleekh, Amal, da Zayd. ​Farha ta ɗago hannu tana shirin yiwa Maleekh magana. Da sauri ya riƙe hannun yana ɗan shashshafa mata. Ta sa ɗayan hannun ta buɗe tafin hannunsa ta ajiye masa mic ɗin da ya sanya mata. Wanda ya gano sirrinsu da shi. ​Maleekh ya ɗago yana kallon Zayd ya ce, “Ga Amal ka kaita gida please, zan zauna da Farha…” ​Amal ta ce cikin kuka. “A’a ka bari zan zauna da ita, tinda mace ce duk abinda take buƙata zanyi mata…” ​Maleekh ya girgiza kai ya ce: ​“Ki je ki kula da yara kawai, Zayd ku tafi…” ​Amal ta juya, suna shirin tafiya sai sukaji an ƙira wayar Maleekh, Ya ɗaga. Jami’ai sun sanar dashi akan cewa an kama waɗanda suka kai farmaki. ​ “Okay ina zuwa yanzu…” Abin da Maleekh ya furta kenam. ​Ya kalli Amal ya ce: “Ki zauna da ita…” Ya ce da Zayd: “Mu tafi…” Nan suka fita.. ​Amal ta zauna a kujerar jikin gado ta ce, “Sannu Farha, ya jikin nakin?…” ​Farha idonta akan Amal cikin sanyayye murya ta ce: ​ “Amal dan Allah ki yafe ni, na miki abubuwa da dama a baya, kuma lokacin da zan tafi ya gabato, nasan bazan cigaba da rayuwa a doron duniya ba, ki yafe mun…” ​Amal ta riƙe hannunta da yayi sanyi sosai tana tayata hawaye da cewa: ​ “Na yafe miki Farha, tun a baya na yafe miki, kuma insha Allahu zaki cigaba da rayuwa damu, kuma na fahimci cewa wannan harin ani aka kawo sai kuma ya same ki, ban so Maleekh ya janye ni ba domin da yanzu kina cikin lafiya da burin cigaba da mijinki, kiyi haƙuri…” ​Farha ta ce, “Kar ki damu, Allah daman ya rigada ya rubuta hakan, idan Allah ya kare bawansa ba wannan ya isa yayi masa komai, don haka kina daga cikin kariyar Ubangiji domin Allah ya dubi maraicinki sannan ki cigaba da kula da yaranki…” ​Farha ta ja dogon numfashi ta ci gaba da faɗin ​ “Waɗanda suke son ɗaukan rayuwarki ba ƙananan azzalumai bane, kuma su ɗin ba wasu bane face iyayena… Suna son ganin bayanki Amal saboda su suka kashe miki iyaye…” ​Amal ta ji wani abu kamar daga sama, tana kallon Farha ido cike da hawaye. ​Ta cigaba da faɗin “Nasan bazaki ji daɗi ba, to amma ya zakiyi kina tare da manyan makiyanki, wanda kike tunani ba shi bane, Abban Maleekh mutumin kirki ne, bashida hannu ko masaniya akan mutuwar iyayenki, sharri aka ɗaura masa…” ​Ta ci gaba da tona asiri.. ​“A lokacin da za a kashe iyayenki, an tilasta wa mahaifinki akan ya sanar cewa Abban Maleekh ne ya kashe su, idan baiyi haka ba to anyi barazana da za a kashe ki da mahaifiyarki hakan yasa yayi haka… daga baya kuma suka aikawatar da kisan.... ​To mahaifina ne da abokinsa Alhaji Gusau sai kuma daga baya Mahaifiyata taji labari itana ta rufa musu asiri… kuma take goyon bayansu… Amal Maleekh ya gano hakan kuma akwai shirin da yake son aiwatarwa dalilin da yasa yaso aurena kenan…” ​Ta bayyana dabarar Maleekh. ​ “Yana so ya ɗauke ni daga gaban iyayena yanda idona bazai ga abinda zai aiwatar ba, sannan yana son aure na saboda mummunan ƙudurin da iyayena suke shiryawa… Nasan zakiji kamar almara amma gaskiya nake gaya miki…” ​ “Maleekh yasan gaskiya ta hanyar dasa mun mic a cikin sumar gashina ba tare da na sani ba, iyayena suna yawan magana a gabanmu ni da Yaya Zayd abinda ya shafi sirrin nan saboda suna ganin sun rufe mana baki ta hanyar asiri, bazamu iya sanar da wani sirrinsu ba, ta hanyar nan Maleekh ya saurari komai ta mic da ya dasa mun…" ​ “Na gano haka lokacin da nake gyaran gashina, na ciro na gani kuma na tuna lokacin da ya sanya mun, a lokacin naji daɗin hakan sosai na ƙara maidawa cikin gashina, daga lokacin nake yawan zama a cikin iyayena sannan ni zanta janyo maganar da zaisa suyi ta maganganu akai suna faɗan abubuwa da yawa da ya shafi rayuwarsu da kuma ƙudirinsu sannan su suka tura a kone asibitin da Abbah yake ciki har aka ɗora miki laifin hakan…” ​Daga nan Farha ta fara jan numfashi da ƙyar. ​Amal ba abinda take sai kuka tana riƙe da hannun Farha. ​ “Jikina ya ɗau zafi da sanyi…” a cewar Farha tana numfashi sama-sama.. ​Amal ta tashi a zabure ta ninka mata mayafi. ​Farha ta ce, “Ƙafata ciwo suke…” ​Amal ta je saitin sawayenta ta fara mata tausa a hankali tana kuka. Taji ƙafar ta ɗau sanyi sosai kamar kankara. ​Amal ta daɗe tana ɗan tattausa mata Ƙafar daga bisani Farha ta ce: “Ya isa haka kizo ki huta…” ​Amal ta zo ta zauna tana riƙe da hannun Farha tana mata wasa da hannu. Har dare ya tsala sosai sai da Amal ta tabbatar da Farha ta fara bacci kafin itama ta kifar da kanta a bakin gado hannunta riƙe da na Farha. Ba jumawa bacci ya ɗauke ta itama.. ​Asirin shekaru ashirin ya tonu! Abokan gaba sune iyayen Farha. Maleekh ya riga ya kama ƴan farmakin da suka harba Farha, kuma zai yi amfani da su don tonawa Wadata asiri.. Da misalin tsakar dare, Maleekh da Zayd suka isa Ofishin ‘Yan Sanda inda aka ajiye waɗanda suka kai farmaki (ƴan ƙunar baƙin wake). An yi wa mutanen dukan tsiya kafin Maleekh ya iso. ​Maleekh ya shiga cikin ɗakin tambayoyi. Ganin waɗanda suka harbi matarsa Farha, Maleekh ya cika da fushi da damuwa game da rayuwar Farha.. ​Da murya mai ƙarfin tsoro da azaba ya ke faɗin “Ku gaya mun wa ya aiko ku! Da sunan waye kuke aiki?!” ​Masu laifin sun yi ƙoƙarin ɓoye sunan Wadata, amma Maleekh bai yarda ba. Ya ɗauki wani ƙaton ƙarfe, ya fara dukan su ba tare da tausayi ba... ​ “Ku faɗa! Ko zan tabbatar da cewa wannan dare shine na ƙarshe a rayuwarku!” ​Maleekh ya ci gaba da dukansu har sai da jini ya fara tsiyaya daga jikinsu. A ƙarshe, ɗaya daga cikinsu ya faɗi gaskiya a tsorace. ​“Mu na roƙonka, Ranka ya daɗe! Alhaji Wadata ne! Shi ya umarce mu! Amal ya ce mu harba, ba Farha ba!” ​Maleekh ya daina dukan su, yana haki breathing heavily cikin fushi. A wannan lokacin, Zayd ya shigo ɗakin tambayoyi. Gaskiyar da Farha ta faɗa wa Amal, yanzu ta raunana layan rufe baki da ke kan Zayd da Inna.. ​Zayd ya kalli Maleekh da idanu cike da hawaye da kuma tuna baya.. ​Zayd murya cikin tsawa kamar an cire katanga a makogwaronsa. “Ni zan faɗa maka! Daddy ne! Gaskiya ne! Shine! Shine makiyinmu duka!” ​Maleekh da DPO wanda ke gefe yana sauraro sun zaro ido suna kallon Zayd cikin mamaki da firgici. ​Maleekh ya ce, “Zayd! Wane ne Daddy?.." Nan Zayd ya gaya musu komai game da mahaifinsa da abokinsa Alhaji Gusau.. Already Maleekh ya san da hakan kawai ya nuna bai sani bane saboda a samu hujjoji.. ​DPO ya tsaya mutum-mutumi, yana jin gaskiyar da ta girgiza shi fiye da harbin bindiga... ​DPO ya kalli Maleekh sannan ya ce, “Malik, a kwantar da hankali! Ku rubuta duk wannan a takarda! Wannan shaida ce mai ƙarfi! Zayd, zo ka rubuta duk abin da ka sani! Yanzu za mu damƙe Alhaji Wadata da Alhaji Gusau nan take!” ​Zayd ya shiga rubuta dukkanin sirrin da aka rufe a kansa na shekaru da yawa. Maleekh ya bar wa DPO waɗanda suka harba don su ci gaba da aiki, amma zuciyarsa ta riga ta koma Asibiti inda Farha ke kwance. Maleekh da Zayd basu bar wurin jami’an ba sai dab da asuba. Suka nufi asibiti kai tsaye domin Maleekh yana fargaban kasancewar Amal a wuri ita kaɗai saboda neman rayuwarta da ake yi, kuma masu son kasheta zasu iya binta asibiti domin suga bayanta.. ​Haka yake ta tunani a tsorace. Basu wuce ko ina ba sai asibiti. ​Da gudu Maleekh ya sauƙa a mota ya nufi cikin Hospital. Zayd a bayansa. Suna isa suka tura ƙofar suka shiga. Daidai lokacin ake ta kiraye-kirayen sallar asuba.. ​Ganin Amal tana kwance da kanta a kan gadon da Farha take kai, tana shan bacci. ​Maleekh ne ya zauna a bakin gadon yana shafa sumar kan Amal da ke bacci. Sannan ya maida idonsa kan Farha wacce itama idonta a rufe suke. Yasa hannu yana shafa mata fuska cikin kulawa... ​Zayd yana tsaye ya sau murmushi tare da faɗin “Yanzu fa duk waɗannan zafafan matan matanka ne koh?” ​Maleekh ya furta “Uhmmm!” ​Zayd ya cigaba da faɗin “Allah sarki masoyiyata da yanzu muna tare a ɗaki ɗaya…” ​Maleekh ya ce, “Yanzun ma zaka iya zuwa ka sameta ai…” ​Ya ce, “A’a kamm! Shalelen ƙanwata tana cikin wannan halin ina zan samu ƙarfin zuciyar aiwatar da wani abu…” ​Maleekh ya sau murmushi yana kallon Fuskar Farha. ​Can sai ga Doctor ya shigo sanye da glass ɗinsa. Ya musu sallama suka gaisa. ​Doctor ya sanar musu “Yanzu na dawo daga masallaci nasan bakuyi sallah ba, ku je akwai masallacin da basu shiga sallah ba yanzu anan kusa…” ​Maleekh ya furta. “Shikenan Doctor amma ya jikin marar lafiya?…” ​Doctor ya ce, “Normal jikinta, amma bari na ƙara dubata ko akwai wani abun da za a mata…” ​Doctor ya ɗora mata stethoscope (abin gwada numfashi) a saitin kirjinta. ​Yana gwadawa nan Doctor ya dube su a ruɗe ganin akwai abun da ba daidai ba. Maleekh da Zayd ganin yanayin Doctor suka zuba masa ido. ​Doctor ya gama gwada ta, yaji ba numfashi. Da sauri ya kalli wurin computer da yake nuna mutum yana numfashi ko ya mutu. Nan yaga ya nuna line mai tsayi (flatline). ​Doctor a tsorace ya cire abun kunnen yana salati. ​Zayd a tsorace ya furta. “Lafiya Doctor?…” ​Maleekh kuwa ba bakin magana ganin yanda Doctor ya zama. ​A hankali Doctor ya furta: ​“Allah ya yi mata rasuwa…” ​Wani irin hajijiya ne ya d'ebi Maleekh sauran kaɗan ya faɗi. Kawai ya dafe jikin bango. ​Zayd hannu ya ɗora a kai yana faɗin.. “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un…” _NEXT NEXT NEXT_ asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* *AMAL AND MALEEKH* Together, they stand between love and loyalty, between public duty and private longing, two hearts bound by fate, yet tested by truth. *Writing and Storytelling By* Asma'u Muhammad Auwal Asmeetah writer *HASKEN JAJIRTATTU* *MARUBUCIYAR:* *Matar Damisa* *My Enemy* *Hasken Ruhi* *And know AMALEEKH* Bauchi State Nigeria. *WhatsApp 09065443871* Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_. "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ BOOK ONE page 99 to 100 🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 ​Maleekh yana jingine da bango, jikin sa na rawa saboda abin mamaki da raɗaɗin rasuwar Farha. Zayd kuma ya fita daga ɗakin, ya tsuguna a bakin ƙofar shiga ya kifar da kai yana kuka. ​Amal tana kan bakin gado, hannunta riƙe da na Farha. A hankali ta fara motsi, tana shirin tashi daga baccin ta na gajiya. ​Ta ɗan murmusa tana tunanin ko Maleekh ya dawo.. ​Amal ta ji sanyi a hannun da take riƙe da shi. Ta so zame hannunta don miƙewa ganin ɗan haske alamun asuba tana son yin sallah, amma hannun Farha na riƙe da hannun. Ta sake janyowa, amma Farha ta kankame hannunta da ƙarfi kamar tana riƙe da wani abu mai daraja wanda take son kare shi kafin ta tafi. ​Amal ta buɗe idon ta gaba ɗaya. Ta kalli Maleekh da ke jingine da bango, da kuma Doctor da ke tsaye kusa da gadon, dukkanin su cikin yanayin tashin hankali da baƙin ciki. ​Sai ta kalli fuskar Farha wacce ke da alamun nutsuwa, amma launinta ya canza zuwa fari fat. Hannun Farha kuma ya yi sanyi sosai kamar kankara. "Ya Maleekh meke faruwa ne?.." A hankali ya furta "ta rasu.." A razane ta buɗe ido sosai tana kallonsa, sai dai numfashinta ya ɗan tsaya kafin ta waigo ta kalli fuskar Farha.. Hannu tasa tana ɗan bubbuganta tana ambaton sunanta "Farha! Farha!! Farha ki tashi mana nasan bacci kike yi..." Doctor ya ce "ta riga ta rasu fa, taya zata amsa miki.." "Innalillahi wa inna ilaihi raji’un " abun da Amal ta iya furta wa kenam. Can tana ƙoƙarin barin wurin tana kuka sai kuma taji still hannun Farha na riƙe da hannunta.. Tana kuka tana ƙoƙarin cire hannunta sai kuma taji abu yaci tura, abu kamar wasa ya zamo firgici, Farha ta riƙe hannunta gamm ko motsi baya yi.. Ganin alamun hannun bazai sake ta ba yasa ta fara ihu tana kuka saboda firgici da tsoro na sanin gaskiyar cewa Farha ta rasu amma kuma hannunta yaƙi rabewa da nata.. ​Wani irin Ihu mai tsananin tsoro ta sake.. “Ahhhhhh! Hannuna! Maleekh! Me ke faruwa? Hannunta yaƙi rabuwa! Nima mutuwa zan yi?!” ​Doctor ya matso da gaggawa, yana ƙoƙarin dabararsa don raba hannun Farha daga na Amal, amma hannun yaƙi sake wa. Ko da ya danna wurin, kankamewar tana nan daram. ​Maleekh ya fara gudu zuwa wurin. Ya san cewa Farha tana ƙoƙarin bayyana wani abu na ƙarshe ne. ​Ya rungume Amal yana rarrashinta duk da raɗaɗin zafin mutuwar Farha da yake ji a zuciyarsa. ​Muryarsa cike da baƙin ciki yake furta... “Shhh! Kada ki tsorata! Ba zaki mutu ba! Farha ta riga mu gidan gaskiya! Ba ta so ta sake ki ne, saboda tana son ta kare ki ne har na dawo!” ​Doctor ya ce, "Wannan kam sai dai a yanke hannun mai rai ɗin a bisine da gawar..." Amal jin haka yasa ta sakin fitsari a wurin.. Fitsari cikin baho duk ta juye shi a wurin, ga yanda jikinta yake kakkarwa gaba ɗaya ta haɗa zuffa tako ina. Idonta yayi jawur.. Maleekh dake rungume da ita yana iya jin bugun zuciyarta. Yayi akan hannun ya rabu shima ya kasa.. A lokacin ya fara tofe hannayensu da addu’a, adduoi yake ta karantowa yana tottofe hannun, bayan can ya matsa kusa da Farha, ya shafa mata goshinta a karo na ƙarshe. ​Ya raɗa mata a kunne “Nagode Farha! Na ji abin da kika yi, kuma na fahimci sadaukarwarki! Na riga na kama su! Kin cika alƙawari! Yanzu ki saki Amal! Zan kula da ita da dukkanin gaskiya da ƙarfi!” ​Bayan Maleekh ya faɗi haka, hannun Farha ya sake hannun Amal a hankali. ​Amal ta ciro hannunta da tsananin tsoro. Ta rungume Maleekh da ƙarfi tana kuka mara sauti. ​Zayd ya shigo ɗakin, jikin a sanyaye. Ya durƙusa a gaban gadon, ya ɗauki hannun Farha ya sumbace shi cikin girmamawa da baƙin ciki. Amal ta durƙusa sai kuka take domin ta ji mutuwar sosai. Haka take ta kuka ba kakkautawa. Da ƙyar Maleekh ya samu ƙarfin zuciyar ɗago ta ya rungumeta. ​Bayan nan aka sa Farha a Ambulance domin kaita gida, ba tare da an sanar wa kowa ba don hana rikici kafin a binne ta. Maleekh da Zayd da Amal sai wasu likitoci masu rakiya. Kai tsaye gidansu Maleekh suka nufa. ​A falo tuni labari ya tarwatsu. Ammy da Mahaifiyar Farha (Hajiya Sa’adatu), wacce tayi danasanin goyawa mijinta bayan aiwatar da laifi, sai Inna wacce ta gama sanar dasu gaskiyar labarin kashe iyayen Amal da akayi. ​Ammy ta girgiza sosai domin bata taɓa tsammanin Alhaji Wadata zai aiwatar da haka ba. Sai kuka take tayi. Hajiya Sa’adatu ta sanar cewa Amal akaje kashewa ba Farha ba. ​Inna tana kuka ta ce, “Yanzu rashin imanin har ya kai a kashe iyayenta sannan itama a kashe ta?!” ​Hajiya Sa’adatu tana kuka itama tana neman yafiyar Inna da kuma Allah. ​Suna cikin wannan sai suka ji ƙarar jiniya na Ambulance. A zabure suka miƙe domin sun san ba lafiya ba. Suna falo sun kasa motsawa. ​Can sai ga Maleekh ya shigo da Zayd suna ɗauke da Farha a nannade da mayafi. A kan kujera suka kwantar da ita. ​Ammy cikin kuka ta furta “Meye wannan Maleekh?…” ​Maleekh kai a sunkuye ya ce, “Ku ƙira wacce zata mata wanka a suturtata, Allah yayi mata rasuwa…” ​Ammy da Inna lokaci guda suka furta “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” Baki a haɗe. ​Hajiya Sa’adatu kam dafe kirji tayi daga nan ta faɗi sumammiya. ​Cikin awanni an sanar da rasuwar Farha a ko’ina. ​Alhaji Wadata da ke gida yana zaune yana shan tea. Aka ƙira shi a waya aka sanar dashi mutuwar ƴarsa. A lokacin kofin tea ya faɗi daga hannunsa. Ya miƙe a zabure tare da furta: “Whatttt…” ​Bayan an katsar da ƙiran a ruɗe ya ɗauki key ɗin mota kai tsaye gidansu Maleekh ya nufa domin an sanar masa tana gidan. ​Yana isa ya samu har an suturtata an fito da ita za a yi mata jana’iza. Mutane an taru sosai. Ta ko ina zuwa suke. Ta samu mutane sosai domin har daga wasu garuruwa an zo. ​Ran Alhaji Wadata ya ɓaci sosai ganin ba a sanar masa a lokacin da ta rasu ba, sai da har daga wasu garuruwa sun zo. Amma haka ya haƙura suka yi jana’izarta sannan aka kaita gidanta na gaskiya. ​Zayd kam ba bakin magana, idonsa yayi jawur domin sai da ya zauna a kabarinta ya yi mata addu’a da kuka gaba ɗaya. Da ƙyar Maleekh ya ɗago shi suka dawo gida. ​Bayan an dawo, Alhaji Wadata ne ya shiga gidan. Ya tarar da mata sun cika a babban falo. Hajiya Sa’adatu itama ta farfaɗowo amma da wani irin bala’in kuka ta tashi, ta kasa yiwa kowa magana sai kuka. ​A lokacin da Wadata ya shigo, bai dubi kowa ba ya fara maganar: ​ “Saboda rashin mutunci yarinyata ta mutu amma a kasa sanar mun a lokacin? Nine fa ubanta kuma ina gari!” ​Sai a lokacin Hajiya Sa’adatu ta miƙe tazo gabansa, kai tsaye ta ɗauki hannu ta zabga masa lafiyayyen mari! ​Alhaji Wadata yana zazzaro ido cike da mamaki yace, “Ni kika mara Sa’adatu?!” ​Hajiya Sa’adatu ta ce, “Ban taɓa marinka ba tun da nake sai yau, kuma yanzu ma idan bakayi wasa ba zan ƙara maka! Marar mutunci kawai! Wallahi nayi danasanin aurenka domin da kai da babu duk ɗaya ne, na auri mijin da zai kashe mun ƴa da hannunsa! Tirrr!” ​Mutane haka suka tsaya kallonsu cike da mamaki. ​Tana kuka tana faɗin “Allah ya isa tsakani na da kai jahili kawai!” “Sa’adatu nine jahili?!” ​Hajiya Sa’adatu ta ce, cikin kuka “Na faɗa jahili, dabba, tsinanne, ɗan jahannama!” ​Amal tana zaune tana kallonsa, ji take kamar ta tashi ta murɗe masa wuya. ​Suna cikin wannan hayaniya kawai Alhaji Wadata yaji an kwaɗa masa katako a tsakiyar kansa. ​Yana waiwayawa yaga Inna ce da katako a hannunta tana kuka. Nan ta cigaba da kwaɗa masa tana tsine masa: ​ “Allah ya isa na Wadata tsinanne! Daman ina jiran wannan ranar da farin cikinka zai ƙare har abada! Ka kashe mun ɗana ɗaya tilo da matarsa saboda rashin imani sannan kazo kana neman rayuwar jikata! To ta Allah ba taka baaa!” ​Alhaji Wadata ne ya riƙe katakon da Inna take kwaɗa masa. Inna ta rungumoshi ta fara cizonsa a ta ko ina. Haka take jan naman fatarsa da ƙarfi. Ta kama naman wuyansa ta ja da ƙarfi sai da fatar ta ɗage. ​Da ƙyar ya karɓe kansa ya ruga da gudu ya fito. A sama sama ya gaggaisa da mutanen da basu san me ke faruwa ba, da sauri ya shiga motarsa ya ja a ɗari ya tafi... Bayan kwana uku da rasuwar Farha, an gama ta'aziyya. ​Alhaji Wadata da abokinsa Alhaji Gusau suna zaune a falon gidan Wadata. Hajiya Sa’adatu da Zayd suna can gidansu Maleekh. ​Wadata da Gusau suna zaune suna shirya neman mafita domin sun san asirinsu ya tonu. Suna shirya barin ƙasar gaba ɗaya ta wata hanyar sirri. ​Sai suka ji an turo ƙofar falon ba tare da neman izini ba. Maleekh ne ya fara shigowa sai Zayd da kuma Jami’an Tsaro sanye da kayan aiki. ​Maleekh ya tsaya yana kallonsu da idanun baƙin ciki da fushi.. ​Maleekh ya furta cikin ɓacin rai “Uhmm, rana dubu ta ɓarawo, rana ɗaya ta mai kaya! Ba tare da ɓata yawun bakina ba, anzo tafiya da ku…” ​Alhaji Wadata ya ce, “Zuwa ina?…” “Kotu!” a cewar Maleekh ​Alhaji Wadata da Alhaji Gusau suka kalli juna a tsorace. ​Wani irin tsawa Maleekh ya daka musu, yana fitar da ikon iko “Ku miƙe mana!” ​Alhaji Wadata ya ce, “Kai Maleekh! Laifin me mukayi haka?…” ​Maleekh ya matso kusa da su, yana kallon su cikin kaskanci. ​**“Kar ku raina mana wayo! Laifuka da dama! ​Laifin kashe tsohon babban gwamna (Mahaifin Amal) da matarsa. ​Laifin cin dukiyarsa ta hanyar juyar da kadarori da asusu. ​Laifin ɗora wa marar laifi sharri na kisa (Alhaji Abdul-Majeed). ​Laifin kai farmaki don ɗaukan ran wacce bata ji ba bata gani ba ta hanyar hatsarin mota tun da farko. ​Sannan laifin kai mata farmakin ɗaukan ranta bayan iyayenta da ka kashe. ​Na ƙarshe, laifin kashe ɗiyar ka daka haifa a wurin shagalin bikinta, wacce ta mutu saboda rashin tausayin ka da miyyatun zuciyarka!”** ​Zayd ya ƙara da cewa: ​“Yau ranar ku ta farin ciki ya ƙare! Yau ka kashe ɗiyarka Farha, gobe kuma akaina harin zai tsaya!” ​Wasu jami’ai ne suka zo zasu sa musu handcuffs. Wadata da Gusau suka miƙe tare da dakatar da su suna so su nuna girman su. ​A fusace, Maleekh ya karɓi handcuffs ya sanya musu da kansa yana nuna mallaka da ikon fansa. Sannan ya turasu gaba da ƙarfi. ​Alhaji Gusau ne yake faɗin: “Ku tsaya, hulata!”. ​Cikin zafin rai, Maleekh ya ɗago hannu ya kai masa wani irin mari akan ƙeyarsa da ya sha askin maluuu sai sheƙi yake kamar mirror. ​Sai wani paattttt!!! Ƙarar mari mai tsanani... ​Alhaji Gusau ya durƙusa saboda zafin marin kuma goshinsa ya bugi ƙasa da ƙarfi, ga shi ƙato dashi ga tunbin ciki kamar wanda ake hurawa kullum... ​Haka aka ja su waje. Sun nemi alfarmar zasu shiga cikin motocinsu su je kotun don guje wa kaskanci, amma samm Maleekh ya ƙi amince wa. Ya sa suka hau motar ƴan sanda ta baya yanda kowa zai gansu a cikin jama’a yayin da ake wuce wa dasu... ​Bayan an kama Alhaji Wadata da Alhaji Gusau, Maleekh ya dawo gida tare da Zayd. Gidan ya cika da nutsuwa da baƙin ciki. ​Maleekh ya nufi ɗakin Amal, inda ta ke zaune tana rungume da jariranta, amma hawaye na zuba a fuskarta. Tana tunawa da furucin Farha kafin ta rasu. ​Maleekh ya zauna kusa da ita, ya ɗauki Arhaan ya rungume shi, yana shafa kan Amal a hankali. ​A hankali ya furta “Amalina... Yanzu komai ya wuce. An kama waɗanda suka aikata laifin kuma an tona asirinsu. Farha ta rasu tana mai daraja, kuma ba zata taɓa mantuwa ba.” ​Amal ta jingina kanta a kafaɗarsa tana kuka mara sauti. ​“Ya Maleekh… gaskiya ne? Iyayen Farha ne? Sune suka kashe Mamana da Baba na? Sune suka ɗora wa abbah sharri? Kuma sune suka sanya ni cikin hatsari?… Farha ta gaya min…” ​Maleekh ya ɗora ɗan yatsansa a kan leɓɓan ta don ta yi shiru. ​Ya ce, “Gaskiya ne, my love. Amma Farha jaruma ce kuma ta sanar da ke gaskiya saboda ta nuna soyayyar gaske. Ba ta so ki rayu da ƙarya. Kuma ba ta so ki mutu a hannun su. Sun shirya miki farmaki a wurin bikin... saboda sun san zaki kawo musu cikass... ​Tun farko, auren Farha dabara ce. Na sanya mata mic a cikin sumar kanta don in ji duk abin da suke shirin yi da sirrin da suke ɓoyewa. Na gano cewa layar rufe bakin da ke kan Zayd tana rage ƙarfin ta idan an faɗi gaskiya a gefe. Don haka, na saka Farha ta zama wakiliyar mu ba tare da ta sani ba, har sai da ta gano mic ɗin kuma ta yanke shawarar taimaka mana da kanta... ​Iyayen Farha sun ɗauki Abban mu a matsayin katangar kariya. Sun sani cewa idan Abba ya shiga kurkuku, ba mai neman su saboda Abba yana da ƙarfi da tasiri. Sun tilasta wa mahaifin ki ya furta cewa Abba ne ya kashe su kafin su kashe shi. Sannan Abba bai san komai ba, duk makircinsu ne..." Amal ta fashe da wani irin kuka na jin daɗi da na yafe wa kai. Ta rungume Maleekh da ƙarfi, ta ji nauyin shekaru ya sauka a kanta.. ​ “Nagode, Ya Maleekh. Ina sonka! Kuma na yafe wa Farha gaba ɗaya! Yanzu Abba kawai zan so ganin sa! Kuma zan so ka kula da Hajiya Sa’adatu saboda ta rasa ɗiyar ta kuma ta rasa mijinta ta hanyar gaskiya.” ​Maleekh ya ce, “Za mu kula da ita. Zayd yana tare da ita yanzu. Kuma yanzu da gaskiya ta fito, lokaci yayi da zan ɗauko Abbah...” Bayan Maleekh ya kwantar da hankalin ta, Ta tashi ya nufi wani side ɗin wardrobe ɗinta inda take ajiye wasu takardun... ​Ta kalli Maleekh ta furta “Ya Maleekh, kadarorin Babana da kudin gado gaba daya Alhaji Wadata ya cinye su ta hanyar juyar da sunayen bankuna da shaidun kwangila. Sai wasu ƙananan kadarori ne kawai suka rage a bankin da na canza sunan su, bayan rasuwar Farha wani ya kawo mun wai Farha ce ta bashi ajiye cewar nawa ne. Me za mu yi?” ​Maleekh ya duba takardun kadarorin da kyau. Wannan kaddarori sun haɗa da gidaje da filaye da kuma manyan asusun banki da ke da alaƙa da gwamnati da ƙasashen waje. ​Ya kuma furta, “Kada ki damu, my love. Tun kafin in tafi, na riga na tsara komai. Waɗannan ƙananan kadarori da kika canza sunan su, sune katangar kariya ta farko. Zan sanya laoyoyin mu su daskarar da dukiyar Wadata da Gusau nan take a dukkanin bankuna na gida da na waje, tare da shaidar Zayd. Kuma za mu neme su a ƙarƙashin laifin cinikin ƙasa (money laundering) da kisan kai.” “Kada ki taɓa komai har sai na dawo. Kula da yara kuma ki kwantar da hankalin ki. Gobe da asuba zan kama jirgi zuwa Ethiopia don dawo da Abbana gida. Ina sonki!” ​Maleekh ya rungume ta da ƙarfi, ya sumbaci yaran sa gaba ɗaya, sannan ya fita don kammala shirin farko. ​Maleekh ya tafi zuwa sashen Zayd inda yake tare da Hajiya Sa’adatu (Mommy) a wani babban daki. Haj. Sa’adatu ta yi kuka mai yawa don rasuwar Farha da kuma tonuwar asirin mijinta. ​Maleekh ya shiga sannan ya ce “Mommy, kar ki damu. Zayd zai kula da ke kuma ku kula da kanku. Bari inyi magana da Zayd a waje.” ​Suka fita waje. ​Maleekh ya ce, “Zayd, tuni na sanya laoyoyin mu sun fara daskarar da kadarorin Daddynka da Gusau gaba daya. Yanzu aikin ka ne ka yi magana da Mommy yadda za ta ba da haɗin kai ga DPO da kuma manyan Lauyoyin mu.” ​Zayd ya ce, “Amma Mommy tana jin tsoron gidan yari!” ​Maleekh ya ce, “Ba zata shiga gidan yari ba muddin ta ba da dukkanin takardun da Daddynka ya ɓoye da kuma takardun shaida na asirin su. Ka gaya mata ta yi hakan don ceton kan ta da kuma girmamawar Farha. Idan ta ki, ba zan iya kare ta ba a gaban shari’a.” ​Zayd ya koma falon, ya yi doguwar magana da Mommy. Bayan awa ɗaya, Mammy ta yarda! ​Zayd ya kira Maleekh a waya. ​“Ta yarda! Ta gaya min inda Daddy ya ɓoye dukkanin kadarorin Gwamna da kuma makudan kuɗi da ya ciyo ta hanyar siya da sayarwa. Ta kuma gaya min sunayen bankuna da kamfanoni da ke ƙasashen waje.” ​Maleekh ya ce, “Haka nake son ji! Yanzu zan kira DPO ya zo da Lauyoyin mu kai tsaye! Ka kiyaye da Mammy har sai na dawo! Sannan ku shirya sirrukan domin su zama shaida a kotu na gobe! Sai na dawo.” ​Maleekh ya kira DPO jami'in ‘yan sanda ya gaya masa dukkanin shaidun da Mommy ta bayar, kuma DPO ya zo tare da lauyoyi don kama kadarorin nan take. ​Yayin da Maleekh ke shirya jirginsa na Ethiopia, a kotun babban birnin tarayya, an gabatar da Alhaji Wadata da Alhaji Gusau gaban babban alkali. ​Wadata da Gusau sun shigo sanye da ancuffs a hannunsu, kuma jama’a sun cika kotun. ​Lauyoyin Maleekh da DPO sun gabatar da shaida ta farko ga alkali. ​Lauyan Gwamnati ya ce, “Mai girma Alkali! Muna gabatar da su a gaban kotun ka a kan laifukan kashe-kashe ciki har da na Gwamna da Matarsa da kuma na Farha, cin dukiyar Gwamnati, cinikin ƙasa (money laundering), kuma ɗora wa mutumin ƙwarai sharri (wato Alhaji Abdul-Majeed).” ​Wadata da Gusau sun yi ƙoƙarin musantawa da nuna iko, amma hannun jami’ai ya dannesu. ​Alkali Cikin zafin rai, bayan ya karanta shaidar da ke cike da sunan Maleekh da Farha da Zayd da kuma Sa’adatu “An tabbatar da cewa akwai shaidu masu ƙarfi da kuma haɗin kai daga waɗanda suke kusa da ku. Wannan kotu ta yanke hukuncin tsare ku a gidan gyara halin na musamman (maximum security prison) har sai an kammala bincike!” ​Wadata ya kalli Gusau da ido cike da tsoro da baƙin ciki. Sun san cewa sun faɗi a wani rami da Maleekh ya haƙa musu. ​An fitar da su daga kotu cikin kaskanci, inda aka sanya su a motar yansanda ta baya a gaban mutane da talabijin yanda kowa zai gansu. Maleekh ya nufi Ethiopia a jirginsa mai zaman kansa (private jet). Ya isa asibitin da ke Ethiopia inda Abban sa (Alhaji Abdul-Majeed) yake kwance. ​Maleekh ya tarar da Abbansa ya farfaɗo daga doguwar sumar da ya shiga. Yana iya aiki sosai da jikinsa amma sai dai tafiya tana ɗan masa wahala kuma yana saurin gajiya saboda yana fama da hawan jini (hypertension) da kuma mummunar rauni na zuciya da ya shiga... ​Alhaji Abdul-Majeed Muryarsa a ɗan raunane, ya ce, “Maleekh! Na san ba ka ci amanata ba wurin kula da Amatu! Na san gaskiya za ta yi nasara! Ina jinjina maka ɗana!” ​Maleekh ya furta. “Haba Abba! Ai gaskiya ta fito! Yanzu Wadata da Gusau suna hannu! Kuma kotu tana buƙatar ka don share sunanka a filin siyasa! A yau zamu tafi.” ​Kasancewar kotu tana buƙatar ganin Abbah, hakan yasa aka bashi keken zama (wheelchair), irin wanda ake tura waɗanda basa iya tafiya. Likita ya ba su takardar shaidar lafiya da kuma izinin tafiya. ​Bayan ƴan awanni a sama, Maleekh da Abba sun dawo gida. Kowa yayi farin cikin dawowar Abbah ciki lafiya. ​A falon gida, Islam da Arfat suka rungumi Abbah suna kuka da murna. ​Amal ta kasa fitowa saboda kunyar haɗa ido take da Abbah saboda yardar da tayi akan shi ya kashe iyayenta tun da farko. ​Alhaji Abdul-Majeed yana zaune a keken sa na zama, kuma ƴan biyu Arhaan da Lihaam Abbah yana riƙe dasu da hannu biyu. Abbah ya ce, “Ina daughter take? Ina Amal? Ku kira min ita yarinya mai juriya!” ​Kowa sai zuwa yake yana gaishe da Abbah. ​Abbah ma yaji mutuwar Farha sosai ya shiga baƙin ciki, sannan ya sha mamakin jin abin da su Alhaji Wadata suka aikata. ​Maleekh ne ya samu Amal a ɗaki, ya rungumeta daga bayanta. ​ Yana faɗin “Ƙaunata, me kike yi a nan? Abba yana son ganinki! Yana son ki fito yaga daughtersa!” ​Amal ta ce, “Kunyarsa nake ji, Ya Maleekh! Ban san me zan ce masa ba! Na zarge shi akan abun da bai aikata ba! Na yi masa laifin da ba zan taɓa mantawa ba! Bana so in fita.” ​Maleekh ya furta. “Bai san kinyi masa haka ba Amal. Ba ya ganin laifin ki! Yana ganin jahilcin makiya ne! Ki fito don farin cikin sa! Sannan don ki girmama shi!” ​Maleekh ya rarrasheta ya bata baki akan ta fito kar taji komai. Ya ɗago fuskarta ya fara shafa mata leɓenta a hankali. ​ “Ki yarda dani, idan kika fito kin nuna tsarki na zuciya! Ki nuna wa Abba cewa yar sa ce ke! I Love You.” Maleekh ya sumbace ta da doguwar sumba wacce ta kwashe duk wani tsoro da kunya a zuciyar Amal. Suka rungume juna da ƙarfi, Maleekh ya bar numfashinsa a jikinta har sai da ta tuna da abubuwan farin ciki da suka faru a baya. Daga nan ya riko hannunta suka fita falon. ​Suna fitowa, Abbah yana kallon ƙofar da murmushi. Ganin Maleekh da Amal sun fito hannu da hannu, ya miƙe duk da wahalar tafiyar, ya ajiye ƴan biyu a kan cinyar Ammy. ​Amal ta gane irin halin da Abbah yake ciki. Ta yi gaggawa ta durƙusa a gabansa da hawaye na gaske.. ​Cikin kuka mai zafi take faɗin “Abbah! Don Allah ka yafe ni! Nayi maka mugun laifi! Na zarge ka akan abinda baka aikata ba! Ka yafe ni! Ina rokonka alfarma!” ​Abbah ya ɗago ta da ƙarfi, ya rungumeta a jikinsa yana faɗin. “Ban taɓa ɗaukar ki a matsayin mai laifi ba! Ke jaruma ce! Ke ƴata ce! Kuma Maleekh ya cika alƙawari! Na yafe miki tun da farko! Yanzu ki daina kuka kuma ki kula da Maleekh da zuriyar ku!..” NEXT NEXT NEXT asmeetahwriter✍️ *🎤AMALEEKH🎤* Asmeetah writer Follow my channel 👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VbBCNlqJUM2RQwWncg43 Anan ne labarin Amaleekh ya kawo ƙarshensa. Nagode da kasancewarki/ka a wannan tafiya tun daga farkonta har zuwa nan. Wasu labarai ba sa ƙarewa a shafi na ƙarshe; suna ci gaba ne a cikin zuciyar mai karatu. — END OF AMALEEKH — Nagode da karantawa. 101 to 102 An shirya zaman kotu na biyu don yanke hukunci a kan Alhaji Wadata da Alhaji Gusau. An ɗauki matakan tsaro masu ƙarfi. ​ Abbah ya zo a kekensa na zama tare da Ammy da Maleekh a gefensa. Zayd da Hajiya Sa’adatu sun kasance a gefen Lauyoyin Gwamnati domin bada hujjoji a kan su Wadata da Gusau. Amal tana nan itama sai Islam da Arfat da suke riƙe da ƴan biyu (Arhaan da Liiham)... ​Zayd ya yi doguwar shaida mai raɗaɗi game da shigar da aka yi masa da kuma laifin iyayensa. Hajiya Sa’adatu kuma ta fallasa dukkanin takardun da Wadata ya ɓoye game da kadarorin Gwamna da kuma yadda aka yi kisan kai. ​Alkali ya yanke hukunci, bayan ya saurari dukkanin ɓangarorin: ​Hukuncin alƙali shine. “Saboda kisan kai da aka yi wa Gwamna da matarsa, da kisan kai na Farha, da kuma cin dukiyar al'umma, wannan kotu ta yanke hukuncin zama gidan yari na tsawon shekara 10 ga Alhaji Wadata da Alhaji Gusau, kafin a sake nazari a kan hukuncin da ya dace dasu a matsayinsu na masheƙa!” ​An yi ihun murna a gefe. ​Bayan an fito daga zama kotu, yayin da ake kama su Wadata da Gusau don a kai su gidan yari.. ​Alhaji Gusau ya tsaya a kusan Amal da wani ɗan sanda yana riƙe dashi. Gusau yana mata wani dariya na izgilanci tare da faɗin: ​“Indai kuɗi na aiki to nan da sati biyu zaki ganmu muna yawo a gari a cikin maka-makan motocinmu… Iyayenki mu muka kashe su har lahira! Mahaifiyarki bayan mun sumar da ita muka sa bindiga muka fasa mata ƙwaƙwalwa! Sannan mahaifinki yana ihu a cikin wuta yana neman taimako babu! Har wuta yayi ƙurmus da shi sai ƙwarangwal ɗinsa! Hahahahhh…” ​Amal ta tsaya mutum-mutumi, zuciyarta ta daina bugawa saboda tsananin zafin maganar da ya yi mata. Daga nan ɗan sandan ya ja shi da ƙarfi ganin zai ɓata musu lokaci. ​Amal tana kuka cikin fushi da damuwa. Ba tare da tunani ba, ta saka hannunta a aljihun wani Police da ke kusa da ita ta ciro ƙaramin bindiga (gun). ​Ta saita Alhaji Gusau da hannu bibbiyu take riƙe da bindigar. ​Ta fara harbi! Bullet bai sauƙa a ko ina ba sai a bayan Alh. Gusau. Haka take ta jero harbi a jejjere kafin a dakatar da ita. ​Har ta harba masa harsashi sun yi biyar a jikinsa: ​Wannan bullet a bayan ƙeyarsa. ​Wannan a wuyansa. ​Wannan a bayansa ta saitin tumbinsa. ​Da sauran biyu. ​Maleekh da gudu ya nufo kanta da wasu ƴan sanda. Da sauri aka karɓe bindigar a hannunta. ​Ta faɗa saman ƙirjin Maleekh tana kuka mai tsananin gaske. Daga nan ta zame ƙasa ta kafa gwiwowinta ta shiga tsananin gigita. ​Nan take ƴan jarida har sun mamaye wurin suna ɗaukar hotuna da bidiyo na wannan mummunan yanayi na kisan kai a kofar kotu. ​Shi kuwa Alhaji Gusau har ya gama shure-shurensa ya mutu nan take.. ​Abbah da Ammy da Inna kowa ya tsorata ganin yanda Amal ta ɗauki hukunci a hannunta.. ​An gama da Alhaji Gusau ta hanyar ɗaukar fansa kai tsaye daga Amal. Bayan Amal ta faɗi ƙasa cikin gigita bayan ta kashe Alhaji Gusau a gaban kotu, Maleekh ya rungume ta da ƙarfi. Jami’an tsaro sun kewaye su, kuma ‘yan jarida sun yi rikici wajen ɗaukar hotuna na wannan abin al’ajabi da ya faru. ​An kama Amal nan take saboda kisan kai a fili. A take aka yanke hukuncin kaita gidan gyaran hali itama amma kafin suyi hakan Maleekh ya shiga tsakani tare da Lauyoyinsa masu daraja... ​Maleekh ya rungume ta sosai yana faɗin “Ba za ku iya tafiya da ita ba! Wannan kisan kai ne na kare kai (self-defense) saboda Gusau ya tsoratar da ita da maganganun wulakanci da kisan iyayenta! Zuciyarta ta buga saboda tsananin zafin da ya faɗa! Lauyoyina suna nan kuma za mu yi garanti na beli nan take! Ba zata shiga kurkuku ba!” ​Lauyoyin Maleekh sun yi gaggawa suka yi amfani da hujjoji na cewa Amal ta kasance wacce aka zalunta kuma tabbataccen bayanin kisan da Gusau ya bayar a gaban ta ya haifar mata da gigita ta kwakwalwa (acute psychological trauma), wanda ya sa ta rasa ikon sarrafa kanta. ​An kafa shari’a ta gaggawa don Amal a kan kisan kai. ​A zauren shari’a, Maleekh da Lauyoyinsa sun yi bincike mai zurfi a kan laifukan Gusau da kuma yanayin taɓin hankali da Amal take ciki. ​Lauyan Maleekh ya gabatar da hujjoji guda uku: ​Laifin Gusau, ya tabbatar da cewa shi ne ya kashe iyayen Amal a gaban ta, wanda ya haifar mata da tsananin zafin zuciya. ​Kare Rayuwa, Amal ta ga bindiga kuma ta ɗauka cewa Gusau yana shirin kashe ta... ​Shaidar Likita, Likitan Maleekh ya tabbatar da cewa Amal tana cikin mummunan tashin hankali tun daga rasuwar Farha da kuma gaskiyar da ta ji. ​Alkali ya yanke hukunci: ​ “Duba da laifukan da aka tabbatar na mamacin Alh. Gusau, da kuma hujjojin taɓin hankali da aka kawo na Amal, wannan kotu ba za ta yanke mata hukuncin ɗauri ba... ​Amma dole a yi hukunci saboda an aikata kisan kai a fili. Wannan kotu ta umarci Amal ta shiga cikin kulawar likita (psychological rehabilitation) na tsawon shekara biyu..." ​Maleekh ya yi murna sosai. Ya ceto matarsa daga shiga kurkuku. An daskare dukiyar Wadata, kuma an tabbatar da cewa Wadata zai rayu a gidan yari har abada. ​An kammala shari’a! An gyara wa Alhaji Abdul-majeed sunan sa, an dawo da kadarorin Amal gaba ɗaya, kuma Hajiya Sa’adatu ta yi nadama ta cigaba da zama a gidan Abbah har Allah ya fito mata da miji nagari tunda ba wuce aure tayi ba.. ​Bayan shekara biyu na kulawa da likitoci, Amal ta warke gaba ɗaya daga raunin zuciya. ​Maleekh da Amal sun ci gaba da rayuwa cikin farin ciki da soyayya. Suna kula da yaran su. Suna yawaita ziyartar kabarin Farha don girmama sadaukarwar ta. Yanzu shekaru sun shuɗe. Maleekh da Amal da yaransu Arhaan da Lihaam sun koma gidansu na Maleekh na kansa. Yara sun girma suna da shekara uku-uku yanzu, suna zuwa makaranta cikin gata da kuɗin uba da na uwa... ​Zayd da Islam su ma suna can gidansu, soyayya iya soyayya suna shanta. Islam ma ta haihu, ta haifi mace kyakkyawa a inda ta samu sunan Ammy wato Maryam Inkiya Ummul Khair.. ​A yau an sha hidimar bikin Arfat itama, ta auri Manager Maleekh. Sun sha hidima sosai. A yayinda ita da angonta suka fita Honeymoon can ƙasar Indian. Zayd da Islam da yarinyarsu su ma sun fita yawon shakatawa ƙasar London... ​Maleekh da Amal suna fita aikinsu a tare bayan sun sauƙe yaransu a School, su kuma sai su wuce babban kamfaninsu wanda ya haɓaka sosai... Suna shan soyayya na gaske, kuma babu wani damuwar komai a rayuwarsu. ​❤️ ​Kamar yau da ya kasance ranar weekend, an kai twins can gidan Abbah ziyara. Iya su biyu suka kasance a gida, lokacin bawa soyayya muhimmanci. ​Suna kwance akan gado (King size bed) a babban ɗakin su mai cike da tsarin zamani da kayan alatu da kuma hasken rana mai launi da ke shiga ta madubin ɗakin. ​Maleekh yana kwance yana rungume da Amal ta bayan ta. Ta sanya kanta a kan hannunsa tana jin numfashinsa mai ɗumi. ​Cikin muryar shagala da kasala ta ce, “Hubby na... na gode wa Allah da ya sanya ni cikin rayuwar farin cikinka… bayan dukkanin abin da ya faru…” ​Ya sumbaci gashinta a hankali “Ni ne ya kamata inyi godiya! Ke ce jarumar rayuwata! Kin yi haƙuri da ni lokacin da ba ki san gaskiya ba! Kuma kin yarda dani a lokacin da kowa ya juyamin baya… Ina sonki Amal! Karshen soyayyar ki shine Farin Cikina.” ​Maleekh ya juyar da ita a kan gadon tana fuskantarsa. Ya sanya hannunsa yana shafa fuskarta da siraran leɓenta masu kyau. ​Ya furta a hankali “Har yanzu ina son ki fiye da yadda nake yi tun farko! Soyayyarki ta ƙare mun damuwa! Ki rufe idon ki…” ​Ta rufe idonta cikin gamsuwa da yarda. Ya sunkuya ya fara sumbatar ta a hankali, yana watsa mata kalmomin soyayya a kunnenta. ​ “You are my Queen, my salvation! I Love You... I Love You... I Love You…” ​Ta kankame shi da ƙarfi, tana mayar masa da martani na soyayya mai zafi da take ji a zuciyarta ga wanda ya kare ta daga dukkanin mugunta kuma ya kawo mata gaskiya. Bayan sun kammala lokacin soyayyarsu a kan gado, Maleekh ya rungume ta a jikinsa, yana shafa mata bayanta a hankali. ​Cikin muryar soyayya da sha'awa ya furta “My Queen, yanzu da rayuwa ta dawo daidai, kuma an yiwa kowa hisabi. Wace ƙasa kike so mu fara kaiwa ziyara da ƴaƴanmu kafin su fara dogon hutu na makaranta? Ina son cikakken farin cikinku!” ​Amal ta lumshe idonta cikin gamsuwa da kwanciyar hankali. ​Ta ɗan matsa jikin shi sannan ta furta. “Hubby, daga cikin dukkanin ƙasashe da za mu iya zuwa, Saudiyya nake so mu fara zuwa. Shine fatana kuma ina so nayiwa iyayena addu'a ta musamman acan, da kuma mu kanmu gaba ɗaya da musulman dake faɗin duniya. Muje mu yi Umrah tare da ƴaƴanmu.” ​Maleekh ya yi murmushin jin daɗi da girmamawa saboda sha’awar Amal na ibada da tausayi. Ya sani cewa yin addu’a a ƙasa mai tsarki zai wanke mata duk wani zafi da ta sha a baya. ​YA furta “Masha Allah! Mafi kyawun zaɓi! Sai anjima zan kira jami’anmu su shirya takardar izinin shiga ƙasa (visa) da kuma jirgin mu na kanmu nan da sati biyu! Duk abin da kike so, za a cika miki!” ​Suka rungumi juna cikin soyayya mai zurfi, suna tunanin tafiya da iyali zuwa ƙasa mai tsarki. ​Bayan sati biyu da shiri mai zurfi, sun hallara a filin jirgin sama (Airport). Dukkanin iyalan su sun zo rakiya zuwa Airport: Ammy da Abbah da Inna. ​Abbah yana tsokanar twins da farin ciki game da tafiyar su. ​ “Ku je kuyi addu’a ku dawo! Iyayenku sun cika ku da gata! Ku kula da Juna kuma ku yiwa kowa addu’a!” ​A ƙarshe, Maleekh ya riƙe hannun Amal da ƴaƴansu suka shiga jirginsu na kansa. Jirgi ya tashi! ​A cikin jirgin da ke ɗaga su zuwa Saudiyya, Maleekh da Amal sun zauna a sashe mai zaman kansa na jirgin, bayan an kwantar da twins suna bacci. ​Maleekh ya kalli cikin idon Amal, inda ya ga alamun farin ciki da tsantsar soyayya suna fito mata daga zuciya. ​YA furta “Gani nan zaune kusa da ke a cikin jirgi, ke da ƴaƴana, muna tafiya ƙasa mai tsarki... Babu abin da ya fi wannan dadi! Komai ya zama daidai!” ​Amal ta rungume shi ta sa kanta a ƙirjinsa cikin kwanciyar hankali. ​TA furta “Wannan duka saboda kai ne! Kai ne jarumin mu!! Na gode da soyayyarka da kariyarka!” ​Maleekh ya ɗago fuskarta ya sumbace ta cikin ƙauna. Ya sanya hannunsa a wuyanta, yana shafa ta a hankali. ​Sannan ya furta “Babu godiya a tsakanin masoya! Ke ce zuciyata! Gaskiya da soyayya sun yi nasara a kan ƙarya da ƙiyayya! Mu more rayuwarmu da yardar Allah!” ​Sun ci gaba da shan soyayya da hira mai daɗi a cikin jirgin har sai da suka isa Saudiyya lafiya, inda suka cika burinsu na yin ibada tare da iyalan su da kuma yiwa iyayensu addu'a ta musamman. ​ Suna gode wa Allah da ya sanya soyayyarsu ta zama ta gaskiya kuma ta ci nasara a kan dukkannin ƙiyayya. ​Anan ne labarin Soyayyar Maleekh da Amal ya ƙare lafiya da zaman lafiya.... ✨ ƘARSHEN LITTAFI ✨ Da sunan Allah Maɗaukakin Sarki. Ina gode wa Allah SWT da Ya ba ni ikon kammala wannan littafi mai suna AMALEEKH. Ina neman yafiyarSa idan akwai kuskure, rashin dacewa ko laifi a cikin wannan rubutu, domin ni ɗan Adam ce mai kuskure. Ina miƙa godiya ta musamman ga dukkan masu karatu da suka bani goyon baya, addu’a da ƙarfafawa tun daga farkon wannan labari har zuwa ƙarshe. Musamman wannan littafi na sadaukar da shi ga manyan fans ɗina na cikin WhatsApp Group: Aunty Habiba Aunty Khadija Aunty Binta Muhammad Naman Zakiyya Aunty Hajjajo Ummu Nihal Allah Ya saka muku da alheri, Ya albarkaci soyayyarku da goyon bayanku. — Asmeetah Writer ✍🏽