[10/02, 9:34 am] Abue Saleh: BOOK 3 2 ........Yanda duk suka zuba masa idanu zai tabbatar maka da ƙagararsu na son jin yace wani abu. Shima ya fahimci zalamar tasu, dan haka kai tsaye ya furta, “Imran bama Dabo yay tracking number ɗin nan?”.       Cikin bin umarni ya amsa da. “Okay”.      Babu ɓata lokaci Dabo ya fidda laptop ɗinsa a jakarta, dan da abinsa yazo. Faro ya miƙa masa wayar. Karo na farko Dada ya miƙe yana kai-kawo a falon hannayensa duk goye a bayansa. Jikin window ya ƙarasa ya tsaya. Yanda ya zubama compound ɗin gidan idanu ya saka Yusuf miƙewa shima ya nufi inda yake hango coffee maker. Sai da ya duba duk coffee powder ɗin dake wajen sannan ya haɗa wanda yasan boss na sha a da, duk da bai sani ba ko ya canja a yanzu. Amma dai ya haɗa ya jira har coffee maker ɗin ta gama matso masa shi sannan ya ɗauka. Koda ya miƙa masa cike da girmamawa sai Dada ya murmusa. A hankali ya furta, “You’re the best”.       Yusuf yay murmushi shima har haƙoransa na bayyana. Cikin ƙara sirinar da kai ya ce, “Yace thanks you Boss”. Daga haka yabar wajen, shi kuma ya fara shan coffee ɗin yana maida hankalinsa ga wajen dai hannunsa ɗaya a aljihu.         “An sauke layin akan waya gaba ɗaya fa. Sannan an goge duk wani information a kansa, tare da hanashi aiki na har abada.”        Gaba ɗaya fuskokinsu ya canja daga sauraren Dabo mai maganar. Amma shi Dada a mamakinsu murmurshi ma yake yi. Dan a hankali ya tako ya dawo inda suke, ya zauna a inda ya tashi yana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Kamar bazai ce komai ba tsahon minti guda yana ta shan coffee ɗinsa. Ganin yanda a yanzu ma suka zuba masa idanun ya sashi sake murmusawa, sannan ya furta, “Wannan ba aikin jahilai bane. Idan lissafi na yayi dai-dai sun ɗauke ta ne dan karkata hankalinmu a kanta kawai su sami yin abinda suke so, Imran, Faro ku janye sojojin ku na ƙofar da sukace su sakar min matata”.        Imran ya zaro idanu saboda kalmar (Matata) ɗin yana gimtse dariya, hakama Faro. Su Dabo kam sun girgiza ne kawai ta ɓangaren aiki duk da sun san Nimrah tun tana ficiciyarta, sai dai batun aure basu san da shi ba, ba kuma su fahimci furucin boss ɗin nasu ba a yanzu. Cikin kasa haƙuri Imran ya ce, “Lissafin ka dai-dai ne. Amma yanke wannan hukuncin duka akwai ruɗani.”       Caraf Faro ya karɓe da, “Tabbas akwai ruɗani Imran, dan kuwa hakan na nufin zasu aikata abinda suka shirya a wannan yankin, sannan ba lallai idan sun sami biyan buƙata su saketa ba, ko kuma su cutar da ita kafin su saketa. Mutanen nan fa sun wuce duk yanda muke zato da tsammani Boss, ni nafi gane kawai mu farmake su, mu amso ta wlhy”.         Dada da kamar baima jin abinda suke faɗa ya wani lumshe idanunsa ya sake buɗewa. Sai kuma ya taɓe baki kaɗan. Hankalinsa kwance ya furta, “Daga lokacin da lissafi ya zama RUƊANI ko mabiyan addini kan kasance a rikice ne. Dan zasu gagara gane waya kamata su bautamawa? Sai dai abu ɗaya tak da zasu nutsu da shi, mafitar mai sauƙi ce. Bayan ANNABIN ƙarshe UBANGIJI bai sake turo wani MANZO ba, kenan duk wanda zai faɗa maka wanene UBANGIJINKA zai koyar dakai bin ALLAH ne da koyarwar MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMAD (S.A.W). UBANGIJI ya halicci abubuwa guda biyu dake bama duniya hasken da har idanun mu ke banbance wanne muke ciki. Hasken RANA, dA hasken FARIN WATA. RANA duhun hadari, ko shigowar dare, ko shigowar hazo na sanyi ne kawai ke iya risinar da ita a garemu, amma hakan baya hana muga hasken DUNIYA. FARIN WATA, canjawar farkon wata zuwa tsakiya da ƙarshe ke canja mana ganin cikakken kaifin haskensa, sai kaga a ƴan awannin nan daya rissina dole muke amfani da fitilu. Shin hakan na nufin mun makanta ne? ko wannan hasken shine dama sandar jagorar idanun mu bisa hukuncin mai hukuntawa?”.          Imran ya ɗan furzar da iska yana mai sakin murmushi. Dan shi ya fahimci komai, saboda yasan Zak-Shadow sanin da ko alfahari yayi da duk duniya babu wanda yay masa irin wannan sanin dole a yarda. Faro dai ba komai ya samu warwara a kansa ba. Amma da yake shima ALLAH ya bashi kaifin basira na tunani, sannan ya yarda da Dada yarda ta haƙiƙa sai ya jinjina kai kawai. [10/02, 9:35 am] Abue Saleh: Dabo, Yusuf dama masu koyi ne daga ƙyawawan hali irin na boss ɗin su. Sannan masu biyayya ne akan ayyukansa musu ƙyau dan sunyi imanin in sha ALLAHU bazai taɓa karkatar da su zuwa mummunar hanyar bijirema UBANGIJI ba.      Shima dai gogan bai sake cewa komai ba. Dan daga haka ma ya miƙe abinsa ya nufi ɗakin nan na sirri ya barsu a falon suna cigaba da tattaunawa. Saboda yanzu dai aiki ya rage garesu.....       <••••><•••><•••><••••>      A gidan Mammah cikin tashin hankalin Ruƙayya suke bayan wanda suke ciki. Dan ta rikice musu ga jikinta ya ɗauki mugun zazzaɓi sai amai take. An kira doctor ya dubata ya tabbatar musu damuwa ce sannan gudun zuciyarta ya canja sosai. Dole ya buƙaci su wuce da ita asibiti. Hakan dole akayi, Ammar ya ɗauketa gaba ɗaya zuwa mota. Yaya Bilal yaja. Ma'aruff da Ja'afar da Mammah suna wata motar. Dan tace bazata iya zama a gidan ba. Suna isa aka fara bata taimakon gaggawa.. Abinda ya sake tada hankalinsu har bayan awanni biyu allurar da sukai mata ta barci taƙi ɗaukar jikinta. Kuma babu abinda sukafi buƙata tayi irin barcin a yanzu. Sunan Ninah kawai take kira. Da ƙyar, da addu'oin da Mammah keta faman tofa mata aka samu nasarar barcin ya ɗauketa. A lokacin kusan 2:30 na dare.         Su Ja'afar sun gagara barin asibitin. Dan cikin ikon ALLAH ma a kusan lokacin sai ga kiran Dada ya shigo wayar Bilal. Ya kira ne dan son jin yaya Mammah ta kwanta dai ko? Sai kuma ya ji akasin lissafi. Yay ɗan jimm na sakanni, kafin ya furta.         “Wane asibiti ne?”.     Sunan asibitin Bilal ya sanar masa. Dada bai ce komai ba ya yanke wayar. Fitowa yay daga ɗakin sirrin daya shiga. Su Imran dake ta faman aiki duk suka ɗago suna kallonsa.          “Faro cikin jami'an daka haɗa ɓangaren masu farin kaya mutum goma suje kk hospital ka tura musu number ɗin su Ma'aruff”.      “Wani abu ne ya faru?”.   Cewar Imran yana tsaresa da idanu. A taƙaice ya ce, “Ruƙayya ce ba lafiya”. Daga haka ya sake juyawa ya koma.       Imran ma aikinsa ya cigaba da yi, sai Faro ne daya ɗauka waya ya fara ƙoƙarin neman ɗaya daga cikin jam'an sirri daya haɗa batare da kowa yasan ɗan uwansa ba..... ★)))((((★))))(((★          “What!”.     Ya faɗa cikin ƙaraji da mamaki yana miƙewa tsaye kamar wanda kunama ta halba a uwawu. Suma sauran duk kallonsa sukayi a razane, kowa na neman ƙarin bayani. Mr Specter ya kalla Oga Jush lips na rawa ya furta, “Wai kasan sun saki hanyar kuwa Oga!”.       Gaba ɗaya meeting room ɗin babu wanda bai nuna razana ba maimakon murna da farin ciki. Black Spider ya ce, “Kai ina akwai matsala. Zak-Shadow ba mahaukaci bane ba fa?.”        “Tabbas ba mahaukaci bane, dan gadararsa ma bazata bari yayi abinda muke so ba cikin awannin goma kacal.” Viper ya faɗa shima cikin tabbatarwa.       Scythe ya ce, “To mi hakan ke nufi?”.      Babu mai wannan amsar, dan haka duk suka zubama Oga Jush da baice komai ba idanu. Sai dai bashi da alamar zai ce ɗin tsahon mintuna uku. Sai da ya gama zuƙe sigarinsa tas kafin.         “Ba mahaukaci bane, sannan ba TSORO yaji ba. Amma dole yay hakan bisa dalilai biyu. Na farko Imran, shine zai tirsasashi dan yarinyar ta dawo, sannan zartarwa da gidan soja a hannun Imran kawai take yanzu tunda shi bai koma aiki ba. Na biyu yana SONTA. Hakan ya nuna a randa ya je station kan case ɗinsu na makaranta...” yaja iska yana ƙoƙarin kunna sabuwar sigari. Dan gaka Iron Fang ya samu damar faɗin, “Amma Oga baka ganin zai yi hakan da wani abu a ƙasa?”.         Baki Oga Jush ya taɓe. “Wannan tunanin naka nakan hanya, dan yana aiki da WAYO fiye da Ƙwaƙwalwa. Amma kar wannan ya dame ka. Ayi mata allurar da zata karya halin da take ciki. A daren nan a kaita inda next plan ɗinmu yake. A ɗorata kan komai cikin awannin da suka rage. Dan hannun karɓa, hannun bayarwa za'ai, kuma a cikin mintunan ƙarshe biyar kacal”.        “What! Oga yanzu nan sakar masa yarinyar nan zamuyi?”. [10/02, 9:35 am] Abue Saleh:      “Muma yin hakan dole ne a garemu. Dan munfi buƙatarta a wajensa fiye da a wajenmu a yanzu. Sannan tana da muhimmanci fiye da komai a garemu a yanzu. Ku ɗauka mune GANGAR JIKI, ita kuma ITACE NUMFASHI. Mi kuke tunani idan da ɗaya babu ɗaya?”.       Tabbas wannan maganar ta Oga ta masifar girgiza su. Dan yanzu sun fahimci girman yarinyar ya wuce ƙaramin tunaninsu a wannan tafiyar. Kuma sai da ita sannan zasu cimma nasarar da suke buƙata. Ashe ba ƙarya bane da akace da yawan yaƙe-yaƙen waɗan nan ƙarnukan suna fara ne ta sanadiyyar MATA. Ga kuwa zahiri suna gani a yau ɗinsu. To bara suga yaya za'a kwashe wannan wasan. SU-NE ko SHI-NE..       Cikin sauke numfashi mai nauyi Viper ya furta, “Tabbas oga mun fahimce ka. Sannan mun gamsu da wannan shirin. Musamman idan mukai dubi da She is a very clever girl. Dan ni ban taɓa ganin mace data bani mamaki ba irinta, idan har a wannan ƙarancin shekarun nata tana a haka ya kake gani nan da wasu 5-years masu zuwa kuma?....”          “A gaskiyar ka Viper, yarinyar KADARA ce mai daraja. Kuma ya kamata ubanta ya ci wannan baiwar tata yanda ya kamata Oga. Lokaci yayi da ƙungiya zata ƙara duba ma Mole ko kuwa ƴan uwa?”.       Yanda ya ƙare maganar da kallonsu su duka. Kai tsaye suka nuna amincewa. Dan girman kai irin na Mr Specter kaga ya yaba wani lallai ko waye ya ciri tuta............✍️ [11/02, 4:36 pm] Abue Saleh:        “Kiyi addu'a, in sha ALLAHU nan da wasu awanni zaki ganta. A yanzu haka muna kan aiki tuƙuru, hasali ma mun san inda take amsota kawai ya rage....”          “Dada da gaske?”.      Ta faɗa cikin washe baki. Murmurshin gefen baki ya mata yana mai lumshe idanunsa da buɗewa alamar tabbatarwa. Ba Ruƙayya kaɗai ba har Mammah da Ammar zancen sa ya musu daɗi. Dan sai da Mmamah ta kauda kai gefe tana ɗauke ƙwallar da suka taru mata a ido, Ammar kuwa ya ɗauki waya ya turama sauran ƴan uwan bayani ta cikin group ɗin su na WhatsApp. Sarai Dada na lure da su su duka har Ammar ɗin. Sai dai baice komai ba. Tea mammah ta haɗa ta bashi. Zai yi magana ta hararesa, murmurshi yayi dole ya amsa. Da zata zuba dankali ne ya lallaɓata yace tea ɗin ya ishesa. Da ƙyar ta yarda. Bai ma wuce sha biyar ba kiran Imran ya shigo masa. Dole ya ajiye yana miƙewa.        “Mammah inaga zan barku, su Imran sun kammala shirinsu. Dole kuma zan rigasu wucewa. Ai mana addu'a”.       Ko bai fito fili ya faɗi inda zasu je ɗin ba Mammah ta fahimta. Dan haka ta fara jera addu'oi masu nauyi sosai a garesu dama al'umma baki ɗaya. Daga haka ya shafa kan Ruƙayya batare da yace komai ba ya fice Ammar biye da shi. Har mota ya rako shi. Sai da ya shiga har ya mata key sannan Ammar ya matsa ya bashi hanya. Dada akwai nutsuwa, sannan komai nashi zaka sameshi a nutse yake. Sai dai akan aiki baya ƙaunar ƙalula ko wasa, in za'ayi kawai ayi, in baza'ai ba a bari, amma maganar wasa anan ɓangaren ba'ayinsa da shi. Yana da zafin nama irin na jaruman maza...       ===============            Kamar yanda suka buƙata an janye sojojin ƙofar yamma tun a daren jiya ƙarfe goma sha ɗaya. Sai dai a maimakon bada Nimrah ko wucewa da abinda suke sonyi wani waje suka kai Nimrah ɗin. Sun kuma nuna mata duk abinda suke son ta sani ta kuma gamsu da su akan zuri'arta. Da farko rashin kunya ta fara zubama su Jagwa dake tare da ita bayan farkowarta, haka ma koda aka kaita gaban wanda sukafi su Jagwa ɗin bata risina ba sai da suka buɗe mata abinda yay matuƙar gigizata. Tabbas tayi shaidar gani da ido, ta kuma shaidar ji da kunne na zahiri. Tayi kuka har hawaye sun daina fita mata. Daga ƙarshe tayi alwashin ɗaukar fansa akan Dada ta hanyar tabbatar masa da DAN HAKKIN DAKA RAINA SHI KE TSOLE MAKA IDO. Dan haka ta ɗauki alwashin zamewa Haysam Abdul-rasheed Shehu Shehu Kobi KIƊA A RUWA. MAI TADA HANKALIN DODO. Idan shi yace ya ƙware a iya FUSKA BIYU zata tabbatar masa da ita kuma RAINON SA ce. Zatai kwanciyar RUWA a gabansa, domin samawa kanta HANYAR wucewa harta ƙofofin gashin jikinsa.....       ★★★★           Ƙarfe 12:pm su Imran suka samu saƙon inda zasu amshi Nimrah. Ba kuma a ko'ina bane sai ta inda suka janye sojojinsu. Dan su Oga Jush sunyi alƙawarin a gaban idanun su Imran zasu wuce da kayansu dan su nuna musu MANYAN ƘWARI ne da sukafi ƙarfin kowa. Dan haka suka shirya sosai kuma akan Nimrah da shirin da ita kanta bata sani ba.        Koda Imran ya turama Dada saƙon ya jima yana maimaita shi shiru cikin nazari, dan ya tabbatar zasu iya wasa da hankalinsu. Idan kuma sukai irin wannan tunanin zasu iya aikata yanda suka ce. Ya kamata ace duka kada suyi sakaci, musamman ma shi, dan wannan shine zaren da zai kama na fara shinfiɗa aikinsa akan su.       Bayan ya gama ƙullawa da kwancewa ya turama Imran saƙo shima. Daga haka ya tashi ya fara shirin cikin uniform ɗin soji domin yin ɓadda kama. Dan shi a yanzu ba jami'in sojoji bane a zahiri. Shi Special Presidential Intelligence & Covert Operations Commander ne a yanzu, amma a wannan gaɓar dole yay ɓadda kama cikin sojojin dan samun abinda yake buƙata. Duk da ya san Imran da Faro zasu iya yin duk abinda zai iya yi in sha ALLAHU..         Kodan ya jima bai saka kanyan ba, ko kuwa dan ya ƙara canjawa da cikar kamalar shekaru ne da nutsuwa. Kayan sun masa ƙyau fiye da shekarun baya ma da yake sakasu da ƙuruciya. Buɗaɗen jikinsa, zuwa shafaffen cikinsa sun zauna fyaram a cikin kayan. Kai da kaga wannan ZAKIN a cikin waɗan nan kayan manyan kasan kasan ba zakin ajiyewa a gidan zoo bane domin kallon yara. Received at 7:46 PM [11/02, 4:37 pm] Abue Saleh: Zaki ne na farauta da in ba'a ma saka masa linzami ko takunkumi ba ɓarnar da zai yi sai ya zama abar rubutawa a tarihin da za'a kafe a bangon gidan gwamnatin ƙasa dan ya zama barazana ga BABBA DA JAKA. Bayan ya saka Handkachiff kamar facemask ya saka baƙin eyeglass daya ɓoye idanunsa da ainahinsa gaba ɗaya. Sai da ya tabbatar kayan aikin da duk zai iya buƙata na cikin jikinsa sannan ya fito compound ɗin gidan. Dan yana a UNIT ZERO ne shi kaɗai. Parking space ya nufa kai tsaye cikin takun sa na masu ƙarfin jini da babu wasa a ciki ko wani rangwaɗar shashanci, dan wannan mazan a mazansu suke kai tsaye. Hannu ya kai kan blue tempol da aka rufe wani abu ya yaye shi, sai ga wani gingimemen ƙaton mashin baƙi wulik mai shegen ƙyau da tsari ya bayyana. Da allama madadin tsohon mashin ɗinsa ne ya dawo a sabon salo, sabon zamani. Hularsa dake ajiye samansa ya ɗauka ya saka, kafin ya haye yana karanta addu'a yay masa key. Koda yazo gate remote ya danna ya buɗe da kansa, yana gama ficewa ya maida ya rufe kansa. Shi kuma ya ɗauki hanya..........✍️ Mun tafi amso Ninah. Wanda ya shirya muje zuwa🤕🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️😎. Received at 7:46 PM [11/02, 4:37 pm] Abue Saleh: 4 ........“Mtsowww!!”. Wani soja yaja tsaki yana kallon agogon hannunsa. Tun 12:30 suke a wajen nan, gashi har 3pm babu alamar abinda suke zaman jira ɗin zai samu. Gashi ko zaman cin abinci a nutse oga ya hana su. Salla kawai ake basu damar yi, wanda ma basayi su basu da ko minti na hutawa. A kaikaice ya ɗan wurgama Imran harara, yana ganin zai juyo ya tsume ya gyara tsaiwarsa. Oho shi Imran ɗin ma bai san yanayi ba, umarni ne dai ya bayar matsayinsa na oga kuma dole-dole abi.       A daji suke iya daji, dan ko dabbobin jeji akace za'a samu masu haɗari a wajen baza'ai musu ba. Dajin mahaɗa ce ta ƙasashe guda uku, daga nan zaka iya shiga kowacce ƙasa cikin sauƙi. Hakan yasa akowane iyaka akwai jami'an soji da aka ajiye na kowacce ƙasa da sauran jami'ai. Sai dai kowa da yanda yake gudanar da aikin sa da kuma iyakarsa. A tasu iyakar babu soja ko ɗaya bayan su ɗin nan da aka kawo awanni uku da suka gabata, gaba ɗayansu su ashirin ne kuma har oganni su guda uku. Abin takaicin kuma wai an kawosu ne kawai dan amsar rai guda ɗaya, ran ma na mace, macen ma yarinya ƙarama ƴar 16years. Wannan wane kalar abin haushi ne, duk da su jami'ai ne masu bada kariya ga al'umma ai bai kamata ace dan rai ɗaya an lalatar da lokacinsu a wajen ba, lalatarwar kuma da suma zasu iya rasa nasu ran. Tunda basu san wane shiri mutanen nan ke da shi ba a kansu. Zata iya yiwuwa sun shirya musu wani tuggu ko kisan mummuƙe bayan sun samu cikar burinsu. “Mtsoww!!” ya sake jan tsakin dai yana kallon agogo. Gulma yake son suyi dana kusa da shi, amma ba dama oga na kallonsu. Dole ya haƙura kamar kowa shima ya dake. A haka 4pm ta cika. Masu salla har sun gabatar.         4:23pm dai-dai kira ya shigo layin Imran. A tare Imran da Dada daya saje cikin yaran Imran ta yanda babu wanda ya gane shi ne suka kalla wayar. Sai kuma suka haɗa ido. Idanu Dadan ya lumshe masa alamar ya ɗaga, sai kuma ya gyara tsaiwa cikin basarwa ya koma kamar yanda yaran keta kai kawo. Sai dai duk abinda Imran ke saurare a cikin wayar shima yana ji, dan sun raba bluetooth ɗin ne kowa da ɗaya a kunnensa.          “Nan da mintuna talatin da bakwai kayanmu zasu iso. Zasu wuce zamu baku ita. Idan kukace zakuyi wani yunƙuri zakuga sakamakon hakanne a kanta. Daga yanzu ka fara ƙirga lokaci, sannan ga saƙo ka faɗama oganka, YA KULA DA KANSA. Idan ya shagala a kula da wannan ƘASAR, shine zai zama ƘASAR dan a maimakon kejin prison wannan karon CIKIN KABARI zai shiga”. Ƙittt. Wayar ta yanke kafin Imran ya iya cewa komai.       Kamar yanda Imran ya ji komai, shi ma Dada ya ji komai. Sai dai wannan ba shine lissafin sa ba a yanzu. Ta inda Nimrah kawai zata bayyana yake kallo.         4:40pm dai-dai baƙar mota mai duhun glass ta iso wajen, sai dai nesa da su kaɗan. Sannan ta ɗayan ɓangaren ba ɓangaren da suke ba. Gaba ɗaya hankalinsu akan motar yake, sai dai tunda ta tsaya babu wanda ya fita a ciki sai da ƙurar da suka tayar ta gama kwanciya kusan mintuna uku. 4:45 aka buɗe murfin motar, jibga-jibgan garada guda biyu majiya ƙarfi suka fito cikin shigar rufe jiki gaba ɗaya dan babu abinda ake gani nasu. Ɗaya ya buɗe baya Nimrah ta fito. Kayan dake jikinta ne dai na jiya, sai dai yanzu an rufe mata baki, hakama idanunta da baƙin ƙyalle. Ƙafarata babu takalmi. Sannan an ɗaure mata hannayenta da aka maida baya. Sun lulluɓa mata towel alamar akwai abinda suka rufe a jikinta. Dan Imran har ya motsa saukar idanunsa akan towel ɗin da suka rufa mata ɗin ne ya saka shi tsayawa cak. Shi fa jam'in soja ne, daya kwashe shekaru yana aiki tun ƙuruciya. Ta ya zai gagara gane kowanne makirci koda daga nesa ne.      Inda Dada yake ya kalla, sai ya ga shima Dada ya kallo shi. Da ido Imran ya masa magana, Dada ya mayar masa murtani alamar ya gane komai. Sake maida dubansu sukai kan Nimrah, a kuma dai-dai lokacin mutanen dake tare da ita suka yaye towel ɗin jikin nata. Bayyanar rigar bomb ta saka yaran sojojin zabura baya a firgice, shi kansa Imran da Dada sai da zukatansu suka buga duk da dama abinda sukai hasashen gani kenan. Received at 7:46 PM [11/02, 4:38 pm] Abue Saleh:         “Da....d...dah!”.     Ta faɗa lips ɗin nata na rawa sosai fiye da da. Murmurshi mai nauyi ya sakar mata. Murmurshin da zata iya rantsuwar bata taɓa ganin irinsa akan fuskarsa ba. Sai kawai hawaye suka shiga silalo mata. Ta sake buɗe baki zata yi magana ya girgiza mata kansa. Tare da ciro dabino a aljihunsa ya sashi a bakinsa ya raba biyu ya cire rabin ya nufi bakinta da shi...         “Haah”.     Ya faɗa a hankali. Ai bama tasan ta buɗe lips ɗin nata ba a hankali ya saka mata. Sai kuma ya shafa lips ɗin nata da yatsa yana sakar mata wani murmushin. Ita dai kallonsa take kamar sakara, tama kasa tauna dabinon. Yanda ma ta shagala a kallonsa kamar wadda ta suma sai da ya fara share mata hawayen da suka gagara tsayawa sannan ta kawo nannauyan numfashi alamar dawowa hayyacinta..        Baiyi magana ba, bai kuma daina murmurshin ba, ya dai maida hankalinsa akan wayoyin bomb ɗin cike da nazari, bayan ya kalla lokacin daya rage musu 18-minutes.........✍️ [14/02, 9:15 am] Abue Saleh: Sai ta samawa kanta lafiya akan ai yau ma rana ce. Dan haka yau ɗin ma ta matsu su taho da wurin nan.       Har akai la'asar ƙawayen nata na nan. Sai da suka gama shaƙiyancinsu da ɗirka mata abubuwa sannan wajen 5 suka tafi. Da Ismat kawai aka barta, dan su Amimah basu biyosu ba. Itama Ismat ɗin Momy bata san ta biyosu ba, so take kuma daga nan ta gudu gidan Abbansu kawai.           Ismat ɗin ta tura yau ma gano mata ko yana nan, idan ma baya nan taje wai dan su Mammah su san ta dawo, ai tasan Mammah ɗin zata saka shi zuwa inda take ko bai niyya ba. Sai dai me, Ismat na zuwa ta dawo mata da labari mara daɗi. Cewar shi baima kwana a gidan ba. Su Mammah kuma duk suna asibiti Ruƙayya babu lafiya. Ga kuma Lailah ma ta faɗi an shiga da ita cs har yanzu ba'a fito da ita ba.         Maimakon hankalin Nabeeha ya tashi tace suje asibitin sai tayi shiru. Sai ita Ismat ɗin ce ta ce, “Aunty kodai asibitin zamuje muma. Dan na fahimci abin fa babbane, hankalin masu aikin nasu duk a tashe yake wlhy”.          “K rabani da wani asibiti Ismat babu inda zanje gaskiya. A gama zuba min wannan uban ƙamshin a jiki da gyara ni na kuma ƙare a asibiti. Ƙamshi nake son D. ya ji ba warin magunguna ba”.       “Amma Aunty.....”    “Kefa matsalata dake kenan. To ALLAH zan kora ki gida yanzu. Haba ki fahimceni mana. Ke bama ƙya ganin idan nace zan fita daga kawoni akwai ganganci a ciki. Karfa ki manta yanda D. Ya tsani yawo”.         “Hummmm”.     Ismat ta faɗa kawai. A ranta ko faɗi take (Baki san ya tsani yawon ba sai yanzu. Bayan tunda yabar gidan kema baki zauna ba Aunty. Kina tunanin kuma baza'a sanar masa ba. Ke matsalar ki baƙya son gaskiya da ɗaukar shawara. Kin bar Momy ta tasirantar da ƙiyayyar dangin mijinki kuma ƴan uwanmu ma ta wani fannin a zuciyarki. ALLAH yasa ki gane, dan inba haka ba wannan karon ma zaman nan naki bamai ɗorewa bane. Dan yanzu mutanen gidan nan bana da bane da suke miki kawaici, sun ɗanɗana zama da wasu surukan sun ji daɗi)...    <<••>><•••••><<••>>       “Dada zan MUTU ko? Zan mutu bazan sake ganin Mammah da Ruky ba, bazan sake ganin su Uncle's Ja'afar ba da su Mu'azz”.          Dada da hankalinsa gaba ɗaya ke kan aikinsa ya saki murmurshi kaɗan. Sai kuma ya ɗan taɓe baki da faɗin, “Bayan kin shiga labor room sau goma sha biyu, kin haifo magadan SOJA, jikokin Abdul-rasheed Shehu Kobi ko Kiddo?”.       Ita sam bata wani fahimcesa ba. Shima kuma yanda yay maganar a basarwarsa yana kuma aikinsa bama zakace shi ya faɗa ɗin ba. Ya sake kallon mintinan da suka rage. 9 kawai. Dai-dai nan Imran dake nufosu ya taka wani abu. Cak ya tsaya yana kallon ƙafarsa. Dan haka Faro dake kallonsa shima ya ce, “Yaya dai?”.      Ƙafarsa ya nuna masa sannan yay masa alamar bomb. Sai kuma yay masa nunin yay shiru kada Dada yaji. Ya ilahi wata muguwar bugawa zuciyar Faro tayi, a take jikinsa ya kama rawa. Ya kalla Imran ya kalla su Dada. Ya rasa ma ina zai kama. Suma sauran sojojin hankalinsu ya tashi matuƙa. A take suka fara zagaye wajen da na'urorin bincike bomb. Dan tunda ogansu ya taka hakan na nufin akwai wasu a wajen. Ai ko sai gasu cikin ikon ALLAH kusan bakwai a cikin ƙasa irin wanda Imran ɗin ya taka. Tuni masu ilimin akansa suka fara aikinsu. Sauran jami'an suka ja baya sosai. Sai dai Faro ya kasa yin hakan. Ya kafa ma su Dabo idanunsa kawai da sukayi jazur na tashin hankali...          “Dada ƙara min Dabino”.     Nimrah ta faɗa idanunta a rufe dan ta sadaƙar kawai lokaci yayi. Shi kansa uban gayyar hankalinsa ya gama kaiwa ƙarshen tashi. Dan saura minti huɗu ya rage musu. Gashi ya katse waya har biyu basu bane, saima ƙara na ƙidaya lokaci da suka saka bomb ɗin ya fara. Dabinon ya ciro ya saka mata a baki, batare daya bar abinda yake ba.        A dai-dai wannan lokacin kuma Faro ne ɗauke da wani ƙaton dutsi yana tafiya a hankali a hankali ta bayan Imran dake tsaye cak a wajen nan har yanzu idanunsa a rufe. Babu abinda yake maimaitawa sai kalmar shahada a zuciyarsa. Dan ya riga ya sadaukar ya kuma sadaƙar yau babu makawa ranar amsa kiran UBANGIJI ce. Babban fatansa Nimrah da Haysam su tsira a idanunsa kafin lokaci ya cika..... Received at 10:47 AM [14/02, 9:15 am] Abue Saleh: 6 .........Fitowar doctors ya sanya gaba ɗayansu zabura, Gwaggo Khadijah da Mammah ne kawai basu tashi ba. Doctor ta saki murmushi mai faɗi ganin duk sun zubo mata idanun cike da ƙaguwa. “Alhamdullahi congratulations. Mun samu nasarar ciro Baby girl cikin ƙoshin lafiya”.        Wasu irin nauyayan ajiyar zuciya suka shiga saukewa a tare. Yayinda Ma'aruff ya kai duƙe yay sujidar shukur. Dai-dai nan Nurse ɗin dake ɗauke da jaririyar ta fito daga bayan doctor. Hannu biyu Ammar dake kusa da ita ya saka ya amshi Babyn, fuskarsa washe da murmushi ya nufi Mammah. Amma saboda kawaici irin nata sai ta nuna masa Gwaggo Khadijah. Ƙaramar dariya yayi cikin jin kunyar abinda yay ɗin shima ya miƙama Gwaggo Khadijah ɗin...        Suna cikin farin cikin kallon Baby aka fito da Lailah da za'a miƙa ɗakin hutu. Ma'aruff ya kai duƙe gaban gadon yana mai kama hannunta. Itama kallonsa take dan idanunta biyu har akayi aka kammala Alhmdllh. Yanda shima ya zuba mata idanunsa da suka rine saboda tashin hankali ya sata sakar masa murmushi. Sai kuma ta ɗaga hannunta takai fuskarsa ta shafa. Hannun nata ya kamo, ya matso da shi a hankali kan lips ɗinsa ya sumbata. Kafin ƙasa-ƙasa ya furta, “ALLAH yay miki albarka Mar'atussaliha. ALLAH ya baki lafiya”.        Kai ta jinjina masa kawai cikin lumshe idanunta da sukai mata nauyi. Isowar su Mammah wajen yasa ta fara ƙoƙarin janye hannunta da har yanzu yake akan fuskarsa. Shi ko idanunsa akanta suke bai gansu ba, sai ya sake damƙeshi. Sai da Ja'afar ya zungure shi cike da shaƙiyanci. Ya ɗago da nufin harararsa sukai ido huɗu da Mammah da Gwaggo Khadijah. Ai da gudu yay ƙasa da kansa yana sakarma Lailah hannu. Su Bilal suka gimtse dariya. Ƙasa-ƙasa Ammar yay magana a kunnen Bilal. “Yaya Billa muma dai ALLAH ya aurar damu. Dan gaskiya an tafi da ni”.       Mintsini mai zafi Bilal ya sakar masa ya gefen ciki. Ya ce “Unch!”. Duk juyowa sukai suna kallonsa. Ruky ta saki dariya batare da tayi niyya ba. Juyawa yay inda take yana kai mata rankwashi. Da sauri ta maƙale jikin Gwaggon Alawiyya. Mammah dake harararsa ta ce, “Yanzu wadda ke gadon asibiti zaka daka Ammar?”.            “Mammah dariya fa tamin”.       “To wannan ihun da tsallen daka buga ba dole tai dariya ba, sai kace wanda kunama ta harba”.      Caraf Ruky ta ce, “Mammah mintsini ya sha wajen Uncle Billa, wai aure yake so dan ALLAH a gaggauta a masa kada ya.....”        Da bala'in sauri Ammar ya waro idanu waje jin harda sharri ta ƙara masa. Bilal ya kwashe da dariya. Dan gaba ɗaya yanda Ammar ɗin ya daburce har yana damƙo Ruky ya rufe mata baki dole abin ya ta baka dariya. Su kansu su Ja'afar daƙyar suka danne. Ruky nata mutsu-mutsun san ƙwacewa yaƙi sakinta sai da Mammah tace, “Malam sakar min yarinya kada ka cire mata haƙori. Badai aure ba, bari Muhammad yazo za'a maka”.      Bashi da zaɓin daya wuce sakin Ruky yabar wajen saboda kunya, ji yake kamar ƙasa ta tsage ya shige. A ransa kam ayyanawa yake sai yayi maganin bakin Ruky. Murmushi kawai su Ma'aruff sukai suna girgiza kawuna. Sai Mu'azz dake ma Ruky gwalo tana harrarsa da gyara hular kanta da Uncle Ammar ya zame tana maƙale da Mammah.        An shigar da Lailah dan haka suma suka koma ɗakin jiyyar Ruƙayya aka fara kiran ƴan uwa da abokan arziƙi kuma. Duk da hankalinsu a rarrabe yake akan al'amarin Nimrah, amma an fita daga wata matsalar Alhamdullah. Dan kasancewar jaririyar a hannunsu har yanzu har hirar da yanzu tana nan data hana kowa ɗauka akayi. Atake damuwarsu ta sake dawowa sabuwa. Kowa ya shiga jero addu'oin gareta. Mammah da batace komai ba kuwa layin Dada ta fara ƙoƙarin kira. Sai dai gashi tana ringing amma ba'a ɗaga ba. Bata damu ba dan tasan tunda har ta yanke bai ɗaga ɗin ba yana kan aiki ne........ ×××××××××××××××         Vibration ɗin wayarsa dake jikinsa ne ya farko da shi daga ƙaramar sumar da yayi sakamakon azababbiyar bugun zuciyar data riski ƙirjinsa a lokacin da ƙarar fashewar bomb ɗin ta nema tarwatsa dodon kunnensa. A hankali ya buɗe idanunsa, ya zubama sauran baƙin hayaƙin dake yawo a samaniyar inda suken. Received at 10:47 AM Viewed 1 time [14/02, 9:15 am] Abue Saleh: Sai kuma tarin sauran sojoji daya karaɗe wajen da ƙananun hayaniya...          “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un Imran...”      Kalma ta farko data sakashi tashi a razane. Bai damu da ƙasar data wanke jikinsa ba. Ya kai dubansa inda ake kiran Imran ɗin. Ganin Faro ya ɗago shi fuskarsa wanke da jini ya saka duniyarsa sake girgizawa. Baima san ya miƙe kan ƙafafunsa ya nufi inda suke ba. A lokacin su ma su Yusuf suka iso da gudu ɗauke da ɗan gadon bada taimakon gaggawa. Dada ji yake kamar kansa zai tarwatse. Dan yana isowa daga can wani soja cikin ƙaraji ya furta, “Bomb ɗin nan ya tashi da yarinyar nan f....”           Ai baima ƙarasa ba duhu ya mamaye idanun Dada. Kawai yaci tuntuɓe da Faro zai zube sai da aka riƙoshi. Dole Faro ya sakar musu Imran ya miƙe yana kama Dada. Zaunar da shi yayi, tare da amsar gorar ruwan da wani soja ya kawo ya ɓalle murfin ya saka masa a baki. Hannu yasa zai ture Faro yay saurin dakatar da shi...        “Dan ALLAH kasha ko kaɗan”.     Kurɓa ɗaya yayi ya kauda kansa. Faro zai sake magana wani soja ya katse hakan ta hanyar ƙwala kira, “Sirs!!!!!”.         Ai a tare suka zabura. Sojoji sukai wajen da gudu. Dole Faro ya miƙe shima. Sai kawai Dada ya miƙe cikin ƙoƙarin danne firgicinsa shima ya nufesu. Yayinda motar data ɗauki Imran tabar wajen dan nufar asibiti da shi...            “Bata mutu ba!”.        Furucin daya nema sakashi amayo zuciyarsa ta baki. Tuni ya fasa sojojin ya shiga. Caraf ta riƙe sojan dake ƙoƙarin kai hannu kan Nimrah dake kwance ƙasa ta buleta har ba'a ganinta da ƙyau. Sojan zai yi magana Faro ya ce, “Leave...”        Dole yaja jikinsa baya. Dada yakai duƙe wajen yana saka hannayesa ya zarota gaba ɗayanta, bai damu da ƙasar dake jikinta ba ya sakata a nashi jikin kawai ya rungume yana sauke wani irin bahagon wahallen jerarrun ajiyar zuciya. Ganin haka Faro yama sojojin umarnin barin wajen domin bincika ya akai haka. Dan bomb ɗin daya tashi dai na jikinta ne. Wanda Imran ya taka yayi nasarar danna masa dutsi a dai-dai lokacin da na jikin nata ke fashewa, shi kuma Imran ya ɗaga ƙafarsa saboda razanin tunanin wanda ya taka ne, shine sukai tsalle gefe kan Imran ya daki dutsin....        “Tabbas yarinyar nan nada wayo, dan sai dai idan cire rigar nan tai tayi jifa da ita Sir”.         Sosai Faro ke jin gamsuwa da abinda sojan ke faɗa. Haka ma sauran sojojin dan sun gama dube-duben su da aune-aune. Kuma gaba ɗaya alama ta nuna musu a sama Bomb ɗin ya tashi musamman yanda yay nesa da inda suke. Sannan itama aka cillata gefe ƙasa ta rufeta. Dada dake ƙoƙarin sake zubama Nimrah ruwa a fuska da Yusuf ke zuba masa a hannu duk yana saurarensu. Sai dai hankalinsa ba'a kansu yake ba. Zubawa ta uku babu alamar zata farfaɗo. Ga masu son bata taimakon gaggawa yaƙi basu dama. Ya zuba mata na huɗu yana ɗan bubbuga kumatunta wani ya yunƙuro zai yi maganar kodai a wuce da ita asibiti kawai saita wani irin banƙare, da sauri ya riƙota da ƙyau ya matse a jikinsa. Wata razananniyar ƙara ta saki mai firgitarwa tana fisga zata fita a jikin nashi gaba ɗaya. Da yake ƙarfin ba ɗaya ba dannawa ɗaya ya maida ita. Dole hankalin su Faro ya dawo wajen gaba ɗaya, cikin sauri aka kawo mota wajen, dan dole a wuce da ita asibiti da gaggawa.... ©️©️©️©️©️©️©️©️©️©️©️          “Done Oga. Komai yazo hannu”.    Wani murmushin ƙasaita Oga Jush ya saki yana kallon Viper. Sai kuma ya miƙa masa hannu alamar yazo gareshi. Matsawa yay suka rungume juna.         “Proud of you darling”.     Oga Jush ya faɗa yana bubbuga bayan Viper. Matuƙar farin ciki Viper ya ƙara jinsa a ciki. Ya rissina cike da girmamawa shima ya ce, “Proud of you too Sir”.       Oga Jush yay murmushi mai faɗi yana jinjina masa kai da lumshe idanu. Kafin ya gyara zama da faɗin, “Yarinyar fa?”.          “Gaskiya tana da wayo, ta kuɓuta. Amma kaɗan ya rage a samu matsala”. Received at 10:47 AM [14/02, 9:15 am] Abue Saleh:       “Hakan na nufin zatai mana abinda muke buƙata sosai ai”.       “Tabbas zata iya, sai dai Oga data mutu fa?”.       “Dama ɗayan biyu ne tsarin ai, kota mutu a wannan gaɓar ubanta ya ƙarasa aikin, shi kuma mu gigita duniyarsa da rashinta. Kota tsira tayi mana aikin. Kaga tunda ta tsira ƴar sa'a ce kenan.”           “Gaskiya ƴar sa'a ce kam Sir. Abinda ma zai saka ka farin ciki shine, duk abinda muka nuna mata tayi na'am da shi, damma bata san waye ke aureta nata ba”.       “Wannan ai shine babban makamin mu a kanta, shiyyasa nace kada ku faɗa mata waye mijin, taje ta bincika da kanta. Yaya batun yaran?”.      “Duk sun bamu haɗin kai. Sannan da yawansu ta tuna fuskokinsu”.        “Good. Sai mu je Batch B. A sanar da kowa akwai meeting gobe da safe.”      “Okay Sir”...........✍️ [14/02, 7:48 am] null: KIƊA A RUWA 3 7 ........★9:pm★          Sai a wannan lokacin Dada da Faro suka sami damar ganin Imran. Duk da tun ɗazun ya farfaɗo allurar da sukai masa ta saka shi barci ya saka sai yanzu aka basu damar shiga inda suke. Duk da daga shi har Nimrah sun kawo su wani sirrintaccen asibiti ne.           Kalma ta farko da ya fara furta musu shi ne, “Ina Nimrah?”.        Murmushi Faro yayi da faɗin, “Relax Colonel. Ɗiyarka na nan lafiya lau Alhamdullah. Duk da itama muna jiran ji daga doctors ne akanta amma in sha ALLAHU komai mai sauƙi ne, bakaga mijinta na tsaye kan ƙafafunsa ba”.       “Alhamdullahi”.     Ya sake faɗa a hankali yana kallon Dada daya zuba masa juyayyun idanunsa. Murmushi kwantar da hankali ya sakar masa. Sai kuma ya motsa a hankali zai tashi. Fuska ya yamutse da saurin kai hannu saman kansa da yay masa nauyi. Riƙe san da yaji anyi ya sashi buɗe idanunsa daya lumshe. Akan Dada ya sauke su, dan shine ya riƙe san.           Hararar da Dadan ya sakar masa ta saka shi yin murmushi. A hakanli ya furta, “Miye na hararata?”.       “Gaggawar ta miye?”.     Ya faɗa yana maida shi ya kwantar. Sai kawai Imran ya sake yin ɗan murmurshi. Koda ya sake jeho musu tambayar miya faru da batun tashin bomb?.          Kaɗan Faro ya masa bayani dan ya samu nutsuwa. Sauran yace sai ya samu lafiya. Dada dai na tsaye yana saurarensu. Sai dai ya zubama Imran idanunsa cike da yanayi na damuwar halin da yake ciki, dan ji yake kamar ya ɗauke ciwon daga jikinsa ya maido nasa jikin. Motsin da wayarsa tayi alamar shigowar kira yasa ya ɗan ja numfashi ya fesar. Batare da yayi magana ba ya ciro ta a aljihu.       Ficewa yay a ɗakin cikin muryarsa data koma ƙasa sosai alamar gajiya, dan rabonsa da abinci ma tun safe. Shima ba wani breakfast ɗin kirki bane ba. Normal black tea ne da dafaffen ƙwai uku. Daga can Mammah tai ɗan tsai tana sauraren gaisuwar da yake mata, sai dai maimakon amsawa tambaya ta jeho masa.        “Yana jika haka? Ko akwai wata matsalar ne?”.       Sai da yay ƙaramin murmushi daya tsaya masa iya lips kafin ya ɗan sauke ajiyar zuciya. “A'a kawai gajiya ce Mammah....”        “Da yunwa kuma ba. Tunda kai da abinci maƙiyan juna ne Muhammad. Yanzu dai ga su Bilal nan zasu kawo muku abinci. Dan naga alamar ba sallamoku zasuyi ba a yau ɗin nan. Kai kuma ka hanamu muzo, gashi kowa ya ƙagu yaganta”.          Yanzu kam murmurshin sa har sai da ya bayyana akan fuskarsa. Ya ɗan zubama ɗakin da Nimrah ke kwance idanunsa. “Ba hanaku nai ba, kawai dai yanayin aikin ne a haka. Suma su Bilal ɗin su bari zan turo Dabo ya amsa abincin”.      “Muhammad kodai wani abu ya samar min Nimrah ne kake ɓoye min?”.            Yasan za'a rina. Dan tun bayan zuwansu asibitin yay kiranta ya sanar mata suna asibiti amma bawani damuwa firgita ce ta sakata suma amma basai sun zo ba saboda yanayin tsaro. Amma sai da yaji Mammah ta jinjina kamar dai bata so ace kar su zo ɗin ba....       “Muhammad!”.   Ta faɗa cikin sanyi dake bayyana damuwarta. Iska ya ɗan furzar da gyara muryarsa, cike da kulawa yace, “Mammah ki kwantar da hankalinki. Babu wata damuwa. Da acema ba barci take ba da tuni na haɗaki da ita. Amma in sha ALLAHU zuwa da safe zasu sallameta. Idan basuyi hakan ba zanzo na ɗaukeki da kaina na kawoki”.          Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi. “Shi ke nan ALLAH ya ƙara musu lafiya. Yaya shi Baban nasu?”.      “Shima Alhamdullah, dan daga wajensa na fito ma ya farka.”              “Masha ALLAH. ALLAH ya kiyaye gaba to. Ka aiko to a amshi abincin. Zan haɗo da kaya kuma ko zaku buƙata dan nasan Nimrah da ƙyanƙyami, kayan jikin nan nata na tabbatar sun isheta”.       A hankali ya ce, “Uhmm”. Daga haka sukai sallama Mammah najin nutsuwa. Suma da daren nan suka koma gida dan tunda Ruky taji anga Nimrah ta sake watsakkewa. Lailah suka baro da Ammie da taje zata zauna da ita...       ★★★    Dai-dai yana katse wayar aka buɗe ƙofar ɗakin da Nimrah take. Ta ƙasan ido ya ɗan duba wajen, sai kuma ya janye lokaci guda. Dan duk ƙwaf ɗinka zaka ɗauka hankalinsa akan wayarsa yake. Doctor da ke fitowa Nurse a tare da ita ta rage yanayin ɗan hanzarin data fito da shi. Dan gaba ɗaya kwarjininsa ya cika mata wajen. Itama ba yarinya bace, sannan da aurenta, sai dai Dada ya girmeta sosai gaskiya. Tun ɗazun yanayin tsare gidansa da gizago yasa ya cika musu idanu. Dan irinsu Dada ko babu alaƙa, ko baka taɓa saninsu ba a gani ɗaya kamalarsu da cikar haiba ke siya musu girma ga mai kallonsu.        “Barka ranka ya daɗe, dama neman ku na fito”.        Baiyi magana ba, bai kuma kalleta ba. Amma ya janye wayar daga idanunsa alamar yana sauraren ta. Itama fahimtar hakan ya sakata cigaba da bayaninta kawai. Itako Nurse a kaikaice ta zubama masa idanu tanata tasbihi ga UBANGIJI mahaliccin wannan nutsatstsiyar halitta...       “Ta farka, sai dai jikinta akwai zafi sosai, dole ko yaya a goge mata shi da ruwa mai ɗan sauƙin sanyi. Sannan akwai yunwa a tare da ita. Ga Nurse zata goge mata jikin yanzu sai abinda zata cin muke buƙata”.           “Uhmm”.      Kawai yace a taƙaice. Doctor data fahimci amsar kenan sai itama ta ɗan sake risinawar girmamawa tana barin wajen. Nurse kam da taso ita kam dai taji yayi magana sai taji kamar ta fasa ihu. Dole tabi umarnin doctor data bata na zuwa ta samar da abin zuba ruwan. Fin minti guda da wucewar su ya taka zuwa kofar ɗakin. Hakan yasa Faro daya tunkaro shi komawa baya kawai yana ɗan murmurshi. Shi ko Dada da bai gansa ba har ya shige...        Yanda ta duƙunƙune jikinta cikin blanket ya sashi zubama gadon ido sosai. Ta rufe har kanta, sannan a dunƙule take waje guda. Hakan na nufin a tsorace take har yanzu, ko tana jin sanyi. Shiru kamar bazai ƙarasa ba, sai da kunnensa ya fara ji masa kamar tana jan shashshekar kuka sannan. Matsowarsa gaban gadon da ƙyau ya tabbatar masa kukan take kuwa. Maimakon yin magana hannu ya kai zai janye blanket ɗin duk da bai ma san ina kanta yake ba saboda yanda take a cure.        Firgigit Nimrah ta zabura. Dan tana cikin wani yanayi ne na wanda abu ke dawo ma a rai. Cikin zafin nama Dada ya tarota, saboda yanda ta zaburan sai ta tafi gaba ɗaya zata wantsalo ƙasa. Ita kuwa batare da tunanin waye ba kawai ta cukuykuye shi a yanda yake a tsayen. Dan kanta ta kwantar a saman shafaffen cikinsa ta zagayo da hannayenta a bayansa ta matse tsamm. Da ace ragon namiji ne babu abinda zai hanashi jin matsar nan har cikin ƙashi. Amma da yake mazan mazan fama ne ko gezau, sai dai abin yazo masa a bazata daya tilasta shi lumshe idanunsa kawai. Fin minti guda suna a haka, zafin zazzaɓinta ya fara shiga jikinsa. Sai ɗumin hawayenta dake sauka masa akan riga har danshin na taɓa jikinsa, ga jikinta na ɗan rawa-rawa kaɗan, sai dai bai sani ba na tsoro ne kona jin sanyi...        Kai tsaye Nurse da bata san da shi a ciki ba ta buɗe ƙofar. Sai da ta juyo bayan ta rufe tai arangama da shi. Da gudun tsiya taja ta tsaya. Lips na rawa ta ce, “Ka...k....”         Wani mugun watso mata idanu yay da mata alamar tai shiru. Aiko kamar wata sokuwa tasa hannu ta dafe bakin nata tana risinar da kanta. A haka ta ƙaraso gaban gadon ta ajiye ƙaramin botikin hannunta na roba. Sai towel ƙarami shima sabo a ledarsa. Ta gefen ido take satar kallonsu da yin gulma a zuciyarta. (Uhumm lallai wannan ƴa na son Babanta. Kaga ƴar shagwaɓa. Ai dake zan kama ƙafa na samu shiga wajen wannan Barden mazajen. Dan daga gani kam ke ƴar lelensa ce...)          Da alama dai Nurse ita tasan ma tana yi. Dan shi dai Dada na tsayensa har yanzu. Ga Nimrah ta masa ɗaurin goro. Shi kuma ya ma gagara yin komai, sai da Nimrah ta ɗan zabura har tana neman sakashi yin baya sannan ya ɗora duk hannayensa biyu a jikinta batare daya shirya ba. Ɗaya a gadon bayanta ɗaya akanta da ɗan kwalin ya fita. Sai dai akwai kitso ƙanana da suka mata ƙyau cikku dan tana son cikku sosai. Itama Nurse ɗin zaburowa tai kamar zata tare Nimrah ɗin duk da taga a jikinsa take amma da yake neman uwawun zama take itama sai tazo nuna bajinta. Received at 10:47 AM     Yanzun ma kallo irin na ɗazun yay mata, dole ta dakata da gudu tana kai hannu ta sosa ƙeya tana jan jikinta baya. Shima daya tabbatar wannan yanayin zai iya saka cutuwa, a karo na farko ya furzar da iska yana shafa kan nata, ƙasa-ƙasa ya furta, “It's okay Babie” sai kuma ya kamata slowly ya maida saman gadon ya zaunar. Taƙi sakin hannunta dake zagaye da ƙugunsa, dole ya kai nasa hannun da kansa ya janye natan. Kuka ta sake fashewa da shi tana ƙoƙarin sake cusa kanta a jikinsa. Bai bari tayi hakan ba ya kai zaune kusa da ita. Sai kawai ta sake faɗa masa a jiki tana cukuykuye kan nata dai..........✍️       [14/02, 7:48 am] null: KIƊA A RUWA 3 8 .........Nurse data fahimci yanayin Nimrah ɗin cike da son birge shi ta zabura tana faɗin, “Yallaɓai bari na sanar da Doctor, dan kam akwai matsala a firgice take. Dama Doctor tayi magana ɗazun data farka akan ALLAH yasa kada ta shiga yanayin...”        Yanda bai tanka ba a ɗazun yanzu ma hakan ne. Itama bata jira amsar tashi ba ta fice a hanzarce. Ai ko babu jimawa sai gasu sun shigo. Har yanzu kuma Nimrah ta hanashi ko motsi tsabar yanda ta cukuykuye sa. Dan zuwa yanzu gaba ɗaya rabin jikinta akan nashi yake. Cikin lallashi Doctor tai magana tana kamo hannunta. Amma sai ta fisge tana fashewa da kuka da sambatu irin na tabbacin bata cikin hayyacinta...         Doctor ta rasa yanda zatai aikinta saboda yanda take jikinsa. Gashi maganar duniya Nimrah taƙi ɗagowa....          “Miye matsalar?”.    Dada ya faɗa yana ɗan kallon likitar a karo na farko. Sai kuma ya janye idanun nasa duk a lokaci guda. Itama ba iya kallonsa take ba, dan haka ta fara masa bayani yanda zai fahimta...... Da ga ƙarshe ta ce, “Yanzu akwai allurar dazan mata, in sha ALLAHU ƴan mintuna ne nutsuwarta zata dawo, dan har yanzu abinda ya faru bai bar brain ɗinta bane gaba ɗaya. Rashin tabbacin zata tsinta kanta a hakan yasa ban mata allurar ba tun ɗazu.”        Bai ce komai ba, sai dai ya gamsu da bayanin nata, dan haka ya kama Nimrah da kansa ya ɗagota sosai. Tana mutsu-mutsu da son ƙwacewa dai akai allurar. Kusan a tare shi da Doctor suka sauke ajiyar zuciya bayan wasu mintina ganin Nimrah ta fara nutsuwa. Sai dai shi a ciki yay tashi, doctor kuma a bayyane. Knocking ƙofar da akai ya saka Nurse da Doctor kallon wajen, sai kuma Nurse ɗin taje ta duba. Dabo ne ɗauke da kaya, bayan sun gaisa ya miƙa mata kayan, ya ɗauki sauran ya nufi ɗakin Imran.       Itama bayan ta ajiye kayan inda ya dace doctor ta bata umarnin gogema Nimrah jikinta dake sake ɗaukar zafi. Miƙewa Dada yay abinsa, dan tun da akai allurar ya kwantar da Nimrah gefensa yanzu ba'a jikinsa take ba. Sai da ya maida ƙofar ya rufe Nurse ɗin dake binsa da kallo ta ƙasan ido ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi tana nufar Nimrah. Murmushi Doctor tayi, sai ma taji Nurse ɗin ta bata tausayi... ÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷÷ Wani wawan birki Malam Buba yaja yana waro idanun mamaki ganin wanda ke ƙoƙarin tsaida shi. Duk da ya rufe fuska da handkachiff ga p-cap hakan bai hana shi gane shi ba. Wuff Dagger ya buɗe motar kuwa ya shigo. Ya furzar da iska mai nauyi yana janye handkachiff ɗin daya rufe fuska da shi...        “Amma Oga wannan gangancine da mu duka zai iya sakamu a haɗari. Mizai sa kazo har nan anguwar, gari da haske kuma irin haka?”.        Harara Dagger ya jefama Malam Buba kafin ya janye handkachiff ɗin da yake goge fuska yana gyara zama. “To faɗa min ya kake so nayi Mole? Tun randa ka kirani an ɗauke Nimrah ka sake nemana? Tsabar rashin mutunci ma waya ka kashe min gaba ɗaya. Jiya da shekaran jiya duk naje gidanka ance baka dawo ba. Sai da na kira Ari akan ya bincika min tunda na tabbatar bazai rasa huɗɗa da wani a gidan ba ya tabbatar min kana nan anan ma kake kwana. Mole mi kake nufi? Mi kake shiryawa? Ko Nimrah na hannunka?”.         “Amma Oga wannan wace irin magana ce? Kasan dai duk wuya bazan ci amanarka ba, duk abinda zakaga nayi ina da dalili na, ko bakazo ba zan zo na kawo maka dukkan bayanai. Na farko dai kwana a gidan nima a gareni tilas ne, dan yarinyar nan Ruƙayya ce babu lafiya, sai kuma wajen jiyyarta ɗayar matar waɗannan ƙannen nasa ta faɗi akan ciki sai ta akai mata tiyata aka riro jaririn. Hakan yasa inata kai kawo na jigilar kai abinci da abubuwa. Sannan wlhy hankalina ba'a kwance yake ba, ina nane da su ko zanji bayanin an sami Uwa dan har yanzu mutumin nan bai sake dawowa gidan ba daga shi har Imran....”          “Amma ba waya ya kamata ka kashe min ba, tunda nima ina buƙatar son jin abinda ke faruwa ko.” Received at 10:47 AM 3 people reacted with     “Itama fa wayar ba kashewa nai ba oga. Wannan wawan Sanda ɗin ne ya ara ya shiga bayi saboda fitilar bayin ta lalace shine ya tsumbulata a ruwa, yanzu haka inda zan kai gyara nake nema”.            “Mtsowww!”.       Dagger yaja tsaki. Sai kuma ya miƙa masa hannu da faɗin, “Bani wayar.”     Ba musu Malam Buba ya cirota ya bashi, Dagger ya ɗan jujjuyata a hannunsa sai kuma ya saka a aljihu. Wata ƙarama ya ciro ya bashi. “Ga wannan, daga yanzu na dinga sanin halin da ake ciki”.        “Amma Oga ya batun Nimrah? Wlhy abin ya fara bani tsoro.”     “Nima a tsoracen nake, dan itace rayuwata. Amma ina kan bibiyar iyayen yaron can da suka daka a makaranta satin daya gabata”.        “Tsohon shugaban ƙasa fa naji ance”.     “Eh su. Dan ina zarginsu gaskiya. Musamman matarsa bata da mutunci daman.”        “To amma ta yaya Oga?”. Wata dariya Dagger ya kece da ita. Sannan ya ce, “Humm Mole har yanzu kanka a tukunya yake kai kam. Baka san waye Dagger ba a ƙasar nan. Kodan kai kana ganina arhar banza ne. To bara kaji, wannan damar ina baka ita ne saboda Nimrah. Za kuma ka iya samun fiye da hakan. Kai dai bari na aureta”.       Harga ALLAH sai da ƙirjin Malam Buba ya jijjiga. Har ya kasa dannewa cikin suɓutar baki ya furta, “Aure Oga?”.          “Eh mana, ko bazaka bani ba?”.     Dagger ya faɗa cikin tsatstsareshi da idanu. Yawu mai kauri Malam Buba ya haɗiya, zuciyarsa kuwa wani irin dukan take yi. Cikin rawar baki ya ce, “Ba..b...ba haka nake nufi ba Oga. Kawai dai naga ita ƴa take a wajen ka”.       “A'a a wajenka dai, dan kai ka haifa. Ni masoyiya ce, kuma uwar ƴaƴana. Sai dai idan baka son bani”      Yawu mai ƙauri Malam Buba ya sake haɗewa. “Oga ai kaima mai aurama wani ce. Kawai dai kasan ance wannan mutumin yana au.....”       Cikin katseshi Dagger ya ce, “Oh kai harma ka ɗauki wannan auren aure? Shi jakin wace ƙasa ce zai aure ta babu iyayenta. Sannan ma wannan tsohon da aƙalla ma zai iya girmarka ne bakinka ke iya jinginawa da ƴarka. Jibeshi mutum a murɗe kamar ɗan damben turawa, dan ni banga abinda ya rage ba a zaman prison ɗin shiyyasa bamma yarda a can yake shekara takwas ba......”       Sam Malam Buba ba jin Dagger yake ba a yanzu. Dan tsakani da ALLAH hankalinsa ya tashi. Ai koda rayuwa ta maidashi haka baya fatan yarsa ɗaya tilo ta auri mutum irin Dagger da babu sbinda ya sani a rayuwarsa sai mugunta da kisan kai. Ga neman mata kamar ɗan bunsuru. Tabbas baya ƙaunar Zak-Shadow, kuma ko zai rasa ransa wannan auren bazai bari ya tabbata ba akan ƴarsa. Amma kuma bazai so Dagger ya maye gurbin Zak-Shadow ɗin ba a rayuwar Nimrah. Dole ne yayi wani motsi a wannan gaɓar, kuɗin nan da su Oga suka bashi gida zai nema ya saya a wata ƙasa cikin maƙwaftan ƙasashen nan, ya ɗauke ƴarsa ya maida can, ya sama mata ma'aikata masu kula da ita, ya biya mata ta cigaba da karatunta har ta samu miji irin wanda yake fata a gareta amma ba Dagger da Zak-Shadow ba.....       “Wai tunanin mi kake yi?”.    Dagger ya faɗa cikin tsawa-tsawa. Ajiyar zuciya Mole ya sauke yana girgiza kansa. “Ba komai Oga, babbar damuwata kawai ina ta shiga? Waye ya ɗauke ta? Saboda mi ya ɗauke tan?”.          “Karka damu zata dawo. Yanzu haka su Ayu nakan aikin nemanta. Bari naje yau inada meeting dasu oga aiki zai fara da zafinsa saboda kayan aiki sun iso, duk halin da ake ciki dai na dinga sani. Kaima kuma ka zama cikin shiri, idan ta kama kazo dole zaka zo”.       Kai Mole ya jinjina masa. Daga haka sukai sallama ya fita a motar anata kiran sallar magrib shi kuma yaja motar ya ƙarasa gida. Dan dama daga asibiti yake yakai abinci. Sai da ya dakata wata mota da Malam Almu ya buɗe ma gate ɗin ta fito sannan ya shige, har yay parking idanunsa akan Nabeeha dake komawa ɓangarenta da alama motar data fita baƙinta ne..... °°°°°°°°°°°°°°    °°°°°°°°°°°°°°°        Kusan mintina ashirin Nurse ɗin ta ɗauka tana gogema Nimrah da barci ya ɗauka jiki. Ta canja mata kayan da aka sako marasa nauyi. Dan simple doguwar riga ce sai hula. Tana ƙoƙarin saka mata hular ne ta buɗe idanun ta da sukai jazur tana yamutsa fuska. Hannu takai ta dafe kan. Received at 10:47 AmDan haka Nurse ɗin ta dakata daga saka mata hular tana tambayarta kanta na ciwo ne?. Kan ta jinjina mata tana lumshe idanu, a lokacin Dada ya sake dawowa ɗakin.        Tunda ya iso gaban gadon Nimrah ta buɗe idannunta a kansa, sai kuma tai narai-narai da su hawaye na taruwa a ciki. Cikin muryarta dake fita ƙasa sosai ta ce, “Dada kaina”.     Bai wani jita da ƙyau ba, sai dai a motsin lips ɗinta ya fahimci abinda take faɗa. Maimakon zama a kujerar gaban gadon sai ya zauna a bakin gadon kusa da ita sosai, bayan hannunsa ya kai saman goshin nata. A dai-dai lokacin Nurse ɗin ta fito daga bayi hannunta ɗauke da ƙaramar tasa da ruwa a ciki, sai towel ɗin data goge mata jiki data ɗaurayo. Cikin in-ina take sanar masa zata sake saka mata towel a kanta. Hannu kawai ya miƙa mata alamar ta bashi, ai ko da hanzarin ta ta matso towel ɗin daga ruwan ta miƙa masa. Amsa yay batare daya kalleta ba, ya janye hannun Nimrah data riƙe kan ya ɗora towel ɗina. Sosai ta sauke ajiyar zuciya, tana mai ɗora hannunta akan nashi da yake ɗan daddana towel ɗin. Idanun su ne suka shige cikin na juna a hankali. Tai saurin janye nata tana rufesu. Shi ko ya cigaba da kallon fuskarta da tai fayau..........✍️ Received at 10:47 AM 9 ..........Ita dai Nurse nata kallonsu kamar ta samu television, sai in ya cire towel ɗin ya miƙa mata ta sake jiƙashi da ruwa ta matse ta miƙa masa. Sai da sukai haka sau kusan uku ya tabbatar zafin kan ma ya sauka sannan ya barta. Badan Nurse ɗin taso ba ta shige ta fita. Shi kuma ya fara ƙoƙarin haɗa tea. Sai da ya kammala a karo na farko yay mata magana. Idanunta dake rufe ta buɗe, sai kuma ta janye ganin ita yake kallo, ga hannunsa ɗaya ya miƙa mata alamar ta kama. (Sun ɗaura miki aure da wani a gidan tun kina 7years, sunyi hakan ne kuma dan cimma burinsu akan ki da mu. Babu shakka a yanzu kuma zasu fara aiwatar da bukatarsu a kanki. Sai ki lura, ki kuma fahimce su musamman shi tun kafin yay miki illa, ki yaƙe shi tun kafin ya karasa kassara mu ahalinki. Dan yana da wayo, bazai taɓa nuna miki saɓanin abinda yake so ki sani akansa ba. Mun baki assignment kuma ki nema sanin wanda suka aura miki idan kin koma.....) Waɗan nan zantukan ne keta dawo mata acikin kai. Ƙirjinta ya sake bugawa sakamakon dawowar hirar Dada Da Daddy Imran da taji kalmar aure suma a bakinsu. Mi hakan ke nufi? Wa aka aura ma ita ne? Waye mijin nata?. Bata da mai bata wannan amso shin a yanzu, dan haka ta zubama hannun nasa idanu har kusan mintina biyu. Ita bata kama ba, ita bata tashi bisa umarnin daya bata ba.        Dada dake kallonta cike da nazarin yanayin nata yay ɗan gyaran muryar data sakata yin firgigit, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi tana risinar da idanun nata. Zuwa yanzu ta ɗan ji daɗin jikinta saboda goge matan da akayi, daddafawa tai ta tashi kawai batare data kama hannun nasa ba. Shima bai ce da ita komai ba ya miƙa mata tea ɗin kawai. Maimakon ta amsa sai ta fara magana cikin rawar murya...         “Dada! Dan ALLAH zan je wajen Mammah.”      “Ni zan cinyeki ne anan?”.   Yanda yay maganar kai tsaye yana danna waya ya sata saurin girgiza kai. Sai ga hawaye sharrr. Hannunta ɗaya takai tana sharewa. Hakan yasa shi ɗan dubanta, sai kuma ya janye idanun a lokaci guda. “Kisha ga magani da safe zaki je”.         Kamar wadda bata gane yaren nasa ba ta ce, “Wajen Mammah ɗin?”.     Yanzu kam gaba ɗaya ya ɗago yana kallonta sosai. Da sauri ta janye nata idanun data wara a kansa ta fara shan tea ɗin. Sai faman sauke ajiyar zuciya take a jajjare. Bata sake gigin kallon inda yake ba dan yaƙi ɗauke idanunsa a kanta harta shanye tea ɗin tas. Sai ga zufa na wanke mata jiki alamar ƙoshi...           “Zaki ci abincin?”.      Da sauri ta girgiza masa kanta. Shima sai kawai ya jawo ledar maganin nata da robar ruwa. Duk yanda suka rubuta haka ya bata, tana gama sha ta zame zata kwanta...         “Tashi zaune”.      Ya faɗa cikin umarni. Ba haka taso ba, amma bazata iya masa musu ba duk da itama dai kwanciyar ta isheta daman. Da kansa ya gyara mata filo ta jingina. Knocking ƙofar da akai ya saka Dada bada umarnin shigowa. Faro ne, dan haka Nimrah dake lullumshe idanu ta buɗe su da ƙyau tana gaishe shi. Ya amsa mata da kulawa yana tambayar jikinta. Tace masa da sauƙi. Hankalinsa ya maida kan Dada yana magana. Sai kawai Dadan ya miƙe alamar yafi son suyi maganar a waje. Dole Faro ya take masa baya suka fitan. Nimrah ta bisu da idanu abu na tsaya mata a maƙoshi. Dan taso maganar da Faro ɗin ya fara ayita a gabanta ƙwarai da gaske. Amma yanda Dadan yayi sai maganar mutanen can ta sake samun gurbin tasiri a zuciyarta.      Fin mintuna talatin da fitar tasu, tun tana saƙe-saƙe har barci ya fara ɗibarta a hakan. Koda Dada ya dawo bataji motsinsa ba. Shima daya ƙaraso ya ɗan zuba mata idanu daga tsayen da yake, kafin ya duƙo kanta a nutsensa cikin rashin gaggawa ya fara gyara mata kwanciya. Ya rufa mata bargo zai janye jikinsa caraf ta riƙe hannunsa kawai ta juya kwanciyarta ta kwantar da fuskarta akan tafin. Da wani irin ƙarfi ta sauke ajiyar zuciya. Shi sai abin nata ma yaso bashi dariya. Amma sai ya gimtse yana kallon kyakkyawan fuskarta da hannun nasa. Kaɗan yay ƙoƙarin janye wa ta sake cikukukyesu ta matse har tsintsiyar hannun na kwanciya a ƙirjinta. Hakan ya saka shi kaiwa zaune dole. Received at 10:47A ransa kam ayyanawa yake (Yarinyar nan tana da son tada zaune tsaye fa) a fili kam lips kawai ya ɗan damtse da haƙori. Vibration da wayarsa keyi ya tilasta masa buɗe idanunsa dake rufe. Dole yay amfani da hannunsa na haggu. Ganin Mammah ya sashi ɗagawa.      Yanda yay sallama muryarsa a ƙurya gashi tana shaƙewa ya saka Mammah faɗin, “Lafiya dai?”.         Gefen fuskar Nimrah ya ɗan zubama idanunsa da launinsu ya canja. Kamar Mammah na kallonsa ya girgiza kai kaɗan. “Ba komai Mammah. Har yanzu baki kwanta ba?”.            “Yanzu dai nake shirin kwanciyar. Ina fatan dai kunci abincin ko?”.        “Tasha tea tasha magani har tayi barci. Nima yanzu zanci. Dan ALLAH ki kwanta ki huta Mammah. In sha ALLAHU da safe da wuri zan kawo miki kayar ki”.         Murmurshi Mammah tayi har yana iya jiyo sautinsa. Ta ce, “To ALLAH ya tashe mu lafiya. Kadai ci abincin kaima. Sannan kai mata addu'ar barci, dan ALLAH kada kai nisa da ita wani ya sake sace min ita”.       Kaɗan ya rage yayi dariya. Ya dai daure ya murmusa kawai. Yana yanke kiran ƙasa-ƙasa ya furta, “Ni ai gashi nan tana neman sace ni idan ita wani bai sace miki ita ba Mammah.”      Tamkar Nimrah ta jishi ne, tai juya kwanciyarta zuwa rigingine. Har yanzu dai hannun nasa bata saki ba, sai ma gyara shi tai akan ƙirjinta ta rungume sosai kamar wadda ta samu filo. A yanzu kam ya fahimci dukan zai masa yawa. Dan an kai wani matsaya ne na ga mari ga tsinka jaka. Ba arziƙi yay dabarar janye hannunsa, zata warto ya warce abinsa yana miƙewa. Yafi ganewa ƴar nesa-nesa, in ba haka ba za'ayi ja ya faɗo ja ya ɗauka ne a asibitin mutane....       =============       Gaba ɗaya ran Nabeeha a dagule yake. Ta rasa inda zata tsoma ranta taji sanyi. Ga Ismat tayi tafiyarta saboda taji haushi ta bata shawara taƙi ɗauka. Ko yanzu datai ma wata ƙawarta rakiya da tazo wai tayata murnar dawowar Dada sai da ta sake tambayar maigadi yace ƴan gidan har yanzu suna asibiti babu wanda ya dawo.       Haka ta zauna ta zabga tagumi komai baya mata daɗi. Kewarsa take ji mai tsanani, so take ta ganshi cikin idanunta ta tabbatar gaskiya ne ya dawo. So take ta jita a cikin jikinsa kota samu nutsuwar shekara takwas da rabi data rasa. Amma sai ƙwalelen ɓoye kansa yake a gareta. Shin har yanzu yana fushi da ita ne? Miyasa bai nemeta ba? A tunaninta yana fitowa ita zai so fara gani duk duniyar nan. Amma sai taji saɓanin haka. Miyasa Haysam zai mata haka? Shifa ya mata laifi mai girma... Kiran daya shigo mata ne ya katse tunaninta. Ta sauke ajiyar zuciya tana ɗaukar wayar ganin Momy ce.       “Momy wlhy har yanzu fa bai dawo gidan ba. Suma kuma duk suna asibiti wai”.       Ta ɗan yi shiru alamar sauraren ɗayan ɓangaren.     “Ni gaskiya bana son zuwa asibitin, ai saina koma warin magani”.            “Shi ke nan naji Momy zanje goben”.       Bayan katsewar kiran ta harari wayar tana ƙunƙuni. Dan zuwa yanzu ta fara fahimtar akwai abinda Momy ke nema ne. Inba haka ba har itace ke mata faɗa akan ƴan uwan Haysam. Bayan da itace ke zugata ma akansu. Baki ta taɓe tana miƙewa ta wuce bedroom, dama a falo take.....              <%><%><%><%><%>          Barcinta yay nauyi sosai ta yanda yake jin saukar numfashinta na sauka a hankali. Dan haka ya sakama ƙofar key ya cire kayansa domin yin wanka. Dan gaba ɗaya a takure yake, kayan sun damesa ainun. A hakan ma ya canja su daga kakin da akai gumurzu a jejin can. Wanka ya fara gabatarwa yayo alwala. Koda ya fito jallabiyar da Dabo ya sayo masa ya saka, yay shafa'i da wutri sannan yay zaman shan tea da abinci kaɗan dan yunwa yake ji sosai. Duk da yanda ya cisa kaɗan sai da yaji ya takura, dan shi ƙa'idarsa baya wuce 8 na dare baici abinci ba. Amma gashi yau har kusan 12 ma ake magana. Yanayin takurar da abincin yay masa ya sashi buɗe ɗakin ya fita, ɗakin Imran ya leƙa, shima barci yake akwai kuma Yusuf a tare da shi. Sai kawai ya dawo wajen Nimrah. A cikin ɗakin ya gabatar da push-up da shi kansa bai san adadi ba, dan mintina kawai ya saita, suna cika ya miƙe yana sauke numfashi, a kujera ya zauna yasha ruwa, sannan ya kwantar da jikinsa ya lumshe idanunsa. Received at 10:47Sai da jikinsa ya daidaita ya ɗauka laptop ya fara sana'ar tasa, duk da dai akan aiki ne...       Kusan 1:am Nimrah ta farka a firgice har tana neman faɗowa a gado. Cikin zafin nama ya miƙe ya tareta, gaba ɗaya zufa ta jiƙeta, ga jikinta na rawa tana sambatu. Dole ya sakata a jikinsa ya rungume ta ya fara mata addu'a. Ƙafafunsa ne suka fara dayi, dole ya zame ya zauna a gadon jiyyar tata, har lokacin kuma tana a jikinsa. Ƙoƙarin kwantar da ita yay amma ta ƙanƙamesa har tana ƙunƙunin kuka a cikin barci. Babu yanda ya iya dole ya barta, sai ma zama daya gyara ya sakata a tsakanin ƙafafunsa shi kuma ya jingina da filo. Kanta na saman jikinsa ta zagaye cikinsa da hannayensa duk biyu. Hakan yasa numfashinsa ke sauka a saman cikinsa..........✍️ Received at 10:47 AM [14/02, 9:15 am] Abue Saleh: 10 ........Iska yaɗan furzar kawai ya ɗauki laptop ɗinsa ya cigaba da aikinsa. Shima zuwa 1:47am idanunsa suka fara yajin barci. Dole ya rufe Laptop ɗin ya zama a hankali ya kwanta a gadon duk da ya musu kaɗan, sai dai ya tabbatar yace zai tashi wata sabuwar futinarce kuma. Dan shi kam lamarin Nimrah da rigimarta sun fara fin ƙarfinsa. Aiko kamar abinda take jira kenan. Mutuniyar ku sai aka sake gyara kwanciya a jikin Dada ɗare-ɗare.          Addu'a yayta ambata duk wadda tazo bakinsa. Har ALLAH ya taimaka tarzomar dake neman turniƙewa ta lafa cikin amincin ALLAH, daga haka shima barcin yay gaba dashi saboda yana jinsa sosai. Kiran sallar farko ya farka, baya buƙatar farkawarta taga a yanda suke kwance, dan haka cikin dabara ya zameta a jikinsa ya kwantar da ita a tsakiyar gadon yana gyara mata blanket shi kuma ya sauka. Duk yanda yaso tashi kasawa yay, sai da ya jinkirta zaune a bakin gadon hannunsa ɗaya dafe da kansa, ɗayan riƙe da cikinsa daya ƙulle masa tamau, ya ja mintuna a haka har ya ɗan sarara sannan ya miƙe zuwa bayi. Bayan wasu mintina ya fito yana goge kansa zuwa wuya alamar jiƙashi yayi, dan jallabiyar jikinsa ma ta nuna hakan kasancewarta coffee color. Sauri-sauri ya ƙarasa kimtsawa ya tafi masallacin cikin asibitin.... Kan Nimrah neman tarwatsewa yayi da mamakin ganin alamar fa Dada a ɗakin ya kwana. Duk da sai da ya dawo salla massalaci ya tashe ta. Daga yanda take zaune a bakin gado ta zubama ƙasan farar jallabiyar jikinsa idanu. Dan ba itace a jikinsa jiya da daddare ba.       Gyaran muryar da yay ya saka ta ɗagowa gaba ɗaya ta kallesa. Sai kuma tai saurin kauda idanun nata dan shima ita yake kallo. Miƙewa tai kamar wadda ƙwai ya fashe ma a ciki ta nufi toilet dake a cikin ɗakin. Dan ɗaki ne guda da gado guda biyu kacal, komai na buƙata akwai a cikinsa har fright. Abinda ya bata mamaki ɗayan gadon babu alamar an kwanta akai, shiyyasa taketa wasiwasin a ina to ya kwana shi? Badai a zaune a kujerar nan ba?. Bata da mai bata wannan amsar, dan haka ta fito a bayin, daga inda take ta ɗan ɗago ido ta saci kallonsa, tana ganin zai ɗago tai saurin maidawa gefe.         Shima dake binta da kallo ta gefen ido janyewa yay ya maida kan Alkur'anin hannunsa. Bata wani jimaba ta fito, sallayar data gani shimfiɗe alamar shi yay amfani da ita ta hau bayan ta ɗauki hijjab data gani ta saka. Koda ta idar sai da tayi har azkar sannan ta miƙe a wajen. Sum-sum ta iso inda yake, kanta a ƙasa takai duƙe a ƙasa kusa da shi tana faman cuɗa yatsunta cikin juna.           “Dada ina kwana”.      Idanunsa ya ɗago a slowly daga kan Alkur'anin ya zuba mata su, cike da nazarinta yake kallon hannun da take cuɗawa cikin juna. Ita kuma jin shiru bai amsa ba ta sake maimaita gaisuwar tana ɗagowa da nufin satar kallonsa sai suka haɗa ido. Rasama ya zatai tayi sai kawai ta tura baki gaba.        Ɗan motsi lips ɗinsa sukai kamar mai shirin yin murmushi. Sai dai baiyi ɗin ba. Alkur'anin ya rufe ya ajiye a drawer gefen gadon jiyyar tata. Babu zato kawai taga ya miƙa mata hannunsa dake fari tas, ga faratan a gyare sai sheƙi suke fes-fes da su. Nata hannun ta kalla, sai kuma ta sake kallon nashi tana ƙoƙarin noƙe nata..        “Baƙya son mu samu ladan musabaha Kiddo?”.        Wani irin yuuuu Nimrah taji tun daga yatsan ƙafarta har tsakiyar kanta sakamakon yanda Dadan yay magana muryarsa a shaƙe, gashi ƙasan maƙoshi kamar mai raɗa. Ya kuma kamo hannun nata cikin nasan harda ɗan matsawa yanda ya sata dole ɗagowa ta kallesa. Shima kallon nata yake da wani irin yanayi data kasa fassarawa, ya kuma riƙe idanun nata cikin nasa ta kasa janye wa.       Ruwa idanun nata suka fara tarawa, har yana iya ganin ƙyallinsu. Lips ɗinta na rawa kamar zata fashe masa da kuka ta ce, “Dadahhhh”.             Idanun nasa ya janye daga cikin nata. Sai kuma ya janye hannun batare daya amsa kiran da tai masan ba ya koma cikin kujerar da ƙyau ya gyara zamansa. Sai da ya tabbatar abinda ke masa kai-kawo a maƙoshi ya koma ya kwanta sannan yay magana cikin dakewa. Received at 10:47 AM [14/02, 9:15 am] Abue Saleh:          “Yaya jikin naki?”.     Sharrr hawayen da ita kanta bata san na miye ba suka zubo mata. A haka ta furta, “Na warke”.     Kallonta yay da mamaki. Ganin kuka fa take bil-haƙƙi abinta.  Sai kawai yakai hannu ya shafa kwantaccen gashin fuskarsa. Itama dai-dai tana miƙewa zata bar wajen. Hannunta ya riƙo kawai ya dawo da ita, sai dai yanzu tana daga tsaye ne tana sharɓar hawaye taƙi kallonsa.           “Negar! bana son kukan banza fa. Ko kina son bugu ne?”.      Kafaɗa ta maƙe masa tana ƙara matso hawayen.           “Wani guri na miki ciwo ne?”.    Nan ma kafaɗar ta noƙe. Jimm yay yana kallonta, sai kuma ya sake faɗin,          “Mi kike so?”.      Yay maganar yana matso da ita sosai jikinsa ta sake duƙawa cike da lallashi, har tana ɗora hannunta saman cinyarsa bata farga ba.         Cikin rawar murya tace, “Ina jin tsoro”.      Wani irin motsawa zuciyarsa tayi, ya dai dake ya furta, “Tsoro dai? Na miye?”.    Kuka ta sake fashe masa da shi taƙi magana. Sai kawai ya miƙe itama ya miƙar da ita ya sakata a jikinsa ya rungume. Daburcewa tai gaba ɗaya, dan abin yazo mata a bazata. Kodan jiya ba cikin hankalinta take ba duk bata san mita dinga masa ba da yanda shima yayta rungumeta.               “Kar kiji tsoro Kiddo. Matsoraci baya zama gwani. Kiyi addu'a, amma miyasa kike jin tsoro? Sun miki wani abu ne?”.         Kanta dake kwance a jikinsa ta girgiza.      Ɗagota yay ya zaunar a bakin gadon, ya matso kujerar sa kusa da ita sosai har jikinta na gogar nashi, dan ƙafafunta ma tsakiyar nashi ƙafafun daya ɗan wara suke. Idanunsa a kanta, hannayensa cikin nata ya ce, “Faɗa min tsoron mi kike ji?”.         Ta kasa danne abin, dan ya tsaya mata a rai matuƙa har zuciyarta da ƙwaƙwalwa sun kasa ɗauka kamar sauran abubuwan. Tana kuka sosai ta ce, “Dada sun ce an min aure. Da wani mutumi”.          Wani irin Bimmmb!! Yaji zuciyarsa ta bada sauti. Ya danne da ƙyar yace, “To shine abin kuka Kiddo. Dama duk mace dole tai aure ai ko?. Kuma kema ai kin girma.”       “Dada ni dai zan zauna wajen Mammah ta. Ban girma ba. Ba'aina Small Mom aure ba da su Uncle Billa sai ni”.      Murmushi yayi kaɗan a ransa yace (Kiddo ki illatani har duniya tasan halin da nake ciki kawai ki huta). A zahiri kam ɗan gyaran murya yay da faɗin, “A'a Kiddo, zama wajen Mammah kam na lokaci ne. Sai dai randa na aurar daku halan da Mammah zaki tafi?”.        Jin abinda ya faɗa ya sata kallonsa, ganin ita yake kallo tai saurin janye wa tana shagwaɓe fuska da faɗin, “Ni bazan yi auren ba fa kwata-kwata bana so Dada?”.        Idanunsa ya ɗan waro waje shima kamar yanda ta waro masa nata a furucin ƙarshe. “Kice malam gari su fara addu'a, Kiddo bata san aure ai asirin Dada ya gama tonuwa”.           Kunya ce taji ta kamata a karo na farko, duk da dai dama dakewa kawai take tun ɗazun, dan maganar ta mata nauyi, amma tana son ta amayar ko zataji sauƙin nauyin da ƙirjinta yayi saboda girman ta a ranta. Tasa ɗayan hannuta ta rufe idannunta tana haɗiye ƙwallar da suka sake cika mata ido. Shima da yanayin ya fara masa tasiri sai ya gyara zama yana ɗan matsa hannunta da har yanzu ke riƙe a cikin nashi.      “Uhmmm faɗa min miyyasa. Kinga idan naji dalilin ki mai ƙarfi ne sai nima na yarda bazan miki auren ba. Kawai muyi zaman mu muna cin tuwon Mammah kullum”.          “Ai banda kai. Tunda kana da mata”.     Ɗan tsai yay yana kallonta cike da nazari. Sai kuma ya basar da faɗin, “Waya gaya miki?”.           “Na sani ai. Ba itace ta taɓa yankamu ba, ga tabon a cinya na ma. Ranar ma kuma ta dawo sunyi jere a part ɗinka itada masu kama da karuwan nan.” takai ƙarshen maganar tana yaye rigar jikinta cinyarta ta bayyana. Da sauri ya haɗiye yawun dake neman sarƙe shi, ya ɗan zubama tabon da ya zama dogo sosai idanunsa da suke rinewa, ga yanda fatar jikinta ke wani sheƙi da kwanciyar ɗaukar idanun mai kallo ya saka tsigar jikinsa tashi. Yanda yanayinsa ke canjawa yasa shi kai hannu da kansa yaja rigar ya maida mata. Received at 10:47 AM [14/02, 9:15 am] Abue Saleh: Cikin rashin damuwa ta gyara zama da faɗin, “Dada kaga nasan kana da mata ko?”.      A ransa yace (Wata sabuwa, wannan ficikar fa da wayonta) a zahiri kam sai ya basar ta hanyar faɗin, “Shike nan ke faɗa min miyyasa baƙya son kiyi?”.           “Saboda bana son na bar Mammah da su Uncle's, da Ruky. Da Daddy, da su Ammie. Nafi son muyita zaman mu a haka lullum-kullum muna jin daɗin mu, muna hira. Dada ƙarya suke ai ba'a min aure ba ko?”.      Ji yay kamar ya kwashe da dariya saboda yanda tai tambayar cikin marairaicewa, amma ya gimtse abarsa “Uhmm ƙila da gaske suke yi dai, amma miyasa baki tambaye su waye mijin ba to tun acan?”.         Baki ta sake turawa. “Wai sunce assignment ne naje na bincika kai ko Mammah zaku faɗa min”.          Maimakon ya bata amsar sai ya waske da faɗin, “To amma ai naga kina son yara sosai. Kuma sai anyi aure ake haifar yara ai ko, yaya zakiyi kenan?”.          Yanzu kam har cikin ranta ta ce, “Dada baga su Afrah ba. Kuma su Ammy suna ƙara haifo mana wasu, ai sun ishe mu mu duka.” “Duk da haka kema zamu so ni da Mammah da Uncles ɗinki muga naki ai”. “To kawai basai na haife su a haka ba?”. “Babu auren?”. Ya faɗa cikin ɗan waro idanu. Kawai sai abin ya bama Nimrah dariya, ta shiga ƙyalƙyalawa. Shi kuma ya shagala kawai yana kallonta. A ranta ko rayawa take (Dada fa kallon ƴar yaye yake min ko? Bari muje a hakan to). Sai da tai dariyarta sosai sannan ta jinjina masa kai. Kai tsaye ta ce, “Eh, ai ko bakai aure ba idan malamai suka maka addu'a sai kawai kaga ka samu Baby”. Samun kansa yay da tsareta da idanu kawai. A ransa yace (Zakiga malamai kuwa yarinya, harda ma masu addu'ar saukar aljanu nan kusa kaɗan).........✍️ 🤣🤣Zamu so ganin malam saukar aljanun nan kuwa Dada🥱🤭. Received at 10:47 [14/02, 9:17 am] Abue Saleh:          “Yaya jikin naki?”.     Sharrr hawayen da ita kanta bata san na miye ba suka zubo mata. A haka ta furta, “Na warke”.     Kallonta yay da mamaki. Ganin kuka fa take bil-haƙƙi abinta.  Sai kawai yakai hannu ya shafa kwantaccen gashin fuskarsa. Itama dai-dai tana miƙewa zata bar wajen. Hannunta ya riƙo kawai ya dawo da ita, sai dai yanzu tana daga tsaye ne tana sharɓar hawaye taƙi kallonsa.           “Negar! bana son kukan banza fa. Ko kina son bugu ne?”.      Kafaɗa ta maƙe masa tana ƙara matso hawayen.           “Wani guri na miki ciwo ne?”.    Nan ma kafaɗar ta noƙe. Jimm yay yana kallonta, sai kuma ya sake faɗin,          “Mi kike so?”.      Yay maganar yana matso da ita sosai jikinsa ta sake duƙawa cike da lallashi, har tana ɗora hannunta saman cinyarsa bata farga ba.         Cikin rawar murya tace, “Ina jin tsoro”.      Wani irin motsawa zuciyarsa tayi, ya dai dake ya furta, “Tsoro dai? Na miye?”.    Kuka ta sake fashe masa da shi taƙi magana. Sai kawai ya miƙe itama ya miƙar da ita ya sakata a jikinsa ya rungume. Daburcewa tai gaba ɗaya, dan abin yazo mata a bazata. Kodan jiya ba cikin hankalinta take ba duk bata san mita dinga masa ba da yanda shima yayta rungumeta.               “Kar kiji tsoro Kiddo. Matsoraci baya zama gwani. Kiyi addu'a, amma miyasa kike jin tsoro? Sun miki wani abu ne?”.         Kanta dake kwance a jikinsa ta girgiza.      Ɗagota yay ya zaunar a bakin gadon, ya matso kujerar sa kusa da ita sosai har jikinta na gogar nashi, dan ƙafafunta ma tsakiyar nashi ƙafafun daya ɗan wara suke. Idanunsa a kanta, hannayensa cikin nata ya ce, “Faɗa min tsoron mi kike ji?”.         Ta kasa danne abin, dan ya tsaya mata a rai matuƙa har zuciyarta da ƙwaƙwalwa sun kasa ɗauka kamar sauran abubuwan. Tana kuka sosai ta ce, “Dada sun ce an min aure. Da wani mutumi”.          Wani irin Bimmmb!! Yaji zuciyarsa ta bada sauti. Ya danne da ƙyar yace, “To shine abin kuka Kiddo. Dama duk mace dole tai aure ai ko?. Kuma kema ai kin girma.”       “Dada ni dai zan zauna wajen Mammah ta. Ban girma ba. Ba'aina Small Mom aure ba da su Uncle Billa sai ni”.      Murmushi yayi kaɗan a ransa yace (Kiddo ki illatani har duniya tasan halin da nake ciki kawai ki huta). A zahiri kam ɗan gyaran murya yay da faɗin, “A'a Kiddo, zama wajen Mammah kam na lokaci ne. Sai dai randa na aurar daku halan da Mammah zaki tafi?”.        Jin abinda ya faɗa ya sata kallonsa, ganin ita yake kallo tai saurin janye wa tana shagwaɓe fuska da faɗin, “Ni bazan yi auren ba fa kwata-kwata bana so Dada?”.        Idanunsa ya ɗan waro waje shima kamar yanda ta waro masa nata a furucin ƙarshe. “Kice malam gari su fara addu'a, Kiddo bata san aure ai asirin Dada ya gama tonuwa”.           Kunya ce taji ta kamata a karo na farko, duk da dai dama dakewa kawai take tun ɗazun, dan maganar ta mata nauyi, amma tana son ta amayar ko zataji sauƙin nauyin da ƙirjinta yayi saboda girman ta a ranta. Tasa ɗayan hannuta ta rufe idannunta tana haɗiye ƙwallar da suka sake cika mata ido. Shima da yanayin ya fara masa tasiri sai ya gyara zama yana ɗan matsa hannunta da har yanzu ke riƙe a cikin nashi.      “Uhmmm faɗa min miyyasa. Kinga idan naji dalilin ki mai ƙarfi ne sai nima na yarda bazan miki auren ba. Kawai muyi zaman mu muna cin tuwon Mammah kullum”.          “Ai banda kai. Tunda kana da mata”.     Ɗan tsai yay yana kallonta cike da nazari. Sai kuma ya basar da faɗin, “Waya gaya miki?”.           “Na sani ai. Ba itace ta taɓa yankamu ba, ga tabon a cinya na ma. Ranar ma kuma ta dawo sunyi jere a part ɗinka itada masu kama da karuwan nan.” takai ƙarshen maganar tana yaye rigar jikinta cinyarta ta bayyana. Da sauri ya haɗiye yawun dake neman sarƙe shi, ya ɗan zubama tabon da ya zama dogo sosai idanunsa da suke rinewa, ga yanda fatar jikinta ke wani sheƙi da kwanciyar ɗaukar idanun mai kallo ya saka tsigar jikinsa tashi. Yanda yanayinsa ke canjawa yasa shi kai hannu da kansa yaja rigar ya maida mata. Received at 10:47 AM [14/02, 9:17 am] Abue Saleh: Cikin rashin damuwa ta gyara zama da faɗin, “Dada kaga nasan kana da mata ko?”.      A ransa yace (Wata sabuwa, wannan ficikar fa da wayonta) a zahiri kam sai ya basar ta hanyar faɗin, “Shike nan ke faɗa min miyyasa baƙya son kiyi?”.           “Saboda bana son na bar Mammah da su Uncle's, da Ruky. Da Daddy, da su Ammie. Nafi son muyita zaman mu a haka lullum-kullum muna jin daɗin mu, muna hira. Dada ƙarya suke ai ba'a min aure ba ko?”.      Ji yay kamar ya kwashe da dariya saboda yanda tai tambayar cikin marairaicewa, amma ya gimtse abarsa “Uhmm ƙila da gaske suke yi dai, amma miyasa baki tambaye su waye mijin ba to tun acan?”.         Baki ta sake turawa. “Wai sunce assignment ne naje na bincika kai ko Mammah zaku faɗa min”.          Maimakon ya bata amsar sai ya waske da faɗin, “To amma ai naga kina son yara sosai. Kuma sai anyi aure ake haifar yara ai ko, yaya zakiyi kenan?”.          Yanzu kam har cikin ranta ta ce, “Dada baga su Afrah ba. Kuma su Ammy suna ƙara haifo mana wasu, ai sun ishe mu mu duka.” “Duk da haka kema zamu so ni da Mammah da Uncles ɗinki muga naki ai”. “To kawai basai na haife su a haka ba?”. “Babu auren?”. Ya faɗa cikin ɗan waro idanu. Kawai sai abin ya bama Nimrah dariya, ta shiga ƙyalƙyalawa. Shi kuma ya shagala kawai yana kallonta. A ranta ko rayawa take (Dada fa kallon ƴar yaye yake min ko? Bari muje a hakan to). Sai da tai dariyarta sosai sannan ta jinjina masa kai. Kai tsaye ta ce, “Eh, ai ko bakai aure ba idan malamai suka maka addu'a sai kawai kaga ka samu Baby”. Samun kansa yay da tsareta da idanu kawai. A ransa yace (Zakiga malamai kuwa yarinya, harda ma masu addu'ar saukar aljanu nan kusa kaɗan).........✍️ 🤣🤣Zamu so ganin malam saukar aljanun nan kuwa Dada🥱🤭. [16/02, 10:58 pm] null: KIƊA A RUWA 3 11 .........“Amma mutanen nan ƴan iska ne Haysam. To taya ma suka san ka auri Nimrah? Nifa abin nan na bani mamaki”. Dada dake zaune a kujerar kusa da gadon jiyyar Daddy Imran ɗin yaɗan furzar da iska yana jan ƙaramin tsoki. “Imran ba abin mamaki bane dan nasan mutanen nan dama dole suna zagaye damu. Kawai yanda suka gaya mata wannan zancen ne sai na fahimci akwai manufa, akwai kuma abinda suke son isarwa ga yarinyar musamman da suka ce taje ta bincika mijin da kanta...” “Tabbas nima na fahimci hakan, tunda kaga harta kasa riƙewa ta faɗa maka. Indai haka ne to ya kamata mu zauna da ita a mata bayani. Dan a yanzu ni kaina banga amfanin cigaba da ɓoye mata kai mijinta bane. Sannan dolene fa ta koma kusa da kai gaskiya.....” “Imraaan!”. “Haysamm!”. Shima ya tari numfashinsa. Sai kawai suka zubama juna idanu. Babu wasa sam a idanun Daddy Imran ya cigaba da faɗin, “Wai mi kake shakku ne? A tunaninka Nimrah bata san komai bane? Kana ganin lafiya-lafiya idan tana hannun iyayenta ne zuwa yanzu basu jima da mata aure ba, maybe ma ta haihu to wlhy. Balle yanzu da a cikin birni take tana samun abinci mai ƙyau. Ni bance dole sai ka kasance da ita ba, amma ta zama kana sanin duk motsinta tunda har mutanen nan suka fara da wannan salon. Sannan karka manta Nabeeha ma ta dawo gidan a yanzu. Ita kanta idan taga kana cigaba da ɗaukar Nimrah yarinya har yanzu zata tsiro maka da wasu fitinu ne. Amma idan ta tabbatar da fa da gaske kake shike nan sai kowa tai yaƙin kanta. Kaifa kake gaya min yanzu Nimrah ta gama faɗa maka tasan kana da mata, harma bata manta ta yanke ta ba. To kasan waye Nimrah kuwa a rashin ji? Har yanzu ƙananun ayyukansu kake gani wlhy, amma tunda har bata manta wannan batun yankan ba ni nake faɗa maka sai tayi wani abu.....” Yanda Dada ke masa kallon mamaki yasa shi yin ƴar dariya. “Hummm sa wasa, kai dai ka saka ido kawai a kanta. Amma kasan ALLAH Nimrah Zakanya ce ta gaske. Kawai sauƙin abun tana shakkarka ne tunda baƙo kake a idanunta har yanzu. Amma ka ma shirya, dan in dai tsoro ne Nimrah bata san wani abu wai shi tsoro ba”. Hararasa Dada yayi da faɗin, “Duk baku kuka ɗaure mata take yi ba. Yanzu haka idan ta sakani gaba da fitina rasa ma abin yi nake yi. Ina ga ta dawo kusa dani, ai wannan aikin ma bazai yiwu ba, dan bazan iya haɗa rikicinta da aikina ba gaskiya. Kana maganar ta girma, to yanzu take cemin ai idan malamai sukai addu'a ko ba'ai aure ba ana samun Baby, ina hankali anan Imran?”. Duk yanda Daddy Imran yaso gimtse dariyarsa ya kasa, sai da yayi mai isarsa. Sai kawai Dadan ya kuma zuba masa harara. “To miye abin dariya anan kuma?”. “To kai miye na tsarguwar? Ko kaji nace wani abu?. Tunda dai in malamai sukai addu'a ana samun Babyn kai ba sai ka zama Malamin nata ba. Miye abin wahala a ciki ba koyar da karatu bane kawai ta fahimci baƙaƙe da wasilla”. “Wlhy kaji kunya uban banza”. Dada ya faɗa yana miƙewa ya nufi hanyar fita. Shima Imran miƙewar yayi yana ƙyalƙyala dariya dan an sallamesu har Nimrah ɗin ma. Duk da bakwai sun zama normal bane gaba ɗaya musamman ma shi mai rauni akai. Kawai dai zaman asibitin ne bashi yiwuwa a wannan gaɓar..... ©©©©©©©©© A ɓangaren shugaban ƙasa Yusuf Shu'aibu Tafida ƴan jam'iyya sun bala'in saka rayuwarsa gaba ta ƙarƙashin ƙasa akan naɗin muƙamai. Dan tun suna ƴar percentage har sun fito masa ƙuru-ƙuru da sunayen waɗan da suke buƙatar a bana manyan muƙamai. Hankalinsa ya tashi, duk da kuwa wanda suka kawo ɗin shi bazai ce suna da wani baƙin hali na zahiri bane. Amma a muƙaman da suka riƙe a baya a bayyane take su masu rauni ne ga sauke haƙƙokin talakawa. Babu abinda suke yi sai raya kansu da iyalansu da dukiyar ƙasar. Shiyyasa babu wani ayyukan cigaba na zahiri da suka fito daga yankunan su a sanda suke mulki na shugabanci ko na wani office da suka riƙe. Received at 12:22 PMReactions: Rasa wazai tunkara yay shawara yayi. Gashi kwanaki uku kacal suka bashi. Yau hatta office yaƙi fita da wuri har kusan sha ɗaya. Wani gefe na zuciyarsa keta kawo masa Zak-Shadow da Imran. Kuma tabbas yana jin gamsuwa da yaran. Dan wannan rikitaccen mulkin baya yiwuwa sai da ɓoyayyun mashawarta. Wlhy badan fidda Haysam da yayi ba da yace shi wannan mulki baiga amfaninsa ba, dan rikicin cikinsa da kitumurmura sun wuce tunanin mai tunani. Wanda ke waje shike kallon shugaban ƙasa a mai zartarwa sama da kowa. Amma a zahiri hotone kawai a kujerar mulki shugabancin ƙasar nan. Ainihin masu mulkar ƙasar suna gefe ne kawai suna busa sigari kalar wadda suke buƙata. Sai abinda suke so, sai abinda sukace dole za'ayi, idan kace zaka bijire su ƙasƙantar da kai a idon talakawan ƙasar a bayyane, a ɓoye su raunana lafiyarka da kuzarinka. Duk mai baka goyen baya su siyesa da kuɗi, idan yaƙi bi shima su ɓatar da shi ko su tsigesa a kusa da kai ɗin. Wannan itace zahirin ƙasar da talaka bai sani ba, wata shari'ar dai sai anje can kawai. Wayarsa ya ɗauka da mutane masu muhimmanci ne kawai a ciki yay gajeren text ya tura. Daga haka ya miƙe domin shirin fita office..... °°°°°°°°°°°°°°°°°°°° Saƙon shugaban ƙasa ya shigo wayar Dada ne a dai-dai lokacin da motar su ke hawa kan babban titi bayan fitowarsu a cikin asibiti. Dabo ne ke driving ɗin, gefensa Imran. A baya Nimrah sai Dada dake ta aiki da laptop a kusa da ita. Tana lafe ne jikin ƙofa idanunta a lumshe, ji take kamar tai tsuntsuwa ta ganta a gida saboda ɗoki. Duk da dai akwai ajiyayyar damuwa dake danƙare da zuciyarta da brain ɗinta. Amma kamar yanda tai alƙawari zata bi komai a sannu kamar yanda ta fara. Dan a yau ta sake fahimtar gane ainahin Dada ba abune mai sauƙi ba. Dole ta dake, dole ta shirya, dole ta jajirce, dole ta ƙara wayo da taka tsantsan. Sai dai duk da haka maganar auren nan na ɗaga mata hankali. Tana son taji tabbaci a bakin Mammah da sauran Uncles ɗinta da Daddy Imran. Harga ALLAH indai da auren nan batama san yanda zata fassara shiga ukun da take ciki ba. Waye wannan miji? Tana son ta sanshi, ta ƙagara ta sanshi. Duk halin da take ciki Dada na lure da ita. Dan yanda take yamutsa fuska, ta cije lips, ta matse idanu yasa shi fahimtar akwai abinda take tattaunawa da zuciyarta. Kuma ko minene yana da girma da rikitarwa a gareta. A lokacin da yake ajiye wayarsa dake tsakkiyarsu bayan kammala karanta saƙon Mr President sai yaga tasa hijjab ta share hawaye. Hakan ya sake tabbatar masa da zarginsa. Baiyi magana ba ya cigaba da aikinsa yana sauraren tattaunawar Imran da Dabo akan Ojo da suke ƙoƙarin gano inda yake yanzun... Gidan Daddy Imran suka fara zuwa domin sauke shi. Nimrah nason shiga taga Ammie tana kuma zumuɗin zuwa taga Mammah. Sai kawai ta saka a ranta tunda weekend za'a shiga zasu zo ita da Ruky. Isowar su gate ɗin nasu gidan sai taji ƙaguwar a buɗe, dan badan Dada bane a motar da tuni ta ɓalle murfin ta shiga da gudu. Amma jikinta sai tsuma yake ta yanda har shi ma ya gane. Aiko Dabo na tsayar da motar ta buɗe ta fice dan haƙurinta yakai maƙura. Dada ya bita da kallo kawai, dan kamar ƙyatawar ido har taje ƙofar falo. Kansa ya ɗan girgiza yana miƙama Dabo daya buɗe inda yake laptop ɗin daya rufe. Daga haka ya sakko ƙafafunsa ya fito gaba ɗaya. Sauran kayan Dabo ya tattauro, dai-dai kuma isowar maigadi da malam Buba dake noƙewa a baya wajen. Cikin girmamawa suka fara gaida Dadan. Dada ya janye idanunsa daga kallon da yay ma malam Buba na seconds, kafin ya amsa gaisuwar tasu. Suka ɗora da nuna farin cikin dawowar Nimrah, sunata ambaton godiyar ALLAH. Shi dai wajen yay ƙoƙarin bari. Amma sai maigadi ya miƙo masa abinda ke hannunsa yana faɗin, “Af naso na manta. Ranka ya daɗe dama ga saƙo yanzun nan babu jimawa wani ya kawo shi a baka. Dan zanje nakai ciki ne ma kuka iso na dakata buɗe muku ƙofa.” Received at 12:22 PM reacted with ❤ Idanu Dada ya ɗan zubama hannun maigadi, sai kuma ya miƙa hannu ya amsa batare da yace komai ba. Yana barin wajen Malam Buba ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi da har sai da maigadi ya kallesa. Kamar zai yi magana sai kuma yay shiru suka koma bakin gate. Sanda da ya shige ɗaki wufff tun buɗe gate da akai ya fito shima sum-sum yana leƙa hanyar sashen Mammah da har Dada ya shige.... Yanda Dada ya samu falon ya kacame da murnar ganin Nimrah sai yama tsaya kawai yana kallonsu. Dan Ruƙayya na rungume da ita tana kuka ana lallashinsu. Su duka biyun suna jikin Mammah. Mu'azz ma sai sharar hawaye akeyi na farin ciki. Shigowarsa tasa su Bilal dake zagaye da su maido hankalinsu kansa. Sai kuma duk suka zaburo cike da farin cikin ganinsa suma. Mammah kanta yau ta kasa dannewa kallonsa take farin cikinta a bayyane. Gwaggo Alawiyya tazo ta kama hannunsa tana faɗin, “Sannu kaji Haysam, ALLAH yay maka albarka. Maza zo ka zauna ansha fama kwana biyu”. Murmushi kawai yayi yana kaiwa zaune. Ya gaida Mammah sannan su Gwaggo Khadijah. Suma su Ja'afar suka gaisheshi. Kafin wani lokaci Aunty Mimi ta kawo masa ruwa. Dan suma duk suna gidan daga asibiti suke duba Lailah. Mammah tasan duk yanda suke son jin yanda aka samo Nimrah bazai faɗa ba, dan haka ta tambayesa a shirya masa abinci ne. Miƙewa yay yana amsa mata da zai yi wanka tukunna. Ya ɗan kalli Nimrah da Ruƙayya ke bama abinci a baki itama yana bata ya wuce abinsa. Dai-dai Ammar na sakkowa daga kai kayansa ɗaki da Dabo ya kawo. Umarnin kawo masa coffee ya bashi yana wucewa...........✍️ ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels WhatsApp Number: 09017242889 Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** [16/02, 10:58 pm] null: KIƊA A RUWA 3 12 .........“Aunty wlhy Dada ya dawo”. Zimbur Nabeeha ta tashi daga barcin da take yi tana kallon Rayhana mai maganar. Dan yanzu babu jimawa suka zo gidan ita da Amima. Iske Nabeeha na barci yasa sukai zamansu a falo suna kallo bayan sun saka mai aiki da suka zo da ita yanzun nan shiga kitchen ta musu abinci batare da ko matar gidan sun bari ta san da zuwanta ba. Momy ce tace su kawota kasancewar Nabeehar tayi mata complain a jiya game da aikin gidan. Tasan ragwantar Nabeeha sarai, ita kuma a wannan lokacin bata son a samu matsala kodan First Lady shiyyasa tai gaggawar samar mata da mai aikin, ko muce First Lady ta samar. “Aunty badai can ɓangaren zakije ba?”. “To mi kike so nayi Rayhana. Kin san dai mugayen can bazasu faɗa masa na dawo ba. Gara naje da kaina ya ganni.” “Hu'umm da dai kin bari ya kawo kansa wlhy. Amma kije ai babu aji, bayan kin san shegiyar yarinyar nan tare suka dawo. Ƙilama babu wani saceta da akayi shiyya ɗauketa yaje yasha shagalins.....” Kallon da Nabeeha ke mata ya hanata ƙarasa faɗa, sai kuma tace, “ALLAH ya baki haƙuri. Amma magana ta gaskiya yanzu fa ba da bace Aunty. Dole ne ki gyara wasu abubuwan musamman zumuɗin nan akansa.” tana gama faɗa ta fice a ɗakin. A ranta kuwa tana saƙa abinda ya daɗe a zuciyarta ne. Dan wannan karon tayi alwashin zatayi yaƙi domin kanta. Bazata iya haƙuri da ciwon dake ranta ba. Sai dai ayi ɗayan biyu. Kota samu, ko kuma kowa ya rasa... Nabeeha kuwa ƙwafa tayi kawai. Ta nufi bathroom. Babu jimawa ta fito fuskarta jiƙe da ruwa alamar wankota tayi. Gaban mirror taje ta fara gyara fuskar da kayan kwalliya, sannan ta cire kayanta ta canja da wani arnen lass da yay masifar ƙyau ta saka turare sosai a jikinta. Koda ta fito daga Amima har Rayhana da kallo suka bita. Amima data saki baki na mamaki ta ce, “Aunty ina zuwa haka da rana tsaka?”. “Sashen Mammah”. Ta bata amsa a taƙaice tana ficewa abinta. Kallon juna sukai ita da Rayhana, Rayhana ta taɓe baki da faɗin, “Kin san bata da wayo sam.” “To ALLAH ya ƙyauta wannan ai zubar da mutunci ne”. Cewar Amima... ()<>()<>()<>()<>() Tunda Nabeeha ta shigo falon kowa ya saki baki yana kallonta. Mammah kam kallo ɗaya tai mata ta ɗauke kanta. Koda ta gaisheta ma a haka ta amsa hankalinta akan Nawal ɗin Aunty Mimi. Su Ma'aruff da suka zo wuya zasuyi magana Gwaggo Khadijah tai musu gargaɗi da idanu. Dole sukai shiru. Sarai Nabeeha ta lura da yanayinsu, amma ta danne dan a ganinta basu bane a gabanta. Idanunta akan Mu'azz ta tambayesa ina Dada yake. Mu'azz ba komai ya sani game da lamarin Nabeeha ba. Duk da dai da wayonsa tabar gidan amma ba komai ya sani ba. Da hannu kawai ya nuna mata sama. Bakuwa ta sake magana ba, ba kuma kunyar kowa balle jin nauyi ta nufi stairscase ɗin tana taku ɗai-ɗai cike da gadara ita ga matar boss. Aunty Ummi dake jin kamar ta amayo zuciyarta dan takaici taja hannun Aunty Mommy suka shige kitchen bayan tama Mimi signal da ido. Fakar idanun su Mammah tai itama tabi bayansu. Basu wani jima ba suka fito, hannun Aunty Mimi da tray an haɗa kayan abinci akai. Cikin sa'a dai-dai nan Nimrah da Ruky da Biebah ke fitowa. Nimrah tayi wanka ta canja kayanta. Kuma wando ne fari daya kwanta a jikin nata da riga iya gwiwa Pakistan style na yadi mai taushi. Sai siririn gyale kalar yadin rigar. Babu wata kwalliya a fuskarta sai rosy lips data shafa daya saka lips ɗin taushi da santsi, yay pink sosai, ko daga nesa kake da ita zakaga hakan.... “Yauwa Nimrah zoki miƙama Dada abincinsa”. Aunty Mommy ta faɗa kai tsaye. Ɗagowa Mammah tai da sauri, ta buɗe baki zatai magana Gwaggo Alawiyya ta katseta da faɗin, “Dama yanzu zan yi magana kuwa. Amsa kinji ƴar albarka. Ruƙayya ke kuma zo nan na sakaki aiki”. Haɗa ido Mammah da Gwaggo Khadijah sukai, Mammah tayi yanayin kai ƙara gareta, amma sai Gwaggo Khadijahn ma tai mata murmushi alamar tana goyon bayan abinda ƴan ta kife ɗin ƴaƴanta ke shirin yi. Kanta ta girgiza kawai tana kallon su Ma'aruff, a mamakinta suma duk sun washe fuskoki ba kamar yanda suka ciskule ba tun shigowar Nabeeha. Received at 12:22 PM reacted with ❤ Nimrah dai da ba sanin abinda ya faru sukai ba tuni ta shagwaɓe fuska zata fara langare. Aunty Ummi ta balla mata harara dole tazo ta amshi tray ɗin. Wucewa tai tana ɗan tuttura baki, dan harga ALLAH tana son yin ɗan nesa da shi har sai taji amsar tambayiyinta akan batun nan ɗaya tak daya zame mata ƙayar kifi a maƙoshi.... A wannan lokacin da Nabeeha tuni ta iso ƙofar ɗakin na Dada bayan ta hauro taci karo da Afeef dake fitowa a ɗakinsu shi da Mu'azz ta tambayesa ya nuna mata. Knocking tayi a hankali, sai dai shiru babu motsi balle ta samu amsa. Sanin halinsa yasa ta sake yi har sau biyu, daga nan ta buɗe Kofar kawai ta shiga dan ta kasa daurewa. Da wani irin ƙamshi ta fara cin karo, dan ƙamshin turaren wutar SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. na Maman Abdull ya gama kama lungu da saƙo na sashen Mammah. Sai da ta lumshe idanu ta buɗe tana sauke ajiyar zuciya kafin ta ƙarasa shiga ɗakin. Ko ina fes a gyare, babu tarkace kamar yanda ta sanshi mutum mara son hayaniya. Jin motsi a bayi yasata zama a bakin gadon tana murmushi, babu abinda take hangowa sai yanda zaiyi mamakin ganinta da farin ciki. Ta sake gyara zamanta da ƙyau. A dai-dai lokacin kuma Nimrah data iso itama tai knocking ƙofar. Sai dai jin shiru da sanin halinsa na in ba shi yaso ba bazai tanka ba yasata murɗa handle ɗin ƙofar kawai ta tura ta shiga da sallama. Wani kalar zubo mata idanu Nabeeha da zuciyarta tai zallo cikin ƙirjinta tayi. Ta buɗe baki zatai magana tana ƙoƙarin miƙewa kawai aka buɗe ƙofar bathroom. Dada da bai san dasu ba su duka biyun ya ɗan yi tsaii yana kallonsu. Nimrah kam jitai ƙirjinta ya buga, a lokaci guda tai saurin duƙar da kanta. Gaba ɗaya ji take ta daburce, a hakan ma ALLAH ya sota bathrobe ce a jikinsa ba towel ba. Sai dai kuma abinda bata taɓa gani bane daga garesa dole ta rikice. Dan bathrobe ɗin ma dai kaɗan ta wuce gwiwarsa. Har cikin ransa bai ji daɗi ba shima. Idan Nabeeha ta ganshi a haka normal ne ai, amma Nimrah ina, da sauran lokaci. Jallabiya ya ɗauka batare da yayi magana ba ya juya cikin bayin. Babu jimawa ya sake fitowa da ita a jiki. Abinda ya bashi mamaki har lokacin Nimrah na'a inda ya barta. Kanta a ƙasa ga kaya a hannu kamar wadda aka dasa. Yayinda Nabeeha ke mata wani mugun kallo sai dai itama bata iya tayi magana ba saboda wani curarren abu daya dunƙule mata ƙirji ko numfashi bata fitarwa da ƙyau. Zuciyarta tsara mata take taje ta fisgi tray ɗin abincin ta kife mata shi a jiki, sannan ta kamata da shegen duka har sai ta daina numfashi. Kai itafa da tana da dama ko macen sauro bazata sauka mata a jikin miji ba.. Tana can tunanin ya kwasheta kawai sai hango Dada tayi a gaban Nimrah. Itama Nimrahn daba sanin isowarsa tai ba jin an riƙo tray ɗin hannunta ta ɗago da sauri alamar dawowa hayyaci, dan ya fahimci tsayuwar da tayi tunani ta tafi mai zurfi. “Kina lafiya?”. Ya faɗa cikin zurfin lafazi daya sakata jin wani sanyi ya dira tsakkiyar kanta yana bin jijiyoyin jikinta yana sauka har ƙafafunta. Slowly ta ɗago idanun da suka kaɗe sosai da ja a ciki, kasancewar shima ita yake kallo sai suka shige cikin nasan har sai da yaji wani dummmm a ƙirjinsa. Dai-dai lokacin Nabeeha ta matso kusa da shi, cike da salon daya ƙona ran Nimrah kawai ta rungume shi ta baya tana kwantar da kanta a faffaɗan bayan nasa. Cike da shagwaɓar iskanci ta furta, “I miss you baby”. Gefe Nimrah tai da fuskarta tana lumshe idanunta da suka cika da ƙwalla. Dan wani suka da ƙirjinta yayi zata iya rantsewa tunda tasan kanta bata taɓa jin irinsa ba. Gaba ɗaya taji duniyar ta mata ƙunci, wani irin tsanar Nabeeha da haushin Dadan suka zagaye ƙirjinta batare data san dalili ba. Bata motsa ba a wajen da take balle nuna alamar zata fita tabar ɗakin kamar yanda ta fahimci Nabeeha naso, sai ma ji tai a ranta saita baƙanta mata rai itama, sannan wlhy bazata bar ɗakin nan ba yau sai da su zauna su ukun, in banda iskanci da ballagazanci miye na wani rungumeshi a gabanta, ai ko ba komai shi uba ne, yakamata itama ta mutunta kanta a gabansu dan su bata irin darajar da suke bashi koda bata da ita Received at 12:22 PMa zahiri kamar shi. Amma tunda tace ita ta iya yanzu zata nuna mata shege ma da ubansa ba aruwa ake shawosa ba. ALLAH saita gogema matar nan hadda yanzun nan. Idan ita mijinta ne ai suma Babansu ne.........✍️ Tofa Madam Nimrah mutum da matarsa. Tunda kin yarda ita mijinta ne ku babanku ne basai ki fita ki barsu su jiƙa kansu ba🥱. Anya kuwa kikaji shine mijin ba akwai yaƙi ba? To bari muga ya wasan zai kaya a yanzu💃💃🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️☺️. Received at 12:22 PM [16/02, 10:58 pm] null: KIƊA A RUWA 3 13 .........Dada shi kansa jiyay wata kunya mai tsananin ta rufeshi. Haba shi girma abin a riƙe ne ai. Baiyi ma Nabeeha magana ba amma ya zame jikinsa daga nata, yana nufar kan center table ya ajiye tray ɗin abincin. Yazo ya sake raɓasu ya wuce gaban mirror, wayarsa ya ɗauka ya sake gittasu dai again ya koma kan sofa ya zauna. Nimrah dake ƙoƙarin controling ɗin kanta ta kalli ƙafafun Nabeeha dake tsaye itama kamar an dasata, da alama abinda yay ɗin ya ɓata mata rai ne ko wani abu oho mata. Kawai sai taji murmushi na neman kufce mata sakamakon abinda zuciyarta ta ayyana mata akan matar. Amma sai ta danne shi ya tsaya cikin ƙirjinta. Dada dake ƙoƙarin kai waya kunnensa ya ɗago ya kallesu, shi sai ma suka nema sakashi yin dariya. Ya dai gimtse baiyi ba, dan saima ƙara ɗaure fuska da yay cikin bada umarni ya furta, “Kiddo zoki bani abinci”. Duk da wani haushinsa da take ji saboda rungumar da Nabeeha tai masa sai ta jinjina kai tana nufarsa, dan kurama ai tasan gidan mai babbar sanda. A kusa da shi gab takai duƙe gaban table ɗin, ta bubbuɗe kwanikan abincin sannan ta kalleshi, duk da waya yake da Imran dan taji ya ambaci sunansa bata fasa faɗin, “Dada mi za'a zuba?”. Yanda tai maganar cikin raɗa da masa nuni da hannu tana wara masa idanunta manya ya sashi ɗan zuba mata nasa idanun. Sai da ta sake waro natan sosai ta ce, “Dadaaaah”. Sannan ya farga da abinda yake ya janye yana nuna mata da hannu. Ta jinjina kai ta fara zubawa, sai dai ta raba hankalinta a kallon Nabeeha da har yanzu ke tsaye inda suka barta tabbacin ta shaƙa da abinda yay mata. A cikin zuciya Nimrah tace (Tun banyi komai ba aunty masu miji) a zahiri kuwa sai da ta kammala zuba abincin tsaff kawai ta saka murfin kwanon tangaran ɗin da aka zuba salad ciki baki-bakin table ɗin da gangan ta kaɓoshi ya wantsalo ƙasa sai kuwa akan ƙafarta. Duk da dai tayi dabarar saka hannu sai da ya taɓa bisa tsautsayi. Zabura tayi cikin gigita sai kuma hannunta ya tsumbula cikin kular farfesu. Aiko ta fasa ƙarar data saka Dada sakin waya ya juyo kanta... Itako tuni ta miƙe a zabure ƙafar damƙe a hannunta ɗaya tana tsalle da ɗaya, hannun daya shiga miya kuma tana yarfa shi har tana neman faɗawa kan abincin nasa. Ba arziƙi ya tarota gaba ɗaya sai kawai ta faɗa saman cinyarsa. Anan kam harga ALLAH bata san kansa take ba, dan da gaske zafin ya ratsata har cikin kai, gashi bibbiyu hannu da ƙafa, dama ga Nimrah da shegen ragwantaka. Rasa ina Dada zai kama mata yayi, dan ita kanta Nabeeha sai da ta zaburo, sai kuma taja ta tsaya tuna wacece da kuma yanda ya riƙota jikinsa. Tai bala'in waro idanunta waje ganin ya kama hannun Nimrah kawai ya saka yatsun data saka a farfesu cikin bakinsa. Ɗayan hannun kuma ya riƙo ƙafar tata. Itama kanta uwar haɗa wajen tsittt tayi a karo na farko, dan abune da yazo mata a matuƙar bazata, bazatar ma mai gigitar da zuciya. Dan yanzu kam ta fahimci an sauka daga layin abinda tai niyyar aikatawa an tafi wani layin sabo data gagara bama suna ko kalma. Dada da shima sai yanzu ya fahimci halin da suke ciki sai ya runtse idanu, kafin ya buɗesu a hankali kan fuskar Nimrah data zuba masa nata idanun cikin yanayin ruɗani. Sai kawai suka sarƙe cikin juna, kamar kuma waɗan da aka hana motsi kowanne ya kasa janyewa suka shagaltu. Shagala a kallon juna irin yanda basu taɓa yi ba cikin idanu dai kamar haka..... ============= “Baƙo kuma?”. Hajiya Hasiba ta faɗa da mamaki tana kallon maigadi. Kansa ya jinjina mata. “Eh Hajiya. Kuma kamar ma baɗan ƙas.....” Ya kasa ƙarasawa sakamakon shigowar Adeel falon. Miƙewa Hajiya Hasiba tayi, dan ita kaɗaice a gidan su Amima na gidan Nabeeha. Cikin in-ina maigadi ya ce, “Ya....ya..yauwa Hajiya ai gama shi nan ya shig.....” Hannu ta ɗaga masa. Sai kuma tai masa nunin ya fita. Babu musu ya nufi hanyar ƙofa yana waigen Adeel. A ransa faɗi yake (Yau gani ga Balarabe ikon ALLAH) sai da ya kusa cin tuntuɓe ya dawo hayyacinsa... Received at 12:22 PM Adeel dake kallon Hajiya Hasiba fuska a ɗaure hannayensa duk a cikin aljihun wandonsa ya kai zaune cikin kujera cike da isa da gadara. Sai wani bin falon yake da kallo a yatsine. Duk da kuwa ba laifi falon ya haɗu, kuma a gyare yake tsaff ga ƙamshin air freshener na tashi. Sake maida idanun nashi yay a kanta. Da sauri ta fara gaishe shi murya na rawa. Maimakon amsa mata sai yaja siririn tsaki. Cike da wulaƙanci ya furta, “K! Nine zakima ƙaryar kinyi tafiya?”. “Wlhy ba ƙarya nake maka ba. A cikin satin nan na dawo. Kuma na nemeka amma ban samu ba. Ban san ka dawo ƙasar nan ba shiyyasa nake neman layin Abu-dabi.” “Mtsoww!” ya sake jan tsaki. Sai kuma ya sake watsa mata kallon banza. “Nayi alƙawari dake kin saɓa. Kince mijinta na prison na bincika ance ya fita. Baki zo kin min bayani ba saboda kina ɗaukata wawa....” “Wlhy ba haka bane Sir! Idan baka manta ba nata ƙoƙarin mu haɗu kafin kayi tafiyar farko. Amma hakan bai samu ba. Lokacin daka dawo nan ma naso hakan amma baka ɗaga kirana ba, sai daga baya nake jin ka wuce a wajen First Lady”. “Wannan kuma damuwarki ce. Na baki kwana bakwai ku koma Dubai da ita. Idan ba haka ba zan yi abinda naga dama. Sannan duk abinda na baki komin ƙankantarsa ne babu sai kin cika. One week”. Daga haka ya miƙe abinsa ya nufi ƙofar fita. Cikin rawar jiki Hajiya Hasiba ta yunƙuro zatai masa magana. Hannu ya ɗaga mata tare da watsa mata kallon daya sakata dakatawa da sauri. Sai da ya fice ta bugo musu ƙofar ta zabura gefe..... (Idan kwaɗayi.....🥱🏃🏼‍♀️) >>>>>>%<<<<<< A ɓangaren Daddy Imran da ƙarar Nimrah ta tayarma hankali tun yana kiran hello! Hello! Har ya haƙura ya yanke kiran. Vibration ɗin kiran daya sake yi da yanda Nabeeha da ke jin kanta na juyawa kamar zata sume a wajen ta nufo inda suke a matuƙar fusace jikinta har yana rawa ya dawo da Dada da Nimrah hayyacinsu. Hannu Nabeeha ta kawo a zafafe zata cakumi Nimrah. Amma sai aka riƙe hannun nata caraf a bazata. Ido cikin ido suka kalla juna ita da Dada. Da wani kalar kallon dake tabbatar da gargaɗinsa da barazanar da bata taɓa gani ba ya furta, “Kada ki taɓa koda mafarkin tsallaka wannan layin a karo na biyu. Dan tabbas bazaki ajiye ƙafarki kan ƙasa tana tare da gangar jikinki ba. Ni mai RIKICI ne akan wannan ANANAR. Ba lallai na iya kauda idanun TAƁATA ba koda akan kaina ne.” Sosai zuciyar Nabeeha ke bugawa da sauri-sauri a cikin ƙarjinta. Lips ɗinta na rawa ta buɗe zatai magana..... “Shiiii!!!” ya faɗa cikin ƙatseta yanama bakinsa alamar zipping da nuna mata hanyar ƙofar fita. Nabeeha dai tasan halin kayanta, ta kuma san mi zai iya. Ta kuma san fassarar gargaɗinsa da umarni musamman idan har ya buɗe baki yay magana akan abinda ke ransa. Ita ko tsuntsuwar tasa bama ta fahimci inda kalaman nasa suka dosa ba. Hasalima ba maida murtani ga Nabeeha datai niyya bane a wannan gaɓar damuwarta, kasancewarta akan cinyarsa ne tashin hankalin ta. Gashi ya riƙeta ta yanda ta gagara koda motsi. Sai da Nabeeha ta buga ƙofar da ƙarfi Nimrah ta zabura, tsalle ɗaya tai ta wantsalo ƙasan lallausan carpet ɗin wajen jikinta na tsuma, ga zuciyarta na wani kalar bugawa diff-diff-difff. Dada ma idanu ya runtse da ƙarfi, sai wani motsa yatsunsa yake kamar mai kiɗa akan hannun kujerar. Sai da ya tabbatar ya samu nutsuwar da yake buƙata sannan ya buɗe idanun tare da yin gyaran murya yana sake tsuke fuska tamau. Cikin dakewa a ainahin Dadan sa ya furta, “Naga hannun”. Nimrah dake jin kamar tayita kwarara ihu saboda kunya, har idanunta sunyi jawur ta ɗan kallesa. Sosai taji shakkarsa da kwarjinin sa na sake mamayeta. Dan duk da ba dariya yake mata ko surutu ba ƴar sakewar da yake da ita na sakata jin sauƙi. Amma yanda yay ɗin yanzu ita tasan wargi ma waje yaka samu. Sai da ya ƙarema yatsun kallo, ya kamo ƙafarta itama ya duba, duka farcinan sunyi ja daga na ƙafar harna hannun. Baiyi magana ba ya miƙe zuwa fright ɗin ɗakin, ice ya ciro babba ya dawo inda take ya zauna. Received at 12:22 PMIta dai binsa take da kallon mamaki, handkachiff ɗinsa dake ajiye a saman kujerar ya ɗauka ya saka ƙanƙarar a ciki. Kai tsaye ya kamo hannun nata ya ɗora a wajen data ƙone ɗin duk da baiyi alamar tashi ba. Tako sauke ajiyar zuciya da har sai da ya lumshe idanu ya buɗe. Sai da ya saka mata kusan na minti uku sannan ya miƙa mata alamar ta cigaba da sakawa. Shi kuma ya ɗauki wayarsa. Bata san waya kira ba, kawai jitai cikin umarni ya furta, “Turo min Ruƙayya”. Daga haka ya yanke kiran.........✍️ Hajja Ninah Ai wanda bai ji bari ba yaji hoi🥱🏃🏼‍♀️. Received at 12:22 PM [16/02, 10:58 pm] null: KIƊA A RUWA 3 14 ........Anan falo Ammar na ajiye wayar su Aunty Ummi suka shiga masa alamar yaya dai. Dariya yayi, dama kuma ita suke yi tun fitowar Nabeeha da gudu tana kuka da basu san abinda ya korota ba. Tun wucewar Nimrah sama Mammah ta bar falon. Hakan yasa Gwaggo Khadijah da Gwaggo Alawiyya binta, dan sun san dai bai wuce lamarin Nabeeha ne ke damunta ba duk da tana ƙoƙarin ganin ta danne. Amma dai abinda Nabeehan tayi yau rashin kunyar tayi yawa ai. Wucewar iyayen nasu ciki daɗi yay ma su Ja'afar, dan a take suka shiga amaye abinda ke bakinsu game da Nabeehan suma, kowa cin alwashi yake akan koyama Nimrah abubuwan da zata ƙona Nabeeha da ruwan jikinta. Sai kuma gata ta sakko a kiɗime harma tana kuka. Tsabar wulaƙanci sai suka fashe da dariya a tare har wasu na tafawa. Aiko kamar sun izata, sai ta ƙara gudu tana danne bakinta saboda tahowar wani sabon kuka mai ƙarfi. Suna cikin dariyar ne kiran Dada ya shiga wayar Ammar. Da sauri ya ce, “Kuyi shiru Dada ne”. Tsitt sukayi ya gama amsa wayar, shine yana yankewa suke tambayar mike faruwa. Abinda Dadan ya faɗa ya sanar musu. Biebah ta ƙwalama Ruky dake kitchen tare da Mu'azz wai suna ma Nimrah special girki kira. Amsawa tai tana fitowa. Saƙon Dada ta gaya mata, da yake bata san wainar da ake toyawa ba ta nufi saman cikin farin cikinta.. Rikicewa Ruky tai da ganin Nimrah kamar tayi kuka. Ta shiga tattaɓata tana tambayar mike damunta. Har sai da Dada daya shagala a kallon su yay gyaran murya. Cikin shagwaɓa Ruƙayya ta kalleshi, kamar zatai kuka ta ce, “Dada Aunty Nabeeha ce ta dake ta?”. Idanu ya waro waje dan mamaki. Wato dai halin iri ɗaya ne ita da aminiyar tata. Ji wani sharri kuma. Bashi da zaɓin daya wuce girgizama Ruƙayyan kansa, kafin cikin umarni ya ce, “Kamata kuje ta kwanta”. Kamata Ruky tai, har suka fita yana binsu da kallo, a ransa kam yana jinjina wannan ƙaunar juna. Bayan soyayyar jini, da soyayyar ma'aurata soyayya mafi muhimmanci da ban mamaki ga ƴaƴan adamu itace ta abokantaka da babu alaƙar jini a ciki, lallai duk abokan da sukai tarayya akan soyayya ta gaskiya zasu shiga aljanna suna masu farin ciki da juna. Idan riya ko cin dunduniya ta shigo sai su ƙare da zage-zage da aibanta juna a ranar rarrabe ayyuka. (Ya Rabbi kasa mu rayu da masoya na gaskiya, mu kuma kasance a aljanna tare muna masu farin ciki da juna. Duk wanda zai zo garemu da fuska biyu, ya rabbi kasa shartinsa ya zamewa rayuwarsa bargo akan kansa can ya ƙarata shi kaɗai🙏). Cahh iyayen nasu suka yo musu da tambayoyi a falo. Sai da Nimrah ta sanar musu abu ne ya faɗo mata a ƙafa sai kuma ta ƙone sannan suka nutsu. Amma da kowa ya hau da tunanin Nabeeha ce. Har sun fara ɗaukar alwashi a zukata. Dariya ce ta nema suɓuce ma Mammah dake ƙoƙarin fitowa. Ta girgiza kai tana gimtsewa. A ranta kam ta fahimci dole tai wani abu kafin waɗan nan iyayen banzar su ɗora Nimrah kan wani layin daban, a haka ma yaya lafiyar kura tunda itama ba ƙyalen bace ƙyallece ita da aminiyar tata Ruƙayya da basa ɓoyema juna sirri.... ^^^^^^^^^^^^^^ A ɓangaren Nabeeha kam yanda ta shigo sashen nata ya saka Amima da Rayhana dake cin abinci kallon juna. Sai kuma suka taɓe baki a tare. Amima ta ce, “Lafiya kuwa?”. “Ƙya tambayeni bayan muna tare”. Cewar Rayhana fuska a yamutse. Amimah ta ce “Hummm maybe korota sukai ko”. “Mtsowww matsalarta ce. Banda zubar da kai ka dawo miji baizo inda kake ba kai ka ɗauki ƙafa ka tafi nemansa. Itafa wannan da cikin aljihun baya aka haifeta muguwar kidahuma za'ayi. Bata gane komai sai son miji.” “Ikon ALLAH to miye dan taso mijinta Rayhana. Wani kike so taso to ne?”. Hararar Amima mai maganar Rayhana tayi, cike da takaici ta ce, “Kema fa wawuya ce wani lokacin. Inba hauka ba son miji ne kawai rayuwar aure?. Mijin ma irin Haysam daya san martabar kansa, wlhy sam bata dace da shi ba.” Received at 12:22 PM Galala Amima tai tana kallonta yanzu kam. Sai kuma tace, “Tofa wata sabuwa. Sai yanzu duk kika san wannan? Toke auren kikai da kika san mima mijin ke buƙata? Anya Rayhana babu wani abu a ranki?”. “Ubanki ne a raina. Shegiya munafuka”. Cike da son tura haushi Amima ta kwashe da dariya tana miƙewa da faɗin, “Oh to lallai abin ya girma. Ubana kam ai ubanki ne kema dole ya zauna miki a rai. Adai bi a hankali. Kar wajen tone-tone kaza ta tono wuƙar yankanta. Shi wannan NAMIJIN ZAKI ne ba Mazan club ba. Baya ɗaukar wargi balle shashanci. Itama data samu bata kasance ballagaza bane kuma tana cin darajar Abbanta. Amma kinga matsayarta, balle ke da aka saba leƙe-leƙ...” Jifan da Rayhana ta wurgo mata da saving spoon ya sata barin wajen da gudu tana dariyar iskanci data sake shaƙe wuyan Rayhana... •••••••••••••••••••• 9:pm na dare Dada daya fita a gidan shi da su Ma'aruff tun bayan sallar magriba suka dawo. Asibiti suka rakashi ya duba Lailah da Baby, daga can suka je duba Daddy Imran gida. Zuwa lokacin su Aunty Ummi duk sun wuce gida. Falon ma babu kowa alamar duk sun shige barci. Baiyi mamaki ba dan yasan masu ƙiriniyar gidan na fama da kansu. Mammah kuwa dama akwai barcin wuri. Su Bilal kuma office gobe. Har ya nufi upstairs sai kuma ya dawo da baya, ƙofar Mammah ya nufa, yay knocking a hankali. A mamakinsa sai yaji tana bada umarnin shigowa. Koda ya shigo a zaune ya sameta bakin gado tana duba wani littafin addu'oi. Ta ɗago tana kallonsa da amsa sallamarsa. Dai-dai yana kaiwa zaune take faɗin, “Ai har na fara tunanin kiran wayarka. Dan zaman jiranka nake daman”. Ƙaramin murmushi yay da faɗin, “To Mammah lafiya dai ko?”. “Lafiya lau. Yaya jikin Imran ɗin?”. “Alhamdullah ai ba a jigace yake ba. Kawai dai harda razani”. “Alhamdullah ALLAH ya kiyaye gaba. In sha ALLAHU zan je na duba shi gobe nima.” “ALLAH ya kaimu”. “Amin ya rabbi. Shaiɗancin mutanen nan ya fara bani tsoro Muhammad. Tunda har tunaninsu ya fara basu yin amfani da makusantanka domin samun biyan buƙatarsu. Abin akwai haɗari sosai a ciki, idan na farko an tsallake rijiya da baya nan gaba kuma fa?”. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke, dan shi da farko ma yayi tunanin maganar Nabeeha zatai masa. “Kar ki damu Mammah in sha ALLAHU hakan bazai sake faruwa ba. Wannan ma da suka aikata zasu biya bashinsa harda riba da hannayensu. Akwai shirin da nake yi musamman akan su ƙananun nan. A cigaba da mana addu'a dai. Dan in sha ALLAHU nasara ce ke tunkaro mu. Ko ba komai abinda sukayi yanzu ɗin ya ƙara buɗe min tunani na akan sanin su waye su.” “Addu'a har mu koma ga UBANGIJI bazamu daina yi muku ita ba, ALLAH ya cigaba da baku kariya. Ya ɗora nasararku akan maƙiyanku. Suma ALLAH ya shirye su su gane gaskiya kafin lokaci ya ƙure musu idan masu shiryuwa ne.” “Hummm Mammah kenan, to Amin. Amma waɗan nan mutanen basa buƙatar shiriya.” “A'a ba'a yankema UBANGIJI hukunci akan ikonsa ai.” “Haka ne kam, ALLAH yasa mu dace. Ranar asabar iyayen Haydar zasu zo a tsaida magana. Kuma ina son ne kawai a saka rana batare da wani jeka ka dawo ba. Lahadi mu kuma sai muyi batun Bilal da Asma'u. Sai dai shima Ammar kawai zan haɗa da shi”. Murmushin Mammah ya faɗaɗa sosai. Ta ce, “Alhamdullahi ALLAH yasa ayi damu. Ya kuma sanya albarka a ciki. Amma Auta yana da budurwa kuwa?”. Yanzu kam sai da Dada ya ɗan murmusa. Kai tsaye ya ce, “Zan bashi Ruƙayyana in sha ALLAHU”. Wani irin farin ciki ne ya daki zuciyar Mammah. Har bama tasan ta zabura ta kamo hannun Dada ba. Ta ce, “Muhammad da gaske? Aiko idan kayi haka ka gama min komai. Wannan tunanin ya daɗe a raina. Tsoron halin ɗan yau yasa na shanye abina. Ya rabbi yanda ka bani wannan farin ciki a wannan dare kaima ALLAH ya faranta maka har ƙarshen numfashinka”. Received at 12:22 PM “Amin Mammah, tare dake da zuri'armu”. Sosai take farin ciki, dan har sai da tai sujidar shukur. Bayan ta ɗago ne take masa maganar shima lokaci yayi da Nimrah zata san wanene shi a gareta. Dan ɗazun Imran ya kirata sun tattauna sosai. Shiru Dada yay baice komai ba, itama bata damu da shirun nasa ba ta cigaba da faɗin, “Tunda har sun gaya mata yin shirun mu zai sakata a wasi-wasi. Amma idan mun sanar da ita zata kasance a nutsuwa koda zata shiga ruɗani. Nimrah yarinya ce mai wayo, suna da iliminsu da fahimtar abubuwa gwargwadon iko, idan bamuyi saurin yin hakan ba a yanzu suke tasowa samari na kawo musu caffa, idan sun tsallake tarkon wani bazasu tsallake na wani ba dan zuciya ba'ai mata shamaki ƙo ƙa'idar wanda zata iya so. Makarantar ma idan zata zama damuwa kawai su zana ssce wannan shekarar, maybe idan suka ga kansu a jami'a a samu sauƙin wannan ƙiriniyar tasu”............✍️ Hhuummmm! Received at 12:22 PM [16/02, 10:59 pm] null: KIƊA A RUWA 3 15 .........Ya gamsu da shawarar Mammah kam. Dan haka yace, “Hakan yayi sosai. In sha ALLAHU zan duba naga yiwuwar komai Mammah.” “To ALLAH yay muku albarka. Ka sanar ma Jamilu ne?”. “Eh, in sha ALLAHU. Yace ma yana tafe ranar juma'a. Sai dai Uncle Naseer zuwa gobe in sha ALLAHU zanje shima muyi maganar. Sai waɗan nan yaran, su basa komai ne a gidansu suka zo nan suka tare?”. Ta san su Hanoon yake magana. Dan haka tai murmurshi. “To ban sani ba Muhammad. Amma dai nayi waya da Tasi'un ya tabbatar min sati mai zuwa shima zai dawo ƙasar. Amma ina son ka zauna dasu ko sau ɗaya ne ka tsawatar musu akan wasu ɗabi'u nasu marasa ƙyau kodan a taimaki rayuwarsu.” “Hummm Mammah, nifa akan abinda na isa kawai nake tsawa. Ki bar masa ƴaƴansa a yanda kika gansu yazo ya kwashe abinsa. Ai ya fiki sanin ba'a dai-dai suke ba. Amma ya zaɓi barinsu a haka. Yanzu dai kwanta ki huta. Nima zanje barci nake ji sosai.” Sarai ta fahimci dan ya kaucewa maganar ne kawai. Dan haka ta ɗan murmusa tana girgiza kanta. Har yay mata sallama ya fice tana binsa da kallo.... Koda ya maida ƙofar ya rufe dole ya ciro wayarsa ya kunna fitila dan an kashe hasken falon gaba ɗaya. Takunsa bai wuce biyar ba yaja ya tsaya gab da fara hawa staircase saboda kamar nishin kuka yake ji. Duk da anayi ne ciki-ciki ƙarfin ji da ALLAH ya bashi ya saka shi ji, ga kuma darene ko ina yay tsitt. Juyawa yay saitin inda yake jiyo sautin. Tabbas a kitchen ne, dan haka ya zubama ƙofar shiga idanunsa tsahon sakanni. Kafin ya ɗaga ƙafafunsa ya nufi wajen cike da takunsa na jarumta da lafiyar jiki irin ta baraden maza masu tsayin gaɓɓai. Hasken wayar ya ɗan rufe da hannu, kafin ya tura ƙofar kitchen ɗin.... Yanda ya shigo a bazata, tare da haska kitchen ɗin da fitilar wayarsa a lokaci ɗaya ya saka Nimrah zabura. Dan zaune take a ƙasa cikin ɗan lungun jikin cabinet, ta saka kanta a tsakiyar ƙafafunta. Fitilar kitchen ɗin ya kunna, ganin wanene ya shigo ya sata miƙewa tsaye gaba ɗaya jikinta na tsuma. Dada kam idanu ya zuba mata kawai yana kallonta daga sama har ƙasa. Kayan barci ne wando da riga masu taushi a jikinsa. Wandon har ƙasa, sai rigar mai gajeren hannu iya gwiwa. Kanta da hula, sannan ƙafarta da bedroom slippers masu taushi. Tunda tai masa kallo ɗaya ta duƙar da kai bata sake ɗagowa ba. Tana ta dai cuɗa hannun nata cikin juna yanda aka saba.... “Ki dafa lemon tea ki kawo min”. Ya faɗa kawai yana juyawa abinsa ya fita. Sharr hawaye suka sake zubo mata. Takai hannu ta share tana jan hanci. Batare da tace komai ba ta nufi inda tea pot ɗinsu suke ta ɗauka ɗaya ƙarama. Fanfo taje ta ɗauraye sannan ta saka ruwa dai-dai misali ta nufi gas. Ta ajiye tukunyar tana sake share hawayen da suka ƙi tsaya mata da shashshekar kuka. Abubuwane sun mata yawa a cikin ƙirji, musamman wanda ta gano a wajen mutanen can da wanda aka sanar mata game da zuri'arta da shi kansa Dadan da ƴan uwanta data gani jininta a karo na farko a rayuwarta, bayan labarin mahaifiyarta data rasu babu labarin wanda ta taɓa sani a danginta sai yanzu. Addu'ar da take ta ambato ce kawai ke saka mata nutsuwa da babu abinda zai hanata haukacewa a wannan gaɓar. Lemon tsamin data ɗauka babbar guda biyu ta wanke, tare da ganyen na'a-na'a da lemon grass ta koma wajen tukunyar ta zuba. Lemon tsamin kuma ta yanka ɗaya a ciki, ɗaya a cikin flaks data ɗakko shima.... Dada da yay ɗan jimm a bakin ƙofar kitchen ɗin yana kallo tamkar yana hangota jin ta fara kai-kawon aikin daya sakata, amma tana cigaba da shashshekar kuka sai ya furzar da iskar bakinsa kaɗan yana barin wajen. Sama ya haura abinsa. Sai dai bai wuce ɗaki ba sai da ya leƙa ɗakin su Mu'azz dana su Bilal ya tabbatar sun kwanta, sai Afeef ne ma ke latse-latsen waya, yana jin kuma za'a buɗe ƙofar ya kifeta shima yaja bargo yay likimo. Dan ya tabbatar Dada ɗin ne saboda duk dare haka yake musu.. Received at 12:22 PM Ɗakin sa ya wuce. Bayan ya zube wayoyinsa a saman mirror ya shiga kunce agogon hannunsa. Dai-dai nan Nimrah tai knocking. “Shigo”. Ya faɗa a taƙaice. Koda ta turo ƙofar ta shigo da sallama ƙasan maƙoshi saboda muryarta ta ma dishe, bai juyo ya kalleta ba amma ya amsa a lips. Hanyar bayi ya nufa yana rage botiran shirt ɗinsa da faɗin, “Ki jira ni anan” daga haka ya shige ya barta da bugun zuciya da kallon ƙofar bayin. Bata da zaɓin daya wuce bin umarninsa. Dan haka takai zaune a ƙasan carpet tana ɗan wasa da lallausan gashin jikinsa. Sai dai lokaci-lokaci tana share hawayen dake ciko mata idanu amma taƙi bari su zubo... Ya ɗan jima kafin ya fito, sai dai kayan barci ne yanzu a jikinsa saɓanin kayan daya shiga da su. Tunda tai masa kallo ɗaya ta maida kanta ta duƙar. Shi kam baima kalla inda taken ba kai tsaye gaban mirror ya nufa yana ƙara tsane gashin fuskarsa da ƙaramin towel. Ya ɗan ja mintuna a wajen, dan sai da ya saka turare a jikinsa ya kammala uzirinsa kafin ya nufi gado abinsa. Ɗago kai Nimrah tai a karo na biyu tana kallonsa, a tunaninta koya manta da ita ne, ganin ya hau gadon sosai ya zauna, sai dai ya jingina bayansa da fuskarsa yaja bargo ya rufama ƙafafunsa zuwa ƙungunsa, ya kuma kashe hasken fitilar ɗakin gaba ɗaya sai lamp itama ta side ɗin da yake zaune kawai. “Bani”. Ya faɗa a taƙaice yana buɗe laptop daya ɗora saman cinyarsa bayan yasa ƙaramin filo. Shiru Nimrah bata motsa ba, dan batama fahimci da ita yake ba. Sai da ya ɗago ya kalla inda take, tare da faɗin, “Wai bada Nimrah nake ba”. Ƙirjinta taji ya buga, dan bayan a jeji data gudu sanda bomb zai tashi bata taɓa jin ya kira sunanta ba. Miƙewa tai gaba ɗaya ta ɗauki tray ɗin data saka ƙaramin flaks da tea cups guda biyu, sai tea spoons suma biyu da zuma cikin ɗan wani gora mai ƙyau alamar a haka aka sayeshi. A ƙasan carpet ɗin gaban gadon ta ajiye, daga tsugunne ta haɗa masa komai. Saman bed side drawer tai nufin ajiyewa sai ya miƙa mata hannu batare daya bar abinda yake a laptop ba. Hannun ta kalla, sannan ta ɗan kalla fuskarsa dake ciɗin-ciɗin kamar koyau she. Dole ta matsa sosai inda yake sannan ta miƙa masa. Maimakon amsa da ɗan plate ɗin da kofin ke a kai sai kawai ya kama hannun cup ɗin, ita kuma da ba haka tai zato ba sai taji kamar ya tafi zai ɓare ne, caraf ta kama hannunsa cikin nata hannun. Idanunsa dake kan screen ɗin yaɗan lumshe tare da buɗewa a lokaci guda kan hannayen nasu. Da sauri ta janye nata tsigar jikinta na tashi batare data san dalili ba. Shima sai bai ce komai ba, ya dai kalleta shaaa ya ɗauke idanunsa. Daga haka ya fara shan shayin yana aikinsa. Ganin lokaci na ƙara jaa yaƙi cewa kuma ta tafi cikin rawar murya ta ce, “Dada na tafi?”. Shiru bashi da niyyar amsata, bai kuma daina aikinsa ba balle shan shayinsa da yake matuƙar jin daɗinsa. Sai yaji tama fi Ammar iya dafawa. Dan kullum shi yake sakawa ya dafa masa. Ammar daya fahimta ma ko bai buƙata ba sai ya dafa ya kawo ya ajiye a ɗakin in ma baya gidan. Yau ma gaba ɗaya ya shafa'a ne saboda kasancewar su Aunty Mimi a gidan. “Tashi ki dawo sama”. Furucin yazo mata a bazata daga bakin wanda bazata iyama jayayya ba. Gadon ta kalla sannan ta kallesa, ganin har yanzu hankalinsa akan aikinsa yake sai taji kamar ta saki kukan da take ta faman dannewa. Bata da zaɓin daya wuce bin umarninsa, dan haka ta miƙe kanta a ƙasa ta ɗofanu acan ƙarshen ƙafafunsa dake cikin bargo. Sai da taja kusan mintina biyu kafin ya ɗago ya kalleta, kallo irin na tsaiii ɗin nan akan mutum dake sakashi yaji rikicewa, sai dai babu damar yin motsi balle yin magana dan anfi ƙarfinka. “Mike damun ki?”. Ya faɗa kai tsaye idanun nasa dai a kanta ƙyam. Jitai ta sake daburcewa, dan ta tabbatar dai amsar yake buƙata daga gareta kuma dole ta bashi. Cikin rawar lips da in-inar da yanzu tazo mata ta buɗe bakin zata fara magana... Received at 12:22 PM “Kar kimin ƙarya”. Ya katse hanzarinta cikin gizago. Sai kawai taji hawaye sun ciko mata idanu. Lips ɗinta sai rawa suke kuma. Idanunta ta ɗan ɗago kaɗan da nufin satar kallonsa sai taga nashi har yanzu ƙyam a kanta. Da gudu ta risinar da nata. Sai ga hawaye sharrr da take faman riƙewa sun ɓalle. Fuskarsa ya kauda gefe yana furzar da iska. Sai kuma ya janye laptop ɗin gefe, tare da ajiye kofin shayin da har ya shanye a bed side drawer ya miƙa mata hannu. “Zo nan”. Kamar dama abinda take jira kenan ta miƙe, gabansa tazo zata durƙusa daga ƙasa ya hana hakan ta hanyar riƙo hannun nata. A bakin gadon ya zaunar da ita tana facing ɗinsa, har jikinta na gogar nashi duk da shi a rufe yake da bargo. Dan haka ta ƙara duƙar da kai sosai..........✍️ Received at 12:22 PM Viewed 2 times [16/02, 10:59 pm] null: KIƊA A RUWA 3 16 ..........“Yaushe kika zama sha-sha-sha ne da komai kuka-kuka?”. Yanda yay maganar can ƙasan maƙoshi, da sigar lallashi yana ɗan matsa hannunta dake cikin nashi har yanzu ya sata ɗan jin sassauci. Cikin muryarta dake a ɗashe ta ce, “Dada ina son na Mutu ne?”. Idanu ya zuba mata sosai, sai kuma ya ɗan motsa lips kaɗan ya ce, “Mutuwa? To idan kika mutu wazai haifa ƴaƴan soja Kiddo?”. Da sauri ta ɗago tana kallonsa, duk da bawani ta gane zancen nasa ina ya dosa bane ba. Kai ya ɗan jinjina mata alamar tabbatarwa. Ita kuma sai kawai ta tura baki tana janye idanunta daga cikin nashi. Mitsitsin murmurshin da bai shirya bane ya kufce masa. Sai dai bai bari ta gani ba ya gimtse abinsa. Gyaran murya ya ɗanyi, hakan ya sata sake ɗagowa, sai dai bata yarda sun haɗa idanu ba. Cikin son kamata a wuya ya canja salon sigar tambayar tasa. Dan ya fahimci ɗaya daga halayenta shine kafiya, dagiya akan abu. Idan ba ita taso ba akwai taurin kai. Sannan ya fahimci depression ne ke neman kamata. “Miyasa kika daina raba damuwarki da ƴar uwarki, aminiyarki? Bayan kuma sanda na dawo ba haka naga kuna yi ba. Kin fara ɓoye mata abubuwa ne?”. Kanta ta girgiza masa da sauri. “Magana nake so da baki”. “Bana ɓoye mata komai. Kawai dai yau ne naji ina son na dawo kitchen ɗin nayi kukan”. “Ko kuma kiyi mutuwar da kike so ba”. Shiru tai dan bata da abin faɗa. Kamar ma ya shiga ya karanta abinda ke zuciyarta ne. Shima fahimtar hakan ya sashi cigaba da faɗin, “Shike nan tunda baƙya son Ruƙayya tasan damuwarki itama ta damu. Ni kiyi abota da ni mana. Kinga tunda na riga na ganoki sai mu dinga tattauna matsalar a tare ko? Hakan bazai sa Ruƙayya taji ba balle hankalinta ya tashi kamar yanda baƙya so”. “Ai Mammah tace babu ƙyau abota tsakanin namiji da mace”. (Wata sabuwa) Ya faɗa a zuciya. A zahiri kam sai ya ce, “Haka ne gaskiya Mammah ta faɗa. To amma ai ni ne, Mammah bazata hana ba. Bakiga itama da ni take shawara ba. Amma tunda baƙya sona da abokin ai shike nan. Zan nema Ruƙayya mu ƙulla, kar kuma kiga mun ware ki kiji haushi. Dan zanyi duk yanda zan yi na ƙwace miki ƙawa”. Baki ta tura gaba tana kumbura kumatu. Ta ce, “Na yarda to”. Dariya ta kama shi, ya dai gimtse da ƙyar. Sai kuma ya miƙa mata ƙaramin yatsarsa alamar su ƙulla to. Yatsar ta kalla tsawon sakanni, kafin ta ɗago nata hannun slowly ta miƙa masa itama nata ƙaramin yatsan ya sarƙe waje guda. “Shi ke nan daga yau mu abokai ne ba?”. Kanta ta jinjina masa. Shima ya jinjina nasa yana faɗin, “Good. Ƙara zuba min shayin, sai kizo ki bani labarin miya saka ki kuka yau?”. Shayin ta sake zuba masa kamar yanda ya buƙata. Sai dai bata dawo saman gadon ba tai zamanta a ƙasa. Shima baiyi magana ba ya ɗauki laptop ɗinsa ya cigaba da aikinsa. Hammar data saki a karo na uku ya sashi kallonta. Sai da ya sha shayi daya kai baki ya ajiye kofin sannan yay magana. “Kinga barci yazo ma. Tashi na rakaki ki kwanta da safe ƙya bani labarin, maybe ma lokacin kin huce sosai daga fushin ko?”. Kanta ta jinjina masa nan ma, harta yunƙura zata tashi ya dakatar da ita. Cikin tsaurin murya ya furta, “Daga yau karna sake ganinki kina kuka a ko inama ba kitchen ba da daddare. Idan mutum yana cikin damuwa ba kuka bane mafita ko hana kai barci ko son a mutu ne hanyar yayewar damuwa ba. Alkur'ani ake ɗauka a karanta. Ko ai alwala ay salla a nema ɗaukin UBANGIJI. Dan shi mai Rahama ne da jin ƙai ga bayinsa masu dogaro da shi. Ko aita ma ANNABI salati ko istigifari”. Kanta ta jinjina. Tana mai cuɗa yatsunta waje guda ta ce, “In sha ALLAHU bazan sake ba Dada. Zan dinga yin kuma yanda kace”. “Good Negar. Idan kikai hakan zanyi alfahari da ke. ALLAH yay miki albarka”. “Amin”. Ta faɗa a hankali tana satar kallonsa. Ganin ita yake kallo shima sai tai saurin janye wa. Guntun murmushi yayi yana sakkowa a gadon. Dan haka tabar wajen da sauri tana ɗaukar tray ɗin kayan shayinsa. Received at 12:22 PM Viewed “Bar wannan”. Ya faɗa yana wuceta. Maidawa tai ta ajiye tabi bayansa. A haka suka fito a ɗakin tana biye da shi har suka sauka ƙasa. A bakin ƙofarsu yaja ya tsaya, sum-sum kanta a ƙasa ta ce, “Dada sai da safe nagode”. “Uhmmm”. Ya faɗa a maƙoshi kawai yana binta da kallo harta shige. Ta turo ƙofar zata rufe suka haɗa ido. Da sauri ta ƙarasa rufewa tana jingina a jiki tare da runtse idanun tana sauke numfashi. Sai kuma ta zabura tana leƙensa ta jikin Door peephole na ƙofar. Yana tsaye har lokacin shima ya zubama ƙofar idanu da wani kalar kallo data kasa bama suna. Kusan mintuna biyu kafin taga ya furzar da iska yana barin wajen. Itama iskar ta furzar tana sauke ajiyar zuciya. Kafin ta bar wajen zuwa gaban gadon Ruky ta gyara ma bargo daya zazzame a jikinta. Sannan ta nufi bayi yin alwalar barci...... Jin hawowar Dada staircase ɗin ya saka Afeef komawa da sauri cikin ɗakinsu yana danne baki da hannu. Kafin ya tsaida video ɗin da yake recording a wayarsa. Daga waje shima Dada tsai yay yana kallon ƙofar, sai kuma ya wuce abinsa ɗaki batare daya ce komai ba. Hummm Afeef video kuma🤔? _____ Yau da wuri ya shigo gidan. Dan gaba ɗaya baida nutsuwa. Ganin har dare yayi hakan na nufin kwanaki biyu suka rage masa da wannan daren game da umarnin ƴan jam'iyya. Zuwa yanzu ya yanke ma kansa hukuncin da zai fishshe shi ya kuma taimaki ƴan ƙasa da wani abun koda ba komai da komai ba. Dan itace kawai mafitar data rage masa. Yayi alƙawari ma UBANGIJI da talakawan ƙasa da sukai faɗi tashi akan zaɓensa da tunanin ya cancanta wajen kamanta musu abinda ya dace matsayin shugaba. Idan kuma har ya miƙa wuya ga wancan layin ya tabbatar waccan burin nasa da alƙawarin zai tashi a banza ne. Dan shi bai ci ba, ƴan ƙasar basu ci ba, tabbas wasu zasu ci da saka hannunsa. Kuma dole ya amsa tambayoyi akan hakan ranar sakamakon rarrabe ayyukan bayi. ALLAH ne mai kare bawa akan komai. Amma yana buƙatar wani jajirtaccen mutum kusa da shi da zai dinga rarrabe masa gaskiya da saɓaninta tako wace fuskar data dace. Babu kuma wanda zai iya yin hakan sai mutum ɗaya tak. Mutum ɗayan da ya yarda da shi ɗari bisa ɗari a wannan duniyar. Sai dai fidda sunansa akan muƙamin da yake kallo wani sabon kalubale ne da dole sai ya jure, dan hatta ga shi mai sunan zai iya fuskantar tirjiya kodan sanin da yay masa akan ƙyamatar al'amarin mulki da siyasar ƙasar a bayyane. Dan hakama ya yanke bazai sanar ma kowa ba sai bayan ya ƙaddamar ya kuma zartar. Da wannan tunanin ya saki murmurshi, tare da ɗaukar wayarsa yay kiran ogansa na siyasa. Bayan sunyi gaisuwa cikin mutunta juna kamar yanda suka saba. Kai tsaye ya furta, “Sir na amince da buƙatun jam'iyya, sai dai da sharaɗi guda ɗaya tak nima daga gare ni”. Murmushi Oga yayi daga can, duk da yasan dama dole ne Janar ya amince ko yaƙi ko yaso. Kamar yanda ya saba cikin kwantar da kai ya ce, “Ina jinka General, kuma ni mai baka goyon bayane akan duk buƙatunka. Musamman a wannan gaɓar da ka faranta min ka saki wannan jayayyar da zata kawo ma kowa masalaha da kwanciyar hankali musamman ni da kuka saka a ysakkiya.” Murmushin takaici shima Janar yayi, kafin ya gyara zama da faɗin, “Ta ɓangarena Chef of staff zai fito”. Ɗifff numfashin Oga ya ɗauke kamar an daki kansa da guduma. Fin mintuna biyu kafin ya ja iska mai nauyi ya fesar. Bisa ga abinda zuciyarsa ta ayyana masa kawai ya ce, “Shike nan yanda kake so haka za'ayi, zan zauna da su, kuma nasan zasu amsa. Sai dai kayi ƙoƙari kaima ka cika musu alƙawarin su duka”. “Oga! Ni indai akai min hakan na amince da komai game da muƙaman da wanda ma suke buƙatar a baiwa. Daga yau kuma yanzu nan ma chapter closed kawai”. “Shike nan ka saurare ni, zuwa safiya in sha ALLAHU zaka ji dukkan bayani”. Received at 12:22 PM “ALLAH ya kaimu Oga na gode sosai a gaida iyali, mu kwana lafiya”. “Zasu ji. Amin”. Kai Janar ya jinjina kamar yana a gabansa shima yay murmushi yana ajiye wayar. Jinsa yake sakayau kamar an sauke masa kaya bisa kai. Sai ma ya miƙe ya shiga bayi dan watsa ruwa a jikinsa. Amma murmushi ya kasa barin fuskarsa saboda hango ƙurar da zai tayar a wannan satin cikin ƙasar dan tako wane fanni bai hango sauƙin al'amarin ba, dole ai kare jini biri jini tsakanin maƙiyan ɓoye dana zahiri.........✍️ Received at 12:22 PM Viewed 2 times [16/02, 10:59 pm] null: KIƊA A RUWA 3 17 ........Anan Gidan Mammah kam Nimrah ta tashi da ɗan dama-dama. Kasancewar ba makaranta suka koma ba suna gama aikin da duk suka san sunayi suka sake komawa barci. Sai wajen ƙarfe goma Mammah tasa Biebah tashinsu suyi kalaci. Dada baya gidan, dan daga sallar asuba bai dawo ba. A waya ma ya kira Mammah suka gaisa babu jimawa, ya sanar mata yaje wani waje ne amma zai dawo nan kusa. Duk wani motsin Nimrah Mammah na hankalce da shi, ta kuma fahimci a sanyaye take tun jiya. Sannan bata yawan magana. Ganin yanda take kafe mazan gidan da idanu ɗaya bayan ɗaya a kaikaice yasa Mammah fahimtar batun auren da mutanen suka sanar mata ke damunta. Sannan tana son fahimtar waye mijin. Mammah tai ɗan ajiyar zuciya tana ɗauke kanta. Sauran kuwa fahimtarsu daban data Mammah. Dan sunfi jingina batun kidnapping ɗin da akai mata ne da yanayin nata na shiru-shiru yau. Balle rashin lafiyar Imran ta basu tabbacin sai da akai gumurzu wajen samota, dan haka suka maida hankalinsu akan janta da labaran da zata saki jikinta. Alhamdullahi hakan kuma da suke yayi tasiri. Musamman da taji batun zuwa asibiti duba Lailah da babyn ta. Dama suna fitowa saida ta dangana da sashen Shariffa ta gano Nasir, yana mura ne ba'a son fitowa da shi shiyyasa ta haƙura ta barshi ta dawo. Umarnin da Mammah ta bata na zuwa ta gyara ɗakin Dadan ya sakata miƙewa, dan a yanzu babu abinda tafi son buƙatar kusanci da shi kamar ɗakin Dada, ta fahimci dukkan abubuwan da take nema suna a ɗakin. Sai da taje ta tattara kayan sharar da duk abinda take buƙata sannan ta tafi. Bayi ta fara shiga domin gyarawa, sai ta samu underwers ɗinsa ajiye alamar zai wanke. Kunya taji ta kamata. Ta duƙar da kai kusan na mintuna uku tana shawarar ta wanke kota barsu a inda ta gani? Wankewar dai akwai ɗunbin kunya a ciki gaskiya, sannan idan ta bari ma tayi gyaran bayin dole zai san ta gani, idan ta tsallake bayin bata gyara ba bata ƙyauta ba, tunda daga shi har Mammah data sakata babu abin rainawarta a ciki. Da ƙyar ta iya danne zuciyarta ta ɗibesu idanunta a rufe ta zuba cikin worshing machine, ta haɗa ruwan sabulu a ciki ta kunna. Gyaran bayin ta fara, sai da ta kammala tsaf ta dawo wajen worshing machine ɗin daya kashe kansa tun ɗazun ta fara cirosu. Nan ma idanu ta rufe sannan take matsesu ta sake canja ruwa. Sai da ta tabbatar sun mata yanda take so ta ɗauraye ta zuba a dryer ta busar. Sannan ta kwaso su ta fito. A kujera ta ajiye su ta fara gyaran ɗakin shima. Tayi har mopping ta saka turaren SHUWA INCENSE AND MORE +234 704 229 3387. Har zata tattare kayan sharar sai idanunta suka sauka akan underwers ɗin data wanke. Da kunya ta barsu a wajen yana shigowa ya gani, sai kawai taje ta kwashe ta nufi wadrobe da su dan gyara takai can ta ajiye salin alin. Sai da ta babbuɗe harta gano inda ake ajiyesu sannan tai ƙoƙarin ajiyesu gefe domin fara shiryasu a wajen. Babbar brown envelope dake wajen data ɗorasu ta faɗo, take hotuna dake ciki suka watse a ƙasa. Binsu tai da kallo, sai kuma ta kai duƙe da sauri ganin fuskar Dagger, ba fuskar tasa ce ta ɗauki hankalinta kawai ba ganin wanda suke tare, drivern su ne Malam Buba. Gabanta ya faɗi, tuna itace sanadin haɗa Dagger da malam Buba, ta kuma tabbatar ita Dagger ɗin yazo nema. Sauri-sauri ta kwashe hotunan duka tana kallo. Guda uku duk mutumin ne, ɗaya zai buɗe mota data kasance ta gidan ce ya waigo alamar tabbatar da babu mai kwallon sa, sai kuma dai-dai ya fito daga motar dai, wanda ya fara gani suna cikin motar ne ta gaba aka ɗauka kuma tabbas basu san anyi ba. Sauran hotunan bata gane komai ba, dan wasu mitanene daban. Bata da zaɓin daya wuce kwashe hotunan Malam Buba da mutum nan da ko sunansa bata sani ba. Dan inta bari Dada ya gani komai na shirinta zai rushe. Gaba ɗaya ta miƙe tana ware iya nasu, sai dai cikin rashin sa'a ta ɗaga rigar jikinta zata saka cikin skirt aka buɗe ƙofar a bazata. Ba ƙaramin daburcewa tayi ba, musamman ganin mai shigowar. Shima da bai san da ita a ciki ba sai yay ɗan tsaii yana kallonta, dan kai tsaye ya gane a firgice take. Received at 12:22 PM reacted with ❤Waccan ranar da taga file ɗin nan ne yazo masa a rai. Ya sauke idanunsa ƙasa da take ƙoƙarin cusa abu a jiki. Farin abu ya gani, sai dai bai san minene ba, dan itama da sauri ta saki rigar ganin inda yake kallo. Nimrah da illahirin jikinta ke tsuma ta aro jarumtar dole ta yafama kanta tana haɗiye yawu masu ƙauri. Cikin gyara yanayin ta ƙwarai da gaske ta ce, “Dada sannu da zuwa. Ina kwana?”. Bata jira amsarsa ba ta juya tana fara ɗaukar underwers ɗin nan..... Dai-dai lokacin ya ƙaraso wajen, ya tsaya a bayanta gab har tanaji hucinsa. Idanu ta runtse tana karanto addu'ar duk da tazo mata a zuciya. Sai kawai ta fara cusa kayan inda ba'a nan ya dace ba. Hannunta ya riƙo, hakan ya sakata ƙara rumtse ido da cije lips da masifar ƙarfi, ta kuma runtse vest ɗinsa dake a hannunta daya riƙo da nashi. “Mi kike yi anan?”. Wani busashshen yawu ta haɗiye da ƙyar, har tana jin kamar yana yanka mata maƙoshi. Da ƙyar ta iya fisgo kalaman bashi amsa da. “Ina gyara kayan wanki n...ne”. Kayan hannunta ya kalla na sakanni, sai kuma ya ɗan ja baya daga jikinta. Har tana murnar ta tsira murnar ta koma ciki. Dan kuwa kafaɗunta ya dafa ya juyo da ita suna facing juna. Cikin golden voice ɗinsa dake fita da tsantsar gizago da zurfin iko ya ce, “Buɗe idanun ki”. Jitai idanun ma sun cika da hawaye kafin ta buɗe. Tadai yi jarumtar haɗiyesu tana sake kame kanta. Koda ta buɗe ta kasa kallonsa gaba ɗaya, sai dai shi tana jin kaifin nashi har a cikin magudanar jininta. Bata san mi yake kallo ba a jikinta, gashi yaƙi yay magana. Ta takura matuƙa saboda kwarjininsa da yanda ya cika mata waje. Jinta take kamar a gaɓar ramin gacci mai matuƙar zurfi, gabanta kuma zaki dake a yunwace ya zuba mata idanu... “Kayi haƙuri Dada”. Kalmomin uku suka suɓuto daga cikin bakinta batare data shirya ba. “Ba sai anyi laifi ake bada haƙuri ba?”. Idanunta da suka cika da ƙwalla ta ɗago ta kallesa. Zata maida ta risinar ya dakatar da ita cikin umarni. “Idan suka zubo sai kin kwashesu kin maida.” Mar-mar ta shiga yi da idanun tana maida hawayen kuwa. Dai-dai yana kai hannu ya ɗaga t-shirt ɗin jikinta baƙa. Dan skirt ne light brown da bai kai mata har ƙasa ba, sai da ya wuce gwiwa sosai, sai baƙar t-shirt ta mata da hoton katon teddy bear a gaban. Sosai kayan sun mata ɗas. Hannu takai da sauri zata hana shi. Ya wani ɗago birkitattun idanunsa da suka sake juyewa saboda halin da yake ciki ya watsa mata. Tare da faɗin, “Zan karya hannun nan”. Ai da sauri ta janye hannun nata, shi kuma ya ƙarasa ɗage rigar ya jawo hotunan data saƙe a cikin skirt. Maimakon sakin rigar sai ya tsaya yana kallon wani tawwadan ALLAH dake gefen cikin nata babba sosai. Itama jin shiru ta buɗe idanunta, motsin da tai ya saka shi farga shima, sai kawai ya sake rigar yana ƙara tsuke fuska. Hotunan ya fara kallo, guda uku ne, ya zubama fuskar Dagger ido sosai cike da nazari, dan akwai handkachiff a fuskar tashi, ita kanta tsantsar basirar da ALLAH ya bata ne yasa a gani ɗaya ta gane shi. Duk da dai a na cikin mota babu handkachiff ɗin, amma kuma bai fita ba kamar na wajen. Shima ana cikin motar kai tsaye ya gane shi, hakama Malam Buba. Ɗagowa yay yana kallon fuskarta. “A ina kika gani?”. Ai ko musu batai ba ta nuna masa envelope ɗin data danne da ƙafafu. Hannu kawai ya miƙa mata. Dole takai duƙe ta ɗakko ta miƙa masa. Ya kalla fuskarta sannan ya buɗe envelope ɗin ya ciro sauran hotunan. Mutane ne mabanbanta har guda shida, yanayin inda aka ɗauka hotunan yay mugun jan hankalinsa. Cikin envelope ɗin ya sake maida hannunsa, sai dai babu komai kuma... “Waya baki?”. “Dada wlhy anan na gani”. Tai maganar tana nuna inda ta ɗauka. Jimm yay na tunani. Tuna da kansa ya ajiyesu jiya ya sashi ɗan furzar da iska. Sai kuma cikin sauke murya ya furta, “Little Shadow kina da hannun ɓarna. Bincike ko?”. Received at 12:22 PM Viewed 5 times “ALLAH ba bincike nayi ba Dada. Kawai zan saka kayan nan ne na gani.....” “Shine kika buɗe tunda kin raina Dada”. Idanu ta waro sosai da jin furicinsa na ƙarshe tana girgiza kainta. “Wlhy Dada ban raina ka ba, na tuba bazan sake ba”. Yanda tai maganar hawaye na zubowa ga kunnuwa ta kama ya sashi tsayawa yana kallonta kawai. Dan sai kawai tai masa ƙyau a hakan, har wani babban al'amari na tsarga masa. Dole ya kauda idanun nasa da sauri yana haɗiye yawu. Sai kuma ya bar wajen da sassarfa yana faɗin, “ALLAH ya shirya min ke. Shige ki tafi”. Ai kafin ma ya rufe baki ta kusa ƙofa, shima sai kawai ya kai zaune yana sake kallon hotunan. A ƙasan zuciyarsa kuwa tunanin yake waye yayo masa wannan aiken?. Hannu yakai ya riƙe goshinsa, sai kuma ya miƙe tsaye ya fara kai-kawo. Dole yana buƙatar zuwa UNIT ZERO yanzu nan. Hotunan ya maida cikin envelope ɗin, a ya da ya shigo a haka ya sake fita..........✍️ Received at 12:22 PM Viewed [16/02, 10:59 pm] null: KIƊA A RUWA 3 18 ........Lokacin da Dada ke fitowa babu wanda bai bishi da kallo ba a falon. Dan shi bai kalli kowa ba a cikinsu ya fice. Dama sun zagaye Nimrah ne da tambayar miya faru da ita. Dan yanda ya fito ba'a nutsuwarta ba. Duk da tana ta yaƙin danne kanta kuwa. Sai kuma ga Dada ya fito shima ba'a yanda ya shiga ba. Ko kallonsu baiyi ba kuma ya fice. Ta tabbatar musu babu komai, badan sun yarda ba suka ƙyaleta saboda Mammah data girgiza musu kai alamar su barta. Sam Nimrah bata cikin nutsuwarta, burinta ta kira Dagger yanzun nan a waya. Sannan tayi magana da Malam Buba. Amma ta rasa ta yanda zata bar falon ma balle yin hakan.... >>>>>★<<<<< Gudu sosai Dada ke zubawa a titi dan shi ke driving ɗin da kansa. Kusan lokaci guda suka isa da Imran. Kowa na kammala parking ko gaisawa basuyi ba suka nufi hanyar shiga ciki. Daddy Imran ya saka Password ɗin ƙofar, bayan ta gama turance-turancenta daya sakasu matsuwa ta buɗe. Ko zama basu gama yi ba Dada ya miƙama Imran envelope ɗin. Shima da sauri-sauri ya fiddo hotunan ciki yana kallo ɗaya bayan ɗaya. Sai da ya kai har ƙarshe kafin ya ɗago yana kallon Dadan. “Tabbas drivers ɗin da suka wuce da kayan can ne. Domin kuwa motocin ne, sannan jejin ne. Waye da wannan aikin?”. “Wannan shine tambayata Imran.” “Shi kuma wannan waye? Nagansa tare da Buba driver?”. Maimakon amsawa miƙewa kawai Dada yayi zuwa ɗakin sirri. Dole Imran ya miƙe yabi bayansa. Anan ma sai da suka saka Password. Suna shiga Imran ya danna wani abu a jikin ƙofar bayan ta rufe, a take haske ya gauraye ko ina. Lallai wannan ɗaki ya tsaru, dole kuma a kira shi da ɗakin sirri. Wani ƙaton bakin allo dake liƙe da hotuna Dada ya nufa, kai tsaye ya ciro wani hoto a layi na biyu ya miƙama Imran. Sosai Imran ya zubama hoton ido, sai kuma ya kalla Dada. Da ido yay masa nuni da waɗan can hotunan. Baiyi magana ba shima ya sake fiddosu. Cikin sa'a kuwa na cikin mota da fuskar Dagger ke buɗe ne farko. Imran ya kalla hoton ya kalla wanda Dada ya bashi sai kawai ya zaro idanun cikin razani. “What?! Criminal 0079?!. Kenan da gaske binciken Dabo ya tabbata fitar da su akai basu mutu a haɗarin jirgin ba. Ya ARRAHAMAN. Abin mamaki!. To amma miya haɗa shi da malam Buba kuma?”. “Shi ne ɗan leƙen asirinsa. Sannan Nimrah ta san su”. “Nimrah?! How?”. “Wannan shine tambayata nima? Yarinyar nan ta fara rikita min lissafina Imran. Dan Driver ɗin nan yana ɓoye ainahin fuskarsa ne, tun a ran farko dana fara ganinsa na fahimci hakan. Aikina ne kawai bai biyo takansa ba shiyyasa ban damu da shi ba. Amma ya zama dole yanzu nayi hakan”. Rasa ma abin cewa Imran yayi, dan shi zuciyarsa ma bugawa take da ƙarfi. Ta ina Nimrah zata san Dagger to?..... “Ina buƙatar su Faro yanzun nan. Dan daga nan zuwa 24h nake son information akan waɗan nan drivers ɗin”. Kai kawai Imran ya jinjina masa yana ciro wayarsa ya fita. Dan anan ɗakin kira baya shiga kai tsaye sai idan sune suka buƙaci hakan... Zama Dada yay yana furzar da huci. Nimrah ce kawai ke dawo masa a zuciya da yanayinta na daren jiya da na yanzu, dan ɗazun ya danne kansa ne kawai kada ya rikitata. Yana buƙatar shan coffee ko nutsuwarsa zata dai-daita. Dan haka ya miƙe zuwa inda coffee maker take... +++++++++++++ “Kulu ina abincin su maigadi?”. Kallonta Kulu dake ɗauke da babbar kular abincin gidan zata kai dinning tayi. Sai kuma ta nuna kular abincin su maigadin da Hinde ke zubawa. “Gashi nan Hinde na zubawa.” “Okay bani nakai musu”. Ba Kulu kawai ba, hatta Hinde sai da ta juyo ta kalli Nimrah. Duk da sun san hakan ba wani abu bane sunyi mamaki. Nimrah da taga sun zuba mata ido ta ce, “Akwai matsala ne?”. Da sauri suka shiga girgiza kawuna. Kulu tai ƴar dariya da faɗin, “A'a kawai dai yau naga Ninah abin arzuƙa take ji a gidan namu”. Received at 12:31 PM Ƙaramar dariya Nimrah tayi tana nufar Hinde. Ta ce, “Kulu dama nasan kin saka min ido ai. Kawai so nake na ɗan miƙe ƙafafu, bana son fita hakan nan kuma Mammah tai magana”. Sun gamsu da bayanin nata, dan haka Hinde na kammala zuba abincin ta tura mata kular. “Bari to na ɗauka miki plates ɗin ko?”. “A'a barsu zan dawo na ɗauka”. Cewar Nimrah tana ɗaukar abincin ta fita. Da lafiya lafiya ne zatace ya mata nauyi. Duk da kular ba irin ƙatuwar nan bace ba kuwa. Addu'a take ALLAH yasa ta samu baba driver harta ƙaraso. Aiko ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ganinsa zaune shi kaɗai a kujera yana latsa waya. Daga can gefe maigadi na alwala. Sai Sanda na barci a barandar ɗakinsu ya juya baya. Kai tsaye wajen Malam Buba ta nufa. Duk da yanda take jin bugun zuciyarta na ƙaruwa, hakan ya zame mata jiki a duk lokacin data kusanceshi. Tunma yana damunta har ya daina. Ƙasa takai duƙe tana ajiye kular da gaishe shi. Idanunsa a kanta ya amsa, itama sai ta ɗan ɗago ta kalleshi. Cikin raɗa ta furta, “Baba mutumin kwanaki yazo nemana da bana nan ko?”. Sosai gaban Malam Buba ya faɗi, a ransa yace (A ina tasan hakan?) a zahiri kuwa sai ya fara inda-inda. “Baba ka faɗa min dan akwai matsala ne. Wani munafiki ya ɗauki hotonka kai da shi kuna a mota ya kawo ma Dada......” Kaɗan ya rage zuciyar Malam Buba ya fito ta baki. Ba arziƙi yaji fitsari na neman zubo masa. Ita kanta Nimrah taga firgitarsa a zahiri. Amma sai fahimtarta tasha banban da halin da yake ciki. Ta cigaba da faɗin, “Wlhy kuwa Baba nima hankalina ya tashi. Shiyyasa tun ɗazun nake son fitowa na amshi wayar Sanda na kira shi.” Ai malam Buba bai ma san ya furta, “I...ina da lambarshi U...u..w...a. amshi maza kirashi. Idan kuma ni na kira shi to”. “Baba ka tabbatar wadda zaka sameshi ce yanzu?”.. “In sha ALLAHU”. “To Baba dan ALLAH kayi da sauri kawai ka kirashi kai. Dan Dada ya fita da hotunan, kuma ban san mi zaiyi akai ba”. Kansa ya jinjina mata yana haɗiye yawun dake neman sarƙe masa numfashi. Ita kuma tabar wajen... ★Nimran na shigowa falon Abees daya fito a bedroom ɗin Mammah ya tareta da faɗin, “Aunty Mammah tace kizo”. Kanta ta jinjina masa, sai kuma ta ce, “Muje to”. “Aunty zanje wajen Mamy ne, ta aikoni na kawoma Mammah abu”. Anan ma kan nata kawai ta jinjina masa. Ya wuce ita kuma ta shige bedroom ɗin Mammah. Afeef dake zaune a falon yana binta da kallon harara ya taɓe baki. Sai kuma ya saki murmurshi a fili ya furta, “Shegiya ƴar iska. Na kusa maganin ki ai. Sai na tona muku asiri a gidan nan. Dama na faɗa miki, idan na tashi ramawa sai na miki mai zafin da har ki mutu bazaki manta da ni ba.” Daga haka ya miƙe ya haura staircase. Nimrah kam ta samu Mammah na waya. Dan haka ta nema waje ta zauna tana jiranta. Sai da ta kammala sannan ta sake miƙewa ta koma kusa da Mammah ɗin. Mammah ta riƙota tana kwantar da kanta a kafaɗarta. Sai da ta shafa fuskarta cikin damuwa ta ce, “Autana duk kin rame min a ido. Inaga ɗurar abinci zan fara miki gaskiya”. Murmurshi Nimrah tayi, ta kama hannun Mammah ta sumbata. Cikin shagwaɓa ta ce, “Mammah idan kikai min ɗura zan zama ƙatuwa ALLAH. Ni kuma bama son ƙiba no da Buddy.” “Uhm-uhm yaran zamani sai a barku. Yanzu miye abin gudu a ƙiba kuma?”. “Mammah ALLAH ƙiba ciwo ce. Mutanenmu ne kawai ke ganin sai kayi ƙiba wai kake jin daɗin rayuwa. Amma ƙiba ai ba abin so bace.” Mammah tai dariya kawai da sake shafa kumatunta. Sai kuma cikin kulawa da iya sarrafa zuciyar yaro ta ce, “Tun juya nake son mu zauna ki bani labari, amma iyayenki sun zagayeki. Bani labarin miya faru da kika fita ranar?”. Daga Ruƙayya har Nimrah basu san ɓoyema Mammah damuwa ko magana ba. Ko Dagger yaci galaba a kan Nimrah ne saboda barazanar kashe Ruƙayya da yay mata. A yanzu ma akwai dalilan da bazata iya sanarma Mammah komai da komai ba. Amma akwai abinda bazata iya ɓoye mata ba. Sannan tana son sanin wanene akai mata aure da shi, idan taji a bakin Mammah kuma zatafi gane abinda ake nufi. Received at 12:31 PMDan haka ta gyara zama ta fara bama Mammah labari tiryan-tiryan. Har batun fashewar bomb bata ɓoye komai ba. Tadai yanke labarin daga inda su Leo suka fiddata a gidan da aka fara kaita, duk abinda ya faru a gaba bata faɗa ba. Ta share hawayen da suka zubo mata, cikin rawar murya ta ce, “Mammah sunce an min aure, kuma assignment ne naje na bincika waye mijin da kaina.” Sosai ƙirjin Mammah ke duka, amma sai ta danne tana murmurshi da kamo Nimrah ta sake rungumewa a jikinta tana share mata hawaye. “To shine kuma abin kuka Autar Mammanta. Ai aure alkairi ne, sannan Rahama ne. Ɗan gata kuma akemawa da ƙarancin shekaru. Ke da Ruƙayya kuma ƴan gatan Mammah da iyayenku ne. Tabbas basuyi ƙarya ba ke matar aure ce. Kuma kina da shekara bakwai aka ɗaura......” “Mammah saboda mi?”. “Saboda ke ƴar gata ce Nimrah. Duk da dai akwai ainahin abinda ya faru a lokacin, amma bazan faɗa miki ba sai kin ƙara girma”. “Mammah waye mijin?”........✍️ Received at 12:31 PM 2 people reacted [16/02, 10:59 pm] null: KIƊA A RUWA 3 19 ........Sosai Mammah tai murmurshi mai yalwa da hango ƙuruciyar Nimrah a fili. Sai kuma ta shafa kanta. “Miyasa kike son ji tun yanzu? Kiyi haƙuri zaki sanshi. In sha ALLAHU kuma zakiyi farin ciki.” Kai Nimrah ta jinjina kawai tana sauke ajiyar zuciya. Sai dai taso tasan wanene mijin, amma bazata iya jayayya da Mammah ba. Zata cigaba da haƙuri, da juriya har lokacin da Mammah tace ɗin yayi. Mammah data fahimci halin da take ciki, sai ta ƙara gyara zama ta shiga lallashinta da nasiha mai tsada da daraja. Ta yanda a hankali komai ke shigar Nimrah tamkar ruwan allura a jijiyoyin jiki. Daga ƙarshe Mammah ta fara bata labarin tarihin rayuwarta. Ai gaba ɗaya sai Nimrah ta shagala, sai dai daga lokacin da tazo gaɓar rasuwar Baba Abdul-rasheed da ciwon Mama Yakura zuwa rasuwarta duk Nimrah ta rikice da kukan tashin hankali, ita kanta Mammah hawaye take, tama kasa ci-gaba. Sai da sukai kuka sosai sannan Mammah ta ƙarasa mata har ƙarshe lokacin da suka dawo garin nan da zama. Nimrah ta share hawaye, idanunta jajur ta furta, “Mammah kun sha wahala ke da Dada. Amma miyasa tun sanda aka rufeshi na farko baki hanashi aikin soja ba?”. Fuskar Mammah da murmushi ta shafa kan Nimrah. “Nimrah kowanne bawa da irin ƙaddararsa, kowa kuma da irin rayuwar da UBANGIJI ya tsara masa. Dadan ku na son aikin soja, kuma na gamsu da jajircewarsa akan ƴan uwansa marasa ƙarfi irinmu da yake ƙoƙarin bama kariya. Hanashi ba itace masalaha ba addu'a ce komai”. “Hakane Mammah. Nima yau naji ina son nayi aikin soja”. Yanzu kam sosai Mammah tai dariya da faɗin, “Soja fa Auta?”. “Eh Mammah, ina son na zama kamar Dada da Daddy”. “To bazance a'a ba, muyi addu'a ALLAH ya zaɓa mana abinda yafi alkairi”. “In sha ALLAHU zanyi. Amma Mammah a ina shi ƙauyukan Bankaura ɗin da akaima kisan gilla ɗin suke? Ina son zuwa garin”. Yanzu kam shiru Mammah tai tana kallonta. Ta bata labarin komai daya shafi su da al'amarin Muhammad, har abinda ya faru a ƙyauyukan Bankaura daya zama sanadin rufe Dada na shekaru 8. Amma bata gaya mata komai daya shafeta ba balle tasan ita ƴar wannan yanki ce, tayi hakan ne kuma dan tafi son Muhammad ya sanar mata komai da kansa..... “Kinji Mammah”. Nimrah ta katse mata tunani. Ajiyar zuciya Mammah ta sauke. Cikin jinjina mata kai ta ce, “Saboda mi kike son zuwa?”. Nimrah tai murmushi tana haɗiye abinda ke ranta. Cikin nuna rashin damuwa ta ce, “Mammah haka nan kawai. Dan wani ma tunani nake yi...” “Na mi?”. “Zan fara rubutu a kansu. Mammah bayan aikin soja yanzu na ƙara jin ina son zama MARUBUCIYA”....... ××××××××××× “Wlhy Daddy da gaske nake maka. Har video ma na musu jiya. Ai tun randa ya shiga ɗakinsu da daddare na fara saka musu ido. Sai naga ita ɗayar bata shiga ɗakinsa da daddare kamar yanda wannan shegiyar keyi. Aiko jiya dubunsu ta cika......” “Kaga katse kiran nan ka tura min video ɗin”. Babu musu Afeef ya katse kiran, yana wata ƴar dariyar ƙeta ya tura videon da jiya yay ma Dada da Nimrah batare da sun sani ba. Sai da ya kammala ya juyo yana kallon Hanoon datai tagumi... “Afeef wai baka jin tsoro, mutum nan daga ganinsa wlhy ba imani zai yi ba. Itafa shaidar zina ance sai ka gani da idonka...” “Ke ai dama wawuya ce, dan kina son shi shiyyasa ma kike kamar baki yarda da abinda na nuna miki ba. To kar ki yarda ɗin, ni ina ruwana da wani a addini sai an gani da ido. Sannan da kike wani magana baida imani ya kashe ni mana. Kuma ai itace taja masa, dama na rantse sai na mata abinda bazata taɓa mantawa dani ba.....” “To amma tunda itace ta maka laifin ka rama a kanta mana ba shi ba. Sannan kai ne wawa, kuma ina ji maka tsoron Daddy ya fitar da maganar nan ta dawo cikin gidan nan kaine zaka sha wahala”. Tana gama faɗa ta fice a ɗakin. Da kallo ya bita zuciyarsa na wani irin zafi. Sai kuma yay ƙwafa.... Received at 12:31 P ★A ɓangaren Uncle Tasi'u yana kallon video yana faman jinjina kai da sakin murmushi. Jinsa yake rai fess. Dan kuwa ya samu makamin da zai sami abinda yake so gun Adda A'isha. Duk da wani gefen zuciyarsa na gargaɗinsa akan halin Haysam. Amma wadda ke zugashi na dannewa. Fitowa yay daga cikin videon, kai tsaye ya sayi ticket ta online, dan dole ne ya je ƙasar haihuwarsa. Zuwa na bazata a yau ɗin nan. Daɗi sosai yaji na samu jirgi mai tashi nan da awanni goma. Dan haka babu ɓata lokaci ya hau shiri...... >>>>>>>%<<<<<< Washe gari safiyar juma'a aka sallamo Lailah mai jego, duk da jiya su Nimrah tun yamma har dare suna asibitin tuni suka rikice da farin ciki. Dan sun tattare inasu-inasu sun koma sashen su Lailah gaba ɗaya. Tunda dai jarirai sun zama biyu sai aka raba rigima kowa ya ɗauki ɗaya. Sosai farin cikin kasancewa da babys ya kwashe rabin hankalinsu acan. Sai dai wani kaso na tunanin Nimrah nakan Dada ne. Dan tun fitar jiya da yayi bayan ya amshi hotuna a hannunta har yanzu bai dawo gidan ba. Ga Baba Driver ma tun jiyan bata sake ganinsa ba. Abin ya dameta ƙwarai da gaske, batare da ita kanta tasan dalilin yin hakan ba. Bayan sallar la'asar sai ga Mu'azz ya shigo, dawowarsa kenan daga makaranta. Bai ko shiga sashen Mammah ba yayo nan shima. Suna cikin caftarsu Aunty Shariffa na rabon faɗan akai baƙi ƴan barka. Dole suka fito dan basu waje kasancewar suna da yawa. Mu'azz ne ya takali Ruky sabuwar rigima, hakan yasa ta bishi da gudu. Nimrah uwar zuga ta bisu tana faɗin, “Yauwa Buddy na kada ki raga masa”. Tana maganar ne tana dariya har suka shigo falon. Da yake suna gabanta sun rigata. Ta shigo ta samesu tsaye cak, sai kuma muryar Mammah dake magana kamar cikin ɓacin rai ta daki kunnenta. Itama tsayawa tai dan in kaji Mammah na faɗa an kaita bango ne. “Nace Tasi'u mi kake nufi?!”. Furucin Mammah ya sake dukan kunnuwansu. Sai lokacin Nimrah ta fahimci ashe baƙo sukayi a gidan. Ba kuma kowa bane face Uncle ɗin nan da yazo kwanaki kuma Baban su Finga-fiyau kamar yanda Mammah ta sanar musu. Yana zaune a kujera gabansa da abinci da aka jera a Center table. Sai Mammah da itama ke zaunen tana facing ɗinsa. Da waya a hannunta fuskarta kuwa yanayi ne da zasu rantse basu taɓa gani ba... Gwaggo Khadijah da Gwaggo Alawiyya da suka fito suma saboda tsawar Mammah suka ƙarasa inda suke. Gwaggo Khadijah ta zaune tana riƙo hannun Mammah da faɗin, “Ayi haƙuri Maman Ma'aruff. Mike faruwa ne?”. Maimakon Mammah ta bata amsa sai Uncle Tasi'u ne ya amsa mata cikin ɓacin rai. “Yaya ki barta, na rasa miyasa Adda bata son gaskiya akan yaranta, dan fa kawai nace mata gyara kayanka, shine zai zama sauke mu raba......” “Karka kawo min zancen banza zancen wofi Tasi'u”. Mammah ta katse shi a tsawace fiye da tsawar ɗazun da sai da ta saka su Nimrah zabura. Cikin nuna shi da yatsa tare da wurga masa wayarsa dake hannunta ta cigaba da faɗin, “Mika sani akan yarana da har zaka yanke musu hukunci? Dama ka kawo min yaranka gidana dan su dinga saka maka ido akan al'amarin mu.....” Gwaggo Khadijah da hankalinta ya ƙara tashi ta riƙo Mammah. “A'isha dan ALLAH ya isa haka. Ya kuke abu kamar wasu ƙananun yara, wai mike faruwa ne? Ku fiddani a duhu....” Kuka sosai Mammah ta fashe da shi, ta nuna wayar Uncle Tasi'u dake yashe a ƙasa. “Yaya Khadijah na gaji da halin Tasi'u wlhy, ki faɗa masa in dai ba alkairi ya dawo dashi cikin rayuwata da zuri'ata ba dan ALLAH ya tattara yaransa su koma. Wai ki duba video cikin yaran nan wani ya ɗauka na Muhammad da Nimrah, shine yazo yana zancen banza akan hakan. Wai Muhammad na neman Nimrah...” babu wanda bai razana ba a falon, Mammah ta cigaba da faɗin, “To bari kaji kai da masu ɗaukar Videon ko zaku dawo cikin hankalinku. Nimrah MATAR Muhammad ce. An ɗaura musu AURE tun tana da shekara bakwai. Sai ka sake wani shirin”. Received at 12:31 PM reacted with ❤ Wani irin duka kan Nimrah yayi tamkar an saki irin tsawar nan mai girgiza gari a cikin tsakiyar ruwan da ke sauka da manya-manyan ƙanƙara. Kalaman Mammah suka wani irin sake maimaita kansu a cikin illahirin duk wata ƙofa dake amsa suna ƙofa a cikin jikinta. (Nimrah MATAR Muhammad ce. An ɗaura musu AURE tun tana da shekara bakwai). Ai sai kawai tayi luuuuu zata zube. Da wani irin ihu su Ruƙayya da sukai sumar tsaye dan suma kalmar ta dake su da girgiza su suka zabure kanta. Sai kuma suka tsaya cakk sakamakon ganin Dada da babu wanda zaice ga sanda ya shigo falon, da ga gefensa Daddy Imran ne. Nimrah da ta tafi zata zube ya tare da jikinsa. Yana tsaye ne ƙyam akan ƙafafunsa, hannunsa ɗaya tallefe da bayanta saboda tareta da yayi, ɗayan na cikin aljihu. Sai dai idanunsa da sukai masifar juyewa da wani irin hargitsatstsen yanayi tsaye suke ƙyam akan Uncle Tasi'u da shima ya juyo wajen kamar su Mammah saboda ihun Mu'azz da Ruƙayya... Tuni Hanoon da Afeef da Dayyan dake laɓe sun fito suma. Ganin Dada da basuyi zato ba tunda sun san tun jiya baya gidan tuni ya firgitasu. Dan Afeef ya jiƙe sharaf da zufa ga icayi na neman kufce mas a wando.........✍️ Afeef tsuntsun da yaja ruwa ba shi ruwa ke doka ba🤣. Ka ragema su Mammah aiki 🥱🚶👌..........A hankali Daddy Imran da shima ke kallon Uncle Tasi'u cike da ɗunbin mamaki dan duk abinda Mammah ta faɗa a kunensu ne. Shigowar su Nimrah babu jimawa suka shigo. Hakan ta faru ne kuma saboda su ta gaba suka shigo, su Nimrah kuwa daga sashen su Ma'aruff ta kofar baya suka shigo. Dan haka basu san da zuwansu gidan ba. Idanun nasa da shima suka kaɗe ya janye daga kan Uncle Tasi'u ya maida kan Dada. Yasan waye Zakinsa, dan haka ya ɗan sauke numfashi da kai hannu ya akan kafaɗarsa ya ɗan bubbuga alamar lallashi. A hankali kuwa Dada ya juyo ya zuba masa idanun nasa, sai kuma ya lumshe su ya sake buɗewa. Batare da yace ma kowa uffan ba dai-dai Uncle Tasi'u da jikinsa ke rawa na zaburowa da nufin zuwa inda yake lips ɗinsa na motsi alamar magana zai masa kawai Dada ya ɗaga Nimrah dake a sume cak yau wucewarsa. Ai ba Mammah data san halin kayanta ba hatta su Gwaggo Khadijah sai da suka ɗan waro idanu waje. Dan asalin manna wulaƙanci gangariya da babu gauraye Dadan yay ma Uncle Tasi'un. Imran ya duƙar da kai yana danne murmushin dake neman suɓuce masa da ƙyar. Sai kuma ya ɗan sake ɗagowa ya kalla Dadan dake haura staircase da wani irin salon ainahin jarumai. Sai ka rantse ba mutum ya ɗauka ba, dan babu alamar yana jin nauyinta duk da tana a sume ne.... Da wani irin sauri itama Nabeeha ta dafe kanta dake sara mata, sai kuma tai ƙoƙarin riƙo Ruky dake kusa da ita. Da sauri Ruƙayya ta juyo, hakama kowa na falon da sai yanzu suma suka farga da ita. Ashe itama komai a kunnen nata ya faru, dan su Amima na balcony na sashenta motar su Dada ta shigo, shine Rayhana ta kirata a waya ta sanar mata. Sai ko gata ta fito da hanzari, sanda take fitowa su kuma har sun kusa sashen Mammah. Sun shigo kenan itama ta afko amma taja ta tsaya ganin abinda ke faruwa alamar babu lafiya saboda ganin Mammah na kuka. Sai kuma ga bayani taji kamar yanda kowa ya ji. Zuciyarta na neman tarwatsewa duk da tasan wannan amma sai taji kamar ita Mammah ke ma bitar tunatarwar mijin Haysam mijin Ninrah ne ƴar cikinta da da'ace tana zuwa gidan ta samu ciki zata haifi kamar Mu'azz ne. Dai-dai ta ɗago zata kalla Dada dake gabanta kaɗan kawai taga ya matsa da wani irin zafin nama ya taro wadda keta gabansa kaɗan Da sai da ta faɗa jikinsa sannan taga fuskar Nimrah. Sai kawai taji numfashinta ya ɗauke komai ya tsaya mata cak, shine bata dawo a hayyacinta ba sai yanzu, duk da yanzun ma a wani yanayi ne saboda ganin abinda Dadan ya aikata kuma ko'a jikinsa ya ɗauki ƴar yarinya a hannu a gaban kowa ya haura sama inda kowa yasan ɗakinsa zai kaita..... ___ A dai-dai kuma wannan lokacin cikin hikimar UBANGIJI wani al'amari mai girgiza ƙasar da al'ummar cikinta, dama ɓoyayyun munafukai yay amsa kuwwa. Domin kuwa bayani ne mai girma, mai tsauri, daban al'ajabi ya fita daga fadar shubagaban ƙasa akan sunayen waɗanda aka bama muƙamai masu daraja da kima da zasuyi aiki a wannan gwamnatin tasa. Akwai manyan ministoci guda takwas da sunansu ya fara fita, sai babban sakatare. Sai NATIONAL SECURITY ADVISOR (NSA) . da CHEF OF STAFF. Ba muƙaman ne suka girgiza ƙasar ba, sunayen mutanen da aka bama muƙaman biyun ƙarshe ne. Mr. Haysam Abdul-rasheed Shehu Kobi is appointed as the (Chief of Staff to the President). & Mr. Imran Abbas is appointed as the National Security Advisor (NSA). Gan-gan-gan-gan. Wannan fa shine ainahin tashin bomb mai kai goma sha biyu. Shugaban ƙasa kuma na kammala bada umarnin sanarwar dan tun jiya ya rattaɓa hannu a gidansa yau ya ƙaddamar a yanzu kuma ƙarfe huɗu na yamma. Yana badawa kuma yay shigewarsa gida. Gashi yau juma'a ce, za'a shiga hutun weekend. Wannan fa shine (Tarwatsa wara wari jikan Tafida!, rai ya daɗe rai yayi ma alfarma. Kaga mazan aiki sun zo. Ya cika sittin mai ban mamaki🔥....) Aba Nasiru Sarkin waƙa shawara ya yoma shugaban ƙasa Yusuf Shu'aibu Tafida irin wannan waƙar sak ta sarkin Kano shima. (Kai ku bamu kiɗan janaral a sama. Masu gudu su gudu, sai Baba Tafida, sai Baba Tafida. Bana dai janar shine a sama... Amma a KIDA A RUWA..... Masu gudu su gudu. Received at 12:31 PMKu faɗama shaggun can su ware💃💃🥱😂🤣). Tabbas Janar ma KIDA A RUWA ne MAI TADA HANKALIN DODONNI Jama'a to ALLAH ya taroni🥺, sanyi fa ya kankama sai kun haɗa da haƙuri magana ta ALLAH. Yo irin wannan waƙoƙi haka kamar babana ne Janar ɗin🥱😎🥶🧑‍🦯. ••••••••••••••••• “Amma kai Mole wawa ne, jaki ma dabbul arab. Shine sai yanzu kake gaya min?”. Wani irin tafasa zuciyar Malam Buba ta shiga yi a cikin ƙirjinsa. Ya kalla Dagger da idanunsa da suka kaɗe jazur saboda yanda kalamansa sukai masa zafi matuƙa. Amma sai ya danne a kan harshe ya furta. “Oga ya kake so nayi?. Tun jiya da Uwa ta faɗa min fa na baro gidan nake nemanka. Yanzu haka kalla jakkata anan na gama yanke binka sansani idan har ban sameka na ƙarshen nan ba. Sai kuma nayi sa'a kaga saƙona kazo.” Gaba ɗaya Dagger ji yake kamar kansa zai tarwatse dan tashin hankali. Ya dunƙule hannu da masifar ƙarfi ya daki bangon ɗakin Malam Buba yana wani irin ƙaraji daya saka Malam Buba zaro idanu yana kallon ƙofa. Duk da saida ya rufe windows da ƙofar tunda Dagger ya shigo yana tsoron wani yaji ihunsa a gida... “Oga kayi a hankali mana kada wani yaji. A ganina ba rikita kai bane mafita. Tunanin abinda ya dace. Kasan dai tunda Uwa tace taga hoton nan mutumin nan bazai ƙyale mu ba. Dole zai fara bincike akanmu......” “Shiyyasa nace kai wawa ne Mole. Idan kai jaki ne shi ba irinka bane ai. A zatonka zai mance da fuskata ne har ya zauna wani bincike a kaina? Kaima badan wannan gemu da sajen ɓadda kamar daka sanya ba da wannan fentin da kake ma kanka an gaya maka bazai gane ka ba ne tun a ranar farko? Ko a yanzu na fara tantamar guy ɗin nan bai gane ka ba, ya barka ne kawai a cikin takunsa.” Tsuttt fitsarin tashin hankali ya zubo jikin Mole. Jikinsa na karkarwa ya ce, “Amma Oga miyyasa baka taɓa faɗa min haka ba?”. Wata muguwar Harara Dagger ya zuba masa kawai, batare da yace komai ba ya hankaɗesa ya buɗe ƙofar ɗakin ya fice abinsa. Ai gaba ɗaya sai Mole ya sake jin gudawa ma na neman zubo masa ba fitsari ba. Tuni ya zabura ya ɗauki jakarsa da dama ya haɗa komai nashi yabi bayan Dagger. Yana fitowa ya samu har ya shiga mota. Ai shima sai kawai ya buɗe ya shige wufff kusa da shi. Ko kallonsa Dagger baiyi ba ya tada motar yabar ƙofar gidan a guje..... <<<<<<%>>>>>> “Tabbas Oga magana ta tabbata. Nimrah matarsa ce. Dan yanzun nan Mammah ta faɗa da bakinta a gabanmu. Sakamakon cikin baƙin yaran nan sun naɗi video sun turama babansu cewar Dada na nema Nimrah. Shi ne shi kuma ya ɗakko ƙafa ya taho, yanzu dai haka shi ya ɗauketa yayi ɗakinsa da ita. Nan kuma falon ya birkice ga matarsa nan uwargidansa ta yanke jiki ta faɗi tana abu kamar mai farfaɗiya ƙannenta sun ɗauketa zuwa sashen ta”. “Hummm kice anzo dai-dai inda nake so?”. “Anzo kuwa ƙwarai da gaske Sir!”. “ALLAH yay miki albarka, sai ki kasance cikin shiri dan aiki ki gab yake da fa ƙarewa. Lokacin bayyanata yayi.” “In sha ALLAHU Sir”. Ta faɗa cikin ƙamewa da salute ɗinsa tamkar tana a gabansa ne. Shima daga can sai ya saki murmurshi da jinjina mata kansa tamkar yana a gaban nata ya ce, “Proud of you dear”. “Thank you Sir! Proud of you too.” Murmurshi kawai yay mata da har taji fitar sautinsa a cikin kunneta, daga haka ya yanke wayar, itama sai ta ajiye tana sauke ajiyar zuciya. Sai dai kuma cak numfashinta ya ɗauke sakamakon fitowar ƴar uwarta daga bayi da bata san da ita ba. Yanda take kallonta cikin ido ya sakata fahimtar duk taji wayar tata. A rikice ta zabura kanta, sai dai da sauri ta ɗaga mata hannu alamar karma tazo gareta. Dole ta tsaya cak suna kallon juna tamkar tsaiwar zakaru...........✍️ Tooooo barkanmu da juma'a. 🥱Dada ya shige da ƴar mutane marainiyar ALLAH ɗaki. Ga shugaban ƙasa yayi bombing zukatan munafukai🔥😉🤏. Ga Dagger da Mole a kwale-kwale😂🥱. Ga Nabeeha uwargida mai capacity na farfaɗiya🥺🤕. Ga Uncle Tasi'u da ƴaƴansa a lukutar masifa😱. Ga ƴar leƙen asirin mai aiki a ƙaulani🥺🥶. Kai wannan sati yazo da alheri🤭. ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels WhatsApp Number: 09017242889 Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ **************************